duk ni na tura aka ɗauke don na ƙara tunzura ki." A ruɗe na ce. "Ke ce? Kika saka na ƙala wa bawan Allah bai ji ba bai gani ba, amma gaskiya ke ba ƙaramar shu'uma ba ce, haɗuwa ta da ke ba alkhairi ba ne, kin zalunce ni, kin saka na rabu da mijina mai so na da kyautata mini, na rabu da ƴaƴana, na yi bankwana da farinciki, na yi biyu babu, har wani auren na ƙara amma shi ma ban dace ba, wahala kawai na sha na fito, ina zaman zaman kin saka ni aure har biyu." Na ƙarashe maganar cikin jin tarin haushin ta da tsanar ta, yadda na ɗauki matar nan, na ba ta gaskiya da amana, na yarda da ita, ko a mafarki ban taɓa tunanin za ta yi mini haka ba. Ashe da gaske mutum yana nuna yana son ka a zahiri a cikin zuciyarsa kuma ƙiyayya ce? Tabbas dole a ce da masoyi maƙiyi, gara wanda zai bayyana maka ƙiyayyar shi a fili ka san irin zaman da za ka yi da shi. Babu abin da ya fi tayar mini da hankali sama da cewar da ta yi tana son Anas, don ta aure shi tai ta zuga ni na rabu da shi. Sai yanzu na tabbatar da ni wawiya ' mara wayo da hankalin da Naja take faɗa ce. Me ya hau kaina a lokacin na kasa gane gaskiya? Me ya rufe mini ido na faɗa duhu alhalin ga haske nan ƙuru-ƙuru ina gani?
'Son zuciya da tunanin banza da burin hauka.' Zuciyata ta ba ni amsa da haka. Sosai nake hawaye na baƙinciki da takaici.
Numfashi Maman Humairah ta sauke ta ce. "Hmmm, da ma a rayuwar nan duk wanda bai ji bari ba zai ji hoho, kuma *ABIN DA KA SHUKA* shi za ka girba, wannan sai ya zama izna a gare ki Maman Sultan da ke da masu irin halinki, na raina abin da Allah ya ba su suna hangen na wasu. Bare ma wanda ba a zahiri ka san shi ba, haɗuwar media rayuwar ƙarya zalla, ni kina ganin ina magana a cikin group ɗin? Bana yi, saboda na san duk maƙaryata ne, akwai masu kuɗi sosai irinsu Maman Nasman da Aunty Billy, amma majority rayuwar duk packaging ne, to su masu kuɗin su ma kin gani dai kuɗin ya zame masu bala'i da masifa, ita ga yadda ta ƙare, ita kuma Aunty Billy ga kuɗin amma ba kwanciyar hankali, saboda ta san mijinta yana biye-biye, ban da ƙaddara me za ka yi da irin waɗannan mazan? Kina zaman-zamanki cikin rufin asiri da kwanciyar hankali kika buɗe wa kanki ƙofar masifa kika afka, sai ga shi mijin da kika raina ita da kike sha'awar nata ita kuma nakin take so da burin samu. Ni ko a labari ban taɓa jin wauta da shashanci irin wanda kika aikata ba, saboda wani group ki rabu da mijinki! Wa kika ji ta yi haka kaf cikin group ɗin? Ni ko kaɗan abubuwan da suke tutturowa da wanda suke faɗa ba sa burge ni, sai ma haushi da suke ba ni. Don ba wayewa ba ne ka dinga nuna kai wani ne a rayuwa, ka bari dukiyar taka ta bayyana wa mutane kanta ba wai kai ka bayyana ta ba. Ni ƙauyanci nake ɗaukan irin wannan abubuwan, ba alfanu ma ka zo media kai ta faɗar abubuwan gidanka da abin da mijinka ya yi maka, ko da gaskiya ne za a dinga yi maka kallon mai son a sani da fariya, ko ka yi wani abun na alkhairi ka zame ladanka a riya ba tare da ka sani ba. Akwai waɗanda da dama a cikin group ɗin mazajensu ba su kai naki ba, ni na san su, ita ma kuma Hafsat Alƙali ta san su, amma da yake ƴan taya ɓera ɓari ne shiga suke a yi ta hirar ƙaryar da su, su je su yi ta ɗakko hotunan abubuwa masu tsada a media suna turowa suna cewa su ma sun siya. Ke kuma da ba ki da wayo sai kika ɗauka kowacce mijinta mai kuɗi ne, ai akwai abin da a rayuwa hankali ba zai ɗauka ba. Group ɗin buɗe shi aka yi aka watsa link mai so ya shiga, ba wai zaɓar mutanen ciki aka yi ba bare a ce sai wanda aka san mai kuɗi ne za a saka shi. Ni na so fita ma gabaɗaya daga cikinsa, Maman Nasmah ce ta hana ni, amma da tuni na fece don bana son sabgar da babu ilimi a cikinta. Allah ya sa mu dace kawai, amma wauta dai kin tafka ta. Shawarar da zan ba ki yanzu ki je ki nemi tsohon mijinki ki nemi yafiyar abubuwan da kika aikata masa, tun kafin lokaci ya ƙure miki." Da sauri na miƙe ina kuka na ce. "Yanzu kuwa, wallahi na yi nadama, na tuba, kaico na!" Cikin magana da ƙyar Maman Nasmah ta ce. "Don Allah kar ki tafi ba ki ce kin yafe mini ba Hafsah, ki tausaya mini." Wani banza kallo na yi mata na ce. "Ni kin tausaya mini ne a baya? Duk halin da nake ciki ke ce sila, ke kika dinga tunzura ni, wallahi na tsane ki, a yadda zuciyata take tafarfasa a yanzu ji nake kamar na rufe ki da duka, macuciya kawai."
"Idan da tun farko ba ki bayar da ƙofa ba babu yadda za a yi ta tunzura ki, ki tunzuru, ke ma can da halinki, don haka ba ita kaɗai za ki ɗorawa laifi ba." Maman Humairah ta faɗa tana kallo na.
A fusace na ce. "Ko ma dai mene ne ba zan yafe mata ba, kuma idan ina da laifi nata ya fi yawa ai." Girgiza mini kai ta fara yi tana wani irin kuka tare da faɗin. "Kar ki mun haka, ki taimake ni ki rage mini nauyin wani abun kafin na mutu, ban taɓa zaluntar wani ba a duniya kamar ke, ban san ya zan kwatanta miki halin da zuciyata take ciki ba, wallahi na tuba, na yi nadama."
"Da kika gan ki a kwance ba? Ba halin ƙara yin wata muguntar, da za ki warke za ki ɗora daga inda kika tsaya ne." Na katse ta da faɗin haka cikin shouting. Ban jira cewar ta ba na fice daga ɗakin kamar zan tashi sama, ina jin Maman Humairah tana kira na, na yi mata banza. Don a yanzu burina kawai na gan ni a gaban Anas na durƙusa na nemi gafarar shi, zan je na nemo shi a duk inda yake ko da kuwa birnin sin ne, daga nan na wuce gidansu Naja na ba ta haƙurin abubuwan da na yi mata ita ma........✍️
*Zeey Kumurya*✍️
[5/11, 12:13 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
*BRIGHT PENS*
(FREE BATCH)
*35.*
A daddafe nake tafiya don har wani jiri-jiri nake ji, idona ban da tsiyayar hawaye babu abin da yake yi. Da wani ne ya faɗa mini Maman Nasmah za ta yi mini haka ba zan taɓa yarda ba, kallon masoyiya ƴar'uwata nake yi mata, ashe ina yi mata kallon biri ne tana mun na ayaba. Ina zaman zamana ta yi mini ingiza mai kantu ruwa ta kai ni ta baro. A farfajiyar gidan na tsaya na goge fuskata da hancina da ƙasan hijab ɗina, sannan na duba bayan wayata na ga dubu biyun da na saka da zan fito, don Maman Humairah ce ta biya mana kuɗin mota daga gidanta zuwa nan, ni kuma na riƙe ɗari biyu da ma a hannuna, na yi kuɗin motar zuwa gidanta. Lissafi nake Allah ya sa kuɗin ya ishe ni yawon neman Anas, duk da a yadda nake fata da burin ganin shi ko da ƙafa ne zan je ko'ina ne, ni dai kawai na haɗu da shi a yau shi ne kwanciyar hankalina.
Direct gidan cousin ɗinsa Aunty Rahama na ce mai napep ya kai ni. Wajen ƙarfe uku na shiga gidan ina addu'ar Allah ya sa tana nan, don a gurinta ne kawai zan samu duk wani information nasa da nake nema, because ita kaɗai ce ƴar'uwarsa ta jini a garin nan. Na yi sa'a tana nan, da fara'a ta tarɓe ni, ta kai ni ɗaki, ta kawo mini abinci da ruwa. Yadda take nan nan da ni duk da mun rabu da ɗan'uwanta ya ƙara tabbatar mini mutunci a jininsu yake. Bayan na yi Sallah ba tare da na sha ko da ruwa ba na ce. "Don Allah Abban Sultan yana garin nan kuwa?" Ta ce. "Yana nan, da dai ya yi tafiya bayan rabuwar ku, amma ya dawo." Ajiyar zuciya na sauke, a raunane na ce. "Ya yi aure ko?" Kamar mai jin nauyi na ta ce. "Eh, yana nan tare da matarsa da yaranki." Ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta cika mini ido na yi tare da danne kishin da ya taso mini na ce. "A ina suke." Yadda muryata ta yi rawa ya tabbatar asirin da nake ƙoƙarin binnewa a cikin zuciyata ya bayyana kansa. Wani kallo ta yi mini sannan ta ce. "Ya tashi daga gidan da kuka zauna, ya canza unguwa, bari na dubo miki saƙon address ɗin da matar tasa ta taɓa tura mini, don ban riƙe ba." Ban ce komai ba don na lula duniyar tunani, Anas ya yi aure? Ashe duk son da yake yi mini zai iya dainawa? Zai iya rayuwa da wata macan da ba ni ba? Anya kuwa zan iya jurar ganin shi da wata a gida ɗaya? Na san babu abin da zai hana jinina hawa. Runtse idona na yi tare da dafe saitin zuciyata, saboda zullon da take yi, na zallar kishi.
Bayan ta kawo mini wayar na copy address ɗin na yi mata sallama na tafi, ta yi ta yi na sha ko da ruwa ne na ƙi, saboda ba ta shi nake ba, so nake kawai na ga matar da mijina ya aura, na ga da me ta fi?
Ina napep amma gani nake kamar driver'n ba ya sauri kwata-kwata, saboda zaƙuwa. Yana tsayawa a ƙofar layin na ji wani abu mara daɗi yana bin dukkan jikina tare da sanyaya mini shi ya yi lagwaɓ. Da ƙyar na iya yin jarumta na fito na sallame shi. Wayata na latsa na lalubi address ɗin na duba, sai na ga symbol ɗin da aka rubuta ina hango shi ma. Gabana na faɗuwa na ƙarasa gidan da kwatancen ya nuna na fara bubbugawa.
"Waye?" Na ji muryar da ko a cikin bacci na ji ta sai na shaida ta. Muryata na rawa na ce. "Ni ce Sufyan!" Cike da ɗoki da ZUMUƊIN ganin su, hakan ya tabbatar mini ban yi ɓatan kai ba, nan ne gidan. Ban san ya buɗe ba sai ji na yi cikin kauɗinsa ya ce. "Mami!" Ƙasa motsawa na yi na tsaya kawai ina kallon shi, idona cike da ƙwalla. Ya ƙara girma da haske, kuma fes da shi alamun yana samun kulawa.
"Yaya! Yaya! Ga Mami, yau Mami ta zo." Ya faɗa yana tsalle tare da juyawa ya koma cikin gidan. Bin bayansa na yi da sauri ina hawaye. A tsaye na tarar da shi yana jan Sultan, shi kuma ya ƙi tahowa ya tsaya kawai yana kallon bakin ƙofa. Hannu na ware cikin rawar baki na ce. "Ku zo na ji ɗumin ku yarana." Da gudu Sufyan ya zo ya rungume ni, a hankali shi ma ya tako ya riƙe ni. Fashewa na yi da kuka ina jin kamar na mayar da su ciki, tsabar ruɗewar murna jikina har rawa yake, na cutar da kaina, na zalunci ƴaƴana, na nesanta su da ni ba su ji ba, ba su gani ba. Ban damu da a jiyo sautin kukana ba, na ma manta a inda nake, ta yarana kawai nake.
"Sufyan! Ku da waye na ji kamar ana kuka?" Na ji an faɗa daga ɗaki da muryar da tamkar na san ta.
"Maamah, Maminmu ce ta zo, ashe ta san gidan nan." Sufyan ya faɗa yana barin jikina, cikin farincikin da yake. A nutse aka bankaɗo labulen ɗakin tare da fitowa a lokaci ɗaya. Cak kukan da nake ya tsaya, na nemi gani na, ji na da numfashina na rasa, na ji a wata duniyar ta daban da ake yawo da ni a cikin gajimare, ba don Sultan da yake riƙe da ni ba da babu abin da zai hana ni kai wa ƙasa. A hankali numfashina ya fara dawowa daidai, na ƙura mata ido kamar yadda ita ma ta tsaya tana kallo na. Yanayinta bai yi kama da wadda ta zo gidan da sunan baƙunta ba duba da yanayin shigar jikinta, da ɗan ciki da ya tasa ya yi mata das a jikinta. Murza idona na shiga yi kamar ina murza fulawa, ko shi yake yi mini gizo? Ko shi ne ya fara samun matsala? Ko kuma na haukace ne? Amma ina kuma ƙara buɗewa ita na ƙara gani a tsaye a inda take. Magana nake son yi amma na kasa, baza hanci kawai nake don neman ishashshiyar iskar da za ta sadu da huhuna. Jinjina na yi da bango ina jin jikina kamar ba nawa ba, hannuna ya gagara riƙe wayata ta suɓce ta faɗi ƙasa. Korar tunanin ita ce matar Anas na yi na ɗauko wanda ni kaina na san yaudar kaina nake na saka a raina. Wato ba matarsa ba ce, sai dai in zuwa ta yi da ziyara gurin matar gidan. Take zuciyata ta aminta da hakan har ta fara samun salama.
"Maamah kin ga Mami, Mami ce fa." Muryar Sufyan da yake jan hannunta kamar yadda ya yi wa Sultan ta dawo da ni duniyar da suke.
Harshe da ya yi mini nauyi na sarrafa da ƙyar na ce. "Naja!" Ban san maganar ta fita ba don ni ban ji sautinta ba sai da na ji ta ce. "Na'am Hafsah!" A matuƙar rauna ne.
"Ita ce." Na faɗa a fili cikin tantamar ko ɓatan kai na yi ba gidan Anas na zo ba. A hankali ta yi taku kaɗan ta ce. "Bismillah ki shigo mana." Kamar wawiya haka na bi bayanta cikin dokawar zuci.
Bayan mun zauna na zuba mata ido, ina jiran ta yi magana amma ba ta ce komai ba, sai sunkuyar da kanta da ta yi ƙasa kawai. Ba zan iya ko da minti ɗaya ba tare da na ji gaskiyar abin da nake son ji ba, hakan ya sa na ce. "Naja ke ce da gaske ba idona ba ne yake mun ƙarya ba? Ya aka yi na ga su Sultan a tare da ke? Me ya faru? Don Allah ki fitar da ni daga cikin duhu." Na ƙarashe maganar kamar mai naƙuda saboda numfarfashin da nake. Ba tare da ta ɗago ba ta ce. "Me kike son ji bayan wanda idonki ya ganar miki Hafsah?"
"Ban fahimci komai ba ne, bana gane komai, ƙwaƙwalwata ta daina aiki."
"Kin gane mana, kin gane ni ce matar Anas shi ya sa har kike tunanin ta daina aikin." Ta faɗi haka tana kallon cikin idona.
Jujjuya kaina na fara yi saboda ƙoƙarin tarwatsewar da yake yi ba tare da iya kuma magana ba. Miƙewa ta yi ta fice, ban san lokacin da ta ɗauka ba don bana gane komai ta dawo tare da glass da ke ɗauke da ruwa a ciki ta miƙo mini. Girgiza mata kai na yi, cikin kulawa ta ce. "Ki karɓa, addu'a ce, za ki ji sauƙin abin da kike ji." Ban kuma musu ba na karɓa na kafa kai na fara sha a haukace, kamar yadda na tabbatar wa kaina ni ma na haukace ɗin.
Cike da tausayawa Naja take kallon ta, duk yadda ta shirya wa ranar nan amma ba ƙaramin firgici ta tsinci kanta a ciki ba da ta zo. Sosai ta diriri ce a lokacin da ta yi ido huɗu da Hafsah, hatta abin da yake cikinta sai da ya motsa. Ba ta san ya take ji a cikin ranta ba, amma ta san ba ƙaramin ɗaci da ciwo abun zai yi mata ba, ba ƙaramin razana zuciyarta zai yi ba. Ta sha kwatanta idan ita ce a matsayin yadda za ta ji, a lokacin da ta wayi gari ta ga aminiyarta ta auri mijinta. Sai dai kamar yadda ta ƙudurce a ranta, a duk lokacin da Hafsah ta dawo kan hanya, ta gane kuskurenta, a shirye take ta yi duk yadda za ta yi aurensu ya dawo, ko da kuwa hakan yana nufin rasa nata auren. Tana son ƙawar tata sosai, tana matuƙar tausayin ta, za ta iya cewa ta fi kowa baƙinciki da takaicin rabuwar su da Anas. Numfashi ta sauke tare da miƙewa ta fice daga ɗakin don zuwa ta taso shi ya zo a yi wannan yaƙin da shi, ba za ta iya ita kaɗai ba. Saboda ta san next thing da Hafsah za ta buƙata jin yadda aka yi suka yi aure. To ya zo ya faɗa mata da bakinsa kamar yadda ta sha faɗa masa idan irin wannan ranar ta zo.
A tsakar gida suka yi da Sultan, ya zubo abinci a plate, ko da bai faɗa mata ba ta san mahaifiyarsa zai kaiwa, cikin ranta ta ce. 'Allah Sarki uwa da ɗa sai Allah, duk yadda yake ɓata rai idan ta yi musu zancenta ya ce ba ta son su tunda ta tafi ta bar su, amma tana zuwa har ya ɗiba abinci zai kai mata.' Jiki a saɓule ta shiga parlour'n su ta wuce zuwa bedroom. A kwance ta tarar da shi yana latsa waya, ko sallama ba ta yi ba ta tsaya kawai ta harɗe hannunta a ƙirji ta zuba masa ido.
Kawar da wayar ya yi daga fuskarsa ya kalle ta na sakanni sannan ya miƙa mata hannu alamar ta zo. A hankali ta taka ta zauna a gefen gadon kusa da shi ta juya masa baya, saɓanin kan cinyarsa da yake nuna mata. Bai ce komai ba ya matsa kusa da ita ya kwantar da kansa a kan kafaɗarta ya fara goga mata sajensa a gefen kuncinta, tare da saka hannayensa duka a kan cikinta ya fara shafawa. Lumshe idonta ta yi ta buɗe ta ce. "Ya aka yi ka tashi?" Yana zagaye lips ɗinta ya ce. "Saboda kin tashi kuma kin tafi kin bar ni, ga lokacin Sallah ya taho." Numfashi ta sauke cikin ranta tana ta auna ta inda za ta sako masa maganar zuwan Hafsah. Ƙara ƙanƙame ta ya yi tare da kai bakinsa daidai kunnenta ya ce. "Wa ya taɓa mini ke na gan ki a haka?" Tana sauke numfashi ta ce. "Babu kowa, wani albishir na zo maka da shi kawai." Sakin ta ya yi ya ce. "Na ji a jikina kamar ba mai daɗi ba ne." Kallon idonsa ta yi tare da ɗora hannunta a kan ƙirjinsa ta fara shafawa sannan ta ce. "Daɗinsa ma ya wuce misali, na san zai saka farinciki mijina shi ya sa ma na zo maka da shi." Da ido ya yi mata alamar yana sauraren ta. A hankali kamar mai jin kunyar faɗar ta ce. "Hafsah ce ta zo." Tsam ya yi tare da yatsina fuska ya ce. "Wacce Hafsan?" Da confidence ta ce. "Wacce zan yi maka albishir ɗin zuwanta ban da matarka uwar ƴaƴanka?"
"Ban da wata mata uwar ƴaƴana sai ke, don haka ban gane inda kika dosa ba da abin da kike nufi."
"Kar ka wahalar da ni, don na san ka gane, Mamansu Sultan, mahaifiyarsu, na san daga haka ba ka buƙatar ƙarin wani bayani." Fuskarsa babu walwala ko kaɗan ya ce. "Me ya kawo ta gidana kuma?" Ta ce. "Ganin ku mana kai da ƴaƴanta." Ɗage kafaɗa ya yi ya ce. "Ba zan hana ta ganin ƴaƴanta ko zuwa gurinsu ba, amma ni da mu ƙara haɗuwa in sha Allahu har abada, saboda haka kar ki ƙara yi mini maganarta." Duk da ba ta taɓa ganin ɓacin ransa haka ba tunda suke amma ta dake ta ce. "Kar ka yaudari kanka ko ka yi pretending ba ka yi farinciki da zuwanta ba, ka san na fi kowa sanin irin son da kake yi mata." Bai ce komai ba ya zagaye ta ya sauka daga kan gadon, don ba ya son ɓacin ransa ya yi yawa ya kai shi ga ɓata mata nata ran. Cikin marairacewa ta ce. "Don Allah ka tsaya mu yi magana, please." Ta ƙarashe maganar tare da haɗe hannayenta guri guda. Numfashi ya sauke ya ce. "Maganar me za mu yi a kanta? Ba ta da amfani a cikin rayuwarmu, akan me za mu tsaya muna ɓata lokaci saboda ita, me zan yi mata idan ta zo? Idan yaranta ne ga su nan ban hana ta gan su ba, ke ma kuma ƙawarki ce ba zan hana ku mu'amala ba idan kina so, to me kike so da ni bayan wannan?" A shagwaɓe ta ce. "Ka je ku yi magana mana, na san shi ne babban abin da ya kawo ta duk da ba ta faɗa mini ba." Tsaki ya ja bai ce komai ba ya shige toilet, ta miƙe a hankali ta bi bayan shi ta tsaya tana kallon shi, ya yi abin da zai yi haɗe da alwala ya gama. Zai raɓa ta gefenta ya wuce ta kamo hannunsa, ya tsaya kawai yana kallon ta. Sosai ta ga ɓacin rai a kan fuskarsa da ba ta taɓa gani ba, sai ta ji babu daɗi a cikin ranta, amma duk da haka ba za ta haƙura ba, saboda wani irin tausayin Hafsah take ji, tunda can da ma ba ta taɓa ƙullatar ta ba, don ba ƙaramin tausayi take ba ta ba. A yanzu da ta gan ta, ta hango tsantsar nadama a tattare da ita da yadda duk ta lalace sai tausayin nata ya ninku a cikin zuciyarta, tana son ta sosai, tana son ganin rayuwarta ta inganta, don da tana da hali ba za bari Hafsah ta faɗa halin da ta tsinci kanta a cikin ba. Kamar za ta yi kuka ta ce. "Don girman Allah ka tsaya mu yi magana ta fahimta, ka daina wannan fushin, ka san ɗaga mini hankali zai yi." Janyo jikinsa ya yi, da sauri ta tafi ta rungume shi ta baya, tare da saka hannayenta ta zagaye shi. Dawo da ita gabansa ya yi, yana shafa fuskarta ya ce. "Kin san bana son ganin ki a cikin damuwa ko kaɗan, amma kike ta damar mun kanki." Tana ƙara shigewa jikinsa ta ce. "Dole na damu mana, tunda na zo maka da abu amma ka ƙi saurare na."
"Ba abin saurarar ba ne shi ya sa, an fara kiran Sallah, zan wuce masallaci, kar na dawo na tarar da wannan damuwar a kan fuskarki, waccar maganar kuma bana son jin ta, kar ki ƙara yi mini ita, idan kuma kina son ganin ɓacin raina ki ci gaba." Ya ƙarashe maganar cikin yanayin fusata tare da raba ta da jikinsa. Ba ta ce komai ba, sai dai yadda ta yi da fuskarta kamar za ta fashe da kuka. Har ya fara tafiya ya juyo yana kallon ta, hakan ya sa ta matsa kusa da shi tare da marairace fuska. Cikin kulawa da soyayya ya ce. "Wane ne ya taɓa mini uwar biyuna ne?" Ƙirjinsa ta nuna da hannunta tare da turo baki gaba. A hankali ya fara shafa bayanta, cikin rarrashi ya ce. "Me kuma na yi?" A shagwaɓe ta ce. "Faɗa ka mun." Sai da ya kwantar da ita a jikinsa sannan ya ce. "To na daina my love, sorry." Maƙe kafaɗa ta yi tare da juya masa idanunta. Kissing saman idon da bakinta da ta tura ya yi ya ce. "Wannan rarrashin sai na dawo kenan?" Gyaɗa masa kai ta yi. Yana murmushi ya ce. "Tom shikenan, bari na sake alwala, garin rigimarki kin sa wadda na yi ta karye." Sai da ta bar jikinsa sannan ta yi masa gwalo, murmushi ya yi mai sauti ya ce. "I so much love you bab." Fari kawai ta yi masa da ido ba ta ce komai ba, har ya sake alwalar ya fice. Numfashi ta sauke tare da jingina da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 24