Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuce ban yi bacci ba, ina zaune a tsakiyar makeken gadon da nake na tasa kayana a gaba ina aikin kallon su, sai jujjuya dalleliyar wayar nake a hannuna ina sakin murmushi. "Allah ka cika mini burina, ka nuna mini ranar da ni ma zan yi kyauta ga wani ninkin ba ninkin ɗin wannan." Na yi maganar ina bin bedroom ɗin da ya kusa rabin gidana gabaɗaya a girma da kallo. Gado, wardrobe, mudubi duk suna gefe ko rabin ɗakin ba su ci ba. Ƙuntataccen ɗakina na tuna, wanda space ɗinsa da ya rage bai fi ya ci ƙaramar tabarma biyu ba. Tsaki na ja na tattara kayan ba don na gaji da ganin su ba na kwanta. Sai na ji kuma na kasa baccin, duk da juyin da nake yi a gadon ina bararrajewa son raina. Tashi na yi na rage hasken ko shi ya hana baccin ɗauka ta. Amma still ya ƙi zuwa, tunanin Anas da su Sultan na ji ya cika zuciyata, wata irin kewar su da ban taɓa zaton yin ta ba ta ziyarce ni. Duk yadda na so na yakice su amma abu ya ci tura. Taune leɓena na yi ina ayyana da dare bai yi sosai ba sai na koma gidana a yau, don na gane ba zan taɓa iya rayuwa babu mijina da ƴaƴana ba, ko kuɗin da nake so da shi nake son mu yi ba wai mu rabu ma, amma shi ya ƙi gane hakan bare ya ba ni haɗin kai. Da ƙyar na samu bacci ya ɗauke ni lokacin da dare ya kusa rabawa. Washegari bayan na yi sallar asuba na koma bacci, sai bayan 10 na tashi muka fara shirin tafiya taronmu. Mai kwalliya ta musamman ce ta zo ta yi mana har gida ni da Maman Nasmah. Zuwa bayan azhar mun gama shiryawa cikin ankonmu. Na daɗe ina kallon kaina a mudubi saboda ba ƙaramin kyau na yi ba ni kaina na sani. Maman Nasmah ta dinga yi mini hoto a wayarta, don tawa har yanzu ba a kunna ta ba, ni ban iya using iphone ba ita kuma ta ce sai mun nutsu za ta saita mini komai. A wata luntsumemiyar mota mai numfashi muka tafi gidan Aunty Billy, muna baya driver yana gaba shi kaɗai. Sosai harabar gidan da aka yi wa decoration ya yi kyau, mun tarar da sama da mutum 20 a gidan sun zo. Da gudu wasu suka taho suka rungume Maman Nasmah, ta nuna musu ni, suka ce ko da ba ta faɗa ba sun san ni ce, saboda sun san duk inda suka gan ta za su gan ni a gurin, tunda kowa ya san ita ce babbar ƙawata a group ɗin. Zagewa na yi aka shiga hada-hada da ni, ina jin kaina kamar kowa tunda na saka gold da sauran kayan kwalliya masu tsada. Sama da mutane 60 ne suka halarci taron, kuma duk ƴan group ɗin namu ne, kowacce kuma ta saka anko, ta yi ɗinki mai tsada da sarƙar gold ɗin da aka ce. Sosai muka yi kyau kamar yadda muke fata. An ci an sha, an yi rawa an cashe an tattauna, abin gwanin ban burgewa. Hakan sai ya ƙara mini son group ɗin sosai, na ji ko me za a yi ba zan fita daga cikinsa ba. Mun sha hotuna da video kamar ba gobe. Sai da aka kusa tashi Maman Nasmah ta saka mini sim ɗina a cikin sabuwar wayar, ta nuna mini yadda zan yi kira da wasu ƴan abubuwan, sauran kuma ta ce sai mun koma gida za ta nuna mini. Kaf matan da suka zo taron babu wadda ta kai ni duhu, saboda kowacce sai na gan ta fara ƙal, waɗanda ba fararen sosai ba kuma duk sun fi ni haske, duk da gyaran jikin da aka mun, alaƙanta hakan na yi da don su matan masu kuɗi ne ni kuma matar talaka ce. Messages na gani da numbern Naja, na farko ta ce tana ta kira na a kashe, na biyu kuma ta ce ina ina? Ta zo gidan ba na nan, alamun tun jiya ta yi su kenan. Sai yau da ta ƙara cewa ta je da safe ba na nan, sai na ƙarshe kuma wanda da alama ba ta daɗe da yin shi ba, ta ce duk inda nake na koma gidana don Anas ya mayar da ni tun jiya, idan ba haka ba za ta je ta faɗa wa Kawu duk abin da yake faruwa. A tsorace na bar filin rawar da muke na ja Maman Nasmah gefe na ce. "Ni fa tafiya gida zan yi yanzu, na ga Magriba ta kusa." Kallon sama da ƙasa ta yi mini ta ce. "Saboda me? Ya kira ni ne? Ba gidana za ki koma ba da ma?" Girgiza kaina na yi cikin fargaba na ce. "Bai kira ni ba, amma ƙawata ta yi mini text ta ce ya mayar da ni." Tsaki ta ja ta ce. "Ita ƙawar taki ya aka yi ta sani?" In brief na ba ta labarin tattaunawar da muka yi da Naja. Tafa hannuwa ta yi ta ce. "Shi ne kike wannan rawar jikin komawar? Bai kira ki da kansa ba tun jiya amma daga an yi miki text an ce ya mayar da ke duk kika gigice haka? Hafsah wai wacce iriya ce ke ne? Akan namiji? Namjin ma talaka." Kamar zan yi kuka na ce. "Ba haka ba ne, ina tsoron ƙawar tawa ta faɗa wa Babana ne." Taɓe baki ta yi ta ce. "To bari ki ji, ita ƙawar taki ita ce babbar munafuka kuma maƙiyiyarki, saboda ba ta son ki da arziƙi, da tana son ki da arziƙi ba za ta ce ki rabu da mu ba, bayan kin faɗa mata yadda muke da irin kyautar da na yi miki, amma saboda tana baƙincikin ki yi mu'almala da masu kuɗin da ita ba ta yi shi ya sa ta ba ki wannan gurguwar shawarar, za ta ce kar ki fara gayu ki bar ta a baya." Girgiza kai na yi na ce. "Naja ƙawata ce ta haƙiƙa tun muna yara, tana so na da son ci gabana sosai, ba za ta taɓa yi mini abu don hassada ba gaskiya, kawai dai tana faɗa mini tata fahimtar ne." A sheƙe kamar kashi ta saki baki tana kallo na, kafin ta jijjiga kai ta ce. "Taɓɗijan! Amma gaskiya ba ki san halin da duniya take ciki ba, to ki je ki tambaya ki ce kaf yanzu a rayuwa wa ya fi rashin amana da nuna hassada, za a faɗa miki a ce aminiya ce. Tun yaushe aka daina ƙawancen tsakani da Allah, kowa zuciya da tsatsa burinsa ya ga ya fi ɗan'uwansa ci gaba. Idan kuma kina tantama akan maganata ki je ki ce mata ta auri miji talaka kamar naki, za ki ji abin da za ta ce, wanda zai nuna ba ta so, amma ke tana danƙwarar da ke akan ki zauna." Jinjina kai na yi, zan yi magana Aunty Billy da ta ƙaraso inda nake ta riga ni da faɗin. "Ku ce aminai kuna nan kuna zantawa?" Murmushi muka yi duk da nawa na yaƙe ne. Ta ce. "Ku zo mu je ku gaisa da Ogana, ya dawo yanzun nan, ya gaisa da kowa ban da ku." Maman Nasmah ta ce. "Shi ya sa na ga bakinki ya ƙi rufuwa, ashe rabin ran kika gani." Ta ce. "Bari ke dai, har ya ƙara mini da kuɗin liƙi." Faɗaɗa fara'a Maman Nasmah ta yi ta ce. "Ai na sani da ma, ni da na san dawar garin, duk dawowa da ma kin ce da kyauta yake yi miki sallama, kamar nawa mai gidan, shi ma yana dawowa zai ce ungo." Dariya suka kwashe da ita tare da tafawa suka yi gaba. Na bi su abaya kamar saniyar ware, a raina ina faɗin. 'Wato su mazajen nasu da kuɗi suke tarɓar su kullum? Gaskiya matan masu kuɗi suna shanawa da yawa, ga ƙaton gida, ga abinci lafiyayye, ga sutura mai tsada, ga hawa mota da sauran abubuwan more rayuwa." Wani part ɗin muka shiga daban ba inda ta kai mu da za mu yi Sallah ba, ba ƙaramin dauriya na yi ba gurin ɓoye ƙauyancina, saboda haɗuwa da tsaruwar shi. Na kasa gane tsakanin gidan Maman Nasmah da na Aunty Billy wanne ya fi kyau da girma, saboda kowanne ya kai duk inda ake son gida ya kai a tsaruwa. Cikin fara'a kamar ya san mu muka gaisa da mijin nata, ta ƙasan ido na ƙare masa kallo. Irin alhazawan nan ne da kuɗi da hutu suka zauna a jikinsu, ga shi ɗan dumurmuri ya sha babbar riga cikin kaya na alfarma. Irin dai mijin da mace ba za ta ji kunyar nuna shi ba ko a ina ne. Anas ne ya faɗo mini a rai, na ja tsaki ƙasa-ƙasa, tare da addu'ar kar Allah ya kawo ranar da wata a group ɗinmu za ta ƙara ganin shi a matsayin mijina bayan Maman Nasmah. Don abin kunya ne a gare ni. Bayan mun fito Maman Nasmah ta ce mini. "Wai tafiyar za ki yi da gaske na ga kina abu kamar a ce ƙyet! Ki gudu?" Ɗaga mata kai na yi ban ce komai ba. Aunty Billy ta ce. "Saboda me? Ki bari a tashi mana, ba wani ɗadewa za a kuma yi ba fa, ana yin Magriba DJ zai tafi." Kafin na yi magana Maman Nasmah ta yi karaf ta ce. "Mijinta ne ya kira ta yaron ta babu lafiya, shi ya sa." Ajiyar zuciya na sauke ina ƙara jin son ta a raina, saboda duk yadda za ta yi kar asirina ya tonu sai ta yi. Aunty Billy ta ce. "Ayya, Allah ya ba shi lafiya, bari na zo to ina zuwa." Bayan ta bar gurin Maman Nasmah ta ce. "Ki yi tafiyar ki kar ki yi wa kowa sallama tunda kin nace, saboda su Maman Suhail tun jiya suke ce mini ina ne gidanki za su je, yanzu idan suka ji za ki tafi bin ki za su yi. Gobe idan Allah ya kai mu da safe sai ki zo gidana, zan saka wani a cikin my driver's ya kai ki ɗaya daga cikin guest house ɗinmu, ki zauna a can a matsayin nan ne gidanki, sai su zo nan su same ki, idan za ku tafi zan haɗa miki da wadataccen abincin da zai isa a ci da drinks. Zan ba su address ɗin yanzu idan sun tambaye ni ina ne gidanki. Bana son su je ainihin gidanki su raina ki ne, shi ya sa na yi wannan dabarar." Ban san lokacin da na rungume ta ba tsabar farinciki na ce. "Ya Allah! Na rasa da bakin ma da zan gode miki wallahi, duk abin da za ki yi ki kankaro mini mutunci kin san shi." Tana murmushi bayan ta raba ni da jikinta ta ce. "Ƙauna ce ta kawo hakan, ke dai duk abin da na ce ki yi kawai ki bi, don ba zan taɓa cutar da ke ba." Cikin zumuɗi na ce. "Na tabbatar da hakan takwara, Allah ya bar mu tare." Ta ce. "Amin." Kayan ciye-ciye da abinci da lemuka Aunty Billy ta haɗo ta ba ni, na yi musu sallama na tafi cikin sauri, don na ga Naja ta fara doka mini kira. Allah ya taimake ni ina fita titi na samu mai napep, ya ce zai kai ni har gida a 2k. Ban tsaya ja'inja ba na shiga, saboda ina da ishashshen kuɗi a hannuna ragowar na liƙin da Maman Nasmah ta ba ni. Mun fara tafiya mai napep ɗin ya ce. "Hajiya ga wata mota tana bin mu a baya, ko kin san su ne?" Girgiza kai na yi na ce. "A'a." Ya ce. "To dai wannan mu take bi, amma bari na shiga ta layuka don na tabbatar, idan mu yake bi zai shigo shi ma." Na ce. "To." Don ni hankalina gabaɗaya ya yi gida, burina kawai na gan ni a cikinsa, don ba na son maganar abin da yake faruwa ta je kunnen Kawu, na san na lahira sai ya fi ni jin daɗi a gurinsa. Da gudu motar da take bin bayanmu ta zo ta wuce mu ta tsaya a gabanmu. Cikin faɗuwar gaba na ce. "Innalillahi! Su waye wannan? Me suke nema a gurinmu?" "Sai Allah." Mai napep ya faɗa a tsorace bayan ya tsayar da babur ɗin. Fita ya yi ya je suka yi magana, ina ta leƙen su a tsorace na ga ya dawo ya ce. "Hajiya ke suka biyo, da ma daga layin da kika fito na ga su ma sun fito." Dafe ƙirji na yi a firgice na ce. "Na shiga uku! Me zan yi musu to?" Yana murmushi ya ce. "Ki je ki ji, amma na tabbatar ba cutar da ke za su yi ba." A tsorace na kalle shi na ce. "Ko dai bakinku ɗaya da su?" Ya ce. "Wallahi ban ma taɓa ganin su ba sai yau, ki daure ki je, sun ce ba jimawa za ki yi ba." Girgiza kai na hau yi na ce. "Ka shigo ka ja mu kawai mu tafi, ni sauri nake babu inda zan je." "Ko mun juya sai sun kuma bin mu, ki je kawai ki ji me za su ce ki dawo, don Allah!" Ya yi maganar cikin roƙo. Ina kallon layin da babu kowa sai mu kaɗai na ce. "Wai maza ne ma ko mata?" Ya ce. "Mata ne." Ajiyar zuciya na sauke na fita ina waige-waige a tsorace, sai a lokacin na lura da sababbin kuɗin da suke hannunsa, tabbacin cin hanci suka ba shi, shi ya sa ya dage sai na je. Kamar kar na ƙarasa, saboda haka kawai na ji zuciyata tana bugawa. Tsayawa na yi cak a gaba da napep ɗin amma ban ƙarasa inda motar take ba. A hankali na ga an buɗe front seat an fito, damm! Ƙirjina ya buga da ƙarfi bayan na yi tozali da mai fitowar........✍️ *Zeey Kumurya* [3/8, 1:40 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MIKIYA WRITERS ASSOCIATION *15.* Namiji na gani, saɓanin abin da mai napep ɗin ya ce mini. A fusace na juya na koma na ce masa. "Ka ce mata ne, ya kuma na ga maza?" Ya ce. "Ki yi haƙuri, na yi musu alƙawarin zan fito da ke ne, shi ya sa na ce miki mata ne, don na san idan na ce maza ne bai zama lallai ki je ba." Tsaki na ja na ce. "Matar aure ce fa ni! Idan matarka ce za ka so wasu su tare ta?" Cikin lallami ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah, idan ba hakan ba na yi na san ba za su taɓa daina bin mu ba, ki je sai ki yi musu bayani, na san za su ƙyale ki." Numfashi na sauke tare da dafe kaina na koma, kaina a ƙasa na ƙarasa inda mutumin yake na ce. "Ga ni Malam ya aka yi?" Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Sannu ƴan mata." Da sauri na ɗago don jin kamar na san shi, kallon tsaf na yi masa, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta tuno mini shi, mijin Aunty Billy ne. Cikin mamaki na ce. "Alhaji! Lafiya?" "Lafiya ƙalau mai inganci ma kuwa." Ya faɗa yana murmushi tare da bi na da wani irin kallo. Ajiyar zuciya na sauke ban ce komai ba, ina jira na ji ya ce matarsa ce ta aiko shi, sai na ji ya ce. "Ban san yanzu za ki tafi ba ai da na fito da ke na kai ki gida, don zaman da na yi jiran nake ku tashi daga taron na mayar da ke gida da kaina." Murmushin ƙarfin hali na yi na ce. "Babu komai ma ai Alhaji, na gode." Ya ce. "To mu je mu sauke ki ko? Sai mu ƙarasa tattaunawa a cikin motar." Cikin ɗaurewar kai na ce. "Tattauanawa kuma akan me? Na ɗauka ai Aunty Billy ce ta ba ka saƙo ka kawo mini?" Yana gyara tsayuwarsa ya ce. "Saƙon kaina ne ya kawo ni ba na Bilki ba, hasalima ba ta san zan biyo ki ba." Waro ido na yi kawai don na rasa abin cewa. Ci gaba da magana ya yi da faɗin. "Tunda kuka shigo na yi tozali da ke gabaɗaya na rasa sukuni, kuna fita na kira ɗaya daga cikin yarana na gidan na yi masa kwatancenki na ce ya sa mini ido a kanki, shi ya sanar mini da fitarki yanzu, a gaggauce na biyo bayanki don kar ki tsere mini, Allah ya taimake ni muna fitowa na ga lokacin da kike hawa napep, shi ne muka biyo bayanku." Cikin ruɗewa don ba gama fahimtar abin da yake nufi na yi ba na ce. "Akan me to? Ni fa matar aure ce." Murmushi ya kuma yi ya ce. "Wannan ba matsala ba ce, kawai yardarki nake nema, sai mu dinga komai a sirrance. Zan wadata ki da kuɗi, na siya miki motar hawa duk irin wacce kike so, sannan zan dinga yi miki komai da kike buƙata, matuƙar kika amince da ni." A gigice na ce. "Wacce irin mu'amala za mu yi alhalin ina matar aure? Ka fahimtar da ni har yanzu ban gane mai kake nufi ba." "Calm down Baby, na ga duk kin ruɗe, ba wani abin wahala ba ne ba fa, kawai na gan ki na ji kin mun ne, kin tafi da hankalina sosai da ba zan iya haƙura da ke ba. So I decided kawai duk lokacin da nake gari zan kira ki sai mu haɗu a hotel, mu yi some hours na sallame ki, ki wuce gida, ba kwana za ki dinga yi ba tunda kin ce kina da aure." Wani jiri na ji yana kwasa ta, don duk da bai fito ƙarara ya bayyana mini ba, na gane me yake nufi. Kallon shi kawai na tsaya ina yi, ga shi dai mutum har mutum cikin kaya na kamala amma bai da halin arziƙi ashe. Girgiza kai na yi na ce. "Ba haka nake ba Alhaji, kuma gaskiya ba zan iya abin da kake nufi ba." Murmushi ya yi bai ce komai ba ya zaro wani kati ya miƙo mini tare da faɗin. "Ba zan tursasa miki sai kin amince a yanzu ba, amma ga card ɗina nan, ki je ki yi shawara, abin da kika yanke sai ki kira ni ki sanar mini. Ki ba ni account number ɗinki yanzu na saka miki 1 million ki saka kati." Zaro na yi tare da girgiza kaina, ba tare da na karɓi card ɗin ba na ce. "Ban da account." Daga haka na juya cikin sauri na shige napep ɗin tare da baiwa direban umarnin ya ja mu tafi." Bai yi musu ba ya kunna ya ja muka bar gurin. Har muka je gida zuciyata bugawa take, gabaɗaya kaina ya kulle, mamaki da al'ajabin mijin Aunty Billy sun suka kashe ni. Gefe guda kuma ina ta jinjina million ɗayan da ya ce zai ba ni wai kawai na saka kati da ita? Lallai ba ƙaramin kuɗi ne da shi ba, sai dai babu halin ƙwarai. A ƙofar gidana na tarar da Naja a tsaye tana latsa waya. Da mamaki nake duban ta bayan na sauka daga napep, har na ƙarasa kusa da ita ba ta ɗago ba, ga dukkan alamu ba ta gane ni ba duk da akwai wutar nepa. Fuskata babu walwala na ce. "Ga ni, sai ki faɗa mini abin da za ki mini da kika azalalo ni na taho." Ta ɗauki sakanni tana kallo na bayan ta ɗago kanta ba ta ce komai ba, sai can ta numfasa ta ce. "Hafsah ke ce a haka mayafi a gefen kafaɗa? Ba da ban kin yi magana na shaida muryarki ba da ko bangaza ta kika yi ba zan gane ki ba, saboda yadda gabaɗaya kika canza." Jujjuya jikina na yi na ce. "Ya ranki?" Ta jijjiga kai sannan ta ce. "Sai da kika je taron kenan?" Na ce. "Na je ɗin." "Me kika ƙaru da shi to don Allah ?" Ta yi maganar cikin takaici. "Abubuwa da yawa mana, na je na ga masu kuɗi na shiga manyan gidaje, ko banza na kafa tarihi, ga kayan ƙawar da aka ba ni na saka a jikina, ban da haɗaɗɗen abincin da na ci da wanda na yo guzurinsa." Kallo na kawai take yi kamar wadda na canza mata, tsaki na ja na ce. "Kin saka ni a gaba da kallo, wai mene haka ne?" A sanyaye ta ce. "Babu komai, ga shi nan kuwa kin yi kyau abinki." Sarƙar wuyana na riƙo ina jin kaina ya ƙara kumbura na ce. "Kayan kyan ne suka saka na yi kyan ai, har da sarƙar gold fa." Kama haɓa ta yi ta ce. "Allah ya ƙara arziƙi Hajiya Hafsah, ni dai abin da zan faɗa miki duk daular da za ki je ki gano kar ki ƙara raina ƙoƙarin Anas, arziƙi ne a rayuwa kowa da yadda Ubangiji ya ga da ma ya ba shi, ke kina hangen wasu, wani kuma yana can yana hangen ki, yana cewa da ma shi ne ke." Baki na taɓe na ce. "Kuɗi abin so ne fa, ba zan taɓa daina son irin rayuwar ƙawayena da fatan kasancewa kamar su ba har abada." Ta ce. "Tom shikenan, amma ki sani hakan tamkar yake da ki ɗauki wuƙa ki daɓa wa cikinki ne, matuƙar kina tare da waɗannan matan da ba ajinki ba ne, saboda rabuwa da su shi ne kawai masalaha a gare ki." "Abin da ba zai taɓa yiyuwa ba kuwa kenan." Na faɗa cikin haƙiƙancewa. Gyaɗa kai ta yi ta ce. "Allah ya taimaka, ga fili ga mai doki." "Saura sukuwa mai kyau in sha Allah." Na faɗa cikin tarar numfashi. Murmushin takaici ta yi ta ce. "Ni zan wuce, da ma so nake na tabbatar da kin dawo kafin na tafi, don ba na son na ƙara jin kunya a gurin mijinki, jiya na gama yi masa daɗin bakin kin canza amma kika ba ni kunya, ya zo yau ya tarar ba ki dawo ba." Cikin gatse na ce. "Allah ya kiyaye." Daga haka na buɗe ƙofar gidana na shige. Naja ta bi ta da kallo kawai, cikin ranta tana addu'ar Ubangiji ya dawo da ƙawar tata cikin hayyacinta da gaggawa, don ta ga alamar ta yi nisan da ba ta jin kira. Ba ta bar ƙofar gidan sai da ta kira Anas ta sanar masa dawowar da Hafsah, ta kusa awa biyu a zaune a ƙofar gidan kafin Hafsah ta dawo, saboda hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba idan ba ganin dawowarta ta yi ba, saboda ba ta son Anas ya ƙara zuwa ba ta dawo ba, don ta san hakan zai iya ƙara janyo musu wata matsalar. Ita kuma abin da take gudu kenan, ba ta son ƙawar tata ta yi rashin nagartaccen miji, shi ya sa ta ɗaukar wa kanta alƙawarin duk yadda za ta yi wajen ganin ba su rabu ba za ta yi iya yin ta da yardar Allah. Ina shiga cikin gida ana ɗauke NEPA, wani irin ƙunci da takaici ne suka cika ni, na tuno tunda na je gidan Maman Nasmah ko motsi wutarsu ba ta yi ba, haka ma gidan Aunty Billy. Tsaki na yi na zaro sabuwar wayata na kunna fitila na haska gidan. Kayan hannuna na fara kaiwa kitchen sannan na shiga toilet na yi alwala na yi Sallah. Bayan na idar na zauna bitar abubuwan more rayuwar da na gano, babban abin da ya fi burge ni yadda idan mutum zai shiga unguwar su Maman Nasmah sai an tsayar da shi a bakin gate ɗin ginin da ya zagaye unguwar, an tambaye shi gidan wanda zai je ya kira shi sun yi magana da security ɗin. Sabga cikin mutunci da arziƙi dai. A cikin gidanta kuwa babu wani abu mara kyau da ƙayatarwa, toilet kaɗai ya isa ɗauke wa mutum dukkanin damuwarsa saboda tsananin kyansa, ga fanfon ruwan sanyi daban na ruwan zafi daban. Gabaɗaya yanzu da na gan ni

Chapter 9 of 24