Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [3/8, 12:45 PM] Bahaushiya👍: *YI WA KAI* *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) MIKIYA WRITERS ASSOCIATION 1 Iskar hadarin dake kaɗawa ba ta saka na yi yunƙurin tashi don kwashe abubuwan dake tsakar gidana ba, saboda gudun kar ruwa ya sauko. Ina nan zaune kamar an dasa bishiya ban ko motsa ba, ina ta kuncewa da saƙa yadda za a yi ni ma na zamo ɗaya daga cikin fitattun mata na wani group ɗin WhatsApp da nake ciki. Ganin wankin hula yana ƙoƙarin kai ni dare ya sa na sauke wani wahalallen numfashi tare da miƙewa na fara kintse-kintse. Ina yi ina tunanin da wani hamshaƙin mai kuɗin nake aure ko gida mai tsakar gida ba zan yi rayuwa a cikinsa ba, bare na yi fargabar kar ruwa ya taɓa mini abubuwan amfani. Bayan na gama na shiga ƙaramin falona na zauna na kishingiɗa akan kujerar zaman mutum biyu. Kallon ko ina nake yi a ɗakin ina bitar kayan cikinsa kamar ba nawa da na saba gani kullum ba. Kujeru ne kawai saiti da labulaye, sai ƙaramar TV ta ƙasa. Ban san lokacin da na ja wani dogon tsaki ba lokacin da hoton wata Hajiya da ta turo ɗazu ya faɗo mini a rai, wanda aka ɗauke ta a gaban tamtsamemiyar TV'n bango dake cikin wani rantsatstsen falo. A karo na barkatai cikina ya murɗa saboda yunwar dake ƙwaƙular hanjina, tsabar karanta wasiƙar jakin da na tsaya ina yi ko abincin rana ban ci ba, ga shi Magriba ta kawo kai. Ba don son raina ba sai don ban da zaɓi na miƙe na zubo shinkafa da waken da na girka na zuba mata mai ishashshe, ga salad da tumatir a gefe da yajina da ya ji magi. Cikin takaici na fara cakuɗa ta ina keɓe fuska kamar na ga kashi. "Ko ɗan kifi babu akai balle ƙwai." Na faɗa a fili ina tuno haɗaɗɗun girkunan da matan group ɗin nan suke turowa, wanda yake wadatuwa da lafiyayyen nama. A maimakon kidahumar ƙwaƙwalwata ta tuno mini waɗanda ba su da shi, waɗanda da za su gan ni za su ce dama ni ce su, waɗanda kullum suke kwana su tashi da fargabar abin da za su ci. Haka na tuttura abincin na tashi na je na kwanko hannuna, ina ƙoƙarin komawa ɗaki yarana maza guda biyu Sultan da Safyan suka shigo da gudu bakinsu ɗauke da sallama. Bin su na yi da kallo ganin yadda uniform ɗinsu ya yi datti, komai dare ko gobe da safe sai na wanke musu kafin su kuma sakawa. Hasasowa na yi da matar mai kuɗi ce ni kamar matan cikin group ɗin nan da sai dai masu wanki su wanke musu. Cikin rige-rige suka zo suka rungume ni kowa na ƙoƙarin karanta mini abin da aka koya musu a islamiyya. Zare su na yi daga jikina, cikin tsawa da zare ido na ce. "Mene haka? Ba ku da hankali ne?" Bi na kawai suka yi da ido don hakan baƙon al'amari ne a gare su. Ni kuwa gare ni haushin mahaifinsu da nake ji ne ya shafe su, na baƙincikin bai zo a mai kuɗi ba. Ina shiga ɗaki suka biyo ni jikinsu duk a sanyaye. Kamar yadda mahaifinsu ya horar da su idan sun yi mini laifi su ba ni haƙuri haka Sultan ya dube ni ya ce. "Mami mun yi miki laifi ne? Ko gudun da kika hana mu muka yi ne ya ɓata miki rai?" Kallon shi na yi kafin na yi magana Safyan ya riga ni da faɗin. "Ni ban yi ba Mami, Yaya ne ko?" Numfashi na sauke tare da janyo su jikina na ce. "Kuna yi wa Abba addu'ar Allah ya ba shi kuɗi mu koma ƙaton gida kuwa?" Bi na da ido kawai Sultan ya yi, Safyan ne ya ce. "Irin gidansu Zuhura?" Da sauri na ce. "Eh, ko ba kwa so?" Sufyan ya ce. "Muna so." Shafa kansa na yi ina murmushi na ce. "Yawwa yaron kirki, mu ma mu zama ƴan gayu yanda mutane za su dinga sha'awar mu, mu dinga cin abinci kullum da nama da kaji." Cikin tsallen murna ya ce. "Eh Mami." A hankali Sultan ya ce. "Mami amma da ba kya cewa mu yi wannan addu'ar, haka kawai kike cewa mu ce Allah ya buɗa wa Abba." Na ce. "To yanzu ku fara, don in ma bai yi kuɗin ba barin shi za mu yi mu je mu samu wanda zai kai mu ƙaton gidan, don ba zan ci gaba da rayuwa a wannan akurkin ba." Bi na kawai suka yi da kallo don ba su gane abin da nake nufi ba. Bayan na cire musu uniform na zuba musu abinci suka fara ci na fita na ɗauro alwala na dawo parlour'n don tayar da Sallah. Ina tsaki na kunna torchlight ƴar madaidaiciya wadda ake yi mata chaji saboda babu Nepa. Cikin raina ina tunano yadda matan cikin group ɗin nan suke labarin kodayaushe suna samun Nepa a unguwanninsu, saboda ta masu hannu da shuni ce, idan ma an ɗauke za a tayar da inji ko kuma a kunna solar. Idar da Sallahta ya yi daidai da shigowar kira cikin wayata. Sultan ne ya miƙo mini na karɓa na duba mai kiran, ɗaya daga cikin members ɗin group ɗinmu ce ta kira ni, wadda muka fi mutunci da ita saboda sunanmu ɗaya. Ɗagawa na yi tare da yin sallama. Ba ta amsa ba saboda maganar da take yi, daga yadda na ji tana bayar da umarnin a kwashe kajin da mijinta ya zo da su a saka a fridge na san da mai aikinta take. Wani yawu na haɗiye tare da tambayar kaina yaushe ni ma zan gan ni a wannan level ɗin? "Namesake." Na ji muryar Maman Nasma ta faɗa. Cikin fara'a kamar tana gabana na ce. "Na'am, kin gama maganar ne?" Ta ce. "Eh, ya gida? Ya sa Sultan da Dad ɗinsu?" Na ce. "Duk suna lafiya, ya su Nasma da Abul?" Ta ce. "Alhamdulillah, yanzu ma suka hau sama gurin Dadinsu, ya dawo sun tafi karɓar chocolate." Na ce. "Ayya." Kawai. Ta ce. "Ban gan ki online ba ne, na ga kuma an ci gaba da gabatar da kai a group kowa yana turo pic ɗinsa da na yara, shi ne na ce bari na taɓo ki na ce ki zo ki ba mu naki, na san yadda muryar nan taki take da zaƙi zankaɗeɗiyar mace za mu gani." Yaƙe na yi na ce. "Toh shikenan, bari na hau yanzu na tura, su Safyan ne suka dawo daga islamiyya na tsaya sallamar su, da na gama na yi Sallah, shi ya sa ban hau ba." Daga haka muka yi sallama na katse wayar. Shiru na yi ina jujjuya ƴar akwalar wayata a hannuna, wadda kuɗinta ko dubu ashirin ba zai yi ba. Uzurin da na ba wa Maman Nasma ba shi ya hana ni hawa online ba, chaji ne ishashshe ban da shi, kuma ba tabbas ɗin kawo Nepa, ga fitilarmu idan chaji ya ƙare sai dai na koma haskawa da ta wayata. Dogon tsaki na ja cikin takaici na kunna data, direct WhatsApp na shiga cikin group ɗin *Zumuncinmu* na fara kallon hotunan da aka tutturo, hannuna har rawa yake gurin bubbuɗewa. Zuƙa-zuƙan mata kawai nake gani a haɗaɗɗun background, na wannan yana wane na wannan. Na ga yadda ake ta wow wow tare comments. Fita na yi na shiga gallery na fara duba nawa hotunan da na yarana wanda duk aka yi su da wayar hannuna, sai na gan mu wasu dususu kamar almajirai. Jinjina kai na yi na ce. "Taɓɗijan! Yanzu ta yaya zan tura wannan hotunan? Ai ko karen hauka ne ya cize ni ba zan soma ba." Ficewa na yi na koma WhatsApp na shiga group ɗin, tagging ɗina na ga an yiyyi akan na tura nawa, don sun gan ni online. Cikin tsinkewar zuci da sanyin gwiwa na ce zan tura musu yanzu, bayan na bibbi pictures ɗin da aka turo da. 'Masha Allah.' Direct ta group ɗin na shiga gallery na fara bin pics ɗin cikin wayata ɗaya bayan ɗaya, akan na wata ƙawata da muka yi secondary school tare da take auren mai kuɗi na tsayar da idona. Tana sanye cikin abaya mai kyau a gaban ka'aba, a ƙasa mai tsarki aka yi mata hoton, last zuwan da suka yi Umrah da mai gidanta ne ta turo mini hoton. A take zuciyata ta ba ni umarnin na tura musu shi kawai na ce ni ce, ba tare da nazari ko tsoron abin da zai je ya dawo ba na danna shi ya cika screen ɗin wayar. "To ni ma ga ni, ina yi wa kowa fatan Alkhairi." Na rubuta caption da haka tare da turawa.......✍️ *Zeey Kumurya*✍️ [3/8, 12:45 PM] Bahaushiya👍: Drama section ko comment section ba a tura littafi can comment kawai da surutu za a zuba https://chat.whatsapp.com/J0sit2lZquWHwDxJaARjR3 *YI WA KAI* MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION *BRIGHT PENS* (FREE BATCH) 2 Dif! Wayar ta ɗauke babu chaji, dogon tsaki na ja na dangwarar da ita a kan dardumar da nake kai. Dama na san hakan za ta iya faruwa, shi ya sa na ƙi hawa online ɗin tun ɗazu. "Mamy me ya faru kike ta tsaki yau?" Cewar Sultan da ya miƙe da plate ɗin abincin da suka gama ci a hannunsa. A kufule na ce. "Ubanka ne Sarkin tambaya ɗan gidan tanbai." Cikin rawar murya kamar zai yi kuka ya ce. "Ki yi haƙuri don Allah." Ban ce komai ba amma jikina ya yi sanyi, miƙewa na yi na ce. "Ku je ku yi alwala ku zo ku yi Sallah, kar ku manta da addu'ar da na ce ku yi wa Abba kun ji yaran kirki." Gyaɗa mini kai suka yi suka fice a tare bayan Safyan ya ɗaukar musu fitila. Kwanciya na yi a maimakon zikiri da na saba yi a irin wannan lokacin, na fara tunanin da ban san ranar gama shi ba, babban takaicina rashin sanin pic ɗin da na tura ya tafi ko bai tafi ba. A haka mijina ya shigo ya same ni. Duk da ban kalli fuskarsa ba amma na san ɗauke take da murmushin da yake shigowa da shi a kullum, a zuci na amsa masa sallamar da ya yi, saɓanin da da nake tashi da hanzari na tarɓe shi. Kunna torchlight ɗin wayarsa keypad ya yi yana faɗin. "Ina ƴar aljannar tawa take ne?" Harara na zabga masa a duhu tare da jan tsaki a zuciyata na rufe idona, cikin raina ina tambayar kaina me ya rufe mini ido lokacin da ina budurwa na amince na aure shi? Ban kai ga ba wa kaina amsa ba na ji yana faɗin. "Subhanallahi! Hafsah ba dai ba ki da lafiya ba?" Saboda in dai ba cuta nake ba, ba ya taɓa zuwa ya tarar da ni a kwance a irin wannan lokacin. Buɗe idona na yi tare da tashi zaune kamar an yi mini dole na ce. "Sannu da zuwa." "Yawwa, me yake damun ki?" Ya yi maganar yana taɓa goshina, muryarsa da alamun ruɗewar da yake yi a duk lokacin da ban da lafiya. Ture hannunsa na yi na ce. "Babu komai." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Kin tabbata my love?" Wani kallo na yi masa tare da faɗin. "Sai aukin soyayya amma babu ko sisi." Yadda na yi maganar dama na san ba zai ji abin da na ce ba. Zama ya yi a kusa da ni yana ƙoƙarin janyo ni jikinsa ya ce. "Ban ji me kika ce ba." Na ce. "Cewa na yi ƙalau nake." Ya ce. "Amma me ya sa na gan ki a haka? Don Allah ki faɗa mini idan ba ki da lafiya mu je chemist ɗin Kamilu ya duba ki." "Lafiyata fa ƙalau." Na faɗa cikin zunɓura baki. Tsayawa kawai ya yi yana kallo na, daga baya ya sauke numfashi ya tashi ya fita daga falon. Raka shi na yi da wani mugun kallo, a fili na ce. "Wai chemist? In ma cutar nake da gaske ba za a kai ni asibiti ba sai wani chemist." Ranar da su Maman Nasma suke zancen family doctor a group ce ta faɗo mini a rai, ƙwafa na ja na koma na kwanta ina wadaran auran talaka a cikin raina. Ina jin shi suna ta hira da ƴaƴansa a tsakar gida, suna biya masa karatun da aka yi musu a makaranta, yana gyara musu inda suka yi kuskure. Tare suka je masallaci suka yi sallar isha'i. Bayan sun dawo ya ƙara tisa ni a gaba da tambayar abin da yake damu na cikin kulawa, banza na yi da shi na juya masa baya. Ya bar ni na ji da rashin chajin wayata ma amma ya bi ya ishe ni, na san yanzu ana can ana ta shan hira a group. Gabaɗaya sai ya tashi hankalinsa, ya dinga lallaɓa ni da roƙon na faɗa masa idan wani laifin ya yi mini ya ba ni haƙuri, sai da na gaji da magiyara sannan na ce masa gajiya ce kawai take damu na. Ko rufe baki ban gama yi ba ya tashi ya ɗauko mini maganin gajiya da ruwa a cup ya kawo mini na sha, sannan ya ce su Sultan su mammatsa mini ƙafata shi zai fita ya wanke musu uniform da takalma. Sai da ya yi wanke-wanken kwanukan da muka ɓata ya dawo ɗakin. Sannu ya yi mini tare da faɗa mini abubuwan da ya yi, na ɗaga masa kai kawai cikin ƙosawa. Bai zauna ba ko ya nemi abinci ya kama su Safyan ya yi musu wanka shi ma ya yi. Ya kai su ɗakinsu ya shirya su ya kwantar da su. A lokacin aka kawo wutar nepa, cikin tsananin farinciki na miƙe na rarumi wayata na nufi socket na soka chaji. Daidai lokacin ya dawo falon yana faɗin. "Bari na goge wa su Sultan uniform ɗin da na wanke yanzu, da safe kin huta aikin ya yi miki sauƙi, ga ruwan wanka can na haɗa miki, ko ba za ki iya zuwa toilet ɗin ba na kai ki?" Kallon shi na yi ba yabo ba fallasa na ce. "Zan iya, ka zo ka ci abinci, na ga tunda ka dawo ko ruwa ba ka sha ba." Ya ce. "Zan ci ne, so nake na gama duk ayyukan don gobe ki samu hutu da bacci ishashshe, kar gajiya ta ƙara damar mini ke." Taɓe baki na yi a raina na ce. 'Hutun ai na banza ne tunda ba a gidan da ya amsa sunan gidan hutu nake ba.' Daga haka na miƙe na fice daga falon. Bayan na fito daga wanka na zarce ɗakin baccinmu, ina cikin shiryawa na ga wata ƙaramar baƙar leda a kan mudubi. Ɗauka na yi na duba abin da yake cikinta, biscuit ne ɗan goma-goma guda biyar da alawa ita ma guda biyar ɗin. Na su Sultan ne da yake siyo musu kullum, idan za su school na ba su bibbiyu, islamiyya ma haka. Taɓe baki na yi na mayar na ajiye. A fili na ce. "Aikin kenan, kullum siyayyar yara ba ta wuce ta Naira ɗari, wasu kuwa komai katan-katan ake dire wa ƴaƴansu, abubuwa masu tsada ma ba ƴan goma da biyar ba." Har na gama shirina ban daina mita ni kaɗai a cikin raina ba, don ban da wani buri a duniya a yanzu da ya wuce na buɗe ido na gan ni a cikin ƙaton gida, mai ɗauke da komai na kayan alatu da abubuwan more rayuwa irin wanda matan cikin group ɗinmu suke ciki. Idona gabaɗaya ya rufe, babu abin da ƙwaƙwalwata take ganewa sai wannan tunanin. Da na koma falo ko sannu ban yi wa Anas ba na zauna na janyo wayata na kunna. Hakan bai hana shi duba na ba cikin murmurshi tare da faɗin. "Kin yi kyau autar matana." Haɗe rai na yi na ce. "Ka faɗa ne kawai don na ji daɗi, amma ka san ba a kyau sai da kayan kyau." Cak ya tsaya da gugar da yake ya zuba mini ido, cikin wani irin yanayi ya ce. "Me yake damun ki ne yau Hafsah? Ban gane me kike nufi da wannan maganar ba? A da idan na ce kin yi kyau murmushi kike yi tare da yi mini godiya ki kuma ba ni tukuci da abin da kika san ina matuƙar so." Cikin ko in kula da yanayin da na gan shi na ce. "Lokacin ban gane halin da duniya take ciki ba ne sai yanzu." "Wanne hali kuma? Ai ƙara saka ni a duhu kika yi." Ya tambaya fuskarsa da alamun damuwa. "Ka ci gaba da abin da kake yi kawai." Na faɗa hankalina akan wayata lokacin da na shiga cikin group ɗinmu. Bai kuma magana ba ya ci gaba da gugarsa, hakan ya yi mini daɗi, don ko ya yi ma ba tanka masa zan yi ba. Chat ɗin da aka yi ba na nan na fara bi, na ga wanda ba su tura pic ɗinsu ba duk sun tutturo, nawa wanda na tura kuma bai tafi ba. Ban ce komai ba na fita daga cikin group ɗin, Na buɗe saƙon Maman Nasma da ta yi mini ta private. 'Takwara ina kika shige ne? Don Allah ki zo ki ba mu hoton nan naki, ko rawar ganin ki kike mana?' Na karanta abin da ta ce a cikin raina, reply na yi mata na tura, sai na ga bai yi tick alamar ya tafi ba. Kashe datata na yi na ƙara kunnawa amma still ya ƙi tafiya. Fita na yi na duba data balance ɗina, sai na ga ashe ta ƙare ne, dama tun yamma da na duba saura kaɗan. Dogon tsaki na ja na ajiye wayar. 'Kai bawa daga wannan sai wannan, Ubangiji ka raba mu da tsiya da talauci.' Na faɗi haka ƙasa-ƙasa tare da miƙewa na bar falon, ina ganin Anas yana bi na da wani irin kallo wanda na san na zallar mamakin sabbin ɗabi'un da bai san ni da su ba ne. Juyi kawai nake a kan gadona cikin rashin sanin mafita, ina tsoron kar na tura hoton Sa'adatu ƙawata na je wata ta san ta a cikin group ɗin, ko kuma tsautsayi ya sa mu haɗu da wata a zahiri ta ga ba ni ba ce. Ni kuma gaskiya ba zan iya tura hotona da na yi da wayata ba, saboda rashin fitarsa da rashin haɗaɗɗen background, sai yanzu nake jin daɗi ma da hoton bai tafi ba. Don duk waɗanda suka turo hotunansu kowacce da kyan ganin ta, alamun da manyan wayoyi suka yi ba jagwal irin tawa ba. 'Ko dai gidan Sa'adatun kawai zan shirya na je gobe ta yi mini hoton a gidanta na tura musu?' Na tambayi kaina cikin tantama don na san ba lallai ya bar ni ba, saboda ban san me ya sa ba, ba wani son alaƙata da ita yake ba. Tashi zaune na yi ina bin ƙaramin ɗakin nawa da kallo, hoton wata Maman Fa'iz ne ya faɗo mini a rai, wanda aka yi mata a gaban mudubin ɗakinta, ta cikin mirror tamfatsetsan gadonta na ƙasar waje ya fito, ga ɗakin daga ga ni ƙato ne. Saukar da idona na yi a kan wardrobe ɗinmu, wadda na san a irin gidansu Maman Fa'iz ko a ɗakin mai gadi ba za a saka irinta ba. Komawa na yi na kwanta, saboda tsabar tunani kaina har wani juya mini yake yi. A lokacin Anas ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, na amsa masa ciki-ciki. Bai damu ba ya dube ni cikin kulawa tare da faɗin. "Ya kika kwanta kuma ba ki saki net ba? Duk da akwai Nepa ai sauro yana yawo." Na ce. "Zan saki ne." Yana sakin net ɗin ya ce. "Kin je kin tofa wa su Sultan addu'a ne?" Cikin ƙosawa da maganar tasa na ce. "Eh." Ya ce. "To bari na kakkashe ƙwaiƙwaye na zo mu yi magana, don wannan yanayin da kike ciki na san ba ƙalau ba my love." Baki kawai na taɓe ban ce komai ba, ya gama abin da zai yi ya hawo kan gadon ya ja ni jikinsa ya ce. "Don girman Allah ki faɗa mini abin da yake damun ki, wallahi ganin ki a haka gabaɗaya ya hautsina zuciyata." Na ce. "Ba komai fa, ka yi baccinka kawai." Ƙasa ya yi da murya kamar kodayaushe idan yana rarrashi na ya ce. "Ba ma haka da ke, kar mu fara a yau, kin san babu yadda za a yi na iya yin bacci kina cikin ɓacin rai, ko kun samu saɓani da wani ne ta waya? Na ga da tana hannunki kina ta tsaki." Hararar shi na yi na ce. "Ko ɗaya, tunda na ce maka babu komai ka ƙyale ni mana!" Shiru ya yi kawai, duk da duhu ne amma na san kallo na ya tsaya yana yi. Barin jikinsa na yi na koma can ƙarshen gado ina jan tsaki a cikin zuciyata. Don ni gabaɗaya gani nake shi ne matsalata, da ya zo a mai kuɗi ai da yanzu ba na cikin fargabar fita kunya a cikin group ɗinmu. Ina jin shi yana sassauke numfashi na yi banza da shi. Na san abu biyu ne ya haɗar masa, baƙon halin da na tsiro da shi da kuma tabbacin rashin samun haɗin kaina da zai yi idan ya buƙace ni, don ba ƙaramin tanadi ya yi wa wannan daren ba, saboda yau da safe na yi

Chapter 1 of 24