ce Allah shine sheda ta naje ɗakin Hajiya Hafsa dan yi mata sallama amma taƙi bude ɗakin har na gaji" jinjina kai yarima yayi gami da cewa "karka damu Abi dan bata buɗe ɗakin ta ba kaide kawai kaiyi ta addu'a Allah ya kauda fitina" jikin amace Abi ya ce "Allah yayi maka albarka ɗana" murmushi ya ce yanzu lokaci yana ja tashi muje ya faɗa cike da ƙwara-rawa Abin na shi guiwa tashi sukayi suka nufi ma'ajiyar motocin gidan yarima ne me tuƙa motar Abi kuma yana wajen ɗan zaman banza suka ɗauki hanyar Dorayi.
bayan wani ɗan lokaci suka isa Dorayi
misalin ƙarfe 12:00 dubban mutane suka sheda ɗaurin Auren Alhaji Saadiƙu Yahya da Zainab Yunus, ciki kuwa hada Alhaji Aminu mai kasuwa, Babban Aminin Alhaji Saadiƙu. bayan an kammala komai kowa ya watse.
ƙarfe biyar na yammaci aka kawo Amarya Zainab gidan Alhaji Saadiƙ, ƴar aikin gidan ce tayiwa ƴan kawo Amarya jagora zuwa ɓangaren Ammi, ɗaya daga cikin ƴan matan ce ta murɗa ƙofar ɗakin Ammi da niyar sushiga, abin mamaki ƙofar arufe haka suka ƙonƙwasa amma ba a buɗe ba, juyawa sukayi izuwa sashin Amarya basu daɗe ba suka gama abinda zasuyi suka bar gidan.
haka rayuwa taci gaba tafiya a kowane ɓangare babu sauyi wani lokaci farin ciki wani lokaci baƙin ciki,
Siyama da Aaminat suna zaune a ɗakin Anti suna hira Walid ya shigo da sallama "ya Aaminat kije inji Guda" rasss!!! rasss!! gaban Aaminat ya shiga faɗuwa, ta kalli Walid ta ce "kace bana garin kaji" dariya yayi gami da cewa "Banda abinki taya zan cewa mutumin da duk wani motsi naki ya sani bakya gari ya yarda bayan ya ganki ɗazu zaki shigo gidan nan" wani huci tayi gami da kallon Siyama, Siyama kuwa ta kauda kai gefe, "ki tashi ko nace mai kin ƙi zuwa yazo da kanshi" faɗar Walid, muzurai ta shigayi zuciyarta tana bugu ganin bata da mafita yasa ta tashi ta na cewa "shikenan tawa ta ƙare Abdul yaga zuwan Yarima jiya" Siyama ta ce nide babu ruwa na da rigimar ku da Abdul keda shi" Aaminat ta ɗan kalli Walid ta ce "dogon munafuki shine ka wani ɗakko tsawo ka tawo kirana" tintsirewa yayi da dariya ya ce "muje ya ce na tisa ƙeyarki gaba na kaiki har gabanshi" fitowa tayi yasa ta gaba suka yi waje, yana ƙofar gidan yaja ya tsaya yana jiran fitowar su, suna ƙarasowa ya kalli Walid ya ce "nagode ƙanina" murmushi Walid yayi bece ko mai ba ya tafi.
gyara tsayuwa yayi gami da zuba mata narkakkun idanunsa, yaɗan matsa kusa da ita sannan ya ce "Assalamu'alaiki" murya ciki-ciki ta ce "wa'alaikumussalam" murmusawa yayi kafin ya zuba hannayen sa cikin aljihun sa na wando ya ce "Aaminat gargaɗi nazo yimiki" dan da nan jikinta ya ɗau ɓari, ya kula da yadda Aaminat take shakkarsa kuma ya na matuƙar jin daɗin hakan,
ya ɗan shafa sumar kanshi kafin ya ce "daga yau se yau karki kuskura ki ƙara tsayawa da wani ɗa namiji idan har bani ba!!!!!! kuma ki sanarda wannan kucakin cewa na hanaki tsayawa da shi, karya ƙara zuwa inda kike in kuwa yazo to zansa a kusa rabashi da numfashin sa... ya ɗan tsagaita kafin yaci gaba da cewa "kuma idan na ƙara kiran wayarki kika ƙi dauka ko kika kara katse min kira to tabbas zan ɗauki tsatstsauran mataki akanki, wanda dagani harke bazamuji ɗaɗin sa ba!!!!!!" Siyama ce ta fito daga gidan cikin baƙin ciki da takaici tace "wai kai wana irin maye ne ance ba a sonka to ka haƙura mana tunda bata sonka ko ana dole ne!!!!!!!?????" wani lafiyayyan mari ya sakar mata, tayi saurin dafe wajen hawaye na zuba,
cikin tsananin bacin rai ya ce "Siyama inde akan Aaminat ne zaki iya kirana da abinda yafi maye muni bazan damu ba amma kuskure ne kice na haƙura da Aaminat dan kuwa bazan iya hakan ba..., Aaminat kuwa kuka take tana cewa "haba Abdulkareem a haka kake sona kana sani kuka kana ƙaramin baƙin ciki???!!!!! aduk lokacin da na haɗu da kai idan banyi kuka ba to sena share hawaye to wannan shi ne soyayyar taka iyee????!!!!" ta ƙarasa maganar cikin shashshekar kuka
©️INDO tare da SALMA AUTA
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 17
Abdulkareem ya ce "Ba haka nake so ba ke ce ba kya iya hana kanki kuka, amma ni kullu yaumin burina naga farin cikinki, sani ne ba ki yi ba amma na fi kowa jin zafin kukan nan naki."
Kasa magana ta yi ta cigaba da rera kukanta, Abdulkareem ya ce "Ki tafi gida, kuma ki kula da gargaɗina."
Dama jiran ƙiris take ya na faɗa zaizai ta wuce hanyar gidansu, Siyama kuwa ya na jiyowa kanta ta yi saurin juyawa za ta koma cikin gida, ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, juyowa ta yi kanta a ƙasa ta na wasa da ƴan yatsunta jikinta sai tsuma yake.
Ya ɗan matsa gaf da ita ya na binta da zara-zaran idanunsa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Siyama ki yi haƙuri ba a son raina na yi hakan ba, ina da zafin rai ne wani lokacin, kuma kin zo min da maganar da hankalina ba zai iya ɗauka ba, ba na jin akwai wanda zai iya sa ta farin ciki bayan ni, ni ne na dace da rayuwarta." ba tare da ta ɗago kai ba ta ce "Haka ne, ni na haƙura, amma ya kamata a ce yanzu Aaminat ta san gaskiya." Abdul ya ce "Na cika da fargabar abin da zai biyo baya shi yasa nake tsoron sanin nata, amma zan yi shawara." gyaɗa kai ta yi alamar eh, bai ƙara cewa komai ba ya juya itama ta shige gida.
Tagumi ta buga ta na tunanin irin shirmen da su ka tafka, Allah i sa komai ya zo da sauƙi shi ne addu'arta a halin yanzu.
Yarima
Cikin shirinsa ya fito Falo ya na tafiya ya na gyara zaman agogon hannunsa, muryar Yayarsa Raheena ce ta sa ya fara slow ya na zazzare ido, idanunsa su ka sauka akanta suna tsaye ita da Ammee su na tattaunawa Khausar Ƴarta ta na gefe ta coge ta na danna waya.
Ƙarasawa ya yi gurin cikin sanyin jiki Zuciyarsa fal mamakin haɗewar da Ammee da Raheena su ka yi lokaci ɗaya saɓanin Da da Raheena ta fita daga sabgar kowa na gidan a cewarta Duk sun fi son shi akanta don haka ta yi fushi ta fitar da kanta daga cikinsu, amma yau sai gasu sun haɗe kai, Addu'a yake Allah i sa ba Kishiyar Ammeen su ke son cutarwa ba.
Lura da zuwansa ne ya sa su ka yi shiru da zancen da suke yi, Ammee ta kalle shi a fizge ta ce "Menene?" ya ce "Zan fita ne, Aunty Raheena yaushe ki ka zo?." a yatsine ta ce "Meye naka a ciki? ai gidan ubana ne ina da ƴancin zuwa a duk lokacin da naga dama." ya ce "Ba ina nufin wani abu bane, Allah i baki haƙuri, kuma dama ba ni na hanaki zuwa ba ke kika sa kanki." Ta buga tsaki kafin ta ce "Allah wadaran ɗan da yake zigawa a yiwa uwarsa Kishiya ni ban taɓa ganin irinka ba; ai ga irinta nan Ammee kun fifita shi a kaina yanzu ga abin da ya jawo miki nan."
Ammee ta rausayar da kai ta taɓe baki gami da cewa "Umm!! kin ga ranar Duniya, amma dai kinsan ni ina sonki ai Mahaifinku ne dama me nuna bambanci wai shi ya fi son Namiji." Yarima ya ce "A'a ba ruwansa fa Ammee wallahi itace kawai ta ɗorawa Zuciyarta haka amma shi dukkanmu ya na sonmu." a hantare Ammi ta ce "Kai dallah gafara shashashan da bai san ina ke masa ciwo ba, kai ai anyi Mahaukaci tinda har ka fifita wata akan Uwarka , ka je ka rungumeta nima ina da tawa ƴar."
Yarima ya kasa cewa komai ya yi gaba zungui-zungui Ammee da Raheena su ka rufa masa baya da harara, Khausar ma ta bi bayansa da kallo kafin ta zabga tsaki.
Raheena ta ce "Ni fa in fayyace miki gaskiyata Ammee na tsani Abubakar tin da ya zo Duniya na dena jin daɗin rayuwa, sai ma da na fita daga cikinku ne na samu nutsuwa, gashi duk wani abu da za ka yi masa don ya ƙuntata ba ya tasiri akansa." Ammee ta rausayar da kai gami da cewa "Uhm!! Allah i kyauta dai, Nima ai yanzu kinga ya yi min sabi da Namiji ɗan kunama ne, shi yasa ake cewa in ka haifi Namiji wata ka haifawa, yanzun haka kwalliyar nan da ya yi ya cokara hula in ba sa'a ba wajen wata zai tafi." Raheena ta yi tsaki gami da keɓe baki, har cikin ranta neman makasar Yarima ta ke yi don a cewarta shine duk wata damuwa ta-ta, ci gaba su ka yi da tattaunawa, sun daɗe a wajen kafin Ammee ta raka Raheena wajen Mota dama fitowa ta yi za ta tafi shine aka tsaya ana ƙara tattaunawa.
Yarima.....
a ƙofar gidansu Aaminat ya tsayar da motarsa, zazzafar iska ya furzar hankalinsa duk ya rarrabu kashi-kashi wani kan Aameenat wani kan Ammee da Raheena har ma da Abi da Matarsa wadda yake kira da Aunty Zainab ko Aunty. waya ya cira ya turawa Aaminat kira kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka gami da sallama, ya sauke ƴar ajiyar Zuciya sannan ya ce amsa sallama ya ci gaba da cewa "Na zo fa." da sauri ta ce "Ka zo??" ta yi tambayar ƙirjinta na bugun shalugude...
Ya ce "Kin manta na ce miki zan zo ne?" da sauri ta ce "A'a ban manta ba na zata dai ka fasa,, gani nan zuwa." ta na faɗen haka ta yi ƙitt ta kashe wayar, Yarima ya bi wayar da kallo ya na mamakin abin da ke damunta.
Cikin sauri-sauri ta ɗakko gogaggen Hijab ɗinta a sif ta saka ta fesa turare, ba ta saurari inda kayan kwalliya su ke ba bare ma ta yi tunanin za ta yi, cikin sauri ta fita ta na alla alla ta je ta bashi haƙuri tare da uzurin rashin lafiya don kar Abdulkareem ya ƙyalla ido ya gan shi.
A hanyar soro ta yi katari da Abba ya na ƙoƙarin shigowa, ta raɓe gefe cike da ladabi ta ce "Sannu da shigowa Abba." bai amsa ba sai ma cewa da ya yi "Na samu labarin wani ya na zuwa gurinki, to ki gaya masa wata ɗaya ya rage masa idan Aurenki zai yi ya fito a wata ɗayan nake so in aurar da ke." Zuciyar Aaminat ta bada Durummmmm!!!! Abdulkareem ne ya fata faɗo mata, ba shakka idan Abba ya ce dole a wata ɗaya zai aurar da ita ya jefata a masifa, Abba ne ya katse mata tunanin nata da cewa "Ko ba ki ji ba??" ta ce "To Abba in sha Allah zan faɗa." ya jinjina kai sannan ya wuce ciki, Aaminat ta yi waje cikinta ya na ƙugi da rugugi na tsoro.
Yau ma kamar kullum ya na tsaye a jikin mota ya na jiran fitowarta, kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake tare da yi masa sallama ya amsa ya na murmushin ƙarfin hali. shiru ne ya ɗan biyo baya na wani lokaci kafin ya ce "Mun gaisa da Abba ai." ta yi murmushi gami da cewa "Na ji daɗin hakan." Ya ɗan gyara tsayuwarsa kafin ya ce "Na zo kuma na yi shiru, hankalina ne duk ba a kwance ba, ni ba na son fitina wallahi ko yaya take." da ɗan mamaki ta ce "Fitina kuma?" ya ce "Aff! yi haƙuri don Allah wallahi abin da ya shafi cikin gidanmu ne kinsan mata da kishi kuma Abi ya yi sabon Aure." Aaminat ta rausayar da kai cike da tausayawa ta ce "Allah sarki, am..um... dama ni kam zan ce maka ka yi haƙuri yau ba ni da lafiya ne so na ke na yi sauri naje na kwanta." "Subhanallah! me ke damunki? ai ba kwanciya ya kamata ki yi ba magani ya kamata ki sha. ido ta zaro a ɗan razane, har ga Allah ta manta cewa shi ɗin likita ne take neman jibga masa ƙaryar rashin lafiya, Yarima kuwa ya kafeta da idanunsa da su ka fara kawo ruwa, cikin inda-inda ta ce "Au..ai..am. dama fa ba wata rashin lafiya ce me girma ba da zarar na yi bacci shi kenan, don Allah ka yi min uzuri, amma kafin haka dole ne in isar maka da saƙon Abba, ya ce in gaya maka indai Aurena za ka yi to ka turo manyanka su yi magana." ta ƙarasa maganar kanta a ƙasa cikin ɗan jin kunya.
Yarima ya ja numfashi kafin ya ce "Aaminat! nima ya gaya min haka kuma ya ce nan da wata ɗaya yake so komai ya faru, Aaminat ki yi haƙuri da jin abin da zan gaya miki, ki ɗauka hakan ƙaddararmu ce baki ɗaya." Ɗan numfasawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Ba ni ne asalin Masoyin naki ba Abdulkareem ne!" rasss gabanta ya faɗi ta yi zaram ta ɗago kai ta zuba masa idanu cike da rashin fahimta, ya gyaɗa mata kai cike da son tabbatar da gaskiyarsa, "Abin da kunnenki ya ji shi na faɗa, Abdulkareem Aminu Mai Kasuwa, yaron da ki ke rainawa ba ki ɗauka a matsayin Namiji na shine ya turo ni gareki, na yanke hukuncin faɗa miki ba tare da ya sani ba domin dole-dole wata rana gaskiyar za ta fito kuma ko ba haka ba ma a yanzu ake buƙatar hakan domin shi Abba mijinki yake nema ba ɗan Aike ba." tasssss!! Aaminat ta wanke shi da mari cikin kuka ta fara magana "Ashe kai mayaudari ne macuci maci amana?! me na yi wa maza ne da suke son tarwatsa rayuwata? shin menene laifina a Duniyar nan da ƙaddarata ta fi ta kowace mace muni? ashe kai ma ba so na kake ba ashe kai ma yaudara ce ta kawo ka gareni!! Kaicona, ni dai ban yi sa'ar zuwa Duniya ba.
Marin da ta yi masa ne ya bawa hawayen da suka cika kwarmin idonsa damar zubowa ya dafe kumatunsa ya na binta da idanunsa wanda su ke masa suya tamkar an watsa masa gaurashi. sai da ta gama magana sannan ya samu damar motsa bakinsa ya fara cewa "Idan ki ka ce haka kin butulcewa Allah gami da ni'imominsa gareki, ke zawarci kawai ki ka yi amma wata tin tana ƴar ƙarama aka keta mata haddi aka yi mata illar da ba wanda zai yi sha'awar aurenta, wata kuma sai da ta girma ta na burin samun miji na gari aka keta mata haddi ƙarshe ki ganta har da Ɗa bayan ba ta taɓa aure ba, wata kuma ta na so ta yi Auren amma har shekarunta su wuce ƴan-matanci ta koma babbar mace Allah bai kawo mata mijin Aure ko da sau ɗaya ba, amma duk da haka Aaminat ki ce taki ƙaddarar ta fi ta kowace mace muni?? shin kinsan adadin dubban Matan da suke jiran zuwan Namijin gaske irin Abdulkareem cikin rayuwarsu? tabbas Aamimat samun miji nagari kamar Abdulkareem a zamanin nan sai an tona, shine me sonki da gaskiya me son farin cikinki ko da kuwa shi zai kwana da baƙin ciki, ya na son ganin dariyarki ko da shi zai kasance ya na kuka a koda yaushe;, Aaminat wallahi ni kaina da na shigo rayuwarki ba don ni shaida ne akan irin son da yake miki ba da ban fara aikata hakan ba, ya so share miki hawaye da tafukan hannunsa amma kin ƙi amincewa kuma ya san kina buƙatar temako hakan ne ya sa ya turo ni gareki, idan ba ki manta ba a ranar da ki ka fara ganina na gaya Hajiya Maimuma cewar na zo ganin wani Patient ne , ba kowa bane face ke, Asibitin Aminu Abdallah mallakin Abdulkareem ne da sunansa aka gina shi kuma ya zaɓe ni a matsayin Babba me kula masa da Asibitin,, shi ɗin Ogana ne kuma Abokina, Babana Abokin Babansa ne; ya gujewa Abinci ya sa kansa a damuwa ya jawowa kansa Cuta duk sabi da ke, yana bala'in tausayinki; Aaminat na roƙe ki ke ma ki tausaya masa ki jiƙansa ko da sau ɗaya ne ki nuna masa Halacci, ki ƙaunace shi ko da Zuciyarki ba ta so, shi ɗin mutum ne me sauƙin kai kuma ya na sonki, za ki yi farin ciki indai har ki ka zaɓi rayuwa da shi, amma in ki ka bari kika rasa shi tabbas kin tafka asarar da ba za a iya kwatanta ta ba, wannan shine saƙona na ƙarshe a gareki Aaminat!,, ni kuma da na zo miki a matsayin ɗan yaudara ki yi haƙuri ki yafe min ba don halina ba." ya ƙarasa maganar ya na shashshekar kuka kamar ba namiji ba namijin ma Garƙeƙen saurayi.
Ba iya suma ko mutuwar tsaye ba in da gaba da nan Aaminat ta gama kaiwa, idanunta ne kawai ke zubda hawaye yayin da ta kafe su akan Yarima, gangar jikinta kuwa sun dena aiki don in ba ka saurari bugun Zuciyarta ba ba za ka ce mutum ce me rai da lafiya a tsaye ba.
*©️INDO Tare da SALMA AUTA*
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 18
Yarima ya ƙara da cewa "Ki kasance me ɗaukar ƙaddara a duk yadda ta zo miki, ba komai ne ake so kuma a samu ba, ita rayuwa ta gaji haka, ina yi muku fatan Alkairi." ya na gama faɗen haka ya juya ya shiga Motarsa ya ci gaba da tafiya ya nufi gidan su Abdulkareem.
Umar ne ya ƙaraso kusa da Aaminat da ke tsaye cokam ta ƙi gaba ta ƙi baya, "Wuce ciki!" ya faɗa cikin sigar umarni, sai a lokacin ta ja dogon numfashi ta sauke tare da fashewa da kuka ta fara tafiya a hankali a hankali kamar karyayya.
a gefen Katifarsu ta zauna ta haɗe kai da guiwa ta ci gaba da rero baitin kuka, ba abin da take tunowa sai Abdul sama da ƙasa ya mamaye tunaninta a wannan lokacin.
Ba zato sai jin muryar Omar ta yi ya na cewa "Ke fa duk yadda ki ka ɗauki Duniya ba haka take ba, abin kuka ba ya yi miki wahala kamar wadda ba ta san ciwon kanta ba, ki na da dama amma kin ƙi amfani da ita ga ci gaba kina maida kanki baya tsabar kin san takan shiririta, duk fa ƙarancin shekarun mutum indai Namiji ne kawai ki sa a ranki Namiji ne, domin in azzalumi ne komai yawan shekarunki ko da kin yi sa'ar mamarsa ba zai yi duba da ƙarancin shekarunsa ba hakan zai zalumce ki kuma ya nuna miki ya isa ya kai a kira shi Namiji, babban kuskure ne Mata suke tafkawa na Raina ajin Maza da faɗa musu cewa ba su kai ba hakan ya na tunzura yara ƙananu su aikata abin da ba shikenan ba ƙarshe su barku da mugun tabo, amma ya rage naki ki yi shawara da Zuciyarki sai ki yanke hukunci."
Ya na kaiwa nan ya fice ya bata guri, ta bi bayansa da ido tsaiii, ta daɗe ta na kallon ƙofa ta na tunani iri-iri kukan ma ba ta san lokacin da ya ɗauke ba, gajiyar da ta yi da zama ya sa ta zamewa ta kwanta ta ci gaba da tufka da warwara.
Yarima
a harabar gidan ya tsaya ya turawa Abdulkareem kira, ya na ɗauka ya ce "Likita Bokan Turai." murya a cunkushe Yarima ya ce "Abdul ina Parking Space ɗinku ka zo ka sameni in kana gida." rasss gaban Abdul ya faɗi sabi da jin muryar Yarima sak irin ta wanda ya ci kuka ya ƙoshi.
Tashi ya yi ba tare da ya ce ƙala ba ya zabari silifas ɗinsa ya na jin Nana Khadija ta na tambayar inda zai je ya yi mata banza.
Yarima ya na tsaye jikin Motarsa ya jingina hannunsa ɗaya harɗe a ƙirjinsa ɗayan kuma ya na kan ɗayan ya tallafo haɓa da shi.
Abdul har shirin tuntuɓe yake wajen ƙarasowa inda Yarima yake, ko tsayawa bai ba ya ce "Lafiya kuwa Yarima?" ya girgiza kai gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya Sannan ya ce "Ba zan ce lafiya ba, Mahaifin Aaminat ya na buƙatar Aurar da ita cikin wata ɗaya ya nemi iyayen Masoyinta, ni kuma ban yi ƙasa a guiwa ba na gaya mata gaskiya domin rufewar shine kuskuren." tamkar Mutum ya yi gware da Babbar Mota Gingimari haka maganar Yarima ta zo wa Abdulkareem, cikin rawar baki da rashin sanin abin yi ya ce "Yanzu kana nufin ta san ni na turaka gurinta??, kuma a wata ɗaya Abba yake son aurar da ita? anya baya shan wani abu kuwa? ko an ce masa haka ake auren sama taka?" Yarima ya ce "Ya yi bazata kuwa, amma a shawarce wannan dama ce ta sameka ka san yadda za ka yi ka aureta don ba na so ka rasata, idan aka ƙara kawo min kai ba lafiya Allurar Dogon bacci zan yi maka ka yi shekara baka farka ba kowa ya huta da rigimarka." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, Abdul ya ce "I'm seriously, ban san wanda zan tinkara da maganar ba, to amma zan yi tunani sosai, na gode da temakonka."
Yarima ya jinjina kai kafin ya ce "Ni zan wuce, ka kula sosai."
Ya na gama faɗen haka ya shiga motarsa ya fice.
Abdulkareem ya shiga zagaye a gurin a matuƙar rikice, ba zato ya ji an cafki kwalarsa, ya juyo da zafinsa don ganin wanda ya yi masa hakan, karaf su ka yi IDO HUƊU da Abdulmajeed fuskarsa a murtuke ba alamun wasa, cikin kakkausar murya ya ce "Mu je ciki dan ubanka yau ka yi mana bayani da bakinka." bai saurari maganar da Abdulkareem yake ba ya ja shi zuwa babban falo, har Dadda ma ya na zaune. a tsakiyarsu ya ja dinga kafin ya fara magana a mugun fusace, "Ashe munafukin yaron nan tayar mana da hankalin da yake wai aure yake so, amma shine ya ke ta ƙumi-ƙumi, yanzu banda tsaurin ido i na Abdulkareem ina shi ina aure yaron da ko gama iya sa riga bai yi ba?" tsananin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 16