Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gami cewa "kwana biyu baka da lokacin da zamu ɗanyi faɗa ko yanzu da nace maka Audu babu abinda kace shi yasa na ce haka amma kayi haƙuri" murmushi ya ɗanyi kana ya ce "to yanzu dai zanje nasami Uncle Rabi'u kuma kinga shine sama da Dadda dole Dadda ya risina" amma fa matsalar ɗaya ce kai ma kasan Dadda kaifi ɗaya ne" cije gefen laɓɓan sa yayi kana ya ce "Allah ya dafa ma lamarin kawai shi ne" daga haka suka cigaba da tattauna wa *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* "ya Aaminat kinsan kuwa Mama ce ta ziga Abba wai yace a wata zai Aurar dake" sakin baki tayi tana kallon Umaima, cikin mamaki ta ce "wai sai yaushe Mama zata bari nasha ruwa??! ta kurar tata tayi yawa kinga yanzu ta ƙara jefani a masifa" tsaki Umaima tayi gami da cewa "ai wallahi ko samun mata kamar Umma da wahala a gabanta fa ta faɗa amma ta kasa cewa komai saida ta dawo ɗaki naji tana kuka dana tambaye ta sai tace babu komai, saida na matsa mata sannan ta faɗa mini kuma tace karna faɗa miki ni kuma yau na faɗami" wani numfashi Aaminat taja ta sauke tare da gargiza kai" ta ce Ummm Mama kenan haryau bazata karaya ba ai gashina ƴata da tafi fifi-tata yanzu ita ce take mata fitsara iri-iri amma taƙi ganewa" Umaima ta ɗan gyara zama gami da cewa "nifa wallahi ina ganin Auren ki da Abdul kamar ba zaiyuwu ba" Aaminat tayi wani murmushi mai kama da yanzu aka fara kana ta ce "nima ina wannan tunanin amma innna tuna waye Abdulkareem sai na kauda tunanin hakan" murmushi Umaima tayi kana ta ce "nimafa na faɗa komar so yanzu in na kira Abdurrahim baya ɗauka kuma baya kirana" rausayar da kai Aaminat tayi kana ta ce "kinga ai dama haka komai yake, keda Fati baku da aiki sai yaudarar samari gashi kema anyi miki saikiji da daɗi ko babu" ƙasa tayi da kai cike da nadama Aaminat ta ce "amma kita addu'a Allah zai cire miki sonshi" "to" tace suka cigaba da hirar duniya, tuni Abdulkareem ya shirya tsaff ya ziyarci gidan Uncle Rabi'u ya zayyane masa duk a binda kefaruwa, Uncle Rabi'u ya ɗan gyara zama gami da cewa "to duk naji bayanin da kayi mini in sha Allah yau da yammaci zanje Abuja amma nan da kwana uku zanje nasame shi" Abdul ya murmusa, Uncle ya dafa kan Abdul gami da cewa "karka damu kaji in sha Allah ko mai zai dai-dai ta Allah yayi muku albarka" "Amin" Abdulkareem ya ce tashi yayi gami da cewa "Baba ni zan koma a gaida su ya Abbas" har zaka tafi???" "eh Baba zanje in zagaya masana'antar mu" Baba ya ce "to Allah ya tsare ka gaida ƴan uwan ka" "Amin" ya ce ya fita inda ya ajiye motar sa, Bayan kwana uku Yarima ya shrya tsaf yayi kyau sosai babban Falo ya nufa yana tafe yana tunane-tunane harya ƙarasa falon zama yayi akan kujera sannan ya dubi Ammi ya ce "Ammi ina kwana" "lafiya ƙalau" ta faɗa fuska babu yabo babu fallasa, tashi yayi ya ce "Ammi natafi" "ina zaka???!!!" ko ɗarrr baiji ba ya ce "gidan su E'iye" wata muguwar harara tabuga mai tare da ya mutse fuska, juyawa yayi zai tafi ta ce "waɗannan kakan nin naka mayune sun kama kurwar ka yaro tun kana ƙarami nake nesanta ka da su amma sun liƙema" ran Yarima in yayi dubu ya ɓaci, dan haka yaci gaba da tafiya ko waiwayon ta baiyi ba yanaji tana surfa masifa amma yayi ficewarsa, Bai ɓata lokaci ba ya ƙarasa gidan su E'iye kai tsaye Falon Inni ya nufa yana tafe yana kiran sunan ta cike da tsokana, fitowa tayi daga ɗakin dake cikin Falon tana cewa "sannu da zuwa saurayi na" murmushi yayi gami da zama ya ce "budurwa ta nayi kewarki kwana biyu" murmushi tayi kana ta ce "Allah sarki rabin raina ai kana zuciya ta" dariya ya ɗanyi gami da cewa "ina E'iye" Inni tace "inaga dai tana ɗakin ta ai yanzu rana tayi" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Inni ta ce jikalle na baka da lafiya ne???? naga ka rame" murmusawa yayi gami da cewa "A'a lafiya ta lau kawai dai jiki da jini" "to saika faɗa mana mara jini ajika"! E'iye ta faɗa gamida ƴar dariya juyawa yayi ya kalle ta ya ce "ko sallama bakiyi ba amma kunnan ki yaji abinda nace" murmusawa tayi kana ta ce "ai kunacan kuna soyewa kaida budurwar ka nayi sallamar baku amsa ba" dariya yayi ya ce "to mata ta irin wannan kishi haka" "Allah ya kyauta nayi kishin ka ni yanzu ma ba Auren ka nake ba nasake ka" "subhanallahi dama mata ce take sakin mijin ta" dariya tayi ta ce "ni dai bana Auren" shima dariyar yayi cikin jin daɗin barkwancin da suke shida kakan nin na sa, Inni ta ce "Habu zaka kaini nayi siye'siye??!" "kai Inni banason tsokana ki daina cemin Habu" dariya ta ɗanyi ta ce "to ai sunan ka ne" "to kishirya kuma bazamu da E'iye ba karta samana ido" dariya sukayi sudika, Inni ta shirya tsff tashe hijab ɗinta suka kama hanyar shopping, INDO CE &&& Salma Auta [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S Association Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi *21* Basu ɓata lokaci ba suka kammala siyayyar da zasuyi suka koma gida, kashingiɗe yake a kan kujera yana waya cikin nishaɗi da farinciki sai faman fara'a yake sam ya manta a inda yake ya ce "Aaminat Ina sonki, so na har a bada, in dai inaraye bazan bari kisake kukan baƙin ciki ba" wani ni'imtaccen murmushi ta saki, kamar tana ganin sa, ya ƙara da cewa "Aaminat kece ƴa mace ta farko da nakejin bazan iya rabuwa da ke ba"! "yazama dole karabu da ita kuwa" rassss!! rassss!!! gaban sa ya buga yayi saurin katse kiran yana muzurai, Abdussalam ya ɗan yi murmushi mai cike da ma'anoni ya ce "yaro man kaza" ƙasa yayi da kai, Abdussalam ya zauna gami da cewa "Auta mai yasa ka koma haka???, naga Uncle Rabi'u yazo duk da ban san dalilin zuwansa ba amma na alaƙanta zuwan da kai kaika ce ya zo ko" cikin sanyi ya ce "eh ni nace yazo ya sami Dadda", kallon sa ya ɗanyi cike da tausayawa ya ce "Abdul kayi haƙuri ka taushi zuciyar ka, kabi Umarnin iyayenka" har ga Allah Abdussalam baya jin daɗin yadda suke yiwa Abdul saidai acewar su hakan shine zaisa ya janye maganar sa ta Auren Aaminat, a raunane ya ce "Ya Abdullah ina sonta wallahi ku tausaya mini ku dubi halin da ɗan uwanku yake ciki, ita ɗin abar tausayi ce ina tausaya mata, kutayani ƙoƙarin shawo kan su Dadda," wani lafiyayyan mari ya zuba masa, sai da yaga taurari sun gifta, cikin ɓacin rai ya ce "ni zaka dinga faɗawa kana sonta dan baka da hankali, cikin kwanaki kaɗan ka canza mana gida komai namu ya canza kuma duk ta silar wata matsiyaciyar yarinya," ƙasa yayi da kai dan kuwa ko kashe sa Abdussalam zaiyi baya jin zai iya ɗaga mai murya, rai a ɓace Abdussalam ya bar wajen, tunda Uncle Rabi'u yazo suke ƙarda da Dadda akan yabar Abdul ya Auri wadda yake so, saidai Dadda ya kafe ya tsaya tsayin daka a kan ra'ayin sa, Uncle Rabi'u ya gyara zama gami da cewa "bai kamata ka hana yaro abinda yake so ba, tunda yace Aure yake so to ka rabu da shi mana yayi kuma ai ba haramun bane dan ya Auri bazawara", Dadda ya rausayar da kai, cikin girmama yayan nasa ya ce "bawai na hana shi Auren bazawara bane, No, Ina buƙatar ya ƙara hankali ya san inda ke masa ciwo, ga Abdulmajid ga Abdurrahim ga Abdussalam duk ba wanda ya taɓa zuwa min da zancen Aure sai ƙaraminsu wai Abdulkareem, maganar Gaskiya Yaya ina girmamaka ne shi yasa nake bi a hankali amma ba zan iya bari ɗana ya yi aure ya na da shekara ashirin da ɗaya ba, don bance ya kai da biyu ba ma, ka yi haƙuri in sha Allahu indai ya ƙara hankali to wannan ba ni da matsala ko wa zai aura indai ba mara tarbiya bace" cike da gamsuwa Uncle Rabi'u ya ce "Eh na fuskanceka sosai kuma in sha Allahu zan ƙara yiwa Yaron nasiha, zan nuna masa cewa haƙurin ma ya na da amfani, amma ku tayashi addu'a kawai Allah i zaɓa masa alkairi idan yanzun ne idan sai nan gaban ne." murmusawa Dadda yayi gami da cewa "In sha Allah za mu ƙoƙarta, na ji daɗi da ka fahimce ni." murmushi Alhaji Rabi'u yayi ya ce "to Allah yayi mana mai kyau, kuma dan Allah ku daina fushi da ɗana shifa yaro ne," ƴar dariya Dadda yayi gami da cewa "ai ɗan na ka yana da kafiya sam ya koma tamkar bashi ne wanda nake kira da Babban mutum ba!" Alhaji Rabi'u ya ce "toni zan koma sai akira min Abdulkareem ɗin" Dadda ya ce "to" sallama sukayi da Alhaji Rabi'u cikin fara'a da sakin fuska Dadda yanufi ƙofar da zata sada sa da labun gidan, ba a ɓata lokaci ba Abdulkareem ya shigo Falon kai a ƙasa, zama yayi a ƙasan kafet, ya ce "Uncle gani" murmushi Uncle Rabi'u yayi sannan ya ce "Abdul kayi haƙuri kasa Allah a ranka kaji ka maida komai ba komai ba, mahaifinka yaƙi Amincewa da maganar Auren ka, nayi iya ƙoƙari na amma ban sami nasarar shawo kanshi ba amma ina ganin kayi biyayya wa iyayen ka," wasu hawaye ne masu zafin gaske suka fara tsere a kumatun Abdul, "kayi haƙuri ka daina kuka kowa da tashi ƙaddar idan Allah baiyi matar ka bace to babu makawa sai kun rabu,...." ya ɗan tsagaita kafin ya ce "ka sanar da yarinyar cewa mahaifinka bai amince ba idan tana da wani tace ya fito" zuwa yanzu Abdul ya fara fita haiyacin sa, kuka yake razgawa tamkar ƙaramin yaro Uncle Rabi'u kuwa sai faman rarrashin sa yake, "Abdul kaifa musulmi ne ka ɗauki ƙaddara a yadda ta zo ma, ka gode wa Allah da ya wadata ka, ta ko ina ka kana da damar da zaka taimaka mata, ita rayuwa dama haka take wani lokaci farin ciki,.. wani lokaci baƙin ciki, kuma a rayuwa Ɗana ko a da ma ba yanzu da zamani ya juya ba, Ba komai ake so kuma a samu ba ɗana, ka tuna waɗanda su shuɗe kafin mu, ko ba ka sauraren tarihi ne? gashi za ka ga su na son abu to kuma ba shi Allah yake basu ba, wasu lafiya suke nema sun rasata, wasu ƴan uwa suke so gashi ba su da su, wasu ƴaƴa suke buƙata kuma me kyautar bai basu ba, wasu kuɗi ne abin son su amma Allah bai yi da rabonsu ba, za ka ga wasu ido ne ma basu da shi, wasu ba su da damar jin magana duk da suna da kunnuwa, amma duk a haka muke raye kuma muke farin ciki da abinda Allah ya bamu, to ita rayuwa a haka take, ta yuwu ita ba matarka bace shi yasa hakan take faruwa" cikin kuka ya ce "Uncle nagode da nuna damuwar ka akaina Allah ya saka da alkairi kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin nayi wa iyayena biyayya koda hakan zaiyi silar rayuwa ta" yana gama maganar ya ƙara fashewa da wani matsanancin kuka mai tsuma zuciya, cike da tausaya wa Uncle ya ce "Abdul kasa a ranka haka Allah ya rubuta Aaminat ba matar ka bace kaji kataya ta da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zai riƙeta da gaskiya da Amana!" daker ya iya ɗaga harshen sa ya ce "na..na..na..nagode!!!!" jiki a matuƙar sanyaye Uncle Rabi'u ya tashi sannan ya dafa kan Abdul ya ce "Allah ya baku ikon haƙuri da juriya da kai da ita Allah ya haɗa kowa da rabon sa na alkairi, katashi ka koma sashin ka ka daina kuka domin kuwa kukan ka yana karyar min da zuciya" bai ce ko mai ba sai aikin kuka da yake babu ƙaƙƙautawa jiki a mace Uncle ya nufi ƙofa, *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Abdul kuwa yana wajen ya kasa koda motsa ɗan yatsan sa ɗaya ne da nufin tashi" baya jin zai iya rayuwa gani yake tamkar numfashin sa a duniya ya zo ƙarshe, ya daɗe a haka kafin ya tashi jiri ne ya fara ibarsa, yayi saurin dafa kujera yana wani numfashi sama-sama cikin hanzari da tashin hankali Ummi ta nufo wajen da gudu tana ƙarasowa ya ɗaga mata hannun sa dake rawa, Alamar da katar wa, tsayawa tayi cakkk kamar wadda a ka riƙe, Nana Kadija ce ta nufo wajen tana kuka, hannu ta miƙa mai ya kama, ta jashi suka bar wajen da ido Ummi ta bisu cikin tashin hankali, ta rasa abinyi hakan yasa ta juya gudu-dugu sauri-sauri tanufi inda Dadda yaka Aaminat kuwa wannan furicin ne yake mata yawo aka yazama dole karabu da ita, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zarya take haka kawai zuciyar ta, ke raya mata Abdul yana cikin tashin hankali hakan yasa hankalin ta ya ƙara tashi ko tsakar gida ta kasa fita tana ɗaki kuka kam tayi ta gaji kanta har ya fara ciwo "maiyasa duk wanda ya shiga rayuwa ta saiya haɗu da ƙalubale dama gidan su Abdul basa ƙauna ta" wannan tambayar take yiwa kanta saidai bata da amsoshin su hakan yasa ta koma ta kwanta tayi lamo tana jiran Siyama ko Umaima su leƙota, Yarima yana zaune a office wayar sa ta fara ringin da sauri ya ɗauka don gani mai kira sunan Abdulkareem ne ta fito a kan wayar jiki a sanyaye ya kara a kunnan sa tare da sallama "salamu'alaika" "kana ina??!! muyar Kadija ta daki dodon kunnan sa, ya ce "lafiya??? ina Abdul ɗin??!" murya a cunkushe ta ce "tambayar ka nayi kana ina??!!" "ina Asibiti" "to ka hanzarta zuwa gidan mu" tana gama faɗin haka ta katse kiran, sororo Yarima yayi ya kasa gaba ya kasa baya "mai yake faruwa" ya furta a fili zimbur ya tashi cikin hanzari ya fice daga office ɗin ya nufi ma'ajiyar motar sa yana zuwa bai jira komaiba ya faɗa motar ya jata a guje, ya bar Asibitin, Ummi ta sanar da Ddda abinda ke faruwa murmusawa yayi gami da cewa "ki ƙele sa zaiyi zai gama" sakin baki tayi tana kallon Dadda, shi kuwa ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karatun jaridar sa, juyawa tayi zata tafi yayi saurin cewa "zoki zauna" babu musu ta koma ta zauna, hankalin ta yana kan Abdul saidai babu yadda zatayi ya zama dole su hane sa da abinda yake shirinyi, Yarima yana zuwa yayi parking kai tsaye ya nufi ƙofar da zata sada sa da sashin Abdul, yana tafe yana tunane-tunane ya saƙa wancan ya warware wannan har ya ƙarasa ɗan ta ƙaitacan Falon, rasss rasss gaban sa yayi wata mummunar faɗuwa ganin Abdul a dur ƙushe a wajen, cikin hanzari ya ƙarasa wajen ya ɗaga Abdul yana cewa "Abdul mai yake faruwa" cikin sarƙaƙƙiyar muyar sa ya ce "Abubakar taimoko zakayi mini a karo nabiyu" "taimako??" ya maimai ta cikin sigar tambaya, baki na rawa Abdul ya ce "ka taimaka mini ka Auri Aaminat" zindummmmm!!!!!!! gaban Abubakar ya yanke ya faɗi tare da zazzaro ido ya kalli Abdul, Abdulkareem ya ɗaga masa kai a lamar eh ©️INDO &&& Salma Autar Jarumai [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S Association Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Association Shafi 22 Aruɗe Yarima ya ce "Abdul anya kuwa kaine??, ka kuwa san mai kake faɗi??!!!" rintse ido yayi yana jin zuciyar sa tana wata muguwar ta fasa kamar zata fasa ƙirjin sa ta fito waje, dafe kai yayi tare da sakin yarima ya tafi taga-taga zai faɗi cikin zafin nama da hanzari Yarima ya riƙo Abdul, zaunar da shi yayi a kujera sannan ya nufi firji ya ɗauko ruwa mai sanyi, ya buɗe gorar ruwan sannan ya kafa a bakin Abdul, kamar magani haka yake jin ruwan, saida ya sha ruwan sannan kuma ya fara sauke ajiyar zuciya, Abubakar kuwa hankalin sa yayi mugun tashi, cikin wata iriyar murya Abdul ya ce "Abubakar kai kaɗai ne zaka iya taimaka mini ka Auri Aaminat, dan kuwa a yanzu bani da halin Aurenta kuma mahaifin ta zai iya Aura mata duk wanda ran sa yaso hakan kuma zai cutar min da ita!!!" ya ƙarasa maganar cikin marai-raicewa, "A'a bazan iya Auren Aaminat ba Abdul" hawaye sai zarya suke a fuskar Abdul yayi murmushe mai cike da bayyanar da ciwo, ya ce "Yarima kaima bazaka iya Auren (BAZAWARA) ba ko " girgiza kai yayi ya ce "A'a bawai bazan iya Auren bazawara ba, Abdul ka na son Aaminat fa, ni zan temaka maka ka aureta a kowane hali, don Allah kar ka ce min ka haƙura zan yi maka komai, idan na aureta gani nake kamar na ci amanarka" Ya ƙarasa maganar ya na goge hawayen da suka fara sauka kan kumatunsa. wani murmushi yayi mai cike da raɗaɗi, ya ce "hakan ba yana nufin kaci Amanata bane, ni fa musulmi ne don me ba zan iya yin tawakkali ba? ba na son saɓawa iyayena don haka na haƙura da ita, duk son da nake mata iyayena sun fi ta muhimmanci a gurina; ba abinda nake so gareta wanda ya wuce in ganta cikin farin ciki in cireta daga cikin ƙunci, kuma na san za ka iya, ka yi min alƙawari za ka yi don Allah ba tare da tunanin wani abu ba" Yarima ya ce " na san da hakan kuma hakan ya na da kyau, amma ta ya zan iya Auren Aaminat bayan kai take so?? kuma kai ma ita kake so No bazan iya hakan ba," zamewa yayi daga kan kujerar da yake a kai ya zuba guiwoyin sa a ƙasa sannan ya dubi Yarima ya ce "na roƙeka ka tausaya mini ka taimaki baiwar Allahn nan Aaminat badan ni ba dan girman Allah ka Aureta koda zuciyar ka bata so," zuwa yanzu ƙafafuwan Yarima sun gaza ɗaukar sa hakan yasa shima ya durƙushe a gaban Abdul yana wani irin kuka mai taɓa zuciyar me saurarensa, dakyar Abdul ya iya fizgo muryar sa ya ce "Yarima ka aminta zaka Aure ta??????!!!!!!" cikin kuka Yarima ya ce "tabbass a da na so ta amma yanzu sam banajin zan iya rayuwa da Aaminat" Abdulkareem ya girgiza kai ya ce "Abubakar kaifa Aminina ne,, kai kaɗai ne zaka iya taimako na dani da Aaminat ka tausaya mata" Shiru ya yi ya na tunani har na tsawon wani lokaci sannan ya ja numfashi ya sauke sannan ya ce "na aminta zan Auri Aaminat don farin cikin ka" taune gefen leɓensa yayi sannan daga harshe da ƙyar ya ce "kayi mini alƙawarin bazaka taɓa bari Aaminat tayi kuka akan komai ba ka yi min alƙawarin za ka yi mata kowane irin gata" Yarima ya ce "zanyi ƙoƙarin cika maka burinka" wata zazzafar a jiyar zuciya ya saki sannan ya miƙe da niyar shiga bedroom ɗin sa, Yarima ya kalle sa cike da tausayawa, tabbas Abdulkareem yana cikin wani halin na rayuwa ko mutuwa, duk wani mai imani yaga yadda Abdul ya koma tamkar zautacce saiya tausaya masa, tashi Yarima yayi ya nufi inda ya Ajiye motar sa yana tafiya yana haɗa hanya tamkar wanda yasha giya, Abdul kuwa yana shiga bedroom ɗinsa ya faɗa kan gado yana wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciyar duk wani ɗan Adam me imani, ya daɗe yana kuka kafin ya tashi, da jan ƙafa ya shiga toilet ɗin dake ɗakin, ruwa ya watsa ya fito zama yayi a gefen makeken gadon sa tare da riƙe goshin sa, wata farar takarda ya ɗakko tare da biro, ya runtse ido yana kiran sunan Allah, rubutun ya fara, ya nayi yana kuka hakan yasa ƙwallar sa ke zuba kan ta kardar saida ya kammala rubutun sannan ya lankafe ta ya ajiye a gefen sa, wata ta kardar ya ɗauka yayi rubutu sannan ya ajeta agefe ita ma. *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum

Chapter 11 of 16