Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ta karɓa ta yi yadda Siyama ta ce duk da ba daɗi. Cikin kayanta ta duba ta ɗakko mata Hijab ta zura mata sannan ta ɗakko mata takalma, ba ta zauna ba ta ce "Ai jikin ya yi sanyi tashi mu tafi." "Ni wallahi da ƙyale ni ki ka yi Siyama, ki ka sani ko Ajalina ne ya yi in mutu in huta?" cike da takaici Siyama ta ce "To inaga Ajalin naki ne, kuma zuwa Asibiti ya zama dole ko ki tashi ko in sa Abdulkareem ɗin ya ɗakko Motar gidansu ya zo ya kai ki da kansa, kinsan ba kan gado gareshi ba har cikin gidannan zai shigo ya taitayeki, Allah i sa ma ya na nan." ta ƙarasa maganar ta na ƙoƙarin fita daga ɗakin, da sauri Aaminat ta ce "Wallahi Siyama ba na son irin wannan, haba don Allah ba tashi zan yi ba shine za ki fara ambato min sunan Shaiɗanin Yaron nan?." Siyama ta ce "Da ki zauna ma". riƙe hannunta ta yi sannan su ka fito, Umma ta ce "Ina za ku je ne??" Aaminat za ta yi magana Siyama ta yi saurin cewa "Ba ku san ba fa da lafiya ba Umma? Asibitin tsallake zan rakata ai, don abin ya ci tira." Umma ta rausayar da kai gami da cewa "To Allah i yaye." Ko kulata Siyama ba ta yi ba su ka ci gaba da tafiya. Sun yi sa'a su na zuwa Wata Malamar Asibitin da ta ga jikin nata ba daɗi ta ce su shiga wajen Likita don samun temakon gaggawa. Bayan sun shiga Ɗakin Likitar ta yi mata nuni da kujera gami da cewa "Zauna." zaman ta yi ta na maida numfashi duk ya bi ta gaji ga tafiya ga rana. Likata ta ce "Meke damunki??" "Zazzaɓi da Ciwon Kai sai kuma wani ciwo a ƙirjin...." sallamar wani matashin Saurayi ce ta katse mata magana, Likitar ta fara fara'a gami da miƙewa tsaye ta na cewa "A'ah marhabin da Manya, Yallaɓai yau ku ne a Asibitin namu?" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Hajiya Maimuna mu ne da tsakar ranar nan." Hajiya Maimuna ta ce "Sannu da zuwa; ke patient Allah ya temake ki ga Babban Likita sai ya duba ki don na ga larurarki babba ce, kin zo a sa'a." ya ɗan shafi sumarsa ya na dariya gami da cewa "Kai Hajiya Maimuna, ba daɗewa zanyi ba fa, wani Patient zan duba shi yasa ma ki ka ganni." Hajiya Maimuna ta yi dariya gami da cewa ''To ai Dr aikinku ne temakon Al'uma kar mu yi haka yau, temaka mata." ya ce "Idan na fito sai a turo ta." Hajiya Maimuna ta ce "To Mu na godiya." bai ce komai ba ya ɗauki abin da zo ɗauka sannan ya fice, Hajiya Maimuna ta zauna kafin ta ce "Na fa yi miki murnar ganin DR Yarima Ƴar nan." a marairace Aaminat ta ce "Ni fa ban damu da ganin Babban Likita ba, Allah shi ke yayewa don Allah ki saurare ni ba na son jira, ko a zaunen nan ma wahala na ke sha" Hajiya Maimuna ta ce "Minti nawa ne zai gama ya dawo kanki?, ke ba za ki gane komai bane; ki ga yadda ki ka wani ɗauke gabaki ɗaya, ki na fa da babbar matsala Yarinya, koma Kujerar nan ta gefe ki bawa Al'umma guri, don ma kin samu zai ganki shine za ki yiwa mutane iyayi." cike da takaici Aaminat ta miƙe ta koma gefe ta zauna, ta na jin Hajiya Maimuna ta na cewa "Zazzaɓin naki ya samo asali gwara ki zauna a ɗora ki akan layin magani daidai da larurarki." ba ta ce mata komai ba don kuwa itama ta shiga sahun waɗanda ta ke jin haushinsu. Ta daɗe ta na jira sannan wata Ƴar Budurwa ta shigo da sallama, bayan Hajiya Maimuna ta amsa ta ce "Dr Yarima ya ce a tura masa wadda ki ka ce." Hajiya Maimuna ta ce "Ga ta nan, rakata " a yatsine budurwar ta ce "Ki taso" Aaminat ta tashi ta mara mata baya. ya na zaune ya harɗe ƙafa akan kujera sai danne-dannen waya ya ke, ko ɗago kai ya kallesu bai yi ba, Budurwar ta bata gurin zama sannan ta fice. Aaminat ta ce "Zazzaɓi da ciwon kai nake sallame ni sauri nake." ɗan murmushi ya yi ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ba shi kenan ba, faɗi gaskiya." Sai a lokacin ta tuna zafin da ta ke jin Zuciyarta na yi ta zaro ido tare da tambayar kanta ba dai Ciwon Zuciya bane?, Sai a lokacin ya ɗago ya zuba mata idanu gami da cewa "Zuciyar ta na ciwo ne??" tsuke bakinta ta yi ta kauda kai, sai a lokacin ma ta tuna ashe a zahiri ta yi magana; banza ya yi mata ya ci gaba da danna waya ganin haka ya sa ta ce "Zafi nake jin ta na yi haka kamar Ciwo ko da yaushe sai na dinga jin Ƙunci." ya ce "To Hawan Jini gareki ko Ciwon Zuciya??." da sauri ta ce "Kai Malam ba na son neman bala'i cewa nayi zazzaɓi nake." ya yi dariya kafin ya ce "A alamunki ba ki da faɗa amma zafin ciwo ya sa kin fara; kan ki ya na juyawa ne ko kuma jiri?" ta gyaɗa kai alamar eh, ya ce ''Ina Mijinki ??" duk da ba lafiya gareta ba sai da ta harare shi sannan ta ce "Meye haɗinka da shi???" "Kamata ya yi na yi magana dashi akan lafiyarki mana." "To ba ni da Miji yanzu a gaban iyayena nake, kar ka ɗakko min abin da ba zan iya ba kawai ka rubuta min maganin zazzaɓi." tuntsirewa ya yi da dariya kafin ya ce "Wallahi zafin nan naki ya na bani armashi Aaminat!; Dole fa sai kin yi gwaje-gwaje, gobe ki dawo." ganin ta zaro masa ido ya sa shi cewa "Ya dai?" ta ce "Wa ya faɗa maka sunana??" idanunsa ne su ka ƙara girma, lallai ya kusa ya yi ɓaramɓatama da sauri ya ce "To kin taɓa ganin anga Likita a Asibiti ba tare da an bada suna ba?" ta yarda da hakan don haka ta ce "Yanzu sai me? gida nake son tafiya." Rubutu ya yi a Farar Paper sannan ya miƙe gami da cewa "Mu je Pharmacy ki karɓi magani." ba ta yi musu ba ta bi bayansa, da kansa ya harhaɗa maganin sannan ya ce ta biyo shi kuma ya ƙi bata maganin, ba dan ranta ya so ba take binsa zaizai duk inda ya yi ta na biye da shi, Siyama ta na kallonsu cike da mamakin ta yadda akai lokaci ɗaya Ƙawarta da Dr Yarima su ka zama kamar da can sun saba, ganin za su fice daga Asibitin ya sa ta miƙe ta bi bayansu cikin sauri. Wajen Motarsa ya nufa ya buɗe mata baya gami da cewa "Shiga na raka ki gida." banza ta yi masa kamar ba ta ji shi ba, Siyama ta yi zuruf ta shige ta na cewa "Mun Gode Dr Dama da kyar ta iya zuwa wallahi ka temaka." "Ke kuma daga ina?" "To ai ni ce na kawota Asibitin ni ƙawarta ce; ke Aaminat idan ba za ki shigo ba sai ki daɓa a ƙasa, ai kinsan Dr Yarima dai kuma kowa ya san shi ba sace ki zaiyi ba kuma bai yi kama da mutanen banza ba bare ko ki ce." Dr dai ya na jinsu nashi aikin dariya kawai don kuwa yanayin Tirjiyar Aaminat ya mugun sa shi a kwalba. Sun daɗe a tsaye ita da shi sannan ta ji wahala ta shiga Motar, ga rana ga rashin lafiya. Su na tafiya DR da Siyama su na hira yawanci tambayoyi ya ke mata akan abin da ya shafi Aaminat da rashin lafiyarta, Ita kuwa sai bashi amsa take yi daki-daki. ©️ INDO Tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 11 Bismillahirrahmanirrahim Hirar tasu ta na bala'in Ƙona Zuciyar Aaminat don ita gani take duk sun dameta. abin da ya bata mamaki har ƙofar gidansu ta ga ya je tsaf ba tare da wani ya yi masa kwantance ba, ta tambayi kanta ta yadda hakan ta faru amma sai ta basar don kuwa ba wannan ne a gabanta ba. Siyama ta buɗe murfin Motar ta fita ta na cewa "Ni fa ban san da yaren da zan yi Godiya ba Yallaɓai." Ya yi murmushin gefen baki, daidai lokacin da Aaminat ta ke shirin fita daga Motar ya ce "Ƙawarki ta na da Mutunci sosai, ba ruwanta da faɗa ga sauƙin kai, a taƙaice dai ta haɗu ta ko'ina." Tsam ta tsaya kamar wadda ya ɗaure har sai da ya gama maganar sannan ta ja sangalalen ƙafafunta ta yi gaba. Cikin Hanzari ya fito har tuntuɓen harshe ya ke garin kiran Sunanta, ta tsaya sauraren abin da zai ce ba tare da ta waigo ba, "Aaminat ki kwana a shirye kuma cikin zaɓi biyu, ko in zo ƙofar gidanku in ɗauke ki ko ki zo Asibiti ki sameni." sai a lokacin ta juyo hawaye sun cika kwarmin idonta, cikin rawar murya ta ce "To duk na meye? ba dai Magani ne ba to ai ka bani." ya girgiza kai gami da gyara tsayuwarsa, cikin muryarsa me cike da nutsuwa ya ce "Aaminat ki na buƙatar test ai na faɗa miki tin ɗazu, ba zan iya zuba Ido ina kallo ki cutu ba don ni likitan Al'uma ne ko kuma in ce na waɗanda ba za su iya ba, temaka miki a wannan Ƙadamin kamar Alhakin da ta rataya a wuyana ne, Allah i ƙara lafiya." ya na kaiwa nan ya saka Baƙin Galashinsa wanda ya rufe kyawawan idanunsa sannan ya juya cikin takunsa irin na Cikakken Namiji wanda ya amss sunansa, Ƙasaita nutsuwa ɗagwarmashi ƙwarewa, kaɗan daga cikin salonsa. Haka kawai Aaminat ta tsinci kanta da tsayawa kallonsa ta kasa gaba ta kasa baya kamar tsohuwar Bishiyar da ta daɗe da kafuwa a guri, sai da ta dena ganin biɗi-biɗin motarsa sannan ta samu ƙwarin guiwar shigewa ciki, ta na jefa ƙafarta ta tsorata sabi da jin dariyar Siyama, ta saki baki ta na kallonta cikin sirkakken yanayi, takaici da kuma mamaki. Siyama ba tare da ta dena dariyar ba ta ce "Iskancin Loko; ka ga Dr da patient ɗinsa?" ta ƙarasa maganar tare da riƙe haɓa alamun mamaki. Aaminat ta ja dogon tsaki sannan ta wuce ciki ba tare da ta cewa Siyama ko Ƙwal ba. Washegari Da misalin Ƙarfe 10:00am ta na zaune ta buga tagumi bayan ta gama haɗiyar Maganinta, takaicin shan maganin duk ya isheta don kuwa ba ƙaunarsa ta ke yi ba. Siyama ce ta yi sallama fakatan-fakatan ta shigo ta tsaya ta riƙe ƙugu kafn ta ce "Aaminat! fita idona in rufe, na aiko Walid ya ce ki fito mu tafi Asibitin sabi da gardama kin ce ba za ki je ba ko?" Cikin matuƙar takaicin rawar kan Siyaman ta ce "Allah i yaye miki Siyama, ni dai ba na samu sauƙi ba? to ban ga me sa ni na fita ba yanzu, ni ba na son temakonsa; ba wani gwajin da za a yi min." Siyama ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta tunkuɗo shi gaba ta fara tattafa hannaye gami da cewa "To wallahi ko Mutuwa za ki yi sai dai ki mutu bayan mun je Asibitin!" ta na kaiwa ƙarshen maganar ta maida hannun kan ƙugunta ta riƙe gami da cellaro ƙafa ɗaya gaba, Aaminat ta tsaya kallonta ta na tunanin ta yadda akai ta zama Ƴar Buyagi haka. Cikin sigar rarrashi Aaminat ta ce "Siyama ki fahimce ni don Allah, ba ki san komai ba a halayen Maza shi yasa ki ke dagewa akan sai na bi shi, temakon nan zai iya zamewa wani sabon babin Baƙin ciki na rayuwata, ki yi haƙuri ki bar ni zan lallaɓa Ya Umar ya kai ni Asibitin duk wani abin da za a yi sai a yi min." Siyama ta sassauta murya sannan ta ce "Nima ki fahimce ni Aaminat, tare da ni fa za mu je, kin ga in ma tsoron zargi ke ke yi kin fita tinda da ni, idan kuma ki na tsoron Dr Yarima ne ina me shawartarki da ki dinga kyautatawa mutum zato, jiya ki ka fara haɗuwa da shi kar ki yi masa zaton da shi ba haka yake ba, ki nemi Kariyar Allah in kin yi haka ba abin da zai faru in sha Allahu. Aaminat ta yi shiru ta na nazarin kalaman Siyama, ta daɗe ta na tunani kafin ta tashi ta ce "Ɗakko min Hijab ɗina Dogo, a shirye nake tinda ba kwalliya zan yi ba ni." Siyama ta ce "Ki ma yi kwalliyar mana, Mutum ba lafiya ba sai Ƙilinbo iri-iri kamar rainon Jinnu." Aaminat ta yi mata banza don kuwa ta lura akan Guiwa Ƙawar ta-ta take. Su na fita Ƙofar gida su ka yi Tozali da Fallatsetsiyar Mota Fara kar da ita, Siyama ta ce "Alhamdulillahi, dama ina tsoron tafiyar Ƙasan nan, Allah ya kawo shi." a ɗan Fusace Aaminat ta ce "Wai way....." kasa ƙarasa maganar ta yi sabi da IDO HUƊU da su ka yi ita da shi, ya zuba mata Brown Eyes ɗinsa masu zaiba-zaiba, suƙut ta haɗiye Yawu tare da sauran Kalamanta. Ya haɗe Cikin Riga Baƙa me ɗan Gajeren Hannu da Wando Blue (Bulu), ya wani Coge a jikin Mota ya na ɗaiɗaita idanu akanta. Ganin ta tokare ta kasa tafiya ya sa Siyama ta ja hannunta kiiii ta na cewa "Yanzu in biye miki za mu yi sai Wankin Hula ya kaimu Dare." Sai da ta tura ta cikin Motar sannan hankalinta ya kwanta, ta kalli Dr Yarima da yake dariya Ƴar ciki-ciki cikin yanayinta na shiririta ta ce "Yallaɓai Ina kwananka? ga ta nan na fito da ita da ƙyar, Allah ya sauwaƙe min da tuni Na yanka Kazar Wahala na Fige na cinye." sai da ya tuntsire da dariya sabi da jin kalaman nata, ta taɓe baki ta yi masa kallon ba ka dameni ba sannan ta shige Motar, Dr Yarima ya Zagaye ya shiga Mazaunin Direba ya fara Tuƙi cikin nutsuwa. Aminu Kano Teaching Hospital Su ka nufa, su na zuwa ba ɓata lokaci ya yi abin da zai yi su ka fito daga Aminu Kano zuwa AA Hospital. Cikakken sunan Asibitin shine, AMEENU ABDULLAH HOSPITAL a nan ma gwaje-gwaje aka yi mata sannan ya tarkato su ya dawo da su gida. sallama su ka yi bayan ya jaddada musu gobe zai dawo tare da Bayanan Gwajin nata, Aaminat dai sai gyaɗa kai da girgizawa ba Baki, Siyama kuwa ita da shi babu gwani a fagen Magana idan ya faɗi Ɗaya za ta shirya masa goma shi kuma zai ƙara mata da wata ɗayar Zazzafa, ta ari bakin Aaminat wajen yi masa godiya sosai da nuna farin ciki akan Temakon da ya yi musu. Sai da su ka shiga cikin gida Aaminat ta kasa Aradun Mita, motsi kaɗan sai ta yi maganar surutunsu, da Siyama ta gaji sai ta bar mata gidan. Washegari Gwajar ɗin wayarta ce ta ta fara ƙara, ta janyota Zuciyarta cike da takaicin kiran ko ma waye, sai da ta katse wani kiran ya ƙara shigowa sannan wayar ta taɓu da ƙyar don kuwa ta fara cin sensor, ta yi sallama a ɗaya ɓangaren Dr Yarima ya amsa, Sai da ta kusa yarda wayar sabi da ɗan firgitar da ta yi na wucin gadi, ya yi mata bazata ba ta taɓa tunanin za ta ji shi ba, don kuwa da hannunta ba ta bashi lambarta ba, kai tsaye ta ɗorawa Siyama laifin. "Aaminat ki na tare da ni??" ya jefo mata tambayar cikin lallausar murya, gyaɗa kai ta yi a sanyaye ta ce "Eh." ya ce "Na zo fa, za ki fito ne ko na haɗu da Siyama kawai?" cikin sauri ta ce "Ya ma fi sauƙi, ka haɗu da ita yanzu aiki na ke yi." ya yi murmushi me sauti ba tare da ya ƙara magana ba ya katse wayar, Siyama da ta hakimce a kujerar ɗan zaman banza ya kalla kafin ya ce "Yau ba zan samu ganinta ba, don haka mu yi magana." ta maida hankalinta kansa sannan ta ce "To Dr ina jinka." "Da na yi tunanin fa Hawan jini ne ke shirin tasarwa Ƙawarki, bayan bincike kuma na gane Ƙarancinsa ne ya fi damunta sabi da yawan ciwoce-cowoce da take, amma inda matsalar ta ke, ta fiye sa kai a damuwa hakan kuma ka iya janyo mata Taɓuwar Zuciya anan gaba; ya na da kyau ki kula da ita yadda ya kamata ki dinga sa ta shan magani sannan ki dinga ƙoƙarin hana ta zaman tunane tunane da damuwa; za ki iya ganina kwatsam na zo ganinta a koda yaushe don haka ki zauna cikin shiri domin ke ce abar dafawata. Siyama ta zuba tagumi ta na kallonsa, sai da ya gama dogon bayanin sannan ta rausayar da kai ta ce "Allah Sarki Aaminat, dama na yi tunanin haka shi ya sa na damu akan mu je Asibiti, mun gode da temakawarka Yallaɓai, ai ka yi mana mutunci idan ka dawo ganinta in sha Allah za ka ganta." ya saki lallausan murmushi gami da cewa "Na gode." buɗe murfin Motar ya yi ya fita, itama Siyama ta fita, a gidan baya ya ɗakko Ledar Magunguna ya miƙo mata ta karɓa gami da ƙara masa wata Godiyar. Sai da ya tafi sannan ta shiga gida ta kaiwa Aaminat Magungunan tare da kora mata jawabi, jikin Aaminat ya yi sanyi Salam da ta ji abin da ke damunta, Siyama ta ce "Ya ƙara da wasu dokin ma fa, kuma ya zama dole ki kula ni zan dinga ku la da ke ma, ga shi ko Abinci ba ƙaunar ci ki ke ba." Cikin rauninnZuciya ta ce "Siyama Abinci ne sai ka ce ba na gidan Mahaifina ba, da gori da gore-gore ake ba ni shi kullum ko da ni na girka." Siyama ta rausayar da kai gami da cewa "Allah i kawo ƙarshen abin." Bayan wani lokaci Aaminat jiki ya yi ƙwari ta samu lafiyarta, Siyama ba ta yi mata da wasa wajen ɗura mata Abinci da magani da sauran abin da ya kamata kuma takan zauna ta dinga bata labarai ko kuma ta karanta mata Littafan da ta ke karantawa. hakan kuwa ya matuƙar samawa Aaminat nutsuwa duk hayaniyar kanta ta yi sauƙi, ƙarin farin cikin nata kuwa, Abdulkareem da ba ya shiga shirginta tin lokacin da ta fara rashin lafiya za ta iya cewa Ba ta yi IDO HUƊU da shi ba (Sunan Wani littafi nawa IDO HUƊU me ban tsoro) hakan ya sa ta farin ciki sosai ta saki jikinta. Fitowarta kenan daga gidan su Siyama kamar daga sama ta ji ya kira sunanta, Gabanta ya yanke ya faɗi, a ranta ta ce Shi kenan baƙar ƙaddarar tawa ta dawo. "Aaminat na samu wasu baƙaƙen labarai da ba su yi min daɗi ba." ©️ INDO tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 12 Bismillahirrahmanirrahim Aaminat ta doka tsaki kafin ta ce "To sai me? ko a bakina ka ji baƙaƙen labaran? ina da asara ne ni ko sun yi ma ko ba su yi ba?" Ya yi murmushin takaici gami da cewa "Hmm!!! Aaminat! a tunanina kinsan martabar SO kuma kina sauraren Huɗubar Manya na cewar ka so me sonka, a bakin kowa za ki iya jin wannan furucin me yasa ba za ki ɗauki wannan Nasihar ba? Wallahi ba na wasa da soyayyarki tsakanina ga Allah ina sonki kuma ina son Aurenki; ko da a yau ki ka Amince a Ɗaura a shirye nake, kinsan na riga na mutu akan sonki amma ki ke saurarar wani gaja da bai son inda ke masa ciwo ba?" a fusace Aaminat ta nuna shi da yatsanta manuniya gami da cewa "Kaii!!! ka shiga taitayinka wallahi ka kama kanka tin kafin ka tsinci Juma'arka a Laraba, banda ba ka da kunya wai ka kalli tsabar idanuna ka ce ka na sona? kai ba dan nasan daga gidan Daraja ka fito ba da ka sha wankin Rashin Mutunci a gurina, duk haƙurina ka fara kaini ƙarshe zan rufe ido in yanka maka tikitin rashin Mutunci" ta ƙarasa maganar ta na raka shi da wani mugun kallo wanda ya ke ƙara murtsika Zuciyar Abdulkareem, a take idanunsa su ka sauya kamanni, ya girgiza kai alamar a'a sannan ya ce "Aaminat Ko a yau nace zan Aureki zan iya sai dai ba na so na Aureki ta hanyar tilastawa domin ina matuƙar Tausayinki kuma ina darajaki in banda haka da ko ta wane hali sai na Aureki." "Sabi da Auren abin banza ne? me ka ɗauke ni ne? ka yi kuskuren raina Ƙarfin Ƴa mace wallahi, ina fa da Ƴanci Abdulkareem!" ya yi murmushi gami da shafar ƙeyarsa ya ce "Hmm!! Aaminatu tawa, kin yi kuskuren raina Hatsabibancin Ɗa Namiji musamman akan abin da ya ke so; Ta sigar lumana na ke so komai ya faru don haka na ara miki lokaci ki gama sha'aninki ki dawo gareni." Mewtch!! ta buga tsaki ta yi gaba ta na cewa "Saurararka ma ɓatawa kai lokaci ne." "Aaminath I Love U!"ya faɗa tare da raka bayanta da ido, duk da ta ji furucin nasa har cikin ranta amma ta ƙi juyowa ta ci gaba da tafiya gabanta na wata muguwar faɗuwa a kai a kai. a diririce ta shige gida dan kuwa zuwa yanzu jikinta har rawa yake bata bi takan kowa ba tashige ɗaki, "Aaminat! Aaminat!!" Mama ta ƙwala mata kira tana ce wa kina ina zonan ki karɓi wankinnan da su fati suke dama ke ya kamata kiyi dan kuwa su yanzu su ke zamaninsu" "Yasalam" ta furta tana dafe kanta wata sarawa yake mata jitake kamar ta mutu ta huta sede babu yadda zatayi haka zataje tayi wankin, ta shi tayi tana haɗa hanya labulan ta bankaɗa zata fita taji sallamar yaya Hamza da sauri ta tsaya tana zazzaro ido danda nan bugun zuciyarta ya ƙara tsananta. "Ummi ya kamata ki ɗauki mataki akan ya Abdul dan kuwa komai ƙara ta'azzara yake dan ɗazu kuka natarar ya nayi" Nana kadija ta faɗa fuskarta cike da

Chapter 6 of 16