tsagwaron damuwa, numfasawa tayi kafin ta ce "nima nalura kullum lamarin nashi ƙara taɓarɓarewa yake ya dena cin abinci kuma na rasa meke da mun shi" shuru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Hauwa'u ta ce "Ummi nakira Anti Maryam ta ce suna hanya" tsaki kadija tayi tare da cewa "wai ke kina hauka ne yanzu se kija tazo itama ta biyemai mukasa gane kansu" Ummi kuwa ta faɗa duniyar tunane tunane, Abdulkareem Abdussalam Abdurrahim Abdulmajid suka shigo tare da sallama cikin shiga iri ɗaya riga da wando baƙaƙe sunyi bala'in kyau sosai yayin da tsantsar kamarsu ta ƙara bayyana, zama sukayi kusa da Ummi Abdulkareem ya tada kai da cinyar Ummi Abdulmajid kuwa gefenta ya kashingiɗa Murmusawa Ummi tayi tare da ce wa Allah yayi muku albarka ya shirya mini ku Allah ya karemin ku a duk inda kuke Allah ya kauda idon maƙiya daga kanku" da Ameen suka Amsa baki ɗaya shuru ne ya ratsa na ɗan lokaci kafin Kadija ta ce "Na ga ka yi jan Ido Mutumina, wallahi ka rame." Cikin takaici da baƙin ciki ya zuba mata harara aransa ya na tunanin tsawwalawa irin ta ta duk ta bi ta dame shi a memakon ta barshi da Iyo a Kogin azabar da Aaminat ta jefa shi.. ya fara tunanin Kalmar da zai bata martani Abdussalam ya riga shi da cewa "Ke kuma Jar Munafuka ko? ba ki da magana sai can na yi masa ciwo sai ka ce jikinki." cikin sauri Abdulkareem ya ce "You're Right, I Like You Wallahi." Nana Kadija ta cika baki da iska gami da ɗauke musu kai cike da takaici, a ranta tana cewa "Ai gaskiya na faɗa kuma na damu da damuwarsa ne ba wai takura masa na ke yi ba." Abdulmajid ya ce "Zaginmu ki ke ne??" Zaro ido ta yi cikin sauri ta ce "Ni na isa?" Abdulkareem ya yi ƙwafa kafin ya ce "In Mutum ya isa ya gwada mana." ta raka shi da hararar ƙasan ido ba tare da ta ce ƙala ba. Hira su ka ci gaba da yi ana yi Abdulkareem da Nana Kadija su na faɗa kamar tagwayen Kaji.
danda nan Mama ta sauya fuska ta koma kalar tausayi ta ce "yanzu nikike faɗawa haka daga cewa kizo ki tayani wanki???" dafe ƙirji Aaminat tayi tare da zaro ido tabbas Mama azzaluma ce tafaɗa cikin ranta, wata tsawa Hamza ya daka mata gami da ce wa "mahaifiyar tamu kikewa rashin kunya dan ubanki kodan ba uwar ki bace" murya na rawa ta fara magana "wallhi ya Hamza banyi mata rashin kunya ba yanzu ma nafito daga ɗaki" Mama kuwa jin Hamza yana sauke ƙwandon bala'i ya sa ta fara matse hawayen makirci, Abba ne ya shigo da sallama da sauri Mama ta ce "yawwa Alhaji nagaji ka zaɓa koni ko ƴarka dan kuwa na gaji da futsarar da Amina take mini" ran Hamza kuwa in yayi dubu ya ɓaci jiyake kamar ya nakasa Aaminat yahuta Abba kuwa haƙuri ya shiga bawa Mama,
Umma kam kuka me ƙarfine ya kufce mata, ta rasa meyasa Mama ta tsaneta ita da ƴaƴanta kodan ita bata da ƴaƴa da yawa, itama ta gaji da cutarsu da ake agidan dan kuwa yanzu Abba ko ta ita bayayi,
jikake tassssss Abba ya wanke Aaminat da mari ya na ce wa "ke wace irin yarinya ce??!! mara tarbiya kin ƙi zaman aure sabida Uwarki da ta ɓataki kullum baki da aiki se tayar da masifa da bala'i to kinyi na farko kinyi na ƙarshe daga yau se yau na rabaki da duk wata alaƙa da zata haɗaki da iyalina kuje can ku ƙare keda Uwarki!!! Ni dai ban taɓa haifar Ɗa na yi nadama ba sai ke, a gidan Miji ma ba ki fasa iskanci ba Aaminat ina ki ke so ki kai Alhakin mutane? Da Mijinki fa ki ka dinga neman Mazan wasu kuma ya sake ki kin dawo ki na tayar min da hankali a Gidana Aaminat ki je don kanki, na yi bakin ƙoƙarina don naga na nema miki wani mijin kin yi Aure kin gyara rayuwarki amma duk kin Fatalar sabi da idonki a tsakar kai ya ke, Ba komai ki je don kanki" yana gama faɗin haka yajuya fuuuuuu ya fice daga gidan don kuwa in ya zauna ba abinda zai tsintsa sai ɓacin rai. durƙushewa tayi awajen tana wani kuka metsuma zuciya tayi da nasanin rayuwar ta a duniya wani juyi take ganin gidan yana yi.
Hamza kuwa har yanzu ranshi aɓace yake ganin yadda Mama take matsar hawaye "shikenan haka zamu zuba ido ta dinga yiwa Mama rashin kunya to wallahi haƙurinmu ya ƙare" Fati ta faɗa tana goge hawaye A hassale Aaminat ta ce "mukuma tamu uwar fa ta mutu sabida baƙin cikin da kuke ƙunsa mata???!!! ko a tunaninku bata jin zafin abinda kuke wa ƴarta kodan kunga tana kauda kai tana bawa uwarku girmanta?????!!!" "ke dan uwarki mu kike faɗawa haka??!" cike da ɓacin rai da baƙin ciki Aaminat ta ce na faɗa sede kakasheni nagaji da wulaƙancin ku yau sede ayi duk wadda za'ayi" wani zazzafan mari ya kifa mata ya ɗaga hannu zeƙara mata yaji an riƙeshi da sauri ya juya dan ganin waye idon shi yayi tozali da Omar, rai a tsananin ɓace ya ce "kayi kuskuren marinta da farko amma yanzu na iso wajen ba za ka ƙara ba, Zawarci fa ba hauka bane, Idan ita ƴar iska ce ƴan iskan nawa ku ke tare da su kuma ba kwa nuna musu ƙyama sai ita da take jininku sabi da Asararru ne ku? Kun lalata mata ƙaunar da ke tsakaninta da Mahaifiyarta har ma da mu ƴan uwanta, Ba Uwar kwabo sama da taku uwar kai ma ka sani." Hamza da yake wani huci kamar yunwataccen Zaki ya fizge hannunsa daga riƙon da Umar ya yi masa ya cafki kwalar Umar ɗin ya na cewa "Uwarka itace Uwar Kwabo domin ita ta ɗora yarinya a turbar Karuwanci, kuma ƙarya ka ke ka ce mu muka ɗora Uwarka akan tsanar ƴarta ai ta na da hankali ko mahaukaciya ce da za mu faɗa ta yarda?" Fati ta ce "Ƙila dai Mahaukaciyar ce." Wani lafiyayyen Mari Aaminat ta saukewa Fati a kumatunta, Fati ta ƙwalla ƙara gami da rintse ido sabi da azabar da ta risketa lokaci ɗaya; Aaminat da jikinta ya ke kakkarwa ta ce "Wallahi tallahi ki ka ƙara zagar min Uwa sai na lahanta rayuwarki, Kai kuma Hamza na dawo kanka, Ni Karuwa ce na faɗa na ƙara Idan akwai wanda nake bautawa sai ya hanani Karuwanci, Miji ɗaya ya yi min kaɗan don hakan na ke neman wasu ka gane?? Ƴan Iska Ƴaƴan Baƙar mace!" yuuuuuu Yaɓar!!!! Mama ta yi zaman Ƴan Bori a gurin ta na cewa ''Na shiga uku na Lalace wannan Ƴa ta zageni ta zage Mutuncina, ni ki ke kira Baƙar Mace duk baƙina ai ban kai baƙin Halin Hasiya ba, Allah zai min sakayya Azzaluma Hasiya kin haifi bala'i da Masifa Allah ya isa Tsakanina da ku." jin haka ya ƙara ta'azzara Fusatar Hamza ya yiwa Umar wata Muguwar Shaƙa wadda ta sa numfashinsa ya fara rikirkicewa.
Umma da Umaima su ka ƙara ɓarke baki su ka ci gaba da kuka, Aaminat kuwa idanunta sun ƙeƙashe hawayen ma babu, tsananin Fusatar da ta yi ya sa take jin kamar ta kama su ta yi musu mugun dukan ko Mutuwa ko Rayuwa, Fati Sai zubo Maganganu ta ke yi amma Aaminat ta yi mata banza don kuwa Hamza ta ke Hari.
©Autar Jarumai & INDO
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 13
Cikin kuka Umma ta ce "Aaminat! Umar! indai kun tabbata ni Mahaifiyarku ce to na ce ku bari domin ni, ku kuma Hamza ku yi haƙuri komai ya wuce ba na son tashin hankali." a hasale Hamza ya ce "Ba zan haƙura ba har sai mun kece raini ni da Wannan Yaron." Umar ya ce "Yaro ya na bayan uwarsa don ni ba yaronka bane, kuma in ka isa ka fito waje mu yi Wallahi sai na saɓa maka kamanni kawai zan ƙyaleka ne sabi da Umma ta sa baki." ya na gama faɗen haka ya hankaɗa Hamza da ƙarfi, ya yi baya taga-taga, daidai lokacin Abba ya dawo gidan, cikin ɓacin rai ya ce "Au ku na nan ɗin dai ba ku dena ba??, kowa ya ɓace min da gani ko ranku ya ɓaci, shashashan banza da ba ku san ciwon kanku ba, don fita sai ku zo tsakiyar gidana ku kama yi min tashin hankali iye?, to ba zan ɗauka ba, idan na ƙara jin labarin wani ya taso fitina sai na saɓa masa, marasa mutunci shashashai." nan fa ya ci gaba da faɗa ta inda yake shiga ba tanan ya ke fita ba. Umar da Hamza su ka yi sum-sum su ka fice su Aaminat ma su ka gudu ɗaki, Fati kuwa ɗakin Mama ta gudu su ka dasa Labarin Aaminat, Fati ta na bawa Maman labarin yadda ta so ayi ba ta so faɗan ya ƙare iya haka ba.
Aaminat kuwa banda kuka ba abin da take yi bayan ta shiga ɗakin.
Haka aka ci gaba da rayuwa a gidan salin alin kowa ya dena shiga harkar kowa tsakanin Ƴaƴan Umma da na Mama, Musamman Umar da Hamza, Fati kuwa tsakaninta da Aaminat sai dai baƙar magana da habaice-habaice, Aaminat kuwa duk hakan ba ya damunta burinta ɗaya ne ta ga ta bar gidan don haka ta zage da Addu'a tuƙuru.
Umaima kuwa duk jikinta ya yi sanyi, daga ita har Umman, sai yanzu su ka gane shigo-shigo ba zurfi Mama take yi musu ta cusa ƙiyayyar Aaminat a Zukatansu har ta sa su ke tsangwamarta.
A ɓangaren Mama kuwa ƙiris take jira ta samu abin yi ko ta samu abin da za ta laƙƙabawa Aaminat sharri, kullum cikin masifa da kumbure-kumbure take ba dan komai ba sai don ganin Umma da Umaima har ma da Umar duk sun koma jikin Ƴar uwarsu sun dena nuna mata ƙyama kamar yadda su ke yi Da.
Yau ta kasance Ranar Laraba, an tashi da Sanyi gami da Hazo sosai kasancewar Yamma ce ya sa sanyi ya ƙara yawaita.
DR Yarima
Sanye yake cikin Riga da wando Ƙananu dukkansu Farare sai Baƙar Jacket da baƙin Takalmi ya rufe idanunsa da baƙin Glass, hannunsa sanye da agogo golden.
cikin nutsuwa ya ke takawa har ya isa wajen Motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin Direba, ya na so ya tayar da ita domin tafiya amma ya kasa sabi da dogon tunanin da Zuciyarsa ta tafi yi. ba kowa yake tunani ba face Aaminat wadda komai nata yake matuƙar burge shi. "So ka ke ka ce ka kamu da Sonta?" ya tambayi kansa, da sauri ya zaro ido gabansa ya yanke ya faɗi, ko shakka ba ya yi kuma hakan ne, bai taɓa kawo cewa abin da ya ke ji zai iya zama so ba sai a yanzu wannan tunanin ya faɗo masa, girgiza kai ya yi gami da cewa "Ba zai yuwu ba, ba zan zama maci Amana ba, Kar ka yi gangancin haka." a sarari ya yi maganar duk da cewar shi kaɗai ne a gurin.
Cikin sanyin jiki ya shiga tuƙa Motar, ba ya son zuwa Gida Ammi ta tsare shi da tambayoyi don haka ya nufi gidan Kakanninsa a cewarsa sai ta yi tambayar da dalili.
*Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
A Falon Farko ya tarar da E,iya ta na zaune kan kafet ta na Azkhar, ta sha Hijab wanda ya karɓi fusukarta ta yi kyau sosai, zama ya yi kan kujera ya saka guiwar hannunsa na dama akan cinyarsa sannan ya buga tagumi ya zuba mata ido cike da shakiyanci.
Da farko banza ta yi masa sai da ta ga ya na neman sawa ta ƙware sabi da kallo ta yi sauron kammala Azkhar ɗin ta yi Addu'a sannan ta kalle shi cike da sababi ta ce "Kai in ba a san asalinka ba sai a ce Mayene Wallah!" ya tintsire da dariya gami da cewa "Hajiya E'iya Matata ta kaina, gani na yi kin yi kyau sosai shi ya sa nake kallonki." "Aff!! Ƙarya ka ke yi, da dai bansan halinka ba sai ka shogama ni." dariya ya yi sannan ya ce "To Ina wuni" ta ce "Da ban wuni ba ai da ba ka ganni ba." ya ce "Daɗina da ke Sababi wallahi, Ina ƴan ƙannen nawa?" ta taɓe baki sannan ta ce "Ƙannenka sun tafi Yawon Ta Zubar" cikin sauri ya ɗora hannunsa akansa gami da cewa "A'uzubillah!!" ya furta ya na dariya, ci gaba ya yi da cewa "Wai ba na ce ki dena cewa Yawon ta zubar ɗin nan ba? kin fa san me ake nufi da hakan" "Na sani sarai kuma ba zan dena faɗe ba, yawo ba dalili ina ya ga amfani? gaskiyar ce ba kwa so kuma sai na faɗa, tsabar iskanci fa Huzaif Baby ya ke kiran kansa." Dr Yarima ya ƙara Kecewa da dariya ya na cewa "Wallahi ba ki da dama Matar nan, shi ya sa fa da tunani ya yi min yawa na gudo wajenku don nasan anan ne zan samu farin ciki, in banda rikicin tsufa don ya cewa kansa Baby ai ba wani abu bane, kema ai Babyn ce." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, ta riƙe haɓa da sauri gami da cewa "Ni!!!!? rufa ni ba da ni ake wannan Tumɓelen ba, ba na so, in haifi ubanka ka ce min Baby banda ka raina ni?" Miƙewa ya yi ya na cewa "Ina Budurwata? na lura yau a fusace ki ke ma." ta ce "A'a zauna mana, ko ruwa ban baka ba fa, ka ce ka na neman Budurwa bayan ga mata? zauna maza za ta zo ta sameka ta na Sama ƙila ma kwalliya take maka." ya koma ya zauna tare da cewa "Ai daɗin budurwa kenan in ciki ta ƙi sai a fita waje." ta taɓe baki murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ka ji da shi dai." Ɗakko masa ruwan ta yi a gora tare da kofi ta dire masa sannan ta koma ta zauna. shiru ne ya biyu baya kafin ya buɗe baki zaiyi magana Inni ce ta katse shi da cewa "Ah marhaba da zuwanka Saurayina." ya saki murmushi gami da cewa "Yauwa dama ke nake nema, tin da na shigo kin ganta nan banda faɗa ba abin da mu ka yi, kai amma gaskiya kin yi kyau Budurwar Mijin Wata." ya faɗa ya na kallon E'iya taɓe baki ta yi ta kauda kai. shi da Inni su ka sa dariya, Inni ta ƙaraso kusa da shi ta zauna, bayan sun gaisa su ka ci gaba da hira.
Sai misalin ƙarfe 9:53pm ya shiga gida, Mamy ta na zaune a Falo ta na kallo, ya na ganinta ya yi ƙasa da kai ya na shirin zillewa sashinsa, "Yarima!!" ta kira shi ba tare da ta kalle shi ba. tin daga yanayinta ya fahimci a cike take fam, shafar ƙeyarsa ya yi a ransa ya ce "Shi kenan rigima ta tashi." ƙarasawa ya yi, ya gaisheta ta amsa kadaran kadahan sannan ta ci gaba da cewa "Tin Yamma ka ce min za ka ɗan je can kuma ga shi har goma, ina ka je? me ka zauna yi?" "Gidan su E'iya na je." mewtcss!!! Mamy ta ja tsaki kafin ta ce "Wai me ya sa ni ba za ka ji maganata ba sai dai ta ubanka??? ban haneka da zuwa wajensu ba wai??" a rayuwa Yarima ya na bala'in takaicin ƙiyayyar da Mahaifiyarsa ke nunawa Kakarsa ta wajen Uba, ya rasa me ta yi wa Mamyin da ta tsangwameta haka har ta kai ga hana shi zuwa wajensu, "Mamy su ɗin fa Kakannina ne ai ba komai bane don na je na gansu, don Allah ki dena irin haka kema fa uwa ce, yanzu idan Ƴaƴana su ka yi miki haka ai ba za ki ji daɗi ba." Mamy ta saki baki gami da cewa "Auu?? lallai ma, ni ka ke faɗawa haka??" ya ce "Ki yi haƙuri kawai ina takaicin hakan ne." Ta jinjina kai gami da cewa "Danƙari Maƙari" bai bari ta ci gaba da wata maganar ba ya miƙe tare da yi mata sallama ya sanar da ita ba zai ƙara sakkowa ba.
Ko amsawa ba ta yi ba ta bi shi da ido har ya ɓacewa ganinta.
Bayan ya watsa ruwa ya yi shirin Bacci sai kuma tunane-tunane su ka sake yi masa sallama, bai iya rintsawa ba har sai da ya yanke hukunci zai gayawa Aaminat ya na sonta kuma ya tsara zuwa gidansu gobe.
Sai mu ce Asbha ta gari.
(To masu Karatu ya yi Bacci kuma ku kwanta kafin gobe mu garzaya Gidan Alhaji Aminu Mai Kasuwa don jin Halin da Abdulkareem yake ciki😍)
*Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai
Share Fisabilillah
©️©️
INDO tare da SALMA AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 14
Washegari.
Abdulkareem ne kwance kan Gadonsa ya lulluɓe gangar jikinsa da bargo fuskarsa ce kawai a buɗe sai muzurai yake ba alamar walwala a tare da shi.
Tunanin irin Yankan ƙaunar da Aaminat ta ke yi masa yake yi gashi duk yadda ya nemi hanyar da zai dakatar da hakan ya kasa samu, ya rasa ta inda zai bi ya shawo kan matsalar.
Nana Khadija ce ta yi sallama ba tare da ta jira ya amsa ba ta shigo ta zauna a gefen gadon, fuskarta a ɗaure ba alamun wasa, ko kallonsa ba ta yi ba ta ce "Sai wani ɓoye-ɓoye ka ke yiwa mutane, idan ba ka gayawa wani ba a cikinmu ai ka gayawa wani, ko an gaya maka ana iya samun maganin cutar da ba'a santa ba? ni na san akwai wani abu a Zuciyarka amma sai raina mana hankali ka ke yi." "Ke har wani hankalin da za a raina gareki?" ta ce "Ka ga ni fa ba wai na zo mu yi faɗa bane; na zo ne da batun sirri tsakaninmu, banda abinka in ka gaya min ai ka samu abokiyar jaje ko da ba za mu iya yin maganin abin ba. Nazari ya ɗan yi kafin ya ce ''Ba na son gaya muku ne duk ku tayar min da hankali." "Faɗi indai ni ce ba ni da matsala. "Kinsan Aaminat? ta gidan su Waleed.
ta zaro ido gami da cewa "Me ta yi maka?" "Ni ne na yi mata laifin domin kuwa na kamu da sonta, a da kawai tausayinta nake ji amma yanzu abin ya wuce nan, ina son ganin farin cikinta ko ta wane hali, amma ita ta ƙi ƙaunata ƙarshe ma nema take ta ba wani damata ya yi amfani da ita. jikin Nana Khadija ya yi mugun sanyi murya a sanyaye ta ce "Amma Ya Abdulkareem kai ma ka san hakan da kamar wuya ya akai ka bari hakan ta faru?" ya ce "Ni ma ban sani ba, amma kema kin sani ba a yiwa so shamaki, ki bar zancen nan kawai tin da kin ji, ki tayani da Addu'a kawai, tashi ki ban guri yanzu nima zan fito." miƙewa ta yi jiki a sanyaye ta yi hanyar fita, duk hankalinta ya tafi a tunanin ta yaya Abdulkareem zai iya Auren Sa'ar Yayan yayansa? ta yaya ma Iyayensu za su yarda?, da wannan tunanin ta koma Falo ta nemi guri ta zauna sannan ta ci gaba da tufkawa da warwarewa.
"Yaya Aaminat kin karya kuwa?" Umaima ta faɗa tana zubawa Aaminat ido "Umaima meyasa yau kike tambaya ta na ci abinci??" murmusawa tayi sannan ta ce "da da yanzu ai ba ɗaya bane" murmushin ita ma tayi kafin ta ce "to na karya Umma ta zuba mini abin kari" "ai na zaci baki karya ba shiyasa" "Umaima kina son wata abaya tawa??" ina so mana kogi ai bai ƙi daɗi ba" "sawa ɗaya nayi mata naji ta fita daga raina" "nikam ina so wallhi dama akwai wani takalmi naki ko kibani ko mudinga sawa tare" tintsirewa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 16