Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi da dariya Umaima ta zaki baki tana kallon ta ta ce "yaya Aaminat dariyar mekike??" "kece kika bani dariya wai ko na baki ko musa tare" "A'a to bazaki bani ba" Aaminat ta ce "A'a zan baki mana ai baki taɓa tambaya ta abu na hanaki ba, kin manta lokacin da ina budurwa kafin nayi aure wata ranar se na zo sa abu se naga kinyi ɗagwass-gwass a ciki" dariya sukasa Umaima ta ce "rayuwa kenan dan ma sharrin shaiɗan ya ratsa da zigar Mama da Fati suka sa na juya miki baya amma ki yi hakuri ki yafe ni don Allah, yanzu na gane kuskurena" dandanan annurin fuskar Aaminat ya ɗauke ta ce "ba na son naji kina irin wannan magan-ganun ai baya tawu ce ni na yafewa kowa" rausayar da kai Umaima tayi ta ce "ai nadena daga yau" "kyaji dashi de" Aaminat ta faɗa fuska ɗauke da murmushi dariya Umaima tayi kafin ta ce "wai kina da labarin wani sikarin guys da yace yana sona??" "A'a bani da labari se kin shaƙamini" "Ummm ai nake faɗamiki shiɗin maƙura ne wallhi gashi kyakkyawa" "Allah ƙanwata kice kin kware masa?" dariya ta ɗanyi ta ce "ai dole sabida tsabagen kyanshi gashi ɗan wanka babu ruwan shi" Aaminat ta riƙe baki ta ce "lallai Autar ɗakinmu haka kika kama da wuta??? ya fini kyau kokuwa?" dariya suka sa cike da nishaɗi Umaima ta ce "ai kowa da matsayi shi kin fishi kyau" haka suka cigaba da hira suna dariya da nishaɗi. Misalin ƙarfe 4:30 na yammaci Yarima ya shirya cikin dakakkiyar rantsats-tsiyar shadda fara ƙal har ɗaukar ido take baƙar hula dara yasa baƙin agogo baƙin takalmi yayi kyau sosai fitowa yayi Falo a ya na taku ɗaiɗai, Ammi na zaune ta na kallon TV dama aikinta kenan ko Abi ne yadawo bata kulawa da shi abinci ma sede ƴan aiki su kai masa ko Yarima, ɗan ƙaramin tsaki yayi sannan ya ce "Ammi ni zan fita" "Allah ya tsare kuma saura kabiya gidan kakannin ka" ya ce "Ameen" yafice zuwa harabar gidan Kai tsaye wajen ajiye Motoci ya nufa, wata tsuleliyar mota baƙa ya hau me tsadar gaske yanufi Gadon Ƙaya gidan su Aaminat. *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* be ɓata lokaci ba ya ƙarasa Unguwar wayarsa ya ɗauka ya danna wa Siyama kira bugu biyu ta ɗauka tare da sallama ya sanar mata ya ƙaraso "to" kawai ta ce ta tashi ta yafa mayafinta tayi waje sai gidan su Aaminat. Ta zaune tana rera karatun alƙur'ani maigirma cikin nitsats-tsiyar muryar ta me daɗin saurare. zama Siyama tayi Aaminat ta taƙaita karatun dan ganin Siyama ta yi addu'a suka shafa Siyama ta ce "kin fa yi baƙo" "nayi baƙo kuma wanene?" ta faɗa cikin sigar mamaki Siyama ta rausayar da kai ta ce "ke de kizo muje" "kinga nifa babu inda zani sekin faɗa min kowaye" "Yarima ne" rassss!!! taji gabanta ya faɗi takasa cewa komai se kallon Siyama da take to meya zo yi wajenta ta tambayi kanta Siyama ta ce "yana kira fa kihanzar ta"! taɓe baki tayi kafin ta ce "wai na hanzar ta sabida ga ubana ya zo ko??" Siyama kuwa roƙon Aaminat ta shigayi tana magiya akan tafita, Siyama ta ce "tunda bazaki ba bari na faɗawa ya Omar shiya tilastaki koma dole kije" tana shakkar ya Omar sosai dan kuwa ba shi da wasa hakan yasa ta ce "zanje base kin faɗawa Ya Omar ba amma da sharaɗi bazan daɗe ba!" Siyama ta ce kokefa harkinfi kyau yanzu" Aaminat ta kai mata duka ta ce "dani mummuna ce??!" "A'a karki kaini inda Allah be kaini ba" ta shi tayi ta zura zumbulelen hijabi ta feshe jikinta da turare meƙamshin gaske, Siyama ta ce "sekizo muje ai ko" ƴar dariya tayi gami da cewa "sekace wata babata se wani magana kekemin sama sama" Siyama taja hannuta ƙiii zuwa ɗakin Umma, cikin jin kunya Aaminat ta ce "Umma zanje nayi baƙo" Umma ta ce sekun dawo kukula kunji ko Allah yayi muku albarka" Siyama da Aaminat suka amsa da Amin. Ɓangaren Yarima kuwa yana jikin motar sa ya jingina ya harɗe hannayen sa a ƙirjin sa kanshi a ƙasa kamar tsohon munafuki sallmar da yaji ce ta dawo dashi hayyacin sa yayi saurin ɗagowa karaff suka haɗa ido da Aaminat wani kallon kallo suka shigayi babu kiftawa dariyar da Siyama tayi ce ta dawo dasu hanyyacin su, Aaminat tayi saurin kauda kai gefe, sannan ta ce "i...ina wuni" wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da cewa "lafiya lau" wani sihirtaccen kallo yabita da shi yana wani limshe ido wani tartsa-tsi yakeji zuciyar sa nayi sede ya ɗaura ɗamarar bayyanawa Aaminat soyayar shi. Siyama ta ce "To ni dai sai anjimanku." Yarima ya ce "Na gode Siyama ki gaida Aunty." ta ce "To" Maida kallonsa ya yi ga Aaminat kafin ya yi gyaran murya sannan ya ce "Aaminat kin bani dama na bayyana soyyata agareki??" rasss-rasss!!!!!! gaban Aaminat ya faɗi tunanin Abdulkareem ne ya keto mata, Yarima ya ɗan ƙara takawa yaje gaf da ita kana ya ce " kitaimaki wannan bawan Allahn da idanunsa su ka rufe akan sonki Aaminat." shiru ya ɗan yi kafin ya ci gaba da cewa "Ina sonki!!! ba na so ki ce min a'a don Allah ki yi tunani me kyau akaina." a hankali ta ɗago kanta ta zuba masa idanu Zuciyarta na wani irin tsalle, ba shakka idan ta ce Ba ta burgeta ta yi ƙarya, haka idan ta ce ba za ta iya son shi ba ta yi babbar ƙaryar da ƙarshe ta zo ta ji kunya, sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba, Abdulkareem kawai take tunani don ba ta san yadda za su ƙare ba, bayan haka kuma ta gaji da sanya shi ƙunci duk ta dalilinta. tattausan murmushi Yarima ya sakar mata wanda ya ratsa dukkan sassan Zuciyarta, tayi saurin yin ƙasa da kanta yayin da itama murmushin yake neman kufce mata. murmushi me sauti yayi kafin ya ce "kin amince da Soyayyata???!!!" murya a harɗe ta ce "Zan yi shawara" ya ce "shikenan kiyi shawarar amma dan Allah karki sanarmi mummanan saƙo" bata ce komai ba ta juya zata tafi taji ya ce "kitsaya muyi sallama mana ko" cakk ta tsaya batare da ta juyo ba, ya juya mota ya ɗakko wata ƴar ƙaramar leda sannan ya nufota, miƙa mata ya yi gami da cewa " ga wannan waya ce da layi aciki inna koma gida zan kiraki" ƙin karɓa tayi ta ce "A'a kariƙe kayarka nima ina da ita" "nasan kina da ita shiyasa na baki wannan" ajiyar zuciya ta sauke aranta ta ce "wannan bawan Allahn yafiya ta kura" ya ce "Don Allah ki karɓa ba don ni ba, sannan duk shawarar da ki ka yanke ki kirani da ita kar ki barni ina tunane-tunane." karɓa ta yi gami da godiya sannan ta wuce cikin gida. seda ya ga ta shige gida sannan ya juya ya nufi motar shi cike da farin ciki da kuma zullumi kar Aaminat ta ce bata son shi.... INDO tare da Ƴar Uwa Salma Auta [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 15 Tana shiga gida ta faɗa kan gado tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Siyama ce ta shigo ɗakin tare da sallama, Aaminat ta amsa tare da cewa "dama so nake naje gidanku yanzu se gaki," Siyama ta ce "Yariman ya tafi??" wani kallon sheƙe-ƙe Aaminat tayi mata gami da cewa "to in be tafi ba a ɗakin nan kikeso ki ganshi? ba daga ƙofar gida kike ba?" Murmusawa Siyama tayi ba ta ce komai ba ganin haka yasa Aaminat cewa "Siyama Yarima yana sona nace zanyi shawara ki bani shawara" rausayar da kai tayi sannan ta ce "ni a ganina Yarima bashida wani aibu mutum ne me dattaku da kuma sanin ya kamata sabida haka ki amince masa kawai" shiru ta ɗanyi kafin ta ce "Siyama kiyi tunani ya Abdul zeji idan har naso wani ba shi ba kuma shi ya fara cewa yana sona sannan Yarima" tsaki Siyama tayi kafin ta ce "kinga kema kinsan kina son Yarima kuma me zesa kidinga tunanin Abdul shifa ba sonki yake ba kawai tausayin ki ya keji kuma shi Abdul inde har Yarima ze saki farinciki to ze iya haƙura ya barwa Yarima" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Siyama ta ce "ni zantafi" "ince mai ina sonshi??!" "ruwa ya rage naki" "Siyama wai meyasa kike wani fushi-fushi ne??" murmushi ta ɗanyi ta ce "ba fushi nake ba kede kawai in Yarima ya kiraki to kice mai kin amin ce dan Allah ba don nu ba, nima kaina ina so in ga kin fita daga wannan halin, ace mutum ba shi da aiki sai tunanin bara anci wake" "in sha Allah zan faɗa mai ki de tayani da addu'a Allah yasa Alkairine" "Ameen" Siyama ta ce sannan ta fita. Misalin ƙarfe tara na dare kira ya shigo wayar Aaminat ta ɗauka zuciyar ta na wani bugu-bugu sallama yayi mata, ko ba a faɗa ba tasan Yarima ne "Assalamu alaiki sarauniyata fatan kina lafiya" ta amsa da cewa "Wa'alaikumussalam lafiya lau" shiru ne ya biyo baya kafin Yarima ya katse shirun da cewa "kina farin cikin shiga rayuwarki da nayi kuwa??!!" murmushi me sauti ta ba tare da ta ce komai ba, hakan ya bashi damar ci gaba da magana "amincin Allah ya tabbata gareki a duk tsawon rayuwarki masoyiyata, ina so ki faɗa min ko da hankalina zai kwanta numfashina ya dena sassarfa, shin kin aminta da soyayyata???!!" rasss!!!!!! taji gabanta ya faɗi ta yi shiru ta na zazzare ido, jin ya ƙara maimaita tambayar yasa ta tattaro nutsuwar ta fara magana cikin in ina "na...na.amince" "Alhamdulillah Allah kai ne abun godiya Allah na gode maka da ka mallaka min zuciyar da nadaɗe ina muradin samunta".. bayan ya gama godiya ga sarki Allah ya ci gaba da cewa "Ina Sonki Aaminat !! Ina fatan kema ki so ni da dukkan Zuciyarki" wani murmushi me sauti ne ya kufce mata shima murmushin yayi, ta ce "ina jin bacci se da safe" sukayi sallama cike da farin ciki da jindaɗi. haka rayuwa taci gaba da tafiya na wani lokaci kullum Yarima da Aaminat ƙara shaƙuwa suke.... *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* sanye take cikin riga Abaya marun tayi rolin ɗin mayafin tayi bala'in kyu sosai duk da bawata kwalliya me hayaniya tayi ba amma tsan-tsar kyawun ta ya ƙara baiya na dama Aaminat fara ce ƙal dan Umma ta biyo a fari. mudubi ta kalla fuska ɗauke da murmushi ta ɗauki turare ta feshe jikinta sannan ta zira takalmin ta, Umaima da bata iya shiru ta ce "yaya ina zuwa haka kinyi kyu wallhi" murmusawa tayi ta ce "gidan su Siyama zani" Umaima ta ce "bari nazo muje" kafin kace meye wannan ta yafa mayafin ta, Aaminat ta ce "kai kin fiya son yawo wallhi" "nide muje" fita sukayi ƙofar gida kamar daga sama taga Abdulkareem sanye cikin shigar ƙananun kaya riga fara da wando baƙi yayi bala'in haɗuwa yajingina da tamfatsetsiyar motar sa me tsadar gaske ya harɗe kafa tare da kauda kai gefe, Aaminat kuwa zuwa yanzu ta gama tsinkewa da Abdul ido ta tsira masa babu ƙiftawa, jikinta se rawa yake tabbas ta sani yau haƙurin Abdul ya ƙara kuma seta ɗanɗa na kuɗar ta, a hankali ya fara takun shi me cike da ƙasaita da jin kai da kuma zarra, seda ya zo gaf da ita sannan ya tsaya da hannu yayiwa Umaima Alamar ta bar wajan, jikin na ɓari ta saki hannun Aaminat ta fece, wani tattausan murmushi yayi me cike da baƙin ciki da takaici, sannan ya fara motsa kyakkyawan bakinshi ya ce "Aamaint ina sonki amma ba kiyi la'akari da haka ba kike soyayya da wani wanda baki san kowaye a wajena ba,.. ya ɗan numfasa kafin ya ce ko be faɗa miki muna da alaƙa da shi ba?? Aaminat kinci Amana ta kuma ina so kisani har yanzu ina so ki kuma muddin ina raye bazaki Auri yarima ba,.." "nikam naga rayuwa" ta faɗa cikin ranta wani tsallle zuciyar Abdul take kamar zata fito waje dafe ƙirjin shi yayi tare da cewa "Aaminat ina sonki soyayyar ki tana azabtar dani tabbas zan iya rasa rayuwa ta daga ranar da akace kin Auri wani wanda bani ba".. ya zuba guiwoyin shi biyu a kasa ya karyar da murya cikin sanyi da kuma raunin zuciya ya ce Aaminat ina sonki ina ƙaunar ki kece duk wani farin ciki nawa ido na ya rufe bana ganin kowa seke kunne na ya toshe bana jin komai idan bake ba duk wani mafarki na kece ina sonki soyyayar da ni kaina bansan iya adadin ta ba, son da nake miki ya shafi rayuwar gidan mu dan kuwa yanzu ta sanadiyyar soyayyar ki gidanmu ya canza, Aaminat bata san lokacin da zuciyar ta ta karye ta fara kuka tana cewa, "Dan Allah Abdul karage wannan makauniyar soyayyar da kake min inna ce bana son ka nayi ƙarya amma Abdul shifa Aure ba wasa bane, kaifa yanzu baka isa mizanin da zaka Auri mace kamar ni ba in kuwa ka aure ni to ka tar watsa rayuwar ka karka manta ni BAZAWARA ce" ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me tsuma zuciya, Abdul kuwa ya kasa koda motsa ɗan yatsan shi ne, har yanzu guyawun sa na ƙasa ya sunkuyar da kai, hawaye masu azaba da kuma zafi suna sauka daga idon sa zuwa ƙasa, sun ɗauki tsahon lokaci a haka kafin Abdulkareem ya ta shi ya juya, seda ya taka sau uku sannan ya ɗan tsaya ya ce Aaminat kisa aranki duk tsanani duk wuya sena Aure ki!!!!!!!!!" yana gama faɗin haka ya juya ya shige motarsa ya bata wuta, da gudu ta shiga gida tana kuka ta wuce ɗakinsu... *Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai Share Fisabilillah *©INDO Tare da SALMA AUTA* [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 16 Mama da Fati Suna zaune a tsakar gida suna Taɗi, ganin Aaminat ta shigo tana kuka yasa su jindaɗi Mama ta sheƙe da dariya gami da cewa "Allah sarki bazawara yau ma saurayi ya gudu" Fati ta ce "dama waze Auri bazawara se tsoho ko talaka" Mama ta ce "kekuwa ƴata daga me jirgi se me mota" suka sa dariya kafin su ci gaba da hirar Aaminat. Aaminat kuwa ta daɗe ta na kuka ganin ba zai kaita ko ina ba ya sa ta share ƙwallarta. Yarima da Abi zaune suke a falon Abi suna taɓa hira Abi ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce "Yarima ina neman shawarar ka" Yarima ya tattaro dukkan nutsuwar shi sannan ya ce "Abi ina sauraren ka" Abi ya murmusa gami da cewa "dama ina son ƙara Aure ne shi yasa nake neman shawarar" rassss!! gaban Yarima ya faɗi Abi ya ce "nasan bazakaji daɗi ba a ce na yiwa mahaifiyar ka kishiya amma idan kayi haƙiri komai ze dedeta" murmushi Yarima yayi sannan ya ce "Abi me zesa kace zaka ƙara Aure yanzu bayan girma ya fara kama ka??!" "Abubakar ina son ƙara Aure ne sabida halaiyar Hajiya Hafsa, kai ma ka san ba ta ƙaunar Mahaifiyata" Yarima ya ce "shikenan Abi ina goyon bayanka kuma ni zan taya ka cukucukun Auren" "nagode ɗana" Yarima ya ɗan yi dariya cike da zolaya ya ce "Abi wace amaryar" "Zainab sunan ta tana aiki ne a ƙarƙashin kamfanina kuma na yaba da hankalin ta da nutsuwar ta" Yarima ya ɗanyi murmushi me sauti gami da cewa "Allah yasa Alkairi, kuma ka sanar wa Ammiee kuwa???" "A'a yau de na yanke zan sanar mata duk da nasan hankalin ta ze tashi amma zanyi ƙoƙarin fahimtar da ita" cigaba su ka yi da tattaunawa, Yarima har ya fara tsara yadda za'ayi komai. zaune suke a tafkeken Falon Ummi suna hira cikin nishaɗi gami da ƙaunar juna, "Ummi wai nida ya Abdul wayafi wani kyau??" Nana khadija ta yi tambayar ta na wani mole baki don ta ƙara tatso kyaunta, dariya su ka sa kafin Abdurrahim ya ce "Allah sarki Nanaro wai gasar kyau zakiyi da Abdul??!" cokalo baki tayi kana ta ce "so nake Ummi ta raba mana gardama wai ya ce ya fini kyau ni kuma na ce na fishi" dariya Abdul yayi gami da cewa "Kadija ai kinsan de nafiki" "haba de taya namiji zefi mace kyau??"! Nana Farida ta faɗa cike da nuna gaskiyar ta, ita kuwa Ummi ta kasa cewa ko mai se ido da take binsu da shi gami da murmushi, tana ƙara godewa Allah da ya a zurtasu da ƴaƴa masu haɗinkai da kuma son junansu, "Ummi ki raba mana gardamar nan yau dai" Abdulmajid ya faɗa ya na dariya, numfasawa tayi kana ta ce "nide a ganina baku da banbanci kamarku ɗaya kamar an tsaga kara babu wanda yafi wani kyawu" dariya su ka sa, Kadija ta tumɓuro baki ta ce "ni dai bana kama da shi gaskiya na fi shi kyau" Abdussalam ya ce ƴar zafi ce ta isheki" Abdulmajid ya ce ke kuma me cewa mata sunfi kyau shiyasa naga ai suna ƙarin kyan suje su lafta hoda wai su adole mata" Ummu ta gyara zama gami da cewa "dan Allah kudena musun nan haka" "mundena Ummin mu" Abdul ya faɗa yana kwantar da kai a kafaɗarta. *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* yau ta kasance ranar Juma'a se shirye shiryen ɗaurin Auren Alhaji Saadiƙ (Abi) ake yi. Ammi kam ta kasa zaune ta kasa tsaye se sintiri take hankalin ta ya gama tashi, in ta tuna befi saura awa ɗaya ayimata kishiya ba seta zabura kuka kam Ammi tayi shi gashi ta ɗauki lefin ko mai ta ɗorawa Yarima da su E'iye da Inni a cewar ta su suka sa shi. Abi ya shirya tsaf ya nufi sashin Ammi ƙofar ɗakin ya tura yaji gam a rufe ƙonƙwasawa ya shigayi yana ɗan kiran sunanta, ya kusa minti goma yana aikin abu ɗaya bata buɗe ba haka ya juya jiki a sanyaye, ya nufi ɓangaren Yarima a zaune yake yana danna waya Abi yayi sallama zama yayi a gefen gadon ya ɗan kalli yarima ya

Chapter 8 of 16