gidan duk wani abu da za'ayi ta na ciki ta ƙi fitowa, ta na kallon mutane har zuwa ake ana leƙota ana ɗan nunata, ita dai ba ta ce komai ba sai dai in abin ya yi mata ciwo ta ɗan matse hawaye, jiran tafiyar su Umma take yi su kuwa sai Goman dare sannan su ka tashi tafiya, lokacin da su ka iso gida Sha Ɗaya sauran Ƴan Mintina, ta ji daɗin hakan don kuwa duk Fitinannun yaran layinsu sun shige gida har shi kanshi Gogan, tinda ta yi siff ta shige gidan makonci kawai ta nema don anan ne za ta samu damar yin kukanta ba tare da kowa ya sani ba.
Yau Abdulkareem ya na zaune shi kaɗai sauran Yaran kowa ya tafi uzurinsa wasu makaranta, Walid ne ya tawo ya na taku a ƙasaice kamar wani Yaron Giwa shi a dole babban Mutum, sai da ya kalli Abdulkareem sannan ya watsar ya wuce, Abdulkareem ya miƙe ya riƙe hannunsa kam sannan ya ce "Kai daga ina kake??" "Ina ruwanka? ka aike ni ne? ba na son shishshigi ba kwarjini" Wani kyakkyawan Mari Abdulkareem ya tsinka masa sannan ya ce "Da ni kake gaba ko?? sabi da na doki ƙanwata da ba daga gidanku ta fito ba, ni za ka nunawa rashin hankali?? ashe kasan abin da ciwo? ranar nan da ka dokawa YaYa Aaminat Ƙwallo don ban nuna ɓacin raina ba shine kai za ka yi Gaba dani sabi da na doki Ƙanwata ko??" cike da rashin kunya irin tashi ya ce "Eh an buga mata ɗin ai naga YaYata ce ko, wallahi ka ƙara dukana sai dai mu daku." wani lafiyayyen marin ya ƙara zuba masa sannan ya ce " Na ƙara maka kuma zan ja maka kunne, rashin kunyar da ku ke yiwa Aaminat ta isa haka, nima ina jin zafi bansan ba daɗi ba sai da ka fara gabani wai akan ka na son Ƙanwata, to wallahi ka shiga hankalinka da kai da ita duk ina iya karya muku ƙafafu na zauna lafiya, nima ina jin zafin da ka ji a duk lokacin da kuka wulaƙanta Aaminat kawaici kawai nake muku" Walid ya yi tsaki kafin ya ce "To wai kai me kake nufi?" "Ban damu da sai ka san me nake nufi ba inda ka fahimci akan abin da nake magana, kuma wallahi tallahi ka je ka yi min munafurci ko a gida a Layi sai na lahira ya fika jin daɗi, ni zan rabaka da farin cikin rayuwa ne har ka koma ga Allah, kuma na ƙara yi maka magana kai min banza ka ga in ban sauke maka na tauna ƙashi ba." Walid ya zumɓuri baki, yasan an fi ƙarfinsa don haka bai yi ƙoƙarin wani abu ba, ya na sakinsa ya wuce gida ya na gungunai da kumfar baki.
Mama ta bankaɗe labule ta fito ta na cewa "Wa ya taɓa ka???" "Wancan Dan Iska Abdulkareem ɗin ne har da marina ya yi ba abin da na yi masa kuma." "Kanbutar Duma???, sai na sa an ci uwar Abdulkareem ɗin nan sannan zai fita idona in rufe, Umar! Umar ! maza kira min Umar ai ya dawo" Walid ya fita kiran Umar Mama kuwa ta ci gaba da zazzaga masifa, Umar ya na zuwa ta ce "Wannan Abdulkareem ɗin nake so ka ci min Ƙanwar Tsohuwarsa, ya raina min Ƴaƴa yanzu Fati in ka ga wulaƙancin da yake sa yara su yi mata sai ka sha mamaki, yanzu ka ga ya kama min Auta ya mammara ba tare da laifin komai ba, to wallahi in ya na da ƙarfin damtse ai doka ta fishi, ni zan iya yin shari'a da shi tinda ba shi da hankali" Umar ya yi murmushin takaici kafin ya ce "Mama indai Mari ne kawai ayi haƙuri don kuwa Kinsan Waye Alhaji Aminu Mai Kasuwa, ya na da kuɗi kuma ya ɗaurewa ɗansa abun shi yasa ya ke tata iskancinsa, ba za mu iya nuna masa yatsa ba gwara ma ki yi haƙuri, Shari'ar da ki ke taƙama da ita ba za ta goyi bayanki ba bare har ki ga ribarta, ba iya ku ya ke yiwa ba ya gagari kowa a layin nan, ki na gani fa ko Ball da su ke yi a layin Matasan Layin sun yi ƙoƙarin hanawa daga nan har gaban hukuma yaron sai cewa ya yi ai idan ana so su dena sai dai a basu babban Filin Ball, kuma lokacin manya ne su ke yin wasa a a wai sai dai manya su haƙura su ba yara, ance su dinga yi da rana ya ce ai su ba cima zaune bane su na sana'a kuma suna neman ilmi ba su da lokaci sai da yamma, dole fa muna ji mu na gani mu ka ƙyalesu, Kina gani a layin nan manyan samari ƴan shekara Ishirin da Bakwai ma ba za ki gani ba bare ƴan talatin sabi da tsabar bala'in yaron nan duk sai dai su bar unguwar nan su shiga unguwar maƙota sannan su kafa Majalisa, yanzu babu samarin da za ki gani sai yara ƴan sheka Ishirin zuwa ƙasa, Mama wallahi yaron nan tantiri ne fiye da tunaninku, kaff yara masu tasowa ya lalata su ba sa ganin kowa da gashi sai shi.
Mama ta ja tsaki sannan ta ci gaba da yayyafin masifarta sai ma ta koma cewa don ba Ita ta haifi Umar ɗin ba ne ya sa ya ƙi ƙwatarwa Ɗanta haƙƙi, shi kuwa Umar sai ya bar mata gidan Umma ma ta na jinta ta yi shiru, Aaminat kuwa ta na son yin magana akan rashin kunyar Walid ɗin amma idan ta tuno waye Abdulkareem sai ta ja bakinta ta tsuke.
©️INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/DkGGck6Es6l4w7KMwiaGVZ
*AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 7
Bismillahirrahmanirrahim
Fati ce ta fito daga ɗaki ta na cewa "wallahi Mama karki yarda, ai ɗa befi ɗa ba haifar shi ki ka yi shima haifar shi akai" cikin baƙin ciki da takaici Mama ta ce "kina gani fa na kira Umar ya je ya rama masa sabi da ba ni na haife shi ba yaƙi ya kama ƙalabusan banza, shima yaron ai ɗan iska ne dama ƴaƴan masu kuɗi haka suke iskanci iri-iri"
Aaminat ta kasa jurewa sai da ta shiga zancen, "Haba Mama shi fa yaron nan anan gurin babu ruwan shi Walid ne da shegiyar tsokana, na san halinsa ba kunya ce da shi ba" "to? lamarin hada zawarawa dama?" Fati ta faɗa tana riƙe baki kafin ta ƙara cewa "ai dole ki ce haka tun da yana ce miki Anti kuna sheƙe ayar ku" dole tasa Aaminat ta fito daga ɗaki tana dafe kirji Umaima ta ce "ko bahaka bane kike ɗafe ƙirji?" wata shewa Fati tayi kafin ta ce "Hee!! ni naga abun mamaki Mama Ranar bikin Bilkisun Umma Sa'a fa Abdulkareem ne yakai ta a Mota"
Mama ta yi salati tana tafa hannu tana cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirajiun Aamina dama haka kike?" Fati tace tafi ma haka ku ne baku sani ba, ai wallahi Allah ne kaɗai ya san abin da su ke aikatawa ita da Abdulkareem ɗinnan" Umma da ke jin maganar su kamar ana zuba mata wuta ajiki bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana cewa "Aaminatu da abinda zaki saka min kenan? kin san dai na baki tarbiya shine za ki dinga biyewa wannan Ɗan iskan Yaron da kowa ya san bai da kyakkyawar Ɗabi'a?, na gaji da baƙin cikin da ake sa ni a gidan nan, wallahi na gaji" jiri ne ya ɗebeta luuu tayi ƙasa cikin hanzari da tashin hankali Aaminat ta sa hannu ta tallafo Umma ta na cewa "Wallahi Tallahi Umma ni ban taɓa aikata komai ba, babu wani abu tsakanina da Abdulkareem, hasalima ni na tsane shi kawai sharri ne aka son yi min" Umaima ta fashe da kuka tana cewa "wallahi baza mu yarda ba in ta mutu ke ki ka kasheta macuciya muguwa, ba wani sharri da akai miki ai kowa ya ganki, indai da ke mutuniyar kirki ce ai ba za ki kashe Aurenki ba" cikin tashin hankali take faɗin haka
Aaminat kuwa ta shiga matsanancin hali, Temakawa Umman ta yi ta shigar da ita Ɗaki ta kwantar da ita saman Gado, cikin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Umma ki yarda da ni, in banda Ƙaddara ba abin da zai rabani da Mijina, ba son raina bane kamar yadda kowa ke faɗa, Umma ni ba zan aikata kuskure ina ji ina gani ba." cike da takaici Umma ta ce "Ba ni da baƙin ciki da damuwa sai naki, tin da ki ka dawo gidan nan ba ni da kwanciyar hankali, komai akaina ya ke ƙarewa, Ko me aka faɗa akanki ba zan ƙi yarda ba, Aaminat abin naki ya yi yawa, ba zan iya jura ba baƙin cikinki zai kashe ni." wani sabon kukan ya ƙara sillewa Aaminat cikin rawar murya ta ce "Wallahi ba sa ƙaunata ne kawai sabi da baƙar Ƙaddarata, ki dena yarda da su abin da suke faɗa ba gaskiya bane." Umma ta ce "Aaminat tashi ki bani guri, ki fita kawai ki barni, ni ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai kin bar gidan nan kin tafi gidan Miji." Aaminat za ta yi magana Umma ta katse ta da cewa "Ba na son jin komai, ki tashi ki bani guri." Aaminat ta tashi jiki a sanyaye, sabuwar Ƙiyayyar Abdulkareem ta na ƙara ɗarsuwa a Zuciyarta, dama tasan sai ya ƙara jawo mata wani bala'in sannan hankalinsa zai kwanta, ɗakinsu ta koma ta tsakure a gefe ta shiga rera baitin kuka.
Abdulkareem
Kowa a Falon hira ya ke cikin nishaɗi amma banda shi, ya yi shiru ya na tunanin Aaminat rabonsa da ganinta tin ranar Bikin Bilkisu hakan ya sa duk ya shiga damuwa, abin da ya fi tashin hankalinsa ma rabuwar da su ka yi baram baram bai san a halin da ya jefata ba.
Abdulmajid ya ƙare masa kallo kafin ya ce "Kai tunanin me ka ke ne?? ba na son ɗorawa kai wahala, kai dai ba ka da wani haufi a rayuwa sai dai in kai ka jawowa kanka abin da zai sa ka tagumi." ya ɗan murmusa cikin son kauda zancen ya ce "Ba abin da ya dame ni, kawai jina nake kamar an yi min dukan tsiya, wai yaushe za mu je Abuja ne??" Abdussalam ya ce "Wallahi Ƙarya yake, ku tuhume shi, na lura kwanakin nan ba iya yau ba ma duk ya bi ya wani firgici, ku ce ya ɗaga rigarsa ku ga yadda ƙashin haƙarƙarinsa su ka fito, duk ya bi ya rarrame amma don kafiya idan ance akwai abin da ya dame shi sai ya ce aa." Ƙasa ya yi da kai don kuwa ba shi da ta cewa Zuciyarsa ta wani mugun karaya, yanzu kuwa ya ce musu Aaminat ya ke so ta dalilinta ya shiga wannan halin, Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru, Abdurrahim ne ya katse masa tunanin da cewa "ka Sunkuyar da kai Hakan na nufin dai da gaske ka tsumbula kanka cikin Aradu." girgiza kai ya yi zai yi magana hawaye suka fara zuba sharrrr, ya yi saurin sunkuyar da kai ya na ƙoƙarin goge su. Abdussamad ya tashi ya dawo kusa da shi ya zauna, cikin lallami ya ce "Abdulkareem, ba ka da wasu tamkar mu Ƴan uwanka, mu ne dolenka, kar ka ɓoye mana abin da ke damunka ka faɗa mana." Ummi da ta ke binsu da ido sai a lokacin ta ce "Gaskiya ne Auta, ka faɗa ko da da temakon da zamu iya yi maka, don nima na lura abin har ya fara yawa musamman a cikin wannan Ƙadamin." Murmushi me tafi da hawaye ya yi kafin ya ce "Ba zan iya cewa ga abin da ya ke damuna ba, don Allah ku zuba min ido kawai Sabi da ba ku da abin da za ku magance min damuwata" kallon kallo su ka yi kafin Abdulmajid ya ce "Abin har ya yi tsauri ne haka?? Auta ko ba a haiyacinka kake ba? ka na tunanin duk cikinmu akwai abin da zai gagara mu yi maka??" Ya rausayar da kai kafin ya ce "Ba za ku taɓa Fahimta ba YaYa, ita fa rayuwa komai matsayinsa daban, wani abin da kuɗi ake sayensa wani kuwa ko da kaine mafi kuɗi a Duniya sai ya gagareka ba za ka iya saya ba, kuma a rayuwa ba za ka ce ko da yaushe sai dai ka yi farin ciki ba, akwai Launi kala-kala a Cikin rayuwa, hakan ya na daga cikin jarrabawar ɗan Adam, duk cikar ka da kaiwarka akwai abin da ka rasa kuma ka ke da burin samunsa, don Allah a rufe wannan maganar." dukkansu sakin bakuna su ka yi su na kallonsa cike da mamaki da kuma nazarin inda kalamansa su ka dosa sai dai sun kasa fahimta me yake nufi, Nana Kadija ta ce "Ya Audu ya na da gaskiya fa, a cikin kalamansa babu na banza, a rufe zancen kawai." goge hawayensa ya yi sannan ya dalla mata harara ya ce "Ban hana ki kirana Audun nan ba??" "To ai naga Sunanka ne" "Ki na buƙatar rasa haƙoranki ko??" ta yi farrr da ido ta ce "Ba zan rasa komai ba ai dai sunanka ne kuma ba zan dena faɗe ba." filo ya ɗauka ya wurga mata ta doka tsalle ta koma kusa da Ummi, ya yi ƙwafa kafin ya miƙe ya ce "Ni waje ma zan fita" Abdussamad ya ce "Sai ka dawo!" tin da ya fita magana sai ɗaiɗai a Falon sakamakon da da suka cika shi da surutu, kowa nazarin kalaman Abdulkareem ya ke har Ita Kanta Ummi, abin da su ke ta tambayar kansu shine menene ya sa shi faɗen hakan?
Tin daga ranar da Fati ta faɗi cewa Abdulkareem ya kai Aaminat gidan biki komai ya ƙara rincaɓe mata, Umma ta ɗauki Fushi da ita Mama kuwa tsakaninta da ita sai dai habaici da nuna ƙyama a cewarsu itama ta iskance, Ba ta da aiki sai na kuka sai kuma aikace aikacen tsakar gida wanda ba mai yi sai ita, Ta na son fita amma ta na tsoron ta yi mugun Katari da Abdul, yau dai ta yanke shawarar fita da tsakar rana don ta san a Lokacin yawanci ba ya zama, Ta yi sallama aƙalla biyar kafin Siyama ta amsa ba tare da ta kalleta ba hankalinta na kan wayar hannunta, Aaminat ta ce "Siyama meke damunki haka ne? sai sallama nake kamar ba ki da kunnuwa" ajiye wayar ta yi ta ja numfashi kafin ta ce "Hmm ba a magana Ƙawata, wai Ina ki ka shiga ne kwana biyu?, wani littafi nake karantawa Abin tausayi wallahi, kin ganni nan yanzu na gama sharar ƙwalla, Anti ba ta nan sai ni kaɗai a gidan kuma ba ni da aiki, ai gaskiya Novel ya na temakawa sosai sabi da ya na ɗebe kewa, dan dai bakya ra'ayinsa ne da kin rage wannan koke-koken naki." Aaminat ta ce "Novel wannan ai sai ke Siyama, amma kuma shi ne har da kuka? me ya yi zafi haka?'' "Hmm! ai dole na yi kuka, kema sai kin koka in ki ka ji abin da ke faruwa." "To wai ya sunan littafin? me ya faru kuma?" Siyama ta ce "Sai kin gyara zamanki in kina so sai in baki labari." Aaminat ta murmusa kafin ta ce "Na daɗe ban yi hira da mutane ba ma bare na yi nishaɗi, kema kin dena shigar min, yanzu dai bani labarin ko zan ji daɗi." Siyama ta gyara zama sannan ta ce "Ke ni wallahi ba na son mugun kallon da Mamanku take min, ga habaice habaicen jaraba, yanzu dai ki saurari labari, Sunan Littafin DOGON YARO Marubuciyar sunanta Ayeesha Abdulkareem INDO CE ."
© INDO CE & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 8
Aaminat ta ce "Ni fa ban tambayeki sunan Maru buciya ba." Siyama ta yi dariya sannan ta ce "Eh na sani, amma ai labarin sai ya fi daɗi, ki na ji, Sunansa Muftahul-jannah ya na da yayye da yawa amma Ba Mamansu ɗaya ba, shi ƙanwarsa ɗaya mace Jannatiee, duk yawan yayyen nasa ba sa ƙaunarshi kamar mujiya haka su ka tsane shi, sai dai Babansa ya na son shi sosai itama Ummanshi haka, kullum ƙiyayyar da suke masa ta na ƙara yawa, gasu da son Zuciya da son abin Duniya, su na mugun jin haushin Babansu ya dinga nunawa Jannah Ƙauna amma ba yadda za su yi sabi da komai na baban nasu Jannah ne akan gaba, a kasuwancinsa ma Jannah ya ɗora duk da shine ƙaramin cikinsu, wai kin san abin Tsoron?" Aaminat ta girgiza kai, Siyama ta ce ''Wai sabi da Jahilai ne da su da iyayensi Mata su ka haɗa kai su ka kashe Mahaifinsu sannan su ka sa aka yiwa Ƙanwarsu Jannatiee fyaɗe, sannan su ka ɗorawa Jannah laifin, yanzun haka a halin da ake ciki kenan, sun jefa shi cikin gararin rayuwa, sun rabashi da Babanshi kuma sun yi masa sharri, sun haɗa masa azabu iri-iri shiyasa na ji kawai na fara kuka, yanzu anje sai Shari'a ake yi, sun ce ba za su yarda ba sai an ƙwatar musu haƙƙinsu a gurin Jannah, ki ji fa wani zalumci? ni cewa ma na yi anya kuwa Ƴaƴansa ne?? Yanzu Jannah ba shi da kowa sai Allah sai Ummanshi, Ƙanwarsa ma ta rasa tunaninta, ban san waye zai cece shi daga wannan Ƙangin Wahalar ba." jikin Aaminat ya yi sanyi, sai da ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Kai!! rayuwar nan fa akwai abin tsoro a cikinta, kasan yau ba ka san gobe ba, yanzu sabi da son Zuciya aka kashe masa Babansa, shi kuma tashi ƙaddarar kenan, ni kuma Allah ya haɗani da Kamal duk ya bi ya tarwatsa min farin cikina." Siyama ta yi dariya kafin ta ce "Allah Sarki Ƙawata, wato har labarin ya tsuma miki Zuciya, gaskiya akwai abubuwa da yawa a cikin Littafin, abin akwai ruɗani, ga ban tausayi, masifu iri-iri ya na ganinta Dogon Yaro, sun sha kai masa hari za su kashe shi Allah ya temake shi ya rayu, ƙila ma sai sun kashe shi ɗin don ko a Kotun nan nasan sai sun Yarda shine ya kashe Mahaifinsa kuma ya yiwa Ƙanwarsa Fyaɗe." Aaminat ta ce "Haba Siyama ta ya za ki ce haka bayan kinsan Allah ya na tare da me gaskiya?, ai tinda ya riƙe gaskiyarsa ba za su yi nasara akansa ba in sha Allahu." Siyama za ta yi magana Amiyo ya yi sallama, amsawa ta yi gami da binsa da ido don jin abin da ya kawo shi. ya ce "Siyama wai Master ya na son yin magana da ke." ido a zare ta ce "Master??? fa ya na nufin Abdulkareem." ya ɗaga gira ɗaya gami da cewa "Yessss!!" da mamaki ta ce "Amiyo zan ci ubanka ni kake ɗagawa gira?, to wai me zai ce min ne? ni fa ban yi masa komai ba bana son salawaitun Bala'i irin na Abdulkareem." Aaminat ta ce "Don Allah Siyama dena ambaton sunansa a gabana, ba na so." Miƙewa Siyama ta yi ta wawushi mayafinta ta yafa ta nufi hanyar fita ta na cewa "Allah i sa ba munafurci ku ka haɗa min ba, bansan hawa ba bansan sauka ba, nasan ba mutunci ne da shi ba." ya na raguɓe a jikin bango a ƙofar gidan ya yi wani sumul kamar ba shi ba. Siyama ta na fara'a ta ce "Guda ba Tsagi ba, Allah i sa lafiya ce ta sa kake nemana." murya a cunkushe ya ce "Ta ɓangarenki lafiya amma a gurina zan iya cewa ba lafiya ba." "To fa me ya faru??" ta faɗa cikin mamaki, "Siyama Aaminat! wallahi na yi mata laifi, tin daga ranar ban ƙara ganinta ba shi yasa duk na firgice wallahi, ta dena fitowa amma nasan idan ki ka ce ta zo gidanku za ta zo hakan zai bani damar ganinta." Siyama ta na shirin jirga masa Ƙarya Amiyo ya tari numfashinta da cewa "Master ai YaYa Aaminat ta na gidan su Siyaman, yanzu na ganta." Siyama ta kifa masa wata shegiyar harara, ya buntsire baki alamar ko a jikinsa. a marairaice Abdulkareem ya ce "Siyama don Allah don Darajar Ma'aikinsa ki yi min Izini in ga Aaminat, wallahi akwai damuwa idan ban ganta ba." ganin ya na neman fashe mata da kuka ya sa ta cewa "A'ahh ni fa ba na ƙi bane, kasan ni Ƙawarta ce ta yarda da ni, ka ga bai dace na yaudareta ba." "Ba za ta ga laifinki ba laifina za ta gani, ni kuma duk na yarda da hakan, idan ba za ta fito ba ki ba ni dama in shiga ciki don Allah." Siyama ta rausayar da kai kana ta ce "Zan jarraba kiranta idan ba ta zo ba sai ka shiga, amma ba da yawuna ba." "Na ji daɗi Siyam's , hankalina duk ya bi ya ɗaga na kasa control na kaina Laifi na yi mata kuma ina son bata haƙuri." Siyama ta juya ba tare da ta ce masa komai ba, a ƙasan Zuciyarta kuwa mamakin ƙarfin halinsa take, ba shakka yanzu ta fahimci mugun son ƙawar tata yake, a gefe guda ta na murna da hakan don kuwa za ta so Ƙawarta ta kauce daga Cikin Uƙubar da take, a gefe guda kuwa tsoro da fargabar rigima take don ta san Abdulkareem bai wuce Shekara ishirin da Ɗaya ba bai zama lallai iyayensa su amince ya yi aure a yanzu ba bare ma ya Auri Bazawara a matsayinsa na ɗan masu kuɗin nan. da wannan tunanin ta shiga cikin gidan ko zama ba ta yi ba ta isar da saƙonsa don tasan ƙarshe ma ko ta zauna sai ta tashi ta koma don Aaminat ba za ta amince ba, wani mugun kallo Aaminat ta watsa mata kafin ta ja tsaki ta ce "Siyama ba na son ki shiga sahun masu son lalata min rayuwa, ni kaina na kasa gane meye Manufar Yaron nan a kaina, ya na yi min wasu irin abubuwa da su ke bala'in rikita tunanina, ina tsoron ya bi Sahun Kamal don ba shakka Abdulkareem ba shi da burin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 16