ce "ya shirye-shirye???" "shiri kuma saikace wasu mata" "Au sannu maza" Yarima ya ce "sai yaushe zaka dawo ne, nifa nagaji da zuwa duba mutan gidanku" "dawowa kuma ai sai abinda Allah yayi idan kana son ganina ka zo inda nake" "kana nufin bazaka halacci wajen ɗaurin Auren ba!??" "eh bazan zoba idan nazo ai nadawo gida kenan kuma nasan Dadda zai halacci wajen" "dan Allah ka daure kazo wallahi bazanji daɗi ba in bakazo ba" "kana ruwa nace fa bazan zoba" Yarima ya rausayar da kai ya ce "wallahi mutan gidanku duk sun rame yaufa kwana uku Dadda baya fita bashi da lafiya" dariya Abdul yayi gami da cewa "zuwana ba zaisa Dad yaji sauƙi ba, dan ba danni ya kwanta rashin lafiya ba" "dan kaine kuwa Dadda babu inda baya neman ka amma ya kasa gano inda kake" Abdul yayi murmushi mai ciwo ya ce "Allah ya bashi lafiya kawai, ni yanzu Allah ya taimakeni na dawo cikin nutsuwa ta, kullum ai'kina karatun Alƙur'ani mai girma" "to Allah ya taya mana" daga haka sukayi sallama,
Abdul ya ajiye wayar yana murmushi yanzu abu ɗaya ne ya rage masa, yaga ƴar uwarsa Kadija,
"Fati wallahi ko banso Auren ki da waccan banzar yazo ɗaya ba" wani banzan murmushi Fati tayi ta kalli ƙawar ta Nafisa ta ce "kinsan kodame kurna tafi magarya ƴaƴa," "kuma kinsan wazata Aura??" Fati ta girgiza kai ta ce "koma waye nasan sai dai ya biyo bayan Ahmad, dan kuwa idan kuɗi ne Ahmad ya tara an tara masa," dariya suka yi gami da tafawa, "inaga ma bazawari ne ko mai mata" "to dama ai bazawara sai bazawari," "hahahaha" Nafisa tayi wata dariya kamar wata mahaukaciya, Fati ce ta tashi gami da cewa "zoki rakani gidan su ruma" "to" tace suka tashi suka nufi hanyar fita,
"Ummi dan Allah ku dauwo mana da ɗan uwanmu yau kusan kwana ashirin da wani abu, ba muga Abdul ba" "kuyi haƙuri muna bamu san inda yake ba gashi yanzu hankalina kullum ƙara tashi yake nayi da nasani, yanzu bansan awana hali ɗana yake ba" Nana Farida ta share ƙwalla gami da cewa "laifinku ne keda Dad baku tsaya kun fahimtar da shiba nasan da kunjashi ajiki kun nuna masa bakuso ta sigar salama da duk haka bata faru ba" Ummi ta muskuta tare da rausaiyar da kai, Nana Hauwa, ta miƙe gami da cewa "Allah sarki rayuwa gashi ai kuna da nasani" Abdurrahim ne ya shigo Falon hakan yasa Hauwa komawa ta zauna" "sannu da hutawa Ummi" ya faɗa yana zama, Ummi ta ce "yawwa" "haryanzu dai babu labarin Abdul nifa nafi tunanin yabar india dan kuwa nayi neman na rasa shi" "shikenan su Dadda sun rabamu da ɗan uwan mu" Farida ta faɗa tana fashewa da kuka, Ummi kuwa ta kasa koda magana, Nana Hauwa ta ce "Allah ya baiyana shi aduk inda yake" suka amsa da "amin"
Kadija zaune take a ɗan matsakaicin ɗakin su na gidan Uncle Rabi'u,
waya ta ɗauka tare da danna kira bugu ɗaya ya ɗauka cikin jin daɗi da farinciki ya ce "Dijan gala yakike" dariya tayi gami da cewa "lafiya ƙalau wallahi" "za kizo ɗin" "eh ya Abdul in sha Allah da yammacin yau zan sauka a Abuja" "Allah ya kawoki lafiya amma idan kikazo kije gidan Anti Maryam zanzo nan ɗin" "kana ganin babu matsala idan Anti Maryam kazo, kuma zata iya faɗawa su Dadda" murmushi yayi kana ya ce "a tasani kuma bazata faɗa ba ɗazu ma naje gidan" "yaushe zaka koma" "Jibi kinsan dan naga ya kike nazo kuma da mun gaisa zan ɗaware" "to sai nazo ɗin yanzu ma na faɗawa Mami nace zani wajen Anti Maryam kuma kwana zanyi nace amma karta faɗawa su Ummi" "Allah ya kawoki lafiya" daga haka sukayi sallama cikin farinciki da annashuwa,
"Abubakari kwandon sikari" Anti Zainab ta faɗa tana dariya "kai Anti dan Allah kidaina tsokana ta," zama ta yi akan ɗayar jujerarda ke kallon sa, ta na dariya ta ce "idan uwa bata tsokani ɗanta ba waye zai tsokane shi" dariya yayi gami da cewa "yaya ta tafi ne" Anti ta ce"A'a" Rahina ce ta shigo falon ta zauna Yarima ya ce "yanzu nake tambaya kin tafi" "A'a yanzu nakira Abban Kausar nace masa sai bayan Biki zamu dawo kuma ya amince" murmusawa yayi kana ya ce "Allah ya kaimu amma kun ɗiba da yawa kobaya ƙasar" "eh bayanan amma zai dawo ɗaurin Aure" murmushi yayi ya ce dakince ya barshi basai ya dawo ba" kallon sa tayi cikin jindaɗin yau gata ga ɗan uwanta suna magana, ta ce "ai dole ma yazo bikin fa ƙanina ake" sukayi dariya kana suka ci gaba da hira jefi-jefi don kuwa ba wani sabawa su ka yi ba"
kiran sallar magrib Kadija ta sauka a tafkeken gidan babban yayansu Abdurrahman kai tsaye ta kutsa kai falo, tare da sallama, da gudu ƙaramar ƴarsu Islam ta taso ta rungume ta tana cewa "Oyoyo-Oyoyo" jin haka yasa Anti Maryam fitowa daga kicin ɗin dake falon, cikin murna da dariyar farinciki ta ce "sannu da zuwa ya hanya" "Alhamdulillah" Kadija ta faɗa tana zama kan ɗaya daka cikin kujerun Falon, waya ta ɗakko ta dannawa Abdul kira, yana ganin kiran ya ɗauka, cikin farinciki ya ce "ina harabar gidan yanzu zan shigo," "ok" maida kallon ta kan Anti Maryam tayi ta ce "ina wuni" dariya Anti Maryam tayi sosai ta ce "saida kika gama wayar" "Au wallahi na sha'afa burina naga ya ɗan uwa yake" sallama yayi yana cewa "yau gani ga tsigai dariya sukayi,
ya kalli Khadija ya ce " Khadi ya hanya" "lafiya lau sai godiyar Allah"
"nayi kewarku wallahi kewarku" kaidai bari harfa rashin lafiya nayi" "Allah kice ruwa ya daki babban zakara" "sosaima dan kuwa naji jiki" dariya suka sa Anti Meri kam sai faman kaiwa da komowa take ta cika gabansu da kayan alatu iri-iri, Abdul ya kurɓi shayi sannan ya kalli Anti ya ce "Anti kushirya fa kunkusa Aurar da Dije" "Ah haba dagaske waye sirikin namu" dariya yayi Kadija ta maka masa harara, ya
ce "ai gaskiya ce tun ina gida nagane kuna soyewa da Omar" "kace sunan sa Omar" "eh mana kuma na bashi" tsaki Kadija taja ta ce "kowa yafaɗa maka ma oh'ho" "nina sani da kaina sau da yawa ina lura da lokacin da kike dawowa daga makaranta" "to kaji daɗi ai ka faɗa" "sosaima gashi har ƙiba nayi" dariya suka sa cike da farinciki,,
har wajen shaɗaya suna aikin abu ɗaya, daga baya kowa ya nufi makwancin sa Abdul ma a gidan ya kwana kasancewar gidan babba ne.
washe gari tunda safe Kadija ta kama hanyarta ta komawa gida, Abdul ma ya shrya yayi wa Anti Maryam sallama, da niya shima gobe zai tafi Qatar,
Yau biki ya rage saura kwana uku ko wane ɓan gare shrye-shiye babu kama hannun yaro
inda Anti wato maman su Siyama da ƴar Autar su Umma suka zage dantse wajen shirya Aaminat,
Mama da ƙawar ta sun zage wajen ganin Bikin Fati yafi na Aaminat (Bazawara) inda suke shige da fice na ara aren bashika dan kuwa kashe kuɗi suke sosai,
Ɓagaren su Anti Rahina ma shiri ake sosai wajen ganin sun tsara biki,
Ya Omar ne zaune a ɗakin Umma ya zabga tagumi hannu bibiyu, sallamar Aaminat yaji hakan yasa ya ɗan saki fuska, ya amsa ƙarasowa tayi kusa dashi ta zauna, cikin nutsuwa da girmamawa ta ce "ya Omar anya kuwa ƙalau kake naga ka zabga tagumi ko bakajin daɗi" murmusawa yayi gami da cewa "karki damu ƙalau nake kawai banason hayaniya ne" "haka ne bakason hayaniya amma naga kamar yau kana cikin damuwa" "eh hakane ina cikin damuwa amma ki bar zancen kawai" "sabida me zakace nabar zancen" rintsa ido yayi kana ya ce "Aaminat banajin daɗin yadda Abba yake yiwa Umma" "nima abin yana damu na wallhi" Ya Omar ya ɗan ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce "karkiso kiji irin cin zarafin da Abba yayi wa Umma yau har zagin ta yayi kuma duk ta sanadin Mama ne" ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka, cikin rawar murya Aaminat ta ce "Allah Sarki, ai Allah yana kallo kuma zai saka mana" ta share hawaye sannan ta cigaba da cewa "ita rayuwa haka take kowa da tasa irin ƙaddarar," "Aaminat ina zamu saka kanmu Mama ta sako mu gaba, yanzu naji tana cewa Abba wai nima bin mata nake, haka kema tayi miki sharri tasa muka tsaneki" cikin kuka Aaminat ta ce "taje dan kanta Allah zai saka mana, kuma in Allah ya yarda kamar yadda tasamu a ƙunci itama saita shiga ƙunci da azaba ta duniya"
Ya Omar ya ce "yanzu haka Abba yace bazai ƙara yi miki kayan ɗaki ba" Aaminat tayi murmushin takaici ta ce "wannan kuma dama bana buƙata suje suriƙe kayansu, ai muma Allah ya azirtamu dan kuwa Umma tana da masu yi mata ko babu komai nasan Baba Usman zaiyi mini" shurune ya ɗan ratsa kowa ya faɗa daniyar tunani, Umma ta shigo ɗakin da sallama, murya a dashe dagaji tasha kuka, Aaminat ce ta amsa, Umma ta zauna kan gadon ta sannan ta kalli su Omar ta ce "kutashi yaya Usman yazo zamu bishi" "zamu bishi kuma??" Omar ya maimaita cikin sigar tambaya Umma ta ɗaga masa kai alamar eh "maiyafaru Umma" Aaminat ta faɗa, Umma tayi gyaran murya ta fara magana da cewa "ƴan uwana sun yanke shawarar baza'ayi taron biki anan ba sabida gudun rigima, kunga dangin Mama zasuzo Bikin Fati kuma sai sun tada fitina, ƙarshe kuma tazo ta ƙare akanmu shiyasa su yaya, suka ce muje gidan yaya Usman ayi taron kuma duk wani abu da ake buƙata ya ɗauke mana ya ce shizaiyi komai shima ai ƴarsa ce"
cikin farinciki da jindaɗi Omar ya ce Alhamdulillah wallahi naji daɗi Allah ya saka masu da akairi Aaminat kuwa taji daɗin hakan amma bata nunaba saima sunkuyar da kai datayi
Indo &&&& Salma
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 26
Umma ta murmusa ta ce "Aaminat ko kinfiso ayi Bikin anan" "Aa Umma canɗin sai yafi kwanciyar hankali" Umma ta tashi tana cewa "Aamiant kije ki kira Siyama da ita zamu tafi" "to" tace Umma ta fita, Aaminat ma tashi tayi ta zira hijabi ta nufi waje,
Basu ɓata lokaci ba suka kwashi duk wani abunda zasuyi amfani da shi suka kama hanyar Gidan Baba Usman.
ɗaurin aure saura kwana ɗaya kenan
kowawane ɓangare ya kacame, sai ai'kace-ai'kace ake ko wane gida ya cika da dangi ko ta ina gidan su Yarima ma yayi taff da mutane sai hada hada ake,
haka gidan Baba Usman ma dangi sun taru ba ƙarya manya da yara kowa ya nata shagalinda.
Gidan su Fati ma biki yayi biki, inda su Fati suke ta
sherye-shiryen fita Dinner
Nafisa ƙawar Fati ce ta shigo ɗakin su Fati ko sallama babu sai uwar shewa da ta saki, tana cewa "Amarsu ta ango yau saura kwana ɗaya mu kaiki" Fati ta tashi tsaye gami da cewa "dama ke nake jira kizo ki tayani zaɓar kaya dan wallhi so nake nayi shiga ta kece raini" "haba ai karki ɗaga hankalinki zaki fita da fitarki dan akwai ban-banci tsakanin Bazawara da Budurwa" Walid dake zaune aɗakin ya dubi Fati ya ce "wai Fati maiyasa ba ki da tunani ne,??? ita Aaminat ba sa'ar gasarki bace don kuwa zaran bakalar yadin bane" "dakata munafiki ina ruwanka damu ko kafiso mu zauna muna gani Bikin Bazawara yafi nawa??, to wallahi karka sake wannan tunanin nafi ƙarfin Aaminat ko ta ina" tashi yayi ya ficewarsa, ya barsu suna zage-zage da masifa.
Ammi ce zaune a kan kujera a Falon ta tana latsa waya, Anti Zainab ta shigo da sallama, Ammi ta amsa tare da cewa "Anti ina Yarima ya shige ne tin ɗazu nake neman sa" "kinsan sa baya son hayaniya kuma gidan namu ya fara cika" "to banda abinsa ai shiya tara taron" Anti Zainab ta zauna kusa da Ammi tana cewa "washh wallahi na gaji" "sannu ai da gajiya" Kausar ce ta shigo da sallama, Anti ta amsa gami da cewa "daga ina haka naganki da kaya niƙi-niƙi???" "daga wajen mai ɗinki nake " "kije ki watsa ruwa kizo kici Abinci" "to Anti" Ammi ta miƙe gami da cewa "bari naje madafa naga ya aikin yake tafiya" "to nima yanzu zanzo" Anti ta faɗa tana kashingiɗa,
"Aaminat tana kwance a ɗakin su Iman tana kuka taji wayarta tana ruri, banza tayiwa wayar ta cigaba da kukanta, saida kiran ya katse wani ya shigo sannan ta ɗauki wayar batare da ta duba maikiran ba, karawa tayi akunne, batare da tayi magana ba, "Salamu'alaiki" murya a daƙile ta ce "Amin wa alaikassalam" murmusawa yayi, gami da cewa "Aaminat kin shirya ne" "A'a" "saboda me baki shirya ba shida tayi fa" "nifa nace maka babu inda zanje" "Aaminat kiyi haƙuri dan Allah kije in bakije ba bansan yadda zancewa dangi na ba kuma nace musu zaki je" ɗan ƙaramin tsaki tayi, "Aminat dan Allah ki tausaya min kije," "nifa bazani ba ai ba wannan ne Aure na nafar koba kaga ai ba saina wani je ba" wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauke tare da rintse ido, sun ɗauki minti yakai biyu babu wanda yayi magana, Yarima ne yayi ta maza yace "shikenan tunda bazaki ba saiki zauna, kiyi abinda kika ga dama tinda ba a'isa dake ba," yana gama faɗin haka ya kashe kiran rai aɓace, dan kuwa Aminat ta fara ɓata mai rai, kusan kwana biyar yana fama da ita amma taƙi yarda,
Aminat kuwa kuka ta ƙara fashewa dashi, dai-dai lokacin Siyama Umaima Iman suka kutso kai ɗakin, turusss sukayi ganin Aaminat ta zage tana ɓarzar kuka, da sauri sukayi kanta suna cewa "maiyafaru??" banza tayi dasu, Umaima ta ce "ya Aminat baki da lafiya ne ko wani abu akayi miki??" cikin kuka tace "babu komai" "to maiya faru kike kuka??" share hawaye tayi tare da cewa "Yarima ne wai sainnaje gurin Dinner kuma ni banason zuwa" sheƙewa sukayi da dariya ta saki baki tana kallon su, Simaya ta ce "amma kin bani dariya, akan haka kika zauna kina ta kuka sai kace wadda akace za'a kashe" Aaminat ta shiga goge hawayen gami da cewa "kukan ma baza'a bar mutum yayi mai daɗi ba, sai an takura masa" "iyeeee kukan ma hada mai daɗi ko???" tsaki tayi taja ƙaton bargo ta rufa, wayar ta ce ta fara kuwwa ya duba mai kiran da mamakin ta sai taga wata number ba irin ta ƙasar nan ba, saida ta kusa yankewa sannan ta ɗauka, tare da sallama, amsawa yayi, cikin nutsuwa ya ce "maiyasa bazakije wajen shagalin bkinki ba" wani dummmm taji zuciyar ta tayi, adiririce ta ce "A...a...a....Abdul kaine" "nine Yaya dan Allah kiyi mana alfarma kije dan Allah" tana dariya dariya kuka kuka ta ce "to zani amma bazan daɗe ba, Abdul ka dawo don Allah" "to kitashi kishirya kuma dan Allah ki daina wahalarmin Aminina bana jin daɗin hakan, idan lokacin dawowata ya yi zan dawo" wasu sabbin hawaye ne suka fara sabuwar zarya akan tausasan kumatunta, ta ce "to zan daina" "to Allah ya sanya alkairi ya kauda fitina amma kin ɓatawa Abubakar rai kikira sa ki bashi haƙuri" "to" ta ce daga haka sukayi sallama,
Umaima ta kalli Aaminat ta ce "gaskiya ki rage abinda kikewa yaya Abubakar gobe iyanzu fa kina gidan sa," "nima dai haka nagani haka kawai saita dinga tsangwamar bawan Allah" Aaminat kuwa banda cokalo baki babu abinda take, Ameeera ce ta shigo tana cewa "ga mai kwalliyar nan ta ƙaraso", "to ki ƙaraso da ita nan ɗaki" Iman ta faɗa Siyama ta kalli Aaminat, cikin sanyin murya ta ce "kije kiyi wanka lokaci yana ja", tashi Aaminat tayi ta shiga wanka,
bata jima ba ta fito daga wankan, zama tayi akan ƴar ƙaramar kujera, ta fara shafa mayuka masu ƙamshi da tsada, tin kafin ayi mata kwalliyar ta ɗau harama don kuwa ta sha gyara, fatarta ta yi suɓula sai ƙyalli da walƙiya take ta yi wani ɓulɓul, tana gamawa "Umaima ta kalli mai kwalliyar ta ce kije ki fara yimata", Aaminat ta ce "nifa ba saianyi mini Make-up ba" "ai kuwa dolenki ayi tunjiya kike faman wahalar da mutane dan iskanci, komai akace saiki ce ke bazakiyi ba to dole sai anyi kwalliyar nan" "yauwa maman Humaira tin ɗazu take ta butsewa taƙi yarda" wadda aka kira da maman Humaira ta ƙara ɗaure fuska babu alamun wasa, ta ce "maza ki farayi mata,"... ta makawa Aaminat harara ta ce "idan kika kuskura nadawo na tarar, baki zauna anyi miki ba sainayi rugu-rugu dake ja'ira" tana gama faɗin haka ta juya ta ficewar ta,
dan dole aka fara yiwa Aaminat Make-up anayi tana butsarewa, ko ta cokalo baki gaba tana mita,,
Fati ta shirya cikin tsadadden Leshi marun doguwar riga gown sai walwali take tayi kyau sosai san kowa ƙin wanda ya rasa, cikin yauƙi da yanga da jinkanta, take takawa har suka isa kofar gida inda aka aje motar ango da abokansa, kofar maya aka buɗe mata ta shiga, Direban ya fara jan motar a hankali suka ɗauki hanya,
cikin ɗan lokaci aka gama Make-up ɗin Aaminat wata riga Umaima ta miƙo mata, ta ce "kiyi kisa" batare da tace komai ba ta karɓi rigar ta fara sawa, Dogowar riga ce Baƙa da yarfin golden, mai irin buguzum ɗin nan irin ta indiawa, tayi mata mugun kyau tamkar wata sarauniyar kyawa-wa, takalmi golden tasa da wata ƴar ƙaramar jaka mai ƙyalli da sheƙi, wani ɗan ƙaramin mayafi, Siyama ta miƙo mata, ta karɓa ta yana a saman kanta, Iman da Umaima suka ɗauki wasu tsadaddun turaruka masu mugun ƙarfi da ƙamshi suka fara fesa mata kamar bazasu daina ba, Siyama ce ta kama hannunta cikin sanyi ta ce "muje ko" tirjewa tayi taƙi ta fiya, Siyama ta saita dai-dai kunnan ta ta ce "Aaminat kiyi haƙuri ki bamu haɗin kai dan Allah, karkiyi gardama," wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,, sannan ta fara ɗaga ƙafar ta cikin nutsuwa, ahankali take takawa, kamar mai tsoron takawa, a haka suka isa babban ɗakin da Umma take ita da ƴan uwan ta da sauran mutane, suna shiga ɗakin ya kaure da buɗa, ahankali ta ƙarasa inda Umma take, kai ta kifa akan cinyar Umma, Umma ta shafa bayanta ta ce "Aaminat Allah yayi miki albarka ta shi kuje" ƙin tashi tayi saida Umaima ta kama hannun ta ya ɗagata, bayan anyi kamu, suka nufi ƙofar fita,
Aharabar gidan suka tsaya, inda wata jibgegeyar mota mai tadar gaske take Baƙa ce motar daganin motar kasan ba ta ƙanana mutane bace, wani kyak-kyawan saurayi ne ya buɗe ƙofar baya, kasan cewar duhu ya farayi hakan yasa bata lura da mutu ko babu ba ta shiga motar cikin nutsuwa, ahankali ta rufe murfin ƙofar, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Direba, su Siyama ma tasu motar suka shiga,, cikin nutsuwa Direban ya fara jan motar suka fita daga get ɗin gidan, saida suka hau titi, sannan Aaminat taji motsin mutum akusa da ita, matsawa tayi, gefe, wani ni'imtaccen murmushi ya saki, tare da lumshe ido, waya ya ɗauko ya kunna fitilar wayar, ya haska Aaminat yana wani tattausan murmushi, cikin nutsuwa ya kai hannun sa ya yaye gelen da ta rufe fuskarta, hawaye ne shaɓe-shaɓe kwance afuskarta, cikin tattausar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "sorry ki daina kuka, banason ganin zubar hawayen ki," wani numfashi taje ta sauke tare da, sauke nannauyar ajiyar zuciya, wani maraitaccen murmushi ya sakar mata, sannan ya miƙo mata tissue, ya ce kishare hawayan ki bana son ganin ki kina kuka dan Allah ki daina karki sa kanki ciwon kai,..." ya numfasa kafin ya ce "Aaminat dan Allah ki karɓa ki shara hawayan ki, kidaina kuka karki ɓata kwalliyarki," ƙin kaɓa tayi saima wasu hawayen da suke ƙara shararowa, cikin nutsuwa, Yarima ya fara share mata hawayen yana hura mata iska da bakin sa, hakan yasa ta fara jera ajiyar zuciya akai-akai, gyaran muryar da Sabir yayi ce ta dawo da Yarima cikin hayyacin sa,, Sabir ya kwashe da dariya gami da cewa "ya Abubakar dama ka iya soyyaya haka,???" tsaki Yarima yayi ya ce "kai ina wasa da kai???" "A'a wallahi salon nakane yake matsa ni" "kai Sabir ka fiya sa ido, dama hankalin ka yana kanmu ka saki tuƙin ko??" ƴar dariya yayi ya ce "ai dama shiyasa nace ni zan jaku" "ai kuwa idan na ƙarajin tarinka saina..." muryar Aaminat ce ta katse masa magana, jin tana cewa "kun isheni da surutu" murmusawa yayi ya ce "ranki ya daɗe tuba muke, mun daina" shiru tayi batace komai ba hakan yasa suma sukaja nasu bakunan suka tsuke,
Ɓan garen su Fati kuwa suna isa aka fara cashewa ana rawa kamar ba gobe,
cikin mintina ƙalilan suka ƙarasa ƙaton hall ɗin parking sukayi, a tafkeken filin wajen, Siyama da Ameera ne suka ƙaraso wajen tare da sauran ƴan matan, gaba ɗayansu sunyi ankon material pink ɗinkin dogayen riguna fitet, sunyi bala'in haɗuwa maza kuma su Bilal da sauran ƙannan ta na layinsu irin su cokaki Jabir Walid Salim Ahmad Amiyo da dai sauran sunyi ankon yadi mai tsada Bulu Black suma fa sun haɗu huluna ma iriɗaya ɗinki iri ɗaya, Sabir ne ya fito ya zagayo ya buɗe murfin motar, tuni masu photo sun zagaye wajen, sai ɗauka suke, a hankali da nutsuwa ta zuro ƙafa ɗaya waje, saida ta ɗan kwashi sakanni kafin ta zuro ɗaya ƙafar sannan ta miƙe, Yarima ma fitowa yayi yana wani ƙasaitaccen taku, ƴan matanne suka shiga gaba, mazan kuma suka tsaya abaya, Yarima da Aaminat kuma a tsakiya, ahankali suka fara tafiya, kamar basa son taka ƙasa, daga ita har Yariman wani jinkai da izza ne ya ziyarci zukatan su hakan yasa suke taku ɗaya bayan ɗaya, suna ƙarasa tafkekiyar ƙofar ɗakin taron suka ƙara sauyw taku, wani ƙasaitaccen taku suke da izza zarra mulki, MC kuwa dan da nan ya saki waƙar shigowa da Amarya da Ango, a tare suke jefa ƙafarsu in suka ajen ta hagu sai sun ɗaki sakan uku kafin su ƙara jefa ɗayar, danda nan kallo ya koma sama inda kowa na wajen yake kallon su, guri ya ƙara kacamewa kowa yana farinciki, tabbasss biki yayi biki biki ya tsaru waje yayi waje kai dagani kasan akwai banbanci tsakanin Fati da Aaminat iya wajen zaman su Aminat ma aljannar duniya ne wasu mugaye kujeru ne na gani na faɗe nasa maƙiya jin haushi, ahankali suka ƙarasa wajen zaman Amarya da Ango, kamar yarda su Umaima suka tsara yadda Amarya zata zauna, haka suka zagaye wajen tamkar Sarki zai zau na, mazan suka baza malin malin ɗin su ta yadda babu wanda zaiga zaman Amaryar da Angon ta, zama sukayi sannan su kuma ƴan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 16