Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nana Kadija fa ta girma, Sakuwarka ce fa, ka dena Dukanta don Allah musamman dai a waje gwara ma a cikin gida ya fi rufin asiri, ba ka san ma idan mace ta girma dena dukanta ake ba?" "Wannan ƴar Ummi tinda ba ta yi hankali ba ai kuwa ba ta girmi duka ba." ya faɗa gami da yin gaba ya basu guri don ya gaji da jin gunjin kukan nata. Ummi ta ce "Allah i shiryeka to" Nana Kadija ta ce "Wallahi Ummi bakwa son yi masa faɗa ne shi yasa duk ya bi ya addabi kowa." Murmusawa Ummi ta yi kafin ta ce... © INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 5 "Ba ya aikata abu mara kyau, shi yasa za ki ga kamar ba a son yi masa faɗan ne, ba za ki gane hakan ba sai kin sawa kanki nutsuwa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a kowane ɓangare ba wani sauyi. Aaminat Kullum jiya i yau ne ba ta da lokacin farin ciki, ko da ba ayi mata komai ba idan ta yi tunanin rayuwarta ita kaɗai sai ta kama kuka. Yau su na zaune su na hira Abdulkareem ya ke cewa, "Wai Kwanan nan naga Walid ba ya yi min magana, ko wasa ake yi da shi idan na shigo sai ya fita, me yasa haka???" Kowa ya ja bakinsa ya yi har sai da Abdulkareem ya ƙara maimaita tambayarsa sannan Amiyo ya ce "Ni fa ba zan ɓoye maka ba wallahi, munafukan ba sa son gaya maka gaskiya shi ya sa ka ji sun yi shiru." Abdulkareem ya ce "Yauwa Mutumina zo ka zauna kusa da ni." Amiyo ya furmutsa tsakiya ya zauna sannan ya ci gaba da cewa "In gaya maka, ba ramar nan ka zane ƙanwarka ba? to ai shine ya ke jin haushinka wai shi sonta yake". Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ita Ƙanwar tawa ya ke so??" Amiyo ya ce "Ƙwarai da gaske, kar ka ƙara kar ka raga hakan ne ya sa ya ke ta jin haushinka." Abdulkareem ya ce "Lallai ma yaron nan, bar ni da shi zan ji da lamarinsa." Muktar ya ce "Kai kuma da tsinin bakinka ya gaya muku sirri amma ka zo ka kwashe ka faɗa." "To zaman munafurci da cin Amana kake so ayi da ni? aa ba zan iya ba" Abdulkareem ya ce "Kar ka damu Amiyo gwara da ka faɗa min ai, wai ni kam Ya akai naga Chokali yau ba iyayin nan? "Cokali Cokali!" wai lafiya ka zabga ta gumi?" Bilal ya tambaye shi, kallon shi kawai ya yi ya ƙara maida kai ƙasa, Amiyo ne ya ɗanyi ƙasa da kai yace "Babarsu ce ba ta da lafiya" da sauri Abdulkareem ya dafa Abokin na shi cike da damuwa ya ce "Haba Haisam mene amfanin zaman mu waje ɗaya in har ba za mu magance matsalarmu ba? kamata yayi ka sanar min tun wuri mu kaita asibiti" tashi yayi ya run gume Abdul yana kuka "nagode Allah ya ƙara arziƙi " Abdulkareem ya murmusa "karka ƙara yi min godiya, babu godiya tsakaninmu maza kaje ka ce su shirya za mu tafi Asubiti" da ' to" ya amsa sannan ya nufi gidan nasu, ɗaki ya shiga ya tarar da Sumayya ƙanwarsa se faman kuka take tana shafa mata ruwa cikin rawar murya ya ce "ki kintsa Inna za a kaita asibiti" to tace tana tashi. tuni Abdulkareem ya fito da mota yana jiran fitowarsu Sumayya ce ta rungumo ta suka fito murfin motar ya buɗe suka shiga da Inna, Haisam ya shiga gaba shima ya shiga ya tada motar ya fara tafiya cikin nutsuwa duk da sauri yake amma hakan be hana shi bin hanya a hankali ba se faman jerawa Inna sannu ya ke har suka isa A.I HOSPITAL Asibitin Daddansa duk da babu wanda ya sani cikin Abokan na shi. danda nan aka bawa Inna gado likitoci guda uku ke kanta suna ƙoƙarin ceto ranta. "Ummi ki ƙara kiran shi na kira ba a ɗauka inaga baya kusa ne" Nana Kadija ta faɗa cike da damuwa, wayar ta ta ɗauka kai tsaye ta danna wa shalelenta kira dede lokacin Abdul ya buɗe ƙofar motar ze ɗauki waya ganin sunan Ummi ya baiya na akan fukar wayar yasa yayi saurin ɗauka ya kara a kunne, Muryar Ummi ce ta daki dodan kannan shi tana cewa "ɗana kana ina? ina ka shiga?" "Ummi ina Asibiti Maman Cokali ce bata da lafiya" "ayya Allah ya bata lafiya waye kuma Cokali?" "Haisam Aboki na Ummi" "to jikin da sauƙi ko?" "eh Ummi mun ma kusa tahowa in sha Allah" "to Allah ya ƙara lafiya se kun dawo kakula ka ji?" "to Ummi. daga haka su ka yi sallama ya koma ciki Cike da fustara da rashin kunya Fati ta ke cewa "wallahi sekin biya ni kuɗina wa yace ki ɗaukar mini?" Aaminat ta ce "dan Allah kiyi haƙiuri ranta nayi in na samu zan baki" "taɓ baki isa ba yanzu zaki biya ni kuɗina ko mu daku" jin Fati ta kira dakuwa yasa Aaminat zaro ido ta sani zata aikata, Umaima ce ta shigo dakin tana cewa "ke ƙaramar Bazawara zaki biya ko se mun fara salawaitun bala'i ne" "kuyi haƙuri zan baku in anjima" "wallahi yanzu zaki bani kuɗina ko na faɗawa Abba kin satar min kuɗi" "Haba Fati kin sani bana sata kar kiyi min ƙazafi zan biyaki kuɗinki, yanzu ba ni da su ne in da akwai ai da ban kai ga ɗaukar nakin ba" "to biyani" rausayar da kai tayi tana tunanin inda zata samu kuɗi ta biya Fati tunawa tayi da Siyama ta yi saurin miƙewa ta na faɗin Alhamdulillah. Fati ce ta cakumi wuyan Aaminat ta na cewa "ina za ki je baki biya ni b? wallahi babu inda zakije se kin biya ni!!" ta ƙarasa maganar cike da bala'i. cikin muryar kuka tace "zanje gidan su Siyama na aro na biya ki" "koma ina ne muje tare" kibari na kawo miki karki bini dan Allah" murgu ɗa baki tayi tace "maza ina jira ki da wo" Umaima tace "kuɗi ne de se kin biya shi ehhe" Aaminat ta ce "To sakar min wuya sai in tafi." "Abin ya ci tira ma bayan takura har da sata Alawadai da wannan zawarci, azo a damu iyaye a damu ƙanne yanzu ma an fara sata, Ba dan Allah ya tona miki asiri ba da tuni shi kenan kin sha ni na warke" Fati ce ta ke zazzaga masifa hannunta riƙe da ƙugunta har wani ɗan girgiza take yi, Aaminat ta share hawaye kafin ta ce "Kar ki fitar da ran kema Allah zai jarrabeki Fati, nima ban taɓa tunanin hakan ba gashi ta faru da ni." "Allah i kyauta ya kare hawala, ai wallahi ni nafi ƙarfin zawarci na riga na bashi baya, ke dai da baki da daraja ke Allah ya ɗorawa amma ni wallahi ko tawo mu gama ba zan taɓa yi da shi ba, ya ƙare dai akanki. Umaima ta ce "Ato wallahi fa" Aaminat ba ta ƙara ce musu komai ba ta fita domin samo rancen ta biyata ta huta. Fati da Umaima kuwa zancenta su ka dasa Umaima ta ke cewa "Ni fa wallahi har ba na so ma ta ƙara yin Aure yanzu kinsan sabi da me?" Fati ta ce "Sai kin faɗa, ni dai na fi so naga ta kauce ta bamu guri don wallahi wannan kashe mana kasuwa za ta yi, ba dan ita ba ma ai da yanzu batun Aurenmu ake yi, amma komai sai dai ace Aurenta ita kuma na lura Tafi son me Ido a tsakiyarka (Duniya)" Umaima ta ce "Ke baki kwashe ba dalla, ni aikin da take yi mana ne ya sa ba na son Auren nata, kinga ba ruwanmu da wanke-wanken safe ba na Yamma, girki ma ba kullum ba, share-share kullum sai dai ta yi mu ɓata, shi yasa fa ba na son ta tafi." Fati ta yi dariya gami da ɗakawa Umaima duka a cinya ta ce "Shegiya ke kin gano laƙabin ashe, wallahi fa haka ne, nima sai yanzu na gane amma fa kamata ya yi mu muna da samarinmu Aurenmu za mu yi ita kuma ta na yi mana aiki, kin ga sai ta ƙare a Aikin wanke-wanke, kinga wannan Bikin da za ayi na Ƴar Umma Sa'a? wallahi dagewa Za mu yi mu samo Samari masu aji da kuɗi a Wajen Dinner nan kin ga ai mijin Umma Sa'a ya na da Ƴan Kuɗaɗensa, nasan shima wanda Bilkin za ta Aura hakane, to a ciki za mu ƙure wanka mu zaɓi santalele mu yi wuf da shi" Su ka yi shewa su ka tafa kafin Umaimai ta ce "Wallahi kanki ya na kawo wuta My Sister, ayyiriri!!! ai sai dai ki ji ana mana buɗa, ni kuwa za ta iya zuwa bikin nan ma?" "Sabi da me ki ka ce haka?" "To ai naga ba ta ƙaunar shiga jama'a itama kanta kunyar kanta take. Fati ta ce ''Ba lallai ta je ba kuwa, musamman Dinner ɗinnan, yo mutum ne kamar mujiya ba farin jini." Umaima ta ce "Allah i sittira to" Shigowarta ce ta katse musu hirar, ta miƙawa Fati kuɗin gami da cewa "Ga shi nan ai ba a rasa masu tausayi, tin da ku ƴan uwana ba ku tausaya min ba na samu me tausayina." Fati ta yi mata kallon tara saura kwata ta ɗiba ta watsar ba tare da tace uffan ba, Umaima ta ce "An dai ji, tinda kin biya kin huta da kin yo aman su a gurin nan" cike da takaici ta ce "Umaima uwa ɗaya uba ɗaya mu ke ni dake amma kin ɗauki Tsana kin ɗora min sabi da jarrabawa ta same ni, wai ba ku san ƙaddara ba?" Umaima ta buntsira baki gaba ta murguɗe ɗankwalinta ta ce "Ai ba wani ne ya ce ki kaso Auren ki zo ki dame mu ba." "Wallahi da kunsan waye Kamal da ba za ku dinga cewa na kashe Aurena ba" ta yi maganar ta na sharar ƙwallah, cike da rainin hankali Fati ta ce "Allah sarki!" shiru ta yi musu su ka ci gaba da ƴan maganganunsu. Yau ta kama ranar Wunin Bikin Bilkin Umma Sa'a, sai yamma liƙis ta shirya kowa ya tafi ya barta don babu ma wanda ya ce ta shirya kawai dai ta yi ra'ayin zuwan ne duk da ba a gaiyaceta ba. Riga da Sket na Atamfa ta saka sun kama jikinta sosai, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya ta yafa mayafinta akan kafaɗarta, kamar ko da yaushe iya Kwalli ta saka sannan ta zura Plat Shoe ɗinta, kayan duk sun takure ta kamar ta cire har ta koma za ta canja wata Zuciyar ta ce kibar kayanki, ta ɗauki mukullin gidan ta rufe sannan ta fito. a hankali ta ke tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, tunanin Kamal take yi, ko shakka babu ya taka rawar gani wajen tarwatsa mata farin cikinta, indai ana samun maza irinsu to fa kowace mace ma za ta iya fuskantar rayuwa ta garari kamar yadda itama ta fuskanta. firgita ta yi sabi da jin muryar Abdulkareen a dodon kunnenta "Haba YaYa Aaminat don Girman Allah ki koma ki canja kayan nan, wallahi sun yi miki ƙanƙanta kamata ya yi ki dena saka su ma. Bakinta har rawa ya ke wajen cewa "Bab.. ba.. bazan canja ba, ina ruwanka da ni?" ya ɗan yi dariya kafin ya ce "Ba ruwana da ke kawai karambani ne, ina za ki je ma??" Ta ɗan murguɗe baki ta ce "Bikin Ƴar Ƙanwar Abbanmu ake yi" Idanu ya zuba mata ya na binta da wani sihirtaccen kallo, sai murmushi ya ke wanda bai ma san ya na yinsa ba "Kin iya murguɗa baki YaYa Aaminat" tsaki ta yi gami da ci gaba da tafiya ta na tuhumar kanta ma dalilin da ya sa ta tsaya saurarensa. cikin sauri ya tare hanyar ta fuska a haɗe ba alamun wasa ya ce "Aaminat bar ɗaukar zancena a wasa fa, idan ƙanwata ce ke ba zan bari ki fita da kayan nan ba bare ke YaYata, don Allah ki koma ki canja sai ki tafi." "Ba fa zan canja ba" "Ni kuma indai ba za ki canja ba nima ba zan barki ki wuce ba wallahi sai dai ki fasa zuwa bikin, kin ji har na rantse" "Wai ina kake so in sa kaina Abdo..." ɗaga mata hannu ya yi cike da manyance ya ce "Na gama magana Aaminat, ki yi haƙuri ki dinga sitirta min kanki." ya na rufe baki ta ɗauki hanyar komawa gidan zaizaizai ta na tafiya ta na haɗa hanya bakinta ɗauke da Addu'a a cewarta neman tsari take da sharrin Abdulkareem, duk ilahirin jikinta ya ɗauki tsuma, ai kuwa indai gaskiya ne abin da Zuciyarta ta ke gaya mata akansa ai kuwa Kamal ya sa ta tafka babbar asara a rayuwa, ya yi mata tozarcin da ba lallai a samu tozartacciyar mace irinta ba.... ©️ INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 6 Bismillahirrahmanirrahim Sabi da takaici sai ta ji kamar kar ta je Bikin ma, Doguwar riga Abaya ta ɗakko ta ƙare mata kallo aranta ta ce Wannan dai duk jarabarsa ai ba za ta kama jikina ba, Sakawa ta yi sannan ta Ɗakko Hijab ta saka a cewarta ta ma fasa saka mayafin, ta ƙara fesa turare sannan ta fito cikin sanyi jikinta duk ya mutu, ta cikin mirror ya hangota, ganin yadda ta zuba Hijab ya sa shi sakin murmushi, kwata kwata ba ta lura shine a Motar ba sai da ta zo wuce ya yi Hon da ƙarfi, ta maruƙar razana da artawa za ta yi da gudu sai ta cije, ya fito ya na dariyar shakiyanci, har ya je ya yi shirinsa cikin Ƙananun Kaya Baƙin Wando da Farar riga me ɗan ƙaramin hannu, "YaYa Aaminat zan je gidan mai shiga in rage miki hanya" ya yi maganar ya na murmushi gami da kasheta da fararen idanunsa, cikin sauri ta girgiza kai ta ce "Ba zan shiga ba" Takawa ya yi cikin nutsuwa ya matsa kusa da ita idan ya matso sai ta matsa har sai da su ka kai bango sannan ta tsaya ta zuba masa ido don ganin ƙarshen tsagerancin nasa, asalin ƙwayar idanunta ya ke kalla wanda yake iya karantar abubuwa da dama daga cikinsu, cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Allah Aaminat idan ki na yawan yi min gardama zan nuna miki bambancin Wa da Ƙanwarsa, ki shiga ko na sa ki da kaina, ki ka tsaya kina kallona." cike da takaici ta ce "Wai kai ko kunyar faɗen sunana kai tsaye ba ka ji? aƙalla fa na yi ƙani na biyar ko shida da kai, amma don rashin kunya kake min abu kamar wani Babana don wannan isar taka ta fi ƙarfin YaYa, ba fa zan shiga Motar nan ba sai dai ka yi duk abin da za ka yi, akan na bi ka gwara na fasa zuwa, ba za ka jaza min bala'i ba yanzu ace kuma bin maza na koma yi" Ido rufe take maganar cike da son nuna iyakar gaskiyarta, shi kuwa ya yi shiru ya zuba mata ido ya na wani Sassanyan murmushi, sai da ta gama surutun ta ƙara kallonsa ta ga ko gezau bai yi ba, ta ƙara jan dogon tsaki ta ratsa ta kusa da shi za ta wuce ya yi saurin riƙo hannunta gami da cewa "Ohh Aaminaathhh!!" yadda ya kira sunanta ya mugun taɓa Zuciyarta ta tsaya cakk gami da rintse idanunta ta cije gefen leɓenta, zagayowa ya yi gabanta ya na ƴar dariya ya ce "Me yasa ki ke son ɓata min lokaci har ma da ke kanki, Aaminat tin da ki ka fito sai kin je kuma ni zan kai ki" shiru ya ɗan yi kafin ya saki wani malalacin murmushi ya ce "Komai naki har Zuciyata! kina bala'in girgizani a duk motsinki Aaminathh!!" "Kai Master hannun YaYa Aaminat ɗin ne a cikin hannunka???" Bilal ya jefo masa tambaya cike da mamaki, cikin sauri ta fizge hannunta cike fa baƙin ciki da takaici, ji take inama za ta iya ta kikkifa masa mari ko zai gane ba sa'arsa bace, shi kuwa da ta fizge hannunta sai ya saki murmushi ya shafi sumar kansa sannan ya ce "Bilal wai unguwa zan je shine ba zan rage mata hanya ba." Bilal ya ce "Yaya Aaminat ki yi haƙuri ki shiga mana, kin san shi kin san gidansu ai ba zai sayar da ke ba, ni bari inzo in raka ku ma." tsaki ta ja kafin ta shiga gidan baya don ta lura sabi da naci za su iya cinyeta, Abdulkareem ya dafa kafaɗar Bilal cikin muryar raɗa ya ce "Ba za ka je ba munafuki" Bilal ya yi dariya ya ce "Na ji , wallahi sai in ce kar ta bi ka ma" talle masa ƙeya Abdul ya yi ya na dariya sannan ya shige gidan direba ya fige motar. Tasan dama ba gidan man zai je ba don haka ko da ta ga ya ƙi tsayawa ba ta ce masa komai ba, shi kuwa ya na tafiya ya na waiwayenta daga baya ma sai ya saita Mirrorn cikin motar zuwa kanta. "Wace unguwa za ki je??" "Ba na so fa ka kaini inda dangina za su ganni tare da kai su dinga zagina, gwara ka ajiye ni in tafi a Napep" "Tin ina ɗan shekara goma sha biyar na iya Driving kawai ba a bani mota ne, sannan a gidanmu akwai motoci sai wadda naso nake hawa, kuma duk bayan wannan sai na barki ki tafi a Napep bayan gani ba aikin da nake yi? kema kinsan ai a tsarina babu haka, kawai neman ɓata bakinki ki ke yi, tin da nace zan yi kinsan sai na yi." Dogon tsaki ta rafka gami da zuba tagumi ta ɓoye fuskarta a cikin hijab, ya yi murmushi kafin ya ce "Ya Aaminat! Wallahi in kina murmushi har kusan suma nake yi," cikin sauri ta ɗago kai ta na cewa "Iye???? Abdul me ya ke damunka ne??" dariya ya yi kafin ya ce "Kin ga dai na sa kin ɗago duk da kin ɓuya, kinga bambancin babba da yaro kenan" "Ni kake kira yarinya??" "A haka nake ɗaukarki Aaminat domin ina da muradin zamo miki bango a Rayuwarki" baki na rawa ta ce "Abdulkareem Rijiyar Zaki za ka kaini don Allah ka dena lelewa da ni akan titi kar ka ɗauki raina kafin na je bikin nan, wallahi nayi da na sanin fitowata zamana a gida ya fi Alkairi, yanzu na tabbatar kai Mahaukaci ne, meye haɗina da kai??" "A zahirance ba alaƙa a tsakaninmu ta jini ko ta wani abun ba abin da mu ka haɗa, sai dai shi Allah babu rawansa baya damuwa da matsayin wani ko wani sai ki ga ya haɗasu Alaƙar, ni dai ina jin akwai alaƙa a tsakaninmu kece dai bakya jin haka, a gurina Ba ki da bambanci da Nana Kadija Nana Fareeda Nana Hauwa'u, dake da su duk ƙannena ne." "Ciwon Zuciya ne ajalina na tabbata, abin duniya ya yi min yawa, ka rufa min asiri ka barni na rayu da baƙin cikin da yake damuna kar ka ƙara min wani tashin hankalin, ka tausaya min ka cire ni daga sahun Ƙannen nan naka don girman Allah" murmushi me taɓa Zuciya ya yi kafin ya ce "Ba ni na sa ki da kaina ba, kuma ba ni da ikon cire ki, ki tayani da Addu'a indai cutata me warkewa ce zan warke in kuma ba zan warke ba to fa ba na jin zan iya bari ki zauna lafiya ko ina ki ka shiga, ki ɗauke ni a matsayin ƙaddararki Aaaminathh!" "Abdulkareem Na tsaneka!!" ta faɗa tare da fashewa da kuka, Murmusawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, Zuciyarsa banda ƙuna ba abin da take yi, a take idanunsa su ka canja launi. ba wanda ya ƙara magana har su ka isa unguwar sannan ya ce "Idan za ki iya ki kwatanta min in ba za ki iya ba sai mu zauna tare a motar don ni ba na gajiya da kallonki ko da gaban tsana za ki yi min." ta san aikata hakan ƙaramin aikinsa ne don haka ta murje idanunta ta kwatanta masa. har ƙofar gidan ya kaita ya na tsayawa ta buɗe ta fito, cikin sauri ya fito ya zagayo inda take ya na cewa "Aaminat don Allah in da wata damuwar ki kira ni, duk lokacin da za ki tafi ma kawai ki neme ni." girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ina Addu'ar kar Allah ya kawo min ranar da zan nemeka don kaina." ya ɗan yi murmushi gami da cewa "Na ji Aaminat, amma ni ba zan yanke ƙauna ba , na ce wata rana za ki neme ni." Fiddausi ce ta kasa yin shiru ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da haɓarta, "Aamina?! tabbas ba shakka, ke aka aje a wannan Motar lunƙumemiya??" Abdukareem ta zubawa ido cike da takaici take binsa da kallon ka ga abin da ka ja min, ya rausayar da kai gami da cewa "Ki yi haƙuri YaYa Aaminat na yi miki shi....." ɗaga masa hannu ta yi kafin ta yi gaba, Fiddausi ta kalle shi kafin ta ce "A kawo maka ruwa Yallaɓai??" a taƙaice ya ce "Sauri nake aikena aka yi shine naga Auntynmu na rage mata hanya." "Laaa Abdulkareem me ya kawo ka Bikinmu?? ko dama kasan ana bikin ne??" Fati ce ta yi magana cike da mamakin ganinsa. "Ke ni wa na sani a cikinku, YaYa Aaminat na kawo, an aikeni ne shine na rage mata hanya" a take annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff ta taɓe baki ta ja hannun Fiddausi. Zagayawa ya yi ya shiga mota ya na mamakin sa ido irin na mutane, ya na ankare da tinda ya zo ya tsaya kowa idanunsa na kansu, har ya koma gida tsaki yake ja gabaki ɗaya duniyar ta yi masa zafi, Abdulkareem Na Tsaneka idan ya tuna kalmar sai ya ji kamar ya yi hauka sabi da zafinta da yake ji. Tin da ta shige

Chapter 3 of 16