shigo da Amarya suka jeru a layi maza da mata suka fara rawa,,
Dangin Ango ma ba abarsu abaya ba haka akaita ɓarin kuɗi Anti Rahina ma tayi liƙi kamar ba gobe haka abokanan ango kowa na wajen farin ciki yake da nishaɗi,
su Kausar ma da sauran ƴan mata na dangin Yarima sun fita da fitar su suma sun zubga ankwan su iri ɗaya material fari ƙal, wajen ya ƙara haduwa, abin burgewa,
misalin ƙarfe 12:00 na dare kowa da ya halarci taron ya koma gida Amarya ma tako ma,
gidan su Yarima kwanan aiki kenan wani ƙaton fili ne na cikin gidan wanda ake ta girke-girke an ɗora kangama kangaman tukwane sai hada hada ake,
Gidan Baba Usman ma ba daga nan ba aiki ake tuƙuru ana kaiwa ana komowa, Aaminat kuwa tuni tayi wanka tabi lafiyar gado, su Ameera Iman Siyama Umaima Hasana da Usaina sai fama surutai suke suna shewa da kagansu kasan suna tsaka da farinciki,
Ɓan garen su Fati ma aiki aketayi,
🤕🤕🤕🤕🤕🤕🤕 wai da gaske dai Yarima ne zai Auri Aaminat ba Abdulkareem ba,😭🫣
Indo &&& Auta
[8/9, 1:33 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 27
Washe gari misalin ƙarfe 10:30 ƙofar gidan su Aaminat ya cika da ƴan ɗaurin Aure sai hada-hada suke, ɓangaren mijin Fati ma sun taru ba laifi.
Yarima ya shirya cikin bugaggiyar shadda ruwan toka mai haske, kai maza fa sun ɗau harama yayi wani fitinennen kyau in kuka ga Yarima sai kun girgiza sabida tsabar haɗuwar da yayi, a hankali yake tafiya tamkar baya tafiyar kansa a ƙasa kamar munafuki sai fici-fici yake da ido, ɓangaren Abba ya nufa, Ammi Anti Zainab suna tsaye da alama wani abun suke tattaunawa, sallama ya ɗanyi murya ciki-ciki. Anti Zainab ta dube shi ta ce "Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya," baice komai ba sabi da kunyarsu da ya keji, Ammi ma addu'a tayi masa tare da nasihohi, daga haka sukayi sallama.
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Harabar gidan ya fita, inda su Sabir suke suna jiran fitowar sa, Sabir ya maka masa harara, cike da zaulaya ya ce "kaje ka nemi waje kayi zaman ka sai an ɗaura Auren da wani ko" "cakwakiya ai ko da me suke yawo saiya sake ta an ɗaurawa yayan mu" Sulaiman ya faɗa yana harɗe ƙafa, Yarima kuwa ko kallon su baiyi ba ya wuce ya shige mota abin sa, suma binsa sukayi, suka shiga, Sulaiman ya zauna a mazaunin Direba, cikin nutsuwa ya fara jan motar har suka ɗauki hanyar Unguwar gadon ƙaya,
Basu ɓata lokaci mai tsawo ba suka isa, layin ya cika taf da mutane sai kayam-kayam suke bayan mintina ƙalilan aka shaida Ɗaurin Auren, ABUBAKAR SAADIQ YAHAYA, tate da AAMINAT HABIBU SALEH,
sai
AHMAD ZAKARIYYA, tare da FATIMA HABIBU SALEH.
ma sha Allah Aure ya ɗauru, nan aka shiga gaggaisawa da mutane ana rabon goro da alawa na ɗaurin Aure,
Fati da yayyan ta mata su uku Hajara Faiza Alawiyya, suna ɗaki suna jin an ɗaura Aure suka sa shewa tare da ta fawa, Haja ta kalli Fati ta ce "yarinya kin Auri mai kuɗi ki taka duk wanda ranki yakeso," ko dangin sa bance kiraga musu ba, karki ragawa kowa ko da uwarsa ce in ba haka ba rainaki zasuyi" Faiza ta faɗa tana zazzaro wa Fati ido, Fati ta yi wani shu'umin murmushi gami da cewa "karku wani walar da kanku wannan Mama ta daɗe tana faɗamin," "dama nasan zata faɗamiki amma ki kula da wannan maganin gobe da safe kiyi amfani dashi wajen girki," "to" ta ce Nafisa ce ta shigo ɗakin tana cewa "uwar gida a gidan Ahmad," Fati ta saki murmushi tare da cije gefen laɓɓanta, dariya suka sa hada shewa, Nafisa ta ce "ki tashi muje waje za'ayi photo da Angwaye" zaram Fati ta miƙe tare da gyara mayafinta, tabi Nafisa suka fita,
Ɓangaren su Yarima kuwa ba'ajima da ɗaura Aure ba sukayi ta fiyar su,
Aaminat tana zaune a ɗaki Siyama ta shigo da sallama, murya a sarƙe ta amsa, zama Siyama ta yi, gami da cewa "Aaminat wai bakya son Yarima ne," wani yarrrr taji ta kanta yayi, tunanin amsar da zata bawa Siyama ta shigayi, jin Aaminat bata ce komai ba, yasa Siyama cewa "bakya son sa ko?" ƙasa ta ɗanyi da kai, cikin sassanyar muryar ta mai daɗin sauraro ta ce, Siyama in nace miki banason Yarima nayi ƙarya, abu ɗaya ne yake hanani sakewa da shi tunanin Abdul ina ganin kamar munci amanar sa," dai-dai lokacin ya Omar ya kutso ɗaki da alama yaji maganar da suke, ƙarasowa yayi, sannan ya zauna akan wata kujera madaidaiciya, Aaminat kuwa tuni jikinta ya hau rawa ta sani ya Omar ba wasa, Siyama ma ta kasa ɗaga ido ta kalle shi, gyaran murya yayi gami da cewa "Aaminat dama baki da hankali, yanzu fa kina da haƙƙin wani akanki, mai yasa kike tunanin wani wanda ba muharramin ki ba????,"... ya ƙarasa maganar yana tsira mata ido, jin batace komai ba yasa ya ƙara cewa "Aaminat karki kuskura in ƙaraji kince kunci amanar sa, ba haka cin amana yake ba, hassali ma shi da kansa Abdul ɗin ya roƙe ki da ki Auri Amininsa, to kinga ai sam hakan baiyi kama da cin amana ba".
karyar da murya yayi kamar mai shirin kuka ya ce "Aaminat dan Allah kiriƙe Auren ki da daraja ki riƙi mijinki, kiyiwa mijinki biyayya dan Allah karki bari duniya ta ruɗeki," cikin kuka ta ce "na gode yaya, Allah ya saka da alkairi, kuma zanyi duk abinda kace, zanyi biyayya agidan Aure na, har na tsahon rayuwata," murmusawa yayi gami da cewa "Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya kaɗe duk wata fitina," suka amsa da Amin, tashi yayi ya fita,, Siyama ta maida kallonta kan Aaminat ta ce "na tayaki murna Allah ya baku zaman lafiya, Allah yasa gidan zaman ki ne," "Amin" ta ce suka shiga fira da Siyama, duk da Aaminat ba wani magana take ba sai murmushi ko eh da ummm,
Misalin ƙarfe uku na rana
Ko wana ɓan gare sun sanya anko ko ta ina biki ake ana nishaɗi
Ammi da Anti Zainab sunyi wankan dakakken leshi ruwan kwai sunyi bala'in kyau, Kausar ce ta zo wucewa ta taga su Amma sai faman kici-kici suke a ɗakin Abinci, tsayawa tayi cike da zaulayar kakannin na ta ta ce "su Anti fa an zage wai adole ana Aurar da ɗa" dariya sukayi, Anti ta ce "Kausar baki ƙyale kowa ba," dariyar itama tayi, sannan ta wuce ɗakin Ammi, ta sauya kaya,
Da yamma gafda za'akai Amarya
Gidan su Fati faɗa ya ɓarke tsakanin dangin Abba da na Mama, saka makon ɓatan wayar ƴar ƙanwar Abba, Mama sai zage-zage take kamar mahaukaciya wai an ɗorawa dangin ta sata, haka sukaita turnuƙu ana bala'i, ɗaya daga cikin dangin Abba ta ce "ai Bara'atu kinyi asara ƴaƴa a lalace, ke a tambaɗe, Abinci agidannan gagarar mu yayi saidai kuci keda gaiyar tsiyarki," ta ƙarasa maganar tana huci, rai a ɓace Bara'atu (Mama) ta ce "ni kike cewa atambade to wallahi ƙaryar ki, ni zaki duba kicewa ƴaƴa a lalace,??.. to ai basukai na wadda ta ɗora ƴaƴan akan karuwanci ba, garani na basu tarbiya," wata shewa dangin Abba suka sa,, Jamila ƙanwar Abba ta kalli Umma gami da cewa "to tsohuwar munafuka ai anyi walƙiya mungan ki, yanzu munsan sharri kikewa Umma agidan nan kuma da tanan ƙaryarki ki hanamu Abinci," sakin baki Mama tayi sakaka tana kallon su, ta kasa cewa komai, hakan ya ƙara turnuƙeta, su Alawiyya da ma suna cen suna nasu faɗan, Mama kuwa ganin batayi nasara ba, yasa ta nufi ɗaki, fakan-fakan sharaf-sharaf tana kuka, dangin Abba kuwa tuni sun haɗa kayansu sunce barin gidan zasuyi, kaɗan ne suka zauna suma don ya zama dolen su ne,
Umman Nazir Autar su Umma da Anti maman su Siyama, sai Aaminat da take cikin shirin Atamfa mai kyau da tsada, riga da zani, sai ƙaton mayafin da aka rufeta ruf,, tana zaune agefen gado tana kuka, Umman Nazir ta ce "Aaminat kibi mijinki, kibi duk abinda ya ce indai hakan bai saɓawa addini ba, kiyi biyayya wa iyayan mijinki yanzu sune iyayanki, kinji, ki kyauta tawa dangin Mijinki,, kar inji kar ingani kinyi abinda bai kamata ba kinji ko,"
Auta ta ce "komai yayi zafi maganin sa Allah duk abinda za'ayi miki, toki kauda kai wata rana sai labari, mahaƙurci mawadaci, kiyi koyi da halin mahaifiyarki ki zama mai haƙurin gaske ki jure ki cije,"
Banda kuka ba abinda Aaminat take, Anti ta muskuta gami da cewa "nasanki da kafiya wani lokacin, to ki daina kinji, yi nayi bari na bari, karki kuskura ki ɗauki zigar ƙawaye duk abinda zasuce miki kiyi watsi da shi, kibi mijinki sau da ƙafa, kinji ƴata"
haka sukaci gaba da yi mata faɗa, da nasihohi, masu ratsa jiki,
Maman Humaira ce ta shigo da sallama suka amsa, Anti ta duba gami da cewa "masu ɗaukar Amarya suna jira ance ku fito da ita," "to yanzu ma kuwa in sha Allahu ga mu nan", Anti ta faɗa, Maman Humaira ta juya zuwa wajen ƴan ɗaukar Amarya,
Siyama ce ta shigo ɗakin tana kuka, Aaminat tana jin kukan Siyama ta ƙara fashewa da kuka, da gudu Siyama ta rungume Aaminat tana wani kuka mai tsuma zuciya, cikin muryar kuka Siyama ta ce "Aaminat yanzu rabuwa zamuyi zaki tafi ki barni," Aaminat kuwa ta kasa koda magana sai kuka, ko ɗaga harshe ta kasa, da sunan tayi magana, Umman Nazir ce ta kama hannun Aminat, Auta ta janye Siyama, sukansu su Umman Nazir ɗin saida suka share hawaye, duk wanda yaga yadda Siyama da Aaminat suke ɓarzar kuka saiya tausaya musu, gashi sun shaƙu, "dan Allah kudaina kuka kunji kuyi haƙuri rabuwa ta zama dole saidai ziyara," wani kukan Aaminat ta ƙara rushewa da shi, Umman Bazir taja Aaminat, dan kuwa daƙirewa tayi,
Ɗakin da Umma da su Baba Usman suke, suka shiga da Aaminat, durƙusawa tayi kan guiwoyinta tana kuka kamar ranta zai fita, cikin tausayawa Umman Nazir ta ce "kiyiwa mahaifiyarki sallama ki nemi yafiyarta," cikin sarƙaƙƙiyar murya mai cike da ban tausayi ta ce "U ....u....u...umm..umma ki yafemin!!!!!!" cike da jarumta Umma ta ce "ba kiyi min laifin komai ba Aaminat Allah yayi miki albarka, Allah ya baku zaman lafiya" mutanen ɗakin suka amsa da Ameen,, Anti ta ce "to Umma zamu tafi da Aaminat ɗakinta kuyi sallama," murya na rawa Aaminat ta ce "Um...umma zan tafi ki yafe min dan Allah," "Allah ya tsare hanya, ya kaiku lafiya," hannun Aaminat suka kama zasu tasheta saidai sukeji ta riƙe, Umma gamm, haka sukaita ƙwarbe da ita kana suka samu nasarar raba Aaminat da Umma, kai tsaye mota suka shige kowa ya shiga mota suka kama hanyar gidan Amarya,
Ɓangaren Fati ma tuni an tafi da ita,
Basu ɓata lokaci ba suka ƙarasa gidan su Yarima jagora akayi musu zuwa ɓangaren Ammi, gaisawa sukayi sannan sukayi ƴan addu'oi, Anti ta ce "ga Amana nan mun kawo muku, idan tayi ba dai-dai ba ku gyara mata ku nuna mata, dan Allah, duk abinda tayi in me kyaune kune in mara kyaune kune, mudai ga Amana nan mun baku," Anti Zainab ta muskuta gami da cewa "in sha Allahu zaku samemu masu gaskiya da ruƙon Amana, kuma in Allah yayarda mun zama ɗaya ƴarmu ce", cike da gamsuwa sukayi sallama suka raka Aaminat ɗakin ta dake wani sashi na gidan,
Basu daɗe ba kowa ya kama gaban sa suka koma gidan, Siyama Umaima Iman Ameera, su kai ɗaina agidan suna taya Aaminat zama,
Bayan na ɗan wani lokaci
suna zaune agefen Gado sukaji sallama, amsawa sukayi sannan suka bashi izinin shigowa,
Sabir yana ƴar dariya ya ce "ƴan mata, mai guri yazo sai mai tabarma ya naɗe," tsaki Siyama tayi gami da cewa "ai ba cewa mukayi zamu zauna ba," dariya yayi dama kunnasu yake sonyi kuma ya kunna, "kuma babu wadda zamu mayar, wayace baku bi manya kun koma gida ba" Siyama taja tsaki cike da baƙinciki Iman ta dube shi ta ce "kaga malam ka tattara ya naka ya naka ka bamu waje musha iska," dariya yayi cike da tsokana irin tasa ya ce "ni ai gidan mune kune zaku tattara komatsanku ku bar mana gida",.... zai ƙarayin magana yaji Sallamar su Yarima, da sauri ya ce "yanzu dama zan fito" Sulaiman ya ce "na mata na mata kawai tun ɗazu daga aike kanemi waje kayi zaman ka," ɗan sosa sumar kansa yayi, su Umaima suka gaida Yarima, Siyama kuwa ko kallon sa batayi ba, ta figi Jakar ta ta na "cewa sai ku tashi mu tafi tunda ba gidan ku bane," ba musu suka tashi, Yarima ya ɗan murmusa gami da cewa Iman "mai akayiwa Siyama ne" murmushi tayi gami da cewa "wai fishi take ka rabata da Aminiyar ta," murmusawa yayi gami da cewa "haka dama rayuwar take sai haƙuri," batace komaiba tabi bayan su Umaima, Yarima ya dubi su Sabir ya ce "to ku kuma mai kuke jira," dariya suka sa, sannan Sabir ya ce "babu abinda muke jira tafiya zamuyi" "to sai ku tafi" Yarima ya faɗa yana hararar su, fita sukayi, Sabir ya wuce harabar gidan, yana zuwa ya tarar su Siyama sun shiga motar Iman sun tafi sai ƙyellinsu ya hango ta get, baiji daɗin hakan ba so yayi sun ƙara casuwa, hakan yasa ya juya y nufi ɗakin da suka sauka,
Ɓan garen su Yarima kuma saidai na ce Asuba ta gari,,
Indo ❤🩹 Salma
[8/9, 1:33 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 28
Bayan Biki da kwana uku kowa da ya halarci taron Bikin ya koma gidan sa, su Umma ma sun koma gida taro ya tashi lafiya Alhamdulillah,
Sanye take cikin dakakken leshi fari ɗinkin buba yaji adon duwatsu masu sheƙi da ƙelli, a hankali da nutsuwa take sakkowa daga benen dake ƙaton Falon, wanda yaji kayan more rayuwa, da kayan alatu iri-iri, komai na Falon pink da fari ne, kama daga kan kujeru kwalliyar Falon, komai pink da fari ne, kai Falon fa ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru, Ma sha Allah, zama tayi akan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun Falon, kai dagani kasan an zuba kuɗaɗa na tashin hankali, wani tattausain murmushi ne ya kufce mata, har saida fararen haƙoranta suka baiyana, sallamar da akayi ce ta fargar da ita tayi saurin haɗe fuska, ƙarasowa yayi cike da jin daɗi da farin ciki, ya ce "wa na kama???" ya faɗa yana dariya, murmusawa tayi kafin ta buɗe baki ta ce "yanzu ma ai baka kamani ba," "haka zakice ko??" "A'a nifa banyi magana ba," "mai kika ce??" ya faɗa yana zuba mata wani sihirtaccen kallo mai rikitarwa, murya ƙasa-ƙasa ta ce "ce wa nayi sannu da zuwa" dariya yayi gami da cewa "Aaminat wato kin rainani ko" "ni na isa in raina ka," murmusawa yayi, batare da ya ce komai ba, shirune ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Yarima ya ce "ni zan wuce Asibiti kije sashin su Ammi ki zauna kafin na dawo" "to" ta ce tana tashi, kallon ta yayi gami da cewa "saura kuma inna dawo kiyi zamanki ki ƙi zuwa," dariya tayi, yaɗan harareta harara mai tafe da saƙonnin so, kala-kala, wani murmushi ne ya kufce mata tayi saurin rufe fuskar ta da tafukan hannunta, juyawa yayi ya fara tafiya cikin nutsuwa, bayan sa tabi, ma'ajiyar motocin gidan ta rakashi, sannan ta juya ta koma,
.
.Fati tana zaune a hamshaƙin Falon ta tana latsa waya, Ahmad ne ya shigo, wani kallo yayi mata mai cike da ma'anoni, sannan ya zauna kusa da ita, cikin yauƙi ta ce "Baby na sannu fa" "yauwa ya gidan,??" "lafiya" wani musmushi ya kumayi mai cike da tsantsar ma'ana, tashi yayi zai wuce ta ce "gaskiya mota nakeson ka siyamin," "mota kuma??" "eh mota ko bazaka siya ba?" murmusawa yayi gami da cewa "yaufa kwananki uku agidan nan, mai ki ke ci na baka na zuba, Habibti na" cingam ɗin bakinta ta tauna tare da "cewa shikenan"
haka sukaci gaba da ƴar hira tana nuna masa son duniya ƙarara, shima ya na nuna mata na sa salon.
Atsaye suke cirko-cirko, kowa yana tunane tunane, Nana Hauwa ce ta dubi Abdussalam gami da cewa "anya kuwa Abdul zai dawo garemu, kusan wata ɗaya kenan baya garemu kuma duk ta silar ku ne" ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye, Abdussalam ya jata jikinsa cikin sigar kwantar mata da hankali ya ce "sorry Nana ki daina kuka, in sha Allah komai zai dai-daita, kuma muna ta addu'a Allah ya juyo da hankalin sa gida" Nana Farida ce ta tashi daga kusa da Dadda ta ce "kalli fa Ummi bata da lafiya, ya zama dole in muna son rayuwar mahaifiyar mu mu nemo ya Abdul," Abdurrahim ya girgiza kai kana ya ce "ta hanya ɗaya zamu sami Abdul"
Abdulmajid ya ce "wace hanya ce???" "ta hanyar roƙon Kadija ta faɗa mana inda yake domin kuwa ina da tabbacin ta san inda yake" da sauri Dad ya tashi zaram yana zaro ido ya ce "haka ne Maza ku kira ta " "to" Abdullah ya faɗa yana nemo number Kadija, kira ya danna mata bugu huɗu ta ɗauka da sallama, hankali tashe ya ce "don Allah kadija ki taimaka ki faɗa mana inda Abdul yake karki ce baki san inda yake ba, hakan na iya silar rasa mahaifiyar mu," ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka, Kadija kamm tayi suman zaune ta kasa koda magana ne, jin ya ƙara cewa "Kadija Abdul shine rayuwar mu baki ɗaya dan Allah" yasa tayi fifgigit, cikin muryar kuka ta ce "Abdul yana india, dole ce tasa na faɗi inda yake," "Kadija kidawo gida Abdul ma zai dawo" hawaye ta share tana tuna lokacin da su Dadda suka murzawa idon su toka suka hana Abdul Abinda yake so, "Kadija yanzu in sha Allah zamu shirya tafiya, kuma hada ke gobe zamu je inda Abdul yake mu dawo dashi gida", wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke gami da ce wa "ganin nan zuwa yanzu" sallama sukayi, Abdulmajid cikin jindaɗi ya ce "Alhamdulillah mun kusa dawo da Autanmu," kowa na ɗakin farin ciki ya hauyi ciki kuwa har da Dadda Ummi ma murmushi take tana miƙa saƙon godiya ga sarki Allah buwayi gagara misali,
Washe gari da sassafe Jirgin su Dadda Abdussalam Abdulmajid Nana Kadija, ya tashi izuwa ƙasar india,
Umma na zaune a ɗaki ta kammala karatun Alƙur'ni mai girma ta na yin addu'a, wayar ta ta fara ruri, ta mayar da Alƙur'anin mazaunin sa, sannan ta juyo inda wayar take kafin ta ƙaraso wayar ta katse, ɗaukar wayar tayi sannan ta zaune a gefen godo, kira ne ya ƙara shigowa wayar, ta ɗauka da sallama, "Assalamu'alaikum Ummana ta kai na," "Aminwa'alaikisalam," ta faɗa tana murmushi, cikin farin ciki da jin daɗi, Aaminat ta ce "Umma ya kuke ina kewar ku wallahi, dan Allah kice ya kawoni" "A'a Aaminatu kefa ba yarinya bace, ki zauna agidan ki kinji ko?" turɓune fuska tayi, kamar tana ganin Umma ta fara magana cikin shagwaɓa, "ni Umma na zan gani yaufa kwana huɗu rabo na da Umma na" "to kinga kwana huɗu ai bakyazo gida ba kuna zaune lafiya," "nifa Umma ji nake tamkar nayi shekaru ban ganku ba" Umma ta murmusa, Aaminat ta ƙara cewa "ina su Walid da Umaima suzo dan Allah" "A'a bazasu zo ba, kedai ki nutsu ki zauna agidan mijin ki banda yawon banza"
"kai Umma kin sanni fa ko a nan bana zuwa ko ina sai gidan su Siyama, anan kuma wa na sani, gidan da ko yara babu, ni duk na gaji, jinake kamar akan ƙaya neke, wata tsawa Umma ta darka mata ta ce "ba ki da hankali gidan mijin naki kike kira kan ƙaya? to karki sake na ƙara jin wannan maganar a bakin ki" tsitt Aaminat tayi baki na rawa ta ce "Umma dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba, kinji Ummu na" tsaki Umma taja, sannan ta ce "sai anjima" tana gama faɗin haka ta katse wayar, Aaminat kuwa ajiyar zuciya ta sauke.
Koda su Dadda suka isa masaukin Abdul, basu sha wahalar shawo kansa ba, kwanansu ɗaya suka juyo gida.
Zaune suke Falon kowa sai farin ciki yake kamar ba gobe, Ummi kam tunda taga ɗan Autan ta sai ta nemi cuta ta rasa sai rashin ƙwarin jiki, Abdussalam kuwa sam ya kasa sakewa da Abdul dan kuwa bai manta lokacin da yake marin Abdul ba da maganganu mara sa daɗi, Dadda ya dubi Abdul ya ce "babban mutum" Abdulkareem ya ɗago da runannun idanun sa ya zubawa Dadda su, Dad yayi gyaran murya gami da cewa "Abdulkareem kayi haƙuri mun sani bamu kyauta maka ba, amma mu muna gyara goben ka ne, inaso ka sani ita rayuwa ba komai ne muke nema mu samu ba, wani abun muna neman sa ido rufe, amma sai Allah ya hana mu kuma duk dan ya jarraba mu ne, wani abun kuma zakuga bamu nema ba Allah ya bamu,"...... zuwa yanzu Abdul yayi ƙasa da kansa sai sharar hawaye yake, Dadda ya ce "komai na rayuwa haƙuri ake dashi, saika ga mai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 16