Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Kadija ce ta shigo ɗakin da ka ganta kasan taci kuka har ta gaji zama tayi a kujerar da ke kusa da gadon, murya a cunkushe ta ce "ya Abdul dan Allah ka daina sakanka cikin damuwa ai kin gama ya riga ya gama sai haƙuri ka fauwala wa Allah, ka kai kukan ka ga Allah" bai ce ko mai ba ya bita da kallo,
hannu yasa ya ɗauko takardar da yayi rubutu sannan ya miƙa mata ya ce "ki kaiwa Walid ya kaiwa Aaminat" hannu tasa ta karɓe ya miƙo mata ɗayar ya ce "ki aje a inda su Dadda zasu gani" "to" tace tana bin sa da kallon tausayi, tashi yayi ya fara takawa ɗaya bayan ɗaya sanna ya tsaya batare da ya juyo ba, ya ce "SAI ABINDA ALLAH YAYI" rasss raaass gaban ta ya yanke ya faɗi cikin tashin hankali ta ce "ina zaka???!!!! bana so murasa ka" tafiya ya cigaba dayi ta shiga roƙon sa ya faɗa mata inda zaije batare da ya tsaya ba ya ce "India" wani kuka ta saki, tana so ta dakatar da shi sai dai bata da dama, tanaji tana gani ya ɓacewa ganin ta,
Da taimakon Allah Abubakar ya isa gida ya daɗe a mota yana aikin kuka kafin ya fito kai tsaye ya nufi sashin sa, kayan jikin sa ya rage sannan ya watsa ruwa ya fito, komawa yayi ya zauna tare da runtse ido, Anti Zainab ce ta shigo ɗakin da sallama, ciki-ciki ya amsa, ta ƙaraso hannun ta ɗauke da filet da abinci zama tayi gefen gado gami da cewa "mijin E'iye lafiya kuwa naga kamar kayi kuka kuma ba kaɗan ba???!" bai ko kalli inda take ba ya ce "babu buƙatar Abinci ki koma da shi" sakin baki tayi sakaka tana kallon sa, tunda take agidan bai taɓa faɗa mata magana irin wannan ba ko makamancin ta, ganin bata da niyar tafiya yasa ya ce "dan Allah Anti kiyi haƙuri ki tafi" zaro ido tayi ta kalle sa ta ce "babu inda zani sai naji ko mai yasa ka kuka" tabbass yau da ba Antin sa bace da sai ya lakaɗa mata duka, "dan Allah ka faɗa min kasani ko nataya ka nemo mafita????" bai ce mata komai ba, taci gaba da magiya, da naci,
hakan yasa ya zaiyane mata komai tundaga farko har izuwa ƙarshe, ta tausaya wa Abdul jikin ta yayi sanyi ƙalau hada matse ƴar ƙwalla, ta ce "Abubakar ina ganin ka taimake sa ka Aure ta dan Allah" rausayar da kai yayi ya ce bazan iya zama da wadda Aminina ya fiso a duniya ba"
murmusawa tayi ta ce "kenan bazaka iya taimaka masa ba aduk halinda yake ba???" shiru yayi ta ce "zan sanarwa Abi yaje suyi magana da mahaifin ta" bai ce komai ba ya bita da idanu, tashi tayi gami da cewa "kaci Abincin nan ko kaɗan ne" wani mugun kallo ya maka mata, tayi saurin da wowa ta kinkimi Abincin tayi waje
kuyi haƙuri babu yawa
A A &&& Auta
[7/26, 3:03 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 23
Abdulkareem bai jima da fita ba Kadija ta kaiwa Walid takardar da yace ta kaimasa ya kaiwa Aaminat
Aaminat tana zaune A ɗaki jikinta yayi sanyi salam ta zabga uban tagumi Walid yayi sallama amsawa tayi, Walid yace "gashi inji Guda yace abaki!" rasss gabanta yafaɗi, karɓa tayi tace "Walid wani abunne ya faru ko???" jiki a sanyaye ya ce "nima ban sani ba amma ɗazu Abdulkareem yazo yayi mana sallama yace zai nesanta kansa da gida",
juyawa yayi ya fita daga ɗakin Aaminat kuwa ta riga ta gama saduda ta sallama , dama tunda taji mugun firicin Abdussalam ta saduda,
warware takardar tayi ta fara karantawa kamar haka
Assalamu'alaiki, fatan alkairi gareki, Aaminat kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara haka Allah ya rubuta ni ba mijinki bane, Mahaifina yace bai amince na Aureki ba, amma dan Allah na roƙeki ki taimaki rayuwata ki Auri Aminina Abubakar zai kula dake tamkar yadda zan kula dake, ina son ki Amma ƙaddara ta gifta tsakanin mu, ina cikin wani mugun hali ki tayani da addu'a
ina miki fatan alkairi tare da farinciki na tsawon rayuwarki.
tuni hawaye sun wanke mata fuska, da sauri ta ɗauki waya ta kara akunne bugu ɗaya aka ɗauka, cikin muryar kuka da tashin hankali, ta ce "me...meyasa zaka barni alokacin da nake tsaka da buƙatar rayuwa da kai wallahi ina sonka" ƙit ya katse kiran sai a lokacin zafafan hawayen da suka cika ƙwarmin idon sa, suka sami damar sakkowa, ƙasa yayi da kai yana ambaton sunan Allah don samawa kansa sauki.
zuwa yanzu Aaminat ta gama fita hayyacinta kuka take mai tsuma zuciya Umma da Umaima kuwa sai faman rarrashin ta suke, Umma tace "kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara haka Allah yaso daku" haka suka cigaba da rarrashin ta,
Mama da Fati kuwa ransu fafess sai nishaɗi suke suna ɓaɓɓaka dariya Mama ta kalli Fati kana ta ce "ni dama banaso ahaɗa bikinki da na Bazawarar can wallhi, sai gashi saurayin ma ya fece" dariya suka sa hada shewa,
Abi ne zaune a Falon Anti Zainab, Yarima ya shigo kai aƙasa, zama yayi kusa da Anti Zainab gami da cewa "barkan ku da dare " Abi ya ce "yauwa" Anti Zainab ta muskuta gami da cewa "Abi dama tun ɗazu nakeso zamuyi magana da kai" ya ce "to ina jinki" "dama batu ne akan Abdulkareem" Abi ya murmusa sannan ya ce "Abdulkareem yayi mini bayanin komai gaskiya abinda Aminina yayi bai kyauta ba, banji daɗi ba," Anti ta ce "to ya za'ayi sai haƙuri nima ya bani tausayi wallhi" tashi Yarima yayi, Abi ya dakatar dashi ta hanyar cewa "zo mana Abubakar" dawowa yayi ya zauna, Abi ya ce "Abdul ya roƙeni na taimaka masa na nema maka Auren Aaminat domin yana ganin zaka iya maye gurbin sa arayuwarta" ƙasa yayi da kai, Abi ya ƙara da cewa "kuma na yanke hukunci zuwa jibi iyayanka su Alhaji Kabiru zasuje gidan su yarinyar saika faɗa mata ta sanar da mahaifin ta" cikin rawar murya ya ce "to"
ya tashi ya nufi sashin Ammi,
Washegari da safe
ahankali Dadda yake sakkowa daga benen dake tsakiyar Falon gaban sa ne yayi wata muguwar faɗuwa ganin hawaye shaɓe-shaɓe afuskarta, da sauri ya ƙarasa inda take sai alokacin ya lura da takardar dake riƙe ahannun ta, hannu yasa ya karɓi takardar sannan ya zauna kan kujera ya fara karantawa,
kamar haka
"Salam Daddana da Ummina, tabbas ban taɓa zaton haka daga gareku ba, nayi tunanin zaku iya cika duk wani buri na ɗanku ashe ba haka bane, dama ƙaunar da kukemin ba har cikin zuciyar ku bace???? Uhmmm ban taɓa tsammanin hakan ba, nayanke hukuncin nesan ta kaina daku, nabar ku lafiya" wata zazzafar iska Dadda ya furzar cikin dakakkiyar muryar sa ta jajirtaccen Uban da ya amsa suna Uba, ya ce "kar hakan ya dameki kuma hakan ba zaisa na sauya ra'ayi na ba" yana gama faɗin haka ya juya zuciyarsa na wani mugun tar tsatsin azaba tabbass a zahiri bazaka taɓa iya gane iya tashin hankalin da Dadda ya shiga ba, a baɗini kuwa zaka iya cewa yafi kowa shiga tashin hankali dan kuwa tafiya yake a harabar gidan amma baisan inda yake jefa ƙafarsa ba,
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
su Abdussalam suma suna ɗaki suna nasu zaman makokin, babu mai iya cewa ɗan uwan sa ƙala saidai kallon kallo su Farida kuwa sunyi kuka mai isarsu sun gaji, Kadija kam tun daren jiya ta haɗa kayan ta tsaf ta koma gidan Uncle Rabi'u,
"Aaminat ki daure kici abincin nan, ki fauwala wa Allah komai" Umma ta faɗa cike da damuwa,
Umaima kuwa tana gefen Aaminat ita da Siyama sun zabga tagumi sai muzurai suke,
haka kowa ne gida suka wuni cikin baƙinciki,
Bayan kwana biyu su Alhaji Kabiru da Baba Usman sukaje gidan su Aaminat suka gana da mahaifinta da ƙaninsa Baba Auwalu, cikin kamala suka bawa Yarima Auren Aaminat,
Haka rayuwa ta cigaba da garawa a kowane ɓangare.
Gidan su Abdulkareem kuwa har zuwa yanzu
babu wanda yasan inda Abdul yake agidan sai Kadija ita kuma tayi musu ƙaura daga gidan Alhaji Aminu kuwa yayi cigiyar yayi neman amma shuru,
Yau ta kasance ranar lahadi saura sati ɗaya bikin Aaminat da Abubakar (Yarima)
Ammi tana zaune a falon ta ta zabga ta gumi, Yarima yayi sallma, zama yayi kusa da ita gami da cewa "Ammi lafiya kuwa???, naga kwana biyu bakya walwala" hawaye ne suka fara shatata tayi saurin kauda kai, "Ammi meke faruwa haka dan Allah ki daina kuka banason ganin kukan ki," cikin muryar kuka ta ce "mahaifinka ya juya min baya sam ya daina saurara ta ko magana nayi masa baya kulani rabon da yazo sashina har na manta kullum sainayi kuka mai isa ta" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kama hannunta ya ce "Abi yace mini ba zai iya zama da wadda bata ƙaunar iyayansa ba, shine dalilinsa na juya miki baya" hawaye ta sharen gami da cewa "Allah natuba kayafeni wallhi duk zigar su Hajiya Bilki ce suka ce karna bi iyayan mijina wai E'iya ta fiye tsugudidi da munafurci ga masifa, sun cuceni gashi sun rabani da miji na" ta ƙarasa maganar tana kuka Abubakar yasa hannu ya share mata hawayen sannan ya ce "tunda Allah ya ganar dake gaskiya ina ganin kije ki nemi yafiyar su mahaifiyar tasa daganan saiki faɗa musu abinda yake faruwa tsakanin ku da Abi ɗin zasuyi masa faɗa kuma zai ɗauka, banda abinki dama Amma kema fa uwa ce idan na yi Aure matata ta tsaneki kamar yadda ki ka tsani su E'iya nasan ke ba ma za ki iya haƙura ba"
rausayar da kai tayi ta ce "Ai Ƙaddara ce yaro, ni bansan hakan kuskure bane, kana ganin su Hajiya E'iye zasu yafemin abinda nayi musu harfa kiransu nake da mayu, kaicona nayi asara" ta ƙarasa maganar tana kuka mai ƙarfi, cikin ƙwarin guiwa Abubakar ya ce "zasu yafe miki in sha Allah, ki shirya na kaiki gidan" "to" tace cike da tararradin zasu karɓeta ko kuwa,
bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf suka ɗauki hanyar gidan su E'iye
cikin mintina ƙalilan suka ƙarasa gidan Yarima yayi gaba Ammi na biye da bayan sa kai tsaye sashin E'iye suka nufa
E'iye da Inni suna zaune a Falo sukaji sallama, fuska babu yabo babu fallasa Inni ta amsa, Abubakar ya ce "yadai Budurwas naga kin wani haɗe fuska" zumɓura baki tayi ta ce "naga ka shigo mana da baƙuwar fuska ne" murmusawa yayi ya ce "Ammi ce tazo ta naimi yafiyar ku" Ammi kuwa kanta yana ƙasa sai sharar ƙwalla take, Abubakar ya ce "ni bari naje wajen su Huzaifa" Ammi ta zauna murya na rawa tace "dan Allah ku yafe mini na tafka babban kuskure da ban ɗaukeku da daraja ba, dan Allah ku gafarce ni badanni ba dan Allah na roƙeku" ajiyar zuciya E'iye ta sauke a ranta ta ce Alhamdulillah Allah kaine abin godiya, Inni kuwa tashi tayi zata bar wajen, Ammi tayi saurin durƙushewa agaban ta ce "dan Allah ba danni ba ku yafemin dan girman Allah" E'iye ta ce "nayafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya" Inni ta sake ajiyar zciya ta ce "nima na yafe miki kinji ai ɗa na kowa ne, ina fatan Allah i shiryi duk masu irin halinki" Ammi bata san lokacin da ta fara murmushin farin ciki ba, ta ce "Na gode Allah i saka da Alkairi....
Indo and Autar Jarumai
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 24
E'iye ta ce "ya zaman gidan naku komai lafiya ko!???" da sauri Ammi ta girgiza kai ta ce "da sauki dai, Abi ya juyamin baya yanzu ko magana bata haɗani da shi sai kallo amma karku ga laifinsa nice da laifi dan kuwa mugun halina ne ya ja mini" E'iye ta ce "sabhanallahi mekikayi masa har haka!??" murya ƙasa-ƙasa ta ce "rashinyi muku biyayya ne kuma yanzu na gane kuskure na wallhi nayi nadamar abinda na aikata, duk nice silar rabuwar Abubakar da ƴar uwarsa, nidai banyi dacan hali ba" cike da manyance E'iye ta ce "kinga dama haka duniya take abinda ka shuka shi zaka girba, ko akan Abubakar zaki gane Allah ɗaya ne, tun yana goye yake ƙaunar mu har ya girma kinsha jifanmu da munanan kalamai, amma yanzu komai ya wuce, zankira Alhaji Saadiƙ ɗin" ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayar ta ta dannawa kira Abi bugu biyu ya ɗauka, cike da girmamawa yayi sallama, ko amsawa batayi ba ta ce "ka hanzarta zuwa ina nemanka" rasss gaban sa ya faɗi cikin rawar murya ya ce "lafiya kuwa" "inkazo kaji" ta faɗa tana sauke wayar,
bayan ɗan wani lokaci Abi ya ƙaraso gidan kai tsaye yayi ɓangaren E'iye, sallama yayi a Falon turusss yayi ganin Hajiya Hafsa tayi muzu-muzu gaida su Inni, yayi rai a ɓace ya kalli Ammi ya ce "meya kawoki gidanmu kokinzo ki haddasa mana fitina agida???? to kisani makircinki babu inda zaije"...
numfashi yaja ya cigaba da cewa "idan kin manta ni ban manta ba, lokacin da sukaje gidanki kikasa akayi musu korar kaji kikace ke baki sansu ba, dama zama kawai nakeyi dake amma yanzu zamanki yaƙare agi...." "ka dakata karka yanke hukunci cikin fushi" muryar Inni ta dakatar dashi
E'iye ta ce "bawai nakiraka bane dan ka dawoda bara bana ba, nakirakane domin inaso ka daina abinda kake ka ka koma ga iyalinka, indai akanmune ka fita shirgin matarka to kakoma, ta nemi yafiyarmu kuma munyafe mata, saura kai" ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "tinda kun yafe mata nima na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗaya, kuma darajarku da ta ɗanta ta ci" suka amsa da amin, shurune ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Abi ya ce "nizan koma sai anjima zan dawo" Inni ta ce "to Allah ya kaimu anjiman, nima zan fita nayo siye-siye kar naje Amarya tafini kyau" dariya sukayi Abi ya tashi E'iye ta ce "ai bamu gama magana ba" komawa yayi ya zauna, ta ce "inason da kaida Hafsa ku haɗa kan ƴaƴanku da yarabe" Inni ta ce "gaskiya dai yakamata wannan gabar da take tsakanin su tazo ƙarshe" "to in sha Allahu zamuyi hakan, Allah ya saka da alkairi," kallon Hajiya Hafsa yayi ya ce kikira Rahina kice ina nemanta yau ɗinnan," cikin jin daɗi Ammi ta ce "to" sallama yayi musu sannan ya fita,"
Yarima ne ya shigo Falon yana tafe yana haɗa hanya Inni ta ce "saurayin ya dai naga kamar bakajin daɗi" zama yayi gami da cewa "kin fiya ƙaga min cuta banace muku Dr baya rashin lafiya ba???" E'iye ta maka masa harara gami da cewa "shiyasa naga ai Dr kullum sai yayi kuka," dariya yayi ya ce "to su E'iye kinshin ya motsa" badole ya motsa ba zakayi mini kishiya kuma kace dagani ka gama Aure" Haba uwar gida nimafa ba ason raina zan miki kishiya ba" dariya suka sa, Ammi cikin raita ta ce "dama haka suke gudanar da rayuwarsu nake ƙoƙarin shiga tsakanin su???" Inni ta muskuta gami da cewa "ai tare zaka Aure mu nagaji da zaman budurci" dariya sukayi suka cigaba da hirarsu cin farinciki,
"Wai a haka za'a kaiki gidan mijin ko gyara babu" Siyama ta faɗa Aaminat ta ce "gyaranme zanyi" "Au bazakiyi ba kenan" Aaminat ta murmusa ta ce aini agyare nake koda yaushe" dariya Siyama tayi ta ce "kyajidashi dai" Umaima ta ce "Siyama gobe fa zamuje rabon katin gaiyata" "Allah ya kaimu kowa a layinnan sai mun bashi," "kedai bari har maƙiya sai mun gaiyata wallhi ɗazu ma naje fagge wajen mai ɗinki na karɓo" Aaminat ta ce wai ku baku da aiki saina zancan wani biki can" "iyeeee lallai to kokina so ko bakya so sai mun cashee" Siyama ta faɗa tana murguɗa baki Aaminat ta bita da kallo, "Siyama nifa da sosamu ne wallhi da gobe zan fara shagali" Siyama ta ce "to uwar zumuɗi" dariya sukayi, Aaminat ta ce "dan Allah ku bani katin nan na bawa su Bilal" Siyama ta ce "taɓ ai'dasu ake komai suma zasuyi tasu gaiyatar, sune ƴan shigo da Amarya fa" ɗigimi wai shigo da Amarya saikace wata mage" "kinga sai wani babbasarwa kike munfa san komai wallhi" "mekuka sani???, ƴar rainin hankali kawai" Umaima ta ce "ba saikinji ba" "to karku faɗa" dariya sukasa, Aaminat ta ce "wallhi ko kwana biyu tinanin Abdulkareem kawai nake" "Allah sarki rayuwa ɗazu naga ƙanwarsa Farida" Aaminat ta tayi murmushi mai tafe da hawaye, "kinga matsalata dake komai kuka saikace wata kaza" Aaminat ta ce "ina tunanin halinda Abdulkareem yake ciki ko yana ina???" Umaima ta rausayar da kai gami da cewa "haba yaya Aaminat ki daina damuwa na san yasan ankusa bikinku kuma inaga yana nan yana farinciki dan kuwa shi rayuwarda kike ce baya so kuma ai Amininsa ne zai Aureki kuma shiya nemi haka" ƙwalla ta share ta ce "Allah ya bamu haƙuri da dangana," suka amsa da Ameen,,
Abi Ammi Anti zaina Rahina Abubakar zaune suke a babban Falo.
Cikin nasiha Abi ya ce "ke Rahina na kira ki ne akan tsakaninki da ɗan uwanki daga yau sai yau karki kuskura na ƙara ganin kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya, idan baki riƙeshi da daraja ba wazai riƙe miki ɗan uwa kin kuwa san irin baƙin cikin da nakeji idan naga kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya????! babu dare babu rana addu'a nake Allah ya haɗa min kanku Amma ke ce babba kuma kece babbar banza ciki ɗaya amma ace baki da maƙiyi sai wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya anya kuwa kina da hankali????!" Yarima kuwa banda sharar hawaye babu abinda yake, kansa na ƙasa, Ammi ta ce "duniya abin tsoro wata rana in mune wata ranar bamu bane, yanzu itace damarki ki gyara kusakuren ki" "kin kuwa san waye yayi nasarar ceto rayuwarki lokacinda kikayi hatsari???, to ɗan uwanki ne wanda kika ɗauka maƙiyinki, shi ko da yaushe ƙaunarki yake, amma kallon da kike masa daban, sau da yawa ba tare da kin sani ba shi ke temaka miki, wai me ya yi miki ne haka?" da sauri ta ɗago suka haɗa ido da Abubakar yayi saurin yin ƙasa da kai yana goge ƙwalla,
itama maida kai ta yi ƙasa ta kasa cewa komai, jikinta ya yi mugun sanyi,
Ammi ta ce "Wallahi Rahina da ni da ke duk duniya ce take ruɗarmu, amma ko iya abinda ki ka yiwa Abubakar ba ki yi nasara akansa ba su kaɗai sun isa ishara, bai yi miki laifin komai ba, kuma duk nice na fara nuna miki hakan sabida shi yana nunawa kakanninsa ƙauna ki nemi yafiyarsa don Allah" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, Anti ta ce "rashin sanine, ki godewa Allah da ya ganar dake tin yanzu" cikin kuka Rahina ta ce "Abubakar ka yafemin dan Allah wallahi sharrin shaiɗan ne" cikin muryar kuka ya ce "yaya wallahi ni ban taɓa ƙullatarki ba kullum burina naga mun zauna inuwa ɗaya muna zumunci da juna" tashi tayi taje gaf dashi sannan ta durƙusa ta ce "ina neman yafiyar ka kayafe min duk abinda nayi maka" hannu yasa ya share mata hawayen sannan ya kalle ta ya ce "na yafe miki nima ki yafe min" cikin kuka ta ce "na yafe maka dukda bakayimin komai ba" Abi ya ce "Alhamdulillah Allah kaine abin godiya" Ammi kuwa murna take sosai sai sharar hawayen farin ciki take, Abi ya miƙe gami da cewa "lokacin sallah yayi"
tashi suma sukayi kowa ya nufi inda zai ɗaura Alwala"
INDO TARE DA AUTA
[8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 25
Yarima yana dawowa daga masallaci ya nufi ɗakin sa, zama yayi gefen gado ya zabga tagumi, wayar sa ce ta fara ruri da sauri ya ɗauka ya kara akunne, "salamu'alaikum" "likita bokan turai bakaso a mutu bakaso a zauna lafiya" dariya yayi ya ce "mai gaiya mai aiki sai dakai uban gida" dariya sukasa Abdulkareem ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 16