An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
PAGE 1
Bismillahirrahmanirrahim
Kaiwa Waccan Tsohuwar Bazawarar Abincinta, Fati ta faɗa Gami da gyatsine Fuska, Umaima ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta ɗauki ɗan Abincin ta nufi Ɗaki da shi.
Aameenat Ta na zaune ta zuba Tagumi ta na jiyo su amma ba ta da bakin cewa ƙala.
A can gefe Umaima ta ajiye Abincin Sannan ta ce "Ga shi nan in za ki ci"
rausayar da kai tayi sannan ta taso zata ɗauka seda tazo gaf da Abincin Umaima tayi maza ta ɗauke tana cewa "Ahayye ƙwalelanki ƙaramar bazawara"
"da kin zauna a gidan miji ai da kinci" Fati faɗa tana ya mutse fuska, dariya suka kwashe da ita suka tafa.
hawayen da suka cika mata Ido ne suka samu damar gangarowa fuskarta wani kallo Umaima ta watsa mata sannan taja Fati suka fice suna waƙe waƙen su na fitsara .
wani sabon kuka ta fashe dashi tana cewa "kacuceni bazan taɓa yafe maka ba azzalumi"
ganin kukan baze amfane ta ba yasa ta tashi ta nufi ɗakin wanka ruwa ta watsa ta fito ta shirya cikin doguwar riga Abaya yaluwa taji duwatsu masu sheƙi da walwali tayi kyau sosai madubi ta kalla wasu hawaye masu zafi suka fara gangarowa da sauri ta kauda kai tana tauna laɓɓan ta kafin ta tashi ta nufi ƙofa Mama ce tace " zawar zawar ce yau tafito kenan" "haba kekuwa Mama ba dole a fita neman bazawari ba"
dariya Su ka sa Kafin Mama ta ce "Allah ya raka taki gona" Aaminat ta murmusa ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar fita, a ƙofar gida ta coge ta na leƙawa, kasancewar yamma ce ga iska na kaɗawa a hankali a hankali ya sa yanayin ya yi mata daɗi sosai, yaran layin da su ke Ƙwallo ta ke kalla, a zahiri idanunta su na kansu amma a cikin ranta tunanin Yau da Goben Rayuwarta kawai ta ke yi, "Wace irin Rayuwa ce Ƴan Adam su ka ɗorawa kansu??, ba sa tunanin ita Ƙaddara ba kai kake tsarawa kanka ita ba??" tunanin da ya fi yi mata yawo kenan, ta na cikin tunanin ta ji saukar Ƙwallon a Fuskarta, ta yi baya cikin sauri gami da dafe fuskar tata, hawayen azaba ne su ka fara tseren zubowa kan kumatunta, yaran su ka yo yuuu akanta wasu suna "Don Allah ki yi haƙuri" wasu kuma su na cewa "Wallahi Walid ne ya jefo miki ita" Goge hawayen ta yi ta ɗago fuskarta ta na kallonsu, murmushi wanda ke ƙara nuna zallar haƙurinta ta yi kafin ta ce "Na haƙura" Sauran su ka Ɗauki Ball ɗin su ka koma wasa. Abdulkareem ne ya tsaya Ya na Kallonta cike da tausayawa, "Yaya Aamimat!" ya kira sunanta cikin sigar Tambaya, cikin sauri ta zuba masa idanu, sai a lokacin ma ta san ya na gurin domin kuwa a kowacce daƙiƙa tunani ne tsarin rayuwarta, "Abdulkareem sun ci gaba da wasan ba kai" ta faɗa ta na masa ɗan murmushi wanda ya ke bala'in sumar da Zinariyar Zuciyarsa "YaYa Aameenat ban ji daɗi ba, wallahi dan dai Walid Ƙaninki ne kuma ba'a shiga faɗan dangi banda haka da sai kinga yadda zan yi da shi, don ni da a raina ki gwara a mutu har liman, ban damu da rashin kunyar Yayyensa Ƴan Matan nan ba" Ita har ga Allah ya takura mata, don kuwa ganin tsaurin idonsa ta ke yi ta yadda ya ke iya zama ya na tsara mata kalamai kamar irin Namiji Ɗan 35-37 Years ɗinnan, ashe nan Bai fi 20 Years zuwa 21 22 ba, yadda ya ke iya jefa ƙwayar idonsa a cikin nata ya fi komai bata takaici, shi don bai sani bane amma ba ƙaunar ganinsa take ba. Jin ta yi shiru ya sa shi yin dariya ya ce "YaYa Aaminat haƙurinki ya na bala'in Taɓa Zuciyata!" ya ƙarasa maganar gami da ɗora ɗan yatsansa akan Ƙirjinsa saitin Zuciyar tashi, haɗa hannunta ta yi guri ɗaya alamar roƙo, cikin sassanyar muryarta ta ce "Abdulkareem don Allah ka koma ku ci gaba da ƙwallonku Me yasa sai ka dame ni ne???" "Ba na gajiya da kallonki ne" lokacin da ya yi maganar ya juya mata baya har ya ɗanyi tazara da inda take, ta saki baki ta na kallon bayansa, ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma ciki aranta ta na cewa "Ciki ba daɗi waje ba daɗi Abdulkareem ka fiya shiga rayuwata, Mara kunya da tsayayyun idanunka"
Ta na shiga Mama dake shara ta ce "A'ah Zawar me mu ka samu ne naga kin shigo baki na motsi??, ko mun yi sabon kamu ne??" Girgiza kai ta yi alamar "a'a" ta ratse ta shiga ɗaki, Mayafinta ta fizge ta jefar sannan ta shiga gyara ɗakin, daga fitarta har Su Fati sun yi abinda su ka saba, sun yi wa ɗakin batsa batsa, ta na aikin ta na Tunanin Kamal wanda ta kasa mantawa dashi, zuwa yanzu ita kanta shaida ce WATA TSIYAR A Jinin Ɗan Adam take, Ba ta taɓa tunanin haka za ta gindaya tsakanin Rayuwarta da Kamal ba.
hawayene suka fara sunturi a kuncinta sosai take sheshshekar kuka tana girgiza kai, jiri ne ya fara ɗibarta tayi saurin dafa bango ta na ambaton Allah, a daddafe ta iya ƙarasa sharar dan ta zamar mata dole, fita tayi tsakar gidan ta fara haɗa kwanuka domin wanke su ba tare da ɓata lokaci ba ta kammala wanke wanken ta shiga ɗaki ta saki labule domin bata son yin kaciɓus da samarin gidan dan kuwa basason ganinta guri tanema ta zauna tana jen carbi.
dariyar da taji ce tasa ta ɗagowa Umaima ce da ƙawarsu Nafisa da Fati suke mata dariya
"Oni ƴasu dama haka zawarci kebsa bawa ladabi"? Nafisa faɗa tana riƙe haɓarta wani murmushi Fati tayi sannan tace "to zawara se a bawa ƴan mata waje ko, ta baro gidan miji ta zo ta dami mutane"
bata musa ba ta tashi ta nufi ɗakin Umma, duk da ta san balalle ta barta ta shigar mata ɗaki ba kai a ƙasa ta ƙarasa kofar ɗakin, Umma ta watso mata harara gami da cewa "Sannu Aameena karki shigo min ɗaki, ki ɓata min, ɗakin naku aikin me yake yi??" "Su Fati ne a ciki" Umma ta ce "Ai ba ƙarfinki su ka fi ba, ni dai ba a ɗakina ba, yanzu na gama share shi" jiki a sanyaye taja ƙafafuwan ta tanufi kicin, karo taci da Umar ya shigo ta sunkuya tace "Ya Umar ina wuni" be ko kalleta ba ya wuce abin shi hakan yayi mata ciwo sosai Amma inda sabo ta saba haka ta tura ƙofar kicin ɗin ta shiga ta zauna tare da saukar da wata ajiyar zuciya yunwa takeji gashi babu da mar dafa abinci domin in mutan gidan suka sani baza taji da daɗi ba. rabonta da abinci tun karin safe ta galabaita sosai dankuwa duhu duhu take gani..
Rai a ɓace ya shiga gidan bebi ta kan kowa ba ya nufi ɗakin su "Abdulkareem"! tafaɗa cikin kwantar da kai batare da ya juyo ba ya tsaya cak bece ko mai ba a hankali ta ƙarasa inda yake ta ɗan shafi gefen fuskar shi tare da hura mai iska da bakin ta batare da ya ɗagoba yace "Ummi ina jin bacci" "maza kaje in katashi ka sanar min da wuri don rabonka da abinci ka daɗe, ka fi ganewa tsalle tsalle" be ce komai ba ya cigaba da tafiya murmushi tayi tare da bin ɗan na ta da kallo tana sa musu Albarka tare da addu'ar Allah ya ƙara haɗa mata kan su mazan da mata ya tsaresu daga sharin magauta.
ɗakin wanka ya shiga yawatsa ruwa ya na fitowa ya nufi firji gorar ruwa ya ɗauka ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya gami da dafa ƙirjinsa....
CommenT
Shere FisabilillaH
© INDO CE & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 3
Matashin ya saki baki da Ido ya na Kallon Abdul, shi kuwa ya karkaɗe kwalar rigarsa da aka riƙe ya yi gefe ya na muzurai. "Me kake nufi ne?? ka yi min laifin kuma sai ka sa a Ɗaure ni?" Abdulkareem ya ce "Ɗan Halak ka fasa, ai kasan yadda doka take, ka riga ka ɗau doka a hanunka ka ga ba ka da dalilin ƙorafi akaina tinda ka rama, Ka ja saɓa ko mu saɓeka da kanmu." Cike da taurin kai Matashin ya ƙara cewa "Wai kai da me kake taƙama ne haka?, gani ka ke kamar ƙarfinka ɗaya da ni ko??" "Ka zo a gwada Gwani mana, na gaya maka dalilin da ya sa na bari ka dokeni amma banda haka da ba za ka bar layin nan lafiya ba daga kai har Motar taka." ya na gama faɗe ya bar wajen ya nufi inda ya wurga Takalminsa, Matashin kuwa ganin an fi ƙarfinsa ya sa shi jan Motarsa su ka bar wajen. Sai a lokacin Aaminat ta samu ƙwarin guiwar matsowa kusa da shi, cike da ɓacin rai ta ce "Ka na Shaye-shaye ne Abdool?? ko kuma dama Mahaukaci ne kai ba mu sani ba??" Rikitattun idanunsa ya zuba mata kafin ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce "YaYa Aameenath!! Ba za ki Fahimce ni ba yanzu, don Allan ki shige gida ki dena tsayawa kan hanya kar a sabauta Mana Rayuwarki." idan Abdulkareem ya yi mata wani abin komai na jikinta dena aiki ya ke sai iya Zuciyarta, yau ma kamar kullum sai ta zama kamar bishiya ta saki baki ta na kallonsa, aranta kuwa irin Manyancensa ta ke tunani. Siyama takama hannunta gami da cewa "Tawo mu tafi ki bar wannan Tantirin Yaron, idan ma Nasiha ki ka yi masa ba zai fasa halinsa ba, ace rigimar da ba da kai ake ba dole sai ka shiga?" muryarsa ce ta dakatar da ita "Ke!! me kike da suna ne?? Siyama ko? to Anti Siyama dai Sabi da darajar masu daraja, ki fita idona in rufe tsakanina da ke daban tsakanina da Yarana daban tsakanina da sauran Ƴan Adam daban hallau tsakanina da YaYa Aaminat ya fi kowane tsakani da na ambata muhimmanci, Tsarin rayuwata ne a haka, ki kula da kanki." zuwa yanzu Siyama itama ta rasa bakinta hakan ya sa ta ja hannun Aaminat ƙiiiiii su ka shige ciki.
Abdulkareem ya ja tsaki kafin ya wuce gida ya na famar mita.
"Aaminat! Aaminat"!! ko kin fiso a kiraki da sunan da ki ka fi dacewa? Bazawara iye Mama ta faɗa tana bankaɗa labulan ɗakin a kwan ce take tana aikin nata na kuka dariya Mama tayi tace "eh lalle ne zawaru
samun guri kina gani dai Fati basa nan ki tashi kiyi girki kuma in kika gama ba ace ki iba ba" da kai ta amsa mata ganin bata da niyar magana yasa Mama ta juya da lukutayen kafafuwanta.
ciwo kanta yake yi kamar ze faɗi gashi babu me bata magani gas ɗin ta kunna ta ɗora girkin, ta zauna a Kicin ɗin tana tunane tunane ya rayuwar ta zata kasan ce?? shin cikin zawarci zata mutu ko kuwa za ta yi Aure? waze Aureta mutane suna gudun bazawara?, kuka ne ya kufce mata dede lokacin da Umma ta danno kai kicin ɗin sosai Umma take jin kukan har cikin ranta kamar bazata kula ta ba se kuma ta kauda kai gefe tace Aaminatu lafiya ki ke kuka haka??" ba ta kula ta ba taci gaba da gursheƙen kukan ta Umma ce ta kama hannun ta da cewa ba ki da lafiya ne?" kai ta gyaɗa mata alamar eh shuru Umma tayi tana kallon Aaminat da duk ta rame
cike da nuna damuwarta akan ta tace "kije Umar ya kai ki asibiti kinji, ke ce bakya jin magana Aamina kin kashe Auren kuma kin ƙi yin wani, darajar Ƴa mace fa Aure ne" to kawai tace mata daka haka bata ƙara cewa komai ba har Umma ta fita.
A haka ta gama girkin ta zuba a kula ta ajiye batare da taci ba ko ta ɗiba ta nufi ɗakinsu,
gado ta faɗa taja ƙaton bargo ta rufa tana rawar sanyi jitake tamkar kan ta ze faɗi sabi da tsabar ciwon da ya ke yi mata.
Zaune suke a Falon Ummi suna fira Abdulkareem ya ɗan daki kafaɗar Abdurrahim yace "kana sha" "amma kaɗan" cewar Abdulmajid dariya suka sa Abdulmajid ya hantsulo daga kan kujerar da ya kashingiɗa, yace "kai anayi muna dariya jiya naga wata Cika ta ci wanka za ta je gaiyar soɗi ta ji fenti an sa mata wannan hodar tasu fuskarta jajir amma wuyan kamar an babbaka kan rago"
wani ihu suka sa suna dariya Abdulkareem ya dafe kai yace "Jar uba jiya kuwa naga anyi yasar wata rijiya a wata unguwa da nasani na ɗebowa su Nana Fareeda su bursuna" ta zabga masa harara ta murguɗa baki
tace " A haka ake gani a ƙyasa ehhe" dariya suka yi "haka zakaga wata ƙafa karsan karsan fuska kuwa taci kwailin" Nana Fareeda ta ɗago tana kallon su tace "nide ai ba bilitin nake ba balle ku ce" Abdulmajid ya ce "waya sani ko kina ɗanawa" Abdurrahim ya ɗan dafa kai yace "gaskiya an ciki wasa"
Abdukareem kuwa kallon ta yayi ya ɗan yamutse fuska yace "wani goshinki kamar jirgi" zaro ido tayi ta shafa goshin nata taji hakan yake ko kuwa kuka tasa tana kwashe littattafan ta da gudu tayi sashin Ummi tana kuka kan Ummi tafa ɗa tana cewa Ummi kinga su Auta ko se tsokana ta suke murmusa wa ta yi tace "kamar baki san halin su ba kike musu kuka kuka?" "To ai ni tsokana ce ba na so, kuma na ce su bari sun ƙi. Ummi ta murmusa gami da rausayar da kai.
Abdulkareem ne ya miƙe gami da cewa "Ni fa Abokaina su na jirana bari in yi waje." Abdulmajid ya ce "To Abokin Abokai, sai ka shigo." bai ce komai ba ya yi hanyar fita.
A Garden ya tarar da Dadda ya na zaune shi kaɗai ya na ƴan aikace aikacensa, har ya wuce Dadda ya ce "Babban Mutum" shafa kai ya yi gami da cewa "Wai Baba sai da ka ganni??" Murmushi Dadda ya yi ba tare da ya ce komai ba, Abdulkareem ya ƙaraso ya nemi kujera ya zauna gami da cewa "Barka da Dare Dad ba ka kwanta ba??" "Lafiya lau! kwanciyar me zanyi bayan na aje ku kuma ku ba ku kwanta ba??, An sanar min wani ya mareka waye shi??" zaro ido ya yi ya na cewa "Waye ya gaya maka??" gyaran murya Dadda ya yi hakan ya sa Abdul ya yi saurin gyara zamansa domin kuwa a tsarin Daddy ba a Maido masa Tambaya ba tare da an bashi amsa ba "Wallahi Dad Glass ɗin Mota na fasa masa" a ɗan mamakance Dadda ya ce "Babban Mutum!!?? Me yasa to??" "Wata Yarinya ya ɓare ne shine nima na ɓare mar Glass ɗin ka ga mun yi ragas" "Wace yarinya ce??" "To dai ga ta nan dai Baba Ƙanwar Abokina ce, to kuma kasan ba na ɗaukar Hau. Daddy ya ce "Tooo!! Ina fatan an kaita Asibiti ita Yarinya" "Ahh!! Dadhh!! ba ina nan ba wai? kasan za a yi komai akan tsari ai" ya yi maganar cikin sigar shagwaɓa, Dadda ya ce "Tashi ka je inda za ka tafi, amma ka dinga kulawa fa" miƙewa ya yi gami da cewa "To"
Ya na fita su ka sake sabuwar hira don jiran zuwansa dama su ke yi.
Aaminat
washegari ta tashi da sauƙi dama yawan kuka ne ya haddasa mata ciwon kan, bayan ta yi bacci kuma ya lafa. Ta na zaune ta na wanke-wanke Umma Sa'a ta yi sallama, amsawa ta yi ta na murmushi ta ce "Umma Sa'a Sannu da zuwa" a yatsine ta ce "Yauwa Aaminat, wanke-wanken ne don lalacewa sai kusan Azhar ake yinsa? akwai girɗeɗiyat mace kamarki a gida amma don baƙar ƙazanta sai yanzu ake yin wanke-wanke?? ba dole ma Aure ya mutu ba" A sanyaye Aaminat ta ce "Wallahi Umma Sa'a ba hakan ake yi ba, yau ne don ba ni da lafiya ban yi da wuri ba" "Ke dalla rufen baki, ai ke yanzu rufin asirinki ki yi Aure kuma ki gyara ƙazantarki don ba mijin da zai yarda da wanke-wanken Azhar, kin ga yanzu ma IV na Auren Ƙanwarki na kawo amma ke sabi da kin sa ido a Duniya ba za ki yi Auren ba" "Ni fa Umma ba ku fahimce ni bane, wallahi gabaki ɗaya mummunar fahimta ku ka yi min, ni ban taɓa ƙin Aure ba, me zai sa ma na ƙi Auren??"
©️ INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 2
Bismillahirrahmanirrahim
Wato ya lura Duniya idan ba ka tsaya mata ba ita kwanta maka za ta yi, mutum ne mara gaskiya amma ba za ka yi magana ba sai ka zama tsinanne.
Da wannan tunanin ya kwana, washegari tin safe ya shirya Ya nufi Kasuwa.
Yau da daddare Aaminat ta na zaune ta na Azkhar Umaima ta shigo ta na dariya "Abba ya ce ki zo" ta faɗa ta na ɗan tsoshe bakinta sabi da dariyar da take yi.
"To ki ce ina zuwa" ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi, ba ta ɓata lokaci ba ta nufi ɗakin Abban bayan ta ƙara gaisheshi a karo na biyu ya ce "Maza ki shirya ki fita Allah ya kawo Manemin Aurenki, kuma kar in ji kar in gani, in ki ka sake ki ka koreshi za ki gamu da ɓacin raina, ko bakya so ki haƙura haka nan don zaman banzan naki ba shi da amfani." "To Abba" ta faɗa kanta a ƙasa. Mama ta yi wani ɗan murmushi gami da cewa "Kamar gaske" ba ta kalli inda ta ke ba ma bare ta tanka mata. Ɗakinsu ta koma ta shirya har ƙasan ranta daɗi take ji gami da Addu'ar Allah i sa mutumin kirki ne ya ce zai Aureta ta huta da tsangwamar Al'umma, Fati ce ta matso kusa da ita ta tsaya ta na ƙare mata kallo kafin ta tuntsire da dariya, "Gaskiya sai kin yi Jagira" Aaminart ta ce "Ke ni ba zan yi ba" Fati ta ja tsaki kafin ta ce "Ƙazamar Mace." Aameenat ta murmusa dan dai ita ba ta iya sa'insa ba kumama Fati ba Abokiyar yinta bace, amma ko Mama Mahaifiyar Fatin ba za ta taɓa kaita tsafta ba.
cikin sauri ta shirya ta fita, ya na zaune kan kujerun da aka aje ɗaya ta shi ɗaya ta-ta, ta ƙarasa da sallama, amsawa ya yi ya na murmushi ya ce "Zauna mana." Ta zauna sannan ta gaishe shi ta yi shiru, bai ce ba ba ta ce ba su ka shiga zaman kurame, Agogon Wayarsa ya duba ya ga dare ya fara yi gudun kar ya makara ya sa shi cewa "Sunana Salis Bara'u, an bani labarinki ne aka ce in zo mu gana ko zamu daidaita kuma ina fatan hakan." ɗan murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba ''Duk da nasan sunanki amma ina son ƙara ji daga gareki. "Aaminat" ya yi murmushi ya ha cewa "Suna me daɗi, an ce min Shekararki Ishirin da Biyar, to amma wace makaranta ki ke zuwa? nasan har yanzu anata neman ilimi ne" ya ƙarasa maganar ya na wani mugun washe baki, in ta fahimta dai ba'a gaya masa gaskiyar cewa ita Bazawara ce ba kenan! jinjina kai ta yi cike da mamakin halin ɓoye-ɓoyen nan na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 16