tazo, ranar da zamu haɗe kanmu," Fati tayi murmushi mai tafe da hawayen farin ciki, sai a lokacin Aaminat ta lura da Ahmad, suka gaisa, sallama yayi musu da niyar da yamma zai dawo ya ɗauki Fati,
Fati taji daɗi sosai, duk wunin ranar, da yamma Ahmad ya dawo ya ɗauketa suka koma gida,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare farin ciki ya wanzu,
Akwana a tashi rayuwa tana ƙara shuɗewa sanyi zafi damuna rani bazara
waiza tana ƙara juyawa,
Yau ta kasance ranar Juma'atu Babbar rana, Aaminat tana zaune a ɗakin ta, ta zabga tagumi, idon ta yayi jawur, Yarima ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa ciki-ciki, zama yayi kusa da ita, ya kama hannun ta, ya ce "mai yafaru, naga kina kuka,??" kauda kai tayi gefe, yasa hannu ya rungumota ya kwantar da kanta cikin ƙirjinsa ya ce "bana son ganinki cikin damuwa, ki sanar min maiyake damun ki," murya asarƙe ta ce "inason na ga ɗana amma har yau shiru Fati har ta haihu," murmusawa yayi cike da son kwantar mata da hankali ya ce "haba abar ƙauna ta, kar hakan ya dameki kinji, wani jinkirin alkairi ne, bamu san alkairin dake tattare da mu ba," ajiyar zuciya ta sauke cikin shagwaɓa ta ce "kullum haka kake cewa" murmushi yayi yana shafa kanta, ya ce "abinda nake so dake kidaina sa kanki adamuwa, Allah ne kaɗai yasan iyakacin alkairin da yake tare da hakan," murmushi tayi tare da cewa "amma inaso naga jarirai," ƴar dariya yayi ya ce "wani lokacin kamar yarinya haka kike, wato jarirai kike so ko" murguɗa baki tayi ta ce "eh jari-rinaye nake so" ta ƙarasa maganar tana tashi, fizgota yayi gami da cewa "ina zaki ki barni bayan ke nake jira" turɓune fuska tayi kamar gaske ta ce "nika cika ni" murmusawa yayi gami da cewa "to shike nan na ƙyale ki, kije inda zaki , daɗin ta ina da wata matar," ƴar dariya tayi ta ce "wai E'iye" "A'a ba ita ba" turɓune fuska tayi ta fara dire-diren ƙafa, shikuwa banda dariya babu abinda yake.
Misalin ƙarfe 8:00 na dare
Abdussalam, Abdurrahim Abdulmajid Abdulkereem,
Nana Kadija Nana Hauwa Nana Fareeda, Ummi Dadda, zaune
suke A babban Falo suna hira cike da jin daɗi, Ummi ta muskuta gami da cewa "Auta anya kuwa lafiyar ka ƙalau," "lafiya ta ƙalau mana mai kika gan?i" ta murmusa gami da cewa "banga komai ba kawai naga baka magana kwana biyu," Dadda ya ce "kinmanta Babban mutum kenan,?? ai ba kasafai ya fiya magana ba," Ummi ta ce "nifa ba Dadda na tambaya ba" dariya suka sa, Nana Fareeda ta ce "yau zamuga Dad da Ummu a rana" dariya sukayi cike da jin daɗi, Dadda yayi gyaran murya hakan ya tabbatar musu zaiyi muhimmiyar magana, kowa ya maida hankalin sa kan Dadda, Dad ya ce "dama magana ce akan Kadija mahaifin Omar ya sameni da maganar Auren su, to sai nace masa ya ɗan bamu lokaci, saboda inaso a haɗa Auren da naku," gaba ɗayan su suka sunkuyar da kai ƙasa, cike da jin kunya, Abdulkareem kuwa yana so yayi dariya ko guda ɗaya ce amma ya kasa, Kadija kam tunda taji inda Dad ya dosa ta miƙe tayi ɗaki, Ummi ta gyara zama kana ta ce "to Alhamdulillahi, saiku sanar da iyayan matayan naku, za'azo ayi maganar manya" Dadda ya ce "nayi magana amma kaf cikinku babu wanda yace komai," Abdulmajid ya taɓo Abdussalam, cikin raɗa ya ce "kaine Babba kai zaka fara magana," wata uwar harara ya zabga masa, Ummi ta ce "kufa muke jira kuyi magana a ina abokanan haɗin naku suke???" Abdurrahim ne yayi ta maza, ya ce "Dadda idan munyi shawara zamu faɗawa Uncle Rabi'u" ya ƙarasa maganar yana sosa ƙeya, Abdulkareem kuwa dariyar da yake dannewa ce ta samu nasarar kufce masa, ya farayi ba ƙaƙƙautawa, Dadda ma saida ya murmusa, Ummi kuwa sakin baki tayi tana kallon sa hada leƙa fuskarsa don ta tabbatar dariyar yake, sai da yayi mai isarsa sannan ya dubi, Abdussalam dake faman shafa kai ya ce "zamusha biki harda yada zani," sai yanzu Ummi ta tabbatar bai fuskanci inda zancen Dadda ya dosa ba, Abdussalam kuwa kallon sa yayi azuciyar sa yace "lallai yaro man kaza, kana taka Dadda na tashi," afili kuwa cewa yayi, "zaku yaga kantin kwari ba zani ba," Abdulkareem kuwa ko ajikin sa, sai nishaɗi yake, Dadda ya dubi Abdulkareem, ya ce "kai kuma in kayi shawarar waza kafaɗawa,??" danda nan annurinn fuskar Abdulkareem ya gushe, ya saki baki yana bin Dadda da kallo, Dad ya ce "eh dakai nake" Abdulkareem ya ce "No Dadda, ni babu Aure a tsarin rayuwa ta," Dadda ya murmusa ya ce "hakan ne yasa na nema maka Abokiyar haɗi, kuma mun gama magana da iyayen ta, ina fatan bazaka watsa mana ƙasa a ido ba," zuwa yanzu Abdul ya saduda, ya sallama Nana Fareeda ta ce "kuce zamu yaga zani" "ke rufe mana baki mara kunya ana magana kina magana," Dadda ya faɗa fuska aɗaure, Abdulkareen kuwa sai mi-mi yake da baki, Dadda ya ce "ka amince wa hakan,??" yana so ya ce shi bai amince ba amma ya kasa, Abdurrahim ya ce "tunda kukaji yayi shiru ai ya amince, kawai kunyarku yakeji, " Dadda ya ce "to Alhamdulillah Allah kaine abin godiya, addu'a sukayi kamar yadda suka saba in sukayi zaman tattaunawa, kowa yanufi makwancin sa Abdul kuwa yana so ya tambayi Dadda wa zai Aura masa amma ya kasa,
INDO & Salma Auta
[8/14, 10:55 AM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 31
Washe gari da safe Ummi tana kicin ita da Nana Kadija, Abdulkareem ya shigo da sallama, amsawa sukayi, Ummi ta ce "ɗan Ummin sa ka tashi lafiya," ƙasa yayi da kai ya ce "Ummi ina kwana" murmusawa tayi ta ce "lafiya lau ƙaramin ɗa," wata ƴar ƙaramar kujera yaja ya zauna, gami da cewa "Ummi wai kinaji kina gani Dad ya ce Aure zai min kuma ni ban san ko wace zai Aura min ba" Ummi ta murmusa kana ta ce "kayi haƙuri da komai, kaji zaka santa kuma nasan zaka sota, ka taushi zuciyar ka, kayiwa mahaifinka biyayya kar hakan ya dawo da bara bana, a baya kowa bai ji daɗin abinda ya faru ba,.." ta numfasa taci gaba da cewa "ina so kazama ɗan da ake kira ɗa, ka bawa mutane mamaki, kabi duk abinda mahaifin ka ya ce," share hawaye yayi kana ya ce "in sha Allahu zanyi biyayya wa mahaifina zan bi duk abinda ya ce," shafa gefen fiskar sa tayi, cike da kulawa ta ce "kaje wajen ƴan uwan ka" "to" ya ce sannan ya tashi,
kai tsaye yanufi ɗan ta ƙaitaccen Falon su,
tsayawa yayi shi bai shiga Falon ba shi bai juyo ba, Abdurrahim ya ce "Ango kasha ƙamshi," tsaki Abdul ya ja ya ce "to ya ranka, ko kana baƙin cikin zamu angwance tare" "kutt lallai yaro ya girma iyeee," Abdulmajid ya faɗa yana dariya, Abdussalam ya ce "karku takurawa Auta Dad ya subirbiɗa ku" dariya suka sa, Abdulkareem ya ƙaraso inda Abdussalam yake, ya kwanta ya tada kai da cinyar sa, fira suka shigayi suna dariya cike da ƙaunar junansu,
Ɓangaren Dad ma cikin kwanaki ƙalilan suka gama maganar Auren su Abdussalam, duk inda sukaje neman Aure an basu cike da gaskiya da amana, nan aka saka bikin wata biyu.
Yarima ne zaune kusa da Inni yana zuba mata tsiya iri da kala, Aaminat kuwa banda murmushi ba abinda take, tana matuƙar son ganin sharholiyar su Inni, E'iye ce tayi sallama, suka amsa, Inni ta ce "bashakka Mijin ki ya juya miki baya kina gani har wata ƙiba yake," dariya E'iye tayi gami da cewa "ai naga alama, tunda yayi sabon Aure ya sakeni" Yarima ya ce "waya ce na sakeki, ina ni ina wannan ɗanyen aikin," dariya sukayi baki ɗaya, Inni ta kalli Aaminat ta ce "ke kin yarda tsohuwa ce kishiyar ki??" Aaminat tayi ƴar dariya, ta ce "yazanyi ai tare na gansu," Yarima ya ɗan harare ta ya ce "eh tare kika ganmu ko zaki raba mu ne" "ai bazaku rabu ba" dariya sukayi cike da nishaɗi.
Akwana Atashi ba wuya agurin Allah, kwanakin da aka ɗiba na Biki sun zo, yau ta kama Asabar inda ake ta shirye shiryen ɗaurin Aure, ta ko ina gida ya cika, sai hada-hada ake yi.
Umaima ce zaune ita da Aaminat da Fati, suna hira, cike da farin ciki, Aaminat tana tayi wa Umaima ƴan faɗa da nasihohi, da dubaru na zaman Aure, Umaima kam jikinta yayi sanyi salam, in ta tuna gobe zata bar gida sai jikinta ya ƙara sanyi,
Ɓangaren gidan su Abdulkareem ma ba'a mgana gida ya cika taf, ciki kuwa hadda su Ammi da Anti Zainab, sai shagali ake,
Washagari misalin ƙarfe 11:30 Dubban mutane suka shaida ɗaurin Auren Abdussalam Aminu mai kasuwa da Iman Usman Kabeer, Abdurrahim Aminu mai kasuwa da Umaima Haruna, Abdulmajid Aminu mai kasuwa da Salma Rabi'u, Abdulkareem da Husna, Habibu, Omar Haruna da Kahdija Aminu mai kasuwa.
Alhamdulillah, Anɗaura Aure lafiya, taro ya tashi lafiya.
ana idar da sallar magrib a nufi kai kowace Amarya ɗakin ta tare da ƴan uwa da abokan arziki.
misalin tara na dare
Abdulkareem ne zaune a ɗakin Dadda, Abdulmajid ya shigo, yana cewa "Auta lokaci yana ja ka tashi mutafi," Abdul ya yamutse fuska gami da cewa "kuje mana ni sai gobe" "haba Auta yazaka ce haka ƴar fa mutane ce ka barta ita kaɗai ta kwana agida," Abdussalam ne ya shigo tare da sauran ƙannan nasa, Abdul suka sa gaba sunayi masa faɗa da nasiha, dakyar suka samu ya tashi, sukaje sukayi wa su Ummi sallama da su Dadda, saida sukayi musu faɗa sosai da rarrashi da jan hankali, sannan suka tafi, Abdul sai ɓarza kuka yake yi, su ma kansu su Abdulmajid sai da su ka yi kuka amma ba kamar Abdul ba.
kowa Abokanan sa sun rakashi gidansa.
Abdussalam, da Iman suna gabatar da sallar nafila da godiya ga Ubangiji suka haye gado domin bacci.
Abdulmajid suna zauna shida Salma sun idar da sallar nafila, ya kalli Salma dake gyan-gyaɗi cike da so da ƙauna ya ce "Salma kici abinci sannan mu kwanta na san kin gai." ni na ƙoshi" wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da cewa "To ba komai" ta tashi ta ɗane gado tare da addu'oi na bacci.
Abdurrahim da Umaima cikin kwanciyar hankali gami da so da ƙauna su ka kasance a cikin wannan dare na musamman a garesu.
a ɓangaren
Omar da Kahdija ma hakance ta kasance.
Abdulkareem yana zaune akan kujerar Falo, ya lumshe ido, yayi nisa a duniyar tunane-tunane, Husna kuma tana daga gefen sa sai sharar hawaye take, kuka take mai cin rai amma bakowa ne zai san tana kukan ba, dan kuwa kuka ne mara sauti, shikan shi Abdulkareem ɗin baisan tanayi ba,
Washe gari da safe kowa ya tashi shida Amaryar sa cikin farin ciki da annashuwa, kowa na kula da masoyinsa,
"Husna" ya kira sunan ta cikin sarƙaƙƙiyar murya, cike da ladabi ta juyo tare da risinawa, ta ce "na'am" murmusawa yayi gami da cewa "Siyama kina sona ko dole akayi miki,??" ya watso mata tambayar gami da tsira mata idanu, ƙasa tayi da kai kana ta ce "ina sonka na daɗe da sonka acikin zuciya ta kawai ina kauda kai ne, ko alokacin da kake son Aaminat lokaci lokaci nakanji ina kishin hakan, ko da yaushe addu'a nake Allah ya nuna min ranar da zan zamo mata agare ka, sai dai kash baka sona" ta ƙarasa maganar tana sharar ƙwalla, da sauri yasa hannu yana share mata hawayen cikin nutsuwa ya fara magana da cewa "ba wai bana sonki bane, nayi tunanin mahaifina ne yasa iyayen ki sukayi miki dole shiyasa, ko jiya da naji kina kuka nayi tunanin bakya sona ne" ya numfasa, kana ya ce "ina sonki Siyama ba tun yauba sai daga baya na gane ina sonki," wani murmishin farin ciki ne ya kufce mata, ta sa tafukan hannayen ta ta rufe furkar ta, wani ni'imtaccen murmushi ya sakar mata, yana kallon, kyawawan hannayen ta da sukaji lalle, ƙoƙarin tashi take taji ya ɗauke ta calak, ya nufi uwar ɗaki.
(😳kutt!!! Abdul!! Indo ta tsorata😳)
Bayan sati biyu da biki duk wani wanda ya halacci taron ya koma gida.
Ɓangaren Yarima da Aminat ma soyayya ba kama hannunn yaro,
Haka ɓangaren Abdulkareem da Siyama ko da yaushe suna manne da juna,
tsakanin Abdulkareem da Aaminat kuwa sun manta da sun taɓa wani abu wai shi soyayya, zumunci suke sosai dama Abdilkareem da Yarima Aminan juna ne Siyama da Aaminat ma tamkar ya da ƙanwa,
Ɓangaren Fati ma da Ahmad sun watsar da duk wani abu, sun kama ga Allah rayuwa suke cike da son juna, suna da ƴa guda ɗaya wadda taci sunan Aaminat ana kiranta da Meenal,
Ɓangaren Kamal ma Alhamdulillah rayuwa tayi kyau,
Umma da Mama ma sun haɗe kansu tamkar wani abu bai taɓa faruwa ba,
Alhaji Aminu mai kasuwa da Alhaji Sadiƙ, Amintar su kullum ƙara gaba take duk inda kaga ɗaya to ɗayan ma yana nan,
Ammi da Anti Zainab ma rayuwa suke tsaftatacciya.
Anti Rahina ma da su Yarima harda su Abdul kai ahaɗe yake ita ce Babba ita da Anti Maryam,
ko wane ɓangare kagan su gwanin ban sha'awa, in ba faɗa maka aikai ba bazaka ce ba dangi ɗaya bane.
Bayan shekaru bakwai,
Allah ya azurta Abubakar (Yarima) da Aaminat da ƴaƴa kyawa wa guda biyu, mace da namiji, na farkon yaci sunan Abdulkareem ƙanwar shi kuma taci sunan E'iye Rukayya ana kiran ta Nihal, Ma sha Allah, saidai muce Allah ya ƙaro zuri'a mai Albarka da kwanciyar hankali na har a bada,
Ɓan garen Abdurrahim da Umaima ma sun Haifi ɗa ɗaya Samid.
Abdulkareem da Husna (Siyama) Allah ya basu kyautar ƴaƴa biyu, ta farkon mai sunnan Ummi Kareematu tana amsa suna, Najwa,
Nabiyun kuma yaci sunan Mahaifin Siyama, Habibu, ana kiran sa, Abba,
Alhamdulillah su Ya Omar da Kahdija Allah ya basu ƴa, ɗaya taci sunan Umma Fa'izatu ana kiran ta, Neehla,
Abdussalam da Iman ma Allah ya basu kyautar ƴaƴa Biyu, ɗaya yaci sunan Dadda yana amsa, Hanif, Sai Hanifa,
Abdulmajid da Salma ma suna da ɗa ɗaya, wanda yaci sunan Uncle Rabi'u.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare sai Farinciki da ƙaunar Juna, Ziyara kam ba kama ƙafar yaro, lokaci lokaci sukan haɗa kwarya-kwaryan taro, ƴaƴan suma sunyi shaƙuwa sosai da ƴan uwan su,
SAIDAI MUCE ALLAH YA ƘARA ZUMINCI DA HAƊIN KAI BAKI ƊAYA.
Alhamdulillah Alahamdulillah
(Mun taƙaita labarin nan sabida wasu ƴan dalilai da abubuwa da su ka yi mana yawa, mu na fatan kun yi farin ciki da karantawa wannan Littafi, Allah i bamu ladan Alkairan cikinsa, kusakuren cikinsa kuma Allah i yafe mana baki ɗayanmu)
INDO&AUTA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 16