da ya wuce ganin ya jefani cikin iftila'i da Azaba, indai har don gaskiya ki ke ƙawance da ni kuma ki na tausaya min to kar na ƙara jin sunansa a bakinki bare ma wani saƙo daga gareshi." Siyama ta numfasa sannan ta juya, ya na tsaye ya zubawa ƙofar gidan ido da alamu jiran fitowarsu yake ko ita ko Aaminat, Siyama ta ce "Guda Wallahi dogon Sharaɗi Aaminat ta ja min don haka ka temaka ka fitar da ni daga cikin zancen nan ba zan iya ba." bai ce uffan ba ya kutsa kai hanyar shiga gidan Siyama ta bashi hanya ya wuce gudun kar ya mazgeta don har ga Allah tsoronsa ta ke ji.
Aaminat ta na zaune a inda Siyama ta barta ta ji sallamarsa, cikin sauri ta miƙe ta na binsa da idanu cike da mamakin ganinsa, lallai rashin kunyar tashi ta ƙara yawa, abin har ya kai ya shigarwa mutane gida, katse mata tunanin ya yi da cewa "Aaminat ki yi haƙuri kuskurena ne amma ba zan ƙara ba..." dakatar da shi ta yi cike ɓacin rai ta ce ''Ya isheka Abdulkareem!! yanzu me ka yi? ka biyoni har cikin gidan mutane ka ga an samu shaidar cewa binbininka nake yi, ka fita kafin ranka ya ɓaci" "Ai raina ya gama ɓaci Aaminat tin da har na ɓata miki naki ran." fassss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, ta na kuka ta fara cewa "Na gaya maka na tsaneka, ka nacewa rayuwata sai kace ni kaɗai ce mace a layin nan? idan da gaske ka na tausayina ne me yasa ba ka tausayawa sauran Matan? Azzalumin yaro ka sa Umma sai fushi take da ni, ka ƙara min wata jarabar yanzu ance bin maza nake duk sabi da kai, na ce ka fita daga rayuwata iya zalumcin da ka yi min ya isa haka kar ka ƙara da wani, na tsaneka na tsani ganinka ko da sunanka na tsani ji." Sai da ta gama magana sannan ya sauke hannunsa daga kan kumatunsa da ta mara, idanunsa sun kaɗa sun yi jawur sun wani ƙanƙance, Zuciyarsa bugawa take yi a fusace tamkar za ta ɓalla ƙirjinsa ta fito, "Aaminat ba ki ji ba daɗi ba da ki ka saka hannu ki ka mareni?? Meye laifina don na shigo rayuwarki? shin na taɓa nuna miki halin banza ne? me na aikata da na cancanci wannan hukuncin daga gareki Aaminat?? kenan don sun yi miki Ƙazafi sai ya zama ni na sa su ko kina zaton zan iya aikata abin da su ke tunani ne? Aaminat na gaya miki gaskiyata ba zan iya fita daga rayuwarki ba kuma na zamo Ƙaddararki ba yadda za ki yi dani." shiru ya yi sabi da wani marin da ta ƙara zabga masa, jikinta sai rawa ya ke yau ta kai maƙurar fusata, cikin rawar murya ta ce "Ƙaddarata ma ta fi ƙarfinka balle ni, mugun nufi gareka a kaina ba alkairi ba, kuma ba za ka taɓa yin nasara ba, ko ina bin maza ma banga abin da zan bi a jikinka ba ba ka isa ba ka yi kaɗan, na gaya maka ka ƙyale ni tin kafin ka kai ni maƙura ka ƙi ji, yanzu na kai ƙarshe wallahi in baka bar gidan nan ba ko me na samu sai na buga maka na illata maka rayuwa ko ma na kashe ka!!." "I LOVE YOU Aaminat komai zafin azabar da za ki yi min har Abada ina sonki, Soyayya itace manufata akanki kuma na yi ɗamara da ita ba zan fasa ba, in kin so kar ki dena marina don ba na jin zafinsa ma kan yadda nake jin zafin kalmar ƙiyayyar da ki ke tofa min, kuma ko da za ki mutu ko ki kashe ni Ina Sonki, akanki idanuna sun riga sun rufe ba abin da ba zan iya aikatawa ba ki sa wannan a tunaninki." ya na kaiwa nan ya juya ya fice, Siyama da Amiyo su ka bashi hanya.
tafiya yake amma bai san inda ya ke tsomala ƙafarsa ba sabi da ɓacin rai, ya na da haƙuri kuma ya na da Zuciya sannan ya na da zafin rai, hakan ne yasa idan ya burkice ya ke fita daga haiyacinsa, kai tsaye Bedroom ɗinsa ya nufa ya faɗa kan gado.
Aaminat kuwa jiri ne ya ɗebeta ta yi luuuu zuwa ƙasa, ta faɗa jikin bango sannan ta zame ta yi zaman ɗaɓaro, kukan da take ma ta dena ta zubawa guri ɗaya ido ita ba a sume ba ita ba a daidai ba.
Hankali tashe Siyama ta yo kanta ta na cewa "Aaminat!! lafiyarki ƙalau kuwa?? ki rufa min asiri ki tashi." jijjigata ta shiga yi ta na cewa "Aaminat! Aaminat don Allah ki tashi ai ya tafi." Wasu zafafan hawaye ne su ka samu nasarar gangarowa gefen idanunta, cikin disashshiyar murya ta ce "Siyama Abdulkareem shine ajalina, nasan dama ba zai taɓa ƙyale ni ba har sai ya gama yi min illah." Siyama ta girgiza kai ta na sharar ƙwallah ta ce "Ba haka bane Aaminat, kinsan a rayuwa kowa da irin fahimtarsa wani ba ya ganewa amma nasan wata rana zai fahimce ki zai dena shiga rayuwarki." Aaminat ta yi shiru sai kuka mara sauti da ta ke yi. Siyama ta tashi da sauri ta nufi Firji ta ɗakko mata Fiyowata duk da ba wani sanyi gareshi sosai ba, miƙa mata ta yi gami da cewa "Ki sha ruwan nan nasan Zuciyarki za ta ɗan yi sanyi, don Allah ki yi shiru ki dena kuka, wallahi ita damuwa ba yin kanta take ba sai dai in mutum ne ya so yinta, ki cire shi daga tunaninki bai isa ya yi miki abin da Allah bai yi ba, mu yi ta addu'a Allah zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, ki yarda da ni Aaminat ni fa Aminiyarki ce." ruwan ta karɓa ta sha ba da yawa ba ta ajiye sannan ta ce "Temaka min in koma gidanmu Siyama." Siyama ta tashi ta miƙo mata takalmanta ta gyara mata zaman hijab ɗinta sannan ta temaka mata zuwa gida.
©️ INDO & AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 9
Ya na kwance Kan Gado ya ɗora Filo ya rufe fuskarsa kamar me bacci, Nana Kadija ce ta shigo ta na ƙwala masa kira, "Auta kai Auta! Auta!!" tsaki ya yi yace "Ki tafi bana son takura" "babu inda za ni se ka tashi" "nace ki tashi ko?"
"haba kai kuwa wata gulma nazo in ɗan gutsura maka" "Nana ki fita kar na mareki" cikin tsiwa tace "Mari? ka daɗe baka mareni ba kawai daga magana se mari ɗan halak ka fasa, Don ka ga ma ina lallaɓaka" banza ya yi mata ya toshe kunnensa da hannun shi yana cije leɓe, masifa ta ci gaba da yi tana tafe tafe wai dole ma ya tashi ko su daku, ganin be ce komai ba yasa ta saduda ta fara tunanin ko bashi da lafiya, fita tayi da gudu ba ta daɗe ba ta dawo da magani a hannunta, ta zauna kusa da shi sannan tace "Ya Abdulkareem ga magani" ta shi ya yi ya zauna sannan ya kamo hannun ta yace "lafiya ta lau, ina son hutawa ne yau shiya sa, kinji zuwa anjima in na tashi se mu dakun"
murguɗa baki tayi tace "oho de ruwa ya daki babban zakara" murmusawa yayi gami da cewa "to koma mene ki je zuwa anjima ma yi shi" jiki a sanyaye ta ce "Amma Ya Audu gaskiya fa ko lafiyarka ƙalau akwai abin da ke damunka, ranar nan su YaYa Abdulmajid sun tambaya na hau bayanka na yi ɗare-ɗare amma yanzu na ga abin ya yi yawa wallahi." "Na rantse da Allah Kadija kawaici kawai na ke miki, idan ki ka ji Biyar ɗina a kumatunki inaga za ki fi fahimta ta, na ce miki ba na son hayaniya. ba ta ce komai ba ta fita saƙol jikinta ya yi matuƙar sanyi dan ba haka ta saba ganin shi ba,
kai tsaye ta nufi ɗakinsu tana tafiya tana tunane tunane.
Aaminat
ta yi kukan har ta gaji sai dai na zuci, sabi da bakin ciki da damuwa Zuciyarta a koda yaushe zafi ta ke yi, don kuwa kalaman Abdul sunyi matuƙar tsaya mata Aaminat I LOVE YOU in ta tuna wannan furucin se ta ji kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu, zuwa yanzu ji take duk duniya babu wanda ta tsana sai su biyu Daga Kamal sai shi, a cewarta Kamal ne ya yi mata silar da har Ƙanin Ƙaninta ya dubi tsabar idon ya ke gaya mata Kalmar So.
kuka ne ya kufce mata yayin da take riƙe da carbi tana Azkhar, ta shiga rera shi tana roƙon Allah i yanke mata wahala ta huta koda sauƙinta shine Mutuwarta ta zaɓi hakan"
Fati ce ta kalleta ta tuntsire da dariya ta ce "Haba Zawar dariya ma wahala ce bare kuka, za ki gaji ki dena ne" dariya suka sa ita da Umaima kafin Umaima ta ƙwace carbin gami da cewa, "Dalla tashi ki ɗora mana girki kin wani zauna kamar wata Malama se jan carbin munafurci ki ke yi" Aaminat ta kalleta cikin muryar kuka ta ce "meyasa kike min haka?? karki manta ni fa yayarki ce Uwa ɗaya Uba ɗaya ko wani ya gujeni sabi da ƙaddara ai ke be kamata ki gujeni ba, kuma ƙaddara ta na kan kowa!!"
shewa suka saki kafin Fati tace "ai muda ƙaddara se kallo daga nesa dan kuwa zaran ba Kalar Yadin bane na gaba yayi gaba wallahi mu ai babu lissafin ƙaddara cikin rayuwar mu" Umaima ta ce "Wallahi ni banga wata ƙaddara a tare da ke ba, kashe Aure ki ka yi don ki dinga tara samari masu kuɗi kuma sai aka yi sa'a ba a gamu ba, in da ba son zawarcin ki ke ba ai da kin yarda da waɗanda Abba ya ke nemo miki." wani kallo Fati tayi mata na kinyi asara gami da taɓe baki ta ce "Wallahi fa kin yi gaskiya Umai." wani kukan ta saki sabo tana da nasanin zuwanta duniya.
jin Sallamar ya Umar ce tasa su tashi dan kuwa yana jin motsin su ze fara faɗa meyasa ba suje makaranta ba,
fitarsu ta bata damar ci gaba da kuka me taɓa zuciyar me saurare.
Tin tana hawaye har sun ƙafe idanuwanta duk sun kumbura sunyi jawur sai ya ji su ke mata kamar an watsa musu dakakken barkono, ga matsanan cin ciwon kai.
Su na zazzaune kan Babban Carpet wanda suke shimfiɗawa su zauna, Salim ya lura da tunda suka zauna hankalin Guda baya jikinsa sai ya ji shima jikinsa ya yi sanyi, "Ɗan Ummi ya dai?? tunanin me kake kai da ka Tara an Tara maka, kuma tunanin me zakayi??" murmusawa yayi ba tare da yace komai ba ya bisu da kallo.
Cokali ne ya ɗan matso kusa da shi sannan yace "wato ainahin me yake faruwa ne kwana biyu ka dena walwala ɗan abincin da kake fito mana da shi ba kullum ba yanzu" "kai de kamar maye haka kake kaje kaci na gidanku mana" Jabir ya faɗa yana tallewa Haisam ƙeya ganin Abdulkareem ba shi da niyar yin magana ya sa suka fara musu wasu suce bashi da lafiya wasu suce muskilan cin shi ne ya motsa, jin hayaniyar ta su tayi yawa yasa ya tashi yana cewa "ni zan shiga cikin gida in na fito to in kuma se gobe to" gabaki ɗaya suka tsaya da surutun cakkk suka bishi da ido suna mamakin canzawar Master ɗin su lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki Haisam yace "wai laifi mu ka yi maka ne?? kwana biyu kadena zama cikin mu kullum kana gida ko baka da lafiya ne??" gargiza musu kai yayi alamar lafiyar shi lau,
"to se munji ka nima gida zan tafi" Jabir ya faɗa cike da damuwa, marmushin yaƙe yayi ya ɗaga gira ɗaya sannan ya juya, Walid ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Guda ko de rabuwa zakayi ne damu??" cakkk ya tsaya shi bai tafi ba shi ba dawo ba kuma bai bashi amsa ba, Walid ya ƙaraso inda yake, ya na shirin yin magana Abdul ya riga shi, ya na murmushin karfin hali yace "Ba haka bane Ɗannan me ya yi zafi da zan rabu da ku bayan ku sashi ne na rayuwata? wai ni kam ina yayarka ne??" Walid ya ɗan ya mutse fuska kafin yace " tana gida bata da lafiya, kuka ne aikinta kullum, duk ta bi ta damu ni bansan me akai mata ba, gashi su kuma ƴan gidanmu kowa harkar gabansa ya ke yi an rasa me kaita Asibiti ma ba wanda ya damu da ita, ni wallahi duk jikina ya yi sanyi bansan me ta yi musu me tsanani haka ba, wai ko Abba babu ruwansa da tambayar ya ta kwana ya ta tashi" rassss gaban Abdukareem ya faɗi har ƙasa, ya wararo ido ya na kallon Walid, ci gaba ya yi da cewa '' Wai kowa ya zare hannushi daga kanta, ni fa Da na zata laifi ta yi musu ashe kawai sabi da Ta rabu da Mijinta ne, ƙila ma ba ta da laifin komai." cikin dauriya Abdulkareem yace "to kace ina mata sannu kaji? to yanzu idan ka ce za ka rakata wajen likita ba za ta yarda ba?" Walid ya ce "Hmm! ba za ta yarda da ni ba don na riga na ɓata wasana tin farko sabi da rashin kunyar da nake mata, kuma gani na yi su Umaima na yi, ni kuma na zata abin kirki ne, tin daga ranar da ka yi min magana akanta na gane kuskurena." Abdulkareem ya ce "Okay Ƙyaleta kawai, Allah i bata lafiya." yana gama faɗin haka ya ci gaba da tafiya zuwa cikin gida.
kai tsaye Babban Falo ya nufa ya tarar da ƴan uwansa su na hira ba abin da ya yi tsalle ya tsinka musu mari, ɗan ƙaramin tsaki yayi ya nemi guri ya zauna kusa da Ummi batare da yace musu komai ba, "Ya Audu ko sallama babu??" Nana Kadija ta faɗa cikin sigar tsokana, sai a lokacin ya tuna da be yi sallama ba, ya sunkuyar da kai yana wasa da zobukan yatsunshi "Ya Audu magana fa nake"
harara ya watsa mata sannan yace "Dije kar ki takura min" "ni kake cewa Dije?" "an faɗa Dijen gala Ƴar Gona" turje turje ta fara yi tana cewa "Ummi ki na ji de yana cemin Dije kin ƙi ki hana shi" murmusawa Ummi tayi kafin tace "ke kuma ki ka ce masa Audu banyi miki magana ba se shi sabi da kece Zinariya ko??" Abdulmajid ya ce " Yaran nan in ki ka bi ta tasu Ummi sai bakinki ya yi ciwo, Ko Nana Fareeda da Nana Hauwa'u da suke ƙananu ba sa faɗan nan da su ke yi, kuma na lura rashin duka ne ya ke damunsu, yauwa kai tin ɗazu mu ke jiran shigowarka mu ci Abinci kazo ka tsaya cecekuce da wannan me ƙaton kan" murmushin baƙin ciki da ta kaici yayi sannan yace "wa ya ce ku tsaya jirana?? ni na ƙoshi" sakin baki sukayi suna kallonsa kafin Abdussalam ya ce "Ƙalubale Gareka Ɗan Uwa, Nana Kadija ta ce ruwa kawai kake ta kurɓa sai Juice a duk tsawon yau Yaro in za ka zauna ka ci Abinci ka zauna don in ka dawo ƙashi ba ruwan wani." ya ɗan ɗangale kafaɗa alamar ko a jikinsa.
Ummi ta ɗan muskuta gami da cewa "haba Autana ba'a horon yunwa ka ci Abinci ka ji Babban Mutum!" tingira kai ya yi a shagwaɓe yace "nifa bana son cin Abincin sabi da Aam" ɗiffff yayi yana muzurai, a ran shi yace taɓ yau na kusa zunguro sama da kara. Abdussalam ne ya katse masa tunani da cewa "sabi da me ka ce??"
Abdurrahim ya ce "Tabbas nima na ji zai faɗi wani abu ya fasa, ni dai nasan da abin da ya ke ɓoyewa, wallahi ku tashi mu yiwa Yaron nan Cali-cali yau ya faɗa mana menene a ransa ya ke sa shi rama ta wuya." Ummi tace "kun samin ɗa gaba ku ƙyale shi ni zanji me yasa ya ƙin cin Abincin" rarrashinsa suka shiga yi da ƙyar ya ce zai ci Nana Kadija tace "nasan yadda zamuyi maka se kayi lauma uku se muyi ɗaya" tafawa Nana Hauwa'u sukayi da Abdurrahim Nana Farida tace "kanki yana kawo wuta kamar fulogi" haka suka sashi gaba in yayi Cokali uku se suyi ɗaya tun yana ƙoƙarin ci har ya gaji ya ɓare baki ya fara kuka wai so suke su kashe shi cin yayi yawa. Ummi ta galla masa harara taɗan hade fuska tace zauna se Abincin ya ƙare zaka tashi" komawa yayi ya zauna ya ci gaba da kuka Abdulmajid ya ɗan yi dariya yace "taɓ Jariririnmu babu lafiya gidan ya koma kamar gidan mutuwa an dena dariya" Abdussalam ya ce "Ni fa duk ba wannan ba." su ka haɗa baki wajen cewa "To me????"
© INDO tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 10
Bismillahirrahmanirrahim
"Maganar gaskiya ba zuba masa ido za mu yi ba don ba shi da lafiya, ga yadda ya ke yiwa mutane kuka kamar an tsoma shi a wuta, kun manta tsabar kwainane da Manyance irin nashi ne? gaskiya ya kamata mu kai shi wajen likita ko da likitan Mahaukata ne" Abdussalam ya yi magana cike da son nuna gaskiyarsa, Nana Fareeda ta ce "Kuma wallahi haka ne YaYa Abdussalam." Abdulmajid ya ce "Ni gardama ce ba na so shi ya sa na zaɓi na zuba masa ido tinda haka ya ce, ko ka manta ya ce mu zuba masa ido kawai?" Abdurrahim ya ce "To ai amfanin hankali kenan don ya faɗa tinda mu da hankalinmu ai ba biye masa za mu yi ba." Ummi ta ce "Gaskiya nima abin ya dame ni sosai, kuma ya na yawan zazzaɓi yanzu, amma sabi da kafiya Magani ko Ɓalli ya ƙi sha." Goge hawayen ya fara yi ya na cewa "Na dena zazzaɓin kuma dama lafiyata ƙalau, da fa hankalina ta ya zan zauna da cuta." Abdussalam ya ce "Da sauƙi dai hankalin naka don in da da shi da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, kukan nan da kake yi ma ba dalili ya na ɗaya daga cikin Ƙarancin hankalin." ya ja numfashi ya busar kafin ya ce "Ka na nufin Mahaukaci ne ni??" "Ahh ba wai ina nufin Mahaukacin gaske ba, hauka irin na Ƙuruciya nake nufi don ya na da yawa a tare da kai. Abdulmajid ya haɗe fuska ba alamun wasa ya ce "Abdulkareem ba na son shirme ka tashi mu je ka ga Likita, idan kuma ba haka ba ranka zai ɓaci ka san ba na son Hau." "To ai dama ba cewa na yi ba zan je ba" Abdulmajid ya miƙe tare da cewa "Abdussalam Ɗakko Mukullin Mota kai kuma Abdurrahim ka tawo min da Abdulkareem." Abdulkareem ya miƙe ya na cewa "Ni ba sai an tafi da ni ba zan biyoka." Abdulmajid ya murmusa ya na tunanin wai a hakan ya ce ba Ƙuruciya a tare da shi ya na magana ya na kuka kamar wani ɗan shekara Uku.
Da su ka dawo bai saurari kowa ba ya wuce Bedroom don kuwa duk haushinsu ya ke ji kamar ya bubbugesu.
Dadda ya dubesu a tsanake sannan ya ce "Na shigo gida na tarar duk bakwa nan ance Babban Mutum ba lafiya." Abdulmajid ya ce "Eh Dadda yanzu mu ka dawo ai." "Me Likita ya ce game da shi?" Abdulmajid ya zauna sannan ya ce "Wallahi Dadda abin akwai ɗaure kai wai damuwa ce ta fara yi masa yawa har Ƙunci ya harba masa zazzaɓe-zazzaɓe.'" Dadda ya zare Glass ɗin idonsa cike da mamaki ya ce "To fa? ikon Allah kenan, Babban Mutum da wace irin damuwa haka?" Abdussalam ya ce "Kullum sai mun tambaye shi me ya ke damunsa amma ba amsa sai dai ya ce ba komai, kuma ni banga abin da akai masa ba." Abdurrahim ya ce "Ko dai a cikin Yaran da ya ke Abota da su matsalar take??" sai a lokacin Ummi ta ce "Kai a'a gaskiya Yaran nan duk ba wanda zai sa Abdul damuwa haka sai dai wani abin, zurfin ciki gareshi ne shi yasa, mu taya shi da Addu'a kawai." Dadda ya Jinjina kai ba tare da ya ce komai ba.
Yau Aaminat ta tashi da zazzaɓi me zafi da ciwon kai, yau ko aikace-aikacen tsakar gida ta kasa yi sai dai ta kwanta in ta gaji ta tashi, fatan ta ɗaya Allah i jefo wanda zai temaka mata ko da ƙwayar Magani ne.
Tana cikin wannan halin Siyama ta yi sallama bayan ta gaida Umma ta shige ɗakinsu Aaminat, da sauri ta ƙarasa kanta ta na cewa "Aaminat me ya faru ne? ba dai zazzaɓin ki ke ba naga jikinki na kakkarwa." A wahalce ta ce "Siyama ba ni da lafiya ki temaka ki karɓo min maganin zazzaɓi in Anti ta na da shi." Siyama ta ce "Ai wannan Rashin lafiya taki ta fi ƙarfin zama, a tsaitsaye ta ke ƙarar dake gashi yanzu har ta kaiki ƙasa, ba zan iya jura ba ki tashi mu je Asibiti." "Ba zan je ko ina ba Siyama, ba na son fita sabi da ina tsoron na yi gamo da wannan mummunan Yaron. "O'o Allah Me Baiwa, ke kuma ki na wannan zazzaɓin amma tunaninki ma kar ki fita ki ga Abdulkareem to in kin ganshi zai ɗauki ranki ne??, wannan fa banzan tunani ne, me yasa ki ke da gardama ne? gaskiya ki tashi mu je yanzu za mu dawo, nan fa ƙaramin Asibitin nan na tsallake za mu je ba wai nesa ba. "To zazzaɓi fa nake ta ya zan iya tafiya? ni dai ki ƙyale ni in ba za ki ban maganin ba. Siyama ta miƙe ta kwance ɗankwalinta ta fita ta jiƙo shi sharaf sannan ta dawo, Aaminat ta miƙawa gami da cewa "Karɓi ki shashshafawa jikinki zazzaɓin zai ragu in sha Allahu sai mu je Asibitin." ba ta yi musu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 16