mamaki ya cika kowa da yake gurin musamman Dadda da bai taɓa zaton ɗan da yake wa kallon me hankali zai iya yin hakan ba.
Cikin sigar tambaya ya ce "Aure!??"
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Abdulmajeed ya ce "ƙwarai kuwa, yanzu na ji suna zanzen shi da DR Abubakar ba su san ina gurin ba, ga shi nan sai ya yi muku bayanin wadda zai aura kuma ku shirya don kuwa uban ƴar ya ce wata ɗaya ya bashi, fitinannen yaro kai! ko ina shi ina aure?" Dadda ya ce "Sake shi to" sakin nasa ya yi Abdulkareem ya gyara rigarsa Zuciyarsa na tsalle, ba tare da tangarɗa ba ya ce "Aaminat nake so ta layin nan Ƴar gidan Alhaji Shu'aibu." Ummi da su Farida su ka sanya salati da sallallami, Abdussalam da Abdurrahim kuwa sai sakin baki su ka yi suna kallonsa.
Dadda ya ce "Na san Baban nata amma ban santa ba." cikin ɓacin rai Ummi ta ce "Wata Yarinya ce ba budurwa ba ma bazawara, yanzu sabi da Allah Abdulkareem aikin da za ka janyo mana kenan? ka na nufin ka watsar da duk tarbiyar da muka baka ne ko me?" cike da takaici ya ce "Ki yi haƙuri Ummi amma sam wannan ba rashin tarbiya bane, Ita ma fa macece kuma wadda take lokacinta, don ita bazawara ce ba ya na nufin shikenan ba ta da galihu ba, Daddy don Allah kar ka hanani abin da nake so wallahi ni ita nake so kuma ina son aurenta a cikin wata ɗayan da babanta ya ce." Dadda ya ninke Jaridar hannunsa ya zare Tabarau ɗinsa ya zubawa Abdul ido har na ɗan lokaci sannan ya jinjina kai gami da cewa "Danƙari, Babban Mutum ni ba zan zauna ina jayayya ko sa'insa da kai ba, kawai ban amince ka yi aure yanzu ba ko Bazawara ko Yarinya Ƴar goye ma duk ban amince ba, kai da Aure sai nan da shekaru Goma lokacin ka gama kafa kanka kasan inda ke maka ciwo, idan kuma za ta jiraka hazawasalam ni dai na gama maganata."
Cikin fitar haiyaci Abdul ya yi saurin durƙusawa kan guiwarsa hankalinsa a matuƙar tashe ya fara magana ba tare da tunanin cewa Mahaifinsa ne a gabansa ba "Dadda ni fa Namiji ne kuma namiji ba ya kaɗan, me zan buƙata a rayuwa bayan wanda Allah ya bani?, ya bani hankali da nutsuwa kai da kanka babban Mutum kake kirana, sannan ina kasuwanci ina da shaguna a kasuwa bayan Asibitin da Ka Mallaka min, ina da ilimi kuma ko da na aureta ban girmin ƙarin ilimi ba, Dadda ka temaka ka canja min wani Punishment wannan ya yi min tsauri hankalina ba zai iya ɗauka ba." sai a lokacin Abdurrahim ya ce "Abdulkareem anya kuwa ba ka fara shan wani abu ba? Daddan ya na faɗa ka na maida martani sabi da ka rasa hankalinka?" ya girgiza kai kafin ya ce "Ka kirani Mahaukacin dai amma Please kar ka kuma ce min ina shaye-shaye, Dadda komai ka ce in yi zan yi amma don Allah karka hanani Aurenta, itama Aaminat abar a tausaya mata ce ku temaka ku bani dama na inganta rayuwarta." Dadda ya miƙe rai ɓace ya ce "Tabbas hankalinka ya gushe ɗin ne shi yasa kake tunanin ma zan canja maganata, ka fi kowa sanin ni kaifi ɗaya ne mutum me tsatstsauram ra'ayi da kuma magana ɗaya, abin da zai yuwu shi nake amincewa da shi ba wanda ba zai yuwu ba, kar ka ƙara tinkara ta da wannan maganar idan kuma ka yi hakan fushina ya tabbata gareka; don muna nuna maka so ba shi yake nufin za mu barka ka dinga katoɓara iya son ranka ba." ya na kaiwa nan ya gangara sashinsa cike da fushi da takaicin haukan Abdulkareem, don a cewarsa hauka ne kawai.
Ummi kuwa da abin duniya ya isheta sai ta fashe da kuka itama ta tashi ta yi nata ɓangaren.
Su Abdurrahim su ka tasa Abdul gaba su na yi masa faɗa da nasihohi, sai dai a nashi ɓangarem in ta shiga ta kunnen hagu ne sai ta fito ta dama.
©INDO tare da SALMA AUTA
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION
Shafi 19
Sai da suka gaji da yi sannan kowanne ya saɓe ya bar Abdul a gurin.
Bedroom ɗinsa ya nufa zuciyarsa cike da baƙin ciki da takaici, gabaki ɗaya haushin kowa yake ji musamman su Abdulmajeed masu bakin yiwa mutum faɗa.
Haka ya kwana cikin takaici ko baccin kirki ya kasa yi sai juye-juye yake yi.
a ɓangaren Abubakar (Yarima) ma haka ya kwana ba kwanciyar hankali, baccin sai ɓarawo.
Aaminat
ita ma haka ta kwana sai kici-kici take ta kasa baccin daga ta kwanta sai ta tashi, sai ma ta ga daren ya yi mata tsayi da yawa sabi da ta ƙagara garin ya waye.
Washe gari kuwa tin safe Abba ya na fita itama ta fita zuwa gidan su Siyama.
Bayan ta gaida Aunty ta wuce ɗakin Siyama
Ta na zaune bakin katifarta ta zuba tagumi da hannayenta duka biyu.
Aaminat ta ƙarasa ta zauna jiki a sanyaye ta ce "Siyama kin ji abin da ya faru dani? ashe wai Abdulkareem ne ya turo min Yarima."
Siyama ta ja numfashi kafin ta ce "Hakan ba baƙo bane a gurina domin kuwa nima da sa hannuna a ciki, Abdul ne ya roƙe ni na yi masa wannan Alfarmar, a lokacin da na ce dole sai na kai ki Asibitin nan ai shi ne ya sa ni, ina ganin fa kar ki tsaya tunanin wani abu daban Aaminat, Abdulkareem ya na sonki tsakaninsa ga Allah ba don wani abu ba."
jikinta ya ƙara yin sanyi salam ta yi shiru ta ja tunani, sun daɗe a zaune curko-curko ba me cewa ƙala sannan Aaminat ta ce "Gaskiya in haka ne ban kyauta masa ba, duk abin da yake yi don ya fitar da ni daga cikin damuwa ne, yadda nake ɗauka duk ba haka yake a zahiri ba."
Siyama ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ta ce "Na godewa Allah da ya baki ikon fahimta, yanzu abin da za ki yi kawai ki ba shi haƙuri kuma ki amince da soyayyarsa idan ba ki yi haka ba kuwa ni ba ruwana, ba gori ba ko me zai faru dake nan gaba ba zan ƙara damun kaina ba."
Aaminat ta ce "To ni ta ya zan ba shi haƙuri??"
Siyama ta ce "Ba ni wayarki in sa miki lambarsa ki kira shi, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba."
Ba musu ta miƙa mata wayar ta karɓa ta jera mata lambobin
sannan ta bata wayar ta.
Karɓa ta yi ta tashi jiki ba ƙwari ta koma gida, tin da ta zauna take tunanin kiran nashi sai dai in ta kira ba ta san ta ina za ta fara ba.
Abdulkareem
Sai 10:00am ya fito lokacin duk yayyensa su Abdussalam sun bar gida su Khadija ma su na makaranta sai Ummi ita kaɗai a Falo ta na zaune kamar korarriya, ita ba magana ba ita ba aiki ba ta na dai zaune kurum sai aikin tunani take.
Kusa da ita ya zauna ya gaisheta ta amsa masa ƙasa-ƙasa, ganin ta na ci masa magani ya sa shi tambayarta abin da ya faru.
Cikin takaici ta ce "Abin da za ka ce kenan? har ka manta tayar mana da hankalin da ka yi jiya?"
Ya rausayar da kai kafin ya ce "Meye abin tashin hankali Ummi? daga na yi zancen Aure ba fa ƙaramin yaro ba ne ni, i'm twenty something years old fa kuma ina da komai da zan iya riƙe mace."
Wata harara Ummi ta zabga masa wadda ta sa shi raina kansa, cikin matuƙar takaici ta ce "Abdulkareem shiga taitayinka, mu ba sa'o'in wasanka bane, mu za ka zo wa da rashin hankali cikin gida? da ƙuruciyarka ka ɓata ta ta hanyar Auren Bazawara?, to bari ka ji ni ko 15 years indai budurwa za ka aura daidai kai ba zan damu ba, amma ina raye ba ka isa ka auri budurwar da ta girmeka ba ma bare wata Bazawara da Allah ne kaɗai ya san tsiyar da ta tufka wancan mijin nata ya rabu da ita, ni dai ba a zuriya ta ba in za ka yayewa kanka ka yaye tin kafin dare ya yi maka."
Ya buɗe baki zaiyi magana ta dakatar da shi da cewa "Na gama maganata, ba na son jin komai, na riga na faɗa ban amince ba kuma idan ka yi ko bayan raina ban yafe ba, tinda na lura kai zuma ne sai da wuta, kar ka ji irin baƙin cikin da na kwana da shi jiya na furtawa da ka yi cewar za ka auri bazawara, wannan ai zubda kima da mutuci ne, to ni ba na son jin komai a bakinka indai ba cewa za ka yi ka janye ba, kuma ni me iya fita shirginka ce indai ka ce za ka bujire mana."
Sakkototo ya saki baki ya na kallon Ummin ta shi, a ransa ya na tsaka da mamakinta bai taɓa zaton za ta iya yin abin da ta aikata ba, kenan itama ta na ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙyamar Bazawara? to wai me yasa hakan?
Tambayoyi ne suke masa yawo a tunaninsa sai dai ba shi da amsarsu ba shi da mai bashi don haka ya tashi ya zabari mota ya bar gidan.
*Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta*
*Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.*
*HALY-JASHERU venture's*
*munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.*
*prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA*
Ya na cikin tafiya ya ji wayarsa ta fara tsuwwa, ya duba ga mamakinsa sai ya ga lambar Aaminat, da sauri ya ɗaga tare da ƙoƙarin tsayar da motar a gefen titi.
Sallama ta yi ya amsa cikin sauri sannan ya ci gaba da tambayar lafiyarta.
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Na kiraka ne don na baka haƙuri akan duk abin da na yi maka, ina fatan za ka manta da komai."
daga jin muryarta za ka san ta na cikin sanyin jiki gami da tsoro tsoro.
Abdulkareem ya saki murmushin farin ciki gami da cewa "Kullum cikin manta abin da ki ka yi min na rashin daɗi nake, kuma kullum farin cikin da ki ka sa ni nake tunawa na tin kafin ma na furta miki kalmar so, ina fatan nima kin yafe min akan turo miki wani da na yi, bayan haka kuma ina so ki faɗa da bakinki cewar yanzu kin yarda ni masoyinki ne ko da kuwa ke bakya sona."
Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta shirya ba, "Eh na amince kai masoyina ne, kuma ni ba ka yi min laifin komai ba."
Kusan tare su ka sauke zazzafar ajiyar Zuciya, Abdul ya lumshe ido ya na godewa Allah.
Jin ta ce "Sai anjima" ya sa shi sauri cewa "Tsaya mana, daga kira kuma sai ki ce sai anjima? nifa na fita ne amma sai na ji kamar in dawo, ko kina wani aikin ne?" zaro ido ta yi ta ce "Ahh gaskiya kar ka dawo."
Ya yi murmushi gami da cewa "Me yasa?" ƴan kame-kame ta fara yi masa don haka ya ce "Ba komai zuwa dare dai za ka ganni in Allah ya yarda, ki tanadar min kyakkyawan murmushin nan naki ma kawai ya ishe ni."
Ba ta iya cewa komai ba sabi da wata ƴar kunya da ta rufeta, don kuwa ta na sane da cewa shi ɗin Ƙaninta ne, a ganinta abin kunya ne ta saki jiki ta yi soyayya da shi.
Shi kuwa hakan bai dameshi ba.
Tuna baya
Lokacin da Abdulkareem ya yi rashin lafiya su Abdulmajeed su ka kai shi Asibiti da daddare.
sai da su ka yi waya da DR Yarima ya sanar musu ya na asibitin Ameenu Abdullah sannan su ka nufi can don dama shi ne Family Dr ɗinsu.
Bayan ya gama bincikar lafiyarsa ya ce su bi shi Office ɗinsa.
Hakan su ka yi nan yake musu bayanin damuwa ce ta sako Abdulkareem ɗin gaba, jin hakan ya tsuma musu zuciyarsu don ba su ga wani abin damuwa a Duniyar Abdulkareem ba.
Dr Yarima ya miƙe gami da cewa "Kai ƙaramin mai gida zo mu je in gana da kai."
Abdulkareem ya tashi ya na ƙasa-ƙasa da ido don ya lura fa kallon tuhumar da suke jefa masa.
Bayan sun fita sarari inda ba mutane Yarima ya tsaya ya na kallon Abdul sannan ya ce "Kai ya ne?" Abdul ya bashi hannu suka tafa ya na cewa "Likita Bokan Turai, ba ka so a Mutu ba ka so a Zauna Lafiya." Yarima ya yi dariya ya na cewa "Ai ku ne ku ka ɗaure mana abin, kai wai meye a ciki ne? faɗa min gaskiya me ya sa ka jawowa kanka ƙunci?? soyayya ka fara yi ko?"
Abdul ya ce "Malam ina ruwanka ba na son sa ido it's my life."
Yarima ya dara kafin ya ce "Ba ruwana amma da ruwan Alhaji Mai kasuwa, zan iya gaya masa gaskiya har ma na ƙara da duk abin da na ga dama."
Abdulkareem ya shafi ƙeyarsa gami da cewa "Ka matsa da yawa; kuma hakane wallahi soyayya na faɗa, amma ba wannan ce matsalar ba Yarinyar ta ƙi yarda da ni ne, ni kuma ina baƙin cikin ganinta cikin damuwa ina so na kawar da wannan tsarin a rayuwarta amma ita duk ta ƙi yarda, yanzu haka ba ta da lafiya amma ta ƙi yarda da temako na, amma yanzu komai ya zo da sauƙi kai ne za ka temake ni."
Yarima ya zaro ido ba tare da ya bi ta kan sauran zancen ba ya ce "Ta ya? kai da masoyiyarka kuma ni meye nawa a ciki?"
Abdul ya ce "Ta na da gardama fiye da kima don haka nake so ka je mata a sigar likita daga nan sai ka fara jan hankalinta, har ku fara soyayya, amma fa ka bi a hankali idan ka kuskure min sai an ji ni da kai har Kotun Ƙoli."
Yarima da mamaki ya cika shi ya ce "Kai, gaskya yaro yaro ne, ni ba zan iya wannan kasassaɓar ba, ka dai nemo wata mafitar." Abdulkareem ya ce "Ba ni da wata mafita sai kai, ka fahimta mana, ni fa wallahi bala'in tausayinta nake ji, ba wai na damu akan dole ta so ni bane, kawai ina sonta ne don na sanya ta farin ciki na gaji da ganinta cikin damuwa da wani mugun hali na rayuwa, daga tausayinta ma na ji gaba ɗaya ita nake son Aura, don Allah ka yi min alfarmar nan Dr in ba da haka ba za ta iya rasa ranta a banza domin ta fi ni faɗawa rashin lafiya."
Yarima ya yi shiru ya na nazari har na wani lokaci kafin ya ja numfashi, ba tare da hakan ya kwanta masa a rai ba ya amince don kawai Abdul ɗin ya nemi temakonsa ba zai iya ƙin yi masa ba.
Abdul ya yi matuƙar farin ciki da amincewar Yariman, su ka rabu da haka da cewar za su ƙarasa plan ɗin ta waya.
Hakan su ka yi Abdul ya zauna ya tsara Siyama da Yarima kuma su ka aiwatar kamar gaske.
Ci gaban labari
kamar yadda ya ce za ta ganshi da daddare bai yi ƙasa a guiwa ba ya je, ta sha surutu sai dai ta kasa sakin jiki da shi.
Abdul kuwa samun kanta ya sa ya manta da rigimar cikin gidansu, har sai da ya ko ya ga suna yi masa gani-gani sannan ya tuna akwai ƙura.
Tin daga wannan lokaci Abdulkareem da Aaminat su ka haɗe, ya na gwada mata soyayya iya iyawarsa, a nata ɓangaren kuwa tunanin halin da Yarima yake ciki take yi, haka kawai ta ji duk ta damu da shi, gashi ta na tsoron kiransa ya gayawa Abdul ta kira shi hakan ya jawo mata matsala don haka ta haƙura ta ci gaba da tunaninsa ba dare ba rana.
a ɓangaren Yarima kuwa tin daga ranar da ya rabu da Aaminat duk ya rasa nutsuwarsa, ba dare ba rana ba aiki ba rashin a kowace daƙiƙa ita yake tunani, a gefe guda kuwa yayarsa Raheena da Ammee sun saka shi gaba da tsangwama, ga sharri iri-iri da Raheena ta ke binsa da shi don kuwa har cikin ranta ta tsane shi.
©️INDO tare da AUTAR JARUMAI
[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT*
(Bazawara)
Littafin Haɗaka ne💪🏾
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER'S
Shafi 20
"salamu alaikum"
Abi yayi sallama ganin yarima be amsa ba yasa ya ƙarasa inda yake, dafa kafarɗar shi yayi, da sauri Yarima ya ɗago tare da zazzaro ido, Abi ya murmusa gami da cewa "Abubakar lafiya ina sallama amma hankalinka baya jikin ka!!!!???" "Abi babu komai" "A'a da wani abu faɗamin" rausayar da kai yayi ya ce "Abi dama... dama.. wata matsala ce" "matsala kuma" ya faɗa cikin sigar tambaya, kafin ya ce "faɗamin" ajiyar zuciya Yarima yayi gami da cewa "Abi maganar gaskiya wata yarinya ce Abdulkareem mai kasuwa yake sonta kuma Bazawara ce bata sonshi, shine ya turani wajen ta a matsayin ina sonta rana ɗaya mahaifinta ya ce nafito nan da wata ɗaya ze Aurar da ita ni kuma na laburtawa asalin masoyin ta yanzu ban san yadda suke ba"
tunda Yarima ya fara magana Abi yake binshi da kallon mamaki, gyaran murya Abi yayi kana ya ce "Abubakar maiyasa kuka aikata haka????.. ƙuruciya da shirme ya rinjayeku kunje kun ai kata ba dai-dai ba" Abi ya ƙarasa maganar cikin damuwa, Abubakar ya numfasa kafin ya ce Abi yanzu a bin damuwar shine ina son Aaminat nima" rassss rassss gaban Abi ya buga ya dubi Yarima ya ce "dama baka da tunani ka rasa hankalinka ne kasan kuwa me kake shirin aikata wa ????!!!!! cin amana fa karka manta shima fa ɗana ne nida mahaifin shi tamkar wa da ƙani muke fa!!!!"
ƙasa yayi da kai yana goge ƴar ƙwallar da ta gangaro kumatun sa Abi ya ce "kayi haƙuri ɗana, karka bari zuciyar ka tayi maka ɗanyan aiki kaji kaida Abdul ɗaya ne a waje na ba zan iya dannewa Abdul haƙƙin shi ba banda haka da na yi wani abu a kai" murmushin ƙarfin hali Yarima yayi ya ce "Abi ni dama bazan iya cin a mana ba ko makamancin haka ba, kuma zanyi ƙoƙari har naga Abdul ya mallaki Aaminat" murmusawa Abi yayi yace tare da cewa "ka kawar da tunanin komai kaji Allah yayi muku Albarka baki ɗaya" "Amin" yarima yace, suka kamo wata hirar suka ɗora,
zaune yake ya buga tagumi yana tunane-tunane Nana Kadija ta shigo da sallama zama tayi kusa da shi, gami da cewa "ya Audu komai fa ƙara zafi yake, ya kamata ka janye maganar Auren nan" wani dummmm!!!! yaji a ƙwaƙwalwar sa tayi, yayi saurin dafe kai, cikin sanyi da damuwa Nana ta ce "yanzu haka Ummi kuka take domin kuwa Dadda ya dora mata laifi ya ce duk ita ce ta ɓata mai yara" a kiɗime ya dube ta ya ce "Ummin ce take kuka???!!!" "eh" "yasalam bari naje wajen ta" da sauri Nana ta riƙeshi ta ce "ko kaje bazata kula kaba nima har nagaji da magana batace komai ba" komawa yayi ya zauna Kadija ya ce "yanzu mafita zamu nemo" ya ce "Dole hakan za'ayi don ba zai yuwu na bar Aaminat cikin wannan halin ba, kuma zan iya yin abinda ba zai yiwa kowa daɗi ba" a gigice Nana ta kalle shi ta ce "nashiga uku ya Abdul a hayyacin ka kake kuwa? me za ka yi kuma haka? don Allah ni dai karka jawo mana abin da ya fi ƙarfinmu ka yi haƙuri" cikin ɓacin rai ya ce "wai ba kince mafita zamu nemo ba??? to mu nemo mana" a jiyar zuciya ta sauke kana ta ce "lokaci yanaja kuma Dadda da Ummi kara sama suke a ganina kaje ka sanarwa da Uncle Rabi'u", da sauri ya ce "Alhamdulillah Allah na gode maka shikenan matsalata kau" Nana tayi dariya kana ta ce "duk kabi ka zauce a kan Bazawara" dan da nan ya ɗaure fuska ya ce "kinga ke fa matsalarki ba a abu da ke sai kin ɓatawa mutum rai" dariya tayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 16