Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haƙuri ya cimma duk wata nasara, da yasa gama kuma Aure nufi ne na Allah idan Allah yayi matarka ce to babu makawa sai ta zama matar ka, idan kuma Allah baiyi ita ce matar ka ba to ko anzauna za'a ɗaura Auren sai Allah yayi yadda yaso, sai Auren ya warware,, Abdul ina so ka zama cikakken musulmi mai yarda da ƙaddara aduk yanda tazo maka, ka daure ka cinye wannan jarrabawar" ɗakin yayi shiru sai shash-sheƙar kukan wasu daga ciki kakeji, tashi Abdul yayi ya durƙusa a gaban Dadda ya fara magana cikin da kakkiyar muryar sa mai daɗin sairaro, ya ce "haƙiƙa ka cancanti zama uba domin kuwa kaine cikakken da ya amsa sunan sa uba, ka jajirce akan iyalin ka ka tsaya tsayin daka don ganin anbi maganar ka, domin kuwa samun uba kamarka da kamar wuya, Dadda kaiɗin uba ne wanda bakowa ne yake da kamar ka ba," ya ƙarasa maganar yana faɗawa jikin Dadda, bayansa Dadda ya shiga bubbugawa, cikin nutsuwa, har saida Abdul ya samu nutsuwa sannan Dadda ya miƙe ckin farin ciki da jin daɗi, ya ce "Babban mutum kazo ka tayani fira," "to" Abdul ya ce ya tashi yabi Dadda sashin sa, Bayan sati biyu komai ya dai-daita a gidan su Abdul sun manta da komai sai farin ciki Abdul ma Alhamdulillah bashi da aiki sai karatun Alƙur'ani mai girma gami da Azkhar. INDO & AUTA [8/9, 2:01 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 29 Ɓangaren Mama kuwa waɗanda ta ciwa bashi sun hanata sakat arana mutum biyar sa zo karɓar bashin da taci musu, yau ma kamar kullum tana zaune, a tsakar gida, Hajja Lantana tayi sallama, gaban Mama ne yayi wata muguwar faɗuwa, kasa amsa sallamar tayi, Umma ta amsa, Hajja Lantana ta kalli Mama kallo mai cike da razanarwa, ta ce "to koriyar munafuka Allah ya kamaki, yau ɗinnan zaki biyani kuɗi na, dan wallahi indai kika ga na bar gidan nan to da kuɗi na in kuwa ba haka ba, zanzo da mota na kwashe kayan ɗakin ki,!!!!!" tuni Mama ta fara zufa, jiki na rawa ta ce "dan Allah kiyi haƙuri idan na samu da kaina zanzo na kawo miki!!" wata shaiɗaniyar dariya Lantana ta saki lokaci ɗaya kuma ta murtuke fuska kamar ba ita tayi dariyar ba, hakan ya ƙara rikita Mama ta fara sharar gumin wahala, Umma kam tana so tayi magana amma ta kasa sai ido, Lantana ta daki bango, cikin hargowa, ta ce "zaki biyani kuɗina ko saina sa an kamaki, dan kuwa wallahi akan kuɗi babu abin da bazan iya ba,!!!" ta ƙarasa maganar tana tafe-tafe cikin muryar kuka Mama ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku, duniya ta ruɗeni,"...!!! "bakiyi salati ba sai kinganki a office ɗin ƴan sanda" sakin baki Mama tayi tana kallon Mara da tashigo, Mara ta kalli Mama sama da ƙasa sannan ta ce "yaro man kaza, rashin sanin wace ce Mara shiya kaiki cimin bashi ki ƙi biya, bana yafiya kuma bana ɗaga ƙafa, yanzu haka tafe nake da ƴansanda, zakije ofishin ƴan sanda ki biyani kuɗi na,, Lantana ta kwashe da dariya gami da cewa "tirƙashi ana wata ga wata, nima dani za'a ofishin nan a ƙwatar min ƙaƙƙi na!!" hannu Mama ta ɗora aka ta fashe da wani gigitaccen kuka ta na cewa "Allah na tuba ka yafemin Alhakin Aaminat ma kadai ba zai barni na sha ruwa ba, na zalumci baiwar Allah nayi mata sharri iri-iri, ni yau tawa ƙaddarar ta zo, nayi kuskuren cewa babu ni babu ƙaddara, gashu ƴar tawa ma ta gujeni kamar ba ni na haifeta ba don ta samu duniya, waiyo Allah na yau zasu tozartani!!!" haka Mama ra fara suntiri a tsakar gidan tana rusa kuka, Umma ma sharar haweye take domin kuwa idan kaga halin da Mama ta shiga sai ka tausaya mata,, cikin rashin imani Mara ta cukumi Mama da ƙarfin tsiya ta jata ƙiiiiii!!!!, Mama kam kuka take tana sambatu, har suka fita waje, mutane taf a layin kowa ya zubawa su Mama Ido, Walid yana zaune a cikin su Abdul, baisan lokacin da wani kuka mai ƙarfi ya kufce masa ba, haƙuri suka shiga bashi, Abdulkareem kuwa kauda kai gefe yayi, Haka sunaji suna gani aka tafi da Mama, Umma kam ta rasa yadda zatayi sai faman sintiri take. Walid kam duniyar tayi masa zafi saiyayi kamar ya daina kuka, sai ya ƙara fashewa da sabo, Bilal ya dubi Abdul ya ce "dan Allah Guda ka taimaka, ka fito da Mama," sai a lokacin Abdulkareem ya kalle su, ganin sun zira masa ido yasa shi cewa "yakira yayarsa ya sanar mata mana," Walid ya kalle shi ya ce "indai Fati ce tayi hannun riga damu ta juyawa kowa baya kusan sati ɗaya kenan Mama tana kiranta, wani lokaci da ta ɗauki kiran tace kar atakura mata, wani lokaci, ma bata ɗaukar kiran," ya ƙarasa maganar kamar zai ƙara rushewa da kuka, kowa yayi zumu-zumu yana kallon Abdulkareem, shi kuwa ranshi fess, saidai bai bari Walid ya gana hakan ba, Jabir ya numfasa gami da cewa "to yanzu ya za'ayi??" Abdulkareem ya murmusa kana ya ce "yakira ɗayar yayar tasu mana," da sauri Walid ya ce "wai yaya Aaminat,??" "eh ita" sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "banajin yaya zata iya taimakawa Mama, domin kuwa alhakin ta ne yake bibiyar Mama" Abdul yaja tsaki gami da cewa "dalla ka kirata an faɗa maka ba'a yafiya, zata yafe mata kuma zata fito da ita ka kira ka sanar mata," yana gama faɗin haka ya tashi, ya nufi gida, yana cikin tafiya yaji garam sunyi karo, ahan kali ya ɗago kansa ya zuba mata wani masifefen kallo, jiki na rawa ta ce "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban kula ba," tsaki yayi gami da cewa "ina idanunki suke, ko aka suke, kina tafiya amma hankalin ki na wani wajen, ƙasa Siyama tayi da kai, ƙirjinta yana wani bugu, Abdul ya kauce ya fara takawa, cikin ƙasaita,, Walid yana kiran Aaminat ya zaiyana mata komai, numfasawa tayi, sannan ta ce "Walid ka kwantar da hankalin ka, kaji zanzo in biya duk bashikan da Mama taci yanzu," cikin farinciki ya ce "ya Aaminat samun kamarki da wahala, kin manta duk wani sharri irin na Mama kan manta munanan ƙazafin da tayi maki," murmushi tayi mai ciwo ta ce "hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka jefar, Mama uwa ce gareni, kuma tana cikin wani hali, kaga dole zanyi ƙoƙari naga na fitar da uwa ta" "haka ne yaya Allah ya saka miki da alkairi," "amin" daga haka sukayi sallama, Yarima ta kira ta sanar masa, yaso ya hana ta amma da ya tuna ko wace Mama a wajen Aaminat sai ya amince, bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf cikin Atamfa riga da zani, ta zindima hijab ɗinta har ƙasa, sannan ta fito ta umarci Direba ya kaita, inda zataje. basu ɓata lokaci ba suka isa, ofishin ƴan sandan, tana shiga ta hangi Mama a cikin ɗan wani ɗaki, tayi muzu-muzu kana gani kasan ta wahala, gaisawa sukayi, cikin mutuntawa, sannan Aaminat tayi musu bayanin duk Abinda ya kawo ta, Mama kuwa tana ganin Aaminat ta ƙara rushewa da kuka mai cike da nadama da danasani, saida suka ɗauki lokaci suna magana da ƴansandan sannan Aaminat ta biya su Mara da Lantana kuɗin su, tayi ƴan cike-cike aka fito da Mama, Aaminat ta juya zata tafi taji, an rungumota, cikin muryar kuka, Mama ta ce "Aaminat ki yafe mini na zalumce ki, ni kuma ga tawa ƙaddarar, ta sanadin Fati na shigo wajen nan amma Fati bata damu dani ba," ta ƙarasa maganar tana kuka, Aaminat ta kama hannun Mama ta jata suka fita, murfin mota ta buɗe ta ce "Mama ki shiga muje ki rakani duk inda ake binki bashi abiya su," Mama tana kuka ta shiga motar. haka suka dinga bi gida gida ta biya su kuɗin su, sannan suka wuce gidan Aaminat, saida Mama tayi wanka taci Abinci, ta ƙara nemar yafiya, Aaminat ta ce ta yafe, tasa Direba ya maida Mama gida, Washe gari da safe Abba ya shirya tsaf zai fita, Mama ta fito daga ɗaki, simi-simi "dan Allah kayi haƙuri Alhaji, ko kallon ta baiyi ba yayi gaba abin sa, Mama ta rushe da kukan nadama da da na sani, Umma ce ta fito daga ɗakin Abba ta fara rarrashin Mama, Abba yana fita yaci karo da wani bawan Allah, baki sake Abba ya tsaya yana binsa da kallon mamaki, da al'ajabi, mutumin yaja ƙafa ya ƙarasa inda Abba ya tsaya, ya ce "Abba Kamalu ne, nazo ne na nemi yafiyar ka da Aaminat dan Allah kuyafe min, cikin mamaki Abba ya ce "Kamalu kaine ka koma haka,???!!!" "nine duniya ta ladabtar da ni, haƙika na cutar da baiwar Allah wadda batasan komai ba sai gaskiya da Amana, Abba duk wasu munanan magan ganu da na faɗa akan Aaminat wallahi ƙarya nake sharrin zuciyane," ya ƙarasa maganar yana kuka, Abba kam ya kasa koda motsa ɗan yatsa ɗayane sai ido, Kamal ya kara cewa "maganar tana bin maza agida na itama sharri ne ƙazafi ne, nayi hakan ne dan na tozarta ta na rabu da ita, na Auri wata, sai gashi wadda na Aura ɗin neman yar uwata take, ina azabtuwa awajen ta ta rabani da duk wani abu da na mallaka, hatta iyayena ta rabani dasu," ran Abba in yayi dubu ya ɓaci ji yake kamar ya shaƙe Kamal ya huta, cikin ɓacin rai "Abba ya ce haƙika ka cuce ni kasa na juyawa ƴar ciki na baya, ƴar da tafi kowa ladabi da biyayya, tafi duk sauran ƴaƴana tausayamin, amma kasa na juya mata baya nake azabtar da ita, amma kaje kaida Allah ni nayafe maka," cikin kuka Kamal ya ce "haƙiƙa nine silar rushewar farin cikin ƴar ka, ko bakomai duniya ta hukunta ni yanzu na rasa duk wani abu na farin ciki, ina fuskantar tsanani," ya ƙarasa magnar yana shash-sheƙar kuka, Abba ya juya zai tafi, zuciyar sa cike fal da baƙin ciki da takaici, tabbas yayi gangancin yarda da abinda Kamal ya faɗa masa lokacin da ya saki Aaminat, cikin sauri Kamal yaja ramammun ƙafafuwan sa, ya tari Abba cikin muryar kuka ya ce "don Allah kayi min hanyar da zan nemi yafiyar Aaminat," cak Abba ya tsaya zuciyar sa tana wani irin tuƙuƙi, Kamal ya haɗa hannayen sa waje ɗaya ya ce "don girmin Allah na roƙeka ka taimaka min na nemi yafiyar ta wallahi in ban nemi yafiyar ta ba ruhina ba zai samu salama ba," Abba ya kalle shi sannan ya ce "yanzu Aaminat tana ƙarƙashin ikon mijin ta ni bazan iya yi maka hanyar da zaka gana da ita ba saida izinin Mijin ta," "na yarda kanema min alfarma awajen mijin ta in nemi yafiyar ta," Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Omar dake tsaye, yana jinsu, ya ce "Omar ka kira Abubakar ka sanar masa, in ya Amince ka rakashi, amma karka kuskura ya shigar masu gida," cike da girmamawa Omar ya ce "to Abba amma ni bazan iya ɗaukar wannan ƙazamin mutumin ya mashin ɗina ba," "kayi haƙuri ka raka shi, dole ce tasa" badan yaso ba ya ce "to" Abba ya wuce yashiga motar sa, Omar kuwa sai jan tsaki yake yana zabgawa Kamal harara, Dr Yarima ya kira yayi masa bayanin komai, Yarima bai musa ba jin ance Abba ne yasa akirashi asanar masa, hakan yasa ya amince amma bawai dan yaso ba, Omar kuwa takokin yadda zai ɗauki Kamal yake amashin ɗinsa acewar zai ɓata masa mashin, ganin bashida zaɓi ne yasa ya ce Kamal ya hau sutafi, yana hawa Omar ya figi mashin ɗin, Basu daɗe ba suka isa, aharabar gidan Kamal ya tsaya, Omar yashiga ya ce da Aaminat ta fito, amma bai faɗa mata kowaye ba, batare da tunanin komai ba ta zira hijabi ta bi bayan ya Omar, suna ƙarasawa harabar gidan tayi turusss ganin Kamal, rai a ɓacen-ɓace ta juya da niyar komawa, Omar ya ce "kiyi haƙuri ki tsaya ki saurare sa," "Babu abinda zanji daga gare sa sabi da haka kace ya tattara mummunar fuskar sa ya barmin gida ko nasa ayi masa korar kare" tana gama faɗin haka taci gaba da tafiya, Omar ya sha gaban ta ya ce "karki manta da cewa muma munayi wa Allah laifi kuma munemi yafiya ya yafe mana" tsayawa tayi tana huci, Kamal kuwa kuka yake yana cewa "dan Allah ki gafarce ni ki yafe min duk abinda na aikata miki dan Allah, "kaje na yafe maka duniya da lahira, Allah ya shirye ka," tana gama faɗin haka ta juya tayi ciki, "Ahamdulillah Allah na gode maka, da kanuna min wannan rana, Aaminat da mahaifinta sun yafe min," Kamal ya faɗa yana jan siraren ƙafafuwan sa, Omar ya kalleshi ya ce "inna ta gaida Ashsha," Kamal ya juyo ya kalli Omar yana goge hawaye, Omar kuwa yana gama faɗin haka ya zuge ƙofar gilashin ya shige cikin tafkeken Falon, INDO &💗 SALMA[8/12, 6:24 AM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 30 Zama yayi ya kalli Aaminat dake razgar kuka ya ce "ke kuma kukan me kike!!" share hawayen tayi ta ce "nifa ba kuka nake ba" "kice dariya kike," sakin baki tayi tana kallon ya Omar, tsaki yaja gami da cewa "nifa wallahi haushin mutumin can nakeji kuma kika zauna kina yi masa kuka" "wai kai ana maganar mutane kana sako zaburarru," dariya yayi batareda yace komai ba, shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci, Aaminat ta katse shirun da cewa, "Bari in kawo maka abinci" "ke nifa da tafiya zanyi amma tinda kin matsa ba komai" miƙewa tayi tana cewa " Ya Omar nawa niko ta Allah" harara ya maka mata, ƴar dariya tayi, ta nufi kicin, Bata jima ba ta dawo da wasu jibga-jibgan kuloli, na alfarma, ajewa tayi, ta buɗe ta zuba masa a wani ƙayataccen Filet, ta kalle sa ta ce "kuma sai ka cinye dika," "ke mai kika maida ni ne???" dariya tayi, batare da tace komai ba, saida ya ɗan kwashi ƴan mintina yana latsa waya, sannan ya fara cin abincin, Aaminat kuwa sai murna take tana mai ƙara godewa Allah, aranta ta ce "duniya juyi-juyi yau gani ga yayana agida na," ta ƙarasa zancen zucin tana murmushi, ƙaɗan yaci ya ce ya ƙoshi dama don karta ga ya ƙi ci ne, tana ya ƙara ci yana ya ƙoshi, ya miƙe ya ce "ni kinga tafiya ta sai wata rana," yanzu tafiya zakayi??" "A'a kwanciya zanyi," ya ƙarasa maganar yana dariya, ita ma dariyar tayi, ya nufi kofa, bin bayan sa tayi domin yi masa rakiya, sallama sukayi, ya hau mashin ɗinsa ya ɗaware, Abba kam tunda ya isa kasuwa, ya kasa komai sai tunanin Aaminat, kozata iya yafe masa, ko bazata yafe ba, wannan tunanin ne yake tayi masa juyi a ƙwa-ƙwalwa, in ya zauna sai ya tashi, sai zarya yake, Hamza ma tunda Abba ya bashi labarin komai, jikinsa yayi sanyi salam har dare yayi Abba ya koma gida, jikinsa amace, tunda ya koma yake zazzagawa Mama ruwan faɗa, banda kuka babu abinda take, Umma ce ta samu nasarar, bashi haƙuri kuma ya haƙura, washe gari ma koda Abba ya tashi bai nunawa Mama bambanci ba sai nasihohi da ya haɗa su ita da Umma yayi musu, Bayan wata ɗaya. Fati ce zaune, ta zabga tagumi sai hawaye take, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin mawuyacin hali, ta rame ta ƙanjame, tayi wani ragwaf-ragwaf kamar tsohuwa, saitayi yun ƙurin tashi saita kasa, tun safe take zaune awajen har shabiyu na rana tayi, amma ta kasa koda motsawa, in tayi kamar zata tashi sai jiri ya ɗebeta ta koma tayi jagab, tana cikin wannan halin Ahmad ya shigo, hannunsa riƙe da waya ya manna ta akunnan sa yana waya cike da jin daɗi, wucewa yazoyi ta gefen Fati, tayi saurin cafke ƙafarsa, ya harbatsar da ita gefe, cikin rawar murya ta ce "Allah ya isa tsakani na da kai macuci kawai, ka yaudareni kaci amana ta," cikin zafin rai ya dubeta ya ce "kekika yaudari kanki, duniya ta rufe miki ido kika kasa gane asalin waye ni," cikin kuka da taurin kai ta ce "mugu Azzalumi Allah saiya saka min, yau kwana biyu baka bani ci ba baka bani sha ba ga duka na rana daban na dare da ban," ta ƙarasa maganar tana wani galabai-taccen kuka, shi kuwa ko ajikin sa, yayi gaba, cike da tsiwa da rashin kunya Fati ta ce "Allah ya isa mugu kawai ɗan is...." marin da ya kifa mata ne ya hana ta ƙarasa maganar, ya ƙara sharara mata wani azababban marin mai rikitar wa, saida taga taurari sun gifta, shiɗewa tayi ta kasa kukan, cikin ɓacin rai ya ce "niki ka zagi, an faɗa miki ni ɗan asara ne da zaki zagi iyaye na, na ƙyaleki, to ki sani ni iyayena basu ce jeka ka gani ba,.." ya numfasa yaci gaba da cewa "ƴar iska ta wuce ke, wato kin samu duniya kin banzatar da iyayen ki, to kisani nine ajalin ki muddin baki daina ɗagamin harshe ba," cikin mawuyacin hali da azaba, Fati ta fara magana muryar ta dakyar take fitowa ta ce "Ahmad kayimin duk abinda ka gadama, Allah ne ya jarabce ni, bazan taɓa ganin laifinka ba, sakaiyar Aaminat ce da waɗan da na cuta na yaudare su, duniya kenan, kaico na da na kasance, mai son zuciya, duniya ta ruɗeni, na afka inda ajali na yake," ta ƙarasa maganar tana gursheƙen kuka, Ahmad jikin sa yayi sanyi, ya nufi inda Fati take, yana ƙoƙarin kamata ta ce "A'a Ahmad bancan-canti ka taimake ni ba, kaɗan na gani daga cikin abinda na aikata, amma don Allah idan Allah yayi na koma gareshi ka nema min yafiyar ƴar uwa ta Aaminat da iyayena, kane mamin yafiya a wajen mahaifiya ta da na juyawa baya," zuwa yanzu Ahmad tausayin Fati ya gama mamaye zuciyar sa, ya matsa kusa da ita ya ce "kiyi haƙuri da abinda nayi miki duk da nasan ba a son raina nake azabtar da ke ba" murya na rawa ta ce "baka da laifin komai, hakan jarabta ce daga uban giji, kuma ta silar hakan nayi na damar abinda na aikata abaya,!" Ahmad yayi murmushi, ya ce "Fati kin gane gaskiyar abinda kika ai kata ba dai-da bane!!!??" ta gyaɗa kai, alamar eh, "to ni da kaina zan taya ki roƙar ƴar uwarki ta yafe miki, kuma zata yafe miki," share hawaye tayi ta dubbeshi, ta ce "banajin Anty Aaminat zata iya yafe min, domin kuwa abun da na aikata mata ya munana, kuma ko ba komai yanzu nasan Aaminat ta wuce inda nake zato" "hakane amma ina mai kyauta-ta zaton zata yafe miki in sha Allah, gigiza kai Fati tayi tana ƙara tuno irin cin zarafin da tayi wa Aaminat abaya, Ahmad ya ce "kitashi kiyi wanka" ƙoƙarin tashi ta farayi, Ahmad ya taimaka mata ta tashi, ya raka ta banɗaki, tayi wanka, kafin ta fito ya haɗa mata shayi, tana fitowa tasha shayin sosai dan kuwa muguwar yunwa takeji, Ahmad ya kalle ta ya ce "Fati kinsan me" ta ce "A'a" ya ce "maganar gaskiya ni ba mai kuɗi bane hassali ma iyaye na a ƙauye suke, ni nataso ne a makarantar allo, daga bisani na samu aikin shara da bawa fulawoyi ruwa a gidan su Abubakar mijin yayar ki, daga baya suka maidani Direban su hakan yasa na iya mota, kuma nake hawa mota kala-kala, kikayi zaton ni mai kuɗi ne, a ranar da muka haɗu dake ma aike na akayi," ya numfasa, kana ya ɗora da cewa "gidan nan ma da muke zaune mallakin Yarima ne, banawa bane bamu da gadon sa, lokacin da na faɗa masa zanyi Aure ne ya bani wannan gidan na zauna na wani lokaci," tuni hawaye sun wanke fuskar Fati, tabbas duniya makaranta ce, ta gama ruwan idon da yaudare yaudare ƙarshe ga inda Allah ya jefota, share hawayen tayi ta ce "naji kuma na yarda zan zauna da kai, amma don Allah tunda kasan inda Aaminat take kayi min Jagora, na nemi yafiyar ta," ajiyar zuciya ya sauke, kana ya ce "karki damu yanzu zamuje kuma zata yafe miki," Fati ta miƙe tana cewa "muje yanzu" shima tashi yayi ya mara mata baya, Aaminat tana zaune ta harɗe ƙafa, ƴar aikin ta tashigo, ta ce "ranki ya daɗe kinyi baƙi," "baƙi kuma" Aaminat ta maimaita cikin sigar tambaya, Na'ima ta ce "eh ranki ya daɗe, kuma naga kuna shigen kama da ita," Aaminat a ranta ta ce "ko suwaye su Umaima da Siyama dai jiya sunzo to ko Iman, ce" afili kuwa ta ce "ki saukesu a Falon baƙi kice ina zuwa" cike da girmamawa ta ce "to" ta nufi inda su Fati suke, Aaminat kuwa ɗaki ta nufa ta sako ƙaton hijab sannan tayi Falon Baƙi, da sallama ta shiga ɗakin, rassss gaban ta ya faɗi, lokacin da idon ta ya sauka akan Fati, ja baya tayi tana watsawa Fati wani irin kallo, "mai ya kawo ki inda nake ko kinzo ki ƙarayi min wani ƙazafin, kina so kice na ai kata wani abun ne?!!!" ta ƙarasa maganar cikin hargowa da ɗaga murya, Fati kuwa wani kuka ta saki, mai cike da nadama da danasani, ta ce "don Alla.....!!!" Aaminat ce ta katse ta da cewa "mai kike so kice dani mai zaki ce ki tattara yanaki-yanaki ki barmin gida, azzaluma, kawai, butulu!!!" cikin kuka Fati ta ce "nazo ne nanemi yafiyar ki koda bazaki yafe min ba, ina roƙonki da kiyi min gafara ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah, kitaimaka min" ta ƙarasa maganar tana durƙushewa agaban Aaminat, tuni jikin Aaminat yayi sanyi, ta shiga share hawayen ta, Fati kuwa kuka take tana ƙara nemar gafarar Aaminat, cikin kuka Aaminat ta ce "Fati na yafe miki kinji ke ƴar uwata ce, ki daina kuka," ta ƙarasa maganar tana rugume Fati, kuka suka shigayi, babu mai rarrashin ɗan uwan sa, Ahmad ma matsar hawaye yake, Aaminat ta share hawaye ta fara rarrashin Fati har saida tayi shiru, sannan ta ƙara nemar yafiyar Aaminat, Aaminat ta ce "na yafe miki, na daɗe ina jiran wannan ranar

Chapter 15 of 16