Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"sannu" Kai na d'aga mata kurin,aka cigaba da wasa danaga zamu sake gamewa zanyi saurin ja baya,kafin su Rukee su sake ankarewa mun sake cinsu,tsalle da ihun dana buga sadda ya jefa kwallon a raga shine dalilin da sulb'in wajen ya dauk'eni ya nanani da k'asa nai wata irin gurd'ewa na fad'i, wata razananniyar kara na fasa mai tada hankali,saboda azabar danaji ga k'uguna da k'afata wajen guiwa,aguje sukayo kaina shine farkon zuwa ba zaka kalleshi kace ya razana ba,amma idonsa kawai zai nuna maka a kid'ime yake,ruwa sosai akeyi kafar ya kama zai murza na fasa kara,rukee ta kamani da mufeey in tashi na kasa,wata irin azaba nakeji ga k'uguna kuka nake ina kiran"nashiga uku K'uguna ya kare,Rukee na bani wayyo umma Abba ka taimakeni na kare k'ugu" Mufeey sai kuka da yake gwanace a kuka,Rukee ma hawaye take tunanin ta dagasken karewar nayi,ganin halin da nake ciki yasa ya nufoni ina zaune dirshen k'asa ya sak'o hannunsa ta kugun ya saka d'ayan karshin kafafuna sai jinai kurin d'afff ya daukeni yai cikin gida dani,azabar da nake ciki bata hanani mamaki da al'ajabin abun ba,rungume nake jikinsa sosai don zan iyajin bugun zuciyarsa,ruwa nata dukanmu bamu damu ba su Rukee suna bayanmu,wata kwarankwatsi da aka saki bansan na k'wak'ume shi ba na saka kaina tsakanin wuyansa da kirjinsa,Ya salam musallim wani abu naji ya ratsa hancina da kwalwata, *K'AMSHIN TURARE* azabar da k'uguna keyi bai hanani dagowa ina kallon fuskar ba cikin mamaki,kamar bai san me nake ba koda wasa bai kalli fuskata ba,har sadda muka shigo cikin main falo ya wuce dani har dakinmu bisa gado yad'orani,bai kallan ba ni kam kamar na samu tv wajen zare hannun sa daga k'uguna ne na zabura nace "wayyo Allah na" Ya mik'e yana ce mun, "Allah ya sawake" Dai-dai Su Rukee sun shigo,shi kuma ya fice sai na saka kuka kurin ina cema Rukke ta kira umma akaini asibiti,mutuwa zanyi duk sun damu sosai Rukee tatafi kiran umma,Mufeey sai sannu take mun. "Laifina ne Roohee nina jawo wasan nan,da ba ayi ba bazaki samu matsala ba ki yafe mun" Kukana kurin nake sosai hadda hawaye,don k'ugun yafi mun ciwo sosai, cikin kankanin lokaci na tara mutan gidan,hadda goggo Habi anata mun sannu ita takira Abba Nura aka kaini asibiti,sun duba babu wani mugun rauni buguwace kurin,aka bani magani na shafawa in angasa,su Mama da najeeba duk sunzo dubani har Abba Habibu kowa yazo amma ban ganshi ba,Abbanmu washe gari yace in ina iyawa zai tura ma YAH RAMADAN KUD'I muje shopping mu siyo duk abunda mukeso yan team d'inmu,jin ance shopping nace zan iya duk da kuwa d'angyashi nake sosai. Na fito wanka ina shafa mai daga ni sai Rukee nace mata, "wani abu yaban mamaki jiya Rukee,ashe guy d'in nan yana saka turare,turaren ma mai aji mai tsada Abbanmu kad'ai nasani da irin sa wallahi Rukee" Mamaki itama take kafin tace, "ya akai kikaji to" Shiru nayi kawai bance komi ba,kamar banji ke tace ba dariya naji tana yi na dago ina kallon ta, "miye ne to?" "Aa mefa,hangoki nai dare-dare a jikinsa,shine nace kunyi kyau..........na jefeta sa robar man da nake shafawa, "Allah ya isa tsakanina dake,ashe kina nan kinyi mun tanaji,dadin abun bance ya daukan ba da ina cikin hayyacina hakan ba zata tab'a faruwa ba" Dariya kurin take tana cewa,"aa ni kam me zaki cemun kuma" Aiko na k'ule-k'ule na hayeta naita jibga har sannan bata daina dariyar ba,saida naji ina fama ciwona na sauka daga cikinta, raina a b'ace haka na gama shirin,Mufeey na can b'angaren mama indai yana gida to ita kam tana nanik'e dashi. _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....14 Mun tafi yin shopping daga ni sai shi da mufeey,suna gaba sai fira take masa bata damu da rashin ansa ta da bayayi ba,sai an dad'e kafin yai sentence da bai wuce three letters ba (😂 miskili kafi mahaukaci ban haushi),duk haushin su ya kamani sosai a haka dai mukaje mukai uwar siyayya don nikam jidar kaya naitayi ban damu da insan ko adadin nawa Abban ya bashi ba,saida Mufeey ta ce "ke kam dai Allah wadaran halinki,duk ina zaki da wad'anan kayan to in kudin basu isa ba fa" Na harareta nai gaba abuna,na bar musu kayan na koma mota nai zamana,yah Rafeeq ya kirani daman yinin ranar van same shi ba,sai nahau mishi kuka ba gaira babu dalili "Ya salam Rooh minene?waya tab'amun ke don Allah kiyi shiru karki dagula mun lissafina" Cikin kukan na ce, "to ni daka dagula nawa fa?kana can kana tare da yan matanka ka manta dani,through out yau ka hanani jin muryar ka,gashi ban da lafiya ko" Shagwab'a zalla naita zuba mishi ina kukan,bilhakki da gaskiya wanda ban san ya akai nake yin sa ba, cikin laushin murya da yake anfani da ita wajen lallashina ya ce, "Roheena pls stop crying kinji babyna,I don't mean to hurt u na fada miki muna da wani practical kuma zaici lokaci,shine ya hanani kiranki kuma in dakin kira zakiji wayana switch off,uhm Rooh kin san ke d'aya nake da a duniyata matsayin masoyiya ta kuma matata,ki daina tada hankalin ki kinji ko" Ahankali na rage sautin kukan ina cewa, "nidai ko yaya ne ka ringa kirana hankalina zaifi kwanciya" "Ayya zanyi hakan inhar zai faranta miki,yanxu gaya mun miye yake damun masoyiya" Bansan na saki murmushi mai sauti ba na ce, "ba jiya bane mukai basketball,shine fa na gurd'e na bug'e k'uguna" Cikin nuna damuwa ya ce, "wayyo Allah na Bbyna I'm sorry kinji,ki daina yin duk abunda zai wahalar mun dake,ko ya shafi lafiyarki inajin abun har raina,ki kula mun da jikinki yana daya daga cikin abun da ya shafi farin cikina" Na lumshe idona ina murmushi,hankalina yana can ga waya ban san sun shigo motar ba,saida na ce masa "uhm ohk love zan kula yanzu munzo shopping in na Isa gida muyi video call kaji" "Baki da matsala Allah ya tsare" Na sauke wayar ina satar kallon su,jira nake inji ya tada motar amma shiru "Wai motar bata tafiya ne mufeey?" Ta jiyo tana kallona ta ce, "kayan ki na can kin baro shiyasa muka jira ki gama kije ki ida biyan kudin sai mutafi" Idona duk a warwaje na ce, "me?kayana na can?wace irin magana ce wannan shine zaku baro mun kaya acan mufeey!in kowa bai tausayina ke ai kina yi shine saiki biye" Kamar zan kuka nake maganar saboda bakin ciki, "kiyi hakuri sister wallahi hanani yai in dauko,wai kudin kayan sunfi karfin abunda Abba ya turo an biya rabi rabin ne suna can" Wasu kwalla su cika idona na ce, "Allah ka raba bawa da talauci,nayi imanin da Yah Rafeeq na nan bazan wulakanta ba,Amma bkomi wannan ma k'addarace..........Haba Rohee miye haka kike yi ne?kudin da Abba ya tura fa duk kayan sun lashe su,shifa ko hanky bai siya ba kayanki sun hana,ni kaina banda set din dove da inears da turare ban sai komi ba,amma shine kike fadar wannan bakar maganar?" Cewar Mufeey,har idonta ya cika da kwallah,ita dai haka Allah yayita mugun tausayi gareta sosai. Tsaki naja dogo nafita a motar daker,saboda k'uguna har yanzu ciwo yake, "Yah RAMADAN don Allah kaya hkur......shiiiit,bana so pls minene zaki ta b'ata ranki akai" Idonta da hawaye ta ce, "bana jin dadi ne in tana maka haka" Murmushi ya saki mai d'an karen kyau,idanun sa sun d'an canza kad'an yace "don't mind her,watarana zai zama lbri ohk?" Ta jinjina kai kurin ya bata hankyn sa dake cikin aljihu ta ansa tana share fuskarta da ta b'aci da hawaye, da karfin hali na isa wajen biyan kudin na kira Yah Fahad na gaya masa abunda ya faru,nan take ya tura musu sauran kudin su sannan na saka aka kaso mun kayan na fito,har mukaje gida bance komi ba raina bace sosai. Koda Rukee taga kayan dana jido ta rik'e baki ta ce, "Roohee kema kin san kinyi k'wara dubi uwar siyayyar da kikai kamar dai kece CBN,haba mana" Ina shirya kayayyakin a ma ajiyar su nace, "ina sane wallahi nayi haka,ban son ya mori koda k'wandala ne a cikin kudin" Rukee tace, "magana ta gaskiya zamuyi Rohee,kin san gaskiya nima na sani mu sassauta hakanan,k'iyayya bata da dad'i fa annabi yayi hani da zurfafa k'iyayya haka soyayyar ma ba ace ka zurfafa ta ba,shiri ne dai ba muyi dasu amma mu daina wannan halin" Rik'e baki nai ina kallon ta, na ce "sannu mu'allima Rukayya yaushe kika iya wa'azi ne haka?" Murmushi tayi ta ce "uhm nasan halin ki ai,inhar ba maganar Yah Rafeeq bace bamai fad'a miki kiji, kiyi yadda kikeso LAYLA" tunda naji ta kira ainahin sunana nasan taji ba dad'i,sai na kyaleta nasan ta inda zan b'ullo mata. Kwana biyu bayan nan mukaji wai YAH RAMADAN kwanan sa biyu asibiti kwance, duk abun nan bamu sani ba,munga dai bamu ganin mufeey kwata-kwata ashe tana can wajen sa ita da Yah najeeb,in dare yai zata dawo gida shi ya kwana dashi, Abba yace ashirya aje a duba shi. Munje mun samu jikin da sauki ba laifi,yana ma shan watermelon lokacin fuskar sa ta d'an fad'a alamun yaji jiki sosai, su Umma ko minty biyar basu ba a dakin suka fito suka koma mota,daman daga nida Rukee sai su Anti Rafeea da Anti sha'awa on ready sunzo su. Yadda Rukee ta saki jiki tana masa magana yaban mmki, hadda dauko masa ruwa daya buk'ata,wani kallo nake mata ban dai ce komi ba tunda nazo,inaso nai masa magana sai inji bakina yai nauyi sosai,ya dubi fuskar kowa ban dani ko kusa da inda nake tsaye bai waigo ba balle ya kalli fuskata,hakan ya sake ban haushi ban san naja wani dogon tsaki ba na juya zan fice, "Keee!da uban wa kike?" Muryar Yah Najib ta katseni daga fitar da zanyi, na jiyo fuska ta aturb'une goggo Habi na gefe tana kallonmu, na bata fuska na ce "ni na ce da wani nake ne?........wallahi zaki fita da ballalallar k'afa a nan don ubanki,ki cigaba kar ki daina" Kamar in sake jan wani tsaki tsoro ya hanani,don Yah Najeeb ba dai mugunta ba. Na murgud'a bakina na juya aiko yayo kaina a fusace, goggo ta tare shi "yi hakuri Najibullahi kai babba ne kyaleta,ke kuma Allah ya shirya ki wannan halin ba halin kwarai bane saboda gidan wani zaki,ki gyara in kina gyarawa" Duk abunda ake bai ce komi ba kamar baya dakin,Haka mufeey da Rukee wadanda suka ban haushi yadda naga duk sunyi mu bayi'a akan shi,fita nai daga dakin don haushi zai iya sumar dani a wajen, ni kam ai banga abunda zai saka na canza daga tsanar da nake ma ahalin Abba Habibu ba,to akan me ma Zan canza?wanda duk wani fitina da tashin hankali suke kirkiro mana su,sun hana uwayen mu mata zaman lafiya da mazajen su,suda ake ka alfarma to kan wane dalili zan jasu jikina. Karshe nabi su Umma Da Mami muka dawo gida,sukuma sai dare suka dawo, Kamar jira nake su shigo daki Rukee da Mufeey na hausu da masifa, "Wallahi kunyi a sara,ko ince dai Rukee kinyi asara ke kam ai na sallamaki indai akan wancen gallafirin ne,ana cimun mutunci gabanki ko ajikin ki Rukee?yaushe kika sallama haka?wai kin mance duk abubuwan da suke k'ulla mana?kin mance irin wulakanci da iskancin da wannan dan isk...........ban san miyasa nai shiru ba,gani nai duk sun zuba mun ido sai kawai naja dogon tsaki na shige toilet,tun daga ranar Rukee bata sake bani hadin kai wajen yima Yah Ramadan wulakanci ko iya shege ba,dana fara zata tashi tabarni ko kuma tabar wajen,har Mami na gaya mawa aiko ranar kamar zata mareta don fad'a, take cewa "Ashe baki kishina Rukayya?ashe duk abunda Ahalin Habibu suke mana ke baki gani,anya kece kuwa Rukayya" Anti sha'awa ta ce "Mami ba rashin kishin ki ne batayi ba,tana so tayi ma Abba biyayya kamar yadda tayi miki,kuma hakan dai-dai ne tunda dai abayyane ba wani abu suke mana ba da zamu k'isu,hasali ma duk gidan nan ba wanda ya kai yaran Abba Habibu sanyin hali in kacire Najeb..........au ashe ba Rukee kad'ai ta sallama ba hadda ke Sha'awanatu?innalillahi wa inna ilaihir raju'un,minake shirin gani haka?" Sai suka tashi suka barta dagani sai ita,na bata hakuri tare da cewa duk rintsi ina tare da ita,ni a cikin tsanar da nake musu bana jin ko da dakwayar zarra zai ragu,da haka na shawo kanta. Wannan dalilin yasa Nida Rukee muka samu matsala,inajin haushinta sosai akan sabon halin data tsiro dashi,bata iya bina akan ra'ayina haka nima ban iya binta akan nata,sai dan danan kowa ya gane mana a gidan bama shiri,har su Mufeey suka tafi bamu shiri da Rukee. Ranar da zasu tafi naga abun mamaki wajen Mufeey,weekend ne ba sch karfe goma suka gama duk shirin su,daman tunda muka tashi ba walwala tare da ita,kadan-kadan ta share hawaye koda tai wanka bata saka komi a fuskar ba,ni dariya ma abun ya bani da yake daga ita har Rukee ba wanda muke wata magana sosai dashi sai ta kama. Inata karatu na a computer da yake mun fara test a sch,ina lura da ita jikin window tana share hawaye,dariya ta kamani nai ta abuna kafin naja tsaki nace, "to kice baki koma wa mana,kiyi zamanki wallahi sai kawai a daura muku aure ba shikenan ba" Daga ita har Rukee ba wanda yace ci kanki,Rukee ta gama gugar kayanta ta shirya su a wadrope inda dane tare take mana,yanzu ko kowa sabgarsa yake ba ruwan kowa da abun kowa,Ummi ta shigo dakin tana cewa "Yaya Mufeda ance ku fito goggo sun fito compound tun dazu" Rukee ta daukar mata wata jikka ita kuma taja akwatin ta,har suka fice ban da niyyar tashi,sai nakejin ba dad'i sosai a raina bamu tab'a irin wannan rabuwar da Mufeey ba,duk sadda tazo mana hutu da kuka muke rabuwa,farkon zuwanta kuwa kodayaushe cikin raha da wasa muke mu ukun nan,amma wannan zuwan yazo da sabbin abubuwa,sai naji can kasan raina babu dad'i kwarai,inata dannewa kar raunina ya bayyana in bada kaina har dai na kasa,na mik'e na isa ga tagar ina lek'ensu amma ban hangota ba,wayata Abba ya kira na dauka ya ce mun "me kike baki fito rakiyar su goggo ba,maza ki fito ki rakasu kibiya Bangaren Yaya kice da Ramadan su ake jira" Bai saurari abunda zan ce ba ya kashe wayarsa,nai tsaye sororo da wayar a hannu har saida ya sake kirana,na dauka nace gashinan na fito,har na iso kofar bangaren nasu inata tunani wanda ban san ma wane kalar tunani bane,Mama ce kawai falon na gaidata sama-sama ta ansa itama kadaran-kadahan, "Daman Abba ya ce ace masa yafito lokaci na k'urewa" Hanyar bangaren su shida Yah najeb ta nuna mun,ta cigaba da abunda take na gama tsayuwata na wuce can,cikin raina ina mamakin yadda itama ta canxa ai da ba haka take mun ba,naja tsaki kurin ina tura k'ofar falon su...........kyakkyawan gani nai musu Mufeey ce rungume dashi ajikinsa,ta zagaya da hannuwanta bayansa,shi kuma yana tallabe da kanta dashi mukai four eye's saboda ita tabada baya,wani mugun fad'uwar gaba naji wadda ban tab'ajin irin ta ba a rayuwata,kallon-kallo muke ma juna nama rasa me zanyi kawai mamaki ne,?al'ajabine ko ko minene ban sani ba,kawai dai ganin su a haka ya dakeni sosai,kuka take tayi masa shi kuma yana lallashin ta,dauke idon sa yai daga barin kallona yana d'ago kanta yana goge mata hawayen,sai kawai na juya da sauri na fice daga dakin,koda na iso farfajiyar gidan duk su Abba na nan sai Mama data fito da Rukee da ummi,sai su Anti Rafeea sai ni har na tsaya gefe guda ban fita daga cikin shock din ganinsu haka ba,Abba ya ce mun "ina suke ne wai?" Nama kasa cewa komi,sai na nuna hanya da hannuna bance komi ba,goggo ta ce "miya sameki ne?" Girgixa kai na nayi kurin kamar wata sakarai,dai-dai nan suka fito suke rik'e da hannun Juna,kallon su nai tayi ban san miyasa al'amarin su yaban mamaki ba,gashi ba magana muke da Rukee ba balle in labarta mata,kai ko muna magana ba bana iya fadar wannan abun,ban kuma san dalilina ba. Ban kwana aka shigayi dasu goggo ta rungume mama tana cewa, "sai Allah ya sadamu kuma Mama,mungode da karamci Allah yabar zumunci" "Haba ba komi Habi,ai anzama d'aya komi mukai muku ai kanmu mukai mawa,sai Biki kuma in Allah ya kaimu da rai da lafiya" Tai ma su Abba sallama on ready sun sallameta da duk abunda zasu bata,ta shiga bayan motar da Yah Ramadan zai tuk'a Rukee ma ta shiga,Mufeey ta shiga baya ana d'aga musu hannu Abbanmu ya ce "Rohee bazaki ma Yar uwar taki rakiya ba,ba haka kuka saba rabuwa ba ko kunyi fad'a" Na sadda kaina k'asa bance komi ba,goggon ta taga tace mun "bud'e kishigo kinji ko,karku biye ma shaid'an ya raba kanku" Ina dago kaina muka hada ido dashi,wani kallo da ban san ma'anar sa ba ya jefan dashi,na kauda kaina gefe Mufeeyn ta ce cikin muryar datasha kuka "please Rohee" Sai na bud'e inda Rukee ke zauna na shiga,Abbanmu ya ce "in kun dawo keda Rukayya ina son ganin ku" Kai muka daga sannan yaja motar muka tafi,tunda aka fara tafiya goggo keta mana nasiha mai shiga jiki,tana nuna mana muhimmancin zumunci da nuna ma d'an uwanka kulawa da soyayya,ta bamu takaitaccen tarihin su ita dasu Abbanmu da Abba Habibu,da dalilin da yasa suke jin duk duniya basu da kamar Abba Habibu bayan Hajja,yai d'awainiya dasu da aljihun sa da karfinsa,sadda suna kananu babansu ya rasu,har kaskare da jan ruwa a baro ya siyar yayi don suci abunci,shine baci shine walda shine gini shine duk wata sana'a mafi kask'anci ga mutum yayi don ya samu suci suyi karatu,shiyasa suke tsaye akan duk wanda yace zai raina shi to sai ida karfinsu ya k'are,"don haka kuyi hakuri da juna kar ku biye ma zuciyar ku ta kaiku ga kogin dana sani,inkuka rik'e zumunci kun tsira a duniyar nan baku da kamar juna,don Allah Rohee akula a gyara wasu d'abi'un kunji Rukayya?" Rukeen ta ce, "in sha Allahu Goggo zamu gyara muna kan gyarawar" "Allah yasa ya baku ikon hakan" Har muka iso tashar jirgin k'asan bamai cewa komi,muka fito shi kuma yaje yai musu duk abunda zai ya fiddo musu kayan su aka kaisu inda ake killacewa,ya dawo inda muke muka zauna don lokacin ya idasa, suna zaune kusa da juna kuma rik'e da hannun juna bamai cewa komi,ni kam idona a sace yana kansu,dana ga zamu had'a ido dashi zan maza in canza direction din fuskata,har aka soma neman su mutane suka fara shiga,mukai ma Goggon sallama ta shiga Mufeey tana ta hawaye sukai sallama da Rukeen,sai ta iso inda nake ta rungumeni tsam tana kukan, "ki yafeni sister in akwai abunda nai kika k'ullaceni,sai watarana" Wasu kwalla masu zafi suka zubo mun nai saurin rungumeta nima muryata tai sanyin sosai na ce, "baki mun komi ba sister na yafe miki,nima ki yafeni karki kullaceni please I'm very sorry" Daker muka rabu da ita ta koma gareshi ta rungumeshi tana kuka shiya kaita har sit d'inta,sannan ya fito muka shiga mota mukai gida,har muka iso kamar masu ciwon hakori ba mai uhm balle uhm uhm,yana yin parking muka fito tuni Rukee kamar walkiya har ta shige gida,banga alamun sassauci a fuskar ta ba dangane dani,sai na tuna inhar tai fushi to saukowar ta abune mai wahala,nima na nufi hanyar part din mu nasan ma Abbanmu ya fita saidai zuwa dare..........."Ba kiji ba" Cak na tsaya saboda dai nasan dani yake duk wajen ba kowa sai ni dashi, "Bakiji ba....?na nanata maganar,to bai san sunana ba kome?juyowa nayi ina kallon sa shima ni yake kallo da idanun sa masu wata irin kala ni banma tab'a lura da yana yin kwayar idonsa ba sai yau,saurin kawar da kaina nayi daga barin kallon cikin idonsa, isowa yai gabana ya sa hannu aljihun wandon jeans din sa ya ciro wani chan din dan hannu,waro idona nai saboda nasan nau ne kuma ko dana tashi a yau yana sanye a hannuna,na kalli hannuna na sake kallon wanda ke hannun sa,mamaki ya kamani na sake kallon fuskar sa har sannan kallona yake,inaso ince ina ka samai?ya akai yazo hannun ka?bakina yai nauyi,sai ya mik'o mun "wajen kallonmu d'axun kika yar" Ya mutsa fuska nayi, "Ban gane ba?" Juyawa yayi yana tafiyar sa ta isa da yakeyi ya ce, "Ai bazaki tab'a ganewar ba" Ya barni nan kamar sakarai, taya d'an hannu na d'aure damtsen hannuna kuma ya zare ban sani ba?tafiya nake zuwa cikin gida ina duba chan d'in,dana lura sosai ya tsinke ba kuncewa yai ba,sai na tuna sadda na juya zan fita lokacin danaje kiran sa dakinsu,naji kamar abu ya rik'eni na fizge hannun nai gaba,to why? *"Ai ba zaki tab'a ganewa ba"* Maganar ta sake dawo mun,tab'e baki nayi na wuce dakin Ummanmu, _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....15 Bamu je ga Abbanmu ba sai washe gari monday zamu je sch,munje gaidashi kamar yadda muka saba ya bamu kudin breakfast sannan yace damu, "Kafin kubar nan inaso inji miya had'aku?ban son jin bakomi kun sani ban son musu ko gardama don haka ina sauraren ku" Mukai shiru na wani lokaci,kafin zuwa can Rukee ta fara magana, "Abba ka gafarcemu,shaid'an ne yaso dagula komi kuma muka biye masa,duk da ni akan gaskiyata nake itace take son nabita akan rashin gaskiya" Ta zayyane masa komi ba rage ba k'ari game da abunda ya hada mu,kaina na soke k'asa don tun kafin yace komi naji kunya ta kamani, saida ta gama naji ya ce mata "Allah yai miki albarka Rukayya,Allah ya baki miji nagari kinji ko,tashi kije karki makara" Ta sadda kai tana ansawa kasa-kasa,sannan tatashi tai ficewar ta bata tanka mun ba,shima sai ya tashi zai barni anan hankalina naji yai mugun tashi,nai saurin rik'o k'afarsa cikin nadama na ce, "Abba na tuba,nabi Allah nabika karkai fushi dani don Allah,fushin ka masifa ce a gareni wallahi zan gyara Abbanmu" Cikin rawar murya nake maganar,saboda inhar ya tafi yana wannan fushi dani na shiga uku,bazai sake shiga sabgata ba balle ma akan wanda yafi dauka da muhimmanci ne,ahalin Abba Habibu yana son su fiye da son da yake ma nashi ahalin. Tsaya wa yayi bai jiyo ya kallan ba,hakan ya sake bani damar rik'esa gam na fara hawaye,don ba abunda ke saurin karyar masa da zuciya irin ganin hawayena,......"Abba ka yadda dani zan gyara wallahi zan gyara nayi alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba,zan yi duk abunda kake so Abba ka yafe mun don Allah" Sai lokacin ya jiyo yana fuskanta ta, fuskar sa da damuwa sosai ya ce, "zan iya yafeki a cikin ahalina LAYLA saboda iyalin Yaya Habibu dashi kanshi,ina masa kallon mahaifina ba yayana ba,idan akwai wani da zai tsine mun bayan Hajja da Alhaji ta binito Yaya ne,don haka zan iya komi akan sa in kina son zaman lafiya dani to karki kuskura a hada baki dake wajen muzguna musu,ina sonki sosai amma son bazai hanani yi miki hukunci mai tsanani ba Rohee" Hawaye nake tayi jikina yai mugun sanyi, na ce "ka yafe mun Abba,zan kiyaye zan gyara zanyi duk abunda kake so" Yai shiru na wani lokaci kafin ya dago yana kallona inata sharbar majina,ya sa hannu ya dagoni ya zaunar dani gefensa,ya shiga yimun nasiha cikin kwantar da hankali da kulawa,jikina yai la'asar ya kare da cewa, "ki tayani mu idasa wannan zumuncin,uwarku ta kasa kuma tana kokarin ta hanaku kubini,karki yadda ki shiga cikin jerin wadanda zan hukunta su" "Bazan shigaba Abba in sha Allah,alfarma daya nake nema wajenka itace, karka tilastani dole mu zama cloth da YAH RAMADAN Abba bamu jituwa,muna yawan fad'a amma zanyi kokari in ringa gaidashi in bashi girman sa,ba sai na zama cloth dasu ba" Murmushi yayi mun yace, "shikenan,na yarda na san watarana shi zai zama favorite d'inki........Aa Abba ai Mufeey ke ce masa haka,nidai mu tsaya a gaisawar ma yayi suje can suyi ta favorite dinsu" Yar dariya yayi ta manya ya ce, "naji,tashi kije kinga har ten tayi.......da sauri na suri jakata ina cewa, "Abba test gareni ten thirty saina dawo ai mun addua pls" Girgiza kai kurin yayi yana adduar Allah ya kara shirya masa zuria,tare da fatan wani buri nasa ya tabbata ba tare da saka hannun sa ba,Allah yake fatan yai masa jagora acikin burin nashi. (Tofa Abba wane burine wannan🤔) ******** Rayuwar ta cigaba da tafiya

Chapter 9 of 16