Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kawo rikici tsakanin ku,inkun had'u ki gaidashi da girmamawa yadda kike ma sauran yayunki,kinajina?" "Naji Abba Zan kiyaye" "Allah yasa,ku bani waje zan magana da Hajja" Tashi mukai muka fito saida muka isa Dakin mu sannan rukee ta zube tana ta dariya kamar ba gobe, tun bata ban haushi ha har ta bani cikin fusata na ce, "wai miye ne?" Tana rik'e cikinta take cewa cikin dariyar, "wai kina nufin Hajja bata baki dariya ba,wai in bacin tsufa huncewa zatai su daku..........murmushi na saki sosai ina cewa, "uhm Hajja ce fa,fiye da haka ma zata aika" Ta zauna tana nishin dariyar ta, ta ce "kin san miya hasala mutuminki?" "Aa saikin fad'a" "Uhm kushe shin da kikai ne fa?baki san bai son ka kushe shi ba koda wasa?ba abunda ke saurin hasala shi irin kushe" Jinjina kai nayi ina Cewa, "ohhh ashe ba dad'i,ai ke gabanki ake komi wace rana ce bai kushe ni?ni abunda yake mun ma ai bana masa irin sa,sai yau daga na d'ana?kuma fa cikin wasa nai maganar" Rukee ta ce "uhmm har yau baki gane waye Yah Rafeeq ba,toshi cikin wasan ma yafijin haushin maganarka,ke dai kawai yanzu kiyi nesa dashi don wallahi a tunzure yake,kuma abu kad'an zai saka ya karya dokar Abba,zuciya ce dashi kamar ta mutanan farko,amma kuma abu k'alilan na iya sawa ya huce nan take ya mance" "Hum shidai ya sani" Daga wannan ranar tsakanina da Yah Rafeeq ya kara tsananta, idan ya ganni kamar yaga kashi iskar data kaso ni baya kallo balle ya tanka mun,ni kuam ba nuna masa ban san ma yana yi ba,abu guda ke had'amu shine gaisuwa amma baya ansawa,ni kuma ban fasa gaidashi ban damu da rashin ansawar ba saboda Abba yace kar muyi gaba,kuma inaso sallata ta ansu to akan me Zan yi gaba dashi. Muna cikin wannan yana yin Abbanmu ya dawo daga Uk,watan sa guda da sati biyu da tafiya,daddare aka had'u babban falon dake bangaren Abba Habibu,bayan anyi dinner aka taru anan ana fira hadda Hajja kuwa,anata raha dasu Abban damu amma bamai sanya MAMa da Ahalinta,inaba su Abban ba da Hajja,itace ma keta janta da fira sai ta saki jiki suna yi tare,amma Mami da Ummanmu bamai ce mata ci kanki,Haka Najeeba da Yah Ramadan ba mai magana dasu inba Su Abban ba,yah Najeeb yana makatanta boadin yake a kano BUK, Abba ya dauko tsarabar kowa ya bashi da hannun sa murna kamar muyi me?saboda abunda mukace muna so ya siyo mana,sabbin abayas ne new design masu kyau hadda jikuna,ba wanda bai ba tsarabar ba su Umma ba yadda suka iya don hadda su MAMA ya yo mawa,don ta Abba Habibu tafi ta kowa yawa. Ya ce"baka gajiya da d'awainiya Taheer,kaida kaje aiki kuma ka b'ige da kashe kud'ad'e har haka" Abbanmu ya ce,"Haba Yaya!ina abun yake anan,kuma ai kunfi karfin komi a wajena don nai maku wannan hidimar wallahi ba komi bace, ba zan iya biyanka abunda kai mana ba nida Yah Nura (Abban su Rukee kenan)" "Shikenan Allah yakara bud'i da arziki,ya kuma kara lafiya" Kowa ya ansa da amin,Abban su Rukee ya ce "yawwa gara da Allah yasa na tuna,saida na ganku gaba d'aya sannan abun ya fad'o mun arai,kai Rafeeq rannan da zaka kai su Roohe makaranta nace yo ina Ramadan d'in mikace mun a lokacin?" Wani mugun fad'uwar gaba ta same ni,muka had'a ido da Rukee kowa cikin zullumi,shi kam ko ajikin sa ya hau bashi Ansa, "Abba ce maka nayi ya aje aiki bai yi,key d'in ma umma yaje yaba wai aba Abba Taheer Hakuri ya aje motar" Tsit kakejin Falon kowa da kalar tunanin sa,kafin Hajja ta katse shirun da cewa, "kar ka soma lafta masa sharri Rafeequ,na san ka nasan waye kai da shegiyar k'arya,waye bai san halin Ramadan ba,ai haka kawai bazai kawo mukulli yace bazai sake tuk'a motar ba,sai inda dalili" Jinjina kai Abbanmu yake alamun maganar Hajja ta shigeshi,Abban su Rukee ya ce "haka maganarki take Hajja,dole ma akwai dalilin ai haka kurin Ramadan bazai wannan abun ba" "Aa ku daina goyon bayan shi Nura,ku barshi yai magana ba lallai yana da gaskiya ba,kila rashin hakuri ya gwada ko?" Kamar jira kuwa ummanmu keyi ai wannan maganar ta anshe da cewa, "gara da ka fad'a da kanka cewa rashin hakurin sa ya nuna,tunda ranar har so yai yamun rashin kunya daga na ce bazai yuwu ace sai su Roohe sun bashi hakuri ba,tunda ba zaginsa sukai ba" D'ago kai yayi yana kallon ta da idanun sa masu kamar an zuba oil a ciki,kallon tuhuma da nuna baki da gaskiya tunda tasa ba haka ta fad'a ba.........."Ramadan" Abba Nura ya Kira sunan sa, ya dago cikin natsuwa yana kalonsa sannan ya amsa, "Gaya mun miya faru?..........watau baka yadda da maganata ba kenan Abban Rukee" Umma ta katse sa fad'ar hakan, cikin tsawa Abbanmu ya ce "maijidda idan kika sake magana anan ba tare da an sanyo ki ba ranki zai mummunan b'aci wallahi" Ranta ya b'aci ainun,ta hau huci kamar kasa magana na cinta ta kasa furta wa,don duk abunta tana tsoron fushin sa, Hajja tayi k'uta tana cewa, "duk iskancin mutum dai akwai na sama dashi,kuma wallahi ka k'i yin abunda akeso kaga karyar iya shege" Mami ta tab'e baki bata ce komi ba,su dukan kowa ta ciki na ciki ne kawai,Abba Nura ya sake tambayar Yah Ramadan yadda abun ya faru, Kanshi k'asa cikin wannan munafukar muryar tashi yake cewa, "ya riga ya wuce Abba,abar duk wani tone-tone daman Abba Taheer ne ya yanke Hukuncin cewa bazan sake kaisu Ruk'ayya school ba saboda sunyi laifi yace har sai sun bada hkr,to shine dai kamar abun baima Umma dad'i ba ta wasu maganganu da raina ya sosu har na gaza hakuri na aje mata key d'in nace taba Abba hkr ga key d'in motarsa nan" Abba Habibu ya ce "kaji ko?kaji dai ai nagaya maku rashin hakuri ya nuna,miye anan to har da zaka aje mukulli?koma miye ta fad'a ai tana sama da kai...........yi hakuri Yaya na katse ka,amma Ramadan bai laifi ba anan duk da bai fad'i maganganun da tayi har ya hasala shi ba,nasan wallahi ba kananun maganganu bane zasu sa ya hasala,ai duk mai zuciya ba zai juri a wulakanta shi ba,kuma ni ya mun dai-dai wallahi sannan hallau hukuncina akan su Roohe yana nan daram,wallahi muddin basu bashi hkr ya ya hakura ba,daga nan har su kammala secondary d'insu a k'afa za suje,in ba zasuje a k'afa ba kuma saidai su fasa zuwa makarantar" "Kash!ban so kai rantse ba, Taheer kullin ina gaya maka su Roohe yara ne,kwatanci da nasiha suke buk'ata ba zafin rai ba,kuma Ramadan yayansu ne da baka shiga cikin maganar nan ba,nasan ma shi bai k'ullace su ba kaine ka zafafa abun.........ai da yake kaine zai yadda,in wani ne ya isa ya furta cewa laifin bai kai laifi ba" Mami ta furta cikin fushi sosai,wani kallo da Abba Nura ya auna mata saida tayi dana sanin maganar da tayi, a kausashe fiye da yadda Abbanmu yayi yake ce mata, "waya sanyo ki anan?Safiya ki fita idona wallahi na kusa sallamarki saboda wannan d'abi'ar" "Yanzu Abban Rukee ni zaka ce zaka sallama akan..........idan kika sa ke kika sake wata magana anan na rantse da Allah saikin je gidanku" Ya sake fad'a cikin tsananin fushi wanda muka jima bamuga irin sa tattare dashi ba, Abba Habibu ya ce "Auzubillahi minna shaid'anir rajim,Nura miye haka?miyai zafi karka soma karka sake furta mummunan kalami irin wannan,agaban yaran zaka ringa wannan maganar" Ransa sosai ya b'aci har Huci yake yake cewa, "saboda raini da iskanci zata sanya baki kana magana yaya?wane irin abune suke son yi haka?kullin basa son a zauna lafiya Maijidda da Safiya,wallahi yaya duk wacce zata raina ka ta nemi wulakanta ka ba dai agidan nan ba,don haka in ana son zaman lafiya a girmamaka akuma mutuntaka,wannan shine" Jinjina kai kurin Abbanmu keyi,alamun hakaan yai masa dai-dai,Hajja ta ce "Allah yai maku albarka,ashe dai kun cika y'an halak wad'anda basa mance alkairi,ina goyon bayanku akan wannan hukuncin duk wacce ta nemi raina HABIBU ta wulakanta shi babu girmamawa wallahi saitabar gidan nan,don da bazar Habibun kuke taka rawa,in bacin Habibun bana jin d'ayan ku zata iya kallon Nura ko Taheer tace tana so zata aureshi,don haka duk wacce bata kiyaye ba k'ofa abud'e take" Hankulan mu sunyi tashin gauron zabi,don irin haka bata cika faruwa ba mudai bamu saba gani ba,yawan cinmu kuka muke Rukee ta rarrafa gaban Yah Ramadan tana cewa "Don girman Allah Yah Ramadan ka ya kuri,ba zamu sake ba in sha Allahu" Tana ta kuka take maganar, kamar bazai magana ba ya ce "ya wuce Ruk'ayya na yafe miki" Wani abune ya k'ulle mun ga mak'oshi,kenan ni ma saina bashi hkr wata tsanarsa ta dirar mun a zuciyata,saboda duk shine ummul aba isin komi har ake kirarin za'a kora uwayen mu gidajen su saboda su,naji duk duniya ba wad'anda na tsana sama dasu Abba Habibu da iyalin sa.......kallon da Abba ke mun yasa na tashi naje daga kusa dashi muryata da kuka na ce, "I'm sorry" A ginshire ya ansa da cewa, "it's ok" Sallamarmu akai su iyayen suka zauna tattaunawa,har iyayen mata muka fito tare dasu,muna fitowa umma ta fashe da kuka gabanmu wanda ya tada mana hankali, ta ce mana "wallahi duk wanda yai huld'd'a da iyalin Habibu ban yafe masa ba nono na daya sha" Ta shige dakinta Mami kam ta kasa magana,sai hawa numfashin ta yake Anti sha'awa ta jata suka wuce bangaren su,haka muka kwana nida Rukee kowa rai babu dad'i saboda abunda ya faru. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....8 Duk yadda Abba yai mana nasiha da kashe di akan su Yah Ramadan mun kasa masa biyayya muyi abunda yake so saboda furucin Umma,kuma muna kishin ta sosai don a ganin mu saboda su duk Abba ke mata abun da yake mata. Yah Ramadan ya koma kai mu school kamar baya,amma ko hak'orin mu baya gani gaisuwar ma mun daina sadda zai fito saidai ya same mu cikin mota,Haka zamu isa baka jin ko tarin mu wanda shi banga alamar hakan yana damun sa ba,daman kuma ko da can hakan muke dashi,ummi ke zaka gaba Nida Rukee da Najeeba a baya wadda Ban san ya akai ta dawo tana binmu ba,kila Abba ne yai mata fad'a. Wannan ya wuce ba kuma don an samu dai-daito ba anyi shiru ne saboda kashedin su Abbanmu,amma badan mun yadda zamu bisu Mama da ahalinta ba,kuma bamu da gamsashiyar hujja da zamu bada da zamu ce ba zamuyi zumunci dasu ba,kawai dai munbi ne tunda ra'a'ayin uwayenmu ne. Hutun yah Rafeeq yazo ya k'ara ya soma shirin koma wa,har sannan babu wata alak'a mai dad'i tsakanin mu,ko zamu bi ta k'ofar allura baya tanka mun,nice dai har yau ban fasa gaidashi ba rannan dana kaishi bango ya hayyak'o mun kamar zai cinyeni d'aya, a falon mami ne muna kallo shi kuma ya dawo daga ball ya shiga yai wanka ya fito ya zauna yana cema Rukee ta kawo masa black tea, tatashi kenan daga ni sai shi na ce "Yah Rafeeq ina wuni?" Zaka rantse ma baisan sani a wajen ba,banyi fushi ba na sake cewa "Yah Rafeeq ina fa maka magana" Wani k'azamin kallo ya watsa min dayai mun ciwo, raina ya sosu na ce "in bacin Abba yace kar nayi gaba dakai wallah.............Roohe kike ko ubanwa?wallahi tallahi kika sake mun magana saina b'allaki,saidai Abban ya kashe ni,ke wace irin mayya ce ne iye?bana son gaisuwar dole ne?" Sai kwallah sharrrrrr suka zubo mun, bakin ciki ya cika ni zan fara kuka kenan yaja dogon tsaki, "sakarai kawai banda kuka ba ubanda kika iya,tashi kiban wajen kafin nayi ball dake.............bazan tashi ba,nace bazan tashin ba!Yah Rafeeq ka isheni ka fitineni, ai ba kai ka kawoni nan ba,kuma wallahi in baka b'allani ba baka haihu ba,kai d'in mi?mi akai akayi ka,don kawai kaga ina yin shiru ina kyaleka zaka ringa cimun fuska,to daga yau na daina kyaleka in kace mun kulle sai na ce maka chass,ai ba tsoron ka nake ba fa, ba kuma bala'in ne ban iya ba" Mami ta fito da sauri Rukee ma haka sukai tsaye cirko cirko,suna kallona da mamakin yau nice nake masifa haka, shi kanshi daska rewa yayi daga inda yake zaune,sannan maganganuna sun sake fusata shi ainun,don ga fuskar nan tayi jajir da idonsa tashi yayi yana nuna kanshi da yatsa manuniya, "ni kike cewa ban haifu ba?kuma in nace kulle sai kince chass?" Numfashina har wani d'agawa yake saboda masifar dake cikina, na ce "ehy haka na fad'a,inhar kaji haushi ka daina abunda kake...........kauuuuuu kakeji ba zato ya dauke ni da wani ba hagon mari saida na zube k'asa saboda azaba da rud'ani, "Rafeeq!!!" Mami ta daka masa tsawa sosai,tana nufo ni da sauri saboda wani rikitaccen kuka dana saka daya kid'ima su,kuka nake sosai da sosai wanda ba zan iya cewa tsayin rayuwaa ta ba nayi sa ko aa, zallar bakin ciki ne da tsanar sa araina suka kara zugani a kukan, Rukee na lallashina Mami nayi kaina cikin cinyoyina ina ta kukan,har sannan tsaye yake don ban daina jin k'amshin sa a inda nake ba,saida na fara gajiya wa da kukan na tashi zan tafi bangaren mu,Mami ta rik'o ni. Ta ce "zo Roohe,babu inda zakije sai kin rama,a yau duk wani girma da yake dashi zai tashi abanza, tunda kai ba mutumin kirki bane Rafeeq, ashe duk irin tausayin ka na banza ne,ka bud'e wannan katakon hannun ka sauke akan fuskar yarinyar mace kamar Roohe,kaje kai mata illa ta kasa auruwa?kai ne zaka aureta ko yaya?ashe baka da imani ban saniba.............kamar almara muka ga ya zube gaban mami yana cewa, "kiyi hakuri don girman Allah Mami kiyi shiru kar aji,na rantse da Allah bana cikin hayyacina,sadda Hannuna ya kai ga fuskarta ban sani ba,raina ne ya hangula" "Dalla tashi ban waje,b'acin rai Hauka ne?to tunda har baka ga idona ba,baka ga kimar maganar ubanka ba,zanje na shaida masa inyaso sai yasan irin yadda zai dakai........." Aguje ya rufe k'ofar yana durk'ushe kan guiwar sa,daka kallin fuskar sa zaka ga zallar tashin hankali,gefe guda kuma kukan da ta ke yana sake tafarfasa mashi zuciya,da jefashi cikin mummunan tashin hankali. "Rukee zoki dauko mun wayata,in kirashi tunda ya tare k'ofar" Aiko ta ruga dakin mamin saboda itama yau yayansu ya kaita kwano,kafin Rukee ta kawo wayar ya kama k'afar mamin cikin magiya da rikicewa, "Kiyi man rai Mami,karki gaya mashi don girman Allah wallahi zan bata hakuri,ba kuma zan sake ba pls mami nine Rafeeq naki" Bata saurare sa ba Rukee ta kawo waya kenan tana ba Mamin,yai saurin anshewa yana sawa aljihu,jikinsa har rawa yake "ashe baki k'auna ta Rukee?shine kika je kika d'auko wayar?kenan ko korata Abba zai bai dameki ba" Fuskar ta a dame ta ce "yah Rafeeq Roohe fa ka mara,mari irin wanda k'ato namiji ya can canta ba mace irinta ba,,,,,"zan bata g Hakuri wallahi,ki yadda dani ban sane kalaman ta ne suka dimautani" Danne dariyar ta mami tayi tana cewa, "zoki kira min shi Rukee" A guje tazo zata tsalla ke shi ya damk'ota yana huci,muryar sa ta roma rawa kamar ba namiji ba duk ya susuce lokaci guda, "Rukee bakiji ba nace zan bata hakuri,Mami wallahi zan bata hakuri har sai ta hakura,karku sanar da Abba zai mun abunda zai jefani cikin masifa" Mamin ta ce "saketa to" Duk ya diririce,ya saki Rukeen yana ta sauke numfashi amma bai bar k'ofar ba, ta ce "ka bata hakuri har sai ta furta da bakinta cewa ta hakura kuma ta yafe ma,da kunnena nake son naji wannan,sannan koda wasa tsonaka ta sake had'a ka da ita ko bakar magana wallahi Rafeeq sai na gurfanar dakai wajen Abban ku,don haka gaka ga Roohe nan ka bata hakuri" Duk drama da ake inajin su ina kallon su,wani abun in bacin ina cikin wannan halin dole sai nayi dariya, to bana cikin mood d'in da zan dara, ina k'asa zaune ina ta sharar hawaye da suka kasa tsayawa, naci alwashin nida masa magana har abadan,inda yake ma bazan sake zuwa ba balle in ganshi. Mamin taja can gefe ta zauna cikin kushin,tana danna wayarta data ansa hannun sa,Rukee ma ta zauna tana kallon mu,jikinsa yai sanyi sosai ya dawo gabana yai zaman cin tuwo ya rasa ta ina zai fara,zaman sa kusa dani ya sake jefani cikin kunci kukana ya k'aru,matsowa yai sosai kusadani ya rik'o hannuwana duka yana saka Hankchif yana k'ok'arin goge mun hawayena, na kaudar da kaina ina k'ok'arin anshe hannuwana, "please" Ya fad'a da muryar da tunda nake ban sanshi da ita ba,ban yadda na kallai ba balle yasa ran zan saurareshi, yana rik'e da hannuna ya saki d'ayan, sark'esu yai waje guda yana cewa "I'm very sorry,I don't mean to hurt u..........cikin kukan na ce "bana son hkr" Matse hannun na wa ya sake yi,kamar zai fashe mun da kuka ya sake cewa, "please Roohe na fa ce bazan sake ba,wallahi daga yau mun zama favorite cousins,ba wanda zai kai mu kusanci da juna" Na daddage na b'alla masa hararar da bansan ma na iya ba,sakin hannun na wa yayi yana had'e nashi waje guda da sigar rok'o da magiya, "Don Allah,dan kaunar da kike ma Abbanki,inci darajar Abbanmu Roohe" Nai shiru wasu hawayen na silalo mun,yai saurin saka hannun sa ya tare su, "in sha Allah wad'anan hawayen sune na karshe da zaki zubar a dalilina, I promise u" Ban tanka masa ba,duk mukai shiru nida shi idonsa kawai ya zuba mun yana mun wani irin kallo,wanda ya fara shigata a hankali-a hankali,na k'i yadda na kalle shi amma kuma yana huda mun fatar jikina sosai, so nake na tashi na gudu amma banga hanyar tashin ba, "Roohe" Ya kirani da wata la'ananiyar muryar saa data jani ga kallon tsakar idonsa, zuciyata saida ta doka sau uku saboda abunda na ke gani cikin idonsa,mai makon na dauke idona sai na samu kaina da cigaba da kallon idonsa,wani abu na ratsa ni nan take,yana shiga jikina da zuciyataa da duk inda banyi tunani ba ma,muryar sa ta sake zama so cool ya ce "forgive me,I will never do it again please" Wani irin abu naji da bazaan iya misalta shi da komi ba, na dai sauke idona k'asa kurin kuma hawayen tuni sun tsaya,sake rik'e hannuna yayi sosai ya matsa kad'an, runtse idona nayi na bud'e kafin na kwace hannun na boye shi,ya sauke numfashi a hanakali ya sake cewa "bazan tashi anan ba har sai kince kiyi hkr kin yafe mun" Inaso nayi magana na kasa,wani abune ya danne mun halsheni,muryata ma bata fita sosai ko naxo maganar kasawa nake, "Roohe" Ahankali na dago na kallai,wani irin lumshe idonsa yayi yana sake sassauta murya, "I'm sorry plsssssss," Bansan na d'aga masa kaina ba da sauri,cikin jin dad'i ya waiga yana cewa, "Mami tayi hkr.........baiga mami ba baiga Rukee ba. Ya juyo yana kallona da wani irin murmushi a fuskar sa,dayai masifar fito da zahirin kyan sa, saurin maida kaina k'asa nayi inajin wani abu mai kama da kunyar sa, to miyasa suka tafi?kuma ban san tashin su ba ya akai haka? "Su mami sun tafi sun barmu" Kasa ansa shi nayi,illa sai jan yatsuna nake dana samu ya cika mun hannuna, Duk'owa yayi yana lek'o fuskata "zaki gaya ma mami kin yafe mun,kuma mun zaka favorite cousins?" Kai na d'aga masa da sauri don ya kyaleni na tafi, "to muje mu gaya mata a dakinta" Girgiza kai nayi ina fizgo maganar, "Aa,anjima ni zan gaya mata ba sai munje tare ba" "Why,tace fa in kaiki ki fad'a" Girgiza kai nayi "Aa nidai ba yanzu ba" Murmushi ya saki yana cewa, "ohk bani yatsan ki mu k'ulla kyakkyawar alak'a wadda ba wanda ya isa ya rusa mana ita," Kallon saa nayi ya d'aga mun girar sa,nai saurin kaudar dakaina ina ta luliyar yatsuna na kasa bashi, "Ayya Roohe pls mana" Ban San na turo baki na gaba ba,sai dai naji ya ce "wow u look so cute" Boye fuskata nayi cikin hannuna ina murmushin da ban shirya mashi ba,naji yana dariya kunya sosai ta kama ni,na mamesa na tashi na ruga bangarenmu na barshi anan,kan gado na fad'a inajin zuciyata na bugawa har yanzu tun sadda ta buga sau ukun nan,bata sake tsaya mun dai-dai ba. Ranar har Rukee nauyin ta na ringaji,duk son da tayi tamun maganar na hana ta damar, nai zama na a daki ko dinner da akacena fito cewa nai kaina ke ciwo,dan danan Abba yazo dakin yana tambayata miya jawo mun ciwon kan,na rasa karyar da zan nace masa ban sani ba, aiko ya kira Yah Rafeeq wai yazo ya dubani tunda yana shirin zama likita, kamar na fashe da kuka,saboda daman ai shi nake ma guje gujen,sai gashi Abba ya jajubo min shi. Ummanmu na gefena ta had'a mun coca oat mai zafi da madara,shi kuma ya shigo runtse idona nayi gam kamshin sa na ratsa hancina zuciyata ta sake dokawa, ya gaida ummanmu ta ce "ina tunanin ma ko fever ne,amma jikinta bazafi" Ya ce "kila stress ne umma karki damu,only paracitomal ma zai iya sata ta warware,amma van sani ba ko bayan ciwon kan akwai abunda ke damunta" "To gata nan tambayarta muji" Zama yayi gefen kafafuna yana kiran sunana, amsa wa nayi ban bud'e idona ba "sai mi bayan headache d'in" "Aa ba komi" Murmushi ya danne saboda ganin umma, ya ce "ok tashi kisha oat dinki saiki sha magani,zan ba rukke sai ta kawo miki" Kai na d'aga mishi,ya tashi yai ma umma saida safe, na sauke ajiyar zuciya na tashi na ansa oat din na fara sha,saida taga nasha maganin sannan tatashi tatafi,su Anti Rafeea suka shigo da Anti sha'awa suna mun sannu,sai ga Mami ita ma da Rukee jinai kamar zan tsere don kunya, daker nake ansa mata maganar har tatafi. Daga wannan ranar komi ya soma.! Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....9 A cikin kwana kin da sukai mashi saura ya koma makaranta wata irin kulawa yake bani,gashi inhar yana cikin sabon feeling to fa kowa gane mashi yake,don haka yanzun ma gidan ba wanda bai san sabuwar alak'ar mu ta kirki ba,kowa sai da yai mamaki ainun da ganin yadda Yah Rafeeq yake mun,yini yake agida duk abokan sa dake sintirin neman sa,daya fita bai jima wa yake dawowa,har na soma rikicewa ta fannin karatun mu,gashi mun kusa fara weac. a wajena abun bak'one don na kasa sakin jiki dashi, zai ta mun magana yana jana da fira daker nake bashi ansa,duk inda zanje yana biye damu har na gaji da magiyar ya daina binmu,makaranta ma in bacin baiga fuska ba shi zai kaimu,to wanda ke kaimun baiga fuskar tun karar sa da wata magana ba,amma kullin safiya saiya rakoni har bakin mota ba zai tafi ba har sai yaga tafiyar mu sannan. Rannan Rukee ta ce "da alamun fa kin susuta mun yayana,irin wannan rawar k'afa haka?" Murmushi kawai nayi don ban san me zan ce mata ba,ummi da Najeeba dai ba wanda yace k'ala balle kuma uban yan fad'in ran duniya. Mun soma weac da kwana d'aya yah rafeeq ya tafi,ban san cewa na soma kamu wa da irin halin daya ke ciki ba sai wannan ranar, duk yadda nake basarwa abun ya ci tura,nashige toilet d'in dakin mu na kama kukan da ban sa dame xan kira shi ba,na dauka ya tafi na fito kenan sai gashi ya shigo. "Shine Kika b'oye don kawai kar ki rakani" Idonsa yai rau rau kamar zai kukan shima,na gama gane akaina Yah Rafeeq baida wata jarumta irinta namiji, ban yadda na kallai ba na ce "Aa ba haka bane" Jingina yayi da kofa yana crossing legs dinsa yana kallona,jinai wasu hawayen sun sake tahowa nai saurin juya baya ina gogewa, nama rasa abun da zanyi, jinai yace "kibar goge hawayen ki a b'oye,ki jiyo ki fuskan ceni nine ya dace na share miki su" Makale kafad'a na nayi inajin kukan zai k'wace mun, ya tako zuwa bayana ya riko hannuna cikin wata irin murya marar amo, "zo muje kimun rakiya airport,mu sake yin bankwanan sosai" (Na manta ban Sanar daku inda yake karatun ba, yana india wata scholarship Abbanmu ya samar mashi) Kasa mashi musu nayi,na dauki hijab d'ina muka fito,anan main falon gidan gaba d'aya kowa na nan har su Abbanmu,kasancewar weekend ne ba aiki ba school, Mami tana ganin mu tayi murmushi don

Chapter 5 of 16