Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan iya cewa tafi kowa shiga farin cikin alakarmu dashi, Abba Nura ya ce "saida ka fiddo ta kenan," Kaina k'asa shi kuma ya sosa kai ya ce "Abba ai bazan tafi bamuyi bankwana ba" Murmushi kawai yayi Anti Rafeea ta ce "duk bankwanan da akai dazun da sauran kwanaki bai yi ba kenan" Harara ya sakar mata,yana cewa "kewai miye naki aciki?" Anti sha'awa ta ce, "ai kai baka son gaskiya,ni wai mike tsakanin ku ne farat d'aya ka zama haka..........."mami ki shiga tsakanin mu da wannan yarinyar,nidai ai ba sa'anta bane da zata ringa gaya mun haka" Dariya duk aka kama yi mashi,saboda angane dai borin kunya yake bai son a gane miyake boyewa, "Bari muje muyi ma Hajja sallama" Yajani muka tafi nidai na kasa cewa uffan,jikina duk amace yake ainun,bamu jima sosai ba wajen Hajja muka fito Abbanmu ya ce muje bangaren Abba Habibu yai masu bankwana,Yah Ramadan xai kaishi Airport d'in. Nida shi duk bamuji dad'in maganar ba,amma bamu isa muce aa ba,koda muka je bangaren nasu Fuska ba annuri yake musu sallama,su kam basu damu ba saima nuna jin dad'in su suke yazo musu sallama, Mama tatashi ta shiga ciki ta fito da wata leda tana cewa, "ga wannan Rafeeq,kila yai maka amfani Rahma ta sani nayi mata shi zasu zo jibi", donuts ne sutu-sutu mai wata madara-madara a ciki,sai dambun kifi mai yawa. Hakan bai sa ya saki ransa ba ya ansa yana cewa, "Angode" Bata damu da yadda ya ansa ba karsashi da nuna jin dad'i ba,ta rakomu har wajen mota inda sauran yan gidan ke tsaye,Abba Habibu yana ta mishi nasiha ya kula da kanshi ya rik'e ibada ya kuma tsaya yayi karatun sa hankali kwance, "karatun ka na son natsuwa da kwanciyar hankali,Allah ya taimakeka kaji yarona" "Amin" kawai yace ni har na soma jin kunya ma,don ba dad'i irin abunda yake musu. Daga ni sai shi sai Yah Ramadan,duk baya muka zauna shi kuma yana tuk'i,muka dauki hanya sai Airport,tunda muka tafi munyi shiru yak'i sakin hannuna kamar zan b'ace mashi, saida mukai nisa da gida sannan cikin sanyin murya ya ke cewa kamar mai baya son aji, "Wane irin alk'awari zaki mun kafin in dawo?" Kaina k'asa na kasa cewa komi,ya sake matsoni yana cewa "kinji Rooh" Har raina sunan daya kira ni dashi ya mun dad'i, daker na iya cewa cikin siririyar muryata "ni ban san wane irin alk'awari kake nufi ba" Iska ya busar yana cewa, "badan tafiyar nan ta zamar mun dole ba,wallahi Rooh ba inda zani inbarki,ji nake kamar zam bar duka rayuwata anan" Saurin kallon sa nayi yajin jina mun kai, "sosai ma" Na rausayar da kaina cikin rashin abun cewa, ya katseni da fad'in "in so ki kasance tare dani a zuciyarki har inje in dawo,sannan inaso ki nisanci ko wane namiji don duk duniya ba wanda zan iya barma ke,nasan kin gane mi nake nufi please Rooh,kimun wannan alfamar zan jima ban dawo ba amma saboda ke zan ringa zuwa duk bayan shekara daya da rabi in ganki in koma,karki ba wani dama akanki koda kun gama weac kima Abba magana kina son nursing,kinga ni dr ke kuma nurse ko had'in bai miki ba?" Murmushin na saki ina kaudar da fuskata,watau duk kewaye kewayen sa dai so yake yace sona yake kuma duniyar nan baida burin auren kowa saini, "yes ban da wani buri a rayuwata illa na mallake ki,ban san taya zan sanar dake ba amma cikin raina kece kawai muradina,duk wani abu da nake miki a baya ba har raina bake yi ba,kawai inayi ne donki maido hankalinki kaina,ganin zan tafka kuskuren da har Abada bazan iya gyarawa ba yasa na dawo hanya, ina fatan babu wani abu da zai mun katanga da cikar burina kinji my Rooh" B'oye fuskata nayi saboda wata irin kunyar sa nakeji matsananciya, ga wata irin kewa da nakejin tana ratsani ko ya zan kasance babu shi a cikin gidan?har muka iso airport ban iya ce masa komi ba,shine yake ta kokarin ganin ya fayyace mun abunda ke cikin ransa,koda yai parking saiya ki fita ya dai bud'e kofar inda yake zaune ya fidda kafarsa guda yana danna wayarsa. Dogon tsaki Yah Rafeeq yaja ganin abunda Yah Ramadan d'in yayi,ya ce mun "kar ki dauka bana nan,ki dauka always ina gida kuma zaki ganni,zan ma Mami magana a siya miki waya I promise u zamu ringa video call at least twice par day, yayi miki hakan?" Na d'aga kaina kurin saboda jinake zan kuka, har na kasa controlling hawayen suka ringa silalowa, muryar na rawa na ce "ka ce zaka ringa zuwa after one year" Murmushi ya saki mai cike da tsananin bege da soyayya, ya rik'e hannuna sosai ya ce "in sha Allah,kodan farin cikin ki zan takura Abba har sai nazo" Ya shiga goge mun hawayen da Hanky d'insa, yana cewa "oya inhar ba kina so na tafi cikin damuwa ba give me smile" Ban san sadda na sakar mashi murmushin ba,yaja iska yana cewa "u are very beautiful Rooh,ban tab'a fad'a miki ba yau na fad'a,kina da kyau mai rud'a duk wani namiji,saidai wanda yasan daman bazai same ki ba,ki kula mun da kanki kinji ko" Daker muka rabu saida yaji ana sanarwar neman su sannan ya bud'e motar ya fita yana d'aga mun hannu,kuka ya kwace mun don alokacin ji nake duk wani jin dad'i na ya kare tunda bai nan,haka muka kamo hanya nida shi kamar sabbin kurame,har gara ni inata shashshekar kukana,shi kam banda tuk'i ba abunda yake kamar daman tukin aka halliceshi yazo duniya yayi,ni ban tab'a ganin mutum irin sa ba kwata-kwata rayuwar sa babu armashi,ba walwala babu farin ciki sai fad'in rai da girman kan tsiya, da tsabar k'azanta wannan dalilin ke sake samun jin tsanar sa araina,bana son namiji babu gayu babu kula dakai,.........ban san sadda naja wani dogon tsaki ba,ai ban idasa jaan shi ba naji wani uban burki ya taka,har kaina na bugar kujerar gaba,a mutuk'ar fusace naga ya bud'e bayan motar inda nake cikin zafin nama ya finciko ni, muryar sa ta wani irin disashe cike da b'acin rai matsananci ya ce "uban wa kike ma tsaki?" Jinai zan saki fitsari a inda nake,tunda nake rayuwata a gidan magana tafatar baki bata tab'a had'amu ba in banda gaisuwa sai yau,cikin tsananin tashin hankalin dana ganshi a ciki yasa na rud'e don ban tab'a jin tsawar data gigita tunanina ba irin yau,idon sa har tsoro ya bani kamar yai shaye-shaye ya bugu,sun wani rikid'e sun juye ban san ina cewa "Aa....Aa ni.....ni banyi tsaki.....banyi maka tsaki b...........mahaukaci kika d'aukan komi?ashe zaki kwana nan" Muryata kerma kurin take na soma girgiza kai, cikin tashin hankali "ka yarda dani ba dakai nake ba,ban san nayi ba don girman Allah ka maidani gida,wallahi bazan sake maka tsaki ba,kuma ba dakai nake ba kubce mun yayi na rantse da Allah Yah Ramadan" Babu sassauci ko k'adan a fuskar sa,ban tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba,inhar ya barni a dajin nan shikenan bani ba sauran wata rayuwar jin dad'i,yadda ake kidnapping d'inan ana kashe mutane,aini tawa ta k'are. Cikin kakkausar murya ya ce, "shiga muje, wallahi na kuma jin tarin ki saina tsaya na zubar dake anan ba abunda ya daman" Aguje na fad'a motar ina kerma, ya ce "fito dalla shiga Gaba uban waye driver ki anan?" Jikina tsuma kurin yake na zaga na shiga,sannan yaja motar muka cigaba da tafiya,mai makon gudun da yake yi da farko sai ya koma yin tafiyar kamar wanda ba shi da lfy,sikiyarin ma daker yake sarrafa shi,ni dai kamar ruwa ya cini nama kasa kallon fuskar sa,mugun tsoron sa ya dirar min tare da tsanar sa mai yawan gaske. Abun kamar wasa tafiyar ta nemi gagararsa,wani irin burki yaja yana dafe kirjinsa,da fari na dauka ko na d'an lokaci ne amma naga mutum ya bud'e murfin mota ya zube k'asa ba numfashi,wata razananniyar k'ara na fasa na fito jikina kerma kurin nake,wace irin masifa ce wanan na shiga ukuna. Jijjigashi nake ina kiran sunan sa ba alamun zai tashi,ko ina rawa yake jikina sosai kuka kurin nake,don gani nake ya mutu kawai kuma ban san wane irin bayani zan yima yan gida ba,banda waya ban ma fito da ko hanky ba ga hanyar ko kare babu,gashi rana tatafi zata fad'i la'asar tataho duk da ban duba time ba,tsabar tashin hankali fitsari naji yai mugun matsata, na fara lalubar aljihun sa naji wayar sa yar karama nai saurin daukota na saka no. Din Abbanmu,bugun farko ya dauka "ke Roohe ina kuka tsaya haka,inata neman ku ban samu lafiya kuwa.........kuka na rushe dashi sosai "Abba ya mutu,gashi nan ya zube a titi ban San Miya samai ba,kawai......kawai naga ya fad'i" "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,bar kuka kuna ina maza gaya mun" Na soma waige waigen inda muke,na samu wata alama na gaya mashi wajen,yace gasunan zuwa yanzu na zauna gefen sa ina kukan,, "ni banga abun da ya faru ba,ko dama baka lafiya?na shiga uku ban tab'a ganin an mutu gabana ba,Allah kasa ba mutuwa yai ba. Mom Muhseen &Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....10 Cikin d'an k'ank'anin lokaci su Abba suka iso shida Abba Habibun,sai naji hankalina ya sake tashi ainun ganin yadda aka kin keme shi kamar gawa aka sa amota,su duka hankalin su a tashe yake jinake kamar zan zauce tunda nake ban tab'a ganin an mutu gabana ba,hawaye kurin nake don ba batun wani abuba ina cikin kid'ima da tashin hankali. Driver akai ma waya yazo ya dauki motar ya maida ta gida, dani suka wuce asibitin da ake kwantar damu in wani bai da lafiya anan gida,gefe guda na tsayaa inata hawaye su Abba ne keta shege da fice har aka anshe shi aka shiga dashi emergency,su ka dawo inda nake suka tsaya Abba Habibu yai shiru kanshi k'asa,duk sai naji ya ban tausayi don kuwa kowa yasan duk cikin zuriar sa ba wanda yake so kamar yah Ramadan,amma yana kokarin dannewa bai nuna ba. "Miya faru a hanyar taku har haka ta kasance?" Abbanmu ya jefeni da tambayar ina cikin wannan halin,kan in bada ansa Abba Habibu Yace "haba Taheer,tana cikin kid'ima har tuhumar ta zakai?taya zata san wani abu?" "Tare fa suke Yaya,kaga kau ai dole tana da masaniyar wani abu" Sai yai shiru bai sake cewa komi ba,Abbanmu ya sake kallona da son karin bayani,hawayena suka k'aru na soma cewa "wallahi ban san komi ba,lafiya lau muka isa airport ya sauke Yah Rafeeq,muka kamo hanya muka taho,to.....to....to......shine sai kawai naji ya taka burki,ya dafe kirji da cikinsa,sai......sai.....kurin naga ya bud'e k'ofa ya fad'i k'asa,wallahi Abba iyakar abunda ya faru kenan" Ina ta sharb'en majina,shiru bai ce mun komi ba zuwa can, sai ga Abba Nura ya iso shima cikin tashin hankalin, "Mike faruwa ne Yaya? Taheer lafiya?Hajja ta kirani tana kuka wai Ramadan yai hatsari,meeting muke dole na dauki excuse nataho" Ajiyar zuciya Abbanmu ya sauke, Abba Habibu yace "ka kwantar da hankalin ka insha Allah ba matsala" "Allah yasa" Ya fad'a yana zama bisa kujerun dake wajen, Abbanmu yake gaya mun bayanin da nai masa,inaji suna tattauna maganar da tunanin ko yana da wani ciwo ba wanda ya sani,shine ya tashi farat d'aya haka. An dauki tsawon lokaci likitan dake kanshi da nurse basu fito ba,har na gaji da tsayuwa na zauna inata masa addua bakin iyawata har raina banaa son ya mutu,koba komi d'an uwana ne na jini akwai kauna ta jini tsakanin mu,duk da ba jituwa muke ba. Cikin taimakon Allah sai gasu sun fito su Abba suka tare shi da neman ba'asin jikin nashi, yace su isa office hadda ni aka bishi don son jin meke damunsa da ya sashi wannan halin, "Karku tashi hankalin ku ya samu,yana bacci ne a halin yanzu amma ulcer yai mishi mugun kamu sosai,don gaskiya sai ankula da abincin sa yana zama da yunwa,kuma itace babbar illa ga mai irin wannan ciwon,in aka kiyaye komi zai zama lfiya lau,in sha Allah zuwa gobe kila na sallameshi in naga yana yin jikin nashi," Hankalina ya kwanta na dawo hayyacina,duk da banga gamsuwa ba afuskar iyayen nawa,bama kamar Abba Habibun duk da bai furta ba amma ga damuwa nan sosai akan fuskar sa, shiga mukai inda yake muka duba shi yana ta bacci ga drip na shiga jikinsa,lokaci d'aya har ya rame a fuska. Nan muka bar Abbanmu nida Abba Habibu da Abba muka koma gida,da ace da kara da zumunci Ummanmu ko mami wani xai zo ya zauna dashi,ba dole sai Mama ba to babu kod'aya shiyasa dubiyar ma saida su Abba sukai masu jan ido sannan suka zo,shima a ginshire sukai masa yajiki,da yake shima gwanine uffan bai tofa musu ba. Inaji maman na mishi magana, "Ramadan ana maka sannu baka ansawa?" Saima ya rufe idanun sa kamar baiji ba,aiko suka kama surfa masifa da muka dawo gida,nidai uffan bance ba tunda bai mutu ba ai da sauk'i, na cigaba da hidimata. Ammin kausar sun sauka Abuja kwatsam,watau Anti Rahma wadda Yah Ramadan ke bima wa,duk halin ko inkular da muke da ita bai hana tayo mana tsaraba ba,mu duka yan matan har su Anti Rafeeq da Anti Sha'awa,sannan tabi uwayen mu har d'akunan su ta gaidasu,bata damu da shan murr da ko inkular da suke da ita ba,mace ce mai kirki duk abuna dole na fad'i gaskiya,ta biyo halin uwarta duk abunda zakai mata na sharri bata tab'a maida maka da sharrin nan,saidai Alkairi,kuma indai zata zo to hidima take yoma su Abbanmu sosai,dankalin turawa ne doyace manja ne da su fruits,jibgi guda haka take kawowa. Indai tazo to kowa sai ya gane,mace ce mai alkairi ga kowa don a wajena tafiye mun Yah Ramadan da sauran yan uwansa,su kam ai yan iska ne miskilan banza da wofi. Ita dasu kausar d'in suka zo kasancewar sun samu hutu acan kebbi inda take aure,ba laifi mijin nata yana samu d'an kasuwa ne ita kuma tana aiki da wata makaranta secondary dake cikin garin kebbin,Ammin kausar duk gidanmu ba mace mai kirkinta,duk hassadarka dole zaka yaba mata da irin son zumuncinta,don zan iya cewa halin su Abbanmu ta dauko na son zumunci da yan uwa,duk safiya in har tazo to har falon Abba zataje su gaisa susha fira duk yadda umma ke had'e rai tana shan kunu bai dame ta ba,haka Mami ma duk shak'a shak'enta bai damu Ammin kausar ba,su gama firar su tatashi abunta. Saidai bata daukar raini ko kad'an,zata sake maka sosai amma bata yadda da raini ba ko iskanci,tsaf zata ci ubanka a zauna lafiya,shiyasa muke shayinta ainun bata daukar wargi,har gara Yah Ramadan zai nuna baisan kana yi ba,amma ita kam nan take zata gurjeka. Wannan kenan.......... An sallami Yah Ramadan daga Asibiti wanda saida ya kwana uku sab'anin dayan da Dr yace zaiyyi,ya warware kamar bai ba haka nan nima na share komi ya wuce kamar ba ayin ba,ba ruwan sa da sabgar kowa haka muma ba ruwan mu da sabgarsa da ta yan uwansa,in baa Abba Nura daya sanya doka ba don dole kowa yaje sashen Abba Habibu ya gaida su mama in gari ya waye,to inba hakan ba babu mai shiga huld'arsu,sai fa Kausar da ummi da suka jone kamar wasu k'awaye,duk fad'an ummanmu da zage-zagen ta ta saka musu ido,saboda ummin taki bata hadin kai hadda kukanta cewa zata gaya ma Abba,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "watau har wuyanki yayi gwab'in hakan ko ummi?saboda wad'ancan matsiyatan zakice zaki had'ani da ubanki?to Allah ya baki sa'a" Daga nan bata sake mata magana ko hanata huld'a da Kausar ba,nida Anty Rafeea dai kadaran kadahan,har gara ma ita don ni gaskiya bazan b'oye ba bana yinsu haushin su nakeji,yadda sun hana ummanmu da Abba zaman lafiya inhar suka samu sab'ani to akan su Mama da Abba Habibu ne taya zanji ina son su? Bangarena da Yah Rafeeq kuwa ba a magana don kamar yadda yace in dauka yana gida hakan ce take faruwa,always muna tare a waya wadda Abba ya siya mana nida Rukee,tare da kwakkwaran warning,ranar ban iya bacci ba kusan raba dare mukai muna magana dashi,jina nake cikin wata sabuwar duniya wadda ban tab'a shigarta ba,wata irin Soyayya ce mai ratsa dukkan zuciya da gangar jiki muke ma juna,son juna muke kamar Allah don juna ya halicce mu,kulawa muke da juna ainun walwalata tak'aru sosai hakaa fara'ata da maganata,ya zamana inhar ina gida to bakin kowa ma bazai huta ba,wani irin farin ciki nake samu dagaa Yah Rafeeq a yadda muke ji da juna ko k'uda bama so ya shiga tsakanin mu,a hankali a hankali gida aka fara fahimtar halin da muke ciki,wanda wannan abun ba wanda yakai su Ummanmu da Mami jin dad'in shi,har Rannan Anti Rafeea ta ce ma ummanmu. "Umma na dauka fad'a zaki ma Roohe akan turb'ar da take son d'ora kanta tun yanzu,ko ni da nake cikin shekara ta biyu a jami'a Abba bai bani damar yin saurayi ba balle Roohe da ke zana weac,a ganina ki dakatar da ita kafin abun ya shafeki in Abba yaji" Ina gefe ina karatun neco da muka kusa gama wa,time to time ina chat da Yah Rafeeq, raina ya sosu sosai da maganarta ina jiran Umma tace wani abu kafin ni ince, "Ai Rafeeq d'an cikin gida ne Rafeea,sannan d'an uwanta na jini yadda ba za aima Roohe Aure yanzu ba shima babu mai yi masa Aure sai ya kammala karatun sa ya samu aikin yi,kinga kenan zasu iya jiran juna har sadda ya dace suyi auren,sannan dukan su idonmu akaan su sab'anin wani na waje da ba ganin sa zamu ba musan abunda ke faruwa,ki kyalesu su so junan su ni abun yayi mun,daman kullin burin mu kenan nida Safiya Allah ya had'a kansu to gashi kuma,don haka kiyi musu Addua" Bata ji dad'in maganar ba Amma bata isa sake cewa komi ba akai,jin hakan da umma ta fada sai bance komi ba,na tashi na bar falon na wuce dakin mu sai eleven na gama karatun,muka dasa video call dashi har Rukee ta shigo. "Allah dai ya sassauta muku wannan k'unatar junan,haba ko gajiya bakwayi" Harara na wurga mata na ce masa, cikin shagwab'a "Yah kayi ma qanwarka magana,nidai yanxu ba tsarar ta bace ato" Daga inda Rukeen take ta hangame baki tana kallon,shi kuma ya ce mata "Ruk'ayya zamu yi mummunan sab'awa dake,ki fita idona Allah ko baki saj Antyn ki bace yanzu"? Nai mata gwalo ina fari da idona, ta ce "Sorry Yah" "Sorry for your self" Ficewa tayi don naga ranta ya b'aci,ni kuma ba dan haka nayi ba nasan zamu shirya,na cigaba da video call d'ina sai d'ayan dare muka rabu,asuba nayi mukai waya dashi sai six muka rabu saboda shirin makaranta da zanyi,shi kuma yana da aji karfe bakwai zai test. Sallama nayi cikin main falon na Abba Habibu,babu kowa tsit kakeji sai k'amshin turaren wuta dake tashi a boner,cikin shirina makaranta uniform ne jikina sun sha guga sosai, don kullin sai munyi wanki da guga saboda karma a raina mu,falon Mama nayi ma tsinke don nasan duk suna can,ba ka cika samun su a babban falon ba inba dare bane,har na d'ora hannuna akan k'ofar naji maganganun su,Mama ke cewa "nidai inhar na isa dake Rahma kar ki sake ki fara tunkarar wani da wannan maganar,ba ruwanki naki ido ne ance abunda ba ruwanka yafi dad'in kallo,inma kinje kin tofa wata magana takice zatai zafi,ni duk abunda zai kawi cecekuce bana so tunda dai ga yadda mutanan nan suka dauke mu" "Yawwa Mama gara hakan,Allah ko Ammi ki fita maganar nan inba ke bama wallahi mudai nan babu mai zuwa yayi ta,har kuwa Yah Ramadan" Cewar Najeeba da alama breakfast take a sadda take maganar, Anti Rahma ta ce "Mama ni bana son irin wannan wallahi,ai na dauka mu da muke manya mun isa mu fad'a aji?taya za'a zuba ido yarinya kamar Roohe ace tana soyayya mai zafi irin wannan,kuma ma ba aure aka tashi yi mata ba,sannan shi kanshi yaron ba aure ne ke gabansa ba karatune saiya gama ya samu aabunyi kafin nan,ai su Rafeea ne ya dace ace suna wannan soyayyar suma da sunan aure za'ai next" "Nidai na haneki,tunda dai iyayen maza ba wanda ya sani kifita maganar nan,inma sun sani su zasu yanke hukunci bake ba" "Shikenan Mama nayi shiru tunda bakyaso nai maganar" Jinjina kai kurin nayi watau duk akaina ake wannan muk'abalar,uhmm walahi ko sama da k'asa zata had'e bazan rabu da Yah Rafeeq ba,naja tsaki na tura k'ofar a hankali tare da sallama, Duk suka ansa ni kuma fuska babu walwala a cinkushe na gaida Mamar, "lafiya lau Roohe har an shirya kenan?" "Ehy" "Ammi ina kwana,daman Abba yace yazo mutafi time yana wuce wa" Yadda nai maganar zaka d'auka wanda akace yazo d'in baya wajen,amma ban kalli inda yake ba balle na tanka masa,Ammin ce ta ce "lafiya lau Roohee y'an mata,amma ai naga bani ce zan kai kun ba ko?sannan kila kin san sunan sa don haka kije ki nemo shi inda yake saiki isar da sak'on naki" Tayi maganar ne cikin sakin fuska,amma kuma cikin maganar akwai bacin rai aciki,kamar zan ja tsaki sai na fasa nai shiru bance komi ba,kuma ban tafi ba na kuma kasa yin abunda ta ce,tunda nufinta inyi masa magana da bakina..........."Kinga jeki abunki gaya nan zuwa" "Aa MAMA karki shiga maganar nan don Allah,ki kyale ni da ita kawai" Sai naji kwalla ta cika idona saboda bacin rai,mamar bata sake magana ba ta kyale mu wani k'ullutu yazo mun wuya bakina na rawa na ce, "Kazo ka kaimu inji Abba time na wuce wa" Da rawar murya nayi maganar wadda kiris nake jira na fashe da kuka,kamar ma baya wajen nayi maganar mama ta sake cewa "Ramadan kanaji ai" Uffan baice ba Ammin ce ta sake cewa, "kila ba a rad'a masa suna ba,kila duk gidan nan shine wanda baida suna............"Rahma!" "Aa Mama ki bari kawai" Ta sake katse mamar da fadin hakan,hawaye suka ringa silalo mun na bakin ciki labbana na rawa na ce "Yah Ramadan Abba yana........sai kuka ya kwace mun na fita aguje ina kukan sosai don bakin ciki kamar zai kasheni. "Miyasa kike haka Mama?bayan ni duk gidan nan sama yake dasu,akan ke ba zasu bashi girma ba?sai ki bada goyon bayan a raina shi?kaima hadda kai daka zuba ido kana kyale duk ubanda yai maka iskanci,har nawa Roohee take da zata kasa risina ma Ramadan,?sanyin halinka yai yawa wallahi ni bazan dauki wannan abun ba" Ya gama kalacin sa ya mik'e ya ce, "Na tafi Mama,daga can zan wuce wurin Abulkhair kila yau zan fara aikin nan" Mamar ta ce, "Ma sha Allah,ubangiji yasa albarka ya kuma tsare ka ya bada sa'a sai a rik'e amana duk da bana jin ka RAMADAN saidai inyi maka tuni" Ammin Kausar ta ce "wane aiki ne haka Ramadan?" D'an murmushi yayi wanda yana jima wa baiyi ba,sai ya kara masa wani irin kyau sosai yace "mama tai miki bayani,Najee muje ko" Yai gaba ita kuma ta ruga ta sanyo hijab d'in kayanta Uniform iyakar guiwar hannu take tsaya musu,saboda rigunan har guiwa suke,bayan tafiyar Ramadan Ammin kausar Ta ce "Wane irin aiki ne haka mama,ni da ina can nida Baban yara muna kokarin bud'e masa boutique yafara dashi,don har ya tura kudin kayan shi dubai" "Nidai Addua nake masa kullin,duk inda arzikin sa yake Allah ya kaishi can,ya kuma zab'a masa mafi alkairi saboda zaman sa haka yana damuna,shiba ga koma wa makaranta ba shiba ga wani aiki ba,kina gani karatun ma daker aka gama Rahma,ki barsa yaje nan d'in in munga ana samun wani abu ba sai yatafi kebbin ba,in kuma sama-sama ne sai ya tafi Allah ya kiyaye" Tana maganar ne duk rauni da damuwa sun bayyana tattare da ita, Ammin kanta duk damuwa ta nuna a fuskarta, taja ajiyar zuciya cikin sanyin jiki ta ce "Abun nan yana bani mamaki Mama,duk cikin gidannan bana jin ko Roohee da Rafeeq zasu nuna ma Ramadan kwalwa da basira,kina gani duk abunda ya shigema Abban yara duhu kan kasuwancin sa shine yake bude masa komi,kina gani duk semester baida c.o ba a tab'a kama shi da wani abu na rashin kokari ba,amma kuma akai ta maida shi baya,kullin abun nan yana raina" "Bakomi Rahma,jarabawa ce kowa da kalar tashi in sha Allah komi zai wuce" "Allah yasa,Allah ya nuna mana lokacin lafiya" "Amin" ********* Da Abba mukai karo na fito da gudu ina wannan kukan bakin cikin,suna tare da umma hankalin su ya tashi ya rik'oni yana tambayata ko lafiya, "Minene Roohee?lafiyarki kalau,daga

Chapter 6 of 16