ina kike haka?kiyi shiru kimun bayani mana,ina shashsheka da jan numfashi daker nake maganar,umma ta rungumeni tana shafa kaina.
Falo muka zauna tare dasu nan main falon mu,umma ke cewa "nasha gaya maka mutanan nan ba kaunar mu suke ba,karma ace Roohee kamar su kunna wuta su jefata ciki saboda ganin yadda Allah ya kyautata halittarta,bayan haka kuma kafi sonta kafi yimata hidima fiye da kowa,shiyasa suka kafa mata k'ahon zuk'a to gaskiya ni nagaji idan ba zaka sama mana wani gidan mu koma ba ni zan tashi nida y'ata..........y'arki kika ce?ashe da ita kika zo gidan ban sani ba?"
Tai shiru bata tanka ba,nidai ina kwance kan cinyarta nai lamo,har sannan ban daina hawayen ba zuwa can ya ce mun, "Roohee"
Na tashi ina ansawa murya a shak'e, "tashi kije ki kira Rukee ku wuce mota kafin ya fito,ban son koke-koke kiyi shiru ya wuce hakanan,anshi nan kud'in break dinku yau na kara muku ma"
Ya zaro kudi ya kirga yana bani, "kiba Najeeba budu biyar,Rukee ma haka saiki dauki goma ke"
Sai naji sanyi yadda yaketa lallashina saina sauko daga fushin,nai masa godiya na tafi sannan ya koma ga ummar,fuska ba annuri ya ce "idan kika sake furta irin wadannan maganganun gaban yarinyar nan wallahi maijidda ranki zai b'aci,ashe bakida hankali ban sani ba,wace irin dauka kike so tai musu?kina so ki dakile zumunci tsakaninta dasu?nai imanin cewa izgilanci da iya shege tai musu wanda na tabbata Rahma ba zata dauki hakan ba shiyasa tai mata haka,don haka ki kiyaye kalamin ki,kuma gida ba zan nemo ba inanan tare da yan uwana har mutuwa ta rabamu,inkinji zaki zauna bismilla in kinji baki iya zama k'ofa abud'e take kije duk inda kike so,saidai bada y'ata ba wallahi"
Daidai nan muka fito ni da Rukee,tai masa godiya sannan muka wuce wajen motar,umma ranta ya b'aci sosai ta ce "ni zaka wulakanta akan yan uwanka Taheer?duk irin karamci da mutuncin da nai maka a rayuwa...........duk abunda kike k'ok'arin cewa kinyi mun baiyi rabin rabin abunda Yaya Habibu yai mana ba shida Matarsa, don haka zan iya zabarsu akanki............alamun shigowa yasa yai shiru har sadda mai shigowar yai sallama, "Ah Ramadan ne?"
Inji Abban yana sakin fuskar shi sosai, Ramadan d'in calmly ya na shafa kanshi ya risina ya gaida shi,sannan ya ce "umma ina kwana"
Tsaki taja tatashi fuuuu tabar wajen kamar kububuwa, binta sukai da kallo harta bace, Abban cikin jin kunya da takaici ya ce "kayi hak.......haba Abba miye na bani hakuri anan,bakomi ai ansaba"
Abban yaja iska ya fesar ya ce, "Allah ya kyauta"
Ramadan ya amsa da "Amin,daman yau ne zan fara zaman shagon da mukai magana dakai rannan"
Abba yad'an dafe kanshi cikin damuwa, kafin ya nisa ya ce "Kayi hakuri Ramadan,Allah shine shaida ta ina bakin kokarina akan neman aikin ka,ban tab'a neman abu mai wahala irin aikin ka ba Ramadan,damar tak'i zuwa"
Murmushi yai yana cewa,"bakomi Abba,ai komi lokaci gareshi"
"Haka ne,Allah ya kawo mana wannan lokacin to"
"Amin Abba,bari na wuce kar su makara........Ramadan!"
Abban yakira shi,ya jiyo yana sauraren shi "ka kara hakuri da k'annan ka don Allah"
Yana murmushi ya ce "to Abba"
A haka suka rabu yazo yaja mu muka tafi,tunda muka dauki hanya banda tsaki ba abunda nake,Har muka so yin Fad'a da Najeeba abunda banmu tab'a yi va kenan,duk abunda zanyi bata saka baki kallo ma ban isheta ba,yau kila abun ne ya cika ta.
Da farko Rukee ta ce "wai miye ne kika dame mu da tsoki kina bakar magana"
"Kyale don Allah,ai kin san dai ba dake nake ba,ni har an isa ai gulmata uhm duk gulmar mutum kanshi zata k'are bai isa akomi ba wallahi,yana ji yana gani za'ai komi abarshi"
Naita maganata ina jan tsaki can Najee ta fusata ta ce, "ke dakata kiji,na gane bada kowa kike ba sai nida Yah Ramadan,to duk iskancin da zaki kiyi da sa'anki inba haka ba wallahi zaki rasa halshen ki,don Yah ba abokin yayanki bane balle ke banza karan kad'a miya.........nan fad'a ya kaure tsakanin mu na cacarbaki,na soma masu gori kala-kala har dai Rukee saida taji ba dad'i,Najeeba ta kama kuka saboda maganganun sunyi zafi,nake ce mata.
"Aikin banza da wofi,da bazar wa kuke rawar zance ci da sha da sutura da wajen kwana duk nauyin Abbanmu ne,banda kashi da tusa babu abunda kuka iya yi,har kina da bakin magana ke a wa?ai in ma ana maganar tunk'aho kidaina yi da Abbanku don kuwa babu abunda zai iya tsinana muk.............nan ne naji ya taka wani mahaukacin burki,zaka dauka hatsari zamuyi, yana yin dana ganshi radda muka raka Yah Rafeeq airport yanzu yafi lokacin, fuskar ka kamar wani dodo saboda rikicin bacin rai, yana bud'e motar ya dauke ni da wani mahaukacin mari saida naga wata wuta ta gilma mun,kafin ya sake dauke ni da wani marin duhu ya mamaye idona na wucin gadi,azabar danaji tunda nazo duniya ban tab'ajin irinta ba.
Mom Muhseen &Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....11
"Duk abunda zaki kiyi mai isarki amma akul d'inki kika zagi iyayenmu,wallahi xan iya sabautaaki akan wannan!kiyi mun zan dauka kiyima kowa ma amma kashedenki da iyayenmu ba tsararrakin ki bane, shashasha ballagaza akuya"
Ya salam,kwatanta irin d'acin dake cikin mak'oshina babban abune, ni kadai nasan irin ciwon da zagin sa yai mun,don marin ma bai mun ciwo irin wannan zagin ba,wani irin rikitaccen kuka yazo mun ban iya tare sa ba dole na sake shi ya fito,don idan na rik'eshi zai iya sumar dani..........anshi nan jeki hau napep ki wuce makaranta"
Yaba Najee kudi ita kadai tana hawaye tace, "Aa ina dasu Ammi ta bani"
"Karb'i nan ban son musu"
Ta ansa ta nufi inda zata samu abun hawa, shi kuma ya jiyo kanmu Rukee tayi hucking inda take, cikin kakkausar murya da ban tab'ajin sa da ita ba ya ce "ku fito"
Sosai nake kuka mai tsuma rai,ko a kwalar rigarsa don yadda yakeji ma tsaf zai iya jibgata ya huce haushin sa dabai ida hucewa ba, "I said get out!!"
Aguje muka fito daga motar,ya zaga ya shiga mazaunin driver ya bata wuta yai tafiyarsa yabar mu tsakar hanya,kukana ya k'aru sosai nafi minty goma ina kuka sanan Rukee ta soma bani hakuri,kasa hakuri nayi saida na gaji don kaina nayi shirun,murya ta shak'e sosai ta dishe ido yai jajir kamar jini zai fito haka ma fuskar.
Daker muka samu adaidaita muka tafi makaranta,sadda muka isa har an soma raba booklet daker aka barmu muka isa sit d'inmu,kowa ya ganni sai ya tambayi dalilin kunburar fuskata,don ga dukkan alamu marin da yai mun ya sabauta kumatuna,don inajin alamun sunyi fushi sosai,Rukee ce ke iya bada ansa cewar banda lafiya,muna gamawa ko tsayawa bamuyi ba muka taho gida.
Wannan al'amarin ya sake dagula zumuncin cikin gidan nan,don saboda rikici har Abba Nura saida ya tura Mami gidansu,Umma kam saida Abba ya sauke mata tafinsa a kuncin ta, rigima akai sosai wadda ta sale dagula lissafin gidan,kwatsam Ya Rafeeq ya diro garin babu wanda yasan da zuwan sa, nidai nasan na gaya mashi abunda ya faru na kuma dauki picture na fuskata na tura mashi,ko alokacin muryar sa kadai zaka ji kasan cewa ransa yakai k'ololuwa wajen b'aci,ashe yana tafe bamu sani ba,Ai ko ranar Abba Nura yace bazai kwana gidan ba saiya juya.
Sanda ya iso direct bangaren Abba Habibu ya nufa,akai sa'a Yah Ramadan d'in nanan kowa ma na nan har Yah Najib daya dawo hutu,Ammi bata tafi ba tana nan itama,kamar daga sama suka ganshi duk suna falo bayan sallar magariba ne lokacin, mama ce tai karambanin cewa, "Aa aha Rafeeq kaine da daren nan?saukar yaushe haka.........ke munafuka ba wajenki nazo ba,kibar wani rawar bakin karya nasan bai kai ciki ba,kinga wajen wanda nazo nan..........ya isa cikin fusata ya cakumi wuyar Yah Ramadan yana jijjigashi yana cewa, "har ka isa ka sabauta mun mata,kai waye?talaka kawai d'an talaka........cika mun riga!"
Ramadan ya fad'a cikin wani irin fushi mai tsanani,ba wanda yace musu komi saboda kalaman Rafeeq sun daskarar dasu a wajen, cikin karaji yace "bazan cika ba,inka isa ka kwace da kanka mana" yaja da karfi har ya keta masa rigar, wata shak'a Ramadan ya kai masa ya buga shi da bango idonsa jajur ya kasa magana,tuni Rafeeq ya fara kakari idonsa suna tafiya luuuu kamar zai suma,Mama sa Ammin kausar sukai kansu suna kokowar rabasu ammaa sun kasa,hayaniyar su ta janyo hankalin Abba Habibun dake can falon shi,ya fito yana ganin abunda ke faruwa yai saurin isowa yana daka ma Ramadan tsawa,amma ko gexau bai ba kiran duniya da tsawa Abba yai masa bai jiyo ba balle yaji,kwata-kwata kamar ma baya cikin hayyacinsa ga rafeeq yana ta kakarin mutuwa idonsa sunyi luiuuu sosai zasu rufe,saida Abba ya dauke sa da zazzafan mari sannan ya dawo hayyacinsa.
"Ashe baka da hankali?kai wane irin mutum ne marar hakiri,komi yai makaa ai ba ka shak'esa kai niyyar kashe shi ba............Hawayen da suka gani akan fuskar Ramadan sunyi masifar sanyayar da guiwar su,jikinsu yai sanyi ainun wanda tunda suke dashi vasu tab'a ganin hawayen sa ba,Ramadan jarumi ne mai hakuri ne kuma mai dakakkar zuciya,wannan hawayen yana nufin komi ma a tattare dashi.
Shiru Abba yai bai sake magana ba,Rafeeq ya kama suka fita xuwa bangaren su sai lokacin aka san da dawowarsa,Abba Nura bai tausaya masa halin k'ak'anikayen da yake ciki ba yaita surfa mashi masifa.
"Daka tako k'afarka kazo ubanka zakai?nace ubanka zakayi?ka fita cikin idona Rafeeq kafin nai mummunan kalami akan ka,uwarku ta koya muku rashin kunya da iyaa shege ko,to bazan dauka ba wallahi bazan dauka ba duk ubanda ya hanani zaman lafiya da yan uwana a cikin gidan nan wallahi zan sallamashi............"Abba ka daina masa fad'a,kana gani baida lafiya duba kaga halin da yake ciki,don Allah Abba kai shiru"
Kuka nake ina maganar,ga ruwa hannuna ina bashi a baki saboda tarin da yaketa faman yi, Abbaanmu ya banka mun harara yace "tashi kibar nan kafin na tattakaki"
Aguje na tafi daki ina kuka sosai saboda ganin halin da yake ciki,sannan ga masifar su Abba shin taya zamu so su Abba Habibu?bacin koda yaushe sune suke hana mana zaman lafiya da iyayen mu.
Acan falon kuma.
"Nura wannan fad'an ya isa haka,ka kyalesa yaji da kanshi fad'a sukai da Ramadan na iske ya shak'esa mafarin yaketa wannan tarin kenan,tashi muje mu kaishi asibiti"
Abba Nura ransa Bace yace "kayi hakuri Yaya ba wata asibiti da zan kaishi,ai shiya jawo koma miye na tabbata Ramadan bashi yajashi da fad'a ba,sanin kowa ne Ramadan baida hayaniya,shine zaije yai masa abunda zai jawo ransa ya hangula yai masa duk abunda yayi masan,ya tashi yaban waje ba abunda zan mashi,kuma ka tabbata gobe kaje kabi wani jirgin ka koma inda ka fito,kuma wallahi kwandala ba zatai ciwon kai ba,sannan daga rana mai kamar tayau idan na ganka gidana ba tare da ka kammala karatunka ba,wallahi tallahi ka manta na haifeka"
"Subhanallahi,Nura wace irin magana ce wannan ka shiga hankalin ka mana"
Abba Habibu ya fada cikin fad'a-fad'a, Sai lokacin Abba Taheer ya ce "kayi hakuri Yaya,yaran ne idan ba haka ake masu ba basu shiga taitayin su,kana gani saida mukai hannun riga da Fahad kafin yake yadda da hukuncina yabi abunda nakeso,don haka kabarshi yai masa hukuncin da ko da wasa bazai kuma abunda yakeyi ba"
"Ai ba ta haka ake hukunta yaro yayi abunda akeso ba,kuyi masu nasiha mana kuyi masu addua kujawo su ajiki,kuna masu kwatanci ahankali zasu gane ba dai-dai sukeyi ba,tashi Rafeeq muje ni na kaika asibitin a dubaka"
Daker ya bud'e baki ya ce "Ba sai anje ba,zan je na shafa magani in nagasa wajen da ruwan zafi"
"To shikenan Allah ya kyauta gaba,kuringajin magana don Allah ku kiyaye bacin ran iyaye masifa ce babba,ka bashi hakuri kayi masa laifi"
Muryar sa tai wani iri gwanin ban tausayi ya ce, "ka yi hakuri Abba in sha Allah bazan sake abunda nayi ba,kaima Abba Habibu kayi hakiri natuba"
Kwallace ke zarya afuskar sa duk jikinsu yai sanyi, Abba Habibun yace "ya wuce Allah ya yafe mana,ka kiyaye gaba kaji ko tashi maza kaje ka gasa wajen"
Ya tashi daker yana tafiya, Abba Taheer yace, "zan maka bucking wani flight d'in ta online,zuwa jibi saika tafi"
"Nagode Abba"
********
Kwana biyu gidan ba dad'i,mudai mun gama jarabawa muna zaune gida zaman banza,sai fa islamiyya da muke fita duk juma'a da asabar da lahadi,mami bata nan har yanzu shiyasa duk bama jin dadin gidan,kowa tsoron Abba Nura yake yanzu balle har ka iya bashi wani hakuri akan yaje ya dawo da ita,cikin kwana biyun kuwa ba abunda ya sauya daga tattali da kulawar da muke dajuna nida Yah Rafeeq,saima abun da yai gaba nice hidimar abincin sa da komi da komi har zuwa daren da zai tafi don tashin dare zasuyi karfe takwas da rabi jirgin zai tashi, muna zaune dashi bayan sallar magariba falon Umman mu daga ni sai shi yake ce mun, "Rooh inaso kiyi mun wani alk'awari guda please"
Yana yin sa ya sauya sosai,nima duk cikin rashin sukuni na ce "miye shi?zan maka shi yah Rafeeq koda bai dai-dai da son raina ba"
Lumshe idonsa yayi ya bud'e su akaina,zuba ma juna ido mukai kamar ba zamu sake ganin juna ba,saida nai karfin halin sadda kaina k'asa inajin ilahirin jikina yana tsuma da soyayyarsa.........."inaso daga yau magana ta fatar baki karta sake had'aki da RAMADAN,In hanya ta matse maki dashi kinji kina iya gaidashi ki gaidashi ki wuce,in kinji baki iyawa ki wucewarki,bana son wani abu kamancin kusanci ya sake had'aki dashi balle har kazamin hannunsa yakai jikinki,idan haka ta sake faruwa wallahi zan iya kashe shi zan iya masa abunda iyayenmu maza ba zasu yafe mun ba,ki janye daga garesu kam yan bangaren su,Abba kurin na lamunce mawa ki gaidashi ki sakar masa fuska,please Rooh kimun wannan alfarmar"
Jinjina kaina nayi kafin na ce,"koda bakace na Yah Rafeeq magana nida shi har Abadan inba dole ba,amma don ka yadda dani nayi maka wannan alkawarin"
"Thank you my love,"
Nai masa murmushin da yakeso har dimples dina suka bayyana,
Sai sannan naga walwalar sa yana murmusawa shima, kafin ya d'ora da cewa "Abu na gaba shine Abba yayi rantsuwa bazan sake dawowa hutu ba har saina kammala karatuna,wannan shine abu mafi d'aga hankalina daya gindaya mun,Rooh ina cikin damuwa sosai tsoro nakeji inacan ke kina nan wani yazo ya rabaki da Soyayyata,karshe ma inji kawai anyi miki aure please ya zanyi i need more advice from u,ga rashin Mami agida yana tada mun hankali"
Hawaye suka cika idona nai kokarin hanasu karsu zuba,saboda iya tashin hankali na shiga jin cewar baxai sake zuwa gida ba har sai ya kammala, idan nace kuka zanyi zan karya masa guiwa zan rabashi da d'an karfin zuciyarsa,shiyasa na danne iyakar dannewa sannan na ce masa,
"Tabbas na Zan shiga rud'u da kewa mai yawa yah Rafeeq,bazan iya kwatanta yawan kewar da zanyi ba taka amma in mukai hakuri mu duka komi zai zama labari,shekara kamar kwana ce in sha Allahu lafiya zaka gama ka dawo ka iskeni ba abunda zai faru,ka sama ranka zaka jure duk son zuwa gida da kakeji kai namijine kafini juriya sosai,abun zai zo maka da sauki inhar ka yadda kayi biyayya ga maganar Abba,tunda na yadda rashin biyayyar shike jefa mu cikin masifa,kayi masa yadda yake so Yah Rafeeq ba zamu tab'e ba,kuma in sha Allah nidai ban da wani miji sai kai a duniyar nan,sannan alkawarin da zan maka mai dad'i shine zan kulle xuciyata,idanuna daga kula kowane namiji da sunan soyayya I promise to u,Mami kuma ka kwantar da hankalin ka zata dawo nasan bacin rai ne daya wuce shikenan"
Shiru yayi na wani lokaci kafin ya d'ago yana kallona irin kallon kewa da soyayya,ya ce "ban da wani buri a rayuwata da nake so illa na mallakeki,akan ki ban da wata jarunta Rooh,komi inhar ya had'a dake bana iya mallakar kaina,amma wannan alkawarin naki shikad'ai ya isa ya rik'e ni har ba gama karatuna na dawo gida,har raina na yadda dake kuma shawarar ki ta ansu 100%, inaso na sake jaddada miki wani abu guda"
Na dago idona da sukai cika da hawaye ina sauraren shi, "in hawayenki suka zubo Rooh zaki karya mun kwarin guiwata,please ki kara jurewa kinji"
Jinjina kai nai saboda idan nayi magana kuka zanyi, "inaso na fad'a miki *_INA SONKI,INA KAUNAR KI,KUMA BURINA A KULLUM NA MALLAKE KI,KECE NATSUWA TA DA KWANCIYAR HANKALINA,KECE KAWAI KIKE BURGENI A CIKIN MATA KOMI KIKAI YANA DAUKAR HANKALINA,KI KASANCE DANI A RANKI,INA NAN KO BANA NAN ROOH"_*
Juriyata ta kare zafafan hawaye suka silalo mun sharrrr ba tare dana shirya ma hakan ba,na sadda kaina jikin hannun kujera ina shashshekar kuka ahankali mai ratsa zuciyar mai saurare,na rasa yadda zanyi da raina da irin abunda nakeji akan tafiyar tashi,muryar sa tai wani irin rauni kamar yana kukan shima yake cewa, "sorry,I'm so sorry Rooh,stopped kukan ki yana kassarani in kika cigaba dayi bazan iya tafiya a yau ba,ina mai tabbatar miki zan kamu da rashin lafiya mai tsanani"
Don dole na sassauta na soma hakura da kukan,ya bani hanky dinsa na share fuskata,munyi shiru kamar ba kowa har lokaci ya k'ure,Anti Rafeea ta shigo ta ce "Abba na jiranka a mota Yah rafeeq,"
Kallon ta yayi cikin yana yi marar dad'i ya ce, "ki kula mun da k'aunata Rafeea,kece takwarar sunana nasan zaki tayani yak'i akan soyayyata,karki bari wani yazo daga waje yace zai shiga inda ba hurumin sa ba"
Dariya tayi ta ce, "angama Yah Rafeeq,baka da matsala indai nan ne"
Ya jiyo kaina ya mun wani sassanyan kallo, "zaki rakani airport?"
Girgiza kai nayi da sauri cikin salo na ce "Aa,zan iya rasa jarumtata,kaje kawai Allah ya tsare ya bada sa'a akan dukkan abunda ka sanya a gaba"
Lumshe idonsa yayi "naji dadin adduar nan,kici gaba da yi mun ita akodayaushe"
Ko bakin mota ban rakashi ba anan mukai sallama ya wuce yaima Umma bankwana sannan ya tafi,sai lokacin nai kuka kamar ba gobe shekarun da zai dauka banganshi a zahiri ba kawai nake hangowa,kuma acikin wannan shekarun Allah kadai yasan mizai faru?
********
Tunda suka dauki hanya shida Abban shi ba mai magana kowa da irin tunanin sa a ransa,saida tafiyar tayi nisa Abban yai gyaran murya ya ce "Rafeeq"
D'ago kanshi yai ya ansa murya ashak'e, Abban ya cigaba da cewa "kana ganin kamar bana kaunar ka saboda wasu abubuwa da nake muku ko?kuna ganin nine nake ba dai-dai ba kune kuke kan dai-dai ko?shiyasa kuka juya mun baya kuka had'e kanku dana mahaifiyarku kuna yak'i da abunda nakeso kuyiko?"
A sanyaye ya ce, "Ba haka bane Abba.........haka ne mana Rafeeq,inda ba haka bane ba zaku k'i abunda ni mahaifinku nake so ba,ba zaku ringa take umurnina ba kuyi nata,shin ni banda hakki akanku komi?"
"Kana dashi Abba"
"Ban cancanci ai mun biyayya ba kenan?"
Ya ce da sauri, "wallahi ka cancanta sosai ma"
"To miyasa bakwa yi mun biyayya akan Yaya Habibu da iyalin sa?miyasa kuka d'ora masa tsana da iyalin sa bacin bai muku komi ba sai alkairi,"
Jikin Rafeeq yai sanyi sosai ya ce, "wallahi zamu gyara Abba,munyi magana da su Sha'awa za a gyara Abba kayi hakuri"
"Idan banyi hakuri daku ba ya zanyi muku?ko nayi hukunci ai ba bin abunda nake so kuke ba,kunga kenan hukuncin ma baida amfani,don haka wallahi ko kaje kayi karatun nan ko kuma inga wanda zai aura maka Roohee,ai nasan duk wannan tada jijiyar wuyar saboda ita kake yi don an daketa shine ka baro uwa duniya kazo ka rama mata ko?"
Soke kai yayi baice komi ba,kunya na kama shi don bai dauka yasan da abunda ke tsakanin su ba, "zan kiyaye Abba"
"Allah yasa"
Saida suka isa airport d'in sannan Rafeeq ya ce, "Abba ba dan halinta ba kaje ka dawo da ita,gidan baya masu dad'i yan matan can in babu ita,kayi hakuri ka dawo da ita"
Dafa kafad'arsa yayi yana cewa, "karka damu lokaci nayi zata dawo da kanta"
Da haka suka rabu saida yaga tashin jirgin su sannan ya dawo gida,cike da tunani kala kala.
Mom Muhseen &Assad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....12
Bayan kwana biyu Mami ta dawo munyi murna sosai,Amma ummanmu tafi mu murna saboda har kwallah tayi data rungumeta tana murnan dawowar ta,ba abunda ya canza daga dawowar Mami saima kara k'ullatar su Abba Habibu da sukai ita da Ummanmu,ko ince mukai don muma mun sake ja baya dasu sosai,har Ammin kausar d'in mun ja baya da ita,in zata shigo sau ba iyaka kauda kanmu ma muke gaisuwar ma mun daina,haka zuwa gaida Abba Habibun ma mun daina lamarin ya sake dagulewa sosai a cikin gidan,rannan Hajja ta tara meeting ranta b'ace hadda kuka saboda yadda abubuwan suke tada mata hankali,kowa ya hallara sai wanda bai nan ne babu a wajen,
Ta so ma magana cike da damuwa ainun, "kowa yasan akan me zanyi magana,ba saina bata bakina nace ga dalilin tara ku ba,kun sani akan zumuncin da kuka dauka ba abakin komi bane, na soma gajiya da abubuwan dake faruwa a gidan nan,wace irin masifa ce kuke son hadda sawa a cikin gidan nan,uwa daya uba d'aya amma kuna son raba mun kan y'ay'a na da jikokina,wallahi abun nan ya isheni haka nan inba so kuke in dauki mummunan mataki akan ku ba,kuma ba kowa ke had'a wannan husumar ba sai SAFIYA DA MAIJIDDA, wallahi in bakuyi wasa ba ungulu zata koma gidanta na tsamiya,na gaji hakanan ku biyu kun addabi iyalina kun hanasu zaman lafiya,ina da rai kenan to randa Na koma ga Allah kuma fa.........sai ta fara kuka haik'an wanda bamu tab'a ji ko ganin tayi irinsa ba, jikin mu yai sanyi sosai kowa yai shiru sai Abba Habibu daketa bata hakuri,....."ka daina bani wani Hakuri Habibu,kai za'a ba hakuri saboda kai ne kake kwankwad'ar bakin cikin da yafi nawa,ban san me kai masu na sharri ba suka kafa maka k'ahon zuk'a irin haka........... "Kiyi hakuri Hajja,wallahi Yaya babu abunda yai masu sai alkairi,tunda in bacin shi kila da yanxu ba wannan mgnr ake ba,kiyi hakuri don Allah kibar kuka wannan kukan naki masifa ce a garemu,zamu dauki mataki yadda ya kamata in sha Allahu,kiyi hakuri kaima Yaya ka kara abisa wanda kake yi,jarabawar mu kenan wadannan matan Allah yasa mu cinye"
Abba Nura ne yake fadar haka,Abban mu kau saboda tsananin b'acin ran dake cinsa ya kasa magana,haka dai taron ya tashi da tsaurarrun matakai da Abba Nura da Hajja suka kafa da Abbanmu,wanda take d'aya daga cikin wad'anan sharud'd'an na nufin hukunci akan ka mai tsananin gaske.
Rayuwa ta cigaba da tafiya a cikin gidan kadaran kada han,ba wannan zumuncin sosai haka babu wannan gabar mai tsanani,saidai kuma har yau su Ummanmu basa hulda da mama itama kuma daman bata shiga tasu Huld'ar,tana dai sauke hakkinsu dake kanta ta kuma ja girman ta ba ruwanta dasu,haka aketa tafiya gidan kullin in muka zauna fira falon Abbanmu nasiha ce da jan hankali tsakanin mu dasu Abba Habibu,ya daina fad'anan sosai saidai janmu ajiki da nuna mana hanyar data dace,har muka saki da tsanar da muka kwallafa musu,amma ta Yah Ramadan na nan daram a sak'e a gefe,don bana jin shi zan daina tsanarsa saboda abunda yai mun.
Shikenan muka koma sama-sama dasu Najeeba,Ammi dama ta koma tun tuni ita dasu kausar d'in,yah najeeb ya dawo hutu shi muna gaisawa duk sadda aka had'u,daga ba gaisuwar ba babu wani abu dake sake had'amu,to wannan abun ya kawo farin ciki sosai a fuskokin Abbanninmu,sai suka zage wajen hidinta mana komi muke so duk tsadar sa Abba da Abba Nura zasuyi mana,don daman komi namu sukeyi tunda Abba Habibu bai aiki tun fil azal bamu tashi munga yana wani aiki ba,komi daya shafi iyalinsa da hidimarsu Abbanmu keyi shida Abba Nura,don ma dai Abbanmu yafi Abba Nura samu sosai don shi Abba Nura Babban lauya ne da akeji dashi cikin garin abujar,shi kau Abban mu NNPC yake aiki kuma yana da babban muk'ami sosai,bayan haka suna kasuwanci shida Abba Nuran sai suka sanya Abba Habibu ciki,duk wata alwuns suna shigar ma kowa ta bankin sa,to inba wannan ba Abba Habibu bai komi gaskiya tunda bai karatu ba,primary kawai yayi.
Wannan kenan!
Tsakanina da Yah Rafeeq kuwa sai dai ince Aure ne kawai ba a daura mana ba,amma soyayya tayi nisa wanda zaka dauka an saka mana rana,amma muna kokarin kiyaye duk abunda bai kamata ba,duk kuwa shaid'an yana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 16