Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
banji ma sadda Abba ke magana ba,saida Ya ce mun "Rohee gashinan ku rok'i alfarmar ya ringa sauke ku in zai fita," Nidai bance komi ba Mufeey da Rukee ne sukai magana, ya amsa musu cikin wata cool voice da najima banji sa da ita ba, "Ba damuwa Abba,saidai ni karfe goma nake fita ban sani ba ko zasu iya jirana sannan" Caraf Mufeey ta ce "zamu jiraka mana,ban bancin awa daya ne kuma nasan kafin mu isa Anti Rafeea ta isa zata fara rage ayyuka" Rukee ma tace"kuma tana da mai aiki duk abun bazai wahala ba" "To ba damuwa bari na gama abunda nake a ciki kafin nan time yayi sai mu wuce." Mom Muhseen & Asad🥰 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....21 Ban garen su Rukee muka koma muka zauna jiran sa,raina duk a duk'unk'une sudai basu ce min komi ba saboda sun san suna tofawa zamu iya samun matsala,sai suka kyaleni kawae. Bai fito ba sai karfe goma da rabi,ya kira layin mufeey yace mu fito sannan muka tashi muka tafi,itace gaba muka zaga baya muka shiga kananun kaya ne jikinsa black din wando sai sky blue din shirt,banga wata karin guga ba akayan haka zalika ba wani cukuikuyewa tare da su,sannan banji wani fitanannen kamshi na tashi ba,Ina mamakinsa namiji kamar sa ace baya saka turare imagine,na tab'e baki kawae na zauna saitin kujerar driver na saka air pies kunnena na cigaba da danna wayata,duk da ban kunna komi ba haka nan nai sha'awar sawa,amma kuma all ears dina akan firar mufeey dashi ne,Rukee na taya su nidai kam uffan ban ce ba amma duka hankalina yana kansu,zuwa caan naji tace "favorite please ga inibi inaso" Bai musa ba kurin yaja ya tsaya dai-dai inda mai inibin yake,ya ciro kudi aljihunsa ya bata kurin ba tare daya tanka ba, sai Rukee da ta ce "kayakuri yah Ramadan mun tsayar dakai" Atakaice ya ansa mata da cewar "Don't mind" Ni dai k'ala bance ba tare suka fita da Rukee suka siyo ina nan zaune,kowa da nashi a leda saida muka cigaba da tafiya mufeey ta miko min wata leda guda tana cewa, "Sister ga naki" Girgiza kai kawai nayi nace, "I'm ohk" Su duka ita da Rukee suka had'a baki wajen fad'ar, "are u ohk?inibin?" Saboda sunyi mamaki matuk'a don cikin kayan fruits ba abunda yafi soyuwa agareni kamar sa, banza nai musu kawae sai basu sake tanka mun ba har Allah ya iso damu gidan Anty Sha'awa. "Favorite karfe nawa zamu jiraka to?" D'an jimm yayi kafin ya ansa cikin sanyin sa yana kallonta, "Indai kun tashi tafiya ki kirani kawae" Cikin murna da jin dad'i tace "ohk Allah ya tsare ya bada sa'a ya kuma dawo dakai lafiya" Kamar wasa ya saki wani kafirin murmushi yana lumshe mata idanun sa ya amsa can ciki "Amin thanks" Bata biyo bayanmu ba saida taga tafiyarsa,na rasa gane miyasa mufeey ta damu dashi har haka,ni bata san haushinta nakeji ba in tana wani nu ta damu dashi,tsaki naja nai gaba cikin gidan, Duk da kasancewar mijin Anti sha'awa baida kudin mijin Anti Rafeea,amma gidanta babban gidane upstairs ke akwai kuma sama da k'asa dakuna ne sai wanda ka zab'a zaka zauna, falukanta hud'u sai bed rooms uku, sai single room uku kuma kowane ba wanda babu furnitures acikinsa, ga Ac ta ko ina dole ma kaji dadin gidan kuma ta ko ina tayils ne har bango,a bangaren gida kam zasu zo daya da Anti Rafeea,saidae kawae samayyar miji da hidimar da yake mata ne ba d'aya ba,don Mijinta mak'one dashi duk da baida halin sosae amma wani abun yana da halin yi mata mak'one kurin irin nasa,sab'anin na Anti Rafeea ba abunda zatace tana so baiyi mata ba,saidai idan bata ce d'in ba. Munsha Aiki sosae saboda Anti Rafeea cikinta baya son wahala,aikin da bai gaza ba shine takeyi a zauna sauran hidimar cikin gidan kau duk mu mukayita,ga dangin mijin nata zaryar zuwa gida fa masha Allah anata zuwa barka,saboda ganin an dad'e ba asamu ba kowa yana musu murna. Sanwa damun sauke zamu d'ora wata don ma Allah yasa mufeey akwai son aiki ita da Rukee aida na bani,Allah ya sani ban son moriya aikin cikin gida wahala yake ban,don ma Allah yasa umma duk ta hutar dani abubuwa shiyasa nake dan hutawa,ummi ce gandun aiki bata ko gajiya aiko Hajja taita Fad'a akan mi za a samun ido bana yin aiki,gidan mijina wani ne zaije yai min. Ni kam daman ai munyi da Yah Rafeeq cewar duk abunda bazan iya yi ba zai daukar min masu aiki,girki ne kurin zamu ringayi da kanmu ko muringa fita cin abinci. (Uhm banji hanya mai bullewa ba anan) Bamu samu kanmu ba sai karfe shidda da rabi na yamma,jikina kamar an bubbugeni su Rukee sai dariya suke min,suna tsokanta wai azo kallona gidan mijina saboda dole zan sha wuya,jinsu kawae nake nidai saida nayi baccin gajiya ina tashi muka hau waya da Yah Rafeeq yana bani lbrin aikinsa,yace in yai sa'a ma bazai wuce kwana goma ba zai dawo,naita murna ina ce masa "gidan duk babu dad'i da baka nan,nasan da ace kana nan akai haihuwar nan kullin tare zamu fita mu dawo," yai saurin cewa "waye yake kaiku?" "Wannan ne mana,ai kasan dae in yana nan Abba baya sanya kowa akan wata hidima saishi kamar yafi kowa" "Rooh" Yai mgnr cikin wani yana yi marar misaltuwa,jikina yai sanyi jinsa kamar cikin damuwa sosai na amsa masa tare da tambayar ko lafiya? "Naji ka so cool,akwai wani abunne?" "Wallahi da ina da hanyar da zan hanaki zama duk inda yake da nayi,kwata-kwata bana kaunar ganinki tare dashi koda hanya ce kau,.........."yah Rafeeq ni kam inaso yau ka gaya min dalilin ka na yawan fadar hakan" na katsesa da fadin haka cikin damuwa,sabda ni nagaji daji tunda yasan dai nid'in tashice ba wani d'a namiji da zan iya ma kallon rahma sama dashi indai akan mgnr soyayya ne da aure..........."Rooh wannan da kike ganin sa munafukine,ni kad'ai nasan irin kallon da yake miki,ke ba zaki gane ba da zai samu dama wallahi zai iya cewa".........."karka karasa Yah Rafeeq!!!" Numfashina har wani sama da k'asa yake saboda yadda naji bugun zuciyata ya karu sosai,kwata-kwata ban tab'a kawo wannan tunanin a raina ba saboda ma duk abunda zai tada min hankali game day aurena Dashi bana kaunarsa......."come down Rooh,Ina so na nuna miki ne yadda zaki nesa dashi,.......Yah Rafeeq ko maza sun kare walahi gara min na dawwama babu aure,Dana auresa gara na mutu wallahi.....sai kawae na sanya kuka sosai sbd yadda hankalina yai kololuwar tashi,kuka sosai nai tayi da yake dakin ni kadai ce yana ta kiran sunana da niyyar lallashi hankalin sa ya tashi sai kawae na kashe wayata. Naci kuka sosae wanda na dad'e banyi ma irinsa ba,bansan dalilin da yasa nakejij tashin hankalin mgnr ba, ni koda wasa bana kawo ma irin haka a zuciyata,sabda nasan nafi karfinsa nesa ba kusa ba,kuma a ganina ko ga kafa aka daura masa ni dagudu zai kunce saboda yasan wutsiyar rak'umi tayi nesa da k'asa,sadda su Mufeey suka shigo da fara shirin tafiya gida suka sameni cikin wannan yana yin,Anti Rafeea ta kalleni ta ce "miya sameki?kinga fuskarki kamar jan kosai?" Mufeey ta ce "Haba Anti,maimakon lallashi saiki ce mata haka?,yakuri sister miyafaru?" Bance komi ba nidai ina kwance abuna har sannan zuciyata bana jinta dai-dai, Rukee tace "bai wuce ita da Yah Rafeeq ba,kila shine ya sata kukan" "To miya shafeki ne idan shine?,sunfi kusa ai inma shiga kikai kunya zasu baki" Cewar Anti Rafeea mufeey na cewa, "yanzu dai abar mgnr,sister ki tashi ga Favorite can yazo ganin baby daga nan mu wuce gida" Kai kurin na d'aga mata bance komi ba,suna ta firar su nidai kallo ne nawa,har suka gama komi sannan na sauki na shiga toilet,gyara jikina nayi na wanke fuskana na tsane da towel na maida kayana danazo dasu na fesa turare na daura veil dina,kana kallon idona da fuskar zaka san nayi kuka ainun,lipstick na saka ma bakina na dauki phone dina nabiyo su,duk suna babban falon Anti sha'awa,mu kadai ne ba wasu yan barka,anata fira shi kuma rik'e da Babyn mufeey na kusa dashi cikin two siter,Ina saukowa daga stairs naji kawae na soma hard'ewa gabana ya fad'i sosae ban d'ago kaina ba har sauko na zauna gefen maijegon........"Roheen Abba lafiya kuwa?kinga fuskarki,ku fararen nan matsalar da kunyi kuka sai angane maku" Uffan bance ba ban kuma tanka ma kowa ba sai suka kyaleni,har sannan inajin alamun ana kallona naki duban ma inda raina ke ban nan ake kallon nawa,.........idona rufe naji Antin tana cewa "Yah Ramadan hadda wata hidima kuma?to Angode Allah yasaka da alkairi" Bud'e idona nayi naga wata leda ce babba da kayan jarirai na tab'e bakina,na maida idona na rufe saida ya fita sannan Muka tashi mukai musu saida safe,Anti Rafeea mijin take jira yazo ita muka baro da mai jegon........ ********* Tunda muka taho a hanya bakin mufeey baiyi shiru ba,ita dai bata gajiya da magana ko kad'an sai in bacci take amma inhar ido biyune tofa bata hutawa, tunda na zauna mazaunina ban d'ago kaina ba saboda bana kaunar koda wasa idona ya shiga cikin nashi,caan naji anja uban burki duk saida muka tsorata ba shiri na ciro kaina da sauri,hakan yai dai-dai da haduwar idanun mu cikin madubin center mirror, jinai zuciyata ta tsinke gabana ya fad'i rasssss da karfi, da sauri na kauda kaina Ban ma tsaya kallon kiya faru ba nasan iskanci ne kawae,ya tada motar muka iso gida muna tsayawa nice farkon shigewa saboda a k'agare nake na ganni a dakinmu. Mom Muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....22 Mun cigaba da zuwa gidan zaman jegon Anti sha'awa har kwana hudu,duk wata hidima mukeyin ta anyi sa'a Ammi tazo ita da kausar mun samu saukin hidimar duk dasu ake tayi,wata ranar Najeeba zata zo ayi da ita duk da bama sake mata itama kuma batamu take ba,Ammi Rahma kuwa bama ruwanta da wani kin sakewar da muke da ita, sabgar gabanta kurin take zata samu aiki dole muyi tunda gaba damu take sosae,in maganarta tazo kanmu zata tanka mana dole mu bata ansa,tun muna kakkauce mata ala dole saimun nuna bama yi da yan bangarensu,dole muka sake da ita anata hidima. Don itace tayi uwa tayi makarb'iya a hidimar sunan,kuma hakan yai mana dad'i har ita maijegon,saboda babu wani babba sosai dazai shige gaba a hidimar,Su ummanmu Abba yace subar mana mune ya dace muyi,to tunda suka zo barka basu sake zuwa ba. Daren suna aiki ya kacame Ammi ta kirani ta bani list d'in abubuwan da za'a siyo kasuwa,su Rukee da Mufeey na can sunata aiki nice na gudu na b'oye ashe rabon ni zanje kasuwar, idona yai narai-narai zan hawaye na ce "wallahi Ammi ban san kasuwar da zanje ba,kuma Abba ya hana shiga taxi ba kamar in yamma tayi sosae" Ni duk dan in zillema aiken,sai kawae naga ta dauko wayarta tana kira,zu wacan naji tace "yanzu nake son ganin ka pls,magariba nayi bana so ace tayi ba asiyo kayan ba,ohk ina jiranka" Na sauke ajiyar zuciya nasan na tsira, sai naji ta ce dani "kijara RAMADAN farfajiyar gida zaizo kuje tare," Ta juya kurin ta kyaleni nan tsaye nabita da ido,na ma rasa mi zanyi inama na ansa mata kurin naje da kaina?inama banyi musu da ita ba balle ta had'ani tafiya dashi,wallahi ba abunda nake gujema wa irin haduwa wuri daya dashi,bana so har raina bana so.........."mikike baki tafi kinjira sa ba,Roohe wallahi ki kiyayeni"........."yanzu zan tafi" na wuce dakin da muka aje kayanmu na dauko veil d'ina,doguwar rigace rafa jikina ta atamfa ta kamani daga sama boobs dina sun fito ma sha Allah,daga k'asa tabi k'uguna ta baje sosai tayi masifar fidda shape dina,yane kaina nayi da veil din inata jan tsaki kurin na fesa turarena da duk inda zani da kayana,da lipstick dina. Ina bud'e kofar mukai kicib'is da ita, "wallahi dana cinmaki baki niyyar fitowa ba dakin sha tafi,ki wuce yana waje yana jiranki,sai hadarin ya taso ruwa ya sauka kuyi mana salalar tsiya" Ina tafiya inajin zuciyata kamar ta fito don bakin ciki,raina b'ace haka na tafi farfajiyar gidan yana tsaye bakin motar yana danna wayarsa keypad,naja tsaki Ina cewa a raina "KO uwar meye acikin keypad din da zaka samesa kodayaushe yana dannawa?............tsaye nayi daga nesa kad'an dashi nace cikin shan murr, "gani nazo" Saida ya gama shan k'amshin sa bai dubi inda nake ba ya zaga ya shiga motar, na ja wani tsakin kurin,na mance ba abunda ya tsana sama da tsaki ni ina ruwana........na bud'e motar na shiga yaja muka tafi KO radio bai kunna ba balle ta dauke mana shirun,inda saboda ma ai mun saba tafiya ba mai cema d'ayan sa ci kanka,ba muyi nisa ba iskan tasowar hadari ya soma kad'awa gwanin dad'i ga sanyi ga k'amshin ruwa,har lumshe idona nayi. Haka mukaita tafiya zuwa can aka kirasa a waya, ya ciro ya saka speaker ya aje daga saman motar naji muryar Mufeey, "Favorite don Allah Ina son kwa-kwa in ka gani kaji" Yadda take maganar cikin wata shagwab'a da salo yaban mamaki,anya mufeey ba son wannan mutumin take ba kuwa?........."ohk Mufeeda,bayan ita bakya son komi" Ta sake narke murya cikin salon daukar hankali, "Ina son dabino to favorite," Ya sake ce mata yana murmushi wanda ya daskarar dani inda nake,Ina satar kallon sa ta gefen ido. Ya sake cewa "To mufeeda bayan shi sai mi kike so?" Dariya tayi mai kyau tana lauya murya "Aa Fa favorite shikenan,bayan wadannan abu d'aya nakeso" Juyo da kaina nai na kallesa sau d'aya shima akai sa'a ya jiyo muka had'a ido,bazan iya fassara kallon sa ba nima bansan miyasa na kallesa ba, ansa yake ba Mufeey amma idonsa ni yake kallo, "miye kikeso fad'a min" Saurin juyar da kaina nayi ga taga kawae,Ina kallon yadda aka d'an soma yayyafi jefi-jefi........"inaso ka dawo lafiya,ka kuma kula da titi" "Ohk angama sai na dawo" "Ohk bye" Ya kashe wayar yasa aljihunsa, ban san sadda wani dogon tsaki ya kubce min ba,saboda haushin mufeey intana wannan zazzak'ewar akanshi wallahi bata min rai take sosae,munzo dai dai bakin get din kasuwar yaci burki,na sake jan wani tsakin na bud'e na fito ina buga k'ofar motar,ashe rigata ta datse sadda naja zan tafi naji rigar ta mak'ale daker na fizgota,saboda naja murfin naji kamar yasa lock ta ciki,Ina d'aga k'afata kenan naji an fizgoni da karfin gaske an had'a ni da jikin motar,wani rasssss kirjina ya ansa saukina wajen ba kowa saika shiga cikin get din zaka ga mutane,idon sa cikin nawa dana fiddosu waje saboda tsorata,nashi idon jajawur da bacin rai nima raina ya b'acin,yadda ya damke min hannu da karfi yasa na fizga da karfi Ina cewa "Dalla malan sakeni..........takalmina mai tsini ya tusgud'e na tafi zan kifa a k'asa,yai saurin saka hannunsa ta wajen k'uguna ya taroni,kamar jira ruwan sama keyi aiko jikake shaaaaaaaaa ya balle da d'an karfi,dagani har shi kamar wad'anda aka d'aure mun daskare a wajen,sai ya zama kamar yana rungume dani ne,hannunsa ya zagayo dashi ta bayana saman k'uguna ya rik'eni,nima hannuwana suna bisan wuyansa na rik'esa gam sadda nazo fad'uwa,tun ina kalon idonsa da suka washe daga jaan bacin rai,har ruwan yasa dola na sauke idona k'asa na runtse su,cikin sand'o na sauke hannuwana dake bisa wuyansa,jikina yana yar rawa saboda abune da bai tab'a faruwa ba sai saudaya radda na fad'i a basketball,amma wannan karon kusancin yafi yawa sosai nake jikinsa har inajin sautin bugun zuciyarsa a kirjina da muka manne,sannan hancina yana shak'o wani sassanyen kamshi daddad'an kamshi mai ratsa hanci da kwalwa daga jikinsa,ruwan nan ya mana shar kaff har d'iga muke kayanmu amma motsin kirki ba wanda ya iyayi acikin mu,zuciyata nima kamar zata fashe saboda yadda take bugawa sosae,bazan iya gane tsawon lokacin da muka d'auka a hakan ba,har ruwan ya rage karfe sosae. Sai lokacin naji ya d'an saki jikina kamar jira nake nai sauri ida fita daga jikinsa,santsin kasar wajen ya kwasheni na tafi zanci k'asa da sauri ya sake rik'oni again muka sake had'ewa waje guda,fuskata cikin kirjinsa Ina sauke numfashi,gaba d'aya na rikice ma hankalina ya tashi natsuwa na neman gagarata,muna a hakan ya bud'e motar ya zaunar dani sannan ya rufe jikina sharkaf har pant dina kanshi a jik'e yake,dunkulewa nai waje guda Ina kermar sanyi nama rasa wane kalar tunani zanyi,haushin kaina zanji komi? "Ina list d'in abun da za'a siyo" Naji sassanyar muryar sa yana tambayata,ai bazan ma iya gane ina na sake shi ba,girgiza kaina nayi kawae bance komi ba,sai ya zagayo inda nake ya bud'e k'ofar yana dubawa,kaina na cikin guiwata shi kuma ya duk'o ya dauko takaddar dake wajen k'afata,jin sa a wurin nai saurin ciro kaina dai-dai shima ya sawo kai a wurin,fuskokin mu suka had'u har hancin mu yana haduwa dana juna........YA SALAM!!! Abunda ya bak'uncin ilahirin jikina tunda nazo duniya ban tab'a jinsa ba,a zabure naja baya da kaina shi kuma cikin sanyin jiki ya dauki takaddar ya fita, bansan ya akai ba nadai ga ya shigo ya kwantar da kujerar sa ya dora hannunsa bisa fuskarsa,ban san hawaye sun balle mun ba na rashin abunyi,nidai nasan harga Allah bada niyyar kaina hakan ke faruwa ba, shima kuma nayi imanin baida wata manufa akaina,to miyasa hakan ke faruwa?ban sani ba,ban San ansar ba shashshekar kukana ta fito fili har yaji da kamar bazai tanka ba,sai zuwa can naji ya ce mun "Sanyi kikeji ne?" Ba tare daya cire hannun sa daga fuskar ba,banza nayi masa tunda banda abun cewa,daga inda yake ya sanya hannu ya kunna heater yadda zamuji gumi don sosai nakejin sanyin. Bayan wani lokaci akai knocking ta glass ya tashi ya bud'e glasse din wani mutum ne yake ce masa, "an had'a komi yallab'ai" Jinjina Kai yayi yace "bud'e kaya ka sanya" Ya bude bayan motar yana loda kayan,sannan ya ce an gama ya biya kudin sannan yace "please kawo mun kwa-kwa da dabino" "To yallab'ai" Har mutumin ya juya sai ya tsayar dashi,yana jiyowa kaina yace "ba kyason komi?" Mamaki ma tambayar ta bani,ce masa nai inason wani abun? Amma banyi magana ba na girgiza kai alamar aa, sai yace dashi "ka had'o da inibi please" sannan mutumin ya tafi,haushi duk ya isan nama rasa abunyi nace, ciki-ciki "Ni bana shan inibi ai" Ya koma ya kwanta yana ce mun, "na sani ai,daman kuma ba naki bane mufeeda na siya mawa" Yadda naji haushin mgnr ban San sadda naja wani tsakin ba mai tsawo tsuuuuuuu,a zabure ya taso kamar wani kubuwa "keeeee!" Na jiyo gabana na fad'uwa,Idona cikin nashi yai mun kuriiii nima ina kallon sa, "idan Kika sake mun tsaki wallahi sai kin gane baki da wayau" Na juyar dakaina Ina murgud'a baki kawae,.........yai k'uta yana cewa, "sai karyar iskanci" Ina gunguni nace, ciki-ciki "wallahi ni ba yar iska bace.........mikika ce?zagina kike?" Ya taso da sauri yana kawo hannu kamar zai buge mun baki,nai saurin ja baya ina turo baki, "Wlh ni ban zageka ba,cewa nai niba yar iska bace........idanunsa a warwaje yake kallona ni kuma na makale jikin k'ofar kamar zan shige cikinta, kanshi ya nuna yana wani kala da idonsa "nine d'an iskan kenan.........Aa wallahi ba haka nake nufi ba nidae" ya sake yin k'uta yana koma wa ya kwanta, har sannan ruwa ake sosae ya dawo kan dazun daya dan rage,munyi shiruu bakajin komi sai karar ruwa zuciyata ansawa kawae take,Allah yasa ma na baro wayata gida da kiran da yah Rafeeq zai mun yawane dashi,kiran salla da akai yasa na jiyo ina kallon sa shima a takuren yake alamun sanyin yakeji,don ma heater daya kunna aida mun gane kurenmu......."ba zamu tafi gida ba?" "Anan zamu dawwama,har saikin gaya mun waye d'an iskan naki" "Ya salam,wallahi ba da kai nake ba, ka yarda wallahi bance ma haka ba" Banza yai ya kyaleni har sannan ruwa ake daman ankwana biyu ba ayi ba zafi ya addabemu, "Wallahi sanyin kayan nan y daman,inaso na canza ka tada motar mutafi.........."kizo kija to,ni kam yanzu bazan iya tuki ba ana ruwan nan" "Ni zanyi," Ya jiyo yana kallona cikin hasken kwan cikin motar,duk na marairaice na ce "ehy zan ja motar wlh na matsu naje na canjaa" Kamar bazai daina kallona ba,ya wani lumshe idonsa ya d'age kafadar sa yace "bismillah bude ki zagayo" "Ruwan dukana zai sakeyi fa" Wani kalar kallo yai mun yana cewa "ohk,lemme exchange" Ya mik'o mun hannunsa in kama in taso daga inda nake zuwa mazauninsa, (uhmmm wadannan sun raina mutane😂🫣)kasa musu nayi da dai in fita ruwan ya sake dukana, rike hannunsa gam nayi na sanyo kafata daya inda tashi take,na dafa kujerar da d'ayan hannun nawa sai ya zamana kamar nai masa rumfa,wajen in ida sanya dayar kafar ne kawae naji na fad'a masa a rashin sani,daman kujerar kwance take sai kawae naji mun tafi gaba d'aya na fada bisa kirjinsa shi kuma bayan sa ya bugu da kujerar har saida yace "Ausshhh" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....23 Fuskata na bisan dokin wuyansa,wanda naji zafi kamar alamun baida lafiya,wata irin kunya da ban tab'aji ba ta lullun'eni,motsin kirki na kasayi kamar yadda shima ya kasa motsawa daga yadda yake,Hannuwansa duka biyun suna bisa bayana,ban san ma ta yadda zan sauka ajikinsa ba,ban san iyakar lokacin da muka dauka a haka ba,saidai naji mgnrsa a kunnena cikin sanyin muryarsa da ta kara zama cool, "*LAYLA please a d'agani haka nan ko*" Wani iri naji kamar in b'ace daga inda nake sai kawae na sanya kukan rashin abunyi,da borin kunya don wallahi sosai naji kunya dubeni duk irin k'iyayyar da nake masa,da k'yank'yamin da nake ji akansa amma gani d'are-d'are ajikinsa kamar zan shiga cikinsa,kasa motsi nai duk haushi ya kamani. Ganin na kasa motsin kirki sai ya d'ago kujerar daga kwantar da itan da yai dazun,d'aff ya cironi ya maida ni mazauni na,zuwa sannan yayyafi ne akeyi ruwan ya rage sosai,tada motar yayi cikin sanyin jiki ya fara sarrafa sikiyarin har muka bar wajen,muka sake zama kurame sosae ko motsin kirki banyi ba,na dunkule kamar curin tunkuza ga wani zazzabi naji ya sauko mun,sannan ba abunda nakeji illa wannan sassanyan kamshin nasa har cikin bakina,ilahirin jikina shine nakeji,zuciyata kamar zata fad'o k'asa so nake na bud'e ido na ganni gidama gaba d'aya ba gidan Anty sha'awa ba,hon din da naji yayi anbud'e get yasa na d'ago kaina har mun iso gidan Antin,magadi yazo zai bud'e ya kirasa yazo Yace"don Allah ka shirgar musu da kayan nan,kace ina sauri na wuce zan sauke wannan yarinyar gida bata lfy" Mamaki ya kasheni ya akai yasan banda lfyr?kamar ya shiga raina ya gano cewar banda lafiyar, daker na ciro kaina nace ma maigadin "don Allah ka ce Rukee ta baka wayata ta kawo mun" cikin girmamawa ya ansa da "to hajiya" Ya kwashe kayan yai cikin gidan dasu,yana shigewa yaja motar yabar kofar gidan,jiyowa nai ina cewa "wayata fa?" Uffan baice mun ba sai na kama kaina nima,in miskilanci ne gidan ka tarar mun kusa isa gida aka kirasa, yai picking yana sa wayar speaker, yanzun ma Mufeey ce take cewa "Favorite lafiya baku iso ba?" Muryar sa ta d'an dishe kad'an yace "Bakiga anyi ruwa ba,shine ya tsayar dani sakon ki na nan cikin kayayyakin kiduba" Cikin murna ta ce "thank you very much Favorite,to ina sister ka barota?" Kai tsaye ya ansa da cewar "gida" "Ohk sai munyi mgn bye" Ya kashe wayar yasa aljihunsa,yana yinsa ya nuna shima baida lafiyar kamar ma yafini jinjiki mgnr daker yake yinta,mun iso gida cikin yardar Allah na bude na fito wani sanyi ya ratsani tsikar jikina tatashi,daker da daker nake tafiya har na shige k'ofar entrance d'in. Falon mu ba kowa haka main falon gidan,alamun dai duk suna cikin dakunan su. ******** "Ramadan Ina kashiga haka?kar dai duk ruwan nan kanka ya k'are subhanallahi" Cewar Mama bayan shigowar sa bangaren su ya zube cikin kujera yana rawar sanyi har bai jin abunda take fad'a sosae, daker yai mgn "Mmn kausar ta aikeni kasuwa nida waccen yarinyar to a can ruwan ya iske mu" "Wace yarinyar?kaifa wuyarka kenan kayi mgnr da mutum zai gane ma ka kasa...........Mama inajin Rohee yake nufi ba kowa ba" Cewar Najeeba dake zaune tana masa sannu, Maman tace "tashi ka

Chapter 13 of 16