d'an samu nasara wani lokaci,amma muna baki iyawar mu wajen ganin bamuyi abunda zai jefamu ga dana sani ba,a wannan lokacin bana jin komi sai nishad'i da annashuwa,don Yah Rafeeq yana samar mun da natsuwa fiye da kima,wata irin kauna da soyayya yake mun mai ratsa dukkan jiki da b'argo,idan ina waya dashi bana son koda k'uda ya gifta tsakanin mu,wata natsuwa nake kamar ina daukar wata muhimmiyar lecture,har an gane mun ma in ina waya dashi ba mai mun mgn,don ba ji zan ba shiyasa na rage zaman fira,ina daki abuna muna soyewa salo-salo na daukar hankali ban san na iyaba sai da nafad'a tarkon sa,nida shi bazan iya gane wanda yafi son wani ba,ko fad'a bama yi sai muyi wata bamuyi fad'a ba shiyasa shak'uwar mu tai k'arfi sosai,muna tsananin ji da juna kamar rai sannan muna kishin juna kamar hauka,inhar yaji zan fita zuwa wani waje hankalin sa tashe hake,haka zaita damuna da kira yana bani umurni ga yadda zanyi,kar in sake inyi murmushi har in dawo,sannan dole na ringa saka nik'af da doguwar abaya,doka kala-kala da yake son sa nake bana iya sab'a ko daya daga cikin dokarsa,Rukee har mamaki nake bata tasha ce mun, "ke kam yar wahala ce,yanzu shida ba ganinki zai ba bainan yana can wata uwa duniya shine kike biyesa kike duk wannan abun,lallai ba ayi namijin ba walllahi"
Murmushi kawai nake mata in ce, "ba zaki gane miye so ba sai ranar daya sark'e ki,a sannan zan gane shin Rukee tana da wani ra'ayi ko saina habibinta"
Sai dai ta girgiza kai kurin ta rabu dani,to shima kuma inhar naji muryar wata a kusa dashi ranar bamu wanye wa lafiya, rigima muke sosai saboda zafin kishin sa da nakeji,gani nake kawai k'wace mun shi za'ai balle can akwai yan mata masu sunan yan mata da suka dameni a komi,india fa!ai karshen kyau kenan.
To da muka gane cewar ko wannen mu nada kishi sosai kan d'an uwansa sai muke kiyaye abunda zai motsa mana shi,muke zaman mu lafiya har Allah yasa muka shiga jami'a muma.
Wata private university dake nan cikin Abuja wai ita *BAZE UNIVERSITY* Abbanmu yai mana komi da komi na zuwa makaranta,hadda sabbin d'inku na mukayi Abba Nura yabamu kudi muka shiga kasuwa muka siyo kayan duk da muke buk'ata,jakunkuna da takalmomi,da sauran tarkace na yan mata masu ji da kansu,shigata jami'a ya jawo mun farin jinin samari sosai ma duk da na kasance mai killace surata,bana yadda na bayyana zahirin kyauna kodan kar wani yace yana sona ina kiyaye ma Yah Rafeeq wannan bangaren,Rukee har ta gaji da mamakina yadda na maida kaina wata matar aure wajen kula da rufe duk inda zai bayyana kyawun ta,amma duk da haka ban tsira ba daga samarin cikin makaranta,yanzu driver na musamman Abba ya samar mana yace saboda Yah Ramadan bai da lokacin da zai ringa kaimu da dauko mu,saboda yana zuwa wajen aikin furniture's ranar da naji wannan labarin munyi dariya sosai nida Ruky,lokacin munje yima Abba Nura sannu da dawowa yayi wata tafiya muka same su suna maganar,wai ana biyan sa a sati dubu goma,wanan yasa bamu san sadda dariyar ta kwace mana ba,sosai mukai tayin dariyar aiko ran Abba ya b'aci sosai da sosai saida muka gwammace bamuyi ba,don wayar charger ya dauko ya dunga tsula mana,rabon kau da adake mu har mun manta har kwalla mukai ya kuma ce mu bashi hakuri.
A rayuwata abunda yake kunsa mun bakin ciki kenan,ace in bashi hakuri ina hawaye da shashshekar bakin ciki na ce, "I'm sorry"
Uffan bai ce mana ba har Abba ya kora mu yace ko kudin break ba zai bamu ba yau,ya kuma sanar da Abbanmu abunda mukai,shima yace sai munyi kwana uku ba abami kudin break ba,aiko munji jiki kuma mun sakejin tsanar Yah Ramadan,saboda duk don saboda shi akai mana haka saidai ummanmu ko Mami wani ya bamu,duk da ba zasu kai yawan wanda su Abba ke bamu ba,don mu a rana ma muna iya had'a 30k ba wani abu bane wajen mu,shiyasa ai mukai dariya jin wai har sai anyi kwana bakwai sannan zai samu 10k abun da dariya wallahi,shi karatun ma bai mashi rana ba tunda almost 2years bai ci moriyar sa ba,daman kuma daker aka sha wajen karatun.
***********
"Gafara dai masu wuri,ai mana iznin shigowa da iznin zama,"
Wata mahaukaciyar dariya ce ta karad'e dajin har cikin dodon kunnenta,duk da cewar ba yau ta fara xuwa ba,amma kuma ta kasa sabawa da jin wannan dariya mai sata jin kamar zatai fitsari a wando,zuwa wani lokaci kuma dariyar ta lafa sanna taji sautin maganar bokan daga can saman wata gingimemiyar kuka bama a ganinsa,saboda duhun dajin da kukar.
"Sai yau kika wai waye mu kenan?hajiya kina wasa fa naga kin Fara tsorata da lamarin,karki sake kija baya inba haka ba komi zai lalace,zakisha mamaki nan gaba inhar kika ja baya damu"
Jikinta na rawa take cewa, "wallahi rashin kud'i sukai mun tsaye kwana kin nan,shiyasa kajini shiru,kai kuma ba a zuwa maka saida kud'i shiyasa saida na tara iya tarawa sannan nazo ayi min aikin gafara"
Wani sautin gurnani mai karfi ya karad'e wajen,saida ta dod'e kunnenta sannan ya ce "ga mutumin nan ya bayyana kiyi masa bayanin komi,yau dai kandala bata kusa na aiketa wani tsibiri inkin dawo wani lokacin sai ku gana,amma kin san kafin kiyi bayanin sai kin aje kud'i ko?"
"Na sani nakan tudu,shiyasa ban fito ba saida na shirya"
Ta zage jikkarta ta aje damen kudi sunkai miliyan biyu,sannan wannan dariyar ta sake karad'e dajin na wani lokaci sannan ta tsaya, "kiyi bayanin ki dan duwala yana saurare"
Ta gyara zama tana cewa, "godiya nazo na karayi maka d'an duwala aiki yana tafiya yadda ya kamata,wannan yaro dai har yau ba batun wani aiki sai kame-kame da yake,to haka nake so rayuwar sa tai ta tafiyar har abadan babu wani cigaba kamar dai yadda aka hana shi yayi karatun kirki wanda yayi ma don shine rabon sa,a hana shi duk wani abu da zai kawo masa cigaban rayuwa,sannan a sake cusa ma mazajenmu tsanar taimakon sa duk da kace zai wuya,to nidai a dage kota halin yaya ne a hana su taimakon shi,sannan bamu son yaranmu su sosu a damalmala tsakanin su,in bacin wannan ni banda wata damuwa sai ta uwar mijinmu dake son hanamu zaman lafiya,itama ai mana magninta karta sake uzzirawa mazanmu balle har su takura mana,sai kuma batun mijina asake kama mun shi sosai yadda duk sadda na nemi kud'i ba sai yaja ba zai bani,wannan shine kawai buk'atata"
Dajin ya sake daukar wannan dariyar fiye data farkon,kusan minty biyar har tafara kerma sannan ta tsagaita,amma tana yi kasa-kasa jitai na kan tudu ya ce, "buk'atar ki ta biya hajjaju,saidai d'an duwala yace kin tabbata babu wata matsala a had'in auren da kuke sonyi da y'ay'anku?"
Tayi shiru na wani lokaci kafin tace, "banda matsala da yar uwata,nasan hakan kuma suma yaran basu sa wata matsala,son junan su suke bilhakki da gaskiya ba za'a samu wata matsala ba"
"Ki je ki sake tunani,ki kuma saka ido ga yar uwar taki tunda kin yarda da ita sosai,kiga ba wata muna-muna da take kokarin yi? Sannan wannan yaro da kike ta kokarin a hana rayuwar sa tayi kyau,aikin sa babban aiki ne don nasha gaya miki daga shi har mazajen naku basu zaune haka nan,suna rik'o da azkhar sosai bama kamar shi yaron munsha wuyar aikin sa wancen karon sadda yana karatu,yana daya daga cikin nasarar gama karatun sa wannan azkhar din da yakeyi,gaskiya ki karo kud'i don na gaya miki taurarin sa sunsha banban da duk wani d'a dake cikin gidan nan,ke har mazajen naku taurarin yaron sun fi nasu kyau nesa ba kusa ba,in akai wasa arzikin da zai saiya kusan haukataki.........dakata nakan tudu bana son jin irin wad'anan maganganun,nidai ko nawa ne zan biya kar hakan ta faru,kai ni inba y'ay'ana ba kar wani yai arxikin da zai fisu,indai kudine zan kawo nawa kake bukata"
Wata mahaukaciyar dariya ya saki ya ce, "shegiya marar imani,to kamar wannan zaki karo daga haka komi kike so ki dauka anyi angama"
Ta Saki murmushi, "yawwa yanzu naji bayani,zuwa jibi zan dawo ma dasu"
Tatafi da baya-baya har ta bar wajen, saida tayi tafiya mai nisan gaske kafin ta shigo cikin wani kauye ta samu d'an mashin ya kawota cikin garin abujar.
*TAUFA! 🤔,A GANIN KU WACECE DA WANAN AIKI? UMMA KO MAMI?*
muje zuwa mu karasa lbrin.
Mom muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....13
Kwanci tashi ba wuya wajen Ubangiji sai gashi har min shiga aji biyu cikin nasarori,don kuwa daga zuwan mu har munyi suna sosai karma ace ni,don kokarina yasa duk malamanmu sun sanni sosai har ma da masu nuna suna sona ina ta kaucewa da guje-guje,ban yadda ma in nuna maka nasan abunda kake nufi to balle student masu nacin tsiya,ahaka dai aketa rarrakawa zuwa sannan su Anty sha'awa da Anty Rafea duk sun gama degree dinsu suna services haka ma yah najeeb shiyama rigasu gama wa,kowa yanxu cikin su services yake har an fara maganar bikin su,don tuni sun samu mazajen aure,tun kafin a saka rana mun fara shiri da tanaji,shi kuwa yah Rafeeq yana can shekara biyu xuwa uku ta rage masa,yayi nacin zuwa gida har yagaji karshe na murje idona na roki Abba Nura ya barshi yazo,aiko nasha fad'a na gwammace ban rokesa ba,don dole muka hakura ni dashi amma muna cikin tsananin kwadayin son ganin juna,duk da ba ranar da bamu video call amma a zahiri muke son ganin junan mu.
Anty sha'awa wani babban Dr ne zata aura yana da asibitin kanshi katuwa tayi suna a cikin garin abuja,sannan kuma yana aiki da babbar asibitin kwalwa dake cikin Garin abujar,da Mami taso ta bada matsala,cikin ikon Allah kuma abun yazo da sauki,ta hakura ta sauko.
Anty Rafeea kuma mijinta mint and print waje buga kudi kenan yake aiki,yana daya daga cikin manyan masu muk'ami a wajen,ita kuma ba wani son shi take ba akwai wani lecturan su a makaranta da suke soyayya kamar su cinye juna,to yana da mata itace matsalar data hana auren su,saboda matar har gida tazo tai rashin mutunci akan zai auri Anty Rafea,da alkawarin mummunan hukunci da tayi zatai mata,wannan ya tsorata Umma sosai daman gwanar tsoro ce indai batun kishiya ne,mafarin tasa Abba ya raba wannan kaunar,sai d'an abokin Abba yazo gidan wajen Abba anan suka had'u ya nace mata,ba wani so take ba kawai dai don su Abba sun nuna suna so ne ta amunce,a haka aka azo sanya rana goggo Habi suka sauka da ita da ahalinta Mufee da kamis da jamil,on ready daman mufeey age mate dinmu ce,sosai muke friending da ita ba kamar Najeeba ba,zuwan su yai bala'in yi mana dad'i gashi daman mun samu hutun mid-semister break,inda kawai muke samun matsala da Mufeey akan Yah Ramadan ne, ba tun yanzu ba indai suka zo to duk inda zaya tana manne dashi,ita kad'ai nake ganin yana sake ma fuska,wai ita Tausayin sa takeji sosai kuma bai mata komi ba akan ke zata ringa misbehave d'insa,don dole muka sa mata ido.
Muna jin dirar motar su a compound kamar wasu yara muka baza aguja nida Rukee,Goggo da Mufeey muka kaima cafka saida muka kusa kai su k'asa,muna ta dariyar farin ciki don ana iya kashe shekara uku zuwa hudu ba a hadu ba,
"Na shiga uku da yara zasu ida gawar da batasu ba,haka kuka zaka wasu broler's.........muka sake fashewa da Dariya Mufeey tace "Mamma ya kike so kiga sister's dina to,ai fiye da haka ma zaki gansu yan gatan Abba Taheer ne fa"
Muna ta farin ciki muka kwashi kayan su mukai ciki,Khamis sai tura baki yake wai bamu yi masa oyoyo ba,nai masa gwalo muka shige aiko ya riga kukan iya shege daya saba,don yaji ana ce masa auta bai ganin ya girma.
Ranar aka anshi kayan saka ranar su Anty,gidan ya cika ba laifi kowa danginsa na bangaren uwa sun zo sunyi hidimar da ya dace, in ana hidima gidan mu abun dad'i yake mun inason inga antaro ana ta shiga da fita,
"Ke nifa banga Favorite d'ina ba tun da muka iso,gashi har anyi sallar isha'i dazu da na gaido Mama na kasa tambayarta na manta"
Cewar mufeey muna dakin mu muna cin danmun naman kaza da lemu,kallon juna mukai da Rukee muka saka dariya bamu ce komi ba, tabi mu da kallo kafin ta ce,
"Wai har yanzu baku canza alak'ar dake tsakanin ku dasu ba,ku kam dai na kusa ince kunyi asara..........haba dai bari mana malama,wace irin asara kamar wani ubanmu ne shi,kinga bama so gaskiya"
Na katseta da fadar haka cikin murguda baki, ta girgiza kai tana cewa "ina jiye maku ranar nadama,abun da kuke ku kanku kunsan ba dai-dai bane ba abunda zance sai Allah ya shirya ku,saboda dai abunda yai Abba Nura da Mamma da Abba Taheer shiyai Abba Habibu,don haka ku cigaba daga inda kuka tsaya"
Ta tashi tabar dakin cikin fushi,tab'e baki nayi ina cewa Rukee "anya waccen yarinyar ba son wancen kazamin take ba"
Rukee ta ce tana dariya
"Wallahi har kin ban dariya,Allah natu ba duk mazan duniya ta rasa abunso sai shi.........saboda shi ba mutum bane komi?wallahi Rukee ku kiyayi kanku,kuji tsoron duniya uhmm wataran akeji,ashe gulmata kuka dasa dana fita"
Mufeey ta shigo tana fadin haka,ta haye gado tana danna waya, Na kurbi lemuna nace "au da gaske dai son shin kike?"
"Inason shi mana,bakiji ma sunan da nake ce masa ba ina son shi kamar yadda nake sonku,ba wai da sunan soyayya ba"
Mukai dariya nida Rukee muna kashewa, Rukee ta ce "Ashe kema kyamar auren sa kike,to ina ga ta waje da bata had'a komi dashi ba"
Mufeey idonta har ya canza saboda bacin rai,ta damu dashi sosai fiye da tunanin kowa, "wallahi tallahi bana kyamar auren YAH RAMADAN, da ace zanji ina masa so na soyayya kuma shima yaji hakan a zuciyarsa wallahi ko sama da kasa zata hade saina auresa,ba ruwana da halin rashi da yake ciki,ba ruwana da rashin gayunsa saboda don Allah zan soshi ba don wani abu da yake dashi ba,"
Tatashi ta shige toilet ta rufe k'ofar,kallon juna mukai nida Rukee saboda ganin hawaye a idonta sadda tana maganar,ba mamaki shigewar da tayi kuka take,
"Sis mubar mgnr Yah Ramadan da Mufeey,inba haka ba zamu samu matsala sosai tunda bata so"
Rukee ta fad'a cikin nuna damuwar halin da ta shiga yanxu, na daga kafad'a "hakan zaifi,fatana kar Allah yasa ta fada son shi don wannan tausayin is too much wlh"
Daga lokacin bamu sake magana irin wannan akanshi da ita ba,za muyi firar mu muyi nishad'i da taga lokacin dawowar sa yayi zamuga ta fita kawai,bangaren su take tafiyarta bata dawowa sai can dare,sadda zata dawo wayarmu muke nida Yah Rafeeq, saidai suyi fira da Rukee.
Goggo Habi sunfi d'a sawa sa Mama don haka can take sauka,hakan yana ma su umma ciwo sosai amma basu isa su nuna ta koda da baki ba,bayan idonta dai sunyi yan maganganun su gabanta kuma su sake mata fuska,khamis da jamil kuwa bangaren Hajja suke kwana abun su,zuwan su Goggo Habi ya d'an kara zumuncin gidan, tare ake breakfast da dinner,aita fira duk da ba acika sanyo mama ciki ba ita da goggo suke maganarsu,Su Abba kuwa abun yana musu dad'i,rannan ana Breakfast da safe ya kama weekend,kowa ya hallara hadda Yah Fahad daya zo gida don daya gama degree dinsa yai joining masters dinsa,shiyasa yana jima wa baizo gida ba.
Daman mufeey ce keyin sarving kowa a wajen,amma duk iyayenmu dake wurin favorite dinta take fara zuba mawa,yau ya zo a makare kamar ma sauri yake ya ce mata cikin sanyin muryar sa, "only tea mufeeyda"
Ta shagwab'e fuska,"Allah Yah ba zaka sha tea kadai ba,kaje ka wuni zungur a wajen aiki baci ba sha Abba kace masa yaci abinci da yawa"
Kowa ya saba da halinta tunda suka zo,Abbanmu da taima maganar yace masa "kai ko miye acikin tea Ramadan,ka kara da ferfesu mana tana ta ji dakai tunda suka zo"
Abba Nura ya ce, "Ai da yake ma itace kwanan nan baka ga yana yawaita murmushi ba"
Duk akai dariya banda su umma,nima d'in dai banyi wata dariya ba wayata nake dannawa ina duba sabbin pictures din Yah Rafeeq da sukai masifar kyau,inka ganshi zaka rantse ma d'an india ne, kamar ance in dago kaina mukai kyakkyawan four eyes dashi kamar an rik'e idona sadda naga yana sakin wani mashahurin murmushi wanda tunda nazo duniya ban tab'a ganin yayi irin sa ba,kai zaka d'auka ba daga fuskar sa yake ba,da mugun sauri na kawar da kaina don in nace bai masa kyau ba na zabga muguwar karya,magana suke da Mufeey ban maji me suke cewa ba,na gadai ta buga tsalle tana cewa thank you favorite.
Bansan miya toshe kunnena daga jin wace firar ake ba,fuskar sa dai cike da walwala yau ba kamar kullin ba,saida na dawo daki ne naji Rukee na cewa "ni yaushe rabona da buga basket ball gidan nan,ai harna manta"
Ina kokarin saka headphone na ce, "kina missing dinta kenan,"
"Sosai ma shiyasa banja ba da Mufeey ta shirya mana ita yau"
Aje headphone din nayi na ce, "ta shirya mana ita kamar ya?"
"Wai duk drama da akai bakiji ba ina hankalin ki yake"
Shiru nayi kafin nace, "inajin pictures din Yah suka dauke mun hankali sadda ya turo mun su,sunyi kyau sosai wlh kamar dan india na gaske"
"Uhm,to saiki shirya karfe biyar na yamma za'a fara,team d'in mu nida yah fahad da anty sha'awa ,sai ummi da jamil din.
Naku kuma Yah Ramadan da yah najeeb,da ke sai anty Rafeea da Mufeey"
Naja d'an tsaki, "da Yah Rafeeq na nan wasan sai yafi dad'i,kuma a rasa team din da za'a sani sai nashi"
"Uhmm kedai kika sani anriga an raba team dole kiyi hkr anan,bari nai wanka ki fiddo mana jessi d'inmu a wanke don sunyi k'ura"
Tun muna yara aka taso da wadannan wasannin a cikin gidan,mune volleyball,mune table Tanis mune basket ball wasanni kala-kala muna yi,da muka girma ne duk aka watsar,gidan babban gidane sosai ma duk muna da filayin yin su,Abbanmu da Abba Nura sun yi kokari sosai wajen k'awata gidanmu,karyar mai karya ya shigo yace bai burge sa ba.
*5:00PM*
A wajen filin wasan an zagaye sa da kujerun roba dasu Abba zasu zazzauna sune yan kallo,kowa na gidan ya fito ba wanda ya fita har su mama da Hajja duk sun fito kallo,yan team kuwa kowa ya shirya ya fito,kasancewar Family d'in kowa kyakkyawane sai jessin sukai masu kyau sosai,ni da Rukee kawai akejira tun a daki dana kalli kaina cikin dark pink dan blue Jessy din na Kara gode ma Allah,domin ya kyautata halitta ta sosai,kayan sunyi matukar yimun kyau rigar am less ce ta fiddo Boob's d'in sosai ma sha Allah,daman gasu a ciki ta fitar da shafaffen cikina,sai three quarter wando daya bi cinyoyina ya lafe,na daure dogo cikekken gashina mai sulbin gaske cikin pink ribbon a tsakiyar kaina sai na saka ban dana blue mai rubutun angel, "na rantse da Allah ban tab'a ganin kinyi kyau irin na yau ba, da ace qalbinki na nan wannan wasan ba zai iya buga shi ba saboda susucewa zai........dariya na kama yi nace "wallahi saina fad'a masa,ke dashi ne"
Tare muka fito muna ta dariya muna zaga yowa na hangi Mufeey ita da mutuminta sun sha nasu jessy din suma sunyi kyau sosai, duk kushen ka da hassadar ka dole ka fad'a,Rukee ta ce "ke mutumin can mugun yai kyau ko baki gani ba,shi gara ma yaita saka jessy din anfi ganin kyan sa"
Ban bata ansa ba saboda wani kallo dana hangi yana bina dashi,duk iya hasashena bazan iya gane ma'anar sa ba ya iya kallon munafurci wanda karyar ka ka fahimci manufarsa a kallon, tsaki kawai naja ina kaudar da kaina gefe,wajen su Anty Rafeea muka je kowa sai yaba shigata yake har su Umma da Mami,kar ma ace mami don wani iri ji take dani tunda muka soma dating da d'an gaban goshinta.
Abbanmu yace azo a fara don fita zai baison ruwa ya sauko baije inda zaije ba,don garin hadari keta had'uwa har ya fara baki hadarin, na ce ma Rukee "ina ma ruwan nan ya sauko ana cikin wasan nan,wallahi dana ji dadi ina son wasa cikin ruwa"
"Kedai Bari,amma kuma kinji ajikin ki inya dakeki ba"
"Ai magani zan sha,amma kam bazan wuce shan dad'in ruwan saman nan ba indai ya sauka yanzu"
Cikin kan kanen lokaci aka fara buga wasan,team d'inmu yawan ci duk aka tara k'wararrun amma duk da haka kusan minty shabiyar ba ajefa kwallon ba,karo na biyu ina isa ga inda zan jefa kwallon da jikina da nashi ya gogu zan saketa kawai inja baya raina b'ace,duk yadda na kai ga son jefawa da mun kusanto juna sakinta nake,karshe ta koma hannun su Rukee,tana koma wa zai ansota cikin hikima da wayon sa,haka aketa fafatawa karon farko ya jefata cikin raga,aiko su Umma da su Abba suka hau tafi da shewa,sai kuma naji kishin hakan haushi duk ya isheni,Abbanmu cewa yake "ai daman nasan Ramadan zai fara jefata a raga,keep it up Babban yaya"
Ya saki wani killer smile yana shafa sumar sa kamar ta india ya ce, "thank you Abba"
Kowa dai yaita yaba mishi,su Rukee kuwa suka hangula aka sake koma wa karo na biyu,nan fa su Yah Fahad suka dage baji ba gani muma muka zage,tuni na manta da banson had'a jikina dashi gogayya muke sosai ana son a cimma nasara,Mufeey tai wata irin fad'uwa Allah yaso ta yana baya ya tareta dalilin da yaja kenan muka fad'i, Yah Fahad ya jefa kwallo a raga,sai ihu da shewa aka hauyi na murnar anzo one-one, raina ya b'aci saboda duk iskan cin Mufeey ne shikuma sauna ya biye mata na ce mata "banza ai duk ke kikaja mana,ko ince kukaja mana daga duzgud'ewa zaki wani lauye,mtss sakarci kawai"
"Allah yasa bada favorite kike fadar sakarcin ba,waike miye damuwarki ne iye?"
Na sake hangula da maganarta, "naje nafad'a kiyi maganin abun,koma da wa nake ki dauki mataki........Roohee shot up karna sake jin wata magana anan,kafin na sab'a muku kuduka"
Abba Nura yai maganar,dole mukai shiru da yake rab'oce har ta fara hawaye,ta juya zata fita daga cikin filin ya riko hannun ta ya ce, "miye haka?oya come in"
Dole ta dawo ta tsaya position dinta,tana goge hawaye aka tillo ball muka cigaba daga inda aka tsaya,wasa ya dau zafi ta ko ina kowa so yake yacimma nasara,mun shafe mintoci sosai ana gwabzawa tari ya sark'e anty Sha'awa dole ta fita taje shan ruwa,fitar ba jima wa na anshe ball nai ciki da ita na buga tsalle na jefata a raga,sadda zan dawo na fad'a jikinsa ban ankare ba muka fad'i warwas a tare,can kuma sunata ihun murnar cin da mukai,kunya ce takaici ne haushi ne bazan iya gane me nakeji ba,saboda yadda na hayesa abun inka gani dole zakasan naji wani abu a raina,na saurin tashi cikin rawar jiki haushi ya tirnik'eni na juya kawai ina kakkabe jikina duk da kuwa babu k'ura a wajen,duk na diririce ne ban san dalili ba fita nai daga filin wasan naje na sha ruwa, su Abba suna ta yaba mun don nima nasan nayi kokari sosai,aka huta sannan aka koma round d'in karshe wanda sukai nasara Abba ya dauki nauyin gift mai tsoka a team din,saidai ana koma wa wasan aka soma yayyafi Abba yace shidai ya tafi komi kenan inya dawo yaji labari,ai kan kace me duk yan kallo sun watse saboda ruwan daya soma yawa,zuwa can Anty Rafeeq ta fece itama kafin Anty Sha'awa ta bi bayanta a takaice dai ko wane team ya rage mutum uku,can nasu Rukee daga ita sai jamil da ummi,namu kuma nida shi da Mufeey,a haka mukai ta bugata ruwa na sauka kanmu wani irin nishadi na ratsani,abunda na lura suma suna jin dad'in wasan da ruwan,jik'ewar da nayi yasa gashina ya bi bayana ya kwanta am less din jikina ta lafe sosai inka ganni kamar wata flawer don tsananin kyau,muna cikin wasan muka sake wani irin karo dashi gaba-da gaba kirjina ya dau zafi sosai, bansan nace "wayyo Allah na"
Yai saurin cewa, "I'm sorry"
A tarihin rayuwar mu wannan ce kalma mai taushi tsakanina dashi,sai na juya kurin bance komi ba,Mufeey ta ce
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 16