Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abubuwa suna caccanzawa yau fari gobe bak'i,mun shirya da Rukee kamar ba abunda ya faru saidai kuma ko yaka junan mu bama firar Yah Ramadan balle yan uwansa, iyakar mu dashi mu gaidashi in hanya ta matse mana,ko wata magana wadda ta zama dole sai munyi dashi,ba shiri amma babu gaba ko kad'an,sabgar gabansa yake muma ita mukeyi,yana yawan kwanciya asibiti lokaci zuwa lokaci wanda hakan ya fara damun su Abbanmu,har ya shirya masa tafiya zuwa india a duba lafiyar tashi sosai tunda nan sun ce ulcer ce ke yawan kwantar dashi,su kuma su Abba sun kasa yadda da hakan shiyasa yafara masa shirin tafiya can,amma kiri-kiri yace bazaije ba shi yana jin sauki jikin sa sosai ba sai anje har india ba,dole aka kyalesa aka sa masa ido. Kwanci tashi ba wuya wajen ubangiji sai gashi biki yazo,zuwa lokacin munyi hutun session zamu koma aji uku,murnar da nake saura shekara d'aya Yah Rafeeq d'ina ya dawo,nida shi kullin ba lissafin da muke inba na dawowar sa ba,ban san waye yake cikin tsananin d'oki da son zuwan wannan lokacin ba,kowa ji yake yafi dan uwan sa son zuwan wannan ranar,yadda nakeji a raina inama yana nan za'ai wannan bikin da abun sai yafi armashi,duk events din da za'ai sai yafi burgewa in muna tare,amma duk da haka bamu fasa shiri ba,tunda muka taso ba ai biki da wayan mu ba sai wannan karon,kuma gagarumin biki na y'ay'a biyu. Kudi Abbanmu yake saki kamar bai san darajarsu ba,su dukan su sune yai musu kayan d'aki na burgewa duk kushen mai kushe bai isa ya kushe kayam nan ba,shi kuma Abba Nura ya dauki dawainiyar duk wani nau'i na abinci da za'aci tun daga satin biki har a wanye,Abba Habibu kuma shine ya dauki nauyin duk wani nau'in lemo da ruwa da za'a sha a bikin,ba laifi yayi k'ok'ori don tunda aka soma hidimar kullin mota guda ke sauke lemuka da ruwa tatafi,kuma shine da wannan aikin. Rannan naje kan batun kudin d'inkunan mu na anko wajen Abbanmu,na ji yana ce masa Haba Yaya don Allah kabari ba abunda zai gagara ahidimar nan,mu so muke ka huta kwandalar ka bamu son tayi ciwon kai,kayi mana a baya yanzu ne lokacin da ya kama ta kaji dad'i,don Allah karka ce zaka dauki nauyin wani abu." Naji yace, "sai Ace ana bikin y'ay'ana Taheer kace kar nayi komi?na zuba ido kurin kuyi saboda kuna dashi,sai dai idan kun raina arzik'ina.........Subhanallahi!miya kawo wannan mgnr Yaya fisabilillahi" Cewar Abba Nura, Abba Habibun Ya ce, "to Nura ba dole ince haka ba,tunda kun kawo karfi yanzu ai dole kuce ku zakuyi komi" Duk jikin su yai sanyi, "kayi Hakuri Yaya ba nufin mu haka ba,wallahi da zuciya d'a mukai maganar nan nan" Murmushi yayi ya ce"na sani ai,don haka kubarni nayi abunda nayi niyya,ba donku zanyi ba y'ay'ana ne zan aurar" "Shikenan Yaya Allah ya saka da alkairi ya k'ara girma ya kuma ja da rai" Sai na koma kurin don kar suce ina musu lab'e, ina mamakin irin kaunar da suke ma junan su irin haka,kullin kara son juna suke bam tab'ajin koda da wasa sunyi musayar yawu ba,ko ja in ja basa yi,sunfi amfani da ra'ayin wanda yake babba karami sai yayi hakuri,hakika zumuncin su yana burgeni in bacin halin mu na mata ko ince in basu su Umma ai da bakaramin jin dadin wanan hadin kan za'ai ba,da ba wani fada ko tashin hankali. Ankuna kala hudu akai ni kam nida Rukee da Mufeey dinkuna kala bakwai mukayi,zamu fara saka wa tun daga monday d'in biki,don baifi saura kwana goma ba bikin shiri kawai ake ta faman yi,wani abu da naji yaso ya tsaya mun a rai naje Bangaren Mami neman Rukee ina daf da shiga bedroom din Mamin naji suna magana ita da wata kanwar ta, Mamin Ke cewa "shiyasa tun farko banso ta dashi ba mutumin nan sailuba,saboda banga wani abu da zai iya tsinana mana ba,ki duba kiga babban mutumin da Rafeea zata aura,wallahi tunda aka fara hidimar nan yake sakin kudi kamar hauka,ko jiya a bakin uwar nakejin yai ma amaryar alert din five hundred thousand kudin kama hall din da zasu kamu kawai,to nasan yau ma ya turo wasu kudin da zasu kwalliya,kina tunanin kafin a gama bikin basu tara dukiya ba,amma sha'awa ta bijire mun saboda tana son aga gazawar mu,ga Abbansu ya makale bakin aljihu ni kam ai na shiga tara wallahi,Allah ya sani inajin kishin mijin Rafeea sosai...........sai nai kwana na koma don ban san me zan sake jiyoma kunnena ba kuma,na jima abun yana damuna to miye matsalarta da kudin mijin Anti Rafeea,ba dole bane Allah ya baka abunda yaba wancen, in ta dauro wanda ya bakan shine alkairi a wajenka da wanda duk yake tare dakai,haka dai na share ban yi maganar da kowa ba muka shiga sabgogin mu. Yau ya kama alhamis saura tara biki,zamuje ansar d'inkunan mu cikin gari gashi Abba baya nan,inata kiran sa baya picking nasan kila abune mai muhimmanci ya hana ya d'auka,gashi dole sai da kudin zamu tafi duk munyi jigum jigum kowa da tunanin inda kudin zasu fito muke,daman Abbanmu yai alkawarin bamu to bainan,don kud'aden da dama gaskiya,ko na mutum d'aya kad'ai zasu kai 35k,naje ga Umma ta koroni wai in rabu da ita itama jiransa take ya cika mata zasu siyo wasu abubuwan,Abba Nura ma bai nan kuma ko hauka muke ba muzuwa ga Abba Habibu,duk damun san zai bamu in har mukaje. "Ga shawara mana" Cewar Mufeey,duk muka zuba mata ido nida Rukee, ta cigaba da cewa "favorite na nan mai zai hana muce ya kaimu,tunda daman taxi zamu shiga,kunga in mukaje sai daya ya shiga shagon yafito irin cikin damuwa kun gane,nasan zai tambaya sai muce sun hana kayan dole saida kud'i,kila ya bamu wani abun koda ba duka ba................ban san sadda dariya ta k'wace mun ba har ina fadowa daga gado,Rukee kan ta saida tayi murmushi mufeey ta soma k'ulewa ta ce,"bana son wannan abun kin sani,miye na dariya shawarar ce ba tai ba komi?" Daker na tsagaita na ce, "ke wai tunanin ki ko 30k yana da ita a account ne?to wallahi har gara ni ma inada 25k shi kau daker ne,ni banji shawara anan ba wallahi" Rukee tace, "ba batun raini bane Mufeey,wallahi Yah Ramadan baida wannan kud'in,in kuma kina ganin kamar mun son wulakanta shine muje kiyi masa magana ya kaimu,sai abi shawarar taki bamu san mizai faru ba koko Rohee?" Inta dariyar kasa-kasa na ce "sosai ma,ba asan inda rana zata fad'i ba" Tatashi ta fita duk jikinta yai sanyi,Rukee ta ce "bata san bai wani aiki babba ba,kila kallon k'udi take masa" Ina kyaran muryata data shak'e nace,"yau zata sani ai,inbam da kankanba sai kawai muce ya biya mana kudin dinki,uhmm bada Rohee ba nan gaba ai maka gori shiyasa Abba kawai nake rok'o kudi ko yai mun gorin banjin komi" Muna nan zaune ta shigo ta ce, "ku shirya shaf-shaf ni dai a shirye nake ina jiranku a mota........ai ke kam indai tafiya ce da shi to baki bata lokaci" Murmushi tayi tafice,doguwar rigace jikina ta Atamfa dinkin rafa tai bala'in yi mun kyau,ko ina ta hau jikina ba kamar daga kasa data bud'e kuguna yai daidai da rigar,haka daga sama ma ma sha Allah,d'an gyalena baki nai rolling kawai na d'an saka turare kadan na saka lipstick fari mai dank'o na zizara kwalli,amma a hakan inka kallan saika ce ma sha Allah. Rukee abaya ta saka bak'a tayi rolling gyalenta ni na daukar mana handbag muka fito,motar dai da yake fita da ita ce kamar kullin,don kamar ta zama tashi ma tunda duk inda zaya da ita yake fita,Abba yabar mishi key hannun sa. Baya muka zauna nida Rukee ita gwanar tana gaba sai d'umi take masa, saida muka fita cikin gidan sannan Rukee ta ce "Yah Ramadan ina wuni duk yau van ganka ba" D'an smile yayi ya ce cikin lallausan lafazin sa mai dad'i, "Ruk'ayya wallahi nima dawowa ta kenan" "Ayya kuma mun tado ka baka huta ba" "No,karki damu mufeeda tafi karfin na tsallake bukatar ta" Inajin su nidai bance komi ba hankalina na kan wayata,duk ina jinsu dai saida sukai shiru sannan na d'an ciro kaina in gaida shi silently na ce, "good evening" ta center mirror muka had'a ido mai makon inji ya ansa mun,sai ya lumshe idonsa kawai bai sake kallona ba,su kuma da basu san miyai ba sai mufeey tace, "Favorite ana gaidaka Roheen Abba na gaida ka" Yana karkata kan motar wajen shiga wata hanyar yace, "ohhh mufeeda na ansa fa" Ta ce, "Allah baka ansa ba,Rukee kinji sadda ya ansa ne?" "Aa gaskiya Yah baka ansa ba" Gajeren murmushi yai yace, "to ku tambayeta mana" "Wai haka sister?"inji Mufeey ta waigo tana kallona,toni mizan ce musu cewa zan ya ansa mun da ido?to yaushe ya ansa da idon shida ke tuk'i,in nace musu ta mirror ya zasu dauki maganar?sai na zab'i cewa "kila ya ansa banji ba" "To kaji abunda ta ce,kodai ta kurame kayi Yah" Jinjina mata kai kurin yayi don magana wuya take masa,nayi mugun mamaki ma yau da yake fira haka ni ban tab'ajin maganar sa data wuce seconds ba,har muka iso shagon mufeey keta masa fira parking yayi sai Mufeey da Rukee suka fita zuwa shagon,jira nake inga karshen wannan game d'in. Suna fita kamar jira sai ga Yah Rafeeq ya kirani,duk yadda na kai ga jin d'okin dauka sai naji na kasa daukar,komi yasa oho saida yai kira biyu a na ukun dole na dauka saboda zai damu, murya k'asa-k'asa na ce "Hello love" "Rooh na ykk" "I'm fine,saida kuma I'm so much missing u love" Murmushi yai mai sanyi ya ce, "me too,naki na fila ne Rooh ko yau na kira Abba na rokesa yabarni ko bikin ayi dani in dawo ko ranar monday ne,amma yaki ya Rooh ina nan saboda damuwa har zazzabi naji ya sauko mun,shiyasa na kiraki kozan samu saukin halin da nake ciki," Tausayin sa ya kamani nama mance inda nake, na ce "kaya kuri love shekara guda kamar gobe ne in sha Allah,inda ina da yadda zanyi wallahi da nayi,saboda ni ji nake nafika son in ganka,Amma tunda Abba ya hana kayakuri kaji ko karka saka damuwa ni ma tana iya shafata,saboda duk abunda da ya dameka to lallai ya dameni............karar buga k'ofar motar yasa nai saurin dubawa,sai sannan na fahimci da wa nake tare,kuma shine ya fita ya bango murfin mota kamar ana yak'i,hango su Mufeey da nai sun fito sai nace masa, "sorry love munzo ansar dinki in na koma gida muyi waya pls" "Ohk karki manta dani,inaso yau inta jin muryarki zai karfafa mun zuciyata" Nai masa murmushin da yakeso nace, "dont mind love" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....16 Fitowa nayi daga cikin motar dai-dai sun iso inda muke jikin motar,shidai wayarsa yake dannawa Mufeey ta shagwab'e Fuska, "favorite" D'ago kai yayi yana kallon ta, kafin ya ce "kun gama?" Ta sake narkewa, "Aa," Idanun sa suna lullumshewa ya ce, "why?" "Ba cewa yai bazai bada ba saboda bamu kawo kudi ba,kuma fa sun san ba guduwa zamuyi ba" Rukee ta ce, "duk Abba ne yaja mana,da yana nan duk haka ba zata faru ba..........aljihu yasa hannun sa ya ciro ATM yaba mufeey, "su cire naki dana Ruk'ayya ku anso mu tafi akwai inda zani" Wani tsalle ta daka da yar k'ara, "thank you so much favorite I really appreciate it" Har ta ruga zata koma sai ta dawo,nidai kallon su kurin nake ta tsaya gaban sa bayan ta dubeni fuska ba walwala yanzu, tace "Yah Rohee fa?" Bud'e motar yai ya shige yana cewa, "ban da ita" Duk sai sukai hucking suna kallona,ni kaina abun ya dakeni na farko har yaushe yake da wannan kud'in da zai iya biyan har na mutum biyu?kafin wannan mamakin sai na maganar sa ta karshe ya sake kama ni,Rukee ta ce "ko kin masa wani abunne bayan shigarmu ciki" Wani abune yazo mun wuyana ya tsaya mun,saboda bak'in ciki nama rasa mi zance don ina bud'e baki hawaye zasu zubo mun, na juyar da kaina kurin ban tanka ba, mufeey ta ce "karki kuka please..........Allah ya kyauta kukan me zan?shi har yana da kud'in da xai iya mun abu aduniyar nan ne?karki sake cemun haka" Duk yadda naso sarrafa b'acin raina abun ya faskara,iyakar k'ulewa nayi watau dole saiya nuna cewar nid'in ba komi bace a wajen sa,Rukee ta rik'o hannuna "come down pls,kiyi hkr danne bacin ranki" Fizge wa nai daga rik'on da tai mun,na shiga motar ji nake kamar zan banka mata wuta,su kuma suka koma shagon don kwaso kayan,kuma da gaske suka hana nawan saboda teloli basu da kirki,nai alkawarin nida sake kai musu dinki har abadan,bayan sun shigo motar ne shi kuma ya tada ta zamu tafi, naja wani dak'ik'in tsaki ni kadai nasan yadda zuciyata take tafasa,maganganun dake kai kawo a kirjina suna da zafi,saidai nasan fad'insu zai jawo mun matsalar da ban san karshen ta ba..........fitowa yai daga motar saidai kawai naji ya bude inda nake zaune, idanun sa jajir daker yake budesu muryar sa ta sake zama cool ya ce, "fito" Da idanuna da suka tun batsa da bacin rai sun firfito waje nake kallon sa, kirjina har wani d'agawa yake don b'acin rai na ce da rawar murya kuka na son kwace mun, "mizan yi?" "Idan kin fito saiki san ke zaki" Fitowar nayi ina jiran ganin ikon Allah,sai kawai naga ya rufe kofar ya juya zai koma motar, hawayen da bake rik'ewa suka silalo mun ban shirya ba muryata da kuka na ce, "Kana nufin anan zaka barni?" Wani kallo ya jefa mun ya bude murfin motar ya shiga, "duk abunda kakeji dashi inaji nima,saidai ka sani baka isa ka tsayar da numfashina ba,kuma yadda kakejin tsanata a ranka ni wadda bakeji akanka da zaka ganta saika tsorata" Ya jima bai tada motar ba,kansa a bisa sikiyarin motar tsawon lokaci yana a haka,zuwa can ya dago ya tada motar suka tafi,kuka na durkushe a wajen inayi mai cin rai,saboda irin yadda bakejin haushi da bakin cikin abunda ya faru,ban san iyakar lokacin dana bata ba naji dai ankira magriba, na tari taxi nahau na taho gida. Ranar kwana nayi cikin k'unci da bakin ciki,nama kad'aice ni kadai a daki na juyama kofa baya,duk iyakar hikimar su Rukee da Mufeey sun kasa shawo kaina,ko wayata kasheta nayi don ko ya kira bazai sameni yadda yake so ba,wajen eleven thirty na dare Mufeey ta dawo daga firar ta ita da Rukee ni kuma sannan nai sallar isha'i ta na gama ina linke sallayar Rukee ta jawo ledar data shigo da ita ta ce, "ga kayanki" Kallon ledar nayi na kalleta na ce, "kaya na?na ina?" "Ankon ki mana" Nai mata wani kallo kafin na ce, "waya biya kudin?" "Abba Habibu ya biya,mufeey tai masa magana" Bance komi ba na haye gadon nai kwanciyata,inajin su suna shirin fara gogesu nidai daga haka bacci ya dauke ni. ******* An shiga hidimar biki ka'in da na'in amare sunsha kyau kamar basu ba,mai gyara ta musamman aka dauko tai aikin kwana goma aka biyata,ita dai Anti sha'awa saidai Anty Rafeea ta biya kudin gyaranta angon bai bada ba,hakan ya sosa ran Mami sosai taita fad'a cikin jama'a daker Umma ta shawo kanta tai shiru. Ko hidimar event ba wasu kudi ya bata ba duk su Anty Rafeea ne keyin komi da kudin da Angota ya bayar,shi kam ai kamar ana masa ruwan su haka yake barar dasu,abu kadan da tai masa magana zai turo dubu dari kaza,mu kam ai gaba ta kaimu muna jikinta muna kwasar rabon bu,ranar alhamis za'ai kamu juma'a ayi Arabian sai asabar dinner za'ai,duk mun shirya tsaf sauran tsararrakin mu yan uwa na bangaren uwa duk muna tare dasu kodayaushe,mufeey ce zamu nema mu rasa tana can wajen wannan mutumin,don sunan da na koma ce masa kenan,inhar zan fadi sunan sa wani kullutun bakin ciki ne yake cika mun zuciyata. Duk inda zan shiga wayata nake da Yah rafeeq ina bashi labarin komi dake wakana a bikin,Bluetooth nasa ga kunnena sai anji ina magana ake gane waya nake. Alhamis tazo aka tafi kamu wani rantstsetsen hall da yagaji da had'uwa,an shirya shi yadda ya kama ta,an kuma tsara komi bisa ka'ida yadda zai tafi ba matsala,in zaka shiga saida get pass in babu KO waye kai saidai kaja baya. Irin wankan da mukai dole ma kace munyi kyau,namiji duk taurin kan sa sai munja hankalin sa akanmu,saboda duk inda muka wuce saidai ace Masha Allah tubarakallah,ankonmu mu uku iri d'aya ne less ne mai sunan less d'an kasar chana haka Abba yabiya kud'in oder sa nida Rukee da Mufeey kudi masu tsadar gaske,baida nauyi shawal yake kamar material red ne da golden sai ratsin light purple a jikinsa,gashi mai d'inkin ya zuba fasahar sa anan wajen,dukan mu gown ce akai mana an ratsa wani abun kwalliyar d'inki tun daga kafadar dama ya ratso ta tsakiya har k'asa,gaskiya munyi kyau sosai kamar wasu triple😂 Saida duk aka tafi ina can ina video call da Yah Rafeeq,na lalace wajen sa sai santin kwalliyata yake duk ya susuce ya hanani tafiya,ni kuma na biye masa muna ta shan kaunar mu,tun Rukee na magiyar in fito mutafi har ta gaji tatafi ita da Mufeey,daker muka rabu da niyyar dana dawo kamu zamu dasa. Sadda na fito naga gidan duk ba yawa,hankalina ya tashi za ayi babu ni na fito compound ba kowa ba alamar ma wata mota,wajen umma na koma "Umma ki kira Yah Fahad yazo ya daukan pls" "To ke miya tsayar dake har kamar yanzu,ai da hakuri kikai tunda ankusa tashi" Kwalla ta cika idona ina diddira kafafu, "please Umma ki kirashi inaso inje in aka tashi banje ba wallahi bakin ciki kamani zai" Dariya take ita da wata yayarta,tace "kin san halin Fahad dai ko?" "Ki jaraba Umma kila adace ya dauka" Nan ta soma kiransa har five missed call bai dauka ba,har na soma hawaye na fito na dawo compound din gidan, ba kowa kamar anyi shara na jingina da bango hawaye na silalo mun kan make up din da aka kashe kudi kanta, can saiga Abba Habibu ya dawo Sallar isha,na kauda kai na dauka wani ne cikin samarin da suka zo biki, "Rohee lafiyarki kike nan tsaye?ba kije partyn ba" Sai hawaye sharrrr suka zubo mun, na ce "Abba duk tafiya sukai suka barni,na rasa mai kaini kowa bai nan" "To daina kukan karki b'ata kwalliyar ki,ai zakije ko?" Nai saurin d'aga kai ya ciro wayarsa ya ce, "Ramadan na gidan nan baije ko ina ba,bari yazo ya kaiki motar tana waje" Wani sanyi ya ratsani,duk da haushin sa bar barni ha har yau amma indai zai kaini banjin komi, wallahi na ce "to Abba nagode" Ya shiga kiran sa a waya bugun farko ya dauka naji yana cewa, "fito ina nan farfajiyar gida ina neman ka" Ya sauke wayar yana cewa, "kwantar da hankalin ki yanzu zaki ganki kunje" Minty biyar sai gashi ya fito,wallahi ban dauka shi bane saboda tunda bake ban tab'a ganin sa cikin shiga mai kyau irin wannan ba,shadda ce mai mutukar tsada a jikinsa kalar golden dinkin zamani rigar iyakar guiwar sa take hannun mai links,tasha aikin computer ya zauna d'as jikin rigar kanshi ba hula sai lallausan gashin sa irin na Yah Rafeeq,ya sha gyara sai daukar ido yake kafarsa cikin cover bakake,.........."gani Abba" Bai tsaya bashi wata damar zillewa ba ya ce, "Anshi key din motar tun dazu na dawo masallaci na shiga, kaje ka sauke Rohee wajen partyn nan..........daskarewa yai dajin batun Abban,amma sai bai ce komi ba ya ansa key din shi Ku ma Abban ya wuce ciki, dagowa nai na kallai yayin da shima ni yake kallo,fuskar na ba fara'a kamar kullin..........."ni drivern ki ne?" Na ya mutsa fuska bance komi ba,don burina nidai ya kaini bazan rigima dashi ba yau duk tsiyarsa, ya waiga yaga Abba ya shige,sannan ya tako kad'an gabana "ki nemi wanda zai kaiki" Cikin sauri na d'ago manyan idanuna ma sha Allah na zuba mashi su,nai narai-narai zan kuka na d'aga murya zan kwala kiran Abba, na ce "Abba.........cikin yan seconds naji hannun sa bakina,da muryar da tunda nazo duniya ban san shi da ita ba yake cewa, "shut up,are u mad?" Ganin yadda na zuba mai ido yasa yai saurin dauke hannun sa ya matsa daga inda yake, yaja tsaki yai hanyar wajen mafarin na sauke ajiyar zuciya nabi bayan sa, mamaki nata kamani ashe ya iya gayu amma yake zama da k'azanta,yanzu inkaji yadda yake k'amshi sai kai mamaki kuma k'amshin mai dad'i mai shiga rai, na tab'e baki a fili na ce "duk da haka bai kama k'afar Yah Rafeeq ba," Sadda na isa har ya shiga motar kamar munafuka na bude gaban na zauna,ina ta duba wayata lokaci nata tafiya yak'i tada motar, har hakurina ya kare na ce "kaji lokacin nata tafiya" Kamar da dutsi nake magana,yai banza dani na danne fushina ban sake tanka masa ba,sai da ya mula ya mulmule sannan ya kunna motar muka dauki hanya, kin yin gudu yai sai ya ringa nawa kamar baida lafiya,a lalace yake sarrafa sikiyarin motar had'iyar bakin cikin kawai nake,har Allah ya kawo mu Hall d'in,saidai muna tsayawa na tuna gate pass d'ina........."innalillahi na shiga uku,don Allah ka maidani na dauko gate pass dina,wallahi ba za a barni na shiga ba in babu shi" Wani lalataccen kallo ya watsa mun,ya kashe motar ya kwantar da sit yai kwanciyar sa,tun ina iya sarrafa kaina har na kasa na soma hasala,amma na danne zafin raina ina rok'onsa.........."karen gidan ku kika maidani?karki cika mun kunne pls" Abunda yace dani kenan,nai shiru ina kai kawon numfashi sai na ja k'ofar in fita ko zan samu nasarar shiga da rok'onsu,sai me?.........ya gark'ameta na jiyo ina kallon sa idona ya cika da hawaye,ba kasafai nake kuka ba sai abu ya kai kololuwar bata mun rai,..........."wai miyasa baka kaunar farin ciki na,yanzu miye na rufe kofar" Kamar bazai tanka ba har na juyar dakaina gefe naji ya ce, "miye amfanin fitar tunda baki da gate pass din" Ban sake tanka masa ba nai shiru inata share hawayena akai-akai,bakin ciki kam ai ina shan shi akan wannan mutumin,baifi saura yan mintoci ba a tashi naji ya fita amotar,can wajen masu gadi yaje bansan meyaje yai ba zuwa can ya dawo ya ce "kije kishiga" Kallon sa nai kurin kullin abubuwan sa mamaki suke ban,bai dubeni ba ya ce "kifita nace,ni ina da wajen zuwa" "Ka mai dani gida" Na fad'a cikin dacin rai wani k'ullutun bakin ciki na mamayata a zuciyata, had'iyar kuka kurin nake ban cika son nayi kuka gabansa ba,rainin zai yawa wanda zai mun...........saboda kin daukan d'an iska,kin sanya an tadoni ina hutawa ta,na kawo ki wuri sanan kice baki shiga in maidaki,watau ga drivern ki ko?" Nai shiru saboda ina bud'e bakina kuka zan saki,kirjina ke kai kawo kurin..........."darajar ubana kikaci in bacin haka" yaja k'uta kawai bai sake magana ba bai tada motar ba saida yaga an fara fitowa daga cikin Hall d'in taron,sannan ya gyara kujerar sa ya ja muka bar wurin,kamar jira kukana yake mubar wajen ya kubce mun mai rikirkita zuciya,zallar bakin ciki ne kurin cikin sa har jijjiga nake saboda yadda kukan ya taho mun,tafukan hannuna na saka fuskata aciki ina kukan,tun yana yin kamar baiji har kukan ya ishe shi yaja burki gefen titi,wanda ba mota ko d'aya dake wucewa kuma akwai duhu,hasken fitilar kotar kad'ai ne sai wanda ya kunna na cikin motar,jiyowa yai yana kallonta yajingina bayan sa da allon kujerar, yai shiru kurin. Ban fasa kukan ba saima cigaba da nayi don ji nake inba kukan nayi bazan huce haushin dake dankare a cikin kirjina ba,Naji dai motar ta tsaya amma ban ciro kaina daga cikin tafukan hannuna ba,..........*"LAYLA PLEASE"* sautin ya ratsa kunnena sosai har ya sanya mun wani irin duka a kirjina,diff naji kukan ya tsaya mun don tsananin mamaki da rud'anin abunda naji,tunda nake rayuwata ban tab'ajin bakin sa ya ambaci sunana ba,sannan bacin sunan yadda ya ambace shi shine ya kid'imani,har hakan ya tilasta mun d'ago fuskata da tayi jaga-jaga da hawaye idanuna sun canza launin su saboda kuka na zuba mashi su,ido cikin ido muka tsare juna da kallo,gabana wani irin mugun fad'uwa naji yana yi,nai saurin kawar da kaina na rasa abunyi,na juyar da fuskata wajen window sai lokacin na ga inda muke. Shiru ya ratsa motar kamar babu bil adama aciki,natsuwa ta fara shigata na duba wayata naga network

Chapter 10 of 16