mun ciwo inyita kuka idan na kasa maida masa,shi kuma daman haka yakeso yaita dariya yana cemun rab'o ashe haka nake ma qawaye kuka suma,irin haka dai tasha faruwa ba iyaka ko inyi kwaalliya zamuje wani waje yai dalilin da zai saka a hana fitar ko ya dizgani inji na tsani kaina, karshe bazan je ko ina ba.
Muna falon Mami watau bangaren su Rukee assignment muke na physic,duk kaina yai zafi daman kuma nice karfin assignment d'in, to yawa ne dashi kuma ga kaina dake ciwo,Rukee daman in inayi take kallo don ta iya saboda ba subject din da bata ganewa irin sa,daker take sha a exam.
Jinai kurin an fige book din ta baya na a zabure na d'ago don ganin waye, "Aikin banza, wai wannan abun ya gagare ku fiddawa ohh ni Rafeeq, ashe daman k'ok'arin a baka yake malaman da alama cin hanci ake basu don su baki overall,yo inba haka ba ta ina zaki iya kawai dai an cuci overall"
Ya fad'a yana jifata da book d'in,tsare sa nai da idanuna da suka rage girma saboda ciwon kai, haushi da bakin ciki kamar suyi mun me?
Kwalla ta taru cikin idona na ce, "koma dai ya ya ne bai shafe ka ba Yah Rafeeq, nidai ka daina shiga sabgata............ked'in banza Roohe,saina shiga sabgarki inyaso kiyi duk abunda zaki"
Sai kawai na fara tattara kayana ina hawayen bakin ciki, "ai don kana ganina a bangarenku shiyasa kake mun duk abun da ka ga dama, ni kuma daga yau bani babu nan b'angar...........Miyai zafi Roohee karki yadda yai nasara akanki,daman ai haka yake so inajin sa yana cewa ganin ki bangaren nan ne baya so,ke kuma saiki biye sa"
Mami ta katseni da fad'ar hakan, Uffan bance komi ba,kuma ban fasa tattara kayayyakina ba ina hawayen bak'in ciki,ganin da gaske tafiyar zan kuma ya sani sarai in na bar Abu na barsa kenan.......keeee doluwa wai tafiyar zaki?amma anyi shashasha,baki san wasa ba ke wai?wallahi ke kam hamago ce, d'an wasan nan na abokin wasa ma baki iya ba,tirr da halinki"
Nai masa banza na nufi k'ofa Rukee da Mami ba wanda yace k'ala dariya suke ma abun su, "kin san waye d'aya?wallahi ba zaki fita anan ba salan kija mun masifa ga Abba ko?"
Na watsa masa idanuna manya tubarkalla masha Allah, nace "Ehy d'in,kuma saina fita tun da ba anan aka haifan ba"
Dariya yai tayi yana sake tare hanya, yana cewa "yawwa ko kefa, haka nake sonki ai,amma mutum kullin dunkum kamar dankali.......duk'ewar da nai ta kasan kafafun sa zan wuce yai wuff ya rik'oni ya zaunar cikin kujera, "kifa kiyayeni Roohe ba inda zaki saikin gama abunda kike, ni zolayarki nake"
Fafur yak'i barina in tafi na fara kuka na gaske ina cewa, "kabar ni natafi kaina ke ciwo zan sha magani ko"
Sauri yayi yaje ya dauki box d'in magungunan gidan yana ajewa gabana, "yawwa gashi nan, gaya mun ta ina kike ciwon kan in san kalar maganin da zan baki kisha,"
Na nuna gaban goshina inata hawaye sosai, "to share wad'anan hawayen tukun, stress ne ke damunki ki ringa hutawa alhuda huda"
Ya bani paracitomal tare da ruwa na sha
"Rukee ki rakata ta kwanta ta huta,in so samu ne kiyi bacci ma dakin tashi zakiji ya sauka"
Nace cikin laushin jiki da sanyin muryata "ni banajin bacci,assignment d'ina zan ida...........wai ke wace irin jarababba ce ehy?assignment din banza da wofi dalla malama kije kiyi bacci zan ida miki"
Ban sake cewa komi ba na mik'e Rukee ta kamani muka nufi dakinmu dake cikin part d'inmu, kwanciyar nayi nai lamo kamar mai baccin, Rukee tai tsaye kaina har saida na gaji nai magana idona a rufen,
"Wai miye ne?"
Murmushi Rukee tayi ta ce, "kawai wata extraordinary caring nagani daga Yah Rafeeq,kin san nafara lura da hakan kwana kin nan.........ya isa don Allah mi kike son cewa?"
Na katse ta dafar hakan ina lullumshe idona, xama tayi bakin gadon tana cewa "kawai ina ga ya fara canza wa daga yar tsama,lamarin sa yayi kama daaa........kinga don Allah kyaleni da maganarsa bana so,kije kawai bacci zan"
Shikenan ta kyaleni,shiyasa bama fad'a da Rukee duk abun da na nuna bana so tofa tabar yi mun shi ba kuma zata sake tada maganar ba.
Shiyasa muka shak'u sosai da sosai nida ita muna kaffa kaffa da bacin ran juna, kamar wasa kuwa sai gashi nayi baccin ban tashi ba sai ana kiran sallar magariba, kuma naji dad'in baccin ainun na sauko na shiga nai alwalla naxo nai salla,na gama na fita zuwa wajen ummanmu anan falon ta na iske su Anti Rafeea da Yah Rafeeq dasu Yah fahad suna fira,hadda anti sha'awa da Rukee...........jikin umma na lafe ina gaida su cikin jam'i muna had'a ido dashi yaja tsaki yana ci gaba da maganarsa kamar bai sanni ba, nima sai na fita sabgarsa nace ma umma yunwa nakeji,
"Rafeea samo ma Roohe abinci mana"
Yah Rafeeq yace, "wai Wannan katuwar za'a sanya ma abinci?haba Umma ke kike lalata ta wallahi,"
Nai banza dashi,Anti Rafeea daman jira take don ta tsani a sata tai mun aiki, "yawwa Yah gaya mata,sai kace dai Roohe ke sama dani don Allah don' Annabi.......to kawai kice baki zuwa mana ba shikenan ba"
Cewar umma,ni kam nai murmushi ina kallon ta tana banko mun harara lodi lodi, na b'ata rai "Umma kice ta daina hararata wallahi"
"Kyaleta Ai bata k'ari,"
Haka tatafi tana jin haushin aikin da aka sata akaina, daman kuma kowa yasan nice yar gaban goshin umma ba ummi ba,don duk da take da sunan mahaifiyarta to tafi ji dani,kuma hakan bai dameta ba tunda itama ana bata kulawa daidai yadda ya kamata, sai gata ta dawo bata zubo abincin ba tana ta fara'a tace "Sak'o mak'ok'o daga Abba,yace kowa yafito aje b'angaren Abba Habibu ayi dinner kamar yadda aka saba"
Haushi ya cika ni ganin yadda kowa ke mun dariya, alamun dai dole ai zan taka naje can naci sab'anin a biyoni dashi har daki.
Babu yadda muka iya dole duk muka tashi kowa ya wuce ya tafi, nice k'arshen tafiya don nawa na tsayayi saboda ba abunda na tsana irinz zuwa bangaren Abba Habibu a rayuwata, ba kuma don komi ba sai don bana son ganin wanan k'azamin Yah ramadan d'in wanda shi rayuwar sa kullin a k'untace take,fuskar sa kwata kwata babu annuri babu farar'a ga uwa uba girman kai kamar d'an wani shege,bacin basu ajeba basu ba wani ajiya ba amma sai fad'in rai, naja tsaki saboda tuna wa da nayi kujerata tana kallon tashi inda yake zama, haka nan na wuce don rashin zuwan nawa matsala ne wajena in Abba ya kamani, kowa ya hallara har an fara cin abincin naja kujerata dake kusa da ta Anti sha'awa na zauna ciki-ciki nake gaida Abba Habibun da shida Mama,na gaida su Abba Nura na soma zuba yar shinkafa yar kad'an na zabga coleslaw na zuba nama son raina har na kai spoon bakina Abbanmu ya katseni cikin b'acin rai........Roohe ashe baki da wayau har yanzu?su sauran yayyun naki kinfi karfin ki gaidasu,ki kiyaye ni fa!zan sab'a miki akan wannan taurin kan naki."
"Bita a hankali Mana Tahir,shi yaro ai d'an kwatanci ne da lallashi,nasiha ma inkai mata zata sa ta gyara,Roohe y'ata duk wanda yake sama dakai ya cancanci gaisuwa koda da shekara d'aya ne kuwa,kuma rashin gaisuwa ga babba rashin d'a'a ne,wanda bai cancanci ace daga gidan ne hakan ke faruwa ba"
Duk Abba Habibu ne ke maganar kaina k'asa ina sauraren sa, saida ya gama sannan nace "ayi hkr zan gyara"
"Allah yasa to,maza ci gaba da cin abincin ki"
Hakan bai sa na bud'e baki na iya gaida wadan da suke son na gaida ba, su Anty Rahma da Yah Ramadan, nai mirsisi abuna kamar ba aimun mgnr ba,haka dai aka gama kowa yaje ya gaida Hajja yai mata saida safe sannan katafi bangarenku,nida Rukee nan muke raba dare fira da Hajja tana bamu labarin k'uruciyarta da sadda take tashen samari,musha dariya musha takaici sai Abba yazo ya kora mu yana fad'a mun hana ta taje ta twanta ta huta, to sannan zamuje mu kwanta.
Washe gari duk masu shirin makaranta mun gama shirin mu,yan secondary daman dagani da Rukee sai ummi da Najeeba, Ada Yah Fahad ne ke kaimu to sai ya tafi makaranta sokoto udus acan yake degree d'insa,sai Abbanmu yace tunda Yah Ramadan baya zuwa ko ina ya daure ya ringa kaimu,wannan abun bai mana dad'i ba nida Rukee saboda kwata-kwata bama son kusanci dashi,haka nan muka tsangwamesa ba laifin tsaye babu na zaune,da mun ganshi ma sai mu kwashe da dariyar iskanci,uffan bai tab'a ce mana ba kallon mu ma bayayi balle ya nuna mana yasan munayi,gaisuwa kau inhar mun gaidashi to Abba na kusa ko Abbansu Rukee,shima a ginshire zamu gaidashi kuma zai amsa kamar bai damu ba,tun da ya soma kaimu muka tsiri iskanci kala-kala,kuma har zaman da ake yanzu bai tab'a tanka mana ba,sai infa Abbanmu na nan ko Abban su Rukee shine zai tsawatar mana kafin mu fito mu tafi.
Anti Rahma babbar gidanmu yayarsu Yah Ramadan,ita yake bi mawa ita NCE kawai tayi har ta gama anyi aurenta har da y'ay'anta mace da namiji ta farkon kausar sunanta,sa'ar ummi ce namijin kuma fauzan shekara biyuce tsakanin su data farkon,daga nan har yanxu shiru haihuwar,don bamu da wayau sosai akai bikinta.
Sai shi mr k'azamin gidanmu sunan da muke yawan ce masa kenan,tunda a ganin mu baya gayu irin wanda su Yah Rafeeq da Yah fahad keyi,ko guga bai damu da ita ba haka zalika nidai koda wasa banjin k'amshi na tashi jikinsa irin wanda su Yah fahad da Yah Rafeeq ke sawa,shiyasa kullin kallon mugun k'azami nake masa,to balle ga fuska koda yaushe kamar fuskar shanu,bana iya cewa ga ranar danaga dariya ko murmushi a fuskar sa, haba mi ake da wannan dunkum d'in mutumin, Anti Rafeea da Anti sha'awa sai Yah najib sune suke level 2 a jami'a sai dai kowane da kalar cause d'in da yake yi,shi Mr kazami one year kenan da gama degree d'in nashi har ya gama service kwanan nan,anso ya wuce masters abun bai yuwu ba kasancewar ba wani k'ok'ari ne dashi ba, akwai shekarar da saida ya maimaita ta a daddafe dai aka samu aka gama shi,duk da cewa ban tab'a zama dashi na minty d'aya ba amma a ganina inba rashin k'ok'ari ba mizai ja ace ka shekara biyar kana degree ka kasa idawa,a ganina kawai babu kwalwar ne kurin, Yah rafeeq duk gidan nan bayan ni babu mai k'ok'arin sa don zan iya cewa zamuzo tangal dashi,watau zamu zo d'aya shiyasa ma Abba Nura ya zab'armasa medicine,yanzu ma hutu ya samu na karshen shekara yana cikin shekara ta uku ne, don ya riga Yah Fahad fara karatun nashi wannan kenan.
Sauran masu zuwa jami'a kuma kud'in taxi Abbanmu ke basu suhau,in kuma driver na nan saiya kai ka in ka shirya,haka tsarin ya taho.
Tun seven thirty na gama shirina nai breakfast duk da bana cin komi da safen sai black tea kawai,a school ne in akai break wajen ten sai inci wani abu shima ba wani mai yawa ba,normally bana cin abinci sosai kuma ban damu da mai nauyi ba, Nida Rukee muna ta firar wani sabon uncle d'inmu da zai ringa mana civic education,muna ta dariyar yadda yake magana kamar wata mace ummi ta shigo cikin shirinta, fuska da fushi-fushi "Haba Yah Roohe,miyasa kullin sai kun makarar damu ne wai?in ku ba a muku tare mu kuma fa?kullin fa sai an mana warning haba don Allah"
Rukee ta kallan muka kyalkyale da dariya hadda tafawa, ta saka kuka tana cewa "wallahi Abba ne xai rabani daku, na gaji da wanan abun yanzu haka Yah Ramadan nacan kun shanya shi yana jira wannan ba dai-dai bane"
Ta juya fuuuuu tabar dakin, Rukee ta diro daga gadon tana cewa "wallahi bazan zauna Abba ya isko ni ba,ke dashi inya zo"
Ta kwashi takalmin ta a hannu da bag d'inta,nima cikin sauri nabi bayan ta da kayana a hannu a falo mukai kicibis dashi ya biyo sahunmu,ga Yah Ramadan a gefe.
Cikin fad'a Abba ke cewa "watau ba zaku canza halin ku ba ko?wane irin kunnen k'ashi ne daku?kodan hannuna bai kai jikin ku ba ko?to shikenan daga yau a k'afa zaku ringa tafiya,kila hakan ya zama darasi har ku gane kuren ku.........wayyo Allah mun tuba Abba,munbi Allah mun bika wallahi ba zamu sake ba,na rantse maka Abba ko bakin titin unguwar nan ba zamu iya kaiwa a k'afa ba,kai mana rai"
Nida Rukee muka zube muna magiya cikin tashin hankali,don mun san halin Abba kafin yai fushi irin haka ana jima wa,inko har yayi to anshiga tara,janye k'afar sa yayi yana nufar hanyar bangarenmu yana cewa, "bani kuka ma laifi ba wanda kuka ma wa inya hakura to,in kuma bai hakura ba wallahi maganata babu canji,Ramadan ka wuce ka kai Ummi da Najeeba kar su makara"
Bai tsaya sake sauraren magiyar da muke masa ba yai shigewar sa, tsaye mukai muna bin bayan su Ummi da kallo da suka bi Yah Ramadan don a sauke su, Rukee ta ce "wai Abba na nufin sai mun bashi hakuri?...........Tabd'ijam kice akwai matsala don wallahi ba zan iya ba"
Na katse Rukee da fad'in haka cikin k'unci,muna nan tsaye mun rasa mafita gashi yau zamuyi submitting na assignment d'in physic,kuma rashin submit din matsala ne,don bazai anshi naka daga baya ba, wata zufa ta karyo mun dana tuna da hakan, Rukee ta buga ta gumi a zaune cikin one siter cikin tashin hankali nace "Rukee yau ne zamuyi submit na Assignment d'in uncle harun,idan muka muce mun rasa 20 Mark fa"
Itama zabura tayi ta mik'e ta ce "na shiga ukuna,bayan rasa mark ma Roohe akwai punishment,innalillahi wa inna ilaihir raju'un ya zamuyi............sallalamin me kike anan kamar wani ya mutu"
Yah Rafeeq ya katse mana maganar,duk muka juya kanshi cikin son samun taimako, tuni idona ya cika da kwalla duk duniya ba abunda na tsana afannin karatuna irin rasa mark ko harf ne kuwa,yana tada mun hankali kasa ce masa komi nayi don nasan ma iza wutar zai bazai wani kawo solution ba.........Yah Rafeeq ka taimake mu yadda Allah ya taimake ka"............ta zayyane masa komi daya faru babu munafurci ko ragi a ciki,mi zai ba dariya ba hadda zama k'asa kamar wani yaro,yana yi yana kallona yadda tashin hankali ya bayyana b'aro b'aro a fuskata ga hawaye suna layi layi,
"Amma Abba ya burgeni wallahi, ba dai kun iya iyashege ba to Abba yafiku iyawa kuma ni nan ba abunda zan iya muku,gara ku gane kuren ku...........kuka na fashe dashi sosai ni kadai nasan bakin cikin da nakeji akan rasa mark din nan,ahankali falon ya fara tara mutane Mami ta fito saiga Anty Rafeea da ummanmu,da Anti sha'awa,
"Subhanallahi!,Roohe miya faru?halan wannan babban kwabon ne ya saki kuka?kai kuwa kaji kunya wallahi Rafeeq,ina anfanin abunda kake yi"
Mami ce ka fad'in haka tana k'arasowa wajena ta janyoni jikinta, har sannan dariya yake yana cewa "Aa karki dora mun laifi Mami,wallahi bani na kar zomon ba ratayar ma ban ansa ba"
Ummanmu ta ce, "mike faruwa Rukee,ya akai baku tafi ba har yanzu?halan Driver nakune saiya bata muku lokaci"
Rukee ta zauna dab'as cikin damuwa take labarta musu abun da ya faru, Anti Rafeea ma tabi bayan Yah Rafeeq wajen yin dariya ta ce, "ni kam dai na wuce umma saina dawo"
Haushi kamar zai mun me,yadda suke dariyar nan kamar zan je na shak'esu nakeji, Mami Ta ce "Miyasa Abban ummi zai haka?har wani abu ne nan da zai saurin yanke musu hukunci,shin miye aikin sa da bazai jirasu ba koma karfe nawa zasu kai?inace har biyansa yake akan hakan?gaskiya bana jin dad'in wannan abun"
"Uhm kema kin fad'a ai,ni na rasa wannan k'unata da yake yi da wad'ancan yaran(su Yah Ramadan) tunda sun nuna basa son shigowa cikin mu dole ne?ya barsu suyi sabgarsu muyi tamu mana,to gaskiyani ban yarda da wannan hukuncin ba,hakuri name zasu bashi sai kace sun zagi tsohon sa,wallahi ba zasu bashi wani hakuri ba saidai ya aje tukin...........dai-dai nan ya shigo da Sallama cikin muryar sa mai cike da mazantaka da kwarjini,naja dogon tsaki wanda nasan dole zaiji fuskar nan kamar kodayaushe ya gaida su Mamin,amma ba wacce ta amsa bai damu ba ya isa gaban umma ya aje key d'in motar yana cewa, "kiyi hakuri umma,indai akai wannan ne kibar b'acin rai nima Abba matsamin yayi,inbacin haka bazan anshi aikin daya bani ba,sannan ubana ne bazai sani abu ince bazanyi ba,amma tunda takai ga haka ki bashi mukullin motar sa kice yayi hkr daga yau bazan sake hawa ba balle rayuwaka su b'aci,har takai ga inda bai kamata ba"
Yana gama fad'in haka ya juya zai tafi, Yah Rafeeq ya ce, "wai kai nan zuciya kayi?ai wanda ke zuciya da abu wanda ya mallakin abun amma ba kai..........enough Rafeeq!!!"
Abunda bai tab'a faruwa ba kenan wai kaji Yah Ramadan ya d'aga murya da sunan fad'a ko b'acin rai,kowa yasan wannan..........
"Kar ka soma,ka tsaya iya matsayin ka zai fiye maka alkairi,kuma ni koda ban da abun to nafi karfin a wulakanta ni saboda shi,wannan shine"
Ya wuce kamar zai tashi sama,duk shiru mukai muka kasa magana,yah rafeeq ransa ya b'aci sosai duk da kuwa shine baida gaskiya, yace mun "ke kuma dalla can ki mana shiru da wannan kukan banzai,duk don zaki rasa mark dinki ne kike wannan kukan zanje nai muku submit,idan Abban ya dawo zanje na bashi hkr ya huce"
Har raina naji dad'in maganar, sai na tsaya da kukan, ya dalla mun harara ya wuce yabar falon,Mami tace "lallai yaron can wuyan sa ya isa yanka,shi nan har wata zuciya ce dashi...........yo ta banza da wofi inhar da gaske akwai zuciyar ya tattara tsaffinsa subar mana gida shine kawai"
Nan muka barsu suna tattauna maganar,muka koma d'aki muna cire kayanmu cikin sanyin jiki,duk da kuwa muna murnar dole Abba zai samar mana driver tunda burinmu ya cika.
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....7
Kwana kin da suka biyo baya Yah rafeeq ke kai mu makaranta,Abba yayi tafiya kwatsam shiyasa ba asake maganar ba Abba Nura kuma ba kasafai ya cika lura da abubuwa ba,kawai dai matsalar fad'an mu da Yah Rafeeq har muje sch muna fad'a dashi,in ya kaini bango inyita kuka dana fara kukan zai fashe da dariya,alamun yayi nasara.
Rannan har Rukee tace "ke kam dai to,har yau kin kasa Fahimtar Yah Rafeeq kukan ki fa shine alamun nasarar shi, da zaki burgeni ki ringa shanye komi zai miki,ni na rasa gane wannan kyara da tsokana tashi akanki,miyasa bai ma kowa ba sai ke?"
Alokacin ina cikin fushi ban bata ansa ba, amma nima abun yana mintsini na a rai miyasa bai tsokanar kowa saini?miyasa baya fad'a da kowa saini?rashin sanin dalilin yasa dole na bar a bun a raina.
Tunda wanan abun ya faru bamu sake ganin Najiba ba, daman kuma ko a sch ba had'uwa muke ba, ita tana B class mu kuma muna A kuma akwai tazara, daman kuma ba magana muke da ita ba itama kuma bata yi damu,don zan iya cewa tama fi yayanta iya b'agarar da mutum,ko iskar data kwasomu bata kallo balle ta tanka mana,inhar ta iske mu waje sallama kurin take bata kama sunan ko d'aya acikin mu,abun yana kara mana jin zafinta ainun,Rukee tace "kyale banza jin zafi ne kurin da Hassada"
To nasan akan Abunda ya faru ne yasa ta daina binmu,bamu san wanda ke kaita ba kila kuma taxi take hawa,.
Muna bangaren Hajja nida Rukee muna taya ta kwalemar bangaren Yah Rafeeq ya shigo cikin shigar sa ta gayu kamar ko yaushe, yai masifar kyau har fiye da kullin, brown shadda ce d'inkin zamani na matasa anyi masa harf jamfer ta d'an kamashi kad'an,ya saka hula milk da brown sai sawu ciki suma brown,kamshi kam kamar kamfanin turare ne a wajen,duk yadda nake zillewa kallon sa saida ya gane kallon sa nake, Hajja ta ce "kai Rafequ,wannan turare kamar na yan bori sai hawan kai yake,kaaji tsoron Allah ka rage sashi da yawa haka,ai saika dauki alhakina"
Me zamuyi ba dariya ba shima ya murmusa yace, "Hajja kawai dai kice nayi kyau ne baki iyawa, saiki b'ige da la'antar turarena"
"Haba dai,miye abun kyau anan Allah yajikan kakanku Alh matawalle in yayi gayu saboda kyan da yake har idon mutum disashewa yake,kaga kuwa ai baka kamo shi a komi ba,...........muka tintsire da dariya ganin yadda yake yamutsa fuska, na ce "gaya masa dai Hajja,"
Ya dalla mun wani banzan kallo, "ki fita idona kafin nai k'asa k'asa dake anan wajen,waya sanya dake iye"
Haushin ankushe masa gayun sa yake,dariya ta kamani Rukee dai tai gefe ta kame baki,don jibga takesha in ta shigar mun in muna abun mu, na ce "yo Yaj Rafeeq sai in k'i magana,ai gaskiya Hajja ta fad'a mu dai nan ba muga wani gayu na azo a gani ba wallahi.......a fusace yayo kaina na ruga bayan Hajja ina ihu.
"Kar ka kuskura Rafequ,akan me zaka daketa don ta fad' gaskiya komi?"
Huci kurin yake yace "wallahi Saina b'ata miki fuska,tun da na shigo na kasa dake?wajenki na zo,Hajjaa ki fita tsakanin mu kawai"
Dariya kawai nake masa Na ce "ashe babu dad'i kushen da kake ma wani,aiko wallahi daga yau na soma rama wa kodan kaji yadda nakeji nima........ban aune ba naji kauuuuu ga bakina,wani zogi ya ziyarce ni cikin azaba na fasa kara ina dafe wajen,dan danan har jini ya fito a lips dina Hajja ta ce "kai kai kai!Amma dai Rafequ anyi mugun mutun Ashe baka da mutunci ban sani ba,daga yarinya ta fad'i gaskiya shine kake son zubar mata da hakora saboda kana bakin ciki da kyawun da Allah yai mata?"
"Allah ya kyauta nayi bakin ciki da wannan yarinyar Hajja, ni kawai bana son rai ni ne kawai ba komi ba,kinga daga yau ba zata sake tsoma mun bakinta ba"
Ya juya ya fice ya barni inata kukana, Rukee keta ban hkr Abba Nura ne ya shigo ya nemi ba'asin kukana Hajja ta soma zayyane masa komi,hadda k'ari saboda itama abun ya bata haushi,cikin fushi ya sa waya ya kirasa "komi kake kazo nan wajen Hajja ka sameni"
Lallashina ya ringa yi yana ban hakuri tare da cin alwashin saiya sab'a ma shi,har sadda ya iso inata shashshekar kukana don ba kad'an ba bakin yake mun zogi ba,tun kafin ma ya zauna Hajja ta soma surfa masa masifa, "watau kai mai karfin duk duniyar nan shine zaka saki k'wanjin ka ka nausar mata baki,to wallahi ba zan lamunta ba ko ubanka ya rama mata ko ni in rama mata,"
Kanshi k'asa jijiyoyi sun fito sosai abunka ga farin fata,idon nan yai jaa sosai alamun bacin rai tsantsa tatare dashi, "watau ba zaka iya bud'e baki ka bata hakuri ba kenan,duk fad'an da zatai taje tai tayi bai dame ka ba ko Rafeeq?"
"Kuyi hakuri kuskure ne............karyar banza da wofi ba wani kuskure ai har shiga tsakanin ku nayi amma hakan bai saka ka fasa abunda kai niyya ba,yo Allah na tuba in bacin tsufa wallahi huncewa zan mu daku nida kai,bazan lamunci abunda zai takura mun takwarata ba eheee".........duk yadda naki cikin kunci saida nai dariya amma na duk'e ban yadda ta Gani ba,Rukee ce saida ta dara Abba kanshi murmushi ya saki,gogan ne kurin kamar ba ai komi ba fuskar nan murtik,nida aka zalinta ma ban kaishi fushi ba...........kalleni nan Rafeeq"
Ya d'ago yana kallon Abban, "sau nawa xan shata maka layi da Roohe?sau nawa xan maka magana akan tsokanarta da kake,watau ni ban isa in baka doka kabita ba ko?.........kayi hakuri"
Rafeeq ya fad'a kanshi k'asa yana kokowa da bacin ranshi, "yo to daman in ba hakurin ba me xaka bada,?ai ka riga ka cuceta kawai saidai Allah yai kata sakayya"
Hajja ta fad'a tana banka masa harara,Abban ya cigaba da cewa "wanan shine karo na karshe dazan ja maka kunne game da Roohe,inhar ka sake take dokata wallahi ni kadai nasan kalar hukuncin da zan maka, tashi ka bani waje"
Haka ya tashi a mutukar fusace,amma sai wanda ya sanshi sosai ciki da bai zai gane yana yin da yake ciki, Hajja taja tsaki bata ce komi ba illa dai nasan hukuncin bai mata ba, yajiyo kaina yana cewa "ki yi nesa dashi,bance kuyi gaba ba amma wannan tsokane tsokanen bana son shi,inkin san kina masa ki daina shi zai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 16