hakuri da yi mata adduar in Allah yayarda addua ta akanku ba zata fad'i k'asa banza ba,Abunda na gaya ma Najeeba Kaima shi zan gaya maka KAYI HAKURI RAMADAN,duk wanda yai biyayya gaa abunda iyayensa suka d'ora shi akai bazai tab'a tab'ewa ba,amma sai kayi hakuri hausawa sunce duk wanda yai hakuri baici ribar sa ba,to baiyyi da yawa ba,nasan abunda kake hangowa nima ina hango maka shi,amma duk in kukai hakuri watarana zaku bada labari,nasanka na san waye kai zaka jure duk fitinar ROOHEE DA MAHAIFIYARTA,zan cigaba da maku addua Allah ya baku nasara ya kara maku hakuri,"
Tunda abun yafaru bai samu natsuwar zuciya da kwanciyar hankali ba irin yanzu,tabbas in Allah ya azurtaka da iyaye na gari ya gama maka komi,
"Na gode Mama,Allah ya taya mu hakurin"
"Yawwa ko kaifa,haka nake so naji maza ka fito ka karya yau ba zaka lek'a wajen aikin naku ba?"
Kanshi ya shafa yana duba agogo, "sai gobe yanzu na makara"
"Allah ya kaimu lafiya,kafa fito ka karya"
Ya juya tafita tana ja masa k'ofar, yaja ajiyar zuciya mai nauyi da numfashi sannan ya mik'e ya shiga wanka.
*******
Daren jiya ba muyi bacci ba saboda firgitar da naitayi tsabar zazzabin daya rufeni,in kana kusa dani har hucin zakaji yana dukan ka tsabar fiver,tun Ummanmu na iya jurewa har ta kasa ta kama kuka sosai saboda in kaga yadda nake zabura ina firgita da kakkafewa zaka dauka raina ake zarewa, tun daga kan ummi da Rukee da umma har Abbana ranar bamu runtsa ba,Yah Fahad Abba ya kira muje asibiti sadda zai zo sai gasu tare da Yah Rafeeq,kowa yai mamakin ganin sa don tunda aka fara wannan kitimillin baya mgn karshr ma kamar zautacce haka ya zama amma yau gashi nan Alhamdulillah, "Rafeeq jeka kwanta ai kai ba lafiya gareka ba"
"Abba zan iya bata taimako ne,I'm fine"
Dole suka hkr ya dubani kasancewar medical doctor ne sosai, bai jima ma da fara aikin sa ba ba'a shekara ba, Yah fahad yaje ya nemo duk abunda ya rubuta masa cikin daren yai mun duk abunda ya kamata,allurai da drip dan danan na samu bacci.
"Koda da safe bata tashi ba kar atashe ta sai tatashi da kanta, kafin sannan kila prasure dake kanta ta sauka,itace tai causing wannan fiver"
Abba ya ce, "Allah ya bata lfy,kuje kowa ya kwanta"
Duk suka fito amma shi ya kasa barin ta ya fito,kallon fuskarta kurin yake yana jin abunda ke zuciyarsa kamar zai kashe shi,saida Yah Fahad yazo yajashi sannan suka wuce dakin su, umma ta ce ma Rukee inhar akwai matsala karkiji komi ki kiramu kinji ko"
Ta ce, "in sha umma Ba abunda zai faru ma"
*Dakin su Abba na*
"Maijidda,bari na gaya maki abu na karshe wanda daga shi ba zamu sake maganar Auren nan dake ba, LAYLA KO MUTUWA TAYI SAI AN DAURA AN KAITA GIDAN MIJINTA SANNAN A KAITA KUSHEWA,don haka daga rana mai kamar ta yau karki sake tun karata da maganar auren Roohee inhar ba abunda zai amfani auren bane, na gama magana"
Ya juya yai kwanciyarsa ya bata baya,umma cike da bakin ciki da takaici haka wuce ta shiga toilet don yin wanka.
Washe gari da safe duk yan cikin gida kowa yazo don duba jikina saboda jin halin dana kasance ciki a jiyan zuwa yau da safen,da sauk'i sosai don karfe goma da raabi na safe allurar ta sake ni,ina bud'e idona akan sa asuka sauka na rufe na sake bud'ewaa tunanin ko mafarkin daya aure ni ne nakeyi,amma still shine zaune gabana muna kallon juna......."How are u feeling now?"
Abunda ya fara fad'a min kenan yana ci gabaa da kallona,dan danan idona yaia rau rau zan fara kuka cikin sauri ya ce, "please stop it,kiji tausayina mana kukan baya isarki haka,bana so kinji"
Ga ummana ga mamin sa,ga Rukke da ummi har ma da Anti Rafeea da tayo sammako tazo gani na,ga Yah Fahad duk za gabansu yake maganar,kamar ma ba kowa gaban mu.
Lumshe manyan idanuna nayi masha Allah,sannan na bud'esu ina kalon kowa dake wajen, "Roohee yajikin,?"
Muryata ta sake koma wa yar firitt fiye ma da sadda nake kal'au, na ce "Da sauki Mami,"
Kowa yai mun sannu da jiki na amsa Anti Rafeea ta ce "mi kike son ci"
Na kalle shi wanda har sannan ni yake ta kallo kamar tv, na girgiza kai "Bana son komi Anty..........ki had'a mata tea mai kauri da zafi ta fara dashi,sannan ki soya mata planten da wainar kwai,idan taci sai tasha magunguna"
Abunda ya fad'a kenan,na turo bakina cikin shagwab'ar da na saba masa, "ni bana so"
Ya harareni kad'an ya ce, "ni kuma ina so"
Ummana da Mami suka fita, Yah Fahad ya ce "tunda kin dawo hayyacin ki ni bari na fita to"
D'an murmushi nayi k'adan wanda rabona dashi kafin a fara wannan dambarwar, shima ya fita yabar mu nida Shi da Rukee ummi ma tabi bayan Anty Rafeea,
Mukai shiru mu duka ba mai magana,Rukee dai toilet ta shige don had'a mun ruwan wanka,ita har yanzu banga wani reaction a tattare da ita ba akan batun auren ta da Yah Fahad,kodan bamuyi mgnr bane oho!
"Kizo kiyi wanka kafin ta gama had'a miki break din"
Kallon sa nayi shima idonsa cikin nawa,wani irin lumshe su yayi ya bud'e akaina yana jinjina mun kanshi alamun inje inyi d'in, na shagwab'e fuska kamar zan kuka "to karka tafi pls"
"Ina nan har sai kin karya,kije kiyi"
Hannuna na mik'a masa alamun ya tadani,ba musu ya mik'o mun nashi muka rik'e juna, wani sabon reaction ya shige ni kamar in dawwama ina rike da hannun nashi,dai dai shigowar Abba Habibu da Mama sai y'ay'an su, Oga kucaki da mabiyan sa, zame hannuna yayi yana mik'ewa cikin bada girma ga Abba Habibun ya ce masa "ina kwana Abba"
"Lafiya lau Rafeeq ya karfin jikin naka?"
"Da sauki Alhamdulillah"
Koma wa nai na zauna ina had'e raina kamar ban tab'a dariya ba, mama tayi masa yajiki kafin Abban ya jiyo kaina yana cewa, "Y'ata ya jikin, ashe jiya bakiji dad'i ba ya karfin jikin"
Murya ba amo na amsa, "Na samu sauki"
"Allah yasa kaffara ne,"
Ya jiya yana cewa Yah Rafeeq "in anjima da yamma ina son ganin ka Rafeeq"
Ya amsa cikin biyayya, "In sha Allah Abba zan zo"
Mama ta iso kusada ni tana mun sannu da jiki,fuska a d'aure nake amsawa, ganin yadda nai kicin kicin da fuska itama sai ta mik'e tana mana sai anjima, naja tsaki kad'an duk da kuwa ganin y'ay'anta dake cikin d'akin........."wa kike wa tsakin?" Cewar Yah Najib dake gefen Yah Kucaki, kallon da Yayan nashi yai masa yasa bai sake cewa komi ba, na sake jan wani tsakin nai banza na kyalesu bance komi ba, Yah Rafeeq naji yai ma magana "Ya mai jikin"
Shi kuma ya wani kalloni yana mun wani irin kallo, kafin ya ansa ba yabo ba fallasa "Alhamdulillah"
"Allah ya Kara sauk'i"
"Amin summa amin"
Daga haka suka fice daga d'akin inajin Rukee na cewa "sai Anjima Yah Ramadan"
Shigewata toilet nayi cike da jin dacin ganin su danai, a duniya yanzu ba abunda ke samun jin zafi a raina sama da ganin shi da ahalinsa.
A cikin toilet d'in na shirya na saka doguwar rigata yar kanti,mai mad'auri na daure su a bayana shafaffen cikina ya fito,wanda yaba Boob's d'ina damar bayyana sosai,kasancewar ina dasu ba laifi kuma yana yin dirin jikina yasa suke a bayyane,irin wanda ake cewa sharp din coca cola (😂),daha k'asa kuma ina Hips suma dai-dai misali ajikina in banda Hips dina da Boob's dina babu wani abu mai kiba a jikina,yar silib ce ni banda nauyi da girman jiki.
zama nai wajen stool d'in madubi ina dafe kaina yayin da nake kallon sa,shima ni d'in yake kallo yana yin idonsa ya sauya sosai,Rukee da Anti Rafeea suka shigo Rukeen ta aje tiren breakfast d'in gefen Yah Rafeeq, tana cewa " kaine alhakin sata ta cinye wannan abin da kasa aka had'a mata,don inba kai ba banajin akwai wani da zai sata taci"
Kallon su kurin nake,Anti ta tsaya tana gyara mun gashina daya jik'e wajen wanka,nai shiru inajin su suna ta firar su hankali kwance,ni dashi ne kawai bama mgn har ta gama mun lotion na shafa a jikina sai d'an roll all,daga haka na koma kan gado na jingina,
"Yah Rafeeq ka tabbatar kasata ta cinye fa"
Murmushi kad'an yayi yana daukar cup d'in tea din yasha madara da sauran kayan shayi,sai k'amshi yake silently yace "Karki damu,"
Fita sukai suka barmu tare,mik'o min yayi yana kallona wanda ni kad'ai nake iya hango abunda yaketa kokowar hidden a cikin idon sa,ko da caj a cikin idonsa nake fahimtar yana yin da yake ciki,tun yana karyata ni da maida abun wasa har ya sare ya yarda, ganin na tsaresa da kallo sai ya janye nashi idon yana cewa, "take it"
Ansa nayi na soma suffing kad'an kad'an,kamar kurame saidai kallon kallo,zukata suna suya suna ko kawa, yadda yake ta son kawar da abunda ke ransa yasa nima na ke kokarin danne nawa,amma abun yaci tura planten d'in da bake ci daker take wuce wa a makoshina,ba shiri wasu zafafan hawaye suka ringa zarya a kan kuncina, kafin na soma shashshekar kukan kirjina yana d'agawa.........."Ya salam! Rooh please stopped,kina son ki rikita ni ne?so kike na koma ruwa kenan?kin san irin ciwon dake cikin raina?gani na kurin ake Amman ni kadan nasan uk'ubar da nake ciki,pls ki daina"
K'ok'arin had'iye kukan nake ya k'i had'iyuwa numfashina nake ja sama-sama,cikin jin ciwo sosai da shashshekar kuka na ke cewa, "Yah Rafeeq.......naka....nakasa yadda a raina.......a raina cewar nida kai shikenan mun......mun rabu".........waye yace miki mun rabu?ba zamu tab'a rabuwa ba,abu d'aya ne muka rabu a kanshi shine AURE,amma kina nan a raina matsayin favorite cousin d'ina,kuma special qanwata"
"Ya zanyi da abunda bakeji akan ka?bazan iya kallon ko wane namiji sa sunan So ko aure ba Yah Rafeeq kai kad'ai nake ma wannan kallon"
Rik'o hannuna yayi duk ya susuce daga yana yin sa kad'ai zaka gane hakan, hawayena suka sake yawa suna zuba akan hannuwan mu, muryar sa da rawa-rawa ta dishe sosai ya ke cewa, "Za a wayi gari kin nemi hakan a ranki babu,Kiyi hakuri da KADDARAR MU haka Allah yaso, daman ba zamu kasance k'ar k'ashin inuwar Aure ba........."Hajja ta zalince mu, ni dai bazan iya yafe mat.....karki ce haka Rooh,"
Cikin fushi nace, "saina fad'a d'in, duk itace azzalumar miyasa tun farko batai kokarin dakatar da alak'ar ba,sai da komi yai nisa sannan?wallahi......ni.....nidai bazan yafe......yafe mata cutar dani da tai ba"
Zafin hawayen sa dake d'iga akan hannuna yasa na sassauta kukan da nake, sai ajiyar zuciya da nake kanshi ya sadda k'asa cikin wani mawuyacin hali,tsayin wasu lokuta ya mik'e kurin ya fice daga d'akin.
Sai kurin na sake rushe wa da kuka mai tsuma rai ainun,bana jin zan iya cire sa a raina haka zalika bana jin zan iya yafewa Hajja,saboda ta cutar damu mafi munin cutarwa,koma wane irin dalili gareta mu miye laifin mu? Da har zatai hukuncin da alak'armu............
*Nasan kowa ya k'osa yajin mafarin duk wanan rikicin,karku damu ana d'aura Aure zamu fara da MAFARI*
MOM MUHSEEN&ASAAD 😍
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....4
Haka na kasance yinin ranar cikin k'unci da k'unan zuciya,idan naga su Rukee na ta firar su ita da Ummi da Anti Rafeea sai inji inama ina cikin su,inama komi bai faru ba da bakina yafi na kowa kaifi,kullin saka rai nake zan bud'e ido inga na farka daga nannauyan baccin daya d'aukeni inga ashe mafarki nake ba gaske bane duk wannan rikicin,amma har yanxu ban farkan ba alamu sun gama nuna zahiri ne idona biyu abubuwan ke faruwa.
Gani nake shikenan nayi bankwana da farin ciki,nayi sallama da wata aba wai dariya,duk abubuwan da suka faru tsakanina dashi sun zaka tarihi,ji nake inama ace in samu losing memories yadda komi Zan wuce a kaina da zuciyata,hakan yafi mun sauk'i akan na zauna suna zo mun ga idanuna babi babi.
Tun da abun ya faru yauce rana ta farko dana kai goshina k'asa nai addua akan haalin da nake ciki,da kau zan sallame ne na koma gado na cigaba da kuka,sai na samu sauk'i kad'an danai adduar inayi ina kuka sosai ina kaskantar da kaina wajen Allah don neman sauk'i da mafita, ina kuma sake neman tsari da auren RAMADAN.
_"YA ALLAH KAFINI SANIN ZUCIYATA,BANA SON WANNAN BAWAN NAKA DA AKE KOKARIN HAD'ANI DASHI,YA ALLAH KA WARGAZA WANNAN HAD'IN,YA ALLAH KA KAWO SILAR DA ZAN MASA NISA,NISAN DA BAZAI IYA ISKONI BA,ALLAH KA SAMAN SAUK'I AKAN HALIN DA NAKE CIKI,BABU ALKAIRI TSAKANINA DA SHI"_
ban damu ba da adduar da nake,saboda inajin idan nayi Allah zai ansa kuma zai rabani da Auren da ake niyyar yi mun da wanda na tsana nake k'yama fiye da komi a rayuwata.
Haka na wuni kwance sai dai azo alek'oni a tafi,a kuma tambayeni ko inada buk'atar wani abu zaan girgiza kai kurin.
*RAFEEQ*
Dakin shi ya wuce ya fad'a bisa gado dafe da kirjin sa cikin wani irin yana yi marar misaltuwa,tun yana murk'ususu har ya soma kiran sunan Allah da d"an karfi,ya mirgino k'asa yana jawo drower dake gefen gado ya dauko maganin sa, yana haki da nishi ya afa abakin sa ya rarrafa ya dauko ruwa a bisa mirror yasha maganin ya wuce, ya zube nan k'asan kafet yana sauke numfashi,bayan minty goma ya fara jin sassauci,idonsa a rufe yana ayyana dole zai nesa da Rooh inhar yana son ya zauna lafiya,hakan shine zaman lafiyarsu shida ita inba haka ba za'a wayi gari ya mutu ta dalilin kaunarta dake neman halakashi,har akai azahar yana nan wajen daker yai salla ya dawo ya kwanta,sadda Mami ta kawo masa abinci bacci yake,ta aje masa tatafi bai farka ba sai karfe biyar agurguje yai wanka yai alwalla ta fito yai sallar cikin dakin,ya ga abincin ya dauka ya soma ci ahankali ba dan yana masa dad'i ba,sai don gujema tashin ulcer...........Fahad ne ya shigo masa da Sallama ya amsa yana kallonsa har ya zauna, sannan ya ce "Bismillah fa"
Murmushi Fahad d'in yayi ya ce, "karfe biyar har da rabi kake cin lunch?"
Jinjina kai yayi silently ya ce, "ya zanyi,bacci yaci karfina,to ya ake ciki"
"Abba Habibu keson ganin mu shine nazo kiran ka,"
Jinjina kai yayi yana aje plate d'in ya dauki ruwa yana cewa, "Abun da bai saba faruwa ba,Abba bai cika tara mu ba kai a ganin ka mekake tunani?"
Ya jefa ma Fahad tambaya, shi kuma ya ce "bai wuce kan batun case dinku ba,........case d'inmu dai ai yanzu kuma kun shiga tunda kuma auren dolen za'ai maku"
Yar dariya Fahad yayi "anya kuwa?nifa dama na jima ina son qanwata Rukee"
Hararar da yaga Rafeeq d'in na auna masa yasa ya fashe da dariya, "da gaske fa Nawan,"
"Ka gaya ma wani wannan maganar banda Rafeeq"
Ya aje robar ruwan yana mik'ewa daga inda yai sallar,links yake sawa na rigarsa Fahad d'in ya sake cewa,
"Ga Shawara mana my man,mai zai hana ku kawo karshen gabar dake tsakaanin ku kaida YAH RAMADAN,kun sani abunda kuke ba dai dai bane,beside Shine babban mu bai kamata ace ana masa abunda bai dace irin haka ba,kuma naga duk fitinar mutum bazai ce ga ranar da YAH RAMADAN yai ma mutum kallon banza ba,saidai ko ta wani bangaren amma ba nan ba............please ya isa haka muje kiran Abban mayi wannan mgnr daga baya."
Rafeeq ya katse masa hanxari,girgixa kai kurin yayi yana mik'ewa suka fice daga dakin.
*******
*ABBA HABIBU*
su duka zaratan samarin gidan ya kira don ya tattauna dasu a hangensa da tunanin sa za'a samu d'an dai-daito ko yaya tsakanin yaran dasu.
Acikin compound d'in gidan can cikin rumfa inda ake parking motoci,shimfid'a akai isassa da darduma babba Abban na tsakiya su suna gewaye dashi, Rafeeq da Fahad sune karshen isowa on ready RAMADAN yana wajen zaune, da alama sun jima suna magana da Abban, Fahad yaba Yah Ramanda hannu sukai musabaha sannan ya zauna gefensa, amma Rafeeq yai mirsisi kamar bai san da akwai mutum a wajen ba, Abban suka gaisar sannan suka natsu don jin dalilin kiran, "RAMADAN bude mana taron da addua"
Ba busu cikin daddad'an lafazee nashi da cikekken tajweed cikin karatun ya kammala tare da bukatar a karanta salatin Annabi aka shafa,sannan Abban ya fara da Rafeeq.
"Rafeeq banga ka ba d'an uwanka hannu kun gaisa ba kamar yadda Fahad yayi"
Sunkuyar da kai yayi kunya na kama shi ainun,Abban ya juya ga Yah Ramadan "Kai ma maimakon ka bashi hannun tunda shi bai hakan ba sai ka share shi, ashe abunda ake gaya mun akanku da gaske ne cewa gabar kuke?.........Abba ni bana gaba dashi wallhi"
Yah Ramadan ya katse Abban da fad'ar haka.........Aa kar ku maida ni sakarai mana,ba gashi kun nuna a gabana ba,ashe ku da zaku ga yara k'annan ku naayi ku tsawaatar ku dai-daita su shine ku ke aikata hakan,to ku gaya mun yadda za ku iya sasanci ko gyara b'araka irin wannan cikin k'ananku?"
Duk sukai shiru bamai magana saboda sun san basu da gaskiya,Abban bai saurari jin tsakanin su ba ta ci gaba da cewa, "kune manya ku zaku gyara zumuncin dake k'ok'arin lalacewa a cikin gidan nan,koma minene yasa bakwa ga maciji da juna bana son inji, abunda nake so shine daga raina irin ta yau inason naga canji a cikin mu'amalarku,inaso ku zama yan uwan da ake kwatance daku,inaso ku had'a kanku ku ukun nan ku yak'i rikicin dake cikin gidan nan,saboda watarana kune iyayen mu bama nan ta Allah ta kasance damu kasa ta rufe idonmu,idan har akace tun yanzu bakwaa shiri da juna ta yaya kenan saura zasu so yan uwansu,?"
Kowa yai shiru yana nazarin maganarsa wanda kowa yasan haka maganar take,don ba shakka zumuncin gidan nan na neman tab'arb'arewa,......."Don haka yanzu ba sai anjima ba kuyi musabaha da juna, tare da niyyar kun yafi juna kuma komi idan ya taso zaku zauna ku tattauna a a Fahimci juna,Ban da Matsala da Ramadan nasan duk abunda na d'ora shi akai bazai tab'a bijirewa ba,to inaso kuyi koyi dashi,Bismilla kuba juna hannu tare da Sallama"
Jikin su yai sanyi sosai karma ace Rafeeq daya dauki abun da zafi fiye da Ramadan d'in, cikin sanyin jiki Rafeeq yaba Ramadan Hannu yana masa sallama,shima ya bashi nashi suna gaisawa tare da amsa masa sallamar.
Fahad yai murmushi yace, "That's my brothers i like"
Abba ma yai murmushin suma duk sukai, Rafeeq yace "Abba kai masa fad'a akan rashin sake fuska,yana d'aya daga cikin abunda ke had'ani dashi"
Fahad yai dariya Shidai Ramadan murmushin kurin yake, Abban ya ce "to kaji Yah Ramadan,ko yaya ne a ringa ma y'an k'annan nan naka fara'a"
Shafa kanshi yake cikin muryarsa irin ta y'an gayu kuma silently calmly ya ce, "Shikenan,daga yau zan fara salan kuma ace tayi yawa"
Duk sukai dariya abun da yai ma Abba dad'i kenan, sannan ya gyara zama ya ce "Alhamdulillah Allah ya kawar da shaid'an tsakanin ku,magana ta gaba itace akan AURENKU ne,nasan kowa baya jin son wacce aka had'a shi da ita,bama kamar kai Rafeeq duba da yadda lamarinku yazo shi ya sake damalmala komi,inaso na baku hakuri kuma na rok'eku alfarma ku ba marad'a kunya,don Allah Ramadan,RafeeqFahad ku zama masu nuna biyayya ga abunda muka d'oraku akai,wannan auren yana daga cikin babban abu da zai kawo lalacewar zumuncin gidan nan,haka kuma shine abu mafi girma da zai kawo cigaba da sake d'orewar zumuncin,don haka ina jan hankalin ku da cewar duk ruwa duk iska karkuyi sake da matanku,kar kuyi abunda zai kawo cikas da yan tsugunne tsugunne,bance mutum in yaga wata yana so nan gaba karya k'ara ba,amma ya zama banda wulakanci banda tozarci inhar aka samu d'aya to ni bazan bada goyon baya ba,don Allah ku nuna mun cewar ni d'in na isa daku"
"In sha Allahu Abba ba zamu baka kunya ba,zamu yi bakin iyawar mu"
Cewar fahad kenan,Rafeeq ya ce "zamu kiyaye in sha Allahu"
Ramadan ma ya ce, "zamu yi duk yadda kace Abba in sha Allah"
Abban ya ce, "Allah ya yarda,sannan Rafeeq inaso ka zaunar da qanwar ka Roohee kai mata nasiha matsayin yayanta,sannan ka nuna mata yadda kai ka hakura ka amshi Kyautar da akai maka itama tayi hkr ta amshi k'addarata da hannu biyu,kila ta d'an sauko daga yana yin da take ciki"
Kanshi k'asa yace a sanyaye, "zanyi mata magana Abba In. sha Allah"
Sun jima yana nusar dasu abubuwa da dama da kuma kara haska musu rayuwa,saida aka soma kiran sallar magriba sannan suka tafi masallaci tare, har cikin ran Abba yaji dad'i sosai.
*Bayan kwana biyu*
Yanayin jikina ya sauya sosai na samu sauk'i don ina yin sabgogina yadda na saba,na kuma koma wajen aikina da nake service bautar k'asa wadda bamu jima da farawa ba, anyi jajena sosai friends d'ina suna ta fad'ar ramata alamun nayi ciwo ban gaya ma kowa ba azo a aganni,yak'e kurin nake musu saboda dai bazan iya musawa ba,saidai na basu hakuri akan cewar zan gyara next time,abubuwa da dama na daina tun dana dawo natsuwata sune bana zuwa b'angaren Hajja kwata-kwata,sannan bana fira da kowa duk nacin mutum,inma ta kama maganata da Rukee kawai nakeyi,sai ummanmu suma d'in daga uhm sai Aa sai tayi wuyar gaske inyi sentence da bai gaza kalma goma ba,sannan na daina zuwa b'angaren Mami in ta shigo wajen Ummanmu zan gaidata,tayi k'orafin har ta gaji kuma sun san dalilina nayin hakan,ba komi bane face bana son koda hanya ta had'ani da Yaj Rafeeq,muddin ina ganin sa ciwon dake cikin raina ba zai tab'a warkewa ba,Abba kuwa yasha jinin jikinsa daga yadda na koma tsani na dashi,iya kata gaisuwa da safe in ya fito zai breakfast ya tafi wajen aiki,daga haka bana sake cewa dashi k'anzil,bana tambayarsa ko biyar bana wata huld'd'a dashi bayan wannan.
Kowa dai yaga canji sosai tattare dani wanda ya kara ma gidan zama silent sosai da sosai,kowa baiji dad'in yana yin da nake ciki ba amma kuma ba su da wani abu da zasuyi mun da zan iya dawowa LAYLA ROOHEE ta ainahi, wani lokacin idan na tashi daga wajen aikin mu zan wuce gidan Anti Rafeea inyi zama na sai dare nake koma wa gidan,don da anga ma ban dawo da wuri ba to ansan inda naje, itace kad'ai bata gajiya da lallashina akan in saki raina,babu wani tsanani da Allah ke d'orama bawa don baya son shi,jarabawa ce yake maka don ya auna girman imanin ka,sannan a duk sadda Allah zai daukaka darajarka tofa sai kasha wahala kafin wannan daukakar tazo..........."Auren Yah Ramadan d'in shine d'aukaka Anti?"
Abunda nake gaya mata kenan,saidai tayi murmushi tace "shin kin san abunda Allah ya b'oye a cikin Auren nashi?bana so kiyi abunda zaki ciji yatsa nan gaba Roohee,.............Anti idan kin san irin wad'anan maganganun zaki ringa mun zan yafe zuwa gidanki na har abada,taya zan zo don na ringa samun sassauci anan amma ki isheni da wadannan maganganun,bana so gaskiya ki daina"
"Allah ya baki hakuri in Allah ya yarda ba zan sake miki magana akan Abunda ya shafi Yah Ramadan ba,in har bake kika mun ita ba"
Dajin kalamin taji haushi ammaa bata nuna mun ba, nace "Allah ma ya tsareni da maganarsa,yo wannan Allah na tuba har abun ai magana akansa ne"
Girgiza kai kurin tayi ta rabu dani,daga ranar bata sake yi mun mgnr auren bama gaba d'aya saidai shawarwari da suka shafi rayuwata.
B'angare guda shirye shiryen Auren ake don an siyo kayan saka rana na kowane b'angare,ana jiran lokaci an sanar da dangi da abokan arxiki da zasu anshi kaya,duk da dai agida d'aya muke amma baza'a fasa al'ada ba,Goggo habi na tafe ita dasu Mufee abunda ya d'an sanya na saki raina amma ba dariya nake ba,don rabona da ita har na manta ma gaba d'aya koba komi zamu had'u da Mufee jinin mu yazo d'aya ainun,acikin sa'anin mu Najiba ce kad'a a ware kuma itama dalilin iyayen mu mata yasa muka wareta,duba da cewar ba a shiri da uwarta da uwayen mu mata,duk da mun san cewa ba dai-dai bane hakan amma mun kasa jawota cikin mu,itama kuma sai ta janye daga garemu inba dole ba bata shiga duk abunda zai shafi sabgarmu.
Ana gobe ansar kayan saka ranar mu na tashi aiki na wuce gidan Anti Rafeea nai zama na, aiki ma na d'an taya ta mijinta zai bak'i da daddare zasuyi meeting shine akai masu meat pie da samosa da cake,sai kaji da aka soya tun rana ake aikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 16