Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai magrib muka kammala,mukai wanka ta bani wasu daga cikin kayanta na saka kasancewar jikin mu guda,saidai nafita Boob's don rigar ta kamani sosai,ina sallame sallar magariba kira ya shigi wayata,haske na gaani tana yi yasa na gane kirane don bana barin wayata da ringtone, wanda banyi tunanin kiransa ba ne ya kirani YAH RAFEEQ........wani irin fad'uwar gaba naji ras ras ras,har saida na rufe idona ban ankara ba ta tsinke ba jima wa kuma ta sake shigowa, ni kad'ai nasan irin bugun da zuciyata ke mun,kamar nayi gudun kilometer dari da hamsin tsabar yadda take bugawa, ban san hannuna ya d'aga kiran ba,ahankali kamar wacce hannunta baya aiki sosai na saka a kunnena nakasa cewa komi. "Kina gidan Rafeea ne?" Abun da ya fad'a mun kenan, kaina na d'aga masa nama mance ba ganina yake ba,daker na dai-daita kaina na iya fad'a "Eh,amma yanzu zan tafi gida" "OK,wait for me" Ya kashe wayar ya barni da zullumi har wata zufa nakejin tana karyo mun tsabar shiga zullumi,to mi zai kawoshi wajena?har cikin raina bana son ganin sa don kuwa ganin nashi maaiface a rayuwata, "Roohe lafiya kuwa?" Sai hawaye sharrrrr na rik'e hannunta muka zauna bakin gado ina hawayen na ke cewa, "Yah Rafeeq zai zo nan,ni kuma bana son na ganshi Anti,pls kice karya zo don Allah ga wayata ki kirashi kice komi zai fad'a mun ya fad'a miki saiki fad'a mun"............tausayi ya kama Rafeea cikin lallashi ta ce "ya isa haka minene na tashin hankali a ciki Roohee?Yah Rafeeq ne fa ba wani ba,babu abunda zai Faru kinji ko,shima nasan babban dalili ne zai sashi neman magana dake a keb'ance,ki kara daurewa komi zai wuce" Kasa magana nayi na dora kaina a cinyarta ina shashshekar kukan har na samu ya tsaya, "in sha Allahu Roohee wata rana zaki bada labarin wannan yana yin da kike ciki,zai wuce har sai kinyi mamakin wucewar sa" Nidai bance komi ba ta sake cewa, "bari naje na idasa shirya musu falon bayan sallar isha'i zasu zo" Na tashi daga bisa cinyarta na koma bisa filo na kwanta idona rufe ban san wane irin kalar tunani zan ba, Na shafe a kalla minty talatin a haka kafin Iklas babbar yar Antin ta shigo ta ce "Ammi Roohee Anna ta ce kizo uncle Rafeeq yazo yana karamin falonta" Kaina na d'aga mata kawai har ta fita na kasa tashi daga inda nake, saida Antin ta shigo ta ce "wai miye haka kike yi,haba Rooheen umma tashi kinji ko" Tashin nayi na dauk'i gyalena madaidaici na yafa ga kafad'ana guda kurin na dauki wayana na fito, ina tafiyar kamar iska zata kayar dani tsabar bana da wani nauyi da kuzari jikina,da siririyar sallama na shiga falon wanda har k'amshin sa ya isko ni wanda ke sake samun son kasancewa dashi a kullim, Ban yadda na ciro kaina na kallai ba na dai zauna cikin kujerar farko dana isko kaina k'asa na ce a sanyaye, "Ina yini Yah" Shiru na wani d'an lokaci banji ya amsa ba mafarin naa d'an ciro kaina na kalli inda yake kyakkyawan four eye's mukai da juna ya tsareni da kallo,idona yai k'wal-k'wal zan kuka na ce "shine zaka k'i ansawa" Sauke wani gauron numfashi yayi yana cewa, "naga ko kallonaa bakya son yi shiyasa,ammaa yanzu sake gaidani zan ansa" Ban san sadda idanuna suka maka masa harara ba na kawar da kaina, naji ya ce, "kai kai kai,ni kike harara ko?uhm kin kara ma kanki hukunci akan wanda ke jiranki," Na sake watsa masa wata na ce, "ni zan tafi" "Kin san fa bana son ana hararata,tau gara ma ki daina yarinya," Sai kurin na saka masa kukan dake ta kai kawo a cikin kirjina, kuka sosai wanda daman jiran abun da zanyi sa nakeyi,ai ko a rikice ya dawo kusada ni a k'asa yana magana cikin kid'ima,don a rayuwar sa babu abunda ke saurin nuna weakness d'insa irin kukana........"Rooh pls stopped,kin sani bana so don Allah ki daina, karki sa na kamu da rashin lafiya,in dan nine kiyi hkr ki fad'a mun me na miki amma pls stopped kinji" A rayuwata babu abunda da nake so sama da a lallasheni idan ina kuka, ya sani sarai shiyasa yanzu ma nad'an sauko na fara rage kukan ina cewa, "gashi nan hankalin ka a kwance shirin aure kake,ga dukkan alamu baka damu da halin da nake ciki ba,watau kama amunce da wacce aka baka kenan" Ina shashshekar kukana kasa-kasa,ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi ya ce "Rooh kece fa kike guduna,duk hanyar da zan ganki kinbi kin toshe ya kike so inyi, sannan koda na tashi hankali na kamar a farko Rooh ba abunda zai canza k'addarar mu,a riga ta faru babu yadda zamuyi da abunda Allah ya shirya a tsakanin mu,daman ba zan zama mijinki ba kema ba zaki zama matata ba,wanin junan zamu aura pls and pls Rooh ki cire komi ya fawwalama Allah kinji ko," Hawayen sunk'i tsayawa nake cewa, "taya zan iya cireka a raina da sunan wanda nake kauna nake burin Aure,taya zan canza wannan mafarkin nawa na sanya wani akai?wallahi bazan iya ba,koda anyi wannan auren sunan anyi ne amma bazan tab'a zama matar wannan k'azamin kuma kucakin ba har abada.............RAFEEQ KABAR PHONE NAKA ANA TA KIRA" maganar kurin mukaji ba tare da munji sallama ko motsin da zai aankarar damu shigowar sa ba, kallon wulakanci na watsa masa na kawar da kaina ina goge hawayena, ko a jikina ban damu dana yaji kalamin da na fad'a ba,sab'anin Yaj Rafeeq da yaketa jin kunya yake kame-kame, "Ayya na shafa'a ne, na barka kana ta jira to ka shigo ka zauna sai mu wuce,har ma kun gaisa da Wife d'in taka to be ko?..........Allah ma ya sawak.........zan sab'a miki idan na sake jin wata magana marar dad'in ji anan LAYLA" Yah Rafeeq ya fad'a cikin fushi sosai da na dad'e bangan shi a ciki ba,fuskar sa ta d'aure ta mau ainun kamar bai san dariya da murmushi ba, Yah Ramadan ya ce "sai ka fito ina jira" Ya fice ya barmu anan zan cigaba da kukana ya ce, "tun da baki san lallashi da banbaki ba zan tattaraki na fita harkar ki,rashin kunya da fitsara ba halinki bane karki sake ki aro su ki yafa ma kanki saboda kina k'insa, don nasan watarana zaki nadama,nasiha nazo inyi miki matsayina na yayanki kuma wanda kika fi shak'uwa dashi a duk cikin yayyenki maza,Aure babu fashi Rooh sannnan masifarki da rashin kunyarki da duk wani kalar wulakancin da kika tana da don shi bazai fasa komi ba,saima dai ke ki jefa kanki cikin wani hali,don nayi imanin RAMADAN ko sama da k'asa zata had'e bazai tab'a SAKIN ki ba,don kuwa shi d'in mai biyayya ne ga umurnin iyayensa,da duk wani na gaba dashi nai masa wanna shaidar,don haka shiyasa muka muka daura d'amarar koyi dashi nida Fahad,zamu zauna da matanmu cikin amana da kwanciyar hankali har Allah ya kawo ranar da zamuji muna son su,tunda zuciyoyin mu ba a hannun mu suke ba suna hannun Allah,a duk sadda yaso yana iya canza komi,don haka don Allah Rooh don girman Allah ki zauna bil amana da RAMADAN, wallahi summa tallahi zakiji dad'in zama dashi baida fitina,baida hayaniya baida mugun nufi akan ki akan kowa ma,in kikai hakan zanji dad'i kinji nasiha ta kuma kin girmama maganata, ina miki fatan alkairi Allah ya canza abunda yake zuciyarki" Sosai nake kuka wanda har bakajin muryata saboda yadda nakeyin sa cikin fidda zallar bakin cikina, Har ya juya zai tafi ya tsaya bai waigo ba saboda kukan yana tsananin ratsa shi,wani yana yi dake cinsa yana neman galaba akansa ya ce, cikin raunanniyar murya "bazan tab'a juya miki baya ba Rooh,duk sadda kike da matsala karki tun kari kowa kizo gareni,duk girman ta ina fatan Allah ya bani ikon warware miki ita, Bissalam" Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....5 Saboda halin dana kasance a ciki yasa saidai a gidan Anti Rafeea na kwana,don kuwa kuka nasha na koshi wanda har sai da ya haddasa mun ciwon kai da zazzab'i, na kuma hana ta sanar da Ummanmu kowa ma hana ta nai ta gaya mashi, saboda bana son wannan taron dangin akaina. Raba dare mukai tana lallashina da bani hakuri tana nuna mun shi namiji ma ya hakura ya kauda komi saini ce zan nace inyita damun kaina da rashin zaman lafiya? Da nasiha da ban baki har dai na samu nai shiru, ta kawo mun meatpie naci da tea mai kauri nasha magani sannan nayi isha'i,na dora da shafa'q da wutri, na jima a sujjadata ina kuka saboda adduar da zanyi nauyi take mun, daker na iya ambatar "Allah ka samun sauk'i da salama a cikin zuciyata,ka sassauta mun zafin kishin yah rafeeq ka sassauta mun kaunarsa ya Allah" Da wannan na samu nai bacci wanda na jima banyi irin sa ba. ******** Tun daga wannan rana na koma yin rayuwata kada ran-kada han,ni bana cikin farin ciki haka zalika bana cikin k'unci,yadda nake da magana amma yanzu wuya take mun ainun,ummanmu duk juyin da zatai inyi fira da ita bana iya wa Abba kanshi duk ya damu da yadda na sauya masa,iya kata dashi ina wuni ko ina kwana,sannan in an had'u cin abincin dare nice farkon gama wa in tashi kuma in na saddar da kaina k'asa bana d'agowa har sai na gama,saboda kowa ma ni bana son had'a ido dashi. Bikin ba fashi an sanya shi wata hud'u anan gaba,don tuni har anfara shirye shirye, daga b'angaren iyayen mu duk yadda basa son bikin amma bai hana sun fara shiri ba baji ba gani, ni kam nuna wa nake kamar ban san me ake ciki ba,nafi zaman gidan Anti Rafeea don can ne kurin nake iya fira sosai,Rukee kanta tasan na canza amma ba yadda ta iya dani dole ta samun ido. Rannan ina kwance uwar dakar ummanmu naji suna wata magana ita da Mami akan aurena da YAH RAMADAN, wadda nan take shawarar bata shigan ba, Ummanmu ce ke cewa Mami, "Safiya wallahi auren Roohe da yaron can neman d'ora mun hawan jini yake, dana zauna ban da wani tunani sai na neman hanyar dazan lalata abun,wallahi ni rayuwata ma ban jin akwai abunda na tsana irin auren nan nasu,duk hanyar da nake tunanin zanbi sai maganar Abban su tai mun tsaye a rai,ban san ya zan ba" Mami ta ce, "Maijidda kenan, ke yanxu har sai hanyar raba wannan auren ta gagareki?ni nan jira kawai nake inji kince mun kin shirya kawai mun nntaya tare," Umma ta ce cikin rashin Fahinta, "Bangane ba?wace hanya ce wannan haka da ban san da ita ba,kimun yadda zan gane" Dariya mamin tayi tana cewa tare da rage murya, "hajiya Huda k'awar nan tawa take bani labarin wani malami wallahi ya kware da aikin sa, tun da taje wajen sa ta samu kan d'anta isah da matar ta rabata dashi, to shine tun da taji halin da muke ciki tace wallahi zata raka mu cikin kwana uku maganar auren zata lalace na Roohe da Rafeeq, don wallahi da ya auri d'iyar mak'iyyata gara ya dawwama babu aure" Umma tai jimmm kafin ta ce, "safiya nifa duk abunda za'a had'a da shirka bana son shi wallahi,malam man nan wasun su basa tsoron Allah bokaye ne wallahi" "Ko d'aya maijidda,wallahi shi ba haka yake ba in munje ai zaki ganema idonki,rubutu ne zai bada ba wani abu ba fa" Jin inda suke son kai kansu saboda k'iyayyar auren mu yasa na taso na fito daga d'akin na d'aga labule ina cewa, "Mami,ummah,inhar don farin cikin mu zakuyi don Allah karku fara kai kan ku halaka,inhar kun yadda dani ba sai kunje wajen wani boka marar tsoron Allah za'a samu mafita ba,ni da kaina zan kashe auren bayan an d'aura nai maku wannan alk'awarin, shi kuma yah rafeeq ku barsa da Najeeba don naga alamar shi ya mik'a wuya,don Allah kar kuje wajen wani boka pls" Mami ta ce, "shikenan Roohe Allah ya baki sa'a,don auren dole babbar masifa ce" Na juya na koma dakin cikin tunani mai tsawo,taya zan iya kashe auren bayan anyi?nan danan zuciya ta shiga sak'a mun abubuwa baji ba gani,hadda wanda ban sanma ya akai ta hasaso mun shi ba,kuma na yadda da kaina dari bisa d'ari inhar nice zan kashe auren in sha Allah,burin su ai a daura ko?to kuwa bayan na tare bazan yadda koda yatsana ya tab'a ba zan bud'e masa shafe shafi na bala'i da masifa, ko baya kaunat uwatai saiya sawwake mun. (Tofah🤔, bari dai mugani Roohe) ******** Bamu sake haduwa da yah rafeeq ba tun zuwan sa gidan anti,ban nemai ba shima haka inda nasan zan ganshi ma bana zuwa kwata-kwata,bangaren nasu ma nai mashi yajin aiki Rukee har ta gaji da mun korafi,duk ita dakin mu guda bacci ke kawota tafi wuni bangaren su. Rannan ranar wani weekend ina ta game a laptop d'ina Ummi ta shigo dakin mu tana cewa, "Yah Roohe Abba na kiran ki" Dagowa nai ina kallon ta bance komi ba,illa nasan da dalilin kiran tunda rabon daa muyi magana nidashi kamar yadda muka saba tun kafin batun auren nan,saukowa bai daga gadon ina sanye da riga da wando kanana rigar iya cinyata wandon pencil ne, sunbi jikina sosai suyi kyau hijab d'in sallata na zira na nufi falon sa. Da sallama na shiga dai-dai sadda ya d'ago manyan idanun sa tubarkalla mukai four eye's,ras ras naji gabana ya fad'i nai saurin kawar da kaina naja tsaki dai-dai yadda xaiji ba tare da Abba shi yaji ba,na wuce da na isa inda Abban yake na zauna k'asa ina gaida shi.........."Abba ina wuni?" "Bazan tab'a ansa gaisuwarki ba Roohe har sai kin gaida Ramadan," Cikin fishi da bacin rai yai maganar,kaina k'asa ban dubi inda yake ba na gaida shi ciki-ciki, "ina wuni" "Lafiya lau" Ya amsa a takaice muryar sa clearly ba wani abu a cikinta,ma'ana haushi ko farin ciki babu ko d'aya, duk mukai shiru na wani lokaci kafin Abban ya ce dani, "LAYLA nasiha zan miki matsayin mahaifin ki daya isa dake,tun da aka fara batun auren ki bance miki komi ba akai,na bari ne inga iya hankalin ki da kuma samun natsuwarki tun da baki da lafiya,a yau daya rage auren ku baifi sati shidda ba shiyasa na tara ku don nai muku nasiha da kwatanci,Aure dai da kuke ganin sa ba abun wasa bane ba abun rainawa bane,kar kuga cewar bakwa son juna akai auren kuje kuyita yin abunda kuka ga dama akai,kowannen ku yana da ilimin addini dai-dai gwargwado,kunsan abunda yake haramun da wanda yake halas ne,kunsan hakkokin miji akan matarsa,haka nan kunsan hakkokin mata akan mijinta,don haka kuji tsoron Allah kuje ku xauna da juna lafiya don Allah,kuyi mun wannan alfarmar bama kamar ke Roohe nafijin ki kece mai taurin kai,kece wadda kowa yasanki da fitina to inhar kikaje kika ringa fitina dashi wallahi zan manta dana haifeki,inhar kina so albarkata tabiki har lahira to kije kiyi biyayya kiyi hakuri a dakin ki,inaso ace sai mutuwa zata rabaki da gidan auren ki,nasan cewa Auren nan ku duka babu maiso amma ku sani bamu da ikon bijirewa umurnin Hajja,yi kata biyayya shine xai saka mushiga aljanna,haka nan kuma in kukai mana zaku ga haske a rayuwar ku,ahankali Allah xai kimsa maku soyayyar juna wadda baku tab'a tsammata ba,sauran yan uwanku duk nai masu fad'a kuma nasan zasuji maganata kamar yadda kuma nasan ba zaki bijirewa maganata ba,don haka ina muku addua Allah yai muku albarka,yasa aalkairi a zaman auren ku ya kuma sanya muku son junan,ya baku zuri'a mai albarka da zasuyi muku biyayya kuma,zan tsaya haka ina fatan kunji kuma zakuyi aiki da abunda nace" "In sha Allah Abba ba zaka a samu wata matsala daga gareni ba" Cewar Ramadan cikin biyayya da ladabi, kaina k'asa zuciyata bugawa kawai take,kalaman Abba sun daure ni matuk'a jikina yai nauyi haka ma bakina, saida naji ya ce "kefa Roohe" Kwalla ta silalo mun ban dago kaina ba nace, "nima haka Abba" "Ma sha Allah,ubangiji yai muku albarka bari na barku ku zanta" Ya tashi ya shige cikin bed room d'insa ya barmu nan xaune kamar wasu kurame kuma makafi,ba wanda ya iya dagowa ya kalli d'an uwan sa,kowa da kalar tunanin da yake yi a cikin ransa,munfi minty goma haka zaune ba mai uhm bare uhm uhm,kafin naji tashin sa da muryar sa yana ce mun, "sai da safe" D'ago kaina nayi ina kallon sa da mamaki,bai dube ni ba ya sa kai yai ficewar sa binsa nai da kallo har ya fice, jinjina kai nayi ina sake jinjina tsabar d'agawar sa da girman kansa,shiba wani shege ba sai fad'in rai,naja tsaki nima na tashi nai tafiyata dakin mu. Abba Nura ne zaune da iyalin sa duka da yaran da matar tashi mami, Rafeeq,Sha'awa da tazo daga gidan auren ta sai Rukee, saida ya gama masu nasiha sosai akan had'in auren da akai yajawo hankalin su da nuna masu muhimmancin yin hakan, da kuma biyayya da iyaye akan abunda baka so. "Wai Abban su kun sani sarai Auren dole haramun ne amma kuka bada goyon bayan yima yaran nan shi..........Safiya kimun shiru!" Ya fad'a cikin yar tsawa,ba shiri taja bakin ta ta tsuke gudun rikici gaban yaran su, ya cigaba da ce mata "idan har ba zaki taimaka mun wajen ganin sunje sun zauna lafiya a gidajen su ba,to Safiya karki kuskure ki bada goyon bayan hana su zaman lafiya da juna,wannan shine kashedi na karshe tsakanina dake,in kuma wani tsaitsayi yasa kikai abunda har yasa wani cikin su ya kashe auren sa wallahi tallahi kema naki zai mutu" Su duka yaran saida suka razana, wajen dagowa suna kallon shi, Rafeeq ya ce "Please Abba" "Ba batun Please bane Rafeeq, na fad'a agaban kune yadda inhar hakan tafaru ba zakuyi blaming dina ba" Sha'awa ta ce "kayi hakuri Abba, Mami ba zata aikata haka ba in sha Allahu" "Allah yasa," Ya fad'a,sannan ya cigaba da cewa "magana ta gaba akan Yayah Habibu ne da matar sa, inaso kusan wani abu guda da baku sani ba akan su, Yaya da matar sa sunyi mana abunda bamu iya biyan su har abada,dani da Abban ku Taheer labarin mai tsayine amma abunda zan iya sanar daku shine Yaya Habibu da matar su da bazar su muka kawo wannan lokacin,sune komin mu tun daga sadda maka taso har kawo yanxu,sunyi hidima damu da jikinsu da aljihun su tun duniya na kwance, shine karatun mu na boko da islamiya har muka zama abunda muka zama,wuyar da Yaya yasha akan mu shida matar sa baki ma bazai iya misaltawa ba,har takai zasu iya rasa abun da zasuci inhar mu zamu samu kuma zamuje makaranta, wannan dalilin yasa Hajja bata had'a kowa dasu ba, duk abun da zai taso bata yadda wani ya raina su ba to balle mu, don haka ina sanar daku da babbar murya inhar kuna so mu shirya daku mu daidaita to ku kyautata masu,yadda kuke zumunci da y'ay'an Taheer suma su ramadan da su Rahma kuyi dasu,hakan shi zai samun cewar eh lallai kun yadda nidin mahaifin kune,sab'anin hakan kuma zai nuna mun cewar ban isa daku ba alamun ban haife ku ba,wallahi rashin bin yaya da matar sa kamar kun tsake kan ku daga cikin zuri'ata ne,don haka yadda zakuyi mun biyayya ku kyautata mun suma haka zakuyi masu,fatan kun jini kuma kun fahimce ni" "In sha Allahu Abba zaka samemu masu yi maka biyayya akan hakan,Allah ya bamu ikon binsu bisa dai-dai" Cewar Rafeeq, Abban ya ce "madallah,Allah yai muku albarka kuna iya tashi na sallame ku" Mom muhseen&Asaad🥰 _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....6 *WAI WAYE...ADON TAFIYA* Hajja kakata ce itace ta haifi ubannin mu maza, su hudu rak gareta Allah ya bata su uku maza sai mace daya mai suna goggo Habi,kuma itace autar su tana aure a lagos tana jimawa ma bata zoba yaranta uku itama, babbar sa'ar muce mufida sai sauran maza kamis da jamil. Abba Habibu shine babba cikin su Babanmu,shida matarsa MAMA suna da yara hud'u Anty Rahma sai Yah RAMADAN sai Yah Najib sai Najiba auta, Abba Nura da matarsa umma Safiya suna da yara uku rak, Yah RAFEEQ Anty sha'awa sai Rukee Abba Tahir shine mahaifina da nakeji dashi duk duniyata,ina alfahari da Abba na ubana da babu kamar sa a wajena,soyayyarsa mai girma ce agareni,shida mahaiifiya ta mai suna Maijidda sun haifi yara hud'u Yah Fahad,Anty Rafia saini LAYLA da naci sunan mahaifiyar Abba watau Tsohuwa mai ran k'arfe HAJJA ake mun lak'abi da ROOHEE,sai auta ummi mai sunan mahaifiyar ummanmu. Tunda muka taso a cikin gidanmu mun ga ummanmu da Mami basa shiri da Mama mahaifiyar su Yah Ramadan,wata irin k'iyayya ce suke mata wanda ko ganinta basa so,kuma suka katange mu daga yin huld'a da ita da y'ay'anta,to kun sani a duk sadda uwa bata son wancen to lashakka y'ay'anta zasu bi bayanta ne ba tare da sanin miye dalili ba,su dai tunda bata son wancen to suma basa son sa, A haka muka taso muna nuna halin ko in kula da Mama,bama yi mata rashin kunya amma kwata-kwata babu ruwanmu da shiga sabgarta kai har shi Abba Habibun in ba hanya ce ta matse mana ba bamu zuwa takanas muce munzo gaidashi, hakan kuma bai dame mu ba mudai tunda basa shiri da uwayen mu muma hakance, koda akai bikin Anti Rahma babu wanda yai anko cikin mu, kuma bamu shiga cikin sabgar bikin ba kamar ma ba biki ake gidanmu ba, duk mun san ba dai-dai muke ba amma kuma bazamu iya gyarawa ba gudun fad'an uwayen mu mata, kuma duk Hajja ce tajawo wannan k'iyayyar a cewar Mami saboda tana nuna tsananin banbanci tsakanin Mama da su,duk abunda ya taso to Mama ce kan gaba kafin su, kuma tafi janta ajikinta fiye dasu hasalima da ita kawai take fira bandasu Mami,wannan abun ya kara taka rawa wajen sake jefa kiyayyar Mama da Ahalinta a zukatan su. Wannan kenan........ Yadda muke kusanci da mami da y'ay'anta abun ba'a cewa komi,don Rukee tamkar Ummanmu ta haifeta haka muke tare,ko ina zamu tare ko a school sit d'inmu guda haka ma islamiyya,Anti shaawa ma ita da Anti Rafeea kamar tip da taya suma haka suke, haka zalika Yah Rafeeq da Yah Fahad suma sosai suke abota da juna,komi ya shafi d'aya to ya shafi d'aya, ummi ce kawai bata da partner, hakan ba kadan yai ma uwayen mu dad'i ba yadda muka had'e kanmu muka ware su YAH RAMADAN,. Zan fara daga sadda muka shiga Ss3 don daga nan ne zakufi fahimtar komi. Tunda mukai wayau da sanin kanmu yar tsama ce ke tsakanina da Yah rafeeq,tun ban da wayau inhar yana waje to ban da sak'at haka zai tisani gaba da tsokana yana jana fad'a, duk da tarin shekarun daya bani hakan bai hana shi tsokana ta ba,don shida yah fahad xasu bamu shekara bakwai-bakwai nida Rukee,amma in kaga yadda yake mun zaka d'auka wata tsarar sa ce, ba irin tsakanin da Abba Nura bai mana ba amma ta inda ta shiga ta nan take fita, kowa yasan a da niba mai fad'a bace balle wata hayaniya, hasalima zaka iya jana inyi kamar ban gani ba,zaka jima kana mun abu ko kallon ka banayi,amma silar Yah Rafeeq na zama mafad'aciyar karfi da yaji,sannan na zama soda uwar magana,har ta kai ga indai babu ni a gidan kowa zai gane,a hankali abun ya soma. Kasancewar duk cikin yan matan gidanmu gaskiya babu wacce ta kawo ni a komi na dirin jikin y'a mace da kyau,don komi na Hajja na kwaso kuma Hajja farace sosai sol da ita kuma ko yanzu ka kalli jikinta kasan sadda tana da kuruciyarta tayi kyau na ban mamaki,to nima haka don shiyasa ma dokar saka Hijab in za'a fita ta zama wajibi garemu duka, duk da wani sa'ilin a sace nake saka gyale ajaka in mun fita mu saka nida Rukee,ban tab'a jin wanda ya kushe ni ba sai akan Yah rafeeq, komi na saka saiya kushe bama akan sitira ba har k'ok'arin da nake dashi a makaranta inhar na anso abun yabo shine nafarko da zai kushe yace satar ansa ce, abun yana

Chapter 3 of 16