ya dauke d'af,kuma lokaci yaja sosai na had'iye wani miyau na ce, cikin sanyin "it's almost eleven thirty yanzu,.........zaki iya jan motar?"
Saurin kallon sa nayi da mamaki,ba dan ban iya na kawai dai miyasa zaice mun haka?kuma Abba ya hanani tuki tunda na tab'a buge wani mai adaidaita, "Aa bazan iya ba"
Na sake juyar da kaina kurin,Inajin mugun son barin wajen bama wajen ba motar nake so inga bana ciki,......."ki gyara kujerar ki kwanta don ban san ranar barin mu nan ba"
A zabure na jiyo ina kallon sa, ko kadan na tsani mu had'a ido idanuwan sa wasu irin idanuwa ne, sai na dauke idona daga cikin nashi kamar zan sake kecewa da kukan na ce, "don Allah mu tafi gida,inma horani zakai da haka don Allah kayakuri nidai mutafi"
Shiru yai kuma inajin kallona yake ta faman yi,kafin ya ce "to ai bazan iya tuk'in bane kizo kija..........idona ya tara kwalla na ce "Abba ya hanani driving"
Ya rausayar dakai yana lullumshe idonsa da sukai jaa,kamar bai da lafiyar dagaske kuma sannan ya ce cikin gajiyawa da magana, "ai yau ne kawai,kuma bazan fad'a masa ba.........Don Allah *YAH RAMDAN*"
Wani irin kallo yajiyo yana mun,mai kama da na mamaki da al'ajabi,nai saurin maida kaina k'asa ina jin nadamar fad'in sunan sa,nasan shi yake ma mamakin jinake nai mugun takura da wannan zaman,haushi ya isan kamar nayi fiffike na ganni gida,nasan bacin daukewar network da yanzu an kirani yakai sau ba iyaka.........."mika ce?"
Naji ya katseni da fad'ar haka,har sannan kallona yake ban dube sa ba na ce "ba komi"
"Ohh na dauka magana kikai sai mu tafi.........cewa nai don Allah ka tada motar"
"In Kika maimaita abunda kika ce zan tada mu tafi"
Ya juyar da fuskar sa can side d'in,na rasa yadda zanyi na goge guntun kwallata ina wasa da zoben dake sanye ga ya tsana, kirjina na kai kawo na ce,
"Don Allah YAH RAMDAN"
Jiyo da fuskar sa yayi yana zuba mun mayun idanun sa,na juyar da kaina wurin taga kurin don na tsani mu hada ido,ni na ma rasa abunda ke damun sa a yau d'in nan............"mu tafi?"
Na d'aga kai na ban dubesa ba,wani numfashi ya sauke kamar wanda yasha kuka ya k'oshi,sannan ya tada motar muka cigaba da tafiyar shiru-shiru har muka k'araso gida.
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....17
Gaba d'aya main falon gidan kowa na nan harda yan biki anyi jigun jigun,Abbanmu da Abba Habibu da Abba Nura duk tsaye Ummanmu kau sai share hawaye take,Mami ce ke ta lallashi da ban baki.
Rukee da Mufeey suma sai kuka suke,cak muka tsaya nida shi bakin k'ofar entrance d'in.........."Laaaa Abba gasu nan wallahi"
Cewar mufeey da muka fara had'a ido da ita, sai kowa ya mimmik'e tsaye ana ta kace na ce na tambayar mu,mun ma kasa ansawa kowa saida aka natsu Abba Habibu ya ce "Ramadan lafiya kau?ina kuka shiga har karfe shabiyu?kun san irin tashin hankalin da kuka samu ciki?"
Kallon juna mukai nidai na wuce wajen Ummanmu na kwanta cinyarta, kafin naji ya lafta k'arya karon farko da naji yai karya tunda nake agidan nan........"Abba wallahi motar ce ta tsaya mana a titi,gashi ba kowa wajen daker na isa na samo wasu suka tura mun ita inda ake gyara,kuma muna ta gwada kiran ku network ya d'auke kuyi hakuri mun saku cikin tashin hankali"
Yadda nake kallon sa galala haka naga Abban yana masa,sai ya sadda kai kurin bai sake magana ba,anan dai aka wawwatse shima ya mik'e yai hanyar bangaren su,har ya kulle ina kallon sa.
********
Washe gari Friday da yamma ranar ne xa'ai Arabian night,ana ta shige da fice ni dai ina d'aki abuna mun gama video call da Yah Rafeeq Rukee ta shigo ta ce, "ni kam tun jiya nake so muyi magana banga fuska ba,gaya mun gaskiya miya faru jiyan nan da daddare?"
Tsaki naja kurin na diro na shiga toilet na fito,sannan ne nake cewa "wallahi duk duniya ban ga d'an rainin hankali irin wancen guy d'in ba,ke ni ban ma san yana magana ba sai jiya ashe iskan cine daman sai yai zuru kamar wani kurma hmmmm kigan shi kawai wannan mutumin..........Dariya Rukee tayi ta ce "to ai ni har yanzu banji abunda ya faru ba sai bayani kike mun"
Na zauna bakin gado ina bata lbarin abunda ya faru, ta ce "uhmmm anya kuwa?"
Na kalleta cikin rashin Fahimta, "ban gane ba?"
"Aa mubar maganar yanzu ba zaki gane ba ai"
Tatashi tana cewa bari naje wajen Mami indawo,ta fice ta barni da binta da kallo ina nanata maganarta har nagaji na mik'e na fita nima.
Karfe bakwai na dare aka Fara tafiya wannan karon ban yadda an barni baya ba,xan iya cewa nice farkon shiryawa abaya ce bak'a sabuwa dal zata kai 45k haka muka siyo su rannan kuma duk Abba ne da wannan aikin,duk cikin namu mu uku tawa tafi ta kowa kyau fad'ar yadda ta hau jikina ma bata bakine,na sagala gyalenta ga kai na jefa jelar gelen hagu da dama,na saka agogo fara ga hannuna yar siririya,sai yar bag d'ina itama fara takalmana ne kurin bakake cover ne masu stones ajiki sai daukar ido suke,nai hotuna na tura ma love nai saurin kashe wayar don zai iya tsai dani yace sai munyi video.
Duk mun gama shiri muka fito zuwa farfajiyar gida inda sauran abokan amarya da yan uwa suke anata dauka zuwa hall din partyn,abokan anguna ne suketa turo da motoci anata dauka,da yake bikin biyune saiya tara al'ummar sosai abokan arziki da yan uwa duk anzo,
"Kuzo muje ga motar abokin Yah fuad can mijin Anty Rafeea saiya kaimu kafin wasu su shiga"
Muna isa muka ga sun fito shida wani........mamaki ya kama mu ganin shi da Yah Ramadan,kallon mu suke muma kallon su muke,kyakkyawan four eyes mukai nida shi,nai saurin juya wa ko gaida abokin mijin Antin banyi ba,zuciyata naji ta doka sosai naji Abokin ya ce "ina zuwa Rohee?kuzo muje mana"
Na waigo ina yak'e tare da in ina ina cewa "ai......ai da....sai dan anjima zamu tafi"
Koda nake maganar bai fasa kallona ba,saima ya jingina da kofar motar yana crossing legs dinsa ya cigaba da kallona, mufeey ke gefensa tana magana amma ba ita yake kallo ba, ya ce "to jiran me kuke yi ne Rukayya?"
Rukee na murmushi ta ce, "aa ba komi ban sani ba ko ita akwai abunda zatai ciki,mudai mun gama komi"
Na dalla mata harara murmushi yayi yana cewa, "RAMADAN muje ko sai mu kaisu"
Ya tilla masa key d'in motar,Rukeey da mufeey suka fara kokarin shiga,dole nima nabi su na shiga suka sani tsakiya duk haushi ya isan, wallahi wallahi duk abunda zai had'ani dashi bana son shi,kwata kwata ni ko a hanya ma bana so ina ganin sa,balle daga jiya zuwa yau wani irin mutum ya zama,bazan ma iya misalta yadda yake abubuwan sa ba,babu ma mai fahimtar ga abunda ke faruwa inba ni ba, to miyasa??? Na tambayi kaina wanda vanda ansar hakan.
Duk jallabiyoyi ne jikin su ta abokin angon ash ce tai masa kyau,shi kuma tashi fara ce sol sabuwa ma kau fadar yayi kyau b'ata bakine,don ya wuce kima sai miskilancin sa ya k'ara masa kyau,motar ta dauki sanyin Ac da wani irin k'amshi na turaruka da suka had'u,ga nasu najikinsu gana motar sai namu dayake da sanyin k'amshi,wani yana yi ya shigeni inama ace Yah Rafeeq na nan,wayyo Allah da anyi kauna iya kauna wannan bikin,amma kashh hakan bata samu ba,tunda muka fara tafiya firar su kawai suke da juna su dukan,amma ni nama kasa ciro kaina daga k'asa saboda gudun abu daya, shine mu had'a ido dashi duk da vanda tabbas din hakan,tunda tuki yake tun ina iya jure wa har kaina yasoma rik'ewa dole na d'agoshi,kamar wasa kau idona cikin nashi ta center mirror wani kallo na samu,ban san ma'anarsa ba yau fuskar sa da wata irin walwala da ban saba ganin sa da ita ba,sai annuri yake samun kaina nayi da danna masa harara na juyar da idona,jinai kurin motar tatafi dakarfi kuuuuu duk saida muka tsorata,daker ya taka burki yaya deeni ya ce "lafiyarka kuwa?kamar wani sabon driver haka abokina"
Kanshi ya shafa daga keya zuwa gaban kanshi yana cewa calmly "I'm sorry wallahi kaina ke ciwo shiyasa"
Rukee da mufeey sukai masa sannu,ya ansa yaya deeni ya anshi tukin shi kuma ya koma inda yaya deenin ya tashi,sannan muka cigaba da tafiya yaya Deenin ya ce "ko mu tsaya ka siya magani kar muje karar kid'a ya kara maka ciwo"
Lamo yai cikin kujerar yace, "No it's normal zai sauka ba sosai yake yi ba"
Tab'e baki nayi nasan karya ce kawai,tunda kwana biyu ya zama shugaban makaryata har muka iso wajen taron bai sake mgn ba,ni daman uffan bance ba,wow,wow wallahi wajen yasha decoration sosai da gani an kashe kud'i over,Rukee har ta soma tsuma saboda kid'an wajen da aka sanya,Mufeey ma haka ni dai rawa bata daban ba,kunya ma nakeji gaskiya.
Babban wajene aka kama sai aka fito daga farfajiyar wurin aka shirya shi sosai yai kyau,can ciki akwai wurin hutawa har toilet akwai da dakuna,da gani kasan an kashe kudad'e mukai parking inda ake aje motoci muka fito daman saida mukai sallar magariba muka fito,duhu yayi sosai sai hasken fitilu ta ko ina,akwai tables da aka sanya kowane table kujera hud'u uku ce a wajen,an dora flowers akai da plate's an zuna snack's a ciki da tsire da pies din kaza uku sai friut drink,sai plax d'in shayi kowane mutum da nashi a gabansa,abun yai tsari sosai mufeey da Rukee wajen kida suka tafi suna rawa,ni kuma na zauna kan kujera yaya Deeni suna tsaye gefena suna magana,amarya basu iso ba sai anjima kad'an.
Na rasa abunda ke mun dad'i duk d'okina na zuwa wajen ya fita kaina,wani iri nakeji duk damuwa ta isan na ciro wayata ina kunnawa na samu sak'on love yana cewa, _"uhm Rooh wannan kyan naki yana bani tsoro,ina wata duniya ke kina wata yadda Allah yyiki dole duk wani namiji yaji kin shiga ransa,please take care for ur self,koda wasa karki ba wani damata kinji Rooh d'ina,i love u so much"_
Murmushi ya kubce mun naji sanyi a raina na maida masa da nawa kalaman masu dadi da kwantar da hankali,baya online nasan daya d'ebe mun kewar da nake ciki,plax d'in black tea din da aka aje na dauka na zuna a cup na saka sugar cube d'aya don bana son zak'i sosai,na zo kaiwa bakina kenan naji ya b'aromin a jikina duk rabinsa ya zube, wani irin haushi ya kamani na aje cup d'in na mik'e.
"Ina zuwa Rohee?"
Cewar Yaya deeni,kamar zan kuka na ce cikin sanyin murya "tea ne ya zubar mun zanje na wanke ne"
"Kinsan toilets d'inne?"
Na girgiza kai kurin,suna tsaye tare dashi nidai banko kalle sa ba,Yaya Deenin ya soma mun kwatance sannan na ce "nagode"
Na tafi inajin ido yana bina kamar zan kifa.
"Baka da kuzari Abokina,anya ciwon kai kad'ai ne ke damunka?"
Cewar Deenin yana kallon RAMADAN din,lumshe kyawawan idanun sa yayi yana magana gently, "Aa bakomi kasan wani lokaci zakaji bakajin dadi"
"Hakane Allah ya kyauta,ka zauna anan bari nayi waya a mota please amaryata keta kirana tun dazu banso ta damu ko ta dauka ina tare da yan mata" murmushi yai masa kurin sannan ya juya ya koma inda sukai parking.
Daker na gano toilet d'in na shiga na kunna famfo na wanke inda ya b'ata ni a rigata,inata tsaki ji nake ma kamar na koma gida kwata-kwata babu wani annashuwa a raina,na gama wanke war na fito zan koma can kawai naji na bugi mutum,wata irin k'ara na fasa yai saurin rufe mun bakina, zuciyata kau kamar zata fito waje don tashin hankali,don wajen lungu yake kuma ba kowa,dole nake tsorata yanzu dana gane waye sai na sake shiga tashin hankali,nai baya ina ture hannun sa daga bakina na aro jarumtata duk da yadda gabana ke fad'uwa, muryata na rawa na ce "miye haka?akan me zaka biyoni har nan,kasan hukuncin ba mutum tsoro a addini?"
Dafa bangon dana ke jingine yayi da hannunsa,yana tsura mun idanun sa yake cewa "Aa ban sani ba sai kin gaya mun"
Na juyar da kaina gefe inason nagudu amma ya tare hanyar, "zunubi ne babba"
"Ita kuma Harara miye hukuncin mai yinta?"
Na jiyo da fuskata muna fuskantar juna,idona cikin nashi ya tsare ni da su nagaza dauke kaina, jinai ya ce "bakiji ba?"
Nai saurin dauke kaina ina cewa, "oho ni bansan ba"
"Amma ai kinsan na mai ba mutum tsoro ko?"
Na masa shiru,ya sauke hannun sa daya tare hanyar aiko nai zuruf zan fece jinai kawai ya cafke hannuna,cak na tsaya ina runtse idona dawo dani baya yai ya tare duk hanyar da zan ruga yana tsaye gabana hannuwan sa cikin aljihun jallabiyar sa,nak'i kallon sa balle ma ingane yana yi..........."ki mai-maita?"
Saida na nanata maganar a raina kafin na jiyo ina kallonsa, na ce "ban fahimta ba"
Taku guda ya kara tsakaninmu ya tsaya yana cigaba da kallona,ni kuma na juyar da fuskata "Hararar da kikai mun na kusa accident"
Idanuna duka a warwaje girar sa d'aya ya d'age na b'ata rai, "ashe ma,to ni banma san da kai ba"
"Really?"
Naci daci naki bashi ansa,takunsa zuwa inda nake naji na jiyo da sauri ina ja baya, bai fasa bina ba nima ban fasa ja baya ba,saina na dan gane da k'ofar toilet d'in,hankalina ya tashi sosai dan danan idona ya raina fata zan kuka har ya tara ruwa "ba....bana son wannan a....abun"
"Mai maita Hararar da kikai?"
"Ni.....ni....ban hararek,hannunsa ya saka ya dafe kofar kusancinmu yakaru sosai,nimfashina nake ja ina hawaye,......."Don Al......don Allah ka matsa anan"
"Zaki Mai maita ko aa?"
Na fara shashshekar kuka,"please kayakuri"
Na fad'a cikin rawar murya cike da tashin hankali, "Aa bazan yi ba gaskiya,ai kince ke bakisan dani ba ai.......Aa na sani kayakuri"
"In Kika sake zanyi hakurin"
Ya Dora gudan hannun jikin k'ofar,ya sani tsakiya tsakanina da kirjinsa kamar tsayin biro ne,hawayena suka k'aru cikin rawar murya mai cike da tsiro,ina shashshekar na ce "kayakuri"
*"Aa LAYLA"*
Ya fad'a da wani irin sauti,silalewa k'asa nayi na saka kaina cikin guiwata ina rera kukan bilhakki da gaskiya, na rasa inda zan saka kaina bana son abunda yake mun ko kadan, dirkushin sa naji gabana muryar sa ba kamar sadda ya fara mun magana da farko ba, calmly ya ce "zaki kara Hararata koda wasa?"
"Don Allah YAH RAMDAN kayakuri"
Hannunsa yasa yana shafar gashin kanshi yasaki iska kad'an sannan ya ce can k'asa, "it's ohk,tashi"
"Kaje Zan taho.......Aa tare zamu fita"
Ya katseni da fadar hakan,na ciro kaina daga cikin guiwar ina mik'ewa tsaye don ma wajen tayils ne yasha guga babu datti da sai kayana sun b'aci, bud'e mun k'ofar yai na shiga na wanke fuskata, ya mik'o mun hanky sa na ansa ina tsane fuskar,na mik'a masa muka fito.
Wajen ya sake cika mak'il,ga duhum dare yayi muna ciki bamu sani ba,har amare sun hallara anguna anata gudanar da partyn yadda ya kamata,komi inka kalla very nice cikin tsari da wayewa,kasa tsaya wa wajen nayi na wuce can wani wuri na ke'b'e kaina,amma ina iya hango komi da yake faruwa,shi kuma ya wuce wajen motar yaya Deeni ya hau sama daga wajen but ya zauna.
Saida aka fara picture's sannan naje akai ta mana dasu,ina iya hangoshi daga wurin baida niyyar zuwa ayi picture's din dashi,to daman ni haka nake so muka sha hotuna kala-kala,sai daga karshe naga Mufeey ta ruga ta jawo shi yazo akai masu shida ita,tana ta wani shige masa ko kallo basu isan ba,akai masu da amaren inajin tana rokon karya tafi amma saida yabar wajen,duk wanda yazo saida ya koma da jikka mai dauke da sunan angowayen da amaren,masu kyau haka aka rarraba ma kowa.
Ba a tashi ba sai wurin karfe shad'aya sannan kowa yai haramar gida,yawanci duk abokan angon suka mammaida mutane gida,wasu kuma suka tafi da kansu.
Ina tare da Anty Rafeea naki binsu Rukee a motar Yaya Deeni,suna can suna jirana ni kuma nak'i tafiya, saiga Yah Deenin da kanshi ya iso wajen, "Roohee ke muke jira"
Na b'ata fuska ina kallon Anty Rafeea na ce, "zan taho dasu Anty nidai"
Murmushi yayi yana mun rad'a kar Anty taji, "ke kau waye yake shiga motar ango da amarya,ki kyale su kizo mutafi please"
Kallon mu Anty keyi cikin rashin fahimta ta ce, "Deeni yadai?ko kana ciki da yar qanwata?"
Dariya yayi "Aa haba kod'aya ki rufa asiri kar kija mun bore a gida "
Tayi dariya kurin,sannan tace mun "miye ne wai kike ta cin d'aci keda wa?"
Na kalli Yah Deeni sannan nace mata "bakomi"
Na bisa muka tafi,wannan karon shine kejan motar Yah Ramadan na gaba,motar shiru Rukee har da bacci Mufeey ce kawai keta chat d'inta,har muka iso gida bamai mgn,kamar jira nake motar ta tsaya nai saurin ficewa cikin gida,Mufeey ta tada Rukee suka wuce ciki suma.
"Aboki na da magana abakina fa"
Sai sannan Ramadan ya bud'e idonsa yana kallon sa na yan second sannan ya maida idonsa ya rude ya ce calmly, "talk"
Deeni na murmushi ya ce, "anya ba akwai wani abu tsakanin ka da yarinyar can ba,na kasa ganewa fa"
Wani d'an iskan kallo Ramadan yai masa kafin ya ce, "wake nan?"
Dariya Deeni yayi ya ce, "Aa karka mun halinka mana Abokina,wace yarinya fa inba Rohee ba"
Dogon tsaki yaja yana bud'e gaban motar ya fito,shima ya bud'e ya biyo sa ya ce "ya zaka wani fito muna mgn"
Ya dube sa sosai sannan cikin sassanyar muryar sa mai dad'in saurare, "kar ka sake mun wannan mgnr please"
"Miyasa?bacin ga gaskiya nan b'aro b'aro............DEENI!,"
Ya kirasa da d'an karfi sannan ya ce, "LAYLA qanwata ce,babu wani abu mai kama da abunda kake tunani tsakanina da ita, beside ma Rafeeq ne suke dating da ita,akan me zaka ringa wannan mgnr pls banaso"
"Sorry Abokina na daina"
"Zan wuce ciki sai da safe"
Deeni na murmushi sukai musabaha kowa ya kama gabansa.
Mom Muhseen&Asaad
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....18
Daga wannan ranar zan iya cewa van sake saka fuskar sa ga idona ba,har aka kammala biki lafiya dangi duk suka watse kowa ya koma gidansa, su Mufeey ne kawai basu kai ga tafiya ba,mu kuma muka koma sch saboda mun shiga sabon session.
Mufeey basu tafi ba sai bayan biki da sati uku,ji mukai kamar kar tatafi wata irin shak'uwa ta sake shiga tsakanin mu,balle yanzu bama fad'a sosai muyita shiriritar mu tare muje islamiyya tare duk wani abu da zai d'ebe mana kewa tare mukeyin sa, shiyasa har kuka mukai da zasu tafi ranar,Yah Ramadan ya kaisu tashar jirgin k'asa,da nayi niyyar rakasu inajin shine drivern na fasa,nace karatun test nake munyi bankwana suka tafi abun su.
Soyayyata da Yah rafeeq uhmm ba acew wa komi,yanzu ba abunda muke sai lissafin dawowar sa,don yace a Nigeria zaiyi house menship d'insa,shiyasa walwata ta k'aro ainun kullin cikin lissafi nake,har Rukee ta gaji dajin labarin ranar dawowar sa,irin tarbar da zan masa da irin abunda zan shirya masa da kaina,musamman na shiga class na snacks a online cikin sati guda na iya abubuwa guda bakwai,duk da na kashe kud'i sosai amma bukatata ta tabiya.
**********
Akwana a tashi baby wuya wajen ubangiji sai gashi mun shiga shekarar karshe a sch,wanda yai dai-dai da haihuwar Anty Rafeea don wata rata cib tayi ta haifo mana ummanmu, muna kiranta da Iklas anty Sha'awa dai cikin bai isa haihuwa ba,ansha suna sosai anyi bajinta kwarai da gaske wajen wannan suna,uban yarinyar ya zubar da naira sosai kowa yazo sai yatai da su a bakin sa saboda irin bajintar da akai.............still naji Mami na cewa wata qawarta "kinga irin abunda nai ma Sha'awa fata nan hajiya rabi,amma ita da ubanta suka watsa mun kasa ga ido,ki duba kiga yadda ake facaka da kaji da namomi,kiga abinci kala har goma akai dubi irin jikkunan da aka rarraba cike da snacks da kaji,don bakiga jibga jibgan ragunan dake can baya ba da aka yanka,haba wallahi sha'awa ta cucemu"
"Ai duk laifinki ne Safiya,halinki ne yaja miki yo in nice wallahi y'ata ce cikin wannan daular...........Mubar maganar nan dai kawai Hajiya Rabi,haka Allah ya k'addara".
Ban sani ba ko ganina yasa suka bar mgnr,oho nidai tashi nai na basu waje daga cikin falon,ina mamakin Ammi akan son dukiyarta duk irin kudin da Abba Nura yake kashe mata bata gani,ban wani maida abun babba na cigaba da hidimata ban kuma yi mgnr dakowa ba,aka gama suna kowa ya watse raguna uku tik'a tik'a aka yanka,munsha aikin soye washe gari.
Anyi sunan Anty da sati uku Yah Rafeeq yake sanar dani albishir din tahowar sa cikin satin,wayyo Allah na karka so kaga murna wajena a lokacin ne Hajja ta fara ankarewa da halin da aka ciki,Ana gobe dawowar sa ne ta kirani bangarenta in mata aiki,daman kuma mune masu mata gyaran komatsanta intatashi nidai Rukee,
Bayan na fara aikin inayi ina janta da tsokana muna wasa da dariya,har ta sako maganar da take son yi mun, "wai ni kam takwarata Kodai da yayanki za'ai abun nana ne?"
Dariya ta kamani na boye kaina cikin filo nak'i magana, ta ce "ja'ira ehy din ce ke wahalar fadi shine zaki mun irin abun y'an da,shakiyya ai ni naga alama ai ubangiji yasa ayi damu to"
Daga haka bata sake cewa komi ba,mukai ta aikin har na gama mata taita samun albarka,daga ranar kuma bata sake tashin maganar ba,ni a tunani na bata da wata matsala da alakarmu,tunda yan uwan junane kuma ba wani aibu tattare da hakan,karewa ma zumunci ne za'a kara karfafawa,
Ashe akwai k'ura baya bamu sani ba.
Ranar da Yah Rafeeq ya dawo tana daga cikin ranakun da bana mantawa, saboda na tsinci kaina cikin farin ciki marar misaltuwa,kowa saida ya gane ina cikin farin cikin dawowar sa,gidan kanshi kanshin girke-girke na yake tunda gari ya waye nake abu guda har bayan sallar magariba,don saukar Dare zasuyi ina gama komi na ruga nai wanka,Rukee ta tayani zab'en kaya sanyawa wasu sabbi ne dana d'inka musamman don dawowar sa kala hudu,na zab'i wani material mai dan karen taushi da sulb'i yai mugun kyau ainun,sannan telanmu ya zuba fasahar sa wajen tsara mun gown d'ita don yace gown tafi yimun kyau,banyi make-up ba yace mun yafi son yai tozali dani fuskana fresh,daman kuma nasha gyaran jiki kamar wata amarya,amma aboye nayi Anty Rafeea da Rukee kawai suka sani,fatana tai wani irin lukui sai daukar ido take har umma saida ta tanka mun rannan, take cewa "Rohee kin fara shafa whitening cream ne?"
Nace"Aa Umma wallahi bana shafa shi,kila zafin nan ne kin san cikin zafi haka skin d'ina yake yi"
Sai ta yadda kuma,amma ni nasan karya nake kayan gyaran Anty Rafeea naita amfani dasu,bani kadai ba duk yan gida jiran isowar sa ake,karfe takwas jirgin zai sauka na gama shirina sai kamshi ke tashi kamar wadda aka daura ma aure,no kadai nasan yadda nakejin zuciyata akan Yah Rafeeq,ji nake in ban auresa ba zan iya rasa raina.
Abbanmu ne ya ce, Yah Ramadan zai je dauko shi,a ranar banji inajin haushin sa ba kuma bance bazan je ba, saboda farin cikin da nake ciki ban damu ba nace ma Abbanmu, "Abba to don Allah kace yaje dani"
Kanshi sadde lokacin a falon Abbanmu,Abban ya ce "ai gaki gashi nan saiki rok'esa"
Cikin shagwab'a nake ce masa, "Kaji YAH RAMDAN, kaje dani don Allah"
D'an ciro kanshi yayi ya mun kallo daya sannan yace, "ohk"
Nadaka tsalle na ruga don dauko gyalena,sadda na fito har yaje wajen mota na bud'e gaban na zauna na rufe ya sanya Ac saboda zafi, ya na yinsa kamar wanda yake rashin lafiya,tukin ma kamar baya so bance masa komi ba nidai sai faduwar gaba danaji inaji ban sani ba ko haduwar face to face zamuyi da Yah Rafeeq ce, inata zuba masa kalamai a waya yanzu kau ai nasan karya nake in kalli donsa in masa su, har muka iso nida shi kamar kurame karfe bakwai da rabi muka iso dole mujira na minty talatin.
Har nakai wajen da aka tanada don jiran baki banji Alamar ya biyoni ba, koda na juya na waiga yana can cikin mota abun sa,dage kafada nayi na samu waje nai zamana ina duba time lokaci zuwa lokaci,banzo da wata shaida da zata sa ya iya ganoni cikin sauki ba,don haka idona akan hanya yake har sadda lokacin ya cika,munajin dirar jirgin dan danan naji zuciyata ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 16