Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
soma bugawa nai nadamar tahowa ni kadai inama Ruky ta biyoni kila da nasamu courage,ahankali mutane suka fara bayyana kowa yana zuwa don tarbo wanda yazo domin sa,zuciyata nata bugawa inata zuba ido amma banga mai kama dashi ba,har na sare da tsayuwa zan koma na zauna kawai naji anyi mun d'ass da yatsa a fuskana, a firgice na jiyo don na tsorata...........caraf mukai kyakkyawan four eyes dashi,mugun daskarewa nayi a inda nake saboda kwata-kwata ya rik'ide mun ya canza muguwar canza wa, wani irin had'ad'd'an murmushi ne yake saki mai dan karen kyau a fuskar sa, yayin da kamshin sa ya cika mun cikina tab tsabar dad'insa, kafin na dawo hayyacina naji dadda'ar muryar nan tashi ta ratsa kunnena yana fad'ar, "Easy mana Rooh,karki cinye ni tun anan bamuje gida ba" Muguwar kunya ta ratsani na boye fuskata cikin tafin hannuna,Ina murmushin farin ciki da annashuwa wani irin kaunar sa na sake samun waje a zuciyata, cikin shagwaba na ce masa "nifa bangane ka bane,halan ma an canza mun yayana" Yar dariya yayi mai kyayatarwa,ya dan matso kusadani yana kallon fuskata kamar me rad'a ya ce "Nima Love d'ina kamar an canza mun ita,u look so cute and more beautiful" Wani iri naji sosai na sadda kaina kasa murmushi sosai, na kasa cewa komi ganin duk kunya ta isheni yasa ya ce, "ke da wa kuka zo?" Na nuna masa hanya Ina cewa, "muje ka gani da idonka ma na" Yana jaye da trolling dinsa ni kuma na daukar masa bag d'in muna tafiya zuwa parking space din motoci,sai tsokana ta yake daman ba kuma gwanine wajen tsokanar mutane,munzo wajen motar kenan suka had'a ido da shi,kallon juna na seconds sukai ma junan su ba wanda yace ci kanka, Yah Rafeeq ya zaga ya bud'e But da kansa ya saka akwatin jikkar kuma ya saka ta a gaban motar,ya bud'e mun baya na shiga sannan shima ya shigo yana rufewa, fira ya fara mun Ina biye masa muna dariya, jira muke muji motar tatashi amma shiru har saida na ce, "lafiya kuwa?" Kafadar sa ya dage sama alamun bai sani ba,kuma ga Yah Ramadan din nan zaune wayarsa yake dannawa, na hadiye miyau na daure na ce "Yah lafiya bamu tafi ba?" Kusan minty uku baice komi ba,saida ya mulmule sannan ya ce "waye drivern ku?" Sai na gane cewar zaman mu duka a bayan ya jawo rashin tafiyar,duk da raina ya sosu sai na danne na ce , "ayya to bari na dawo gaban.......rik'e mun hannu Yah Rafeeq yai dan danan har ransa ya baci gashinan a fuskar sa ma, "ba inda zaki,in bazai ja ba ya fita yatai" Bazan so ai wanan rigimar ba daga isowar sa KO ruwa bai sha ba,na ce "miye aciki Yah Rafeeq just 40minutes ne fa sun kaimu gida kayakuri kaji" Dole ya kyaleni na koma bayan,amma sai tsaki yake da karfi nidai kagare nake mu isa gida saboda a rabu lafiya, na rasa wace irin rashin jituwa ce tsakanin su,duk nima ba wani shiri muke ba amma takun sakar yafi karfi tsakanin su,duk yadda naso jansa da fira muje gida kiyawa yayi,dole naja bakina nai shiru abun yai mun ciwo sosai,kamar sabbin kurame haka muka iso gida. A fusace ya buga kofar motar ya fice,ko waigena baiba abun ya sake bata mun rai watau kaina zai huce aiko wallahi zai gane kurensa,ko jikkar tasa van dauka ba nabi ta hanyar bangaren Abba Habibu na wuce dakinmu, ban samu Rukee ba nasan tana can falo ana jiran shigowar mu,gyalena ya yakice na jefar na kwanta rubda ciki bisa gadon kurin, raina inyai dubu ya baci toni miye nawa aciki?don kawai na bi hanyar da zata hana rigima da tashin hankali tsakanin su? Ban san iya lokacin dana dauka a haka ba,sai ga Rukee ta shigo "Aaha,ke kuma nan kika yo ana ta cigiyarki?lafiyarki kalau kuwa?" Sai kurin na sakar mata kuka saboda iyakar k'ulewa na k'ule da abunda yai min, mamaki ya kama Rukee tai saurin zama gefena tana cewa, "kece ke kuka yah Roohe?abun yai zafi haka?" Ni kaina nayi mamaki yadda kuka ke min wahala amma yanzu abu kadan kuka, "wallahi saiya biya wannan bacin ran,duk irin kokarin da nake akansa shine zai saka mun da haka.............daidai sadda mukaji shigowar mutum,dago kan da zanyi nagansa tsaye hannuwan sa cikin aljihun jeans dinsa, saurin kawar da Kai nayi Rukee kuka tatashi ta fita, kamar daman jiran fitar ta yake yai saurin isowa bakin gadon ya zauna saman bedside, nai saurin tashi zan matsa don a hangule nake, amma sai ya rik'eni gammm yak'i sakin hannun, sai na sanya kuka mai karya zuciyar duk wani lafiyayyan namiji, dan danan ya fara rawar jiki "Rooh sorry pls I'm very sorry,I don't mean to hurt u naji ba dadi ne yadda kika biye masa akan ra'ayinsa, amma banyi don bacin ranki ba,nayi laifi kimin afuwa wallahi kukan ki yana kassarani,zan iya kamuwa da rashin lafiya please Love pls pardon me" Shashshekar Kukana kurin nake lallashin da yake min yasa nafara sabkowa,ba abunda nake so idan Ina kuka sama da lallashi da tattausan lafaxi, haka yaita gaya min dad'ad'en kalamai har naji nad'an huce, na daina kukan sai jan majina nake, "ki yafe mun na sanya kin zubar da kwallarki akaina," Kaina na jinjina kurin bance komi ba, "muje ki zuba mun abunda kika hadamun,bazan iya cin komi ba in bakya gefena" Makale kafad'ana nayi ya sassauta muryasa sosai ya ce, "Ayya my love I'm feeling hungry" Harara na masa na dauke kaina,sai ya saki wani kafirin murmushi mai kid'imani, "naji komi zaki mun zan dauka nidai zaki tashi muje,bazan iya asarar wannan delicious d'in naki ba pls Rooh dina" Da wadannan kalaman ya siye mun zuciya,daman kuma ban iya dogon fushi dashi ba,soyayyarsa bata barina nayi hakan. Ana ganin mun fito tare aka saki baki don sunyi zaton tunda nayi fushi to fa bazan fito ba, dariya aka kama yi mana wai duk wanda yashiga fadanmu zaiji kunya, sai gashi inata murmushi yana mun fira yana zolayata sai santin duk abunda na zuba mishi yake, saida kowa ya watse yabar mu anan, fira mukai tayi ko ince kauna don kamar mu kad'aine a duniyar haka muka ringajin kanmu, naita narkewa kamar wata kankara,saida Allah ya jeho Abba Nura ya ce "firar ta isa duk kutashi kuje ku kwanta" Lokacin daya da rabi tama wuce sosai,badan rai ya soba saida ya biyoni zuwa hanyar dakin mu Abba ya ce, "kai! Ina zaka?" Sosa Kai yayi yana cewa, "raka ta zanyi Abba" Dak'uwa yai masa yana nuna masa hanyar dakin sa, "ban son sakarci kajiko" Dole ya kyaleni amma har yakusa kullewa yana waigo ni, ranar Ina bacci amma murmushi nake ina jinjina irin kauna da soyayyar dake cikin zukatan mu,Ina tunanin to in har Auren mu bai yuwu bafa?cikin sauri nake kauda wannan tunanin don lokaci guda zanji hankalina yai kololuwar tashi,daker nai addua na kwanta. Mom muhseen&Asaad _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....19 Washe gari dana tashi kamar wacce mijinta yai tafi tsayin lokaci ya dawo,haka na kasance nice shirya wannan gyara wannan haka nai tayi na hada masa lafiyayyan breakfast da kaina,wanda ko yai mamakin ganina a kitchen tunda ba sana'a ta bace,na gama naje nai wanka na d'an d'asa kwalliya kamar zanje biki,Rukee dai har ta daina mamakina ma saidai tayi murmushi kawai ta kauda kai,yanzu ma abunda tayi kenan na jiyo ina ce mata, "Na miki uziri baki san gard'in soyayya ba,dakin sani ba zaki ga laifin abunda nake ba amma muje zuwa akwai ranar da zaki zo kina neman shawarata akan kin afaka rijiyar kaunar wani..........dariya ce ta kwace mata ta ce "Allah ya kyauta mun,bana fatan shiga soyayya irin wannan, don cutuwar ta tafi dad'inta yawa,ni hasalima kin ganni nan bana son duk abunda zai hanani sukuni a zuciyata, bance miki bazan yi soyayya ba,tabbas zanyi watarana tunda dole muyi aure amma irin wannan da kike ma Yah Rafeeq uhhh aa gaskiya tayi yawa,ace baka iya ganin laifin mutum inyai maka?kuma baka iya dogon fushi dashi?sannan bakajin kunyar kowa indai akanshi ne?uhhh Aa ba irin wannan ba sai sa sai sa dai mastad'aa" Dariya ma na kama yi mata nace, "we shall see" Na gama kwalliyata na fita zuwa bangaren su Mami,amma saida na biya na gaida Abba na iske Hajja tazo wurin sa suna magana, duk kallona suke kamar wata sabuwar Halitta. Abban ya ce "Ina zuwa mamana?" Na sunkuyar dakai Ina murmushi "Ba ko Ina Abba,gaidaka nazo inyi kawai?" Murmushi yayi ya ce, "Aa gaya mun gaskiya dai?" Na soke kai Ina dariya,Hajja ta ce "zai wuce wajen Rafeeq zataje" Abban ya ce "wai haka?" Na d'aga kai alamar ehy,murmushi yayi sannan ya ce "to a rage rawar k'afar nan kinji ko?kuma a rage shigema juna" Na jinjina kai na kasa magana saboda naji kunya sosai, "jeki abunki,kice da Abbanku Nura Hajja na jiransa anan" Sadda na isa bangaren Mami na iske falo tana shirya dining na gaidata,Ina ansar kayan na soma shirya mata, na ce "Mami Abbanmu yace agaya ma Abba Hajja na jiransa" Ta amsa da cewar bari taje ta sanar dashi,tana tafiya nai wuff na wuce dakin sa,kwance yake yanata bacci na fizge bargon daya rufa aiko yai firgigi ya tashi, aiko na kama masa dariya yai k'urii yana kallona da idanun sa cike da Bacci,sai suka kara kasa kyau sosai naji wani abu ya tsarga mun,na hade hannuwa na alamun ban hakuri "afuwan Yah,ka koma ka cigaba da baccin ka bazan sake tashinka ba" "Ai wallahi karya kike yarinya, ni zaki tada kuma kice na noma nacigaba da baccin,bacin kinfi kowa sanin in natashi bana iya koma wa,bayani zaki.......ya diro daga bisa gadon yana niyyar biyo ni,aguje na yo hanyar waje Ina tsuwwa caraf ya cafke hanuna daidai budewar k'ofar, mukai ido hud'u da Yah Ramadan,kallon mu yake muna kallon sa kafin Yah Rafeeq yaja wani dogon tsaki yana yin kamar bai ganshi na,,ni kuma sai kokarin anshe hannuna nake yaki sakina, "waye yace ki tadani,don haka koki biyani baccina ko kuma bake ba fita dakin nan,anan zamu yini baci ba sha.............Kazo Abba yana kiranka" Abunda Ya fad'a kenan ya juya yai gaba,shi kuma kamar anyi mgn da dutsi bai ma nuna dashi ake mgr ba,magiya naita masa ina cewa "wallahi ba da niyya nayi ba,zuwa nai na ce maka kazo nayi maka breakfast mai dad'i sai muci tare" Kokarin had'e ni yake da jikinsa,nikuma inata ja baya gabana na fad'uwa,duk karfina saida yai nasarar sani cikin kirjinsa,wata nannauyar ajiyar zuciya muka sauke muduka,sai kuma mukai shiruuu,zukata nata biting sosai ahankali na zare jikina gabana na fad'uwa na fice daga dakin, Breakfast din saidai yazo ya dauka da kanshi,kasa sakewa nayi bare muyi tare,kunyar sa ta cika mun ciki shikau ko ajikinsa yakeji, ranar lectures din yamma garemu nida Rukee shine kuma ya kaimu ranar,karfe bakwai na dare muke tashi ya koma ya dauko mu,ya biya damu shopping muka siyo kayan zak'i sannan muka tsaya wani bakery muka siyo cake ice cream da sauran su,ya kashe mana kudi sosai muka dawo gida. Daga wannan rana shi ya zama yana kaimu sch inda baya komi, sannan yaje ya dawo damu hidima yake mun kamar dai anriga an bashi ni, bayajin komi abu duk tsadarsa ya siya mun,kayan kwalliya dana gayu baya gajiya da siya mun,haka kayan shafa masu masifar gyara fata don zan iya cewa shiya lalatani da bana iya amfani da wasu maya-mayai inba dove da Nevia ba,ko wane set dinsa yake siya mun banda su shampoo na wankin gashi turarukan jiki dana kaya,Dana gashi kai yah Rafeeq har turarukan Hq da sabulan tsarki siya mun yake,tun Ina nuna haushi dakunya har na daina,don fara House man ship dinsa abun yakaru,don duk wata yanajin alert na dubu dari biyu asibitin da yake aiki, baya komi dasu sai hidimata da tashi sai Rukee. Yaje gidajen su Anti Rafeea da Anti sha'awa ya kai musu abun arziki,kuma duk tare muke zuwa inka ganmu zaka dauka sabbin amare ne tsabar yadda jikinmu yake glowing yana wani fresh tsabar jin dad'i da kuma kud'i da ake kashe ma jikin,sannan sitira yinsu yake kamar me duk sati saiya je boutique donshi yana son kananun kaya, nima kuma zaisiyo mun duk abunda ya siya ma kanshi. Idan bamu zuwa ko Ina to tabbas muna lambu ko farfajiyar gida muna fira,ko wasanni volleyball ko basketball irin wannan lokutan muka fi haduwa da Yah Ramadan,kallo bamu isheshi ba nice ma nakan iya cemasa Ina wuni,zai ce lafiya kawai ya wuce. Yah Rafeeq ya ce, "ke banga kwakwar dakike ta gaida mutumin da bai damu dake ba,nifa gaskiya vana so ma inga ko kallonsa kinayi" "Arzikin Abbanmu yakeci kai ma kasan ai bai daman ba,akwai alkawarin da Abba yasani na dauka shiyasa,amma badan wai na huce daga jin haushin Saba" Ire iren wadannan maganganun muke yawan yi inmun ganshi,tun Ina gaidashin har na daina saboda hudubar Yah Rafeeq d'in,rayuwar gwanin dad'i yanzu nakan mance da wani b'acin rai ko damuwa,kuka kam tun ranar da Yah Rafeeq ya dawo ban sake yinsa ba,baya bari na nuna damuwata sosai. Akwai abunda yake daure mun kai,sau uku hakan na faruwa ban dai sanar da kowa ba,watarana munyo saloon nida Rukee to tarigani tahowa sabo kiran da Mami tai mata na gaggawa,sai nayo dare ban iso gida ba sai bayan sallar isha'i Yah Rafeeq na wajen aikin sa balle ya dauko ni,muna daf da isowa naga napep ya tsaya wata mata ta fito da dogon hijab jikinta da nik'abi a fuska,ta shiga gidanmu. Amma koda nashiga banga alamun wata bakuwa agidan ba,ba bangaren da ban shiga ba don ganin ko bakuwar ce, amma babu alamun ta har shabiyun dare Ina falo amma banga wata tafito ba,haka naje na kwanta ina kokwanto a raina. Na biyu kuma let evening ne gab magriba,mun rabu da Yah Rafeeq zai je masallaci na zagayo daga baya wajen lambu zan shigo ta kofar entrance d'inmu,na hangi again matar tana ta sauri kamar zata kifa ta shige cikin gida,aiko na ruga da gudu don inaso inga yau wacece ke shigo mana cikin b'adda kama haka,saidai duk shige da ficena na rasa ta sama ko k'asa, zuciyata ta soma tsorata anya ba aljannu keson budemun ido ba,na rasa dawa zan mgnr kar ace na samu tab'in hankali,haka dai nabar abun a raina badan ya daina bani tsoro ba, Na karshen wanda ya kid'imani,karfe d'ayan dare na fito zuwa main kitchen d'in babban falo insha ruwa,na manta ban shiga dashi ba ranar Ina cikin kitchen naji wani kauri haka ga hanci na,nai saurin juyawa naga wulgin mutum ya shige corridor na hanyar bangaren Mami,duk yadda zuciyata take bugawa da tsoro hakan bai hanani bin hanyar ba cikin tashin hankali,don jinake kozan yi miye saina ga wacece wannan? _*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_ _{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_ *ADABI WRITERS ASSOCIATION....* By Mom muhsen& Asaad. Wattpad name Humaira3461. 🅿️.....20 Jikina wani irin tsuma yake ainun,saboda dai Ina cikin tsoro matsanan ci saboda al'amarin yana matuk'ar bani tsoro da mamaki,jiki na rawa nabi hanyar da tabi duk da wannan warin yana bugar hancina yana sani jin jiri kamar juwa na neman kadani,kamar walkiya banga kowa ba saidai k'ofar shiga bangaren Mami abud'e zuciyata keta bugawa,na kasa shiga zuwa can naji duhu ya mamaye idona daga haka ban sake sanin Inda kaina yake ba, Sai farka wa nayi da sanyin asuba na ganni bisa gadonmu,mamaki da al'ajabin abun yai mugun kamani dan danan abubuwan da suka faru a daren jiyan suka soma dawo mun tiryan tiryan, nai saurin tashi zaune cikin wani irin firgici har saida Rukee tatashi tana tambayata lfy "Rohee?" Jikina kamar an zuba mun ruwa,saboda zufar data kwaranyo mun, na kasa bata ansa kaina ya kulle. tashi tayi taje ta d'ebo mun ruwa ta kawo mun, "kisha ruwa, ko mafarki kikayi na tsoro?" Kallon ta nai kamar yau na fara ganinta daker nasha ruwan,na jingina da allon gado ina kallon ko ina nad'akina,kafin na iya bud'e bakina nace mata, "Waya kawoni nan Rukee?, jiya da daddare na farka naji kishirwa,nafita insha ruwa........ Sai na kasa bata labarin abunda ya farun, nai shiru dai. "Sai miya faru? Tsoro aka baki ne?" Ajiyar zuciya naja mai karfi kafin ince mata,"Ehy, to nidai nasan dana fita ban dawo nan ba,yanzu kuma na farka na ganni anan" "Kodai mafarki kikai kin tashi kin fita,inba haka ba ya za'ai haka ta faru, to waya dawo dake nan d'in?" Idona cike da kwallar tashin hankali nace mata"wallahi ban sani ba,kuma ni cikin hankalina nake ba mafarki nayi ba" Cikin son ta kwantar mun da hankali tace"Ki natsu ba fa wani abu bane,irin haka na faruwa sosai koni nasha yin irin wanan mafarkin sai kaga kamar gaske,karki damu kanki kinji ko ki dauka mafarkin kikai, kuma Rohee kina wasa da adduar bacci tunda yah Rafeeq ya dawo, ba dole ki ringa munanan mafarkai ba. " Shiru kurin nayi ina jinta ban sake cewa komi ba,nidai nasan ba wani mafarki danai abunda ya faru zahirin gaskiya ne bakomi ba,abunda ke rikitani shine waye ya maidoni dakin? Wannan ya wuce. ******** Bayan kwana biyu nayi kokarin ganin abun bai dameni ba,duk da idan na zauna ni daya abun yana dawo mun tsoro matsananci ya cika zuciyata,hakan saiya haifar mun da zazzabi mai zafi shiyasa nai iyakar k'ok'arina wajen ganin na cire ma raina abun,na zama Busy a makaranta indai ina ni kad'ai to zaka sameni ina karatu ko research,a d'an tsukin na rage kara kaina sosai,duk na zama sukuku dani Yah Rafeeq Yafi kowa damuwa da hakan,sbd na kasa sake wa kamar yadda muke,ya gaji da min tsogumi har ya gaji,Ummanmu kanta ta damu matuk'a rannan ta zaunar dani take tambayata, "Rohee mike damunki?,kusan sati biyu duk kin rage walwala,abinci ma bakyaci sosai kin faye zaman daki sai a yini ba ajiyo muryarki ba,ni mahaifiyarki ce sanar dani kinji ko" Shiru nayi kwalla suka cika idona kafin nai aune sun silalo kan kuncina, cikin sanyin murya na ce, "Umma kwana biyu mafarkai nake marasa dad'i,abun yana damuna shiyasa.........daidai lokacin Mami ta shigo falon ta zauna,ganin ina kuka take tambayar mike faruwa, umman cikin jimami ta ce " wai mafarkai take na ban tsoro shiyasa duk kwana biyun nan gatanan sukuku" Mamin ta kalleni cikin rashin jin dad'i ta ce "Shiyasa Rafeeq ya dameni akan Rohee kamar bata lfy kwana biyu,kuma nima naga alamar rashin sakewa tattare da ita,Y'ata zonan inji" Na matsa jikinta na dora kaina bisa cinyarta, ta dafa kaina cikin kulawa take mun mgn, "kin rage Azhkar ko?na sani kin rage don haka ki cigaba karki daina,shi daman shaid'an ai inda ake wasa da ibada yake zuwa,ki ringa alwalla in zaki kwanta kinji" Kaina kurin na iya D'aga mata,sai suka cigaba da firar su ita da Umman,har bacci ya daukeni kan cinyar Mamin. ******* A hankali a hankali sai na fara da ya yewa daga yana yin dana ke ciki na rud'u da damuwa,na dawo kamar komi bai faru ba,ban sake ganin matar ba balle wani abu makamancin irin na ranar ya faru, muka cigaba da soyayyar mu da Yah Rafeeq,kamar ma yanzu ne muka farata saboda shauk'in juna, kuma har zuwa wannan lokacin alak'armu dasu Mama su Yah Ramdan bata canza daga yadda take ba,saima abunda yai gaba. Duk yadda iyayen mu maza basa jin dadin wannan wariyar da muke musu amma mun kasa gyarawa,saboda ganin cewar iyayen mu Mata basa son hakan muma muke tayasu k'in abun,mun fara project dinmu tun farkon semester mu ta shekarar karshe, nida Ruky duk Yah Rafeeq ne yake tai maka mana wajen yin sa,lokacin har ya gama horsemanship dinsa yana Hutu kafin ya koma kuma ya cigaba da aiki da asibitin,don kuwa ya samu upper bayan gama horsemanship din shida Yah Fahad lokaci guda suka samu aiki,hakan yai ma su Ummanmu dad'i ba kad'an ba,saboda dai komin su na y'ay'an su yake tafiya tare ba wata tangard'a. Yah Ramadan da Yaj Najib kau jiya iyau rayuwar tasu, an dai gama karatu amma aikin yi yai wahalar gaske,har gara-gara ma Yah Najib ya samu wata privet sch anan cikin Abuja yana koyarwa ana biyasan da d'an auki,sab'anin Yah Ramadan da aikin ma da yake zuwa wani satin ba a biyansa,yana iya kashe sati biyu ko sisi baida,sai in Abban mu ya bashi ko Abba Nura, zuciyar dai a mace ba wani katab'us sai bakin rai da huzunu kamar wani ya d'ora masa. Kwanci tashi asarar mai rai sai gamu an wayi gari mun kammala jami'a da dad'i ba dad'i dai an samu an kammala, zuwa lokacin duk wani nau'i na cikar budurwa maiji da kanta jikina ya gama kammala,wani irin jiki Allah yayi mun mai cikar halitta ga fata ta wani irin daukar ido take kamar ana sani cikin inji a wanke kullin,saboda kalar kulawar da nake bata da taimakon Yah Rafeeq,don kuwa duk rabin albashin sa akaina yake qarewa, zuwa sannan ba inda soyayyar mu bata zagaya ba cikin gidan nan da kuma sauran yan uwa na kusa,har friends dinmu sun san cewar nid'in mallakin yah Rafeeq ce,don wannan mgnr kamar fariha ce a sallar farilla abakina kowa ya sani,hakan yasa na haramtawa kowane saurayi kaina, har malaman mu ba irin naci da k'wak'war da basuyi akaina ba, amma Ansar daya ce nake basu cewar nidin matar aure ce akwai saka rana da sadakin wani akaina, dole suke shafa mun fatiha. Mun gama da makaranta yanzu result kawai akejira da kuma mgnr Bautar kasa,don haka zaman gida muke yanzu sai Kuma zuwa islamiyya, a Wannan zaman namu bama komi ya sake haddasa wasu abubuwan tsakanina da Yah Ramadan,lokacin Yah Rafeeq yaje wani course na sati biyu a Lagos. Anti sha,awa ce ta haihu bayan tsawon shekaru uku da auren su sai lokacin Allah ya nufa,don wancen cikin barin sa tayi yana wata hudu,munyi Murna sosai da sosai saboda dai mun san taso haihuwa kamar hauka,zuwa lokacin ikee din Anti Rafeea shekararta uku an kusa yi mata kane ko qanwa don cikine da ita sannan,murnar da mukai tayi nida Rukee bata wuce ta yawon da zamuyi tayi ba har ayi suna,don yanzu an hanamu wannan gantalin da muke yi sadda muna school, gashi Yah Rafeeq bai nan daman shine yake daure mana gindin yawon, to tunda ya tafi ba wani waje da muke zuwa inba islamiyya ba itama din sau uku a sati ne,anyi haihuwar kamar yau washe gari saiga Goggo Habi da Mufeey sun sauka, wayyo dad'i murna kan murna haka mukai tayi don mun shekara wajen uku rabon da mu hadu,kowa yasan muna cikin farin ciki saboda gidan saida ya dauka da hayaniya. Washe gari karfe tara muka shirya don tafiya gidan jegon,jiya raba dare mukai muna fira itama ta kammala karatun ta kamar mu zaman fara bautar kasa take agida,cikin yan mazan gidan ba wani available dazai kaimu, Yah Najib tun seven thirty yake fita Yah fahad yana sokoto acan yake aiki sai karshen wata yake zuwa gida,Yah Ramadan ne kurin baya fita da wuri sai ten,munje muka gaida Hajja sannan muka wuce don gaida Abbanmu shidai Abba Nura ya riga ya fita, Yana ta aiki akan computer da glasses a idonsa,yana ganin mu ya cire ya bamu hankalinsa,gaidashi duk mukayi ya ansa cikin fara,a da nuna jin dad'in ganin mu yana cewa "an samu hanyar yawo hankali ya kwanta ko Rukee?" Dariya duk mukai muna sake kai k'asa da kanmu, Na ce "Abba Gashi gidan ba wanda zai kaimu mai zai hana ka barni na ringa kaimu tunda yanzu nayi hankali Abba" Murmushi yayi ya ce "indai akwai namiji agida bazan sake gangancin barinki kija mota ba,in kikai aure can tsakaninku keda mijin" Na sunburi baki ina shagwab'e fuska,su mufeey na mun dariya shi kuma ya dauko wayarsa yana cewa, "Ramadan baya fita sa wuri bari na kirasa ki ruk'esa ya ringa sauke ku," Ni sai lokacin ma na tuna dashi don nafi karfin wata van sashi idona ba,tun Yah Rafeeq na nan har raina nama mance ya yake,muna nan zaune ya kirasa ko minty uku ba Acika ba sai gashi sanyi cikin wani sassauk'an yadi marar tsada,ba guga kuma ba suquizing ba kamshi kuma ba wari, kallon sa nai na jima ban sashi idona ba sai naga fuskar sa ta sake haske da shalk'i,sai matashin gemunsa daya had'e da gashin bakinsa sun sake wani irin baki da daukar ido,alamun su yana basu kulawa. Saboda tafiya dogon kallon da nai yasa

Chapter 12 of 16