An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAI DAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....1
Gaba ki d'aya falon ya d'auki wani irin shiru wanda ko Allura ta fad'i zaka iya jin sautin fad'uwarta, banda karar AC baka jin motsin komi saboda yadda maganar Hajja ta daki zukatan kowa a wajen,banda kai kawo babu abunda zukatan su keyi domin kuwa wannan magana tai matuk'ar shammatar su,wannan shine ake kira ga bikin zuwa babu zanin d'aurawa,sannan ana zaton wuta a mak'era sai gata a masak'a, kowa bakin sa yayi nauyi kamar an d'ora dala da gauron dutse, tsayin mintoci ba mai uhm balle uhm uhm.
sai da Hajja ta gama nazartar kowa a wajen sannan ta nisa cikin dakiya irin tata da kuma jaddada maganarta da cewa "wannan shine dalili na,da kuma k'wakk'warar hujjata ta hana Auren *ROOHEE DA RAFEEQ* ,don haka na juyar da Auren ga *RAMADAN*.............innalillahi wa inna ilahir raju'un shikenan ni kuma tawa ta sameni,Hajja kiyi wa girman Allah da manzon sa ki sauya maganar nan, wane irin had'ine wannan ba kan gado ina Roohee ina Wani Ramadan fisabilillahi Hajja?"
Umman mu take wannan maganar cikin kuka da nuna zallar bak'in cikin had'in da ake k'okarin yi da bai daidai da ra'ayinta ba,
Cikin fushi sosai Abba na ya ce, "maijidda!, idan na kuma jin bakin ki anan ranki in yai dubu saina bisu d'aya bayan d'aya na b'ata su, Hajja kike maida ma magana haka cikin k'araji?"
"Kyaleta Taheer,hukunci ne na riga na yanke sa kuma ko bayan raina ban lamunce maku canza wannan hukuncin ba,inhar ba d'ayan su ne ya mutu ba"
umma tashi tai a mutukar fusace tabar falon,wanda yai dai-dai da tashina nima aguje cikin fita hayyaci da firgicin abunda ke neman samu na rana d'aya,nai dakin mu nida Rukee.
Abba Habibu cikin son neman Sulhu yace, "Hajja had'in nan zai iya kawo rashin zaman lafiya agidan nan,sannan mu da muke tsaffi akansu ba ai mana auren dole ba balle su y'an zamani,aganina a kyale ROOHEE ta kawo wanda take so tunda ba gaggawa ake ba,........inji waye yace ba gaggawa nake ba?aini dama tuni na gaji da ganin su haka zube gabana,tunda kowa ya gama wannan la'anannen Bokon ba sai a aurar dasu ba hakanan"
Shiru yayi saboda bashi da ta cewa, amma kam da za'aji tashi da an hakura da wannan had'in tunda har yarinya bata so,
"Wallahi Hajja baki tab'a abunda ya jefani cikin k'unci da bakin ciki ba irin wannan, in bacin ganin girma da darajar Aure wallahi da bazan lamunci wannan............zanci mutuncin ki Safiya anan wajen, idan bakin ki ya sa ke ya furta wata mummunan kalma akan Hajja wallahi summa tallahi sai kin gane kuren ki,zoki bar nan wajen kafin na sassab'amiki"
"Ai dole ka tada jijiyar wuya mana,tunda an maida aure ga d'an d'an shafaffe da mai"
Ta juya tabar wajen cikin fusata da fushi,Hajja bakin ta sake haka ta raka ta da kallo harta b'ace, "Kiyi hakuri Hajja don Allah"
"Aa ko d'aya Habibu kaine da hakuri,ai kowa yasan da kai take wannan maganar, ai saboda inyi maganin iskancin su yasa nai wannan abun, gashi suna ji suna gani abunda suke buri yafi karfin su,kuma in sha Allahu sai sunzo suna jin kunyarku kaida ZEENAH (MAMA KENAN)...........Karar fad'uwar da sukaji ya katse mata cigaba da maganar, kowa yai firgigi yana duban inda karar take,
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un RAFEEQ!!!"
Abba Habibu Abba Taheer sukai kanshi saboda ya mik'e kenan jiri ya daukesa da mugun karfi ya yanke jiki ya fad'i a some,hankalin kowa ya tashi ainun har ita Hajja, wadda dan danan ta soma kuka wiwi ba wanda ya waiwayeta suka kin keme shi a guje akai mota dashi don zuwa asibiti, labarin hakan yaje ma Mami mahaifiyar sa, gyale a hannu ta fito cikin tashin hankali tabi bayansu ita da Anty sha'awa.
Ban san meke faruwa ba a falon saboda tunda na shigo dakin a cikin wani yana yi nake ciki, na fad'a kan gadon mu ina fashewa da wani irin kuka wanda bazan iya tuna tsawon lokacin danai kuka irin sa ba,kuka sosai nake wanda yake fitowa daga kasan zuciyata, duk mai saurare zai gane irin yadda nake jin zallar bakin ciki a cikin raina,don har numfashina yi yake kamar zai d'auke gaba d'aya,dan danan kaina ya d'auki wani irin zafi da ciwo kan kace me jikina shima ya dauka,
Wani irin zazzab'i ya rufeni wanda ya haddasa mun kerma har hakorana suna had'uwa,kamar an jeho ummi dakin ta iskeni cikin wannan yana yin, "kai!Yah Roohee,innalillahi kema d'in ba lafiya, na shiga uku Yah Roohee kina ma jina kuwa?na bani.........ta rud'e gaba d'aya saboda ganin yadda jikin nawa ya rikice bana majin abunda take fad'a sosai, a guje tatafi kiran umman mu.
Atakaice ranar daga ni har Yah Rafeeq a gadon asibiti muka kwana,har gara ma ni da sauk'i shi kam ai abun ba kanta har yanzu bai dawo daga suman da yai ba, likitoci sun tabbatar da cewar ya shiga shock mai girman gaske wanda ya jefa shi shiga wannan halin,ni kam damuwa da tashin hankalin da nake ciki ne da kukan danai suka hadda sa mun azababben ciwon kai da zazzab'i, kaini har zuciyata kanta ciwo take nama kasa yadda da maganar Hajja,gani nake kawai don ta tsani alak'armu yasa ta shirga k'arya da girmanta,don abun da hankali bazai d'auka bane kwata-kwata, na tabbatar Yah Rafeeq ya tashi daga halin da yake ciki bazai yadda da wannan abun ba,duk ta rasa lokacin da zata zo da wannan maganar sai sadda suka shirya yin aure,sun shiryama juna rayuwa mai dad'i rayuwa mai cike da farin ciki da kaunar juna,sun riga sun yadda cewar d'aya baxai iya wata rayuwa mai dad'i ba in babu d'aya, shine zata saka almakashi ta datse musu farin ciki,lallai tazo da abunda bazai yuwu ba,don kuwa ko za'a maida kanta gabas a yanka bata da wani miji in ba Yah Rafeeq ba,wai Ramadan waye kuma Ramadan?kazamin,wanda nera biyar ke masa wahala?wanda daga shi har uwayensa da bazar Abba suke rawa,wanda degree d'aya ma dak'er ya ida saboda dak'ik'anci,abokan kirki ma baya dasu tsabar yana da girman kai magana ma sai ya kwana ya wuni bai iya ma kowa?inaaa da sakel anyi sadaka da karuwa.............duk ina wannan tunanin ne a sadda nake kwance ana kara mun ruwa,Rukee da ummi suna gefena kowa fuska ba dad'i cikin alhini,idona biyu inajin duk firar da Umman mu da Mami suke duk akan Hukuncin Hajja,tsabar yadda zuciyata ke cunkushe kuma take a tunzure ko allurar Baccin da aka saka cikin drip din ma banjin zatai aiki,don idona kamas nakejin sa tsabar rad'ad'in dake cikin raina.
"Wallahi wannan karon zanyi fito na fito da kowa akan wannan Had'in,Haba Mami anyi mun adalci kenan ace a rasawa wanda Hajja xata had'a Aure da Roohee sai RAMADAN?..........Ummah kenan,nasha gaya maki Hajja bata kaunar mu ko kad'an,in bacin rashin k'auna miya kaita yin wannan abun?yara sun shirya kansu ana daf da aure ki bijiro da wannan magana,kuma in bacin zaalinci miyasa tun da suka fara alk'a tagane abunda ke tsakani bata ce komi ba sai da suka shirya aure.....,.wallahi Hajja muguwa ce zeena kad'ai take kauna zeena kadai ce ta gari mai mutunci a idonta"
Mami ta k'arashe tana hawayen bakin ciki, umman mu tace "ki bar zubar da hawayenki Mami,inhar bata karyata maganar nan ba,to wallahi ni kuma Roohee ba zata Auri Ramadan ba,watau duk tattali da kulawa da tanadin da nai akan Roohee shikenan ita a Ramadan zata k'are,wannan kucakin k'azami dashi?Allah ya sawak'e wallahi sai dai idan Abban ya sallameni,"
Cikin kuka da bak'in ciki Mami ke cewa,
"Tashin hankalina yadda Rafeeq zai dauki lamarin nan idan ya tashi,wallahi na k'ara tsanar Xeena sosai a raina saboda duk don ita Hajja tai wanan abun,bazan iya yafe musu ba inhar wani mummunan abu ya samu D'ana wallahi har kotun k'oli zan iya kaisu..........Mami ba abunda zai samu Yah Rafeeq,ki daina cewa wani abu zai samai pls,idan haka taa faru mutuwa zan wallahi bazan iya baaaaa"
Ban San bakina ya bud'e ba ina fad'ar wannan maganar, saboda jinai wani rugugin tashin hankali ya rufto min idan da gaske wani abu yasamu Yaj Rafeeq,rayuwata had'e take da tashi bazan iya jure ganin sa cikin mummunan yana yi ba,na yanzu ma ni kadai nasan abunda nakeji cikin raina,kuka ya kwace mun sosai bayan na gama maganar,saurin dawowa wajena tayi tana dora kaina jikinta ta rungumeni cikin lallashi take cewa,
"Ba fata muke ba Roohee,ba abunda zai same shi in sha Allahu zai tashi lafiya kuyi auren ku"
Daker ta samu na daina kukan nai lamo akan cinyarta, tana shafa kaina har bacci mai nauyi da na hana ya daukan dazu ya sace ni a yanzu ban shirya ba.
*TAU FA!,SHIN WAI MEKE FARUWA NE HAKA DA WANNAN FAMILY?SHIN KUNA SO KUJI?KAR KU DAMU KU BIYO NI ZAN WARWARE MUKU ZARE DA KUMA ABAWAR, TAKU CE HAR KULLUM MOM MUHSEEN MAI NISHAD'ANTAR DAKU DA KUMA FAD'AKAR DAKU A CIKIN DAD'AD'AN LABARANTA, MUJE ZUWA...........*
MOM MUHSEEN&ASAAD🥰👌🏻
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....2
Kwana na d'aya aka sallame ni,yayin da Yah Rafeeq sai da yai kwana uku cib, acikin wad'anan kwana kin daga ni har shi muna cikin yana yi marar misaltuwa, ni dai gani nan ne kurin don ruwa ma kanshi wuyar sha yake mun,kamar mai azumi duk na addabi kaina banda aiki daga kuka sai tunani,kuma har yanzu bamu zauna da Abba ba balle in saka ran zaiyi wani abu akai, Hajja kau ban sake zuwa na gaida ta ba don wani irin haushin ta nakeji ainun,to balle wani Abba Habibu da matarsa wanda ko sunan su bana so inji ankira,don kallon munafukai nake musu.
bana ma fita inba dakin Mami zanje inga jikin Yah Rafeeq,shima har yanzu baya uhm balle uhm uhm abinci kanshi Mami ko umma na ke bashi abaki daker da lallashi da kalamai sannan zai d'anci,ko idan an saka mana tare haka zamu ringa tsakura bamai ma d'aya magana,ni kam inaci ina hawaye masu zafi, baya iya mun mgn saidai ya aje mun hanky gabana alamun lallashina kuma baya son kukan,zan dauka na share hawayen har mu gama ba zan sake ba,ba kuma don na daina yin kukan ba gobe ma zan dasa wani.
Kwata kwata baya iya fita koda falo,tun Abban shi na fad'a yana cewa son jikine da lambo har lamarin ya fara damun su suduka,Yah rafeeq sai dai kallo kurin ba magana,lamarin daya sake gigitani ya sake jefamun tsanar Hajja da su MAMA,Kai kowa ma ni haushin sa nakeji duk na lalace bana ko baccin kirki.
Wajen aikina da nake services sun kira ni yafi sau shurin mu saki ban ma iya dauka balle har inyi wata maganar kare kaina na rashin zuwa kwana biyu, sai da Hajja ta kira wani malami ya ringa yo ma Yah Rafeeq rubutu yana sha don samun daidaiton hankalin sa,don nema yake ya zauce gaba d'aya,ni kaina ina bukatar rubutun dan ganan saboda duk dare ni kadai nasan halin da nake tsintar kaina aciki,zuciyata wani irin ciwo take mun da bazan iya misalta irin yadda take mun ba,kowa gidan ba walwala da farin ciki saboda mud'in mun shafe jigon duk farin cikin gidan, mun kasance cikin yin raha da juna da zolaya da wasa da dariya,in har Yah Rafeeq na gida tabbas kowa bazai b'acin rai ba,daya daga cikin halayyarsa kenan da taja zuciyata ga kaunarsa.
Hmmm ba zaku fahimci me bakeji ba sai na baku labarin yadda rayuwar mu take a baya,amma ku bani lokaci.
Kasancewar dokace duk dare b'angaren Abba Habibu ake dinner kuma baka isa ka take wannan dokar ba inba da kwakkwaran dalili ba,Hajja kad'ai ce ke cin abincin ta bangarenta saboda bata da lafiyar k'afafun da zata iya zarya,babban dining ne mai dauke kujerar kowa na cikin gidan har wadanda sukai aure har yau wajensu na nan,duk yadda naso karna fito dinner Abba ya kirani a waya cikin b'acin rai,
"Kina so inzo har na inci mutuncinki ne komi?kar ki sake ki kara minty biyu ban ganki anan ba"
Bai bani damar furta kalma d'aya ba ya datse kiransa,Hawaye masu zafi suka kwararo mun na tausayin kaina,wannan kad'ai ya nuna mun Abba baya goyon bayan na,koda zan nuna bijirewa to tabbas shine zai mun cikas,kuma zai iya shafe dukkan soyayyata ya hukuntani,Rukee ta turo k'ofar dakin namu tana kamo hannuna don na tashi,ban musu ba na tashi na sauko daga bisa gadon na biyo bayanta, fuskata kamar jaan k'osai saboda kuka daya zamar mun jiki.
On ready sun fara cin abincin su bakajin karar komi sai ta spoon da d'an uwansa plate,kujerar kusada Mami na nufa zan zauna maganar Abba ta dakatar dani ya nuna mun kujerar dake Kusa da YAH RAMADAN, "daga yau can ne mazaunin ki,ku fara sabawa kafin komi ya dai-daita.........wani b'acin rai mai girma ya turnik'eni kuka ya k'wace mun, "Abba please" kar ki sake cewa komi wuce ki zauna kafin ranki ya b'aci,kuma ki rufe mana baki"
Dole na maida kukan cikin cikina,na ja kujerar inajin yadda tsanar sa ke huda zuciyata, abunda ban tab'a kawo wa ba a rayuwata ko amafarki, wai tsayuwa ta minty biyar nida Yah Ramadan matsayin makusanta masu niyyar Aure,sai gani zaune gefen sa na tsayin mintoci ko a wanni,.
"Roohee y'ata"
Abba Habibu ya Kira sunana kamar yadda yake kirana kodayaushe, murya ba amo na amsa mashi daker,
Ya ce "Kiyi hakuri ki daina kuka,me za'a zuba miki kici"
Ina shashshekar kukan na ce, "Abba bana jin yunwa,ba zan iya cin komi ba"
"Aa Y'ata,karki biyewa zuciyarki ki ringa kwarar cikin ki,saboda shi ai baisan wani damuwa ba,shi kawai in lokacin zuba mashi yayi kawai a zuba mai, zakici sinasir na saka miki da kaina,na san y'ata tana son shi"
Kai na d'aga mashi kurin don ba abunda zan iya sake cewa kuma,..........."Bari na zuba mata Abbansu,"
Mama ta fad'a tana tashi da kanta ta fara k'okarin zuba mun,haushinta ya isheni don nasan na munafurci ne ba komi ba, Ummanmu ta kasa rik'e takaicinta taja dogon tsaki wanda ba wanda zaice baiji ba a wajen, wani dak'ik'in kallo Abbana ya watsa mata ya kauda kai ya cigaba da cin abincin sa, kamar tasan ba zan iya wuce cin guda d'aya ba ta zuba mun da namomi a cikin miyar sannan ta zuba mun zob'o mai sanyi kamar dai yadda kowa ya sanni da son abu mai sanyi,har ruwa saida ta zuba mun sannan ta ce "kici a hankali kinji ko"
Banza nai mata don bata san yadda nakejin haushin ta ba,da ba zatai kasadar kusanta kanta dani ba,haka na ringa tsakurar sa ina ya mutsa fuska tsabar yadda nake kyamar Yah Ramadan har cikin bakina nakejin warin jikinsa, ba kuma don yana warin ba tsabar sama rai ne kurin da tsanarsa da nake.
"Idan kowa ya kammala cin abincin zamu sake tattaunawa a falon Hajja,fatan ba zaku b'ata mana lokaci ba"
Inji Abba Habibu yana mik'ewa ya ce masu Abbanmu "sai kun k'araso zan jiraku acan"
Shida Mama da Najiba suka tashi tare,bayan kamar minty biyar Yah kucaki yabi bayan su Yah Ramadan kenan shida Yah Fahad wanda yau ya sauka garin daga lagos wajen aikin sa,duk rikicin da akai baya nan.
Abbana ya gama shida Abba Nura suma suka tashi,daga ni sai Rukee dake jirana mutafi sai ummi da ummana da Mami,
"Kina ganin siyasa ko Mami?"
Inji ummanmu tana kallon Mami tai maganar cikin takaici, "uhm na gani mana,neman gindin zama ne kurin,tunda tasan dai D'anta ko za ai me bazai tab'a samun mace kamar ROOHEE ba,ba dole take rawar k'afa ba"
Ummanmu ta ce, "ki barta wallahi saita d'an d'ana k'ud'arta inhar wannan abun ya faru,daga ita har uban yaron harshi yaron,ke ni ko shekara nawa ROOHEE zatai tare dasu ya saketa bana jin ko d'ar,don nasan tafi karfinsa kuma zata samu miji na nuna ma sa'a..........har ma tunanin anyi auren kike kenan?haba dai Maijidda kima bar wannan maganar wallahi"
Nidai bance musu uffan ba,na gama cakalar sinasir din na tashi muka tafi can falon nida Ummi da Rukee.
Su ummanmu ne karshen shigowa falon,Hajja na kan kujera ta hakimce tana kallon kowa d'aya bayan d'ayan har saida kowa ya gama shigowa,Anty Rahma da Anty Sha'awa Anty Rafeea ne basa nan,Kowacce tana d'akin mijinta........"Habibu bud'e mana taron da Addua"
Cewar Hajja cikin isa da nuna ita d'in walkice daidai k'ugun kowa,kuma kujera dole azauna akanta, cikin natsuwa irin tashi ya karanto addua ya kuma bukaci ai salatin annabi aka gama sannan Hajja tai gyaran murya tana cewa,
"Ba komi bane akan dai maganar ROOHEE DA RAFEEQ NE, a ranar ban gama magana ba taron ya lalace, to yau ban buk'atar kowa ya tashi saina gama maganata, sannan ban bukatar jin bakin kowa inba ni na buk'ata ba,kar kuma wani marar kunya ya katse mun zance na,ato inba mutum so yake yai zawarci da shekarun girma akansa ba"
Kowa yasan dasu Ummanmu take ba sai anje ko ina ba, nikam ko zaman kirki bana iyawa sosai na zame na kwanta jikin Rukee kurin,ina rufe idanuna don ko kallon wasu fuskokin bana so nayi,Yah Rafeeq na zaune facing dina shima idonsa rufe kamar mai bacci.
"Aure tsakanin Roohee da Rafeeq dai an soke har abadan,in kuma kun shirya taka dokar Allah bismilla tunda bani na hana ba,sannan na biyu Kamar yadda na fad'a rannan Ni da nake matsayin kaka wadda ta isa da ubaninku na yanke hukuncin iyayenku maza su had'a Auren ROOHEE DA RAMADAN,SHI KUMA RAFEEQ GA NAJEEBA NAN,RUK'AYYA KUMA GA FAHAD NAN, WALLAHI KO BAYAN RAINA WANI YA CANZA WANNAN WASIYYAR BAN YAFE MASA BA DUNIYA DA LAHIRA, don naga alamar zumuncin neman lalacewa yake,ada vanyi niyyar matsama kowa akan auren wanda bai ra'ayi ba don yana da illa,amma duba da yadda iyayenku mata ke neman tarwatsa mun iyalai yasa na canza wannan shawarar,bazan zuba ido ina kallo ku maida Habibu da matarsa kamar ba kowa ba,bacin sune kominku kuma kune kuke rawa da bazarsu ba wai su ba,kai Nura da kai Taheer ai kune shaidar hakan don haka ku shaida ma matanku da iyalanku cewar HABIBU DA MATAR SA ZEENA ba abun wulakantawa bane ko rainawa ba,sud'in mutanan kirki ne masu daddataku da sanin darajar y'an uwantaka,wallahi koda wasa naji wani yai musu wani abu na rashin kima ko rashin kunya zai gane wacece Hajja,kuma na bada umurnin a tsayar da ranar aure nan da wata guda,wannan itace magana ta in akwai wanda yake da ja sai inji."
Tsiit kakejin falon saboda cikin fusata da hargagi take maganar wanda ya bawa kowa tsoro,don Hajja nada iska insuka tashi to kowa ma ubanshi yake ci,kuma fusatar ta nadaga cikin abunda ke jawo tashin aljannun,tana iya kwana da kwanaki basu sauka ba suna gana mana azaba,shiyasa yanzu kowa ya shiga taitayinsa.
Abba Habibu ne yai karfin halin cewa cikin kwantar da murya da k'ank'an da kanshi, "Hajja ba wanda ya isa ya taka umurnin ki,daga mu har iyalanmu dole mubi abunda kike so,amma alfarma nake nema masu yaran nan mai zai hana abarsu su huce daga yana yin da suke ciki,sannan aba sauran dama su fahimci juna kafin a fara maganar tsayar da ranar aure...........Kai Ramadan kana da jaa akan hukuncin dana yanke?"
Hajja ta katse Abba Habibu da fad'ar hakan ga Yah Ramadan, dagowa yayi cikin yana yinsa na koyaushe watau silently ya ce cikin muryar sa mai sanyi "Aa Hajja banda jaa akai, kuma na karb'a hannu bibbiyu"
"Shin miye baka sani ba akan Qanwarka Roohee?"
"Babu Hajja"
Ta juya ga sauran duk tai masu wannan tambayar,Yah Rafeeq ne yai mata banza tai maganar har ta gaji ta kyalesa, hawaye suka tsinke mun jinake kamar na bar duniyar kozan huta da wannan bakin cikin.
"To Habibu kaji ai ta bakin su,don haka hukuncina na nan inhar ba anaso anuna mun iyakata ba"
"Aa kiyi hkuri ba wanda ya isa,Taheer kaji kaima Nura kaji ko?"
Suka amsa da cewar sunji kuma zasu zartar da dukkan abunda ta buk'ata, tace "na sallami kowa na gama magana"
Mom muhseen&Asaad🥰
_*🔪WUK'AR FID'AR GIWA🔪*_
_{BA GIRMA SAIDAI KAIFI}_
*ADABI WRITERS ASSOCIATION....*
By
Mom muhsen&
Asaad.
Wattpad name
Humaira3461.
🅿️.....3
Shigowar Mamar dakin nashi yasa yai firgigi daga dogon tunanin daya shiga ya tashi daga kwanciyar da yake tun wayewar garin yau d'in, ida sa shigowa tayi ta zauna a gefen sofer tana kallon sa cikin nazari sosai kafin cikin natsuwa ta ce dashi
"Meke damun ka RAMADAN,?kar kace mun babu komi domin bazan yadda da bakomin ba"
Jujjuya kai yake yana tunanin me zai gaya mata,shi bai cika son fadar damuwar sa ba balle ma ga mahaifiyarsa wadda yasan duk duniya tafi kowa shiga damuwa in yana ciki,to mizai gaya mata akan abunda yasan itama bata da wani abunyi.........
"Aduk duniya babu wandaa zai karanci halinka sama dani RAMADAN,saboda nid'in mahaifiyarka ce wadda ke tsaye don y'ay'anta,kuma take iya bakin k'ok'arinta akan ku,ku hud'u Allah ya bani amma ba wanda ban san halin sa ba,don haka karka b'oye mun nasan duk akan Auren ka da ROOHEE NE,ko ba shi bane???"
Ya kasa cewa komi don bai da abun cewar,ta riga ta sani no need ya sake tisa mata........."koda yaushe ina k'ok'arin ganin na magance maku damuwarku duk sadda kuke ciki,Amma a wannan karon RAMADAN kayi hakuri bazan iya yi maka maganin damuwar ba,don abun yafi karfina ta inda bana iya cewa k'ala akai,ga Najeeba can tana kuka saboda itama abun bai mata ba, tana da wanda suka dai-daita kaima shaida ne,amma na bata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 16