safe su taho tare, babu ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah!
Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce duk su yi alwala su yi sallah.
Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan".
Ya ce"To, wasu yara?"
Ta ce"Yaranka".
Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma don Allah ki kau da kai ga matsalolinta".
Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi, ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki".
Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?"
Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su".
Ya ce"Yanzu suna ina?"
Ta ce"Suna ɗaki".
Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba".
Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!".
Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne.
Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?"
Duk suka yi shiru suna raba ido.
Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce babu daɗi?"
Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu".
Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work, ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira.
Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta sannan ta yiwa ƙannenta.
Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku".
Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka".
Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku".
Ta ce"Mu dai a'a".
Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran nan suke haka ne?"
Ya fito ya zo ɗakin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?"
Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita".
Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin.
Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haɗu da ita! Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan".
"Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba.
Yana fita Momy ta shiga banɗaki ta kira Sauda ta sake faɗa mata, ai kuwa ta hasala tana ta zage-zage.
Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun gaishe da Antinku?"
Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, suka karya mai adaidaitansu ya zo suka tafi makaranta.
Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su".
Maryam ta ce"Allah Ya kyauta".
Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun da ni na haife su!".
A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa ƴaƴana yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faɗa mini kalmar matarka?"
Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya! To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!".
Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta bambami.
Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa, idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki".
Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma".
Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!".
Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki.
Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana marari za a samu miji".
Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da Sauda za ta nemi maganin gyara zama".
Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan".
Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta".
Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?"
Aliya ta ce"In sha Allah!".
Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa Inna sai da safe ta bi shi su tafi.
Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka, ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta.
Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna".
Ya zauna yana sauraronta.
Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da kake a yanzu ba".
Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!".
Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta, ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan, lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta ce"Sannunku da zuwa".
Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida".
Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai, tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta wuce fuuu ta yi cikin gidan.
Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya, kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?"
Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani".
Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso".
Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake.
Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a ƙarƙashin katifarku!".
Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba".
Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana.
Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa".
Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata, gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe.
A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu, fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya fara tambayarsu me ya faru?
Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu".
Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?"
Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?"
Suka yi kanta suna kuka.
Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu".
Ta ce"Aljanu kuma?"
Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya ce"Abun ya bani mamaki wallahi".
Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu".
Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?"
Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su don kar ƴaƴana su moru".
Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!".
Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta zan yi muku addu'a".
Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!".
Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a".
Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta.
Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa, yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa ƙeyarta waje.
LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
15
Haka Alhaji ya yi kwanan zaune yana gadin yaransa. Washegari da asuba da zai tafi masallaci suka koma ɗakin Sauda, duk sun yi zuru-zuru ba su samu bacci ba, sai kuma tausayinsu ya kamata, amma tun da buƙatar maje haji sallah wannan ai ba komai ba, sai a lokacin suka samu bacci.
Shi kuwa Alhaji jikinsa duk ya yi sanyi, tun asubar ya kira wani Malami ya faɗa masa, ya ce don Allah ya zo, ya ce ga shi nan zuwa.
Da safe Sauda ta gama haɗa abun karyawa, ta yi wankanta, suna dining ita da Alhaji suna karyawa sai ga Sauda ta fito fuskar nan a murtuke tamkar kunun kanwa, ta ja ta tsaya a kansu riƙe da ƙugu, ta ce"To sannu hamshaƙiya mandiya! Wato ke kin samu miji kin samu gida kike tunanin kina da dabarun da za ki raba shi da matarsa da ƴaƴansa ko? Kai kuma ka ji tsoron Allah, da na yi magana a kan ƙara aurenka sai ka ce kai za ka yi adalci, tabbas ga adalci nan na fara gani ai".
Alhaji tun da ta fara magana ya ajiye kofin hannunsa yana kallonta, saɓanin Maryam da ta yi mata kallo ɗaya, sai da ta kai aya sannan ta ce"Maman Momy kin fito? Ina kwana?"
Ta ce"Ke dakata! Ba na son gulma, ina ruwanki da yadda na kwana? Da shi nake yi".
Ya ce"Haba Sauda, wannan dai ba girmanki ba ne, da sassafen nan kin fito kina ɗaga murya haka? Me aka yi miki?"
Ta ce"E ai dole ka ce haka, tun da ka samu mai siririyar murya ko? Na ga dai ranakun kwananta sun ƙare jiya, amma ka lafe ta baka abinci kana ci a ranar kwanana, me kuke nufi?"
Alhaji ya ce"Ikon Allah! To kuma mene ne abinci? Yanzu don ta ba ni abinci laifi ne da har za a kasa shiru? Kuma ko ta ba ni laifin waye? Tun da ke kina can kina baccinki ita ta tashi ta dafa sai na ƙi ci?"
Sauda ta ce"Au haka ma za ka ce? Ina can ina bacci ko ina can ina kula da yaran da aka firgita su? To wallahi ko ruwan hannunta ka sha a ranar kwanana ban yafe ba!" Ta ƙarasa maganar tana ture kofin gabansa.
Bai ce komai ba ya tashi ya fice waje, ta zabgawa Maryam harara ta ce"Ke kuma mu zuba ni da ke!".
Maryam ta bi ta da kallo tana jin duk da haƙuri ya zame mata dole, amma fa ba za ta ɗauki wulaƙanci ba. Ta ƙarasa cin abincinta ta kwashe komai ta mayar kitchen.
Shi kuwa Alhaji ɗaki ya koma ya kwanta, can anjima Sauda ta shigo ta same shi ta ce"Ai sai ka fito ka karya".
Ya ce"Ba na ci".
Ta ƙaraso cikin ɗakin ta ce"Au don na faɗa maka gaskiya shi ne ka yi fushi? Ka san dai bai kamata a ce tun yanzu ka fara nuna rashin adalci ba, ka san dai hukuncin hakan".
Bai kula ta ba, ta ce"To na ganka a kwance babu shirin tafiya kasuwa, ko dama ka ɗauki hutun amarci ne?"
Ya ce"Akwai malamin da na kira zai zo, shiyasa ba zan fita ba, su ma yaran yau su haƙura da zuwa makarantar, tun da dama ba su yi bacci ba". Ta taɓe baki ta bar ɗakin.
Ƙarfe bakwai da rabi Malamin ya zo da almajiransa su uku, Alhaji ya ƙara yi masa bayanin yadda abun ya faru, aka kunna garwashi suka yi hayaƙin magani, sannan suka yi karatu, malamin ya ja yaran da tambaya cike da kwantar musu da hankali, ya ce me suka gani? Suka ce ba su ga komai ba, Ummansu ce ta ce musu akwai aljanu, abun ya ba shi mamaki shi da Alhajin, Alhaji ya ce"Yaushe ta faɗa muku? Kuma kun gansu?"
Momy ta ce"Ba mu gansu ba, muna bacci ta zo ta tashe mu ta ce aljanu suna ƙasan katifarmu".
Malam ya ce"Kun ga, da wasa take yi muku, gaskiya na duba babu aljani ko ɗaya a gidan nan, kar ku sake jin tsoro ku nutsu, idan za ku kwanta ku yi addu'a, ko da aljanun ba za su iya zuwa ɗakinku ba".
Suka ce"To" Jikinsu duk ya yi sanyi.
Malam ya tabbatar masa babu aljanu a gidan, sannan ya tafi ya bar Alhaji da mamaki.
Sauda da ba ta san yadda aka yi ba sai ganin Alhaji ta yi ya shigo, ya zaune ya ce"Sauda jiya me ya same ki ne? Ashe ke ce kika je kika tashi ƴaƴan nan kika ce musu akwai aljanu?"
Ta zabura ta ce"Ni kuma? Ni da kun ma riga ni fitowa? To sai dai idan ba su gane wacce ta tashe su ba, ƙila matarka ce, to wallahi sai a binciketa ni ba za ta haukata mini ƴaƴa ba, ƙila turen aljanun ta yi musu".
Ya ce"Ke dakata don Allah! Su ƴaƴan naki makafi ne da za su kasa gane ki? Ni na yarda da gaske ke ɗin ce kika aikata, amma na cika da mamakin akan me za ki firgita mini yara? Me kike shiryawa?"
Ta ce"To shikenan! Duk yadda ka ɗauka hakane!".
Ya ce"To dama ai haka ɗin ne, ke ce! Kuma kanki kika yiwa ba kowa ba, idan wata larurar ce ta same ki Allah Ya ba ki lafiya, amma kar ki sake saka yara a shirmenki".
Ta ce"Ni kake faɗawa haka?"
Bai sake cewa komai ba ya tashi ya fice daga ɗakin, sai ya shirya ya tafi kasuwarsa yana ta tunanin dalilinta na yin haka, amma ya rasa.
Su kuwa yaran kasa kwanciya suka yi a ɗakinsu, suka zo jikinta suka kwanta har yanzu sun ƙi yarda wasa take yi musu, gabaɗaya ba su da sukuni.
Ƙarfe goma Maryam ta fito babban falon, ta ga gidan kaca-kaca, duk ga kwanukan da suka ci abinci ma ba kwashe ba, zuciya ta ce mata ta gyara ba don halin Sauda ba, tun da za ta iya yin baƙi ta ji kunya, don haka ta kwashe kayan ta kai kitchen, wanke-wanke dai ba za ta yi mata ba, ta dawo ta gyara falon fess ta saka turaren wuta, ta zauna tana danne-danne a wayarta, sai ga Sauda ta fito.
Ta ƙaraso cikin tafiyar ƙasaita, ta zo ta tsaya ta riƙe ƙugu ta ce"Ke kuma a su wa da za ki hakimce mini a falo?"
Maryam ba ta kalle ta ba ta ce"Ni a matar gida, kuma falo mai gidan ne ya faɗa mini na kowa ne ba naki ke ɗaya ba, shiyasa na zauna".
Sauda ta ce"Inyeee! To ita kuma kujerar daga gidan ubanki aka kawo?"
Maryam ta ce"A'a, amma ya faɗa mini ke ma ba daga gidan ubanki aka kawo ba, shi ya siya da kuɗinsa, don haka nake ganin ina da lasisin zama a kai".
Sauda ta ce"A ƙwarai! Dole ki zage ni tun da kin ga makwancina, to bari ki ji na faɗa miki gaskiya, ki saka a ranki ba ki samu wajen zama ba, don wallahi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 21