magunguna, tun bayan rabuwarsu da Maryam sai yau ya ga makwancin yaran, zanin gado ne na yadi kawai ake shimfiɗa musu a kan tayals, ashe shiyasa suke yawan yin mura wataran ma su tashi jiki a kumbure, sai a ranar ma yake jin ai Hannr dama aikinta kula da yaran ne, ita Sauda babu ruwanta da su, ransa ya ɓaci sosai, da ganin irin ruƙon sakainar kashin da Sauda take yiwa yaran da ba su ji ba, ba su gani ba, shi ma har sai da ya zargi kansa da rashin saka ido har haka ta faru.
Ya shiga ɗakin Sauda ransa a ɓace, yana daɗewa bai shiga ba sai dai idan sauri yake yi ba zai jira har ya kira ta ya ce ta zo nashi ɗakin ko ta fito falo ba, tana kwance tana hutawa ta idar da sallar isha'i, tun da ya dawo gidan bai ganta ba, ko asibitin da Hannen suka je, saboda yana jin haushinta a ganinsa sakacinta ne ya sa yaron ya ƙone, sai kuma ya ga wani ƙarin ɓacin ran, ashe yaran a ƙasa suke kwana.
"Ke Sauda!" Ya kira sunanta a dake.
Ta ɗago tana cewa"Alhaji lafiya kuwa?"
Ya ce"Sauda yanzu tsakani da Allah abin da kike yi wa yaran nan kin yi daidai kenan!? Ashe a ƙasa suke kwana sanyi yana shigarsu? Kin ware musu ɗaki su biyu kamar ba ƴaƴana ba kuma ma wai ba za ki iya yi musu hidimar komai ba shi ne kika saka na ɗauki ƴar aiki ina biyanta? Kuma yanzu saboda ba ɗanki ne ya ƙone ba shiyasa ba ki sanar da ni ba har sai da na dawo na samu labari ko? Idan kin san ba za ki iya kula da su ba a kan me za ki karɓa? To zan auro wacce za ta kular mini da su nan ba da jimawa ba!"
Ta tashi zaune ranta a ɓace ta ce"An zo daidai wajen! Alhajin ka daina kwana-kwana, kawai ka fito ka ce mini za ka dawo da uwarsu tun da ka ji ta fito daga auren da ta yi, to bisimillah! Idan ka dawo da ita ni ai ka rage mini aiki ne".
Ya ce"Au haka ma za ki ce?"
Ta ce"Idan ba ka ji ba ma zan maimaita! Ku maza dama ai ba ku san kunya ba, wannan kaɗan kenan daga halinku, duk tsayin lokacin da na yi ina riƙe yaran yau ɗaya don an samu matsala shi ne za ka zo kana faɗa mini ba daɗi, ko ni ce na ƙona shi ai sai haka".
Ya ma kasa cewa komai kawai ya ce"Za ki gani kuwa".
Ta ce"Na ga alkhairi!".
Ya shiga ɗakinsa ya zauna, zuciyarsa ta raunana sosai, ya faɗa duniyar tunanin me yasa ma ya saki mahaifiyarsu? Anya Allah ba zai kama shi da laifin sakaci da kula da ƴaƴansa ba kuwa? Yau ne karo na farko tun bayan rabuwarsu da Maryam da ya zauna ya fara tuna yadda zaman aurensu ya kasance, ya dinga tuna abubuwan farinciki, soyayya da kulawar da ta shiga tsakaninsu, tabbas Maryam mace ce wacce ta zauna da shi da kyautatawa, ya shiga tuna yadda abubuwa suka canza lokacin da zaman nasu ya zo gangara, ya tuna yadda ya tashe ta daga gidansa haka kawai saboda shawarar Sauda mara toshe ballanatana makama, ya kama mata haya a ƙaramin gida, ya tuna ainahin silar mutuwar auren, sai yanzu ya auna ya ga sam laifin ma bai kai a yi saki don shi ba, ya tuna irin yadda ya dinga bin umarnin Sauda ba ya tsallake maganarta, sai ya fara zargin kansa anya babu wata a ƙasa?
A ranar bai yi baccin kirki ba, kwana ya yi yana tunani, kuma lokaci-lokaci idan ya jiyo kukan Hasan yana leƙawa ya yi masa sannu, tausayin yaran har ma da Maryam ɗin da ya raba ta da su ya yi masa tsaye a rai, har hawaye ya yi babu zato.
Washegari da safe a sanyaye ya je gidan Inna, bayan sun gaisa ya yi shiru, ita kanta ta lura da yanayinsa, ta ce"Hamza lafiya kake kuwa?"
Ya ce"Lafiya lau Inna, jiya ɗana Hasan ya ƙone da ruwan zafi".
Ta ce"Subhanallah! Garin yaya?"
Ya ce"Wallahi kawai zuwa na yi na tarar da shi jiki a saluɓe, wai Sauda ko kirana a waya ba ta yi ta sanar da ni ba, sai yanzu na gane irin ruƙon da take yiwa yaran, Inna ina jin tsoron Allah Ya tashe ni ya tambaye ni akan haƙƙin yaran nan, ashe a ƙasa suke kwana, kuma su biyu a ɗaki, saboda ba ita ce ta haife su ba shi ne take ware su tana yin yadda ta so? Kuma don na yi ƙorafi har take faɗa mini maganganu marasa daɗi".
Inna ta ce"Sai haƙuri, dama fa ba kowa ne yake iya riƙe ɗan wani ba Hamza, idan ka ga babu dama ka dawi da mahaifiyarsu mana, wai me ya haɗa ku ma ka sake ta? Auren naku na ga da albarkarsa, sai haihuwa take yi kuma ƴaƴa mazan da kake nema, ni dai ka ga ba zan iya riƙe ƙananun yara na ce zan yi raino ba, idan kana ganin Sauda ba za ta iya ba to ka dawo da mahaifiyarsu".
Ya ce"To ai Inna ni fa tun rabuwar mu babu wata alaƙa da ta ƙara shiga tsakaninmu sai sanda ta nemi yaran su je wajenta, kuma kin ga da yadda aka ƙare ai, ke ma nan ƙin karɓarsu kika yi, amma jiya Saudan ta ce wai ta yi wani auren ta fito".
Inna ta ce"To ai sai ka hanzarta ka je ka lallaɓa ta dawo kan yaranta".
Ya ɗan yi jim yana auna yadda Innar za ta ɗauki maganar da zai yi mata, sannan ya ce"Inna sannan ni fa ina tunanin a lokacin zamanmu da Maryam kamar ba na cikin hayyacina, saboda wasu abubuwa da suka faru sai yanzu suke dawo mini".
Ta ce"Kamar ya ba ka cikin hayyacinka?"
Ya ce"Gaskiya ina zargin Sauda, saboda yadda na dinga bin umarninta a lokacin kawai yanzu na gane ba haka ta bar ni ba".
Inna ta tsuke fuska ta ce"Ba na son neman fitina, saboda ka ga na ce ka dawo da waccen ɗin shi ne har za ka zaƙe? Me kake nufi? Kana nufin ita Saudan bokaye take bi har ta fitar da kai daga hayyacinka?"
Ya ce"Ba haka ba ne, dama dai zargi ne kawai, amma shikenan a bar maganar".
Ta ce"To sai ka tuba ka nemi yafiyarta kuwa, akan me za ka zargi mutum da shirka?"
Ta dinga sababi, shi ne ya lallaɓa ta yana ba ta haƙuri, ya tashi ya bar gidan, sai ya samu kansa da zuwa gidan wani Malami a nan cikin unguwar tasu, ya yi masa bayanin yana ji a jikinsa kamar a baya matarsa ta fitar da shi daga hayyacinsa, ya yi masa bayanin duk abin da ya faru, Malamin ya ce ya dawo anjima zai haɗa masa magungunan karya sihiri da rigakafi, idan akwai a jikinsa zai warware idan ma babu ko an yi masa ba zai kama shi ba, ya yi masa godiya ya tafi.
Daga nan gidan su Maryam ya wuce, gabansa yana faɗuwa yana ta tuna irin abubuwan da ya yi mata marasa daɗi, lokacin tara da rabi na safe a ƙofar gida ya tsaya ya aika yaro, yaro ya shiga ya ce wai ana sallama da Maryam, Maryam dake wanke-wanke ta yi tsaki ta ce"Wane ɗan wahalan ne kuma da sassafe? Ka je ka ce ba zan zo ba! Mutane sai ka ce suna bi na bashi, da safen nan wasu ma ba su tashi daga bacci ba wai ana sallama, aikin banza".
Fitowar Baba daga ɗaki ne ya katse mata maganganun, kallon da yake yi mata ya tabbatar mata da duk ya ji maganganunta, ya ce wa yaron ya je ya ce tana zuwa, sannan ya kalle ta ya ce"Kenan dai kina nan a kan bakanki na ba za ki yi aure ba ko? To ni ma ina nan a kan bakana, matuƙar maza ba su daina sallama da ke ba, to ba za ki daina fita ba, ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, komai lalacewar gari akwai na kirki a cikinsa ko da ƙalilan ne, ki fita ki ji wane ne, kuma ki saurare shi ki ji da me ya zo".
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken ta saka hijjabinta dake rataye a igiya ta fita tana ɓata rai. Sai da gabanta ya faɗi sanda suka yi ido huɗu da Alhaji Hamza, ta tsaya tana kallon shi, tsohon mijinta, wanda ta haifawa yara uku, mahaifin yaranta biyu waɗanda ta fi tausayi duk cikin ƴaƴanta, mutumin nan da ta ci alwashin za ta zauna da shi mutu-ka-raba, bawan Allah wanda ta nuna mata soyayya tun kafin aure har bayansa, ya kuma ba ta kulawa da soyayya a gidan auren ya ƙaunaci ƴaƴan da ta haifa, mai kyautatawa iyayenta, kafin komai ya canza fari ya koma baƙi.
"Asaalamu alaikum". Sallamar da ya yi ta katse mata tunaninta, ta kau da kai daga dubansa tana amsawa.
Sai kuma abubuwan da suka faru a ƙarshen zamanau marasa daɗi suka shiga dawowa kanta, ta tuna yadda ya rikiɗe mata kamar wanda aka aura masa ita dole, ta tuna ranar da ya sake ta ya ce ko idda ba za ta yi a gidansa ba. Ta fara tunanin dalilin zuwan shi gidansu a yau.
Ya ce"Maryam ina kwana? Mun tashi lafiya?"
Ta ce"Lafiya ƙalau".
Ya ce"Kwana da yawa, kin ɓuya".
Ta yi murmushin takaici tana jinjina rashin kunyar namiji, ya sake ta ya zo yana ce mata wai ta ɓuya, ba ta ce komai ba, ya ce"Dama...dama wallahi matsala aka samu, Hassan ya ƙone jiya".
Gabanta ya yi mummunar faɗuwa har sai da ta dafe ƙirji ta ce"Ya ƙone!? Garin yaya? Yanzu yana ina? Ko ya mutu?"
Ya ce"A'a, Maryam ki kwantar da hankalinki, abu ne ya zo da tsautsayi yarinya ta sauke ruwan zafi za ta juye a flas ba ta san yana bayanta ba ta sheƙa masa, amma abun da sauƙi".
Ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Sai zuciyarta ta karye ƙwalla ta taru a idonta.
Ya ce"Ki yi haƙuri, jikin da sauƙi, dama na ga dacewar na faɗa miki ne saboda ko za ki je ki duba shi".
Hawayen ya sakko mata, ta ce"Ai dama na san alkhairi ba zai kawo ka ƙofar gidan nan ba, sanda ba karɓi yaran su yi kwana biyu ya muka ƙare da kai? Sai yanzu da larura ta same su kuka gajiya sannan za ka neme ni?"
Ya ce"Sam, ba haka ba ne wallahi, ƴaƴana ne ba zan taɓa gajiya da su ba in sha Allah! Kawai dai na ga ke ma kina da hakki a kansu ne, idan larura ta same su ya dace ki sani shiyasa na faɗa miki, na san yanzu idan yaron nan ya warke kika ga tabon ƙuna a jikinsa za ki iya cewa don me ba a sanar da ke ba".
Ta ce"Shikenan zan zo anjima".
Ya ce"Allah Ya nuna mana, sai anjima".
Ya tafi, ita ma ta shiga gida, tana ƙarasa wanke-wanken tana kuka, a haka Uwani ta zo ta tarar da ita, ta ce"Ikon Allah! Ke kuma kukan me kike yi?"
Baba da ya fito daga wanka ya ce"Kukan me za ta yi wanda ya wuce na tilasta mata fita ta kula namiji?"
Maryam ta share hawaye ta ce"Ba fa wani ba ne, Alhaji Hamza ne ya zo, wai Hassan ya ƙone da ruwan zafi jiya, na je na duba shi".
Baba ya ce"Subhanallah!"
Uwani ta ce"Innalillahi! Garin yaya?"
Ba ta sake cewa komai ba, ta haɗa kayan ta kai su gefe ta shige ɗaki, bayan Baba ya fita Uwani ta shigo tana saka hijjabi ta ce"Ai sai ki tashi mu tafi ko?"
Maryam ta ce"Ni fa ba na son zuwa ma, saboda na san halin Sauda, ba na so ta yi mini abin da zan kasa jurewa a zo ana ganin laifina".
Uwani ta ce"Kuma haka ne, to ni ma ɗin kuma idan na je ni kaɗai ban tsira ba, yanzu ya kenan?"
Ta ce"Sai dai na kira shi sai ya zo ya ɗauke ki ya kai ki da kan shi".
Haka kuwa aka yi, ta kira shi a waya ta faɗa masa ya zo ya ɗauki babarta ta je dubiyar, babu jimawa sai ga shi a mota, da ƙyar Uwani ta lallaɓa Maryam suka tafi tare, sanda ta ga yadda jikin yaron ya yi kuka ta dinga yi, tana jin tausayinsu sosai, Hanne kuwa da dama ta same ta sai ta baje ta kwashe duk irin rayuwar da yaran suke yi a gidan ta zayyane musu, ta dinga zuga Maryam a kan ko kotu ne ta shigar da ƙara ta karɓi yaranta.
Da Alhaji ya dawo ɗakin Maryam ta ce"Alhaji zan tafi da yaron nan na kula da shi har ya warke".
Bai yi musu ba ya ce"Babu damuwa Allah Ya ba shi lafiya".
Ta haɗa kayansu har Husainin, ya kai su gida, ta shiga kula da su, ana ci gaba da kai shi wajen tofi.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
30
A hankali jikin yaron ya warke fess, Maryam ta ji daɗin zama da ƴaƴanta har tana fargabar a ce su koma, musamman duk ranar Juma'a idan aka kawo sauran yaran suka haɗu suna wasa, sai ta shagala da kallonsu wataran kuma ta shiga cikinsu su yi ta wasan tare. Kullum sai Alhaji Hamza ya zo duba Hasan tare da tsarabar yara har ya ji sauƙi, a ƙofar gida yake tsayawa sai yaran su fita, don haka ba ma ganin Maryam yake yi ba.
Yau da ta kama wata ɗaya da dawowar yaran gidan, Alhaji ya zo kamar yadda ya saba, sai dai wannan zuwan na dab ne mai ɗauke da manufa biyu, don yau so yake ya ga uwar yaran ba yaran ba, domin su tattauna ya ji a wace Larabar suke? Da ya zo kai katse kiranta ya yi a waya, ta ɗauka suka gaisa ya ce"Ina ƙofar gida".
Ta ce"Ok ga su nan fitowa".
Ya ce"A'a yau wajenki na zo ai".
Ta ce"To gani nan". Ta ajiye wayar ta saka hijjabi a ranta tana ayyana ƙila maganar komawar yaran zai yi mata.
Lokacin abinci suke ci, don haka ta ce kar su biyota su ci abincinsu, ta same shi a ƙofar gida, ta yi masa sallama ya amsa yana kallon yanayinta da ya nuna a sanyaye take, suka ƙara gaisawa, suka yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce"Maryam wajenki na zo".
Ta ce"Ina sauraronka".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce"Abubuwa da dama sun faru a zaman aurenmu, har kawo rabuwarmu da Allah Ya ƙaddara da kuma bayan rabuwarmu".
Ta ce"Haka ne".
Ya ce"Na zo ne na ba ki haƙuri akan irin abubuwan da na yi miki a zamanmu na baya, don Allah ki yafe mini, wallahi sai yanzu na fahimci irin abubuwan da na yi miki na rashin kyautawa".
Maryam ta ce"Wannan duka ya wuce Alhaji, ni dama ban riƙe ka ba, na yafe maka komai da ya faru, ai ita rayuwa ya kamata mutum ya gane wani abu guda ɗaya, duk wanda ya ce zo mu zauna to kamar ya ce ao mu saɓa ne, kuma duk zuciyar da take da adalci idan irin haka ta faru to tana fara duba kyautatawar da mutum ya yi mata a baya kafin ta yi masa hukunci don ya munana mata, Alhaji ka so ni a baya, har bayan auren ma ka so ni ka kyautata mini, ka so ƴaƴana, to ko iya wannan ya isa ya sa na yafe maka abin da ka yi mini na rashin kyautatawa a baya, wannan ya wuce har zuciyata".
Ya ji daɗi sosai, ya ce"Alhamdulillah! Na gode sosai Maryam, tabbas na yi nadamar rabuwa da mace mai kyaun zuciya irinki, kodayake ina ji a jikina ban makara ba, har yanzu ina da sauran dama, ina nufin..."
Sai ya ɗan yi shiru, sannan ya yi huci yana jin nauyin maganar, don bai san a yadda za ta karɓe ta ba, ya ce"Ina nufin Maryam ina roƙonki alfarma da ki dawo ɗakinki, ma'ana zan sake aurenki a karo na biyu, ki dawo kan yaranki ki kula da su".
Ya tsagaita yana kallonta don son ya gano yadda take ɗaukar zancen, amma bai gano komai ba, saboda fuskarta babu yabo babu fallasa, ya ci gaba"Ba don halina, sai don yaranki, su za ki duba ba ni ba, don Allah Maryam kamar yadda kika ce komai ya wuce to ki manta da komai ki dawo gidana, na yi kewarki soyayya da kulawarki sosai" Ya ƙarasa maganar cikin ƙasa da murya tare da raunanata, don isar da saƙon har zuciyarta kai tsaye.
Ai kuwa ya samu nasara, domin sai da zuciyarta ta doka ta kuma yi rauni, sai dai kash! A dai sabon tsarin da ta yiwa rayuwarta ta iya cewa ya makara, alƙawari ta ɗauka ita da zuciyarta ba za ta sake zama da kishiya ba har abada, auren Alhaji a karo na biyu kuwa yana nufin karyewar wannan alƙawarin, alƙawarin da take ganin shi ne mafitar rayuwarta ta gaba, shi ne samun farincikinta a gidan aure da kwanciyar hankali, shi ne zai bata lasisin zaman aure da yin sallama da zawarci har abada, wanda shi ne burinta, don haka take ganin Alhaji ya makara, duk da tana tausayin yaranta sosai da son ta rayu da su, amma ita ma tana son inganta rayuwarta, don sai tata rayuwar ta yi inganci sannan tasu ma za ta yi, indai ta samu yadda take so na aure a gidan da babu kishiya to sai ta dinga bin yaranta da addu'a, ta san za ta zame musu kariya a duk inda suke.
Ya ce"Kin yi shiru Maryam".
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce"Alhaji, ita dama sau ɗaya take zuwar wa mutum, damarka ta riga ta wuce, a gaskiya ba na jin zan iya komawa gidanka a yanzu".
Ya yi murmushin yaƙe don bai ji daɗin maganar ba, ya ce"Ban yi mamakin kalamanki ba, tun da na san ba a samun abu mai kyau ta sauƙi, ban manta sanda nake zaryar zuwa ƙofar gidan nan ina magiya ba, har ta yi tasiri na samu na aureki, to yanzun ma ba zan gajiya ba, amma zan ba ki lokaci ki yi shawara tukunna".
Ta ce"Ba na buƙatar shawara, wannan hukunci ne da na riga na yanke shi tun kafin na san za ka dawo ka ce kana sona a karo na biyu, ba zan taɓa komawa gidanka ba Alhaji, ba kai kaɗai ba, duk wani mai mata ba zan taɓa zaman aure da shi ba, saboda kishiyoyi sun shayar da ni maɗaci".
Ya ce"A wannan karon zan iya ware miki gidanki na da ban, ki zauna ke da yaranki kaɗai, kin ga babu wata matsalar kishiya ai".
Ta yi ɗan murmushi mai ɗauke da manufar kai namiji ne ba za ka gane ba, kafin ta ce"Alhaji abu guda ɗaya ne kaɗai zai saka na aureka, wanda kuma na san ba za ka iya yinsa ba, ni kaina ba zan so ka yi shi ba".
Ya ce"Mene ne wannan abun?"
Ta ce"Da a ce za ka iya rabuwa da Sauda da zan iya aurenka".
Ya yi jim, kafin ya ce"Gaskiya akwai wuya!".
Ta ce"Tabbas akwai wuya, Sauda ita ce uwar gidanka, uwar ƴaƴanka, ta ina za ka fara rabuwa da ita da ƴaƴa biyar? Idan ka yi mata haka ba ka yi mata adalci ba har yaran ma da iyayenka za su yi takaicin hakan, don haka a shawarce ka je ka ci gaba da zama da matarka kawai, ni kuma ina nan ina fatan Allah Ya kawo mini wanda ba shi da aure".
Alhaji ya ce"Maryam a yanzu fa ke ba yarinya ba ce, haihuwarki huɗu, zai yi wuya ki samu saurayin da zai aureki, ba kowane burinmu ne zai cika duka ba, wani abun dole mu yi haƙuri da yadda muka samu".
Ta ce"Ni ban ce sai saurayi ba, mara mata na ce, ko kai idan ka saki matarka yau ai sunanka mara mata".
Ya ce"Amma dai da kin ƙara shawara da ƴan'uwa Maryam, yaran za ki duba".
Ta ce"Abin da na so ka duba kenan kafin ka yanke wancen hukuncin, mu bar yara a hannun Allah shi zai shiga lamarinsu, zan haɗa musu da addu'a, kai kuma ka yi musu adalci ka dinga kula da su".
Ya ce"To shikenan, bari na je sai anjima".
Ta ce"Na gode ka gaida gida".
Ya ce"Yaran za su zauna a wajenki har zuwa sanda zan samu matar da zan aura ta riƙe mini su, idan kuma kin riga ni auren to zan san dai yadda zan yi da su".
Ta ce"Allah Ya yiwa kowa zaɓin alkhairi".
Daga haka ta shiga gida, shi kuma ya tafi, ta dinga tunani akan hukuncin da ta yankewa kanta, anya wannan hanyar mai ɓillewa ce kuwa? Amma a can ƙasan zuciyarta take jin hakan ne kawai mafitarta, kuma burinta zai cika nan ba da jimawa ba.
A ɓangaren Alhaji kwana ya yi da tunanin irin wannan hukunci da Maryam ta yankewa rayuwarta, alƙawari ya ɗauka ba zai dawo da yaran nan ƙarƙashin kulawar Sauda ba, ko da Maryam ba za ta dawo ba to ya zama dole ya ƙara aure, don ya nunawa Sauda zai iya samun wacce za ta kular masa da yaransa ba sai ita ce madogararsa ba, amma dai bai sare da Maryam ɗin ba ma, tun daga ranar yake ta bibiyarta a waya, saƙonni babu dare babu rana duk na ban-haƙuri, da nuna mata muhimmancin dawowa kan yaranta, amma a banza wai an mintsini kakkausa, daga ƙarshe ma sai ta daina ɗaga wayarsa.
To da dai ya ga wankin hula zai kai shi dare sai ya samu Babanta da zancen, yana ta so ta dawo ɗakinta, amma ga hukuncin da ta yanke, ran Baba ya ɓaci sosai, kuma ya cika da mamakin irin zuciyar mace, wai a tunaninta wannan ce mafita, a ranar babu kalan faɗan da bai yi mata ba, amma sai kuka da ta saka masa tare da jaddada ita fa ba za ta sake zama da kishiya ba, a wannan karon ma Uwani jikinta ya yi sanyi sosai, ta nunawa Maryam muhimmancin komawarta gidan Alhajin, don ta san shi ne zai fi dacewa amma Maryam fir ta ƙi ta yi tsayuwar gwamen haki kan ba za ta zauna da mai mata ba, haka kowa ya gaji ya ƙyale ta, aka zuba mata ido a ga gudun ruwanta, tun da duk wanda ya yi sallama da ita to kuwa za ta samu mai mata ne wani ma matansa biyu har da mai uku, har yanzu dai buri bai cika ba.
Shi kuwa Alhaji ya koma gefe yana jiran ranar da za ta ce ta gaji da jira ta ga wannan ba hanya ba ce mai ɓullewa ta zo ta same shi ta faɗa masa ta amince su maida aurensu. Tun da ya hau kan addu'o'in da Malamin nan ta ɗora shi da kuma magunguna na rigakafin karya sihiri shikenan yake jinsa ƙalau da shi, zuciyarsa fess babu wata damuwa, duk wani shakkar Sauda da yake ji a da ta riga ta kau, yanzu yana jinsa namiji mai cikakken iko a gidansa, don haka ba ya ma tunanin Sauda wai don zai ƙara aure.
Watarana da sassafe kowa na gidan su Maryam yana baccin safe, ban da Hassan da Husaini da suka fito tsakar gida suke wasan ruwa, Fatima ta shigo gidan cikin kuka kamar wacce aka yi mutuwa, kai tsaye ɗakin Uwani ta shiga tana sake rushewa da kuka, Uwani ta tashi a firgice tana salati ta kalli Fatima ta ce"Innalillaihi wa inna ilaihi raji'un! Me zan gani haka? Fatima me ya same ki? Hatsari kuka yi?"
Fatima da fuskarta take a kumbure kamar an sakawa fulawa yis, ga baki a fashe, ta sake fashewa da kuka ta ce"Ashiru ne ya yi mini duka, kawai saboda na taɓa wayarsa".
Maryam ta shigo ɗakin jin kukan ya yi yawa tana tambayar me ya faru? Uwani ba ta bi ta kanta ba ta ce"Ya dake ki!? To ke uwar me kike nema a wayarsa?"
Maryam ta ce"Kan bazawara ba gashi! Yanzu wannan duka ne? Kuma kawai don kin taɓa wayarsa? Amma dai ya sake ki ko?"
Ta girgiza kai alamar a'a, Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce"Wannan ai bai kai maganar saki ba".
Maryam ta ce"Haba babarmu ki kalle ta fa! Ya zage ƙwanji ya mata wannan dukan ki ce bai kai a rabu ba? Ai wallahi idan ni ce ko kai ne autan maza
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 21