ana ƙananun maganganu, kawai ina ganin a raba girkin nan, ka ga sai ta dinga dafa abin da ta yi niyya, ba sai na dafa ta raina mini ba".
Alhaji ya ce"Tabbas hakan zai fi, tun da ke Sauda na ga yawanci ranar girkin Maryam sai ki kira ni ki ce ku fa ga abin da kuke so ke da yara, kin ga idan aka raba ta kwana gidan sauƙi, kullum kuna da damar fafa abin da kuke so, wacce take son wani abun da babu a gidan ta kira ni a waya ta sanar sai na aiko".
Sam Sauda ba ta ji daɗin haka ba, amma tana ji tana gani aka raba girkin kowa yake yin nashi, sai kuma ta tsiri duk ranar girkin Maryam sai ta kwashe kayan miya da nama ta ɓoye, ita kuwa Maryam sai ta kira shi ta faɗa masa babu kayan miya, sai ya aiko sai ya dawo ya yi ta faɗa ya ce me aka yi da wannan uban kayan miyan ya ƙare, sai Sauda ta ce ƙarya take yi akwai kayan miya, idan aka duba kuma sai a ga akwai ɗin, ƙarshe dai Maryam sai hoton firjin take yi masa ta tura masa ya gan shi wayam da gaske babu komai, rannan ya zo kawowa Maryam ɗin kayan miyan, tana kitchen tana dafa farar shinkafa, ya miƙa mata yana cewa"Abun yana ba ni mamaki, jiya fa na aiko kayan miyan nan".
Maryam ta ce"Maman Momy ce fa take ɓoyewa saboda kar na yi amfani da shi".
Ya ce"Kamar ya? A kan me?"
Ta ce"Ka tambaye ta, ni dai na tabbata idan aka yi bincike tsakanin kitchen ɗin nan da ɗakinta sai an ga kayan miyan nan".
Ganin ya tsaya tunani kamar bai gamsu ba ya saka Maryam ta fara bincika kayanta, ai kuwa sai ga kayan miya a wata roba ga robar bama ita ma duk a cikin lokarta, ta ce"Ga shi dai gani ya kori ji".
Ta ci gaba da aikinta, shi kuma ya shiga ƙwalawa Sauda kira rai ɓace.
Tana zuwa ya nuna mata robobin ya ce"Mene ne wannan?"
Duk da gabanta ya faɗi amma ba ta nuna ba, ta ce"Ban gane wannan tambayar ba"
Ya ce"Ai dama ba za ki gane ba, to daga yau idan kika sake kwashe kayan miya zan ɗauki mataki, wai me yasa ba kya so a zauna lafiya? Idan kun ɓullo da wannan an kashe sai ki koma wani fannin? To gaskiya ya isa, babu biyar ɗinki a cefanen gidan nan, kuma yadda kike matar gida haka Maryam take, saboda haka ki san abin da kike yi ki kama girmanki".
Ya juya ya bar kitchen ɗin, nan ma sai Sauda ta daina kwashewa, aka samu zaman lafiya na kwana biyu.
Wata biyu da auren Maryam ta samu ciki, ta fara masifaffen laulayi wanda Sauda take ganin kamar da gayya take yi, ta ƙara jin tsanarta sosai, sai dai ta ji daɗin da cikin ya zo mata da laulayi, don ta san Alhaji ya tsani laulauyi, musamman wanda ake yin amai.
Babu wani jimawa Maryam ta gane Alhaji ya ƙosa da laulayin nata, domin babu wata kulawa da yake bata, abincinta ma ba kullum yake ci ba duk da wataran ma dauriya ce kawai take saka ta yi girkin, yanzu har fira ya rage zama ya yi da ita, duk sai ta shiga damuwa amma ba ta yi ƙorafi ba saboda a zauna lafiya.
Sai da cikin ya yi wata biyar sannan ta samu sauƙin laulayin, ya shiga wata na shida da ta yi scanning aka ce namiji ne Alhaji ya kasa ɓoye farincikinsa, domin ya daɗe yana son a haifa masa namiji, sai ya shiga tarairayarta yana nan-nan da ita, har ya fara siyo kayan jariri duka na maza.
Wataran suna falo da Maryam yana ɗaga kayan fa ya siyo yana cewa"Wannan ai ina ganinsu suka ba ni sha'awa na ce sai na siyawa Babana".
Sauda ta shigo ranta a ɓace ta zauna tana kallon su, Maryam ta ce"Wannan Baba dai akwai ɗan gata, gaskiya zai sha gata".
Ya ce"Ke dai bari, ai ranar da kika haihu na ga yaron nan a hannuna har rawa sai na taka, ai ban yi mamaki ba da aka ce namiji ne tun da dama sauran yaran da kika haifa ma duk maza ne ko?"
Ta ce"Maza ne".
Sauda ta ce"Sai ka tashi ka yi rawar ai tun yanzu, yaushe za ka bari sai ta haihu? Daɗin abun dai ita mace duk abin da aka ba ta shi take kawowa, don haka ni da na haifi ƴaƴa matan ba ni na bawa kaina ba, ƙila ma daga jininka ne haihuwar matan".
Ta tashi ta fice daga falon, gabaɗaya haƙurinta ya ƙare na yadda yake nuna zalamarsa akan cikin nan, ko haihuwar fari bai yi haka ba, da tana jin daɗi ganin kamar ya fara baya-baya da Maryam ɗin, amma cikin ƙanƙanin lokaci ya dawo kamar zai haɗiye ta, kuma ba ta yi mamaki ba tun da dama ta san shi yana son ɗa namiji, don kuwa tun cikinta na fari yake addu'ar ta haifi namiji, amma sai ga shi ba a samu ba, sai wannan shegiyar ce daga zuwanta za ta haifo namiji, a fili ta ce"Ai sai ki haihu ɗin na gani!".
Tun daga nan Sauda take ta tunanin hanyar da za ta bi cikin nan ya salwanta, ta yi nan ta yi can, ƙarshe dai ta yanke maganin zubar da ciki kawai za ta siyo ta bata, ta taɓa jin an faɗi sunan maganin zubar da ciki, don haka ta je chamest don ta siyo, sai a ka ƙi siyar mata aka ce sai ta zo da takardar shaidar daga asibiti aka rubuta mata, ta dinga yawo tana bin chamest duk amsar ɗaya ce, daga baya sai ta tuna akwai wani magani da ake sha idan cikin mutum ya cushe ya ka yin bayan gida, kuma indai mutum ya je siya sai an tambaye shi yana da ciki? Idan kana da ciki ba a baka, hakan ya tabbatar mata kenan maganin matsala ne ga masu ciki, don haka da ta shiga chamest na gaba sai ta ce cikinta ne ya cushe yau sati biyu kenan, ai kuwa aka bata magani aka ce ta sha guda biyu.
Ta taho gida cike da farinciki, a hanya ta tsaya ta sayi kunun aya jarka biyu, ta tsaya ta zuba ƙwayoyin maganin guda huɗu a ciki, ta jijjiga sosai ya narke, sannan ta shiga gidan.
Maryam tana falo a zaune, yara suna islamiyya,ta shigo ta miƙa mata kunun ayar roba ɗaya tana cewa"Ga wannan daga gidan Inna nake ta ce na kawo miki".
Maryam ta karɓa tana mamaki, ta ce"To an gode".
Sai dai ta ji bai kwanta mata ba,ta gan shi tsululu kamar ba na gida ba, kuma sanna wane mutunci ne a tsakaninsu da Inna da za ta bada kunun aya a kawo mata? Ta ajiye shi tana nazari.
Ita kuwa Sauda lokaci-lokaci sai ta leƙo Maryam ta ga har yanzu ba ta sha ba, can yara sun dawo daga islamiyya Maryam ta kira Nana ta ba ta kunun ayan, sai ga shi ta dawo mata da shi, Sauda tana biye da ita tana yi mata faɗan rashin makama, tana cewa"Ban hana ku wannan abun ba, ku ga abu a wajen babba ku karɓa? Zuwa kuka yi kuka saka ta a gaba kenan?"
Maryam ta ce"Haba, babu komai wallahi, ni dama ba son sha nake yi ba".
Sauda ta ce"To ai ga nasu can a ɗaki, don Allah ki sha".
Ta ajiye mata, ta haɗa kan yaran suka yi ɗaki tana ta mita, wannan ya ɗarsawa Maryam zargin akwai wata a ƙasa don haka ta yanke ba za ta sha ba.
Dab da magriba Alhaji ya dawo, ya zauna a falon yana amsa sannun da Maryam take yi masa, ya kalli robar kunun aya ce"Wannan fa?"
Ta ce"Kunun aya ne Inna ta bayar aka kawo gidan, ni kuma ba na sha'awar sha".
Sai ya ɗauka yana cewa"Ni kuwa zan sha".
Ya kafa kai a jarka ya dinga kwankwaɗa, Maryam gabanta yana faɗuwa tana tunanin idan maganin mutuwa ta saka mata a abun nan fa? Kenan ita ce za ta kashe Alhaji ko Sauda da ta zuba?"
Yana gama sha, cikinsa ya fara hautsinawa, ya ce "Ina zuwa".
Ya tashi ya shiga banɗaki, ai kuwa gudawa ta ce salamu alaika, yana fitowa daga bayin ya ƙara jin wani, ya koma, wasa-wasa dai sai ga shi ya rasa sallar magriba.
Ita kuwa Sauda da ta fito ta ga babu kowa a falon sai robar kunun aya sai ta yi tunanin Maryam ɗin ce ta shanye, don haka daɗi kamar ya kashe ta, ta koma ɗaki tana jiran a zo a ce mata Maryam babu lafiya.
Ita kuwa Maryam da ta idar da sallah ta dawo falon ta zauna, duk a zatonta Alhaji yana masallaci, amma ta ji shiru bai dawo ba, ita ma Sauda da yake girkinta ne ta kai abinci dining ta ajiye ta ga bai shigo ba, sai can suka jiyo muryarsa cikin galabaita yana kiransu"Sauda! Maryam! Kuna ina?"
Suka tafi a tare da sauri, musamman Maryam da ta san dama akwai matsala a kunun ayar nan, suna shiga suka same shi kaca-kaca, ɗaki ya ɗume da wari, suka fara salati suna tambayarsa mene ne?
Ya ce"Gudawa ce ta ƙi taƙaita mini, cikin sai ciwo yake".
Maryam ta ce"Ikon Allah! Daga shan kunun aya? Kuma dai ga shi na gidan Inna ne ballantana a zargi wani abu".
Nan take Sauda ta ruɗe ta ce"Kunun aya kuma? To wa ya ce ki ba shi?"
Maryam ta ce"To laifi ne? Na ga dai daga hannun Inna ya fito".
Baƙinciki ya turnuƙe Sauda, tsaki kawai ta yi ta fice daga ɗakin.
Maryam ta shiga gyara shi, ta canza masa kaya amma gudawa ta ƙi tsayawa, ta fita ta kira mai adaidaita sahu, ta ce ya shigo su fito da mara lafiya, mai adaidaita yana ganin shi ya ce ai ba zai yiwu a tafi da shi a haka ba, sai dai a saka masa famfas, ta ba shi kuɗi ya siyi adult famfas ta sake yi masa wanka ta saka masa ta canza masa kaya, sannan ya taimaka suka fita da shi, gabaɗaya ya galabaita, Sauda tana kallo suka fita da shi ko Allah Ya kiyaye ta kasa yi musu saboda takaicin tashin samun nasararta.
Sai da Alhaji ya kwana ya wuni a asibiti, da suka je asibitin sai ya sa ta kira ƙaninsa a waya, shi ya zo ya kwana da shi ita kuma ta koma gida, ba ta yi bacci ba sai da ta gyare ɗakin tsaf ta wanke duka kayan da ya ɓata, washegari Sauda ta je ta duba shi, ta kai masa abinci, amma ya ƙi ci sai na Maryam ya ci, don ya ji haushin yadda jiyan ta nuna ba ta damu da halin da yake ciki ba.
Haka ya sha ƙarin ruwa da magunguna sannan aka sallame shi, tun daga nan Maryam ta tsorata da Sauda, gabaɗaya ma ta daina shan ko ruwan dake cikin firji saboda tsaro.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
19
Kafin cikin ya shiga watan haihuwa sun gama siyayyar komai na kayan jariri, har fargaba take yi kar ta haifi mace, saboda komai na maza yake siya idan ta yi magana ya ce ai ya ji a jikinsa namijin ne ma.
Duk yadda Uwani take son bugar cikin Maryam ta ji wani abu da za ta fake da shi ta zugata ta kasa, Maryam ta rufe sirrin rayuwarta ruf, ta ma rage zuwa gidan, sai ta yi wata ɗaya ba ta je ba, yanzu ma waya Uwanin ta yi mata take yi mata maganar ta san yadda za ta yi ta tatso kuɗi na siyayyar kayan jariri, amma Maryam ta ce mata ta sayi komai, don haya yau Uwanin ta yanke shawarar zuwa gidan ta ga uwar da Maryam ɗin ta gani ta maƙale ta ƙi barin gidan.
Ta yi mata waya ta ce za ta zo yau a nan za ta wuni, wajen sha ɗaya na rana ta ƙaraso gidan, Maryam ta tare ta hannu biyu-biyu tana nuna jin daɗin zuwan nata, a falonta suka zauna ta kawo mata donut da lemo, sannan ta tafi ɗora girki, Uwani ta shige ɗakin gadonta ta fara yi mata buɗe-buɗe, ta ga har saitin kayan rubobin jariran an siya, ga kaya nan fal riyo, ta riƙe baki tana mamaki da tunanin lallai Maryam kuɗi ta gani a gidan nan shiyasa ta maƙale, ai kuwa dole ta samo wani aibun mutumin nan wanda za ta ɗora ta a kai ta san shi ma tara yake bai cika goma ba, ita kuwa sai wanda ya cika goma ne kawai ta dace da ita.
Ta dawo falo ta zauna, abun duniya ya ishe ta, ga Murja bayan auren Maryam ɗin nan mijinta ya sake ta, don ma Allah Ya taimaka sati ɗaya da sakin ya mayar da ita, tana can kwata-kwata ba ta jin daɗin auren, amaryar ta kanainaye gidan kamar ita ce uwar gida, kullum cikin kawo mata ƙara take, ban da ƴan gidan babu wanda ya san ma an yi sakin, ko Maryam ba ta faɗawa ba.
Tana nan zaune da saƙa da warwar Maryam ta shigo ta zauna, Uwani ta ce"Zuwa na yi na ga kayan da kike ta cewa kun siya".
Maryam ta yi murmushi ta ce"Shigo ki gani".
Suka shiga ɗakin, ta nuna mata, Uwani ta shiga ɗaga su tana taɓe baki kafin ta ce"Yanzu nawa ya ba ki da kika rasa me za ki siyo sai wannan kayan?"
Maryam ta ce"Duka shi ya siyo su, kin ga ni ma har ya siyo mini na fitar suna".
Uwani ta taɓe baki ta ce"Kuma ke nan gani kike ya miki gwaninta ko? To wannan kayan dai tsohon yayi ne, irin masu arahar nan da ake kaɗa musu ƙararrawa".
Nan take Maryam ta san hassada take yi mata, ta ce"Haba dai babarmu, ke ce dai ba ƴar zamani ba ba ki san ma abun yayi ba, wannan kayan duka babu tsohon ya yi, kuma wallahi masu tsada ne, wai kin ga yadda yake zumuɗin cikin nan kuwa kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba? Wallahi ba zai taɓa siyo abin da ba shi da kyau ba".
Ta shiga mayar da kayan tana cewa"Ni dai kaya sun yi mini wallahi, kuma na yaba na gode masa".
Uwani ta ce"Ni ma fa ba rainawa na yi ba Maryam, Allah Ya amfana, ya sauke ki lafiya".
Ta amsa da amin, sannan ta ɗakko mata nata kayan,lesuka kala biyu shadda ɗaya da atamfofi biyu, ta ce"Kin ga na fitar sunan, kuma shekaran jiya ya ba ni kuɗin kayan sallah dubu saba'in".
Uwani ta ce"Lallai, wannan mutumin kam da alama shi ba kwa samun matsalar komai".
Maryam ta ce"To ni dai ana cewa kowane aure yana da ƙalubalen shi,ni dai wannan ban ga ta inda nake samun matsala ba, hankalina a kwance".
Uwani ta ce"Da sauƙi dai Maryam, amma matsala ba za a rasa ta ba".
Ta ce"To sai dai ko nan gaba, duk da ba na yiwa kaina fata".
Uwani ta ce"To amma ita abokiyar zaman naki fa? Na ga tana wani ɗaga kai sama".
Maryam ta taɓe baki ta ce"Ina ruwana da ita? Ko hanci take ɗagawa can ta matse mata, ko sannu ba ta haɗa mu, kowa harkar gabansa yake yi, ni wallahi mantawa nake da ita ma sai na fito babban falo zan sha iska na ganta nake tunawa".
Uwani ta ce"Inyeee! Lallai Maryam kin samu duniya, amma fa ki sani, ita kishiya ba a bar rainawa ba ce ballantana har ki dinga mantawa da ita, ba ki san shirinta ba, kuma wallahi namiji da kike gani ba abun yarda ba ne, ƙila a gabanki ne yake nuna yana son ki, ko kuma don cikin jikinki ne, kina haihuwa soyayyar ta koma kan ɗan".
Ta ce"To babarmu dama ai maso uwa ya so ƴaƴanta".
Uwani ta ce"To hakane kuma".
Ta ce"To su kuma dangin nashi fa?"
Maryam ta ce"Su so ni ko kar su so ni ba zai ƙare ni da komai ba, ni yardar mijina nake nema kuma na samu, idan sabgar su ta tashi ina zuwa fisha haka na dawo, ba na ma daɗewa".
Uwani ta ce"Ai kuwa wannan babbar matsala ce, an faɗa miki a haka za a dawwama? Yanzu fa mutumin nan marmarinki yake yi, da kin haihu ɗaya biyu ya gama mararinki matsalolin rayuwa za su ɓarke a tsƙaninku, kin ga kuwa ba ki da madafa tun da ba za ki kai ƙarar shi wajen uwarsa ta saurare ki ba".
Maryam ta ce"Wallahi ko a jikina, ni ba na ma fatan na kai ƙarar shi, ko saɓanin ya zo in sha Allah za mu daidaita a tsakaninmu".
Uwani cikinta ya yi sanyi ta ce"Ai shikenan Maryam Allah Ya ƙara muku zaman lafiya".
Maryam ta zubo wa Uwani lafiyayyen abinci da dafaffiyar kaza ta yi mata kunun aya, ta ci ta gyatse ta ce"Ma sha Allah! Lallai ƴata ta samu gidan hutu, irin wanda nake yi mata fata, to amma da sauran rina a kaba sai dai ta kasa gani".
Maryam murmushi kawai ta yi a ranta ta ce'Kya yi ki gama makirar uwa!'.
Uwani ta ce"Gobe iyanzu kuma bakinmu a rufe ruf, ke za ki iya azumin kuwa?"
Ta ce"Zan gwada, duk da ma fa cikin azumin zan haihu".
Uwani ta ce"Ashe ba za a sha suna ba".
Maryam ta ce"To dama wane suna? Haihuwa ba ta ɗaya ba, ba ta biyu ba".
Uwani ta ce"To ai da na ga wannan mijin so ne za a haifa masa ɗan so".
Ta yi dariya kawai, suka ci gaba da firarsu.
Maryam ta tashi ta ɗakko kuɗi ta shiga ƙirgawa. Uwani ta ce"Dubu saba'in ɗin kayan sallar ne?"
Ta ce"A'a, wannan na sana'ata ne, kin ga na ci gaba da siyar da kaya, shi yake sakawa a mota idan an siya, kuma duk wata yana ba mu dubu biyar biyar, to kin ga a gidan ba ka nemi komai ka rasa ba, shi ne nake tarawa".
Uwani baƙinciki ya rufe ta, da ta tuna duk arziƙin mijin Mardiyya kullum cikin ƙorafi take ba ya bata ko sisi, sai dai ya siyo komai ya ajiye, har ta kai yanzu tana ɗibar abinci tana siyarwa.
Ta ce"Ma sha Allah! Lallai Alhaji Hamza akwai ƙorari".
Ta ba ta dubu ashirin ta ce"Ga wannan ki bawa Baba ya sayi suga".
Ta kawo dubu goma sha biyar ta ba ta ta ce"Ga shi kema kya yi wani abun".
Uwani ta ce"Madallah! An gode Maryam, amma kya kwashe kuɗin ki ba mu? Kin san fa akwai yaji idan kin haihu".
Ta ce"Babu komai, wannan cefanen kawai zan lissafa masa ya kawo kayan yajin, yanzu haka ma akwai barkono rabin buhu a gidan nan, yaji ba zai zama matsala ba".
Uwani dai gwiwa a saluɓe ta koma gida, ta bawa Baba kuɗin, yana ta sakawa Maryam albarka, sosai ya ji daɗin yadda ta yi zamanta a gidan miji wannan karon.
A ranar Alhaji ya kawo kayan azumi, sai sannan Maryam ta san ana yin kunun sadaƙa da ƙosai kullum har a gama azumi, sannan ana yin abinci da yawa a kai masallacin unguwarsu, bayan yanayin girkin gidan da yake canzawa saboda buɗa-baki.
A daren ta kira Uwani ta ji ya ta je gida, sai take ce mata ai Alhajin ya zo ya kawo musu shinkafa da gero da suga, ta yi masa godiya, Maryam kuwa ta ji daɗin hakan, ita sai take jin ma sai yanzu ta san ta yi aure, ta nunawa Alhaji jin daɗinta sosai, ta yi masa godiya.
A ranar girkinta ne, gobe azumi kuma girkin Sauda ne, ta yi musu abun sahur ita da Alhaji, yana ta cewa idan ta ji ba za ta iya ba kar ta cutar da kanta, da safe aka kawo ice da yawa, wata mata dattijuwa ta zo ta hau aiki, can da yamma Maryam ta fito tsakar gidan inda suke yin aikin ita da Sauda, za ta saka hannu ta taya su Sauda ta ce"Kin ga Malama ban gayyace ki ba".
Maryam ta ce"To abu na cikin gida ai dama ba sai kin gayyace ni ba, haƙƙina ne na yi".
Sauda ta ce"Ai dama ni ba ƴar wahalaba ce da zan yi miki aikinki, yau ni ke da girki, alhakina ne na yi abun sadaƙa, me kike ci na baka na zuba? Ki jira gobe za ki sha aiki har ki ture ai".
Daga haka Sauda ta juya suka ci gaba da aiki, Maryam ta taɓe baki ta koma ciki, ta fara haɗa abin da za ta yi buɗa-baki da shi.
Ba ta gane nufin Sauda ba sai washegari, Maryam tana ta jiran wannan matar da ta zo jiya su fara aikin ta ji shiru, ta zo falo ta tarar da Sauda tana kallo, ta ce"Maman Momy wannan matar ba kullum take zuwa ba ne? Na ga lokaci yana ta tafiya ba a fara komai ba".
Sauda ta yi mata wani shegen kallo a ƙasƙance ta ce"Wace mata?"
Ta ce"Matar da na ga kun yi aiki jiya mana".
Ta ce"To matar ƙanwar uwar wani ce da za ki saka ran za ta zo ta yi miki aiki? To mai aikina ce ke ma sai ki nemi taki".
Maryam ta ce"Amma dai da fatan ba uwata kike yunƙurin zagi ba ko?"
Sauda ta ce"Au yunƙuri ne ma?"
Maryam ta ce"Yunƙuri ne mana, ai da sai ki ce ƙanwar uwarki, shi ne na san ba zagin masu tsoro kika yi ba".
Sauda ta miƙe don dama mugun haushinta take ji, gani take wannan turon cikin da take yi da gayya take yi, ta ce"Idan aka zagi uwar taki me za ki yi?"
Maryam ta ce"Ki zaga ki gani mana".
Sauda ta ce"An zage ta ɗin, uwar uwarki!".
Tass! Maryam ta wanke fuskar Sauda da mari babu zato.
Sauda ma ta fesa mata mari, ta cukume ta tana cewa"Ni kika mara?"
Nan dambe ya kaure a tsakaninsu, sai dai Sauda ce kawai mai jibgar Maryam don ko babu tsohon ciki dama ƙarfinsu ba ɗaya ba ne, Maryam cikinta kawai take karewa saboda nan Sauda take hari, yaran sai suka fara kuka, babbar ta ɗauki wayar Saudan ta kira Alhaji ta sanar masa, ƙarshe dai Maryam da cizo da mintsini ta ƙwaci kanta, suka rabu suna ta zage-zage, ta shiga ɗaki ta kwanta tana ta haki, ga cikinta da yake ta watsalniya saboda jijjigar da jikinta ya sha.
Haka Alhaji ya faɗo gidan kamar an jeho shi yana haki, ya samu Sauda a falo, ransa a matuƙar ɓace ya ce"Sauda? Me Maryam ta yi miki? Abun naki har ya kai ki yi faɗa da mai ciki? Yarinyar da ba sa'arki ba".
Ta ce"Ai sanda za ka auro ta ba ka san ba sa'ata ba ce, to ni daidai take da ni tun da kana bata abin da kake ba ni, don haka idan ta kawo mini raini lallasata zan yi wallahi".
Ya ce"Tabɗijan! To ashe kuwa watan barinki gidan nan ya tsara cak!".
Ya wuce ɗakin Maryam a ruɗe yana kiran sunanta.
Tana kwance, tana jin muryarsa ta shiga riƙe cikinta har da dakushe murya tana kuka mai ban tausayi tana "Wayyo cikina".
Ya ƙaraso yana cewa"Innalillahi wa inna ilahi raji'un! Maryam, ya za ki biye mata? Ai sai ta illata ki ta cuce ni".
Ya ɗagota ta koma yaraf yana wani far-far da ido, ya ce"Innalillahi, Maryam, Maryam tashi don Allah!".
Ya cire babbar rigarsa ya ajiye a gefe yana cewa"Masifa ta afko mini"
Ya ɗebo ruwa ya shafa mata a fuska, sai ta sauke ajiyar zuciya kamar sai yanzu ta dawo cikin hayyacinta, ta ce"Wayyo Alhaji za ta kashe ni, za ta kashe maka babanka".
Ya dafa cikin yana cewa"Babu abin da zai samu Babana, ya kike ji?"
Ta ce"Motsinsa ya yi yawa".
Ya ce"To ai da sauƙi tun da har yana motsin, rashin jin motsin shi ne matsala".
Ta ce"Tsoro nake kar na ce ko shure-shuren mutuwa yake yi".
Gabansa ya faɗi, ya ce"Tabbas hakane, tashi mu tafi asibiti, innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".
Ta ce"Ai Alhaji kunu da ƙosan sadaka nake ji".
Ya ce"Kai Maryam, ana ta rai wa yake ta kunu? Tashi mu je". Ya yi maganar yana ɗakko hijjabi ya saka mata.
Ta tashi, sai ta tafi luu kamar za ta faɗi, ya taro ta, ta ce"Ba zan iya takawa ba, wayyo ina ga ajalina ya zo".
Sai kuwa ya ɗauke ya fito, Sauda ta miƙe ta zo gabansu tana cewa"Gaskiya Alhaji kana yi mini ba daidai ba a gidan nan? Ya za ka ɗauke ta a gaban yara? Wane bayanin zan yi musu?"
Ya ce"Wallahi Sauda zan iya make ki idan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 21