ba ki ba ni hanya ba".
Ta ce"To kar dai ka manta azumi kake yi, idan ya karye sai ka yi sittin a jere".
Bai saurareta ba ya wuce ya saka Maryam a mota, ya kama hanyar tafiya asibiti. Aka yi scanning aka tabbatar da lafiyar ɗan, aka saka mata ƙarin ruwa, sannan yake tambayarta abin da ya haɗa su, ta faɗa masa akan ta tambaye ta wacce za ta taya ta aikin abincin sadaƙa ne.
Alhaji ya ce"To Marym ina ke ina aikin abun sadaka? Da me za ki ji? Da azumi ko da tsohon ciki? Kar ma ki soma ita za ta yi shi, kuma matar ai ni na sa ta nemo ta nake biyanta, to a kan me za a ce sai ranar girkinta za ta dinga zuwa?"
Ransa ya ɓaci sosai, har mamaki yake yi, shi bai taɓa zaton kishi haka yake ba. Ya koma gidan ransa a ɓace ya ƙarewa Sauda tass ya ce kuma komai dare yau sai an yi abun sadakar nan idan ba ta yarda ba kuma ta tafi gida sai ya neme ta, ya koma asibitin.
Sauda ta kira Inna tana kuka ta sanar mata, ta ce mata ta yi haƙuri ta yi babu komai.
Sai goma na dare aka sallami Maryam daga asibiti, da asuba ya ce ta bar azumin, ta ce za ta yi, shi ta haɗa mata abun sahur, da safe kuwa wajen ƙarfe goma ta gama aikin gida ta fara naƙuda, ta kira shi ta sanar masa, sai da ya kai ta asibiti sannan ya kira Uwani, ta zo asibitin, kafin azhar Maryam ta haifi ɗanta namiji.
Murna a wajen Alhaji Hamza ba a magana, yana ta kiran waya yana sanarwa, Uwani ta ce a wuce da ita gida, amma ya ce a'a gidanta za ta koma, ita ma Maryam ɗin ta ce mata a'a za ta kula da kanta, sai Uwani ta ce to za ta turo mata Habiba, ƙanwarta ce sai ta dinga yi wa yaron wanka.
Tun kafin su bar asibitin kuwa Habibar ta zo, ta je gidan ta shiga aiki ta ɗora ruwa, tana jin sanda suka dawo gidan bayan magriba, amma Sauda ta ƙule a ɗaki ta kasa fitowa, hassada da baƙinciki yana neman sakata fashewa da kuka, shi kuwa Alhaji bai ma lura da halin da takr ciki ba, sai shige da ficensa yake yi, yana siye-siye kamar ba a taɓa yi masa haihuwa ba.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3
20
Kasancewar cikin azumi ne ba a yi wani taron suna ba, ƴan'uwa dai sun zo an dafawa yara abinci, da yamma duk aka watse,yaro ya ci sunan mahaifinsa Shu'aibu, ana ce masa Baba, raguna biyu Alhaji ya yanka manya, a kansu sai da Sauda ta yi magana ta ce sun fi wanda ya yankawa yaranta girma, shi zuwa yanzu ya gama sarewa da halinta don haka ko kula ta ma bai yi ba, shi dai burinsa ya farantawa Maryam kar ta nemi wani abu ta rasa, washegari aka soya nama aka raba, Sauda ko da wasa ba ta fito taya su aiki ba, ƙamshi ya cika hancinta amma da aka raba aka bata nata kason sai ta ce ba ta so, su ne baƙin nama su haɗa su cinye, har yaran ma ta hana su karɓa, ita kuwa Habiba ta ce ba za a shiga haƙƙinsu ba, ta ba su a ɓoye suka ci.
Tun da aka yi haihuwar Sauda ita take yiwa Alhaji girki, tun da ta ji an ce ana karɓar kwana idan kishiya ta haihu sai ta yi arba'in, satin Maryam biyu da haihuwa Habiba ta tafi, aikin gida ya dawo hannunta ga kula da jaririnta, tana jin takaicin yadda ta bar wa Sauda ranar kwananta, wani kishi ne yake soya mata zuciya, kawai don ba ta so Habiba ta ga zalamarta, amma ita sam ba ta yarda da barwa kishiya ranakun kwana saboda ta haihu ba, idan ta ita ce ko a ranar da ta haihu ne za ta shiga ɗakin mijinta, amma shi ma Alhajin ya yi luƙui ya ƙi kiranta tun da ya san yanzu ba ta da wani amfani a wajensa.
Aranar da Habiba ta tafi Maryamta shirya da daddare ta ɗau wanka ta ɗauki ɗanta, ta shige ɗakin Alhaji tu kafin ya dawo gidan, Sauda dake zaune a falo ta bi ta da kallon mamaki, daga haihuwar Maryam ɗin zuwa yanzu babu laifi ta fara samun kan Alhajin, musamman da kwana ya zama nata ita ɗaya, kuɗin kayan sallah ma da ya bata biyu ta raba, rabi ta sayi magunguna kuma tana ganin aikinsa sosai, a shirinta so take kafin Maryam ta yi arba'in a ce ta gama janye shi gabaɗaya, to sai kuma ta ga ta kwaso tsumman ƙafafunta ta shige ɗakinsa, a fili ta ce"Ban da jaraba uwar me za ta yi masa?"
Yau ɗin fira ta yi masa daɗi da Inna, shiyasa bai dawo gidan ba sai sha ɗaya, ya tarar da Sauda a falo, ya ce"Sauda, na zata ma kin kwanta".
Ta ce"To ba sai idan ina da wajen kwanan ba!".
Ya ce"Kamar ya? Ban gane ba".
Ta ce"To ai na ga gimbiyar taka yau ta karɓi kwana, tana ciki tana jiranka". Ta yi maganar tana taɓe baki
Sai ya yi murmushi ya ce"To ban da abunki kuma don Maryam za ta kwana a ɗakina sai ki ce ba ki da wajen kwana? Ina ɗakinki?"
Ta ce"Au wato ka yarda ta karɓi kwanan kenan? Jego fa take yi, me za ta yi maka?"
Ya ce"To sai da wani abun? Kin ga sai da safe".
Ya wuce ɗakinsa, ta bi shi da kallo zuciyarta na tafasa, a ranta ta ce'Lallai namiji!'.
Shigowarsa ce ta farkar da Maryam, ta yi masa sannu, ya ce"Ashe yau kin tausaya min kin shigo, ashe haka ake matan biyun shikenan don kin haihu sai ki ɗauke ƙafa ki bar ni da kewarki".
Maryam ta ce"Ai dama za ka ce haka, inda kana kewata ai za ka ce na dawo, kawai dai wayancewa kake yi Alhaji, ka ga yanzu ban da abun baka shi ne aka ja maman Momy gefe aka ƙyale ni".
Ya yi ƴar dariya ya ce"Kai mata kenan, ita tana fushi da ni saboda kin karɓi kwana, ke ma kuma ashe fushin kike wai ban neme ki ba, ni dai Allah Ya ga zuciyata na yi kewarki, rashin furtawar ne laifina, to ki yi haƙuri, sannu da zuwa, ina maraba". Suka taɓa fira kafin su yi bacci.
Washegari Sauda ta karɓi kwana, da kwana ya zagayo ranar Maryam da rana tana ɗakinta tana bacci sai ga Kausar ta shigo tana ta rafka sallama, ta farka tana cewa"Mene ne?"
Yarinyar ta ce"Ummanmu ce ta ce wai Lami ta zo, ki fito".
Ta tashi zaune tana cewa"Wace kuma Lami?"
Ta ce"Wacce take aikin abinci".
Maryam ta goya ɗanta ta fito, Sauda dake falo ta yi mata kallon sheƙeƙe ta ce"Na ce a taso ki, ki je kamawa Lami aiki, kin san ba za ta iya ita kaɗai ba".
Maryam ta ce"Na ga da tare kuke yi, wallahi har yanzu jikina babu ƙwari".
Sauda ta ce"Heee! An zo daidai wajen, wato jikinki babu ƙwari, amma kike kwana da mijinki? To wallahi ba ki isa ba, dama darajar karɓar kwanan da na yi kika ci nake yi miki aikin, yanzu kuwa wallahi tun da kika karɓe kwananki ni ma na janye tallafina, don haka ki wuce ki je ji taya ta aiki!".
Maryam ta taɓe baki tana yo mata kallon raini ta ce"Au wato ke da murna kike na bar miki miji? Ai wallahi da na san hakane da ko sati ba za ki yi da shi ba, zan ci gaba da kwana da miji, kuma girki ba zan yi ba, sai dai iya cikina da mijina".
Sauda ta ce"To sai mu gani!".
Maryam ta koma ɗaki ta ɗakko wayarta, ta dawi falo ta tsaya sannan ta kira lambar Alhaji ta saka a hans free, yana ɗagawa ta kwaɓe fuska, murya kamar mai shirin yin kuka ta fara yi wa Alhajin magana ta ce"Alhajina ba jiya na faɗa maka jikina ciwo yake yi mini ba?"
Ya ce"E tabbas an yi haka, ballantana jiyan kuma kin rage mini zafi".
Ta yi wani farr da ido tana kallon Sauda wacce take jin kamar ta tashi ta janyo ta ta zaune ta ta yi ta jibga har sai ta kasa motsi saboda takaici. Ta ce"Alhaji wannan girkin sadakar ba zan iya ba, jikina babu ƙwari, kuma ma ba a son mace tana jego tana aikin wahala fa, ka ga Baba ma bai kamata a saka shi a hayaƙi ba, kuma ga girkin cikin gida ga kula da Babanka, ko ba haka ba ne?" Ta ƙarasa a shagwaɓe
Ya ce"A hakane mana, to je da wane ne ya ce ki fito, ai ki kwanta ki huta kawai, girkin naki ma ina ga kawai zan sa Sauda ta dinga yi da yawa sai ta dinga ɗibar miki, kina jego yaushe za ki na wahala".
Ta ce"To yanzu ya za a yi? Ka ga yau girkina ne, ni ya kamata na taya Lami aikin".
Ya ce"Babu komai, bari na kira Saudan".
Maryam ta kashe wayar tana wani jujjuya ido, ai kuwa sai ga shi ya kira ta ɗin, ta ƙi ɗauka, sai da ya sake kira tana ɗagawa ta ce"Ina jinka!".
Ya ce"Aaa lafiya kuwa Sauda? Na ji muryarki kamar a fusace".
Ta ce"Idanma hakane me zai dame ka? Tafi bayaninka kai tsaye".
Ya ce"Dama maganar abincin sadaƙa ne, na ce tun da Maryam jikinta bai warware ba to ba sai ta saka muku hannu ba, kawai ki ci gaba da kula da komai, idan da dama ma ai bai kamata a ce ta ci gaba da girki ba, da sai ki dinga zuba mata".
A hasale ta ce"Wallahi Alhaji babu wannan damar, don ba bautar kishiya na zo ba, sai ka ce ni ta haifarwa ɗan?"
Ta kashe wayar ta ajiye tana huci, ganin Maryam ta ƙi tafiya ta ce"Wai uban me kike yi tsaye a kaina?"
Maryam ta sosa kai tana dariyar shaƙiyanci ta ce"Ya kuka yi da shi?"
A fusace Sauda ta miƙe ta ce"Ubanki muka yi da shi! Wallahi tallahi kin ji na rantse miki wataran sai na yi miki lahani a gidan nan, a juri zuwa dafi!".
Maryam ta ce"Wataran tulu zai fashe, wannan ai tsohon karin magana ne, kuma ni dai tuluna ba zai taɓa fashewa ba!". Ta juya ta koma ɗakinta ta kwanta.
Haka Sauda ta ci gaba da aikin azumin nan tana baƙincikin zaman da Maryam take a ɗaki. A haka sallah ta zo, ana gobe idi aka kawo naman watanda, da Maryam ta fito aiki Sauda ta ce"Ke kuma me ya fito da ke?"
Ta ce"Na ga Alhaji ya aiko da aiki, shiyasa na ce bari na taya ku".
Ta ce"Ke me jego me ciwon jiki me rainon ɗa ina ke ina aiki? Ko dai don kin ga nama shi ne kika kasa ɓoye zalamarki?"
Maryam ta ce"Wannan abin da kike yi ne yanzu yake nuna taki zalamar".
Ta juya ta koma ciki, Sauda ta bi bayanta da harara tana cewa"Za ki gane kurenki! Shegiya makira".
Maryam sai ta shiga aikin snacks, ta yi cincin ta yi donut. Sai dare suka gama suyar naman, Maryam tana kallo Sauda ta kwasa da yawa ta kai ɗaki ta ɓoye, ta gabanta ma ta wuce tana wani ɗaga kai sama ita ga hamshaƙiya, sannan ta kawowa Alhaji sauran, ya kira Maryam ya raba ya fitarwa da kowa nashi, har Uwani. Sannan ya ce"To goben me za ku dafa? Akwai kaji ma za a yanko".
Sauda ta ce"Tuwo zan yi".
Ya ce"Za ku yi dai,wai ke ce babba amma har yanzu kin ƙi jan Maryam a jiki ku zama abu ɗaya".
Ta ce"Ba zamanta nake yi ba, kuma babu dangin Iya babu na Baba ba wata yarinya da zan ja ajiki, ai ba a goya ɗan kunama".
Alhaji ya ɓata rai ya ce"To ya isa haka, Maryam me za ki dafa?"
Ta ce"Fankasau zan yi Alhaji, kuma idan da hali kajin nan idan an kawo a fitar mini da nawa, saboda na san irin suyar da zan yi, sannan zan yi dambun nama".
Ya washe baki ya ce"Za mu ci suya ashe, to babu damuwa sai a kawo miki naki da ban, idan kin buƙatar wani abun ɓa sai ki faɗa".
Ta ce"Ba na buƙatar komai, na ti cincin da donut ma fa bari na zubo maka".
Sauda ta ce"Amma Alhaji yanzu ka gama maganar janta a jika, to yanzu nan ina haɗin kai yake, a ce girkinta da ban nawa da ban, suyar ma ba za a haɗa a yi tare ba".
Ya ce"To kin ji Maryam, ya za a yi?"
Ta ce"Ni dai haka na tsara".
Ya ce"To ke Sauda saboda a zauna lafiya a raba ɗin kowa ya yi nashi".
Washegari da asuba suka tashi suka fara abincin sallah, Maryam tun dare ta yi kwaɓin fankasau, kafin lokacin tafiya masallaci sun gama tsaf, sai da suka dawo daga masallaci suka yi aikin kajin, Sauda ta gama tsara yadda za ta cusawa Maryam takaicin kajin nan, sai ga shi an raba, Alhajin ne ya kwashi yara suka tafi gidan Inna tare da abincin, ita ma ta yi wa Uwani waya ta aiko aka ɗaukar musu nasu. Haka suka dinga yin baƙi, idan ƴan'uwan shi ne sai ta fito ta sallame su. Ranar uku ga sallah suka shirya tafiya gidan Inna, Maryam ta yi sunasir ta tafi mata da shi, ba ta daɗe a gidan ba ta tafi gidansu, ganin an mayar da ita shara, sun shige ɗaki an barta a falo ita da yara da suke ta tsalle-tsallensu, don haka ta yi musu sallama ta tafi inda take da gata, a gida ta wuni sai magriba ta koma gida.
Watan Baba uku ta fara koya masa zama, yaro mai wayo da kuzari, soyayyarsa da mahifinsa sai ƙaruwa take yi, komai ya rakito ya siyowa yaron nan, ba shi da magana sai ta shi, a hallayarsa ma ba mai fita da yara ba ne, amma ranar Lahadi da ba ya zuwa kasuwa haka zai ɗauki yaron su zauna a ƙofar gida, yana dawowa daga kasuwa shi yakw fara nema, ya ɗauke shi ya yi ta masa wasa, ita kanta Maryam ta gane ya fi son shi a cikin yaran, idan ya yi wani abun a gaban Sauda jikinta har sanyi yake yi, saboda ta kasa sabawa da yadda Alhaji yake nuna son yaron.
Sauda ta ɗauki damuwar duniya ta ɗorawa kanta, har rama take yi, ta tsani ta buɗe ido ta ga Maryam da ɗanta a gidan, yanzu neman hanyar da za ta fitar da su daga gidan kawai take, yawan faɗawa ƙawayenta halin da take ciki ya sa ta samu wacce ta ɗora ta a sabuwar hanya, aka ba ta shawarar dole sai ta nemi taimakon Malamai don ita ma Maryam ɗin ba a zaune take ba, idan ta zauna nan gaba ma wulaƙanta ƴaƴanta zai fara yi, kuma tana kallo yaron nan zai girma ya mallake gidan, don haka dole ta yi maganin yaron nan.
Haka Sauda ta rufe ido saboda neman duniya ta manta da lahirarta, ta je waje aka rakata wajen Malami, ta yi masa bayanin komai, ta ce so take kawai a ɗorawa yaron jinyar da Alhajin zai gaji da kashe kuɗin neman magani, har ya tsane shi shi da uwar, ya ce ta je gida za ta ga aiki, ta dawo gida cike da murna tana jin kamar wani ƙaton dutse ya sauka daga ƙirjinta.
08028966015
21
Ba a yi cikakken sati ba yaro ya fara rashin lafiya, daga zazzaɓi kamar wasa abu yake ta gaba-gaba, sai cikinsa ya kumbura ya yi ta kuka, ga ciwon ƙafa su ma sun kumbura, ana ta yawon asibiti ana ta tasa-tasai da siyan magani a banza, ƙarshe ma sai wasu ƙuraje suka feso masa a duka cikin nasa, idan ka ga yadda hankalin Alhaji yake a tashe sai ka tausaya masa, ballantana Maryam da ta fita hayyacinta, ga shi kamar ana linka mata ƙauna da tausayin yaron a zuciyarta, kullum sai ta ci kuka, ita kanta Uwani tausayin Maryam ɗin take ji, sai ciwon ya lafa an fara murna sai ya yi tsanani fiye da da, yaro da haskensa amma ya zama baƙi sosai kamar ba shi ba, ya rame sai idanu zuru-zuru, sai da ya yi wata biyu yana jinya mai tsanani, Maryam har addu'a take yi ta ce idan mutuwa ce hutu a gareka Allah Ya ɗauki ranka Baba, idan Alhaji yana wajen sai ya kwaɓe ta, saboda kullum cikin saka ran ya warke garas yake, daga ƙarshe Uwani ta ce a kawo shi su tafi wani ɗan ƙauye akwai mai maganin da ake saka ran za a dace, Maryam ta haɗa kaya ta tafi gidan, sun tsara da asuba za su tafi, cikin dare Allah Ya yankewa yaron wahala ya rasu. Tsakanin Maryam da Alhaji ba za ka ce ga wanda ya fi wani shiga damuwa ba, sai take jin kamar shi kaɗai ne ɗanta a duniya babu wasu, da ƙyar ma ta yarda ta koma gidan saboda karɓar gaisuwa, Sauda ta saki jiki ana ta karɓar gaisuwa, zuciyarta fess tun da burinta ya cika, faɗi take a ranta tun da ɗan so ya tafi sai kuma mu ga ƙarshen ƙaryarku.
Sai da aka yi arba'in sannan suka warware suka dawo normal, tun daga nan kuma sai ta fara damuwa da sauran yaran nata Al'amin da Abba, yanzu duk sati sai ta saka an kawo su, su zo ranar Juma'a, Lahadi da yamma sai a mayar da su, tun ba su saba da ita ba har suka saba, da farko Sauda ta so ta dinga takurawa yaran da nuna musu ba gidan ubansu ba ne, sai Alhaji ya taka mata burki, saboda yana so ya ga Maryam tana farinciki kuma ya san yaran suna ɗebe mata kewar Baban.
Wata biyu da rasuwar yaron nan ta ƙara samun ciki, lokacin ita ma Sauda tana da cikin wata biyar, wannan ɗin ma da laulayin ya zo mata sosai, ba ta iya yin komai, ga shi Sauda ta ce ko shara ba za ta yi mata ba don jiki bai fi jiki ba ita ma ba lafiyar gareta ba, ƙarshe sai gida ta koma, sai da ta yi wata ɗaya ta dawo, shi ma dauriya kawai ta yi da ƙarfin hali, uwa-uba kuma kishin ta tafi ta bar wa kishiya miji, don haka ta koma ta ci gaba da harkokinta, tun mutuwar yaron nan jikinta yake a sanyaye, yanzu ba ta fiya kula Sauda ba, sai dai idan ta ga za ta kaita bango, kullum cikin tunanin yadda za ra farantawa mijinta kawai take, cikinta na da wata uku Sauda ta haihu ƴarta mace, tun ranar da aka yi haihuwar nan zuwa bayan suna kullum a tijara take, wai ya nuna mata ya fi son jinin Maryam kuɗin da ya kashe a haihuwar ɗanta ko rabinsa bai kashe a tata haihuwar ba, sannan ita raguna biyu ya yanka ita kuma ya kawo rago da wata tunkiya, shi kam ba ya kula ta, sai dai ta yi ta gama, babu wanda ya ce wa Maryam ga naman suna, ranar da aka yi rabon da Alhaji ya zo ya ce mata an bata naman sunan ta ce an bata saboda a zauna lafiya. Sannan Sauda washegarin ranar da ta haihu ma sai da ta shiga ɗakin Alhaji, ta ce babu batun barwa Maryam kwana tun da ita ma ba ta bar mata nata ba, ai kuwa ita ma Maryam ra shafawa idonta toka ba ta taya ta aikin komai, don ma yaran suna yi mata wanke-wanke da shara, sai ta ji da girki da dafa ruwan wanka.
Tun cikin yana wata biyar da ta fara zuwa awo ta yi scanning aka ce ƴan biyu ne, amɓa ta yi shiru ba ta faɗawa kowa ba, sai da ya shiga wata na tara da ta ƙara yi ya sake nuna hakan sannan ta sanarwa Alhajin, ai kuwa ya dinfa farinciki, musamman jin duka maza ne, a wannan karon ita ya bawa kuɗin ta yo siyayyar kaya, amma ba su kai na haihuwar fari yawa ba, saboda a lokacin kuɗin da ya kashe har Inna sai da ta yi masa faɗa, kuma wani abun duk Sauda ce take yin ƙarin gishiri tana tsara mata.
Wannan haihuwar ta zo mata da sauƙi sosai, don ƙalau ta yi sallar asuba, ba ta koma bacci ba tana kwance dai ta fara naƙudar, da suka je asibiti ko awa ɗaya ba a yi ba ra haifo ƴaƴanta maza guda biyu, har kukan farinciki ta yi, Alhaji kuwa ya rasa inda zai saka su don farinciki, a wannan karon ma Uwani ta nemi ta koma gida amma Alhaji ya ce a'a, shi ya nemo mata wata mata wacce za ta zauna da ita har ta yi arba'in.
A wannan karon an yi shagalin suna sosai, bayan arba'in mai wanka ta tafi ta bar Maryam da ƴaƴanta, cikin ƙanƙanin lokaci ta rame, saboda hidima tana yi mata yawa, ko da wasa Sauda ba ta bari ƴaƴanta su ɗauki yaran, duk sa su suna son ɗaukar tasu, idan za ta yi aiki suka ƙi kwanciya haka za ta goya ɗaya, ta riƙe ɗaya a hannunta tana aikin, har tafita kitchen take da kekensu ta saka su a ciki.
To duka ma ba wannan ne damuwarta ba, sai yadda Alhaji ya rage bata kulawa, sannan wannan yaran tun da suka fara wayo sai ta ga ya rage son su, tana kallon matsalar kamar ƙarama sai ta dinga girma a hankali, sanda yaran suka shekara ɗaya suka fara tafiya sai Sauda ta kafa musu ƙahon zuƙa, babu dama su fito babban falo sai dai Maryam ta jiyo kukansu, ta rasa me yake saka su kuka, sai ta ware rana ɗaya, ta sako su a hanyar zuwa falon, sannan ta laɓe tana leƙen abin da zai faru, sai kuwa ta ga Sauda tana zare musu ido kamar wasu sa'anninta tana cewa"Ku koma! Koma!"
Sai kuma ta taso ta kama kunnuwansu a tare ta murɗe tana cewa"Shegu gayyar tsiya!".
Maryam ta ƙaraso a fusace ta ce"Ƙarya ne wallahi! Ƴaƴanki ne gayyar tsiya! Wallahi Sauda kin ji kunya, ba ki ji daɗin halinki ba, ki rasa wa za ki cuta sai wannan yaran da ba su ji ba, ba su gani ba, ai da ni za ki yi, ni ce sa'ar yinki ba su ba!".
Sauda ta ce"Ke a wa?"
Maryam ta ce"Ni a wacce muke haɗa miji da ke".
Sauda ta ce"Ai ke ba sa'ar yina ba ce, ko uwarki na fi ƙarfinta ballanatana ke".
Maryam ta ce"To ai ban ga alama ba, tun da har kika tsaya kina yi da ƙananun yara, wallahi kin yi asara!".
Ta ce"Ubanki ne ta yi asara, kuma bari mijin da kike taƙama da shi ya dawo, yau zan nuna miki da da yanzu ba ɗaya ba ne, zamaninki ya shuɗe a idanuwansa".
Maryam ta haɗa kan ƴaƴanta suka koma ciki.
Da ya dawo kuwa sai ga shi har ɗakinta, ya dinga yi mata faɗa wai ba ya son rashin kunya Sauda ba sa'arta ba ce, idan ta sake zaginta sai ranta ya ɓaci, haƙuri kawai ta ba shi don a yadda yake a hasale ta san ba zai taɓa fahimtarta ba.
Tun daga wannan ranar Alhaji ya ƙara jan baya sosai da ita, yanzu sai ta daɗe ma ba ta ga dariyarsa ba, sai ya shigo da tsarabar yara a bawa kowa ban da ƴaƴanta, haka dai take ta haƙuri tana dannewa saboda ta riƙe aurenta.
Ba ta gama tsinkewa ba ma sai da rana ɗaya ya zo yake ce mata zai canza mata gida, da mamaki ta ce"Amma Alhaji me yasa?"
Ya ce"Ra'ayina ne, idan kuma ba za ki koma ba sai ki faɗa ba san matakin ɗauka". Ya fice daga ɗakin.
Ta zauna ta ci kuka, ta rasa wa za ta faɗawa damuwarta ko shawara ce ya bata, ta yanke za ta zauna a duk inda ya kaita, saboda ba ta san matakin sa zai ɗauka ba, tabbas ta gaji da auren nan, amma tana ra ƙoƙarin dannewa saboda alƙawarin da ta ɗauka na bawa Uwani kunya da karya mata shirinta.
Cikin satin ya zo da mota aka fara kwashe kayanta, a ranar babu kalar cin mutuncin da ba ta gani ba a wajen Sauda, ta dinga juyi tana faɗar maganganu tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 21