Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lafiya kuwa?" Ya ce"Lafiya ƙalau". Ta ce"Yaran nan fa? A nan za su kwana?" Ya ce"E a nan za su ci gaba da zama, zuwa gobe zan kawo kayansu, ina fatan za ki riƙe mini su". Sauda ta ji farinciki ya kama ta, amma ba ta nuna ba, ta ce"Amma Alhaji me yasa? Ina ita Maryam ɗin za ta je?" Ya ce"Na sake ta". Ta ce"Ikon Allah! To Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi". Ta tashi ta koma falo tana jin ranta fess, ta tsani Maryam ta tsani yaranta, amma ya zama dole ta riƙe su saboda tana fargabar ta ƙi karɓarsu Alhaji ya ce zai yi tunanin dawo da Maryam ko don saboda ƴaƴanta. Cikin shirgin kaya ta lalubo wani tsohon zanin gado, wanda ta ware su ne don ta bayar da su, ta yi shinmfiɗa ko net ba ta ɗaura ba duk da kuwa akwai tsofaffi a cikin kayan, suna zaune a falo suna kallo ta zo tana muzurai kamar wacce take yi da sa'anninta ta ce"Ku tashi! An samu kallo an zauna ana maza ido irin na gado kamar mujiya, ku tashi ku je ku kwanta!". Ta tisa ƙeyarsu suka tafi suka kwanta, ta ce"Daga yau a nan za ku dinga kwana, kuma idan safiya ta yi kuka fito sai na ɓalla shegun ƙafafun nan naku kamar na sauro, ku jira sai na zo na tashe ku, gayyar tsiya kawai!" Ta ƙarasa da tsaki, sannan ta kashe hasken ɗakin ta fice, ai kuwa yara suka fara kuka, a haka har suka yi bacci cikin firgici. Bayan duka yaran sun kwanta Alhaji ya fito falo ya ce da Sauda"Ina su Hasan? Sun kwanta?" Ta ce"E, tun ɗazu suka yi bacci". Ya ce"Amma katifar za ta ishe su kuwa? Ko sai na siyo wata?" Ta ce"To ka manta su maza ne? Ai ba zai yiwu su kwana waje ɗaya da mata ba, su suna ɗakin da uwarsu ta tashi". Ya ji babu daɗi a ransa, ganin an ware yara ƙanana, ya ce"Amma Sauda ai su Hasan ƙananun yara ne, nawa suke da har za a raba ɗaki da su don suna maza?" Ta ce"A wannan zamanin da tarbiyya ta yi ƙaranci dai waɗan nan yaran sun kai a raba ɗaki da su, kuma shi namiji ai ba ya kaɗan, yanzu fa yara maza tun suna shan nono suke sanin wata rayuwar, ni fa ta wani fannin ina godewa Allah da Ya ba ni ƴaƴa mata..." Ya katse ta da faɗin"Haba ya isa haka don Allah! Ke dai kawai kin yi niyyar raba musu ɗakin shi kenan". Sai kuwa ta ɓata rai ta ce"Me kake nufi ne?" Ya ce"To idan ba dai kin ware su ba, ɗakin su Momy ai da girmansa, idan na siyo wata katifar ba sai a ajiye ta daga gefe ba? Ko can gidan nasu ai a ɗaki ɗaya muke kwana, ta yi musu shimfiɗa nan ƙasan gado, to yaushe aka haifi yaran?" Ta ce"A haf! Wato ma ɗaki ɗaya kuke kwana? Hmm, to yanzu yaran nan da suna magana da sun baka mamaki, ka ga ni fa ba zan cakuɗa maza da mata ba, wannan ba tarbiyya ba ce, idan kuma hakan bai yi maka ba to kana iya kwasar su ka kai wani wajen". Ta ƙarasa cike da ɓacin rai Ya ce"A'a shi kenan, hakan ma ya yi, Allah Ya taya ki ruƙo". Ta yi tsaki ta tashi ta shige ɗakinta, a ranar ba ta kwana a ɗakinsa ba, haka ya zo ya dinga buga mata ƙofa ta ƙi buɗewa, ya kira ta a waya har ya gaji, yanzu haka take yi masa, magana kaɗan idan ta mata mata rai to kuwa zai gani a gadonsa, ga shi yanzu wani irin yanayi na buƙatuwa yake tsintar kansa a ciki, abun har tsoro yake ba shi, ya yi iya tunani ya rasa dalilin canzawar yanayinsa, saboda bai taɓa kawowa a ransa Sauda tana zuba masa masifaffun maganin maza a cikin abinci don ta samu magunguna da sirrikan da ta duƙufa siya su dinga tasiri da sauri ba, haka dai ya kwana yana tunani. Ita kuwa Maryam daren ranar bacci bai ga idonta ba, bayan ya tafi da yaran ta sauke girki ta zubo ta zauna don ta ci, dauriya take ta sakawa zuciyarta da cewar wannan ba komai ba ne, amma tausayin yaran ya dakushe wannan juriyar ta kasa, ta kasa cin abincin, ta tashi ta hau haɗa kayanta, sai kuma ta fasa, ta saka a ranta ba za ta tafi ba, sai ta sake gwada wata dabarar ai akwai zaman idda, za ta gwada ta gani ko zai mayar da ita kafin ta gama iddar, don haka ta mayar da kayan ta kwanta tana ta tunanin halin da yaranta suke ciki a daidai lokacin. Washegari da safe yaran ne suka fara fitowa, dukansu sun yi kashi a wando, saboda ba su ga fo ba, ba su ga wanda zai ba su ba, bayan fitsarin kwance da suka yi suka kwana a cikinsa, Sauda tana kitchen ta jiyo kukan ɗaya, ta fito tana cewa"Ku! Uban me ya fito da ku?" Ta daskare ganin kashi a jikinsu su duka biyun, wani ƙululun baƙinciki ya zo ya yi mata tsaye a maƙoshi, ta san dole dai ita ce za ta wanke musu, ta fara tunanin anya zai yiwu kuwa, a ce ita ce za ta ci kashin ƴaƴan kishiya? Lallai da sake wai an bawa mai kaza ƙafa. Ba ta da wata mafitar da ta wuce ta wanke musu, don haka ta wanke cike da ƙyanƙyami, tana yi tana kafa musu ranƙwashi suna kuka, ta wanke wandunan, ta mayar da su ɗakinsu ta dire su a ƙasa, sanyi yana ratsa su saboda babu wando, ta kwashe kayan fitsarin ta kullo ƙofar, ta ci gaba da harkar gabanta. Sai da yaran suka gama karyawa suka tafi makaranta, shi kuma Alhaji yana dab da gama karyawa sannan ya tuna da yaran suna gidan, ya ce"A! Sauda ina yaran na suke?" Ta taɓe baki ta yi tsaki ba ta ce komai ba, saboda ta fara jin haushin yadda yake nuna ya damu da yaran da ba ita ce ta haife su ba. Ya ji babu daɗi a ransa, sai dai yana tsoron yi mata faɗa ta ɗauki fushi da shi, ya ce"Ga ni na yi kowa ya karya ban da su..." Ta katse shi da faɗin"To ai sai ka je ka dafa musu nasu abun karin! Kenan dai saka mini ido za ka fara yi a kan yaranka tun yanzu ko? Kana zargin ba zan iya kula da su ba me yasa ba ka kai su inda kake da tabbacin za a kula da su ba? Ni ba da haihuwa ba ni da jego, da karyawa da wankin kayan fitsari da kashi, tun asuba na je na duba su na ga sun yi kashi na wanke musu na wanke kayan, na dama musu costerd suka sha, na haɗa musu shayi da biredi suka ci, na gyara ɗakin nasu, kuma yanzun ma ga shi ba rage musu wanda muka cin, zuwa anjima idan cikinsu ya faɗa sai na ba su su ci! Amma yanzu cewa kake ka ga kowa ya ci abinci ban da su, to gaskiya idan abun nan ba zai yiwu ba a sake lale!". Jikinsa ya yi sanyi, ya ce"Ki yi haƙuri, ai ban sani ba, ni ban ce ba za ki ba su abinci ba dama na ga ko gilmawarsu ban gani ba". Ta yi tsaki ta ce"Ka je ka ɗebo musu kaya, tun da babu wanda za su saka, kuma inda hali ma a siya musu famfas don gaskiya ba zan iya wannan wanke-wanken kashin da farar safiya ba!". Ya ce"To babu damuwa". Da zai fita yana so ya leƙa ya ga yadda yaran suke amma yana fargabar ta ce ya yi ba daidai ba, don haka ya fice, su kuwa suna zaune suna ƙananun kuka, don sun kasa buɗe ƙofar su fito, ga yunwa suna ji. Kai tsaye gidan Maryam ya tafi, ganin ƙofar babu kwaɗo ya tabbatar masa ba ta tafin ba,ya ƙwanƙwasa ta zo ta buɗe, fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Sannu da zuwa". Bai amsa ba ya shige ciki, a tsakar gida ya tsaya ya ce"Ke me ya hana ki tafiya ne? Ko ba ki ji na ce babu kome ba?" Ta ce"Na ji, amma ka san akwai idda ko? To zaman idda zan yi, idan na gama zan tafi, sannan don Allah ka dawo da yaran nan, idan na gama idda zan tafi sai ka mayar da su". Ya ce"Babu wani zaman idda da za ki yi Malama! Ki haɗa kayanki tass ki bar gidan nan, sannan ki shiga ki kwaso kayan yaran nan kaf ki fito mini da su!". Ta haɗiyi wani yawu mai ɗaci da tauri, ta ce"Don Allah ka bar ni na gama idda a nan, ni zan ɗauki nauyin kaina har na gama". Ya ce"Komai dai aka yi da jaki sai ya ci kara! To zan faɗawa masu gidan na saki gidan, idan ya so sai ki sake biyansu kuɗin haya, ki fito min da kayan yara". Ta shiga ta haɗa kayan nasu ta fito ta miƙa masa, ya fice yana ta ƙananun maganganu. Da ya koma bai ma shiga gidan ba, a ƙofa Sauda ta karɓa ta yi masa a dawo lafiya ya tafi, a nan waje ta ajiye kayan ta shiga gyaran gida, sai da ta gama komai tsaf a tsanake, sannan ta shigar da kayan ta je ta buɗe ɗakin da yaran suke, ta ciro kayan ta saka musu ta koma kitchen ta ɗakko sauran doyar da aka rage ta kawo musu, wannan karon ba ta rufe su ba, don haka da suka gama sun fito neman ruwan sha, ta ba su sun sha, sannan ta ce su koma ɗakin, haka suka yi ta wasansu, lokaci-lokaci kuma tana jiyo kukansu saboda faɗa da suke yi irin na yara. A haka har yara suka dawo daga makaranta, ta yi musu wanka suka ci abinci, suka tafi islamiyya sannan ta zuba ta kaiwa yaran, ta tarar ɗaya ya ƙara yin kashi, ta zage ta zuba masa dundu a baya, tana cewa"Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai ya nema muku ƴar aiki, ni ake nufin na dinga cin kashinku? Allah Ya kiyaye". Haka ta wanke masa tana tsine masa shi da uwarsa, ta tankaɗa ƙeyarsu tsakar gida ta ajiye musu abincin a can, da suka gama cin abincin sai suka hau wasansu, ita kuwa ta kwanta baccinta, wunin ranar dai ba su samu arziƙin wanka ba haka suka dinga dabdalar su a tsakar gida, sai da Alhaji ya kusa dawowa sannan ta canza musu kaya ta shafa musu mai kamar ta yi musu wanka ta dawo da su falo cikin yara. Ita kuwa Maryam yana fita ita ma ta haɗa nata kayan, ta rufe masa gidan ta kama hanya, don ba ta son abin da za a ci mutuncinta, ta lura Alhaji da gaske yake so yake ta wulaƙanta. Uwani tana tsakar gida tana girkin rana sai ga Maryam ta shigo da sallama da akwatuna biyu tana ja, ta ji wani sanyi a ranta, wanda har ta kasa ɓoyewa sai da ta yi murmushi ta ce"Yanzu kin gane karatun kenan". Maryam ta ƙarasa ta shige ɗaki ta zauna tana share hawaye, sai da Uwani ta kammala sannan ta shigo, ta zauna tana cewa"Ai tun jiya nake baza idon ganinki, Maryam na faɗa miki wannan fa ba gidan zama ba ne, ba ki samu mafaka ba, da a ce babu kishiya shi ne za ki ce za ki jure, amma kina da kishiya za ki ɗauki alwashin dole sai kin zauna da miji? Ina yaran?" Ta ce"Ya kai su can gidan nata tun jiya". Muryarta ta fara rawa ta ce"Sakina ya yi, kuma ya ce shi ba zai yi kome ba, ko zaman idda ya hana ni, ga shi ya karɓe yara, dama can Sauda ba ta san yarana ballanatana kuma an kai mata su, kin ga sai ta yi yadda ta so kenan". Ta fashe da kuka. Uwani ta ce"Assha! Ai duk wanda bai ji bari na zai ji woho, da na faɗa miki yaji maslaha ne da samun ƴanci ai ba ki yarda ba, inda a jiyan kin biyo ni mun taho kin yi yaji, ƙila idan an kwana biyu ya ga ba kya nan zuciyarsa ta yi sanyi, idan ma wani laifin kika yi masa ya yafe miki, daga nan sai ki ga ya zo ya nemi sasanci, amma sai kika nuna mini kin fi ni sanin rayuwa, to yanzu ba ga shi ba! Ai sai ki gyara zaman zawarci, su kuwa yara ki manta da su, ki saka a ranki a hannun Allah kika bar su, shi zai kawo musu ɗauki ya tallafi rayuwarsu, ba a kansu kika fara barin yara a wani gidan ba ai, abin da za ki ding tunawa shi ne wataran za ki mutu, za ki tafi ƙabari da yara ne? To tun da har ba mutuwar kika yi ba ai da sauƙi, sai ki rage bacci ki dinga yi musu addu'ar Allah Ya shiga lamarinsu, ke kuma Ya ba ki ikon cinye wannan jarabawar". Maryam ta ce"In sha Allah". Da daddare sai da Sauda ta sa ya fita ya siyo famfas ta sakawa yaran sannan ta yi musu shimfiɗa suka kwanta, da safe da ta duba ta ga sun yi kashi, sai ta kulle su a ɗakin, sun gama karyawa zai tafi kasuwa ya ce"Ina yaran nan?" Ta ce"Yanzu na leƙa su bacci suke yi har yanzu, ka san tun sassafe suka tashi na haɗa musu shayi, shi ne suka koma bacci". Ya ce"Ma sha Allah!". Ta ce"Alhaji ina da magana a kan yaran nan". Ya ce"To me ya faru?" Ta ce"Ka san fa shi rainon ƴan biyu sai an daure, ga kuma sauran yaran nawa, ga hidimar gida, abun ya fara yi mini yawa wallahi". Ya ce"To yanzu ya kike so?" Ta ce"Ka ɗaukar mini ƴar aiki, sai ta dinga taya ni da gyaran gidan, ni kuma na ji da yaran". Ya ce"Amma Sauda..." Ta katse shi da faɗin"Babu wani amma, kawai idan ba za ka ɗauka ba ka faɗa kai tsaye, yaushe rabona da haihuwa? Na manta yadda ake yin raino, yanzu na yarda zan yi duk da irin zaman rainin da muka yi da uwarsu, ban duba wannan ba saboda sun ci albarkacinka, yanzu na ce ka ɗaukar mini ƴar aiki za ka fara amma? Shara da wanke-wanke fa za ta yi, ni kuma na ji da girki da kuma yaran". Ya ce"To shi kenan, ki samo sai a dinga biyanta". Ta yi murmushi tana juya ido ta ce"Ko kai fa, amma da za ka wani cije? A dawo lafiya". Haka ta tsaya a ƙofar gidan tana ta leƙe, har ta samu almajiri ya zo wucewa ta kira shi, ta sa ya shigo, shi ya cirewa yaran famfas, ya wanke musu, ya yi musu wanka har kaya shi ta ba wa ya saka musu, ta ce ya saka musu wata famfas ɗin, ta dafa masa taliya ta cika masa roba ya tafi. A gida ta rufe su ta fita maƙota ta sa a yi mata cigiyar mai aiki, a ranar kuwa aka samo mata wata mata dattijuwa, kai tsaye ta faɗa mata aikin kula da yara za ta yi, za ta dinga zuwa da sassafe sai magriba ta tafi, suka yi cinikin yadda za a dinga biyanta, nan take ta fara aikinta. 08028966015 https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs 26 Haka Maryam ta fara shimfiɗa sabuwar rayuwar zaman gida cike da kewar yaranta, wanda ta rasa hanyar da za ta bi ko labarin halin da suke ciki ta ji, ga zugar da Uwani take yi mata mai ɓata mata rai, faɗi take kawai ta haƙura da auren tun da bai karɓe ta ba, ta zauna ta rungumi sana'a, ita kuwa ta saka a ranta aure yanzu ma ta fara, za ta yi ta yi har zuwa kan mijinta na ƙarshe, wato wanda za ta mutu da aurensa. Zuwa yanzu za a iya cewa rayuwar Hasan da Husaini a gidan mahaifinsu babu yabo babu fallasa, saboda Hanne mai aiki tana kula da yaran sosai, sai dai rashin barin barinsu shiga cikin sauran yaran su yi wasa ne kawai matsala, indai Hanne ta gama aikinta ta bar gidan sai Sauda ta tura su ɗaki ta rufe, ƙaramar ƴarta wacce da kaɗan ta girmi yaran tana son zuwa kusa da su, amma da zarar Sauda ta gani za ta zo ta kore su daga wajen, sun yi kukan Ummansu har sun gaji sun daina, shi kuwa Alhaji yanzu hankalinsa ya kwanta sosai, saboda a gabansa Sauda tana nuna kulawarta a kan yaran, har ma idan ya siyo abu za ta ce ina na su? Hakan yana yi masa daɗi, saboda bai san ba ta ba su ba. Bai taɓa hasashen dawo da Maryam ba, saboda da ya rabu da ita ji ya yi kamar ya cire wata ƙaya wacce ta addabi rayuwarsa, don haka ya ƙara rungumar Sauda suke shimfiɗa sabuwar rayuwa. A watan da Maryam ta gama idda ta samu wani, ba wani babba ba ne can, amma yana da mata da ƴaƴa uku, a zuciyarta ba ta wani ji tana son shi ba, amma ta kai tsaye ta yarda za ta aure shi, kawai saboda a ganinta auren shi ne mafitar rayuwarta ko da kuwa za ta fito, da a ce ta ƙi auruwa gara a ce ta ƙi zaman auren, tass ta samu labarin sau biyu yana ƙara aure yana sakin matan, kuma ana zargin matarsa ce take fitar da su, amma Maryam ta ce ta ji ta gani, duk yadda Uwani ta yi da ita kan ta haƙura da auren ta jira wani wanda ba shi da aibu ya zo, amma ta ƙi, har Baba sai da ya saka baki, ya zaunar da ita ya ce"Maryam! Ba ki fi ni son na ganki a ɗakinki ba, amma ita rayuwar aure ba ƴar gaggawa ba ce, rayuwa ce da mutum take fatan idan ya shiga ya shiga kenan har abada,don haka akwai buƙatar nutsuwa ka duba wanda kake tunanin ba za a samu wata matsala ba, ba saurin auren za ki duba ba, nagartarsa za ki duba,idan da hali ki haƙura da wannan ki jira wani mu gani, sannan ki dinga addu'ar Allah Ya yi miki zaɓin alkhairi, sai nake ganin kamar babu neman zaɓin Allah a lamarinki Maryam". Ta share hawaye ta ce"Baba duk na san da hakan, amma zaman ne ba na so, ina kewar ƴaƴana sosai, kuma na yi alƙawarin duk wata matsalar da na tarar zan jure saboda na zauna a ɗakina, in sha Allah wannan ne na ƙarshe". Baba ya zuba mata ido, ta shiga shirin aure gadan-gadan, ba wata doguwar rana aka saka ba, saboda yana da rufin asiri babu laifi, ta so ya raba musu gida saboda gudun fitina, amma ya ce shi a tsarinsa ba zai rabawa matansa gida ba, saboda haɗin kan ƴaƴansa, ya nuna mata bidiyon gidan, ɗakuna ne ciki da falo guda biyu uwar gidan tana cikin ɗaya, sai ita da za ta tare a ɗayan, sai wasu ɗakunan falle-falle guda biyu, don yara, sai kuma nashi ɗaki ɗaya da banɗaki a ciki, sai kitchen da banɗaki a tsakar gida, sai filin tsakar gida, ta haƙura ta yarda za ta bi tsarinsa. Tun da ta baro gidan Alhaji Haruna ba ta sake saka yaranta a idonta ba, saɓanin sauran da ana kawo mata su duk sati ko da ba kwana za su yi ba, su ma suna yawan tambayarta ina ƙannensu? Sai dai kawai ta ce za su zo, a yanzu da aurenta ya rage sati ɗaya ta ji tana son ganinsu ta san kalar rayuwar da suke ciki kafin auren, don haka ta kira babansu a waya, karo na farko da ta kira shi tun bayan rabuwarsu, sai da ta kira sau uku ya ɗauka, suka gaisa ya ce"Ya aka yi?" Ta ce"Dama ina son ganin yarana ne, idan da hali a kawo mini su su kwana biyu". Ya ce"Sai na yi tunani". Kafin ta yi magana ya katse kiran. Ta jinjina kai da mamaki tare da ɓacin rai, wai ita ce yau don za ta ga ƴaƴan da ta haifa sai ta nemi izini kuma sai an yi tunanin banza da wofi kafin a ba ta dama? Lallai mutuwar aure musiba ce, haka ta wuni tana jiran shigowar kiransa idan ya gama tunanin, amma shiru har dare bai kirata ba. Shi kuwa Alhaji sai dare da ya dawo ya ce da Sauda"Maryam ce ta kira ni ɗazu, wai tana so a kai mata yaran nan su kwana biyu". Ta ce"To ni mene ne nawa a ciki?" Ya ce"Ai shawara nake nema, ya kika gani?" Ta gyara zama ta ce"Maryam ba ta da hujjar cewa tana son ganin yaranta, wannan duk salon ta karɓe su ne daga hannunka, ta damu da su har ta aikata maka abin da ya sa ka sake ta? Kuma tun sanda ta bar gidan ko waiwayensu ba ta sake yi ba, kamar ma an raba ta da kaya, ta je ta kafa zawarci a faifai take cin duniyarta da tsinke, ni a tunanina ba don yara ta kira ka ba, neman shiga kawai take yi, tana neman hanyar da za ta bi ka dawo da ita gidanka, shi ne za ta fake da yara". Ya ce"A haba, ai ita ma ta san ba zai yiwu ba..." Ta katse shi da faɗin"Ka ga ka ma daina cewa haka, babu wani daɗin baki da za ka yi mini, na daɗe da sanin munafurcin maza, ƙila ma ba yau kuka fara wayar ba, to ni ba zan hana ta ɗauki yaranta ba, amma ina da sharaɗi, muddin aka kai mata su to sai dai ta riƙe su har abada, kar a sake a dawo mini da su, don ni ba zan lamunci wannan ba, za su zama ma su gida biyu kenan!". Ya ce"Haba Sauda me yasa kike haka ne? Wani lokacin sai na ga kamar kina kishi da yaran nan fa". Tsaki kawai ta yi ta bar masa ɗakin, kansa kulle, ya san dai ba wani abu ba ne don uwa ta nemi ganin ƴaƴanta, amma saboda ɓacin ran Sauda kawai sai ya yanke ba zai kai mata yaran ba, don haka bai kira ta a waya ba, washe gari wajen goma na safe ta kira shi, sai ya ƙi ɗauka, ta tura masa saƙo ta ce"Alhaji na ji shiru, tunanin ne bai kammala ba?" Ya dawo mata da amsa ya ce"Ba zai yiwu su zo ba, idan kuma kin ce dole sai sun zo to sai dai ki ci gaba da riƙe su a wajenki". Murmushin takaici kawai ta yi, a ranta take jin wannan amsar daga bakin Sauda ta fito, ranta ya ɓaci, a duniya babu wandq ya isa ya hana ta ganin yaran da ta ɗauki cikinsu ta yi naƙudarsu, don haka ta tashi babu shiri babu shawara ta saka hijjabi ta fito, Uwani dake tsakar gida ta ce"Za ki fita kenan". Ta ce"E gidan Alhaji Haruna zan je". Gaban Uwani ya faɗi ta ce"Ke kuwa me zai kai ki?" Ta ce"To babarmu da yarana a gidan har a ce me zai kai ni? Zuwa zan yi na taho da su su ɗan kwana biyu". Uwani ta ce"Ikon Allah! Amma kuma da kanki? Irin wannan ai shi ne zai aiko miki su, ko ke ki aika a ɗakko su, gidan da kika yi rayuwar aure aka rabu babu daɗi me zai kai ki ki ƙara shiga? Ballanatana wannan mara kirkin matar ta na nan". Maryam ta ce"Babu komai, zan je ɗin". Uwani ta ce"To Allah Ya kau da hau!". Ta fice daga gidan, ta hau adaidaita ta kama hanya. Lokacin Sauda tana zaune a falo ta gama gyaran gida, jiya da yau Hanne mai aiki ba ta zo ba, saboda ba ta da lafiya, don haka tun jiyan yaran Maryam ba su samu arziƙin wanka ba, kayan jikinsu sun yi duƙun-duƙun, da ta tashi gyaran ɗaki sai ta kora su tsakar gida, suke ta dabdalarsu a can, su yi faɗansu su yi kuka su shirya, su biyu suke rayuwarsu sai idan Hanne ta ja su jikinta, a daidai wannan lokacin Maryam ta ƙaraso gidan, ta fara ƙwanƙwasa ƙofar, Sauda ta fito tana cewa"Waye?" Maryam ta ce"Baƙuwa

Chapter 16 of 21