da dakanta ba tare da ta kalle shi ba.
Ya ce"Maryam kafin na fito daga wanka ki tabbata kin tafi".
Ganin dai da gaske yake ya sa ta cewa"Zan tafi, amma sai na gama girkin nan".
Ya shiga wanka, ita kuma ta ci gaba da girkinta, a ranta tana tunanin ta ina za ta fara zuwa gida ta ce mijin ya koro ta tun yanzu da auren bai cike sati uku ba? Don haka ta yanke hukuncin gidansu za ta tafi, ta gama girki ta juye a kula ta kawo masa nashi a ƙaramar kula ta ce"Ga naka".
Sai ta ba shi tausayi, duk da ya kore ta amma wai ta yi girki da shi, amma dayake yana son nuna mata kuskuren sai ya haɗe rai ya ce"Ba na ci".
Ta saka hijjabi ta ɗauki kulolin ta fice a gabansa, kai tsaye gidansu ta nufa, ta shiga a sanyaye kamar ba ita ce ta kama tijara ba, aka gaggaisa ta ajiyewa Umma abinci, ba ta faɗa mata dalilin zuwanta ba, ta ce mata dai a nan za ta kwana, hakan ya tabbatar mata ba lafiya ba, ta tambaye ta kuma ta ce mata lafiya ƙalau.
Can bayan isha'i sai ga sallamar Usi, lokacin Maryam tana cikin ɗaki ta idar da sallah, Umma kuma tana tsakar gida tare da sauran ƙannen shi, ya zauna yana cewa"Umma akwai abinci kuwa? Zan ɗan ci na sha magani".
Umma ta ce"Naja zuba masa, amma na ga Maryam ma ta zo mana da abinci bata bar maka naka ba ne?"
Ya ce"Maryam kuma? Yaushe ta zo?"
Umma ta ce"Wai me yake faruwa ne? Ta zo ta ce min a nan za ta kwana, kuma ta ce babu komai, kai kuma kana nuna ba ka san ma ta zo ba, to me kuke ɓoye mini?"
Ya ce"Babu komai, dama ɗan saɓani muka samu".
Ya faɗa a ransa yana jin daɗin rashin faɗa mata dalilin faɗan da Maryam ta yi, saboda ya san yadda Umma take jin zafi da buɗe masa wuta a kan wannan kula matan nasa.
Ta ce"Me ya haɗa ku?"
Ya ce"Shi kenan fa, bari mu wuce kawai".
Ya shiga ɗakin ya ce da Maryam"Sai ki tashi mu tafi ai".
Ta ce"To" Ta tashi suka fito, Umma ta ce"To ka tsaya ka ci abincin".
Ya ce"A'a za ta dafa mini indomi" Saboda ba ya son ma su ƙara mintuna a gidan har Umma ta yi tambayar da Maryam ɗin za ta faɗi gaskiya.
Tafiyar kurame ce ta kai su gidan, suna zuwa ta dafa masa indomin ta kawo masa, sannan ta shiga ba shi haƙuri da alƙawarin ba za ta sake ba, sai ga shi ya haƙura sun kwana lafiya lau.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
32
Washegari da safe ya shiga wanka ta ɗauki wayarsa, ta yi nisa a cikin bincike har ba ta ji fitowarsa ba, yana shigowa ta zabura ta ɓoye wayar a bayanta, ya ɓata rai sosai ya ce"Dalla ba ni wayata! Wai Maryam ni me kike nema da ni? Wannan fa raini ne a ce ba ni da damar da zan ajiye waya sai kin bincika, kuma wahalar da kanki kike yi, don kula ƴan'mata ba zan fasa ba!".
Ta ji maganar kamar saukar guduma a kanta, "Ba za ka fasa ba!?" Ta tambaye shi hawaye yana sakko mata.
Tsaki kawai ya yi ya fara goge jikinsa yana shafa mai, sai gani ya yi ta fashe da kuka, ta fara cewa"Duk wannan abin da nake yi ina yi ne saboda ƙaunarka, kuma tun farko sai da ka yi mini alƙwarain ba za ka ƙara aure ba, ni wallahi ba zan iya zama da kishiya ba, kuma ba zan iya rabuwa da kai ba, don haka dole kai ne za ka canza tsarin rayuwarka".
Ta fice ta bar masa ɗakin ta koma falo ta zauna, ya gama shiryawa ya fice. Tun daga ranar sai ya canza password ɗin wayarsa, Maryam ta daina sanin halin da yake ciki ta fannin wayarsa, sai ta fara tunanin yadda za ta san wainar da yake toyawa, da ƙanwarsa Naja ta haɗa kai, take bata labarin ƴan matansa da ta sani, kuma hakan ba ya ƙara mata komai sai saka kantaa damuwa, amma ta kasa ganewa, ita dai kawai gudun famfalaƙi take yi wa kishiya.
A ƙa'ida sai ƙarfe goma yake tashi daga shago, amma cikin kwana biyun nan ta ga ana sallar isha'i yake dawowa, kuma sai ya yi wanka ya fita, da ta tsare shi da tambayar inda yake zuwa sai ya ce mata gida yake zuwa su tattauna da Umma, ta ce ita ma za ta dinga zuwa suna yi tare, ya ce ai zancen na family ne, sam ba ta yarda ba don haka ta tambayi Na ja ta ce mata ba gida nan yake zuwa ba.
Yau ma kamar kullum ya dawo har sauri yake yi ya yi wanka ya baza uban turare zai fita, Maryam ta ce"Tsakaninka da Allah ina za ka je?"
Ya ce"Kai! Wai sau nawa zan yi miki bayani? Gida nake zuwa wajen Umma".
Ta ce"Wallahi ban yarda ba! Sai dai yau mu tafi tare, Umma ai uwata ce, wane zancen family za a ɓoye mini indai ba zancen ƙarin aurenka kuke tattaunawa ba?"
Tsaki kawai ya yi bai ce komai ba.
Zai fita, ta sha gabansa ta tsaya ta ce"Usi babu inda za ka fita yau, idan kuwa za ka fita to ƙafata ƙafarka".
Ya ce"Ni za ki hana fita?" Sai ya yi wata dariya ta takaici, don ya san mangari ɗaya zai yi mata ta baje a wajen.
Ya ce"To ki biyo ni sai ki ga inda zan je".
Yana rufe baki ta saka hijjabi za ta bi shi ɗin, ya ce"Au kenan ke ba ki san gatse ba, Maryam ƙalau kike kuwa? Kar fa wannan kishin banzan ya fara taɓa ki!".
Ya fice daga gidan, yana fita ta leƙo ta ga inda ya yi, ta rofo gidan ta shiga binsa a hankali, Allah ma Ya sa a ƙafa yake bai hau abun hawa ba, ba su yi wata tafiya mai nisa ba ta ga ya tsaya a ƙofar wani gida, ya ciro waya ya yi kira, babu jimawa kuma sai ga wata yarinya ta fito daga gidan, gaban Maryam ya bada rass, ganin ta tabbata Usman zance yake zuwa, wani kishi ya turnuƙe ta, ta ji kamar ta je ta rufe shi da duka don ita buduruwar ba laifinta ba ne, amma ya za ta yi? Dole a kanta za ta huce, Usman da bai san halin da yake ciki ba, har an gaisa an fara ɗan tattaunawa za a fara baje kolin kalaman yaudara kawai sai ganin Maryam suka yi kamar daga sama, shi ba ma zai ce ga ta inda ta fito ba, tana zuwa ta sheƙawa yarinyar mari, tana huci ta ce"Usman wannan ce Umman ko?"
Yarinyar ta dafe kunci tana kallon shi, da jiran matakin da zai ɗauka, a fusace ya ce"Ba ki da hankali?"
Ta ce"E ba ni da hankali, indai akan wannan tsinannun matan ne wallahi ni mahaukaciya ce, ke kuma indan kika yi kuskuren ci gaba da kula mijina wallahi kaf ahalinku sai kun yi nadama, don tsaf zan iya ƙoneku".
Buduruwar ta ce"Usman! Dama wannan mahaukaciyar ka aura? Ta mare ni kuma kana kallo ba za ka ɗauki mataki ba? To wallahi ba ta mari banza ba".
Ta zo za ta mari Maryam, Maryam ta damƙe hannun suka fara kokowa.
Usman ransa ya yi maƙurar ɓaci ya fizgo Maryam ɗin yana cewa"Maryam! Ki bar nan wajen ko na ba ki mamaki".
Ta ce"Mamaki ai ka gama ba ni, tun da dai har za ka rufe shago ka dinga yi mini ƙaryar kana wajen Umma, ashe wannan ce Umman".
Ya ce"Ki wuce ki koma gida!".
Ta ce"Ka wuce mu tafi gida dai, don wallahi ƙafata ƙafarka!".
Buduruwar ta ce"Yau za ki san na fi ki hauka!" Ta shige cikin gidan da gudu.
Hankalin Usman ya tashi ya ce"Maryam ki bar wajen nan!"
Ta ce"To ka wuce mu je!".
Ya ce"Ni kike cewa na wuce kamar ɗanki?"
Ta ce"Kuma ai ka san ni ma ba ƴarka ba ce ko?"
Tana rufe baki yarinyar ta fito a guje da wata luƙeƙiyar taɓarya a hannunta tana zage-zage, Usman ya yi saurin riƙe taɓaryar yana bata haƙuri da cewar"Haba Zee, don Allah ki yi haƙuri, ita wannan na faɗa miki tana da matsalar kishi, don Allah kar ki biye mata".
Maryam ta ce"Ta ma biye mini ɗin, ni da ita a ga wanda zai ci riba!"
Usman ya ce"Wallahi zan bar ki da ita ku yi".
Ta ce"To da wa ya saka ka a tsakani?"
Ya ce"Ki bar wajen nan!".
Ta ce"Mu bar wajen na dai! Wallahi ba zan tafi na barka ba".
A dole ya saki taɓaryar ya wuce a fusace, ganin ta fara tara masa jama'a, sannan ta bi shi a baya kamar ta tiso ɗanta, yana ɗauke sawunsa tana ɗora nata kuma bakinta ya ƙi mutuwa tana cewa"Yara sai shegen naci, ba su san wahalar da mace ta ci ba kafin ta samu kan mijinta sai su yi ta bibiyarsa!".
Ganin sun kauce hanyar gidan nasu yasa ta ce"Wai ina za mu je ne? Ko idonka ne ya rufe saboda na taɓa maka ƴar gwal?"
Bai juyo ba ya ce"Ke ce idonki ya rufe da kike zaton yau ba kwanan gidanku za ki yi ba".
Ta ci wawan burki tana cewa"Me kake nufi? Wallahi babu inda zan je! Wai me yasa kake son yi mini hukuncin da zuwa gidanmu? Yanzu a nan waye mara gaskiya tsakanin ni da kai? Kai ne tun farko ka yi mini ƙarya, inda ka faɗa mini gaskiya ka ce zance kake zuwa ai ƙila da haka ba ta faru, ni na san matakin da zan ɗauka, amma sai ka yaudare ni".
Bai kula ta ba ya ci gaba da tafiya.
Ta ce"Ni fa idan ba saɓa ni a kafaɗa za ka yi ka kai ni gidan ba wallahi babu inda zan je, gidanka zama daram ƙila ma yau kai ne za ka yi kwanan gidanku!".
Ya yi ƙwafa suka ci gaba da tafiya, mai adaidaita sahu ya sauke wata mata a ƙofar wani gida ta je ta shige tana faɗa masa inda zai kai ta, kafin Usman ya ankara ba ta biye da shi tuni har mai adaidaitan ya yi kwana sun tafi, abun ya ba shi mamaki da ƙarin ɓacin rai, sai kawai ya juya shi ma ya kama hanyar gidan nashi.
Kafin ya ƙarasa ita har ta kulle gidan ta yi wanka, tana zaune tana cin abinci tana ta mita ita kaɗai ya zo ya fara buga gidan, tana ji ta san shi ne, ta tsara shi ne zai kwana a gidan nasu yau, don haka ta ƙi buɗewa, ya kirata a waya ta ƙi ɗagawa, bugun duniyar nan ta ƙi buɗewa har dai ya haƙura ganin maƙota sun fara tambayarsa me yake faruwa? Ya kama hanyar gidan nasu, yana shiga Umma ta ce"Usman ne da daren nan?"
Ya ce"Ni ne Umma".
Ta ce"Ina Maryam ɗin?"
Ya ce"Tana gida lafiya ƙalau".
Ya zauna suka ɗan taɓa fira, kafin ta ce"Ai da ka tafi gida ka bar ƴar mutane ita kaɗai a gida, dare ya yi".
Ya ɗan sosa kai ya ce"Ai Umma ina jin a nan zan kwana".
Ta ce"Ban gane ba, akan me?"
Ya ce"Babu komai".
Ta ce"A'a ai banza ba ta kai zomo kasuwa, me ya haɗa ku da Maryam ɗin?"
Ya ce"Haka kawai ta rufe ƙofar bugun duniya ta ƙi buɗewa, kuma na kira ta a waya ta ƙi ɗagawa".
Umma ta ce"Kai Usman, ba dai haka nan ba, gaskiya dole akwai dalili! Miƙo mini wayata".
Ya miƙa mata, ta kira Maryam ɗin, Maryam tana ganin kiran ta san kwanan zancen, ta ɗaga tana gaida Umma kamar ba ta san komai ba, Umma ta ce"Kina ina?"
Ta ce"Ina gida, bacci ma yana ta fizgata ina daurewa, ina jiran dawowar shi".
Umma ta yi wa Usman mugun kallo, shi kuwa mutuwar tsaye ya yi da yake wayar a hans free take, Umma ta ce"Ya ce ya zo yana ta bugu da kiran wayarki ba ki ɗauka ba, ga shi ya zo wai a nan zai kwana".
Kamar gaske Maryam ta rafka salati ta ce"Yanzu Yaya haka zai yi mini? To ni dai ina wanka na ji bugu tabbas amma ba a daɗe ana bugawa ba ma, kuma kin ga wayata babu wani kiransa".
Umma ta ce"To ga shi dai ya ce ta kira ki babu adadi".
Maryam ta ce"Ni dai ko sau ɗaya kira bai zo mini ba, amma fa ba abun mamaki ba ne, kin san shi da ƴan'mata kwando-kwando ƙila wata Maryam ɗin ya samu ya dinga dokawa kira" Ta ƙarasa maganar da ƴar dariya don son nuna ko da hakan ne ma ita ranta bai ɓaci ba.
Umma ta ce"Zai aikata! Sai ki buɗe gidan ga shi nan zuwa".
Maryam ta ce"To sai ya ƙarasa Umma sai da safe".
Ta kashe wayar tana cewa"To ai ka ji, kai na rasa wajen wa ka gado wannan gajen haƙurin naka, inda bugun kirki ka yi ai har ta fito daga wankan ta buɗe maka, kuma ta bakin nata ne ƙila wata Maryam ɗin ka kira, ashe matan ba daina bibiyarsu ka yi ba!".
Ya ce"Haba Umma kenan har kin yarda da ita, ita da na yi saving lambarta da My Wife".
Ta ce"Matsa can! Wa ya san My Waff ɗin nawa ce a wayarka".
Ya ce"Umma..."
Ta ce"Wuce ka tafi, ka barta ita kaɗai, sai da safe".
Ya fice yana cewa"Shi kenan, sai da safe".
Da ta ƙarasa gidan a buɗe ya tarar da shi, ya tura ya shiga ya rufe ƙofar, yana shigowa Maryam ta fito tana cewa"Sannu da zuwa".
Bai ko kalle ta ba ya wuce ɗaki ya ɗakko towel don yi wanka, yana zuba ruwan a bokiti ta zo ta ce"Kawo na zuba na kai maka".
Ya ce"Ke matsa dalla!".
Ta matsa tana sosa kai, ya shiga ta koma kitchen ta ɗakko masa abincinsa, da ya fito daga wankan ta ji shiru bai shigo falon ba, sai ta ɗauki abincin ta bi shi ɗaki ta ga har ya kwanta, ta ce"Ga abinci fa, ko a nan za ka ci?"
Ya yi banza da ita, ta rufo ƙofar ɗakin ta hau gadon ta kwanta, murya a sanyaye ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, na san na yi maka laifi, amma wallahi na kasa jurewa ne".
Ya ce"Nan gaba za ki jure ne".
Ya sakko daga gadon ya fice daga ɗakin, jin shiru sai ta bi shi, ta ga ya kwanta a kujera, ta ce"A nan za mu kwana?"
Ya yi tsaki bai ce komai ba.
Ta zo ta raɓa bayanshi ta kwanta, takaici ya hana shi magana, a haka har bacci ya ɗauke su, ƙarar faɗowarta daga kujerar ne ya farkar da shi, ya ce"Wannan wace irin masifa ce wai? Dole sai mun tare?"
Tana matsa inda ta bugu ta ce"E wallahi dole ne, ka matsa min na kwanta".
Ya yi tsaki ya tashi ya koma ɗakin gadon ta bi bayansa, suka kwana lafiya ƙalau.
Tun daga ranar Maryam ta addabi kanta ta addabi Usman akan kula mata, ta yi mita ta y masifa akan sakawa wayarsa password har ta gaji ta daina tun da ta ga ba zai cire ba, duk da haka kullum da ita yake shiga banɗaki, babu damar ya yi waya a gabanta sai ta tashi hankalinta ta ce da mace yake waya, idan ya ce ya yi ɗin, ta saka kuka har daga baya ta ba shi tausayi, haka za ta tisa shi a gaba da rashin kirki tana faɗa masa maganganu, sai daga baya kuma ta fara kuka tana ba shi haƙuri, babu dama ta ga ya dawo daga shago da wuri zai fita sai ta bi bayansa, sai dai idan ta ga majalisa ya je sai ta koma, sau uku yana kamata da irin hakan, don haka yanzu tafiya ma idan yana yi waiwaye yake gabaɗaya ba shi da nutsuwa.
Ana haka ta samu ciki mai masifar laulayi, irin cikinta na farko wanda take jin ta tsani mijin ta zo kusa da ita, ƙarshe dai falo ta koma da kwana, hakan ta bawa Usman lasisin sakewa da yin yawa da ƴan mata, sau ɗaya da ta fito tsakar dare za ta ɗauki bargo a ɗakin gadon ta ji shi yana waya, ranar ya ga rijara, ta dinga kuka tana zagin wacce yake wayar da ita, har ta ba shi tausayi ga ƙaramin ciki, zuwa yanzu ya fahimci abun a jininta yake don haka ta daina ba shi haushi sai tausayi da mamaki.
Ya zaunar da ita cikin kwantar da hankali ya ce"Don Allah Maryam ki yi haƙuri, na ji kin kama ni ina waya ban kyauta miki ba, amma na daina daga yau in sha Allah, ciki ne a jikinki ki daina tada hankalinki haka, ni Usman naki ne ni kaɗai fa, babu wacce zan sake aura in sha Allah!".
Da wannan kalaman ya yayyafawa ƙurar ruwan sanyi, daga ranar ta dawo da kwana a ɗakin, sai ta dinga shimfiɗa a ƙasan gadon tana kwanciya.
Cikinta yana da wata biyu watarana ta je asibiti duba yayarta Murja, an kwantar da ita ba ta da lafiya, mai adaidaita ya sauke ta a bakin asibitin ta zo shiga suka ci karo da wata buduruwa ta bangajeta har kular abincin hannunta ta faɗi ƙasa.
Ita Maryam duk a zatonta a rashin sani yarinyar ta bangaje ta, ta ce"Subhanallah!".
Da mamkinta sai ji ta yi yarinyar ta ce"Banza jaka!".
Zuciyar Maryam ta doka da ƙarfi ta zaro ido ta ce"Jaka!".
Yarinyar ta ce"An faɗa miki ɗin, wai ke ga ki isasshiya kin hana mijinki aure ko? To wallahi ko da rarrafe sai na shigo gidan nan, sai na zama matar Usi".
Ai Maryam ji ta yi gabaɗaya jikinta ya hau tsuma kamar an kaɗa mata gangi, ta hau karkarwa ta cakumo ta, aka yi sa'a ita ma yarinyar ba daga nan ba wajen masifa, suka fara casuwa a titi, maza suna ta hayya-hayya, ƙarshe dai sai mata ƴan talla a wajen ne suka raba su, Maryam tana ta kuka ba na dukan da yarinyar ta yi mata ba, sai na zafin kishin da yake azabtar da zuciyarta, ana cikin rabon wata ƴar unguwarsu ta zo, suka shiga asibitin tare take faɗawa Maryam ai ta san har gidansu yarinyar, ai kuwa Maryam ta damƙi hannunta ta ce ta zo ta rakata, kular ma a nan ta bar ta, kai tsaye police station ta tafi, ta ce ta zo kawo ƙarar wata ne, ta ci mutuncinta, ta ce mata masiƙa kuma ta kama ta da dambe saboda tana son mijinta, aka nemi lambar mijin nata ta basu, aka kira shi, sannan aka tafi da wannan ƴar unguwar tasu ta nuna gidan su yarinyar, aka taho da ita.
Usman yana shago aka kira shi aka ce daga police staion ne ana nemansa matarsa tana wajen, hankali tashe ya rufe shago ya tafi, da ya je ya ji abin da ya faru ransa ya ɓaci sosai, ya ce"Wannan case ɗin na gida ne, don Allah a kashe kawai, ke Maryam tashi mu tafi".
Maryam ta ce"Ni ce mai ƙara ba kai ba, babu abin da zai sa a kashe case wallahi sai an bi mini hakkina".
Kallonta kawai yake yi da mamaki, gabaɗaya ta birkice kamar mai taɓin hankali, sai da aka kawo yarinyar ya ga ya gane ta, kuma shi ba ma wani sonta yake ba kawai dai yana ɗan kula ta ne, sau tari ma ita ce take kiransa, da ƙyar dai aka kashe case ɗin aka ce yarinyar ta bawa Maryam haƙuri, kuma aka yi musu tsakani.
Dubiyar da ba ta yi ba kenan, kular ma ba ta san inda take ba, ya saka ta a gaba suka tafi gida, don takaici ya ma kasa cewa komai, da ya tabbatar ta shiga gida ya koma shagonsa, ita kuwa har lokacin jikinta bai daina tsuma ba, ga wani ciwo da mararta ta fara yi, tun tana daurewa har ta gane akwai matsala, kafin azhar cikin jikinta ya zube.
08028966015
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 21