Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma dai?" Ta ce"Wallahi duk na kasa bacci saboda kewarka, don Allah ka ɗan taya ni fira ta online kafin na samu baccin ya zo". Ya ce"To shikenan babu damuwa". Ya kunna data kuwa suna ta chart, sai da sha biyu ta wuce sannan ya ajiye wayar ya yi bacci, yanzu sai ya yi fiye da sati bai nemi Maryam ba, saɓanin da har jira da zumuɗin ranar kwananta yake yi. Sai da safe ta kwashe abincin, shi ta ɗumama suka ci, shi kuma ta dafa masa shayi ya haɗa da biredi. Ya gama shiryawa zai fita ta ce"Alhaji ina da magana". Ya ce"To ina jinki". Ta ce"Kayan abincin da ka kawo babu wasu abubuwan". Ya ce"Kamar me kenan?" Ta ce"Irin su wake, ƙwai, fulawa, indomi da sauransu, sannan ka ga yanzu ba ni da firji, ba zai yiwu na ajiye nama da kayan miya masu yawa ba, ko da firjin ma ka ga nan babu sola, kuma ba sosai ake kawo wuta ba, idan da hali ya kamata a saka mana sola, sannan gas ɗin ma ka ga sai wannan ƙaramin nawa na ɗakko, akwai buƙatar a yi masa rifilin, sannan..." "Ke dakata haka!" Ya katse maganar da ta kwaso. Ta zuba ido tana kallonsa, ya ce"Wannan lissafin fa ya yi yawa, akwai komai na abinci a can gidan ai, tun da na riga na siya, Sauda ta ce duk abin da kike buƙata ki je ki ɗiba mana, shi kuma gas zan sa a zubo miki, firjin ma za a siya, sauran abubuwan duk ki yi mini list ta massage zan duba". Har ya tashi zai tafi, ta ce"Akwai sauran magana". Cikin ƙosawa da ita ya ce"Ina ji". Ta ce"A gaskiya abin da ka yi mini jiya ban ji daɗinsa ba". Ya ce"To me na yi miki?" Ta ce"Gaskiya kar ka sake cin abincin wata a ranar kwanana, idan kuwa ka san ba za ka ci ba to ka sanar da ni tun wuri don kar na girka da kai, sannan ni ba zan ce kar ka yi waya da matarka ba, amma don Allah idan za ku yi ka dinga zuwa daga falo haka ko tsakar gida, saboda hakan ba ya yi mini daɗi, sannan ni da yaranka muna buƙatar zama da kai mu yi fira, kuma da take wani zancen kewa ai ni ma ban ce ba na kewar taka ba, amma ban yi mata haka a ranar girkinta ba, to ni ma kar ta yi mini". Ya ce"Kin gama ko da saura?" Ta ce"Zan dai dakata a nan, na ga yadda ka ɗauki abun, don kai kanka ka sani ba iya matsalar ba kenan". Ya ce"To Allah Ya kyauta". Ya fice ya tafi, ta raka shi zaure tana yi masa a dawo lafiya. Gidan Sauda ya tafi don a can ma yake barin motarsa tun da gidan Maryam ɗin babu waje, yana shiga ta tare shi da abun karyawa, ya ce ya ci ya ƙoshi, cikin son sanin halin da suke ciki da Maryam ta ce"Ni Alhaji sai nake ganin kamar ranka a ɓace, ko har yanzu maganar tozarcin siyan abincin ne bai ƙare ba? Shi fa abin da ya faru ya riga ya faru, cuta ta riga ta cuce mu ta ɓata mana suna sai dai kawai a yi haƙuri, amma..." Ya ɗaga mata hannu ya ce"Don Allah Ya isa haka Sauda, ki daina tada zancen, ai ya wuce". Ta ce"Wannan babban abun ne ya wuce?" Ya ce"Kin ga ba wannan ba, yanzu kema idan akwai abubuwan da kike buƙata sai ki sanar na haɗa na siyo muku, kamar na aikin gida haka". Ta ce"Ita Maryam ɗin me za ka siyo mata?" Ya ce"Kin san ba ta da firji, kuma gas ɗin ma ƙarami ne, zan siya mata wanda ya fi shi". Sauda ta ce"Hakane ashe fa daga gidansu daɓa ba a haɗo ta da komai ba". Ya ce"Wannan ni ne na ce ta bar shi ai". Ta ce"Amma ni sai nake ganin tun da ga kayan abinci a nan da ta zo ta kwashi abin da take buƙata, kar ka kashe kuɗi da yawa". Ya ce"To zan faɗa mata ɗin sai ta zo ta ɗiba". Yana fita ya kira Maryam ya ce"Ki zo nan gidan ki ɗauki abubuwan da ba ko da shi, su fulawa da sauransu". Ta ce"Gaskiya Alhaji ba zai yiwu ba". Da mamaki ya ce"Ba zai yiwu ba?" Ta ce"E, saboda na san ita ce ta kitsa maka hakan, ya mun gama magana kuma daga zuwa gidanta za ka canza zance?" Ya ce"Ni kike faɗawa ba zai yiwu ba?" Sai kawai ta kashe wayar, don ba ta da lokacin sa'insa da shi. 08028966015 https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs 24 Alhaji ya tafi aiki ransa a ɓace, a al'adarsa shi ba mutum ba ne mai zafin hali, ba shi da saurin fushi, Sauda ta sha faɗa masa maganganu masu zafi son ranta yana ƙyale ta, da anjima ma zai manta, amma ya rasa me yasa zuciyarsa take yi masa zafi a kan Maryam, abu ƙalilan za ta yi masa ransa ya yi ƙololuwar ɓaci. Wajen azhar ya kira Sauda a waya ya ce"Yarinyar nan ta zo ta kwashi kayan abincin kuwa?" Sauda ta taɓe baki ta ce"Wallahi ba ta zo ba, ko na je na kai mata?" Ya ce"A haba! Ai ba hauka ake yi ba, shi kenan ki rabu da ita, zan yi maganinta". Ya kashe wayar, Sauda ta ce"Kai kake haukan ai da kake tunanin da gaske zan kai mata har kake dakatar da ni". Yana gama waya da Sauda ya kira Maryam, sun gama cin abinci kenan tana yi wa yaran wanka, ta ɗauka da sallama, ko amsawa bai yi ba ya ce"Kin je kin yi abin da na saka ki?" Kamar ba ta fahimci inda maganarsa ta dosa ba ta ce"Me ka saka ni?" Ya ce"Kar ki raina mini hankali mana, abubuwan da na ce ki je gidan Sauda ki ɗauka". Maryam ta yi harara tana turo baki kamar yana kallonta kafib ta ce"Ban je ba". Ya ce"To akan me?" Ta ce"Ai dama ban ce maka zan je ba, Alhaji abin da zai yiwu fa shi ake yi". Ya ce"Kina so ki nuna mini dai ban isa da ke ba ko?" Ta ce"Wannan fahimtarka ce, ni har raina ba da wata manufa na yi hakan ba, abinci ne idan ka yi niyya ka siya mana, amma wallahi ka ji na rantse ba zan je gidan kishiya karɓar abinci ba". A fusace ya ce"Ita ce ta siya ko ni!?" Ta ce"Kai ka siya, amma ai matsayina da nata ɗaya ne a wajenka, don me ni ba za ka siyo mini ba, ko kuma ka je ka ɗibo da kanka ka kawo mini?" Ya ce"Maryam! Ni kike titsewa da maganganun banza haka?" Ta ce"Ka ga ni kawai ka bar shi, na haƙura, wanda ka kawo ɗin an gode Allah Ya amfana, amma wallahi ba zan je gidan kishiya karɓar abinci ba". Ya ce"Na ji ba za ki je ba, amma za ki iya tafiya gidanku ko?" Gabanta ya faɗi da jin kalmar gidanku, wani sashe na zuciyarta kuma yana faɗa mata ta tafin mana, ai miji goma ba uba goma ba ne, ta dake ta ce"Ban gane tafiya gidanmu ba". Ya ce"Idan har kika yarda na dawo gidan nan ba ki yi yadda na tsara ba, to wallahi a gidanku za ki kwana". Bai jira cewarta ba ya kashe wayar, ta je ta ƙarasawa yara wanka, ita ma ta yi, ta zauna tana tunanin mafita, duk da yadda take ganin tana gudun sake zawarci amma ba ta ji a zuciyarta za ta iya zuwa gidan Sauda ba, don haka ta yi zamanta tana jiran dawowar tashi ta ga abin da zai faru. Bayan la'asar Uwani ta dawo daga kasuwa ta biya ta gidan Maryam, saboda ta kwana biyu ba ta je ba, haka ita ma Maryam ɗin ba ta je ba, ta ƙwanƙwasa ƙofar Sauda ta ce"Waye?" Uwani ta ce"Ni ce Uwani, wajen Maryam na zo". Sauda ta fito ta buɗe, Uwani tana shirin kutsa kai ciki, ta tare hanya tana cewa"A'a dakata a nan dai, wajen wa kika zo?" Ta yi tambayar tana yamutse fuska kamar ba ta taɓa ganinta ba. Ran Uwani ya ɓaci ta ce"Wajen matar gidan na zo, Maryam uwar ƴan biyu duka maza". Ta yi maganar da manufa biyu don gorantawa Saudan, tun da a bayyane yake kowa ya gane ta yi baƙincikin haihuwar maza da Maryam take yi. Ai kuwa maganar ta daki zuciyar Sauda, ta ce"Ai babu wata matar gidan nan bayan ni, a da kika san ƴarki a nan, yanzu kuwa ya gaji ya kwashe ta ya mayar gefe inda ya fi dacewa da ita, dama can ƙulle-ƙullen da kuka yi masa ne ya kau da hankalinsa, har kuke tunanin kun samu wajen kasa hajarku, to yanzu lokaci ya yi da ungulu za ta koma gidant na tsamiya, can ki je ki yi cigiya ki nemi kejin da ƴarki take, yanzu gidan nan ya fi ƙarfinta, dama can karambanin akuya ne yasa ta shiga ramin kura". Ta zabgawa Uwani wata muguwar harara kamar idanunta za su faɗo ƙasa, sannan ta banke ƙofar ta rufe. Ta bar Uwani tsaye sake da baki, ta ma kasa cewa komai saboda al'ajabi, sannan ta ƙi yarda da cewar Maryam ba ta cikin gidan, ta nemi waje ta zauna a ƙofar gidan, tana cikin saƙa da warwara ta ga wasu ƴan mata sun zo wucewa ta taso ta miƙa musu wayarta tana cewa"Don Allah ƴan'mata ku duba mini wayar nan za ku ga lambar da aka saka Maryamata ku kira mini". Suka karɓa kuwa suka kira suka ba ta, suka yi gaba. Maryam tana gani kiran ya shigo ta ƙi ɗagawa, saboda ba ta son a ƙara mata wata damuwar da take ciki, tana buƙatar shawara a daidai wannan lokacin ta rasa wa za ta shawarta, zuciyarta shawara ɗaya take bata shi ne kar ta je gidan Saudan nan, saboda kamar zubarwa da kanta daraja da ƙima ne, ta kuma siyawa kanta wulaƙanci, tozarci, har ma da gori a wajen kishiya, don haka take zaune tana jiran dawowarsa, amma duka jikinta a sanyaye yake. Sai da ta ga kiran yana ta shigowa babu ƙaƙƙautawa sannan ta ɗauka da sallama, ko gaisawa ba su yi ba Uwani ta ce"Maryam kina ina?" Ta ce"Ina gida". Uwani ta ce"Wane gidan?" Maryam cikin ƙosawa ta ce"Haba babarmu gidana mana". Uwani ta ce"Yanzu dama kina cikin gidan wannan sangamar kishiyar taki ta fito ta yi mini zagin ƙare dangi? To fito ki shiga da ni". Maryam ta haɗiyi yawun baƙinciki da takaici ta ce"To ke me ya kaiki? Za ki zo ai sai ki kira ni ki faɗa mini". Uwani cikin ƙosawa ta ce"Ni ki zo ki shigar da ni ma yi maganar daga baya". Maryam ta ce"Na fa tashi daga wannan gidan". Uwani ta ce"Au kenan da dai da gaske ne? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu kina ina?" Maryam ta ce"Ki tsaya a nan ɗin bari na zo na tafi da ke". Ta kashe wayar, ta ja yaranta suka tafi, a ƙofar gidan ta samu Uwani, suka taho tare, tana waiwayen gidan a ranta tana jin kamar ta shiga ta karɓi kayan tun da dai ta zo gar ƙofar gidan, amma zuciya ta hana ta, duk sababin da Uwani take yi a hanya ba ta ce mata ƙala ba, don haka ita ma ta haƙura ta yi shiru har suka ƙarasa, tana ganin ƙaramin gidan da Maryam ta fara ƙoƙarin buɗewa ta dafe ƙirji ta ce"Yau ga muguwar shekara! Maryam me zan gani haka? Kar dai ki ce mini wannan ne gidan naki?" Maryam ba ta kula ta ba ta shige ciki, sai da Uwani ta yi jim! Sannan ta shiga, a ƙasan ranta wani farinciki ne yake tasowa yana game zuciyarta, amma a idonta ba za ka taɓa ganewa ba, za ta fi yi maka kama da wacce take cikin firgici da tashin hankali, haɗi da tsoron faruwar wani abu. Kafin ta shigo har Maryam ta cire hijjabi ta zauna, Uwani ta shiga ɗakin tana ƙare masa kallo, ba ta bi ta kan gaisuwar da Maryam ɗin take yi mata ba ta ce"Maryam me zan gani haka? Kar dai abin da kishiyarki ta faɗa gaskiya ne!". Maryam ta ce"Don Allah ki zauna babarmu, wannan duka ba komai ba ne ba fa, ita dama rayuwar aure ta gaji haka, yau fari gobe baƙi". Uwani ta rafka salati har da tafa hannu ta ce"Ba komai ba ne? Maryam anya ke ce kuwa? Kina cikin hayyacinki ko dai kishiya ta haukata mini ke? Yau ke ce kike faɗin wannan maganar da bakinki, ke kuwa uwar me Alhaji Haruna yake ba ki da har kike zaton idan kin fita daga gidansa taki ta zo ƙarshe ba za ki samu wanda ya fi shi ba? Yau ke aka yi wa wannan cin zarafin na ajin ƙarshe, kishiya ta kore ki daga gidanki a mayar da ke wannan akurkin kuma ki zauna?" Maryam ta ce"Babarmu don Allah ki yi mini fatan alkhairi, Manzon Allah ma ya ce ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru". Uwani ta ce"To dama wannan ai sai dai shirun, don duk wasu kalamai da zan yi a kan wannan matsiyacin zaman auren naki to ban amayar da abin da yake zuciyata ba". Maryam ta ce"Ni fa na karɓi hakan a matsayin ƙaddara, wannan gidan kamar gidan Nazifi yake, to a auren fari ma ina amarya na zauna a gida kamar wannan mene ne yanzu don na zauna a nan? Ni fa yanzu zaman aure zan yi domin na gaji da lissafa mini aure da ake yi, ni kenan na yi ta aure-aure wannan ya kwasa ya barwa wannan? Ina ta raba ƴaƴa a gidaje, shi kena ni ba zan buɗe ido na ga familyna a haɗe a kusa da ni ba, yarana sun yi nesa da ni ban san wace wainar suke toyawa ba,ban san ainahin inda rayuwarsu da ta dosa ba? A'a gaskiya abun ya isa haka". Uwani ta ce"Maryam ba haka ba ne, kin san ita rayuwa kowa da kalar ƙaddararsa...." Ta katse ta da faɗin"A'a babarmu, wannan fa ba ƙaddarata ba ce, wane sulhu ne Nazifi bai zo da shi ba? Amma na ƙi, kika zuga ni kika ce kar na koma, tun da dai Alhaji bai bar ni da yunwa ba ni zan haƙura na zauna na kau da kai, saboda rayuwar waɗan nan yaran, don haka ki yi mini fatan alkhairi, a matsayinki na babata". Kalaman Uwani waɗanda suka canza rayuwarta, suka shiga dawo mata kamar yanzu take furtawa ƙawayen nan nata su, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarta, ta fara kuka sosai ta ce"Babarmu ke kaɗai nake yi wa kallon mahaifiya, ke uwata ce, ina sonki ina ƙaunarki, na san ke ma kina sona, domin ni da duniya mun shaida kin yi mini ruƙon da ba kowace matar uba ba ce za ta yi, don Allah ki cike ladanki, kin kusa kaiwa ajin ƙarshe fa kar ki yi abin da za ki dawo ajin baya, don Allah ki zame mini uwa wacce zan yi alfahari da ita har a lahira, ki taimake ni na gyara aurena na zauna a ɗakina kamar kowace mace, yanzu fa ni uwa ce ba yarinya ba, ƴaƴana huɗu amma kin ga yanzu biyu ne a gabana, mutuwar auren nan daidai take da rabuwa da biyun ma, kowa yana zaune da ƴaƴansa sai ni kaɗai?" Kuka ya ci ƙarfinta sosai, ta kifa kanta a cinyar Uwanin, duk da ta san maƙiyiyarta ce ta wani ɓangaren, amma ji take a ranta ita ma gatanta ce, sam ba ta so ta yi mata wata maganar da za ta sa ta gane cewar ta san takunta ba, amma a yau ta gaza yin hakan, tana fatan ta tausaya mata ta janye ƙudurinta a kanta, ko don ta koma ga Allah babu hakkin kowa a kanta, don ko babu komai ita ma uwa ce a gare ta, ta riƙe ta ta yi mata tarbiyya, sannan ba ta nuna bambanci a tsakaninta da ƴaƴan da ta haifa. Jikin Uwani ya yi mugun sanyi, sannan zuciyarta tana bugu, tare da fargabar kar dai Maryam ɗin ta gano manufarta a kanta, ta dafa bayanta ta ce"Maryam! Kina zargina ne? Me ya kawo duka wannan maganar?" Maryam ta tashi daga jikinta tana share hawaye ta ce"Ba na zarginki, a kan me Ƴa za ta zargi uwa? Ba ki taɓa yi mini wani abu wanda zai sa na ji dama ba ke ce kika riƙe ni ba, kawai na kiɗime ne, ina neman tallafinki a matsayinki na uwata, ki taimake ni na riƙe aurena". Uwani ta sauke ajiyar zuciya, tana ji a ranta lokaci ya yi da ya kamata ta ƙyale Maryam ta daina yi mata fuska biyu, sai dai ƙasan zuciyarta wutar ɗaukar fansa ce take ƙara ruruwa tamkar ana zubawa wuta fetur, ta ji tausayin Maryam sosai, amma ko za ta ƙyale ta ba dai yanzu, sai sanda duniya ta shaida ƙaddarar Maryam ce ƙin zaman aure, don haka ta ce"Maryam, ki share hawayenki, wannan ƙaddararki ce, zai wuce in sha Allah, ki faɗa mini me yake faruwa a gidan nan?" Maryam da zuciya ɗaya ta zayyana mata komai, har da cewar Alhaji na za ta tafi gidansu idan ba ta je gidan Sauda ba. Uwani ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Lallai yaro dai yaro ne, tunaninsa ba zai taɓa zaɓa na babba ba, yanzu ke Maryam da waɗan nan matsalolin birjik kike tunanin za ki iya ci gaba da zaman aure a wannan bahagon gidan? So kike hawan jini ya kama ki tun kina ƙaramarki? Wannan matsalolin sun fi gaban haƙuri Maryam, wannan auren rabuwa da shi ne ya fi maslaha ba ci gaba da yinsa ba, ki haƙura kawai, tozarcin ya yi yawa, maza ki haɗa kayanki ki wuce mu tafi gida, idan ya damu da ke zai biyo bayanki sai mu zauna a yi magana a sama miki ƴancinki, idan kuma gajiya ya yi to ya sallame ki, don ba neman kai nake yi da ke ba, kuma Alhamdulillahi ma tun da ba kya kwantai!". Maryam ta girgiza kai ta ce"Ni fa babu inda zan je, don na daina yaji". Uwani ta ce"Ki ma daina rantsewa, indai kin ɗauke ni a matsayin uwa kamar yadda kika faɗa, to ni na ba ki umarnin ki tashi mu tafi gida, ai shi yaji ta wani fannin ba yana nufin neman saki ba, yana nufin nemawa kai ƴanci, da fahimtar da miji amfanin matarsa, don mazan yanzu sai ka ba su waje suke sanin kana da amfani a rayuwarsu, don haka ki tashi ki haɗa kayanki mu tafi". Maryam ta ce"Babarmu ni ban yi jayyaya da ke ba, amma gaskiya ba zan je ko'ina ba, sai dai idan shi ne ya ce na tafi". Uwani ta ce"To shikenan Allah Ya rufa asiri, Ya kawo miki mafita, ni na tafi". Ta fice daga ɗakin ranta a ɓace. Maryam ko rakiya ba ta yi mata ba, tana zaune har aka kira sallar magriba, ta tashi ta yi, ta zubawa yara sauran abincin rana, ita ko yunwar ma ba ta ji, sun gama tana cikin share ɗakin ta ji sallamar Alhaji, sai da gabanta ya faɗi, saboda tunanin abin da zai iya faruwa, a tsakar gida suka haɗu ta fito da sharar za ta zubar, ta ce"Sannu da zuwa". Bai amsa ba ya ce"Maryam kenan barin gidan kika zaɓa ko!?" Ba ta ce komai ba, ta je ta zubar ta dawo ta shige ɗaki, ya bi bayanta cikin ɓacin rai ya ce"Magana fa nake yi miki, kin mayar da ni mahaukaci!". Nan ma ba ta ce komai ba. Ya ce"Ke Maryam tashi ki tafi gidanku, don wallahi na fi ƙarfin wulaƙancinki, ni kika mayar shashasha?" Ta ce"Alhaji ni fa ba da wata manufar na yi shiru ba, kawai na ga shi zai zama maslaha, ka ga bai kamata kana faɗa ina faɗa ba". Ya ce"Dakata! Babu wani zaƙin murya da za ki yi mini na yarda da ke, ya muka yo da ke a waya? Saboda raini ni zan ce ga yadda za ki yi, ki ƙi yi? Ai dama na faɗa miki matuƙar na dawo ba ki je ɗin ba to sai kin tafi gidanku, don haka ki wuce ki ba ni mukullina". Ita ma ranta ya fara ɓaci, ta ce"Me hakan yake nufi to?" Ya ce"Duk yadda kika ɗauka". Ta ce"Ni fa ba zan je gidan kishiya karɓar abinci ba, sannan kuma babu inda zan je, ni ba zan yi yaji ba". Ya ce"Amma idan na sake ki ai za ku tafi ko?" Zuciyarta ta doka, ta kuma yi raunin da har ta kasa tsayar da hawayenta sai da suka zubo, da rawar murya ta ce"Alhaji abun bai kai haka ba, ko don yaran nan..." Ya katse ta da faɗin"Ki bar mini yarana zan iya kula da su". Ta kalli yaran, sai tausayinsu ya kamata, duka-duka nawa suke da za ta tafi ta bar su a hannun kishiya irin Sauda? Har yanzu ba su shekara biyu ba, ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba". Ya ce"Ki je gidan Sauda ki ɗibo abin da kike buƙata". Wani ƙululun bakin abu ya tsaya mata a maƙoshi, ta ce"Ba zan iya ba Alhaji, ka faɗi wani abun bayan wannan zan yi shi". A bazata ta ji furucinsa"To ki je na sake ki saki ɗaya!". Ta kalle shi da sauri, sai dai kafin ta furta wata kalma har ya fice daga gidan, ta rasa me za ta yi, ta kifa kai a kujera ta fara kuka, zuciyarta na faɗa mata ba ta da hujjar yin kukan domin ita ce ta ja wa kanta, wani sashe na zuciyar kuwa yana faɗa mata ba ta da laifi tana kan daidai har yanzu, kuma mutuwar aure ba mutuwar rayuwa ba ce, sannan miji goma ba zai taɓa zama uba goma ba. Bayan ta gama kukan sai kuma ta fara tunanin yanzu ta ya za ta iya rabuwa da yaranta? Ta ya ma za ta koma gida a yau ta sanarwa Uwani abin da take gudu ya faru? Wannan ne ƙarshen wasan kenan? Sauda ce ke da nasara? "Kai! Ba zai yiwu ba! Sai na zauna a gidan nan, dole sai ya mayar da ni" Ta faɗa a fili tana share hawayenta, haɗi da ƙarfafa zuciyarta, a maimakon ta tashi ta fara haɗa kayanta sai ta ɗora girki sannan ta shiga wanka. Tana banɗakin ta ji sallamar Alhaji, ta gama ta fito ta same shi a tsakar gida tsaye kamar baƙo, fuskarsa babu annuri, Maryam ta yi murmushin yaƙe kamar komai da ya faru ɗazu a mafarki ne ba zahiri ba ta ce"Sannu da zuwa Alhaji, ka shiga ciki mana, kamar wani baƙo?" Abun ya ba shi mamaki, ya tsaya yana yi mata kallon me kike nufi. Ta ƙaraso inda yake, bai ankara ba ya ji ta rungume shi ta baya tana cewa"Wanka na yi zan yi maka kwalliya, ai kana so ko? Na yi kewarka fa har na matsu gobe ta yi, mu shiga daga ciki mana". Ta ƙarasa tana ruƙo hannunsa. Sai ya fizge ransa a ɓace ya ce"Kar ki mayar da ni wawa, sususus, shashasha! Ni za ki yi wa bariki? Dalla shiga ki haɗo mini kayan yarana zan tafi da su gidana, ke kuma ki fice ki tafi naku gidan". Maryam ta fara hawaye ta ce"Don Allah ka yi haƙuri ka janye batun nan Alhaji". Ya ce"Ni a tsarina idan kika ga na yi saki to an kai ni a jin ƙarshe ne, kuma na yi alƙawarin duk macen da na furtawa saki na furta kenan ba zan taɓa furta mata kome ba, saboda haka kar ma ki wahalar da kanki!". Daga haka ya shiga ɗakin, ya janyo hannun yaran ya zo ya fice da su ta gabanta, su kuwa da babu hankali sai murna suke yi suna ɗaga mata hannu alamar bey-bey. 08028966015 https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs 25 Sauda da yaranta suna zaune suna kallo a falo, sai ga shi ya shigo da yaran, ta kalle shi ta ga fuskarta babu annuri, hakan ya alamta mata an samu matsala, amma don ta tabbatar sai ta ce"Alhaji yau kuma zumunci ne ya motsa aka kawowa su Momy ƙannen nasu? Sannunku da zuwa ku shiga cikin ƴan'uwanku". Ta ƙarasa tana janyo hannun yaran da suke noƙewa saboda rashin sabo da ƴan'uwansu, da kuma tuna fuskar Sauda wacce kullum cikin zare musu ido take yi da hantarar su. Alhaji ya shige ɗakinsa, ta bi bayansa, ta same shi zaune a bakin gado, ta zauna tama cewa"Alhaji

Chapter 15 of 21