Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gidana ramin kura ne, na daɗe da gagarar mata ƴan tasha irinki masu burin shigowa gidana, ke ma na tabbata tsautsayi da rabon a saka wannan auren a lissafin mace-macen aurenki su ne suka kawo ki gidana, kuma wallahi sai kin fita nan ba da jimawa ba, dama ai na san labarinki ba ki da aiki sai aure-aure, ki haifi ɗa ki bar shi a gidan ki ƙara gaba, to nan ko haihuwar ma ba za ki yi ba, idan kuwa kika haihu sai dai ki tafi da ɗanki". Maryam ta ce"Lokaci shi zai nuna hakan". Sauda ta ce"Tashi ki fice mini daga falo, na fi ƙarfin shan inuwa ɗaya da ƙazama irinki, nan gidana ne, na fi ki cikkken iko da shi, saboda haka matuƙar na fito falon nan sai dai ki kwashi matattun mazaunanki ki fita". Maryam ta yi wata gajerar dariya ta rainin hankali ta ce"Lallai fa mai cikakken iko! Inda ni ce na samu wannan cikakken ikon da ba zan ma yi saken da mijina zai dinga hangen matan waje ba, kuma da kika ce mini ƙazama ke ma yanzu zama ƙazamar tun da mun haɗa miji da ke, sai dai ko idan ya shigo ɗakinki ki dinga canza masa fata ko? Kin ce kin gagari mata ƴan tasha, to tun da ni kika kasa har na shigo gidanki ya kamata a ce ganin buzu a masallaci yasa tinkiya shiga taitayinta, ni ba hayaniya ce ta kawo ni gidan nan ba, na zo ne na yi zaman aure, na farantawa mijina, na raini ƴaƴan da zamu haifa, babu ruwana da ke, idan gari ya waye mu gaisa, idan ba kya so ba dole ba ne". Sauda ta ce"Sai dai ki gaisa da uwar uwarki, ni ba tsararki ba ce". Maryam ta ce"Kin ga ya isa haka, ni wai dama har yanzu ana irin wannan kishin na hauka da jahilci?". "Ni kike cewa mahaukaciya!?" Sauda ta faɗa tana ɗaga hannu za ta mare ta. Maryam ta cafe hannun ta miƙe tsaye, ta ce"Kar ki sake! Kar ki kuskura wallahi, na fi ƙarfin duka a gidan aurena, ko wanda ya ajiye ni ƙarya ne ya dake ni ballanta ke da muke matsayi ɗaya". Ta yarfar da hannunta ta ce"Kin ga ki tsaya matsayinki, ni babu ruwana da ke, kowa ya yi ta kansa, amma fa ɗakinki kaɗai za ki iya hana ni shiga a cikin gidan nan, ke ba ki isa ki saka na dinga zaman ɗaki ba, aure na zo yi ba faɗa ba, saboda haka ki shafa mini lafiya". Ta koma ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Sauda ta ce"Wallahi yawo kika zo yi gidan nan ba aure ba, don haka ki fara haɗa kayanki tun yanzu". Maryam ta yi tsaki ta ɗauki remote ta kunna TV, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta turo ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi. Saudat ta daskare da mamaki, ba ta yi zaton za ta raina ta har haka ba, ta yi ƙwafa ta fice daga falon. Ɗaki ta shiga ta zauna ta yi jugum tana tunanin ta inda za ta ɓullowa yarinyar nan, ta ɗakko waya ta kira ƙawarta, suka gaisa ta ce"Ya ƙawata, ya kika ga aikin magungunan nan?" Sauda ta ce"Wasu magunguna? Na ga sai yau zan karɓi kwanan". Aliya ta ce"Hakane fa, to ki tabbata kin banke su sosai, don ya ce har kin fi amaryar ma, don ba mu san ita shegiyar irin shirin da ta yi ba". Sauda ta ce"Ke wannan ai ta wuce shegiya, a tsaye take fa, wallahi ƙwanƙwararriya ce, ga ta can a falo ta hakimce kamar gidan ubanta, yanzu ta gama zagina". Aliya ta ce"Ke Sauda! Ta zage ki? Kuma kika barta ba ki ci ubanta ba?" Sauda ta ce"Ke da alama fa wannan sai dai mu ci uban juna, wallahi idanunta a soye suke kamar gyaɗa marau, na ɗaga hannu zan dake ta, ta damƙe hannun, kin ga kuwa wannan ai sai dai mu dambatu". Aliya ta ce"A tabbas! Amma fa kar ki sare da wuri, ki ci gaba da muzurai ki gani ko za ta yi laushi, idan ta kafe sai mu canza taku, sannan wannan magungunan ma ƙila su gyara mata zama, su nuna mata matsayinta a gidan, ke dai don Allah kar ki yi wasa da su". Sauda ta ce"Hmm! Har sai kin roƙe ni? Wallahi zan yi, ai dole na zage, jiya ma hana su daren na yi, ƙarshe a ɗakin yara ya kwana". Ta kwashe komai ta ba ta labari. Aliya ta saka dariya ta ce"Kin yi mini daidai, amma nan gaba ki daina tsorata yaranki irin haka". Sauda ta ce"Ai kuwa dai ni ma na ce na daina sako yaran, zan nemi wasu dabarun". Suka sha firarsu tana ta zugata. Can wajen ƙarfe ɗaya Maryam ta fito don ta yi girki, ta samu yaran duka su huɗu zaune a kitchen ɗin, sun saka bokitin dubulan ɗinta a gaba suna yi masa cin yunwa, mamaki ya daskarar da ita na ƴan sakanni tana kallonsu, kafin ta daka musu tsawar da ta razana su, ta ce"Uban waye ya ba ku izinin cin wannan abun?" Suka fara muzurai suna siɗe hannu. Ta ce"Duk ranar da na ƙara ajiye abu kuka ɗauka wallahi sai na saka bulala na zane ku tass! Ku ɓace mini da gani!" Ta ƙarasa a tsawace. Momy ta ce"To ai Ummanmu ce ta ce duk abin da muke so a kitchen mu ci, babanmu ne ya siya". Maryam ta gwaɓe mata baki, sannan ta riƙe kunnenta ta murɗe har sai da ta yi ƙara, kafin ta ce"To ki je ki faɗa mata wannan ba ubanku ne ya kawo ba! Kuma kika sakw yi mini rashin kunya sai na fasa bakinki, don ba zan lamunce rashin kunya ba". Duk suka fice, Momy ta ƙarasa ɗakin babarta da gudu tana fashewa da kuka, Sauda ta miƙe tana cewa"Lafiya? Momy mene ne?" Ta ce"Waccen ce ta dake ni, ta murɗe mini kunne". "Kan bala'i!" Cewar Sauda ta na riƙe ƙugu, ta ce"Uban me kika yi mata?" Ta ce"Wai don mun ci dubulan". Ta ce"A kan tsinannen abun nan ta dake ki?" Sai ta fice tana huci kamar zakanya. Maryam tana gyara kayan miya Sauda ta shigo, ta ce"Zuwa na yi na ji akan me kika dakar mini ƴata?" Maryam ta ce"Ki koma ki tambaye ta mana". Ta ce"Dama an ce duk inda matsiyaci yake sai ya nuna! A kan sun ce wannan banzan abun kika dake ta? To sun ci ɗin, kuma sun ci banza, uban wa ya ce ki ajiye a kitchen ɗin?" Maryam ta ce"Tabbas sun ci banza, ni kuma su ci gaba da cin banza na ci gaba da dukan banza, sai mu ga wanda zai fasa". Sauda ta ce"Ai wallahi ƙarya kike yi! Wannan shi ne na farko na ƙarshe, duk ranar da kika sake dukar mini ƴa sai na rama mata, kuma yanzun ma ba ki daki banza ba, ki jira matakin da zai biyo baya". Maryam ta ce"Ba ni da lokacinki". Sauda ta ce"Za ki samu nan ba da jimawa ba". Ta juya ta fita tana zage-zage. Maryam ta gama girkinta ta koma ɗaki ta ci, ta kwanta bacci. Da yamma ta ci wanka ta zo babban falo, ta tarar da Sauda zaune ita da yaranta, ita ma ta nemi kujera ta zauna tana danna wayarta, Sauda ta yi shiru tana satar kallonta. Dab da magriba Alhaji ya dawo, yaran suna jin ƙarar buɗe get ɗinsa suka tafi da gudu suna "Ga Abba ga Abba". Ita ma Maryam ta miƙe tana cewa"Ga Abba ga Abba" Ta fice da sassarfa. Sauda ta bi ta da kallon mamaki, sannan ta tashi ta biyo bayansu, yana fitowa daga motar duka suka tafi tare da yaran suna oyoyo, Alhaji ya yi dariya yana kallon Maryam ya ce"Har da ke? A cikin yara?" Ta yi masa fari ta ce"E mana, na wuni da kewarka ai dole na taro ka". Ya ce"Wannan dai salon a ɗauki alhakina ne, kin san zan rasa control ɗina, kuma a gaban yara, irin wannan wankan ma ai sai ki bari sai ranas girkinki, idan ba so kike na dinga kwana da kewarki a ɗakin ƴar'uwarki ba". Maryam za ta yi magana suka ji muryar Sauda, ta ce"Wai ni ka manta ba girkinta ba ne yau, ko kuwa duk cikin salon wulaƙanta ni ne?" Alhaji ya ƙarasa yana cewa"Kuma meye idan ta taro ni? Shi ma dole sai mai girki?" Ta ce"Au tambayata ma kake yi? Kenan da ba ka yi ilimin zama da mata biyun ba ka ƙara auren!". Maryam ta ce"Alhajina ni bari na shiga, ka huta lafiya". Cikin suɓutar baki ya ce"To wane hutu?" Sai kuma ya ce"Hmm! Na gode Maryam". A dole ya bi ta da kallo saboda yadda take tafiyar ƙaniya. Sauda ta dafe girji ta ce"Abba! Me kake nufi da babu hutu? Wai abun har ya kai haka?" Ya yi guntun tsaki ya shige ciki. Ya haɗa ruwa ya yi wanka yana tunanin Maryam, yadda ta sangarta shi a kwana ukun da suka yi, sai ya tsinci kansa da sakin murmushi, ya ce"Ina son yarinyar". Ya shirya ya fito falo ya zauna, shiru babu Sauda sai yaran, har aka kira magriba ya tafi masallaci, da ya dawo ma shiru ba ta fito ba, ya saba da irin haka, ko yaya suka samu saɓani to fa idan ya matsu da abinci sai dai ya zuba da kan shi, ya kalli babbar ƴar ya ce"Momy ina abincina?" Ta ce"Ba ta gama ba". Babu jimawa kuma ya ga ta zo ta wuce kitchen ɗin tana ɓata rai, yana nan zaune ta gama ta zubawa yaran ta kawo musu, ta zo ta wuce da nata ɗakinta. Karo na farko da ya ji daɗin ƙara aure, ya ɗauki waya ya kira Maryam, ta ce"To kana cikin gidan kake kirana?" Ya ce"E mana, don na sauƙaƙawa kaina, don Allah zan samu abinci?" Ta ce"Ai kuwa da rana kaɗan na dafa, ka ga ban yi komai ba da dddare, amma ba zau gagara ba, bari na yi maza na sama maka". Ta fito, yana kallonta ta shiga kitchen ɗin, dama akwai miya, sai ta dafa couscous, ta zubo masa ta kawo, daidai sanda Sauda ta fito don mayar da kwanonta kitchen, Alhaji ya ce"Ma sha Allah! Gida biyu maganin gobara, mai mata biyu ɗan gata! Har kin gama?" Maryam ta yi murmushi ta ce"Tabbas ɗan gata kake, idan hagu ta ƙiya a koma dama ba". Sauda ta wuce fuuu, Maryam ta zauna suna taɓa fira yana cin abincin, sai da ta gama ta ɗauke kwanon sannan ta koma ɗakinta. Yana shiga ɗakinsa ya tarar da Sauda zaune a bakin gado, ta fara share hawaye ta ce"Dama ka ƙara aure ne saboda ka wulaƙanta ni? Ka ƙi sakina ne saboda ka dinga muzguna mini?" Ya ce"Ikon Allah! To me aka yi a nan na muzgunawa? Kin hana ni abinci, kuma yanzu ina da wacce zan bawa umarni ta bi, sai na zauna da yunwa? Sauda ya kamata ki sani wannan aure na yi shi ne don na huce takaicinki, saboda haka muddin za ki ci gaba da shakulatun bangaro da ni, ni kuwa zan saka matata ta kula da ni". Ta ce"Shikenan tun da haka ka tsara, amma ka yi mata gargaɗi, ni ce kishiyarta ba ƴaƴana ba, komai za ta yi ta yi shi da ni, kar ta sake saka ƴaƴana a ciki, yau ta kama su ta yi musu mugun duka kawai saboda sun ɗauki dubulan ɗinta sun ci, ta yi ta zaginsu har tana cewa gadon sata suka yi, to ni dai ba a wajena suka gada ba, sai ka tambaye ta inda suka yo gadon". Ta tashi ta fice daga ɗakin. Ya zauna yana mamaki, yanzu ko sati ba a yi da auren ba amma ba za a bar shi ya huta ba? Ya ce"Allah Ya kyauta". Bayan ya dawo daga yiwa Inna sai da safe, sai ya zo zai shiga ɗakin Maryam, Sauda ta ce"Ka manta ba a nan kake ba?" Ya ce"Sauda ba na son irin haka fa! Ya kike neman mai da ni ban san abin da nake yi ba? To sai da safe zan yi mata". Ta ce"A'a ni ban yarda da wannan salon cin amanar ba, babu wani sai da safe indai ya wuce a babban falo". Ya ce"To sai dai kuma ba ki da matsayin da za ki tsara mini yadda zan yi". Ya shige ɗakin ya barta tsaye sake da baki. Ya samu Maryam har ta kwanta, ta tashi zaune tana cewa"Ka dawo?" Ya ce"E, Maryman da gaske yau kin daki yaran nan?" Ta ce"E, saboda..." Ya katse ta da faɗin"Saboda sun ci miki dubulan?" Ta ce"E". Ya ce"Haba Maryam, yanzu wannan ya kai a daki yaro?" Za ta yi magana ya katse ta da faɗin"A'a gaskiya ba zan ji komai ba, duka ba ta cikin tarbiyya, gaskiya mu gidan nan ba ma duka, idan yaro ya yi laifi ki yi masa nasiha, ko ki same ni ki sanar da ni, ni zan ɗauki mataki". A sanyaye ta ce"To, in sha Allah ba zai sake faruwa ba". Ya ce"Yawwa, kin ga Sauda tana kan giyar kishi, sai kin yi haƙuri kin kau da kai ga duk abin da za ta tsiro da shi, kuma ina yi miki kyakkyawan zato, za ki iya in sha Allah". Ta ce"In sha Allah, zan yi iya yina na ga ban kulata ba". Ya yi mata sa da saf ya fice. Sauda fa ta sha magunguna ta bugu, jira take kawai yara su yi bacci, tara da rabi ta ce su je su kwanta, amma me? Sai duk suka noƙe suka ce a ɗakinta za su kwana, da ta matsa suka fara yi mata kuka, ta shiga lallaɓa su, ta samu suka yi bacci, wajen sha ɗaya ta lallaɓa ta zame, ta buɗe ƙofa za ta tafi turakar Alhaji, ƙarar buɗe ƙofar ya tashe su a firgice, suka miƙe za su bi ta, ta fara zare musu ido tana yi musu tsawa, sannan ta fice, tana tura ɗakin Alhaji suma suka fito suka biyo ta suna kuka cike da firgici, Sauda ta fara masifa, Alhaji ya fito ya ce"Mene ne? Ko yau ma kin tsorata sun?" Ta ce"Kamar ya? Bacci fa suke yi daga fitowata shi ne suka hau kuka". Ya ce"To ai sun riga sun firgita ne, dole idan daren ya yi su tuna". Ta ce"Ka ce su koma, ka ga dai ba za mu kwana da su ba ko?" Ya ce"Haba Sauda, kuma yaran idonsu biyu ke sai ki tsallako ɗakina? Kamar wasu yara? Ki je ki ji da su kawai Allah Ya tashe mu lafiya". Wani baƙinciki ya turnuƙe ta, ta kasa magana, ta juya ta koma cike da takaicin ta sha magani a banza, yaran kuwa har rige-rigen binta suke yi. Maryam da ke laɓe ta windon ɗakinta tana kallonsu ta saki murmushi tana cewa"Ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya". LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay Shaidar biya ta nan 08028966015 https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3 16 Haka Sauda ta kwana a ɗakinta da yara cike da takaici, yayin da Maryam ta yi amfani da wannan damar ta ragewa Alhaji kewa ta chart, ta kwana ranta fess, don ta ji daɗin rasa kwanan da Sauda ta yi. Washegari da safe Alhaji da Sauda suna dining suna karyawa Maryam ta fito, ta yi masa wani kallo mai motsi, Alhaji ya sakar mata murmushi, ta ƙarasa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata bisimilla, ta kalli indomin da yake ci ta ce"Na gode, yanzu zan dafa nawa". Ta kalli Sauda da ta kumbura, ta ce"Maman yara ina kwana?" Sauda ta ce"Maman yara!? To ai yaran abun alfahari ne, ni na ajiye yaran ke kuwa ko kaza ba ki ajiye ba". Maryam ta ce"To kwana nawa ne maye ya yi amarya?" Sauda ta ce"A yi mu gani". Alhaji ya ɗaga hannu ya ce"Mene ne haka don Allah? Da sanyin safiyar nan za ku fara a gaban yara?" Sauda ta ce"To nan gaba babu abin da yaran nan ba za su gani ba, kuma dama duk wanda ya ƙara aure ai ya shirya yaƙi, magana idan ta kama da asuba ma yi za a yi ba sanyin safiya ba". Maryam ta ce"Allah Ya kyauta". Ta wuce kitchen. Yau ma haka ta zo babban falo ta yi zamanta, sai dai Sauda ma ta zo ta zauna, haka aka yi zaman kurame kowa yana son nunawa ɗan'uwansa ba a isa a saka shi zaman ɗaki ba. Da daddare bayan sallar isha'i Alhaji ya shigo, Maryam ta tashi za ta tafi ɗakinta ya ce ta zauna, ya ce"Dama tun da aka yi auren nan ban zauna da ku ba, to maganar rabon kwana, kwana ɗaya-ɗaya zan dinga yi a kowane ɗaki, saboda haka yau ina ɗakin Maryam". Sauda ta ce"Hmm! Kawai dai ka ce za ka coge mini nawa kwanan, ai a ƙa'ida kwana biyu ake yi, tun da ba ka yi mana bayani ni a zatona kwana biyun ne, don haka sai ka cika mini ɗayan kwanana sannan a ci gaba da yin ɗaiɗai ɗin". Alhaji ya ce"Kai! Allah Ya kyauta! To don kin zaci abu sai aka ce ya zama dole na zartar da shi? Ni dama can ɗayan na tsara, kuma hakan za a yi, ba na son doguwar jayayya". Ya ci gaba"Sannan maganar girki kuma, gabaɗaya guda ɗaya za a dinga yi, ba wai kowacce ta yi nata ba, a'a duk wacce take da kwana ita za ta yi girkin duka gida, a zuba a kula kowa ya ɗiba ya ci, safe, rana, dare duk haka za a yi, sannan kuma a tare za a dinga cin abinci, musamman na safe da nake gida, babu cewa ni sai an jima zan ci nawa, kowa ya zauna a haɗu a ci, hakan ne zai ƙara mana zumunci da ƙaunar juna, su ma yara su taso babu wani bambanci". Wannan tsari ya yiwa Sauda daɗi, don ta hasasho hanyar ƙuntatawa Maryam ta nan, don haka ba ta da ƙorafi a nan, ita kuwa Maryam sam tsarin bai yi mata ba, amma ta yi shiru saboda a zauna lafiya, ta san dai dole ba za ta ga komai daidai ba, amma ta saka a ranta za ta yi iya yinta, idan kuwa ta ga za a cuce ta za ta faɗa masa a canza tsari. Haka ya kwana a ɗakin Maryam cike da farinciki. Washegari an shiga girkin Sauda, don haka ita za ta yi abincin safe har na Maryam, bakwai da mintuna Maryam ta fito cikin kwalliyarta, sassafe take tashi ta yi wanka ta ci kwalliyarta tun da babu ciki babu goyo, ba ta da wata hidima sai ta gyaran kanta, Alhaji ya fito ya same ta a dining tana danna waya, ya ce"Kin fito kenan, kin yi kyau kamar wata ɗawisu". Ta ce"Daɗin baki dai". Sauda ta fito tare da yara da ta gama shirya su, suka zauna suna gaishe da Alhajin, sai da suka gama tsaf ya lura ba su da niyyar gaishe da Maryam sannan ya ce"Ku wannan ba Antinku ba ce? Sai an ce muku gaishe ta?" Suka fara gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, ya ce"Idan na sake ganin gari ya waye ba ku gaishe ta sai na saɓa muku, ko ba ta fito ba ku shiga ɗakinta ku gaishe ta, ita ma babarku ce". Suka gyaɗa masa kai. Sauda ta fito da kunu da dankali, ta ajiye ta zubawa kowa, ta zuba nata suka fara ci, sannan Maryam ta zuba nata, ta riga su gamawa don haka ta tashi tana yi masa a dawo lafiya ta koma ɗakinta. Da rana Sauda ta dafa shinkafa da miya, Maryam ta yi tunanin ko za a zo a ce mata an gama girki ta ji shiru har ƙarfe uku, ta tashi ta shiga kitchen ɗin, ba ta ga wata kula mai ɗauke da abinci ba, ta buɗe tukunya ta ga wata gubtuwar shinkafa, ta jinjina kai ta juye ta a faranti ta ci, da daddare kuma tuwo ta yi, dayake ta yi dare ma ba ta gama da wuri ba har ya dawo, ya ce ta saka musu a kwano ɗaya su ci su ukun, Sauda ta taɓe baki ta ce"Alhaji kawai dai ka ce kana son ka dinga cin abinci da matarka, tun da ba ka san a ci tare ba sai yanzu da ta zo gidan? Na san za ka ce ni ma na zo ne kawai saboda kar ka ga rashin kyautawarka ƙarara, don haka ni kam na yafe, zan ci gaba da yin yadda na saba". Maryam ta ce"To Alhaji bari na zubo mana, sai mu ci taren". Sauda ta harare ta, ta yi ƙwafa ta shige ɗakinta, ita kuwa ta sako musu, suka ci tare. Can dare ya yi za ta ta fi ɗakin Alhaji yara suka ce ba su san zance ba, da gaske sun riga sun firgita ba za su iya kwana su kaɗai ba, ta dinga yi musu masifa, ƙarshe ta ce duk wanda ya fito sai ta dake shi, ta rufo musu ƙofa ta tafi, su kuwa sai ihu suke yi. Tana shiga ɗakin Alhaji ya ce"Sauda ni kukan me yaran nan suke yi?" Ta ɓata rai ta ce"Wai tsoro suke ji". Ya ce"Kuma sai ki bar su? Idan suka shiɗe fa? Don Allah je ki kula da su". Ta ce"Ni wai me yasa ba za ka fito ƙarara ka faɗa mini tun da ka samu sabuwa ba ka maraba da ni ba? Me yasa ka wahalar da kanka wajen rabon kwana, ka san ba haka ba ne a zuciyarka?" Ya ce"Allah Ya sani babu komai a zuciya na rashin adalci, amma kin san bai kamata ki baro yara ki taho nan ba ko? Ba mu san halin da za su shiga ba". Ta ce"Shekaran jiya kwanana ya wuce saboda yara, kishiya tana kallo tana yi mini dariya, yau ma kuma sai ka kore ni ta gani ta tabbatar da ita kaɗai ce mai amfani a wajenka ko? To wallahi ba zai yiwu ba, yau a nan zan kwana ko da kuwa juya mini baya za ka yi, ai ni dama na sani tun da ka yi amarya na gama maka amfani". Ta haye gadon ta kwanta, har da harɗe ƙafa cike da gadara. Ya ce"To ai ni ba kwananki a nan ne matsalata ba, a'a a bar yaran a razane ne su kaɗai ba na so, tun da hakane ni bari na je na kwana da su". Ya fice ya barta cike da baƙinciki, ta matsu ta fara ganin ingancin maganin nan, amma ga shi abin da ta yi don ƙuntatawa kishiya yana neman zame mata ƙarfen ƙafa, ta gama yanke hukunci wannan ne na ƙarshe, idan ranar kwanata ta zagayo tattara su za ta yi ta kai su gidan Inna su je can su ƙarata. Haka Alhaji ya kwana da yara a ɗaki. Washegari girkin Maryam, ƙarfe shida na safe Sauda ta zo ta fara buga mata ƙofa da ƙarfi, Maryam tana kwance lokacin ba bacci take yi ba, tun da ta san ita ce da girki, jira take nan da wasu mintuna ta fito, ta ga jiya ya siyo biredi shayi kawai za ta dafa a sha, ta taso ta buɗe, ta ga Sauda ce, fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Maman Momy ke ce? An rashi lafiya?" Sauda ta ce"Lafiya ƙalau, dama na ji shiru ba ki fito ba ne, ko kin manta ke ce da girki?" Ta ce"Ban manta dama yanzu zan fito". Sauda ta ce"To ai sai ki fito don kar yara su makara, ga shi Alhajin ya ce kunun gyaɗa da ƙosai za a yi". Maryam ta ce"To". Ta fito ta shiga kitchen, bakwai da rabi ta kammala, Sauda tana ta mitar yara za su yi latti, Alhaji ya ce"Maryam ki dinga daurewa kina tashi da wuri saboda yaran". Ta ce"In sha Allah! Dama don ban kwana da shirin yin kunu da ƙosai ba ne, shiyasa ya ja lokaci, amma gaba zan gyara in sha Allah, tuba nake ranka ya daɗe". Ya yi murmushi ya ce"Wannan halin naki na karɓar gyara yana burge ni". Sauda ta kau da kai zuciyarta na ƙuna. Suka gama karyawa Alhaji ya fita, Maryam tana kitchen tana wanke-wanke Sauda ta shigo, tana yi mata kallon raini ta ce"Yanzu muka yi waya da su Anti Zulai, wato ƴan'uwan mai gidan, sun ce yau za su zo gidan, don haka sai ki yi girkin da dama, su shida ne har matan ƙannen Alhaji, kuma da yaransu, rowa ba halinmu ba ne ni da mijina, saboda haka ki san irin girkin da za ki yi". Ta juya ta fita. Sha ɗaya ta dawo kitchen ɗin,

Chapter 10 of 21