za ta yi shanya sai ta tsinka mata igiya, har zuwa ranar da ta kama ta, ta kama tana yankawa da reza Maryam ta fito daga ɗaki suka yi ido huɗu, sai ta wayance ta fara ƙananun maganganu tana cewa"Haka kawai a zo a shanya kaya a hanya suna jiƙawa mutane gida, dalla ki matsar da su daga hanya" Daidai nan rezar hannunta ta faɗo ƙasa Maryam ta ganta.
Ta ƙaraso tana yi mata kallon mamaki, ita dama ta daɗe tana zargin wannan yawan tsinkewar igiyar tata ba ta Allah da Annabi ba ce, sai yau da ta ga zahiri, ta ce"Amma dai kin yi asara wallahi, ki rasa a kan me za ki yi kishi sai igiya? Allah Ya kyauta".
Cike da borin kunya ta fara cewa"Abin da ya fi kishi, me zan yi da igiyarki ta banza? Lallai kin samu waje, na ƙyale ki na ba ki dama, shiyasa har kika samu damar sa'insa da ni, amma dau kin gama, ai dai kin huta daga zaman gidan kin ɗana zaman gidan miji, daga yau ki fara lissafa kwanakin shigarki zawarci".
Duk da gaban Maryam ya faɗi amma ta dake ba ta nuna ba, ta ce"Aurena a hannun Allah yake, don haka ke ba ki isa ki kashe shi ba, kuma ni da mijinki mutu-ka-raba takalmin kaza".
Lubabatu ta ce"To za mu gani".
Ta shiga wanka ta fito tana ta ƴan waƙe-waƙenta, ta zo ta fice daga gidan, sai dare ta dawo da yake ba ita ce da girki ba, tana dawowa ta buɗe randar Maryam a hankali ta watsa wasu abubuwa a ciki, ta shige ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
28
Sati ɗaya da faruwar haka a wani dare Maryam ta tsinci kanta cikin wani al'ajabi, a ranar ba ita ce da girki ba, da wuri ta kwanta bacci, ƙarfe ɗaya na dare ta farka ta ji ta a cikin abu mai kama da ruwa, gabaɗaya jikinta da katifar ta jiƙe sharkaf, ita dai ta san ba ta ajiye ruwa a kusa da ita ba, ta fara tunanin me ya jiƙata haka, sanda ta tabbatar da fitsarin kwance ta yi ta shiga mamaki sosai, ta san ta yi fitsari kafin ta kwanta, ballanatana a ce matsinta ya yi shiyasa har ya kufce mata, ta sauke ajiyar zuciya ta sakko daga gadon tana sakawa a ranta ɓacin rana ne kawai, ta yaye zanin gadon, ta zuba ruwa a wajen ta matse sosai, Allah Ya taimake ta akwai nefa sai ta saki fanka ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, domin da kunya ta fitar da katifar waje.
Can ta ƙara farkawa ta ji ta a jiƙe alamun ta yi wani fitsarin, ƙirjinta ya fara dokawa ta fara tunanin anya lafiya kuwa? Sai ta kwashe kayan shimfiɗar ta fita a daren ta wanke ta shanya, ta dawo ta kwanta a kujerar falo tana ta tunane-tunane har wani baccin ya ƙara ɗaukarta, dab da asuba ta ƙara yin wani fitsarin, hakan ya tabbatar mata lallai ba lafiya ba, ta wayi gari jiki a mace kamar mara lafiya, Lubabatu tana fitowa da asuba da ta ga zannuwan gado a igiya ta saki murmushin samun nasara tana jin daɗi a ranta.
A ranar girki ya dawo hannun Maryam, yau ko da ta ci abincin dare ruwa kaɗan ta sha, sannan sai da ta tabbatar ta yi fitsari kuma ba ta jin wani sannan suka kwanta bayan sun gama firarsu da Aliyyu, ƙarfe sha biyu da rabi ta farka sakamakon jin ɗumi a jikinta, da alama yanzu ta yi fitsarin, ta tashi da sauri gabanta yana faɗuwa, don har ya taɓa Aliyyu, ta je falo ta zubo ruwa a dogon kofi ta zo ta zuba a wajen ta ajiye sauran a kan lokar gadon, ta saka zani a hankali tana dannawa a wajen, Aliyyu jin sanyi a jikinsa yasa shi farkawa, ya ga Maryam tana goge-goge, yana duba jikinsa ya ce"Lafiya? Me ya kawo ruwa gadon nan?"
Ta ce"Ka yi haƙuri, a nan lokar gado yake, shi ne na farka na ji ƙishi kuma ban sauka ba, na ɗakko shi zan sha, tsautsayi ya sa ya kufce daga hannuna".
Ya yi guntun tsaki ya tashi ya canza kaya, ya hau gadon ya matsa can gefe inda bai jiƙe ba.
Ita kuma da ta gama sai ta ko ma falo ta yi shimfiɗa ta kwanta, ko da ya ga haka bai wani damu ba, saboda ya yi zaton ko don wajen ya jiƙe ne. Washegari da suka kwanta ƙin yin baccin ta yi, har sai da ta ga baccinsa ya yi nisa sannan ta tashi ta koma falo ta yi shimfiɗa, can cikin baccinsa ya farka ya ga babu ita a gadon, ya saurara yana jiran shigowarta don a zatonsa banɗaki ta shiga, sai ya ji shirun ta yi yawa, ya wartsake saboda yana jiran shigowarta, domin a farkon daren ya so nemanta amma gajiyar aiki da ya kwaso ta hana shi, idan irin haka ta faru bari yake sai ya yi bacci ya farka sai ya tashe ta, to yau ɗin ma hakan ce ta faru, sosai yake samun nutsuwa da ita ga shi yau ne kwanan nata zai fita, shiyasa ba zai bari wannan dama ta wuce shi ba, ya sakko daga gadon don ganewa idanunsa zahiri, domin ko wanka take yi ya ci a ce ta gama, yana fitowa falo ya ganta kwance a ƙasa har da shimfiɗa, ya tashe ta yana cewa"Maryam, Maryam".
Ta farka ta tashi zaune tana amsawa.
Ya ce"Mene ne haka? Me zai sa ki dawo falo ki kwanta a ƙasa?"
Ta ce"Babu komai, kawai nan ɗin ya fi yi mini daɗi".
Ya ce"To ai kuma ba zai yiwu ba".
Ta ce"Don Allah ka bar ni a nan ɗin, ka je ka yi kwanciyarka, katifar ciwon jiki ma take saka ni".
Ya ce"To sai dai ki bari ranar da ba na ɗakinki sai ki dinga yin hakan, yanzu dai tashi ki wuce ɗaki kawai".
Ta tashi ta fita ta yo fitsari sannan ta shiga suka kwanta, duk yadda ta so nesa da shi a gadon ya ƙi bata dama, sai da ya kwanta a jikinta, ita kuma ta dinga kokowa da bacci abu ya ci tura, ba ta san sanda ya ɗauke ta ba, sai salatin Aliyyu ne ya tashe ta, dama a ankare take don haka ta farka a firgice tana cewa"Lafiya? Me ya faru?" Duk kuwa da ta ji ta a jiƙe jaƙaf.
Ya ce"Ba dai fitsari kika yi ba?"
ur, shi ne...to ban san sanda ya kufce mini ba".
Ya yi tsaki yana sauka daga gadon cike da ƙyamar jikinsa ya ce"Wannan dai shashanci ne, ya kufce miki sai ka ce wata yarinya ƙarama?"
Ya koma falo ya kwanta a kujera, ita kuma ta cire zanin gadon ta nemi waje ta zauna, jikinta ya yi sanyi sosai, zuwa yanzu ta san tabbas ba lafiya ba, don haka dole ta yi gaggawar neman magani. Washegari da safe ta ce masa za ta je gidansu ya ce a dawo lafiya.
Ƙarfe goma a gida ta yi mata, Uwani ta tare ta da fara'a tana cewa"Har kin fara fitowa kenan".
Maryam ta ce"E wallahi, nan na fara zuwa".
Ta ce"Ya gidan naki? Ƙalau dai babu wata matsala ko?"
Ta ce"Lafiya ƙalau".
Uwani ta ce"Anya kuwa?Don ba ki yi min kama da wacce take zaune lafiya ba, sai na kamar a firgice kike".
Maryam ta fara share hawaye, Uwani ta ce"A haf! Ni dama na gani, kuma auren nan babu yadda ba a yi da ke ba kika ce kin ji kin gani, an faɗa miki kowace kishiya ake alwashin zama da ita?"
Maryam ta ce"Ni fa babu ruwana da ita, wannan matsala ce ta dan".
Uwani ta ce"To matsalar me?"
Ta ce"Ba ni da lafiya, fitsarin kwance nake yi kullum, ba ma sau ɗaya a dare ba, na rasa ya zan yi, tun ina ɓoye masa ga shi jiya ya gani, a jikinsa na yi".
Uwani ta ɗauki salati ta dire kafin ta ce"Danƙari, wannan kuma wata sabuwar ƙaddarar ce? Maryam lallai ke yarinya ce, ke yanzu ki ga haka kuma ki ce ba matsalar kishiya ba ce? Ashe har yanzu ba ki san makircin kishiya ba kenan".
Maryam ta ce"Babarmu zato zunubi, ni gaskiya na fi tunanin wannan wata matsala ce kawai mai zaman kanta, Allah Ya jarabce ni da ita, larura ba ta wuce kan kowa ba, magani kawai za ki samo mini".
Uwani ta ce"Haka ne kuma, zato zunubi, amma ni ina zarginta, ke fa ana yaye ki kika daina fitsarin kwance, yanzu me ya dawo da bara bana?"
Maryam ta ce"Ko ana zarginta ina hujja take? A yi maganin shi ne kawai mafita".
Uwani ta ce"Maryam mafitarki ɗaya ce kawai ki bar gidan nan, ki haƙura da auren nan tun kafin ta kassara ki, wannan ba gidan zama ba ne".
Maryam ta ce"Na gaji, wallahi na gaji da wannan mace-macen auren nawa, ni zan zauna a hakan ko da ba zan samu maganin ba".
Uwani ta yi murmushin ke yarinya ce ta ce"Idan ke za ki zauna a haka shi zai yarda ya ci gaba da zama da ke? Ko yaro ne mai fitsarin kwance ba shi da daɗin sha'ani, ballanata a ce matarka tana fitsari, tana jiƙa katifa sharkaf ana fita da ita shanya, ɗaki yana wari da zarni, yana fargabar kwana a kusa da ke, anya zai jure kuwa? Ke yanzu ba za ki ji kunyar kishiya ba a ce kina fito da kayan fitsari kina shanyawa? Ki dai duba Maryam, ni dai a ganina gara ma duka sauran gidajen da kika fito a kan wannan, wannan sam ba ki samu waje ba".
Maryam ta ce"Na san da wannan, amma dai yanzu a samu maganin na gwada tukunna".
Uwani ta yi jimm kafin ta ce"To ni dai ban san wani magani na fitsarin kwance ba, amma tun sa kin kafe kin ce yanzu kika ga gidan aure ai dole na bazama na samo miki, gobe zan fita sai na ga yadda za a yi".
Maryam ta ce"Gobe kuma? Don Allah ki samo mini yau".
Uwani ta ce"Ke abun nan fa ba na gaggawa ba ne, idan ma an samo a yau ɗin ai ba lallai ya fara aiki a yau ɗin ba, idan ma an dace kenan, don haka ki koma gida yau zan tambaya na ji, idan an samu gobe idan Allah Ya kaimu sai na zo na kawo miki".
Maryam ta ce"Ko kuma na kwana a nan ɗin tun da ba ni ce da girki ba".
Ta ce"Indai ya bar ki ai shikenan kin ga goben sai mu je tare".
Maryam ta ɗauki waya ta kira shi, suka gaisa ya ce"Kin tafi gidan?"
Ta ce"E ina can, dama so nake na tambaye ka ina so na kwana a can".
Ya ce"Ki kwana kuma? Me yasa?"
Ta ce"Ba komai".
Ya ce"A'a ki dawo gida".
Ta ce"To" Ta ajiye wayar.
Ta ce"Kin ga bai bar ni".
Uwani ta ce"Ai dama ba lallai ba".
Maryam ta kwanta bacci ya ɗauke ta, saboda dama jiyan ba ta yi isasshe ba, sai yamma ta tafi, tare suka fita da Uwani ta ce za ta je gidan ƙawarta ta ji inda za a samu maganin.
Can wani ɗan ƙauye aka kwatanta mata wajen wani mai magani, washegari ta yi sammako ta karɓo, gidanta ta wuce kai tsaye ta kai mata, tare da bayanin yadda za ta yi amfani da shi, nan take kuwa ta fara sha da fatan Allah Ya sa ƙarshen wahalar kenan, sai dai jikinta ya yi sanyi ganin a ranar ma sai da ta yi.
A ranar da za ta karɓi girki kuwa har fargaba ta dinga yi na abin da zai iya faruwa, ta saka a ranta ba za ma ta yi baccin ba ballanatan ta yi fitsarin, suka kwanta lafiya ƙalau, can dai dare ya yi nisa bacci ya fara fizgarta sai ta tashi ta koma falo ta yi shimfiɗa ta kwanta, babu jimawa baccin ya ɗauke ta, kuma sai ga fitsarin, ta tashi a firgice, ta je ta wanke kayan, haka take yi a daren take wankewa da asuba sai ta yi sauri ta kwashe, ta gama shanyawa ta dawo ɗaki ta tarar da Aliyyu a falo, ya ce"Wai ke me yasa ba kya son kwana a ɗakin gadon nan? Ko dai guduna kike yi?"
Ta ce"A'a wallahi ba haka ba ne, me zai saka na guje ka? Kawai dai katifar ce ba ta yi mini daɗi".
"Hmm!" Kawai ya ce ya koma ɗaki ya ci gaba da baccinsa, ita ma ta yi wata shimfiɗar ta kwanta.
Tun Aliyyu yana ƙorafi har ya gaji ya ƙyale ta, sai dai idan zai neme ta ya kira ta ɗakin, a hankali ya gane kullum sa ta shanya kaya da daddare, sai abun ya fara ba shi tsoro da ya tuna ta taɓa yin fitsarin kwance a jikinsa, don haka yau ya ƙi yin bacci, har sanda ta yi fitsarin ta fita wankewa, da ta dawo sai ta tarar da shi a falo, ya ce"Maryam daga ina kike?"
Ta ce"Banɗaki na shiga".
Ya ce"Ko dai wankin dare da kika saba ba".
Sai ta sha jinin jikinta, ba ta damar musawa tun da ga kaya a igiya ya raba gardama, ya ce"Zauna za mu yi magana".
Ta zauna, kanta a ƙasa kunya duk ta ishe ta, ya ce"Maryam me yasa tun kafin auren ba ki sanar da ni kina da wannan larurar ba?"
Ta ce"Wallahi a gidan nan abun ya same ni, ni lafiyata ƙalau kafin na aureka".
Ya ce"Subhanallah! To amma kuma sai ki yi shiru? Wannan ai ba abin da za ki ɓoye mini ba ne, dole a nemi magani".
Ta ce"Ai akwai maganin da nake sha, ba a dace ba ne".
Ya ce"To ai sai a ci gaba da gwadawa har a dace, idan Allah Ya kaimu gobe zan cigita a samu wani, Allah Ya yaye".
Ta ce"Amin, na gode".
Ya koma ɗaki ya kwanta cike da damuwa yana ta tunanin mafita, ita kuma ta yi wata shimfiɗar ta kwanta.
Tun daga ranar Aliyyu ya duƙufa nema mata magani, haka ita ma Uwani ba ta fasa nemowa ba, Maryam ta yi ta shan magani a banza babu alamun sauƙi, damuwa ta fara zama a zuciyarta, kana kallonta za ka san ba ta cikin nutsuwarta, abinci ma ta rage ci, tun daga ranar da ya fahimci wannan larurar tata bai sake kiranta a shimfiɗa ba, a nashi tsarin sai sanda ta warke, ga tunanin yaranta, su sauran ana kawo mata su duk ranar Juma'a su wuni a nan, amma ban da ƴaƴan Alhaji, wanda kuma duk ta ma fi damuwa da su, saboda su ne ƙanana, kuma su ne ta san ta bar su a cikin ƙila wa ƙala, ba ta sake cewa a kawp mata su ba tun da ta ga yadda ta kaya a wancen lokacin, sannan Baba ma ya ce mata ta rabu da zancensu, ita uwa ce ta dinga yi musu addu'a kawai, su maza ne idan suka yi hankali dole za su neme ta, damuwar nan biyu ta sako ta a gaba duk sai ta fara rame ta rasa nutsuwarta, yayin da Lubabatu ta jingine ta a gefe, don ta san ta riga ta sallame ta, ko shiga harkarta ba ta yi, ta dai riƙe mijinta katamau.
A kwana a tashi sai da aka shafe wata uku ana magani a banza, zuwa yanzu Aliyyu ya riga ya ƙosa, Maryam ɗin duk ta fita daga ransa, gani yake kura da fatar akuya kawai ce kawai, dama can tana fitsarinta aka rufe masa ƙila shiyasa ma take rabuwa da sauran mazajen, ga shi babu biyan buƙata tun da ba ta samu ciki ba, gabaɗaya sai auren ya fita daga ransa, a ce ya ajiye mace kawai yana ciyar da ita yana kashe kuɗin magani, ko nutsuwa ba zai samu da ita ba ballabatana a sami ribar abun wato haihuwa?
Wata rana ya shiga ɗakinta tana zauna tana duba wayarta, ya ce"Maryam za mu yi magana".
Ta ajiye wayar ta ce"To ina jinka".
Ya ce"Dama ni na yi wani tunani ne, kin ga ko na kwanta a ɗakinki ba wani abu ne yake shiga tsakaninmu ba, illa na shaƙi zarnin fitsari kawai gari ya waye ba kaɗe rigata na fita, don haka na yanke shawarar kawai za ki haƙura da ranakun kwananki zan koma ɗakin Lubabatu har zuwa sanda za ki samu lafiya, sai a ci gaba da rabon kwanan".
Ranta ya fara ɓaci, ta ce"Aliyyu kawai ka faɗi abin da ka yanke kai tsaye ba sai ka ci mutuncina ba, a yaushe kake kwana a cikin zarni? Fitsarin nan idan na fahimci na yi ko minti ɗaya ba na ƙarawa nake fita da shi ba wanke na saka turare, amma ka ce kana kwana a cikin zarni? Babu koma duk yadda ka yanke ka yi kawai, ka je ka yi yadda ka tsara ni kuma Allah Ya ba ni lafiya".
Ya ce"Wannan fa rashin gaskiya ne zai sa ki ji haushin matakin da na ɗauka, tun da dai kin san na yi haƙuri, wata nawa ba mu haɗa shimfiɗa ba? Kuma ana magani abu yana gaba, gaskiya ni na gaji".
Ta ce"Wannan larurar a gidanka ta same ni fa, ya kamata ka yi mini uzuri, amma shikenan ka je ɗin Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Ta tashi ya fita, tun daga ranar shikenan bai sake kwana a ɗakinta ba, tana ji tana gani miji ya zama na kishiya ita kaɗai, ita dai aikinta a kawo mata cefane ta yi girki ta ci, kuma ko shigowa ɗakinta ya yi a tsaye yake yi mata magana ya fice ko zama ba ya yi, tun abun yana damunta har ta saba.
Da dai ta ga abun na gaske ne, sai ta koma ga Allah, ta daina bacci da daddare ta kwana tana sallah tana istikhara Allah Ya yi mata zaɓin alkhairi tsakanin auren nan da mutuwarsa, da safe sai ta sha baccinta don fitsarin sai a baccin dare take yi.
Uwani ta yi fama da ita kan ta dawo gida ta zauna har ta warke amma ta ƙi, a hankali ta fara jin auren ya fita a ranta tana jin rabuwar ita ce mafitarta, amma kuma ba ta so a ce ita ce ta nemi saki a wajen shi, saboda wani abu ne da ta saka a ranta ta daina shi, don ta yi a baya ba ta ga ranarsa ba, to da yake Allah ta bawa zaɓi sai ga shi shi Aliyyun da kansa ya ji a ransa shi ma rabuwarsu ita ce maslaha, saboda gani yake ita ɗin kaya ce kawai a gare shi, gara ya rabu da ita ya huta, don ba ta tsinana masa komai sai dai ya dinga ci da ita.
Watarana da safe tana kwance tana bacci ya shigo ɗakinta, hannunsa ɗauke da farar takardar da ya rubuta saki ɗaya, kamar ya tashe ta ya yi mata bayanin dalilinsa na yanke wannan hukuncin, sai kuma ya ajiye mata a gefen kanta ya fice. Wajen sha ɗaya da rabi ta tashi daga baccin, ta ci karo da takardar, ta ɗauka da mamakin abin da ya kawo takardar nan ɗin, tana dubawa ta ga _Ni Aliyyu na saki matata Maryam saki ɗaya_. Zuciyarta ta doka, amma daga nan ba ta ji wata damuwa ko tashin hankali ba, ta ce"Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Ta ɗauki waya ta kira shi, bai ɗauka ba, hakan ya tabbatar mata da gaske wannan saƙon nashi ne, ta tashi ta haɗa kayan sakawarta ta rufe ƙofar ɗakin ta kama hanyar gida.
Uwani tana banɗaki Maryam ta shigo gidan, tana shiga ta wuce ɗaki kai tsaye, ta kwanta ta ci gaba da baccinta, Uwani ta leƙa ɗakin don ta ji sallamarta, tana ganin akwati ta san abin da ya faru, ta ce"Maryam, lokaci ya zo kenan".
Maryam da bacci ya fara ɗaukarta ta ce"In sha Allah hakan shi ya fi alkhairi, kuma ni dai daga yanzu na gama aure".
Wani abu da ya ba ta mamaki, a yau ƙalau ta kwana a gidansu ba ta yi fitsarin ba duka tsayin daren, tun asubar ta faɗawa Uwani, Uwani ta yi murmushi ta ce"Ai dama na faɗa miki, yanzu tun da kin bar mata mijin ai dole abun ya karye, wata kishiyar fa sai dai ki haƙura ki bar mata miji kawai".
Maryam ta jinjina kai tana sake jin tsoron Allah yana shigarta, da kuma tsoron kishiya, ta saka a ranta ko da za ta sake yin wani auren ba za ta ƙara zama da kishiya ba har abada.
08028966105
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
29
Tun daga ranar wannan larurar ta barta, bayan sati ɗaya aka kwashe kaya aka siyar. Cikin watannin da suka gabata Maryam ta koma ga Allah ta ƙarfafa ibadarta saboda ta fara zargin kanta da sake da ibada shiyasa har sihirin ya yi tasiri a kanta, kullum cikin yi wa ƴaƴanta addu'a take ta nema musu rayuwa mai inganci. Sanda ta gama idda maza suka fara sallama ba ta bi ta kan kowa ba, duk wanda ya yi zuwa ɗaya ba ta bari ya yi na biyu, saboda duk masu mata ne, ita kuwa babu tsautsayin da zai saka ta sake auren mai mata, ta manta cewa ba iya kishiya ce kaɗai matsala a gidan aure ba, an yi dubu ka ga mai kishiyar tana zaune lafiya, mara kishiyar kuma auren ya ƙi daɗi, ko da yake Hausawa sun ce ruwan da ya dake ka shi ne ruwa!.
Tun da Sauda ta ji Maryam ta yi aure hankalinta ya ƙara kwanciya, sai ta daina ƴan abubuwan da take yiwa Alhaji don tsayar da hankalin shi a kanta ita kaɗai, sauran ado da kwalliyar da take yi da nuna soyayya su ma duk sai ta watsar, tana tunanin ai shi kenan ba zai sake tsiro da zancen wani auren ba.
Watarana cikin watan Ramadan yaran gidan suna zaune a falo da rana, Nana ta aiki Hasan ya je kitchen ya ɗakko mata cokali, ya shiga Momy tana ciki ta sauke ruwan zafi kenan daga kan gas, ba ta san da mutum a bayanta ba, juyowar da za ta yi cikin tsautsayi tukunyar ta kufce ta sheƙawa yaron a jikinsa, ihun da ya kurma ya janyo hankalin duka mutanen gidan, ban da Sauda dake ɗakinta tana baccin rana, a gigice Momyn ta fito tana kiran babar tasu da faɗin"Hasan ya ƙone!".
Sauda ta fito da sauri, gabanta yana faɗuwa, sai da ta tsorata ganin jikin yaron har ya saluɓe ya yi ja, ta fara faɗin"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Uban me ya kai yaron nan kitchen? Na shiga uku! Ta ina zan fara jinyar ƙuna?"
Wacce take taya ta aikin abinci ce ta shigo falon jin hayaniya, tana ganin yaron da yake ta kuka kamar ransa zai fita ta ƙaraso da sauri tana salati ta ce"Haba Hajiya ya za ku tsaya surutu, ƙuna ce fa".
Sauda ta ce"To ni me zan yi masa? Ban san yadda ake yi ba, sai dai idan ya dawo ya kai shi asibiti".
Matar ta ce"Na san gidan wani sharifi da yake yin tofi bari na kai shi".
Sauda ta ce"Ina zuwa".
Ta yi zaton ma hijjabi za ta sako su tafi, sai ta fito ta ba ta dubu ɗaya wai kuɗin tofin ne, ta ɗauke shi, ta hau adaidaita sahu ta tafi, har ƙwalla take yo saboda tausayin yaron, ba tun yau ba ta lura da yadda ake nuna musu bambanci shi da ɗan'uwansa a gidan, kamar wasu agola, aka yi masa tofi aka ba da maganin da za a saka masa ta koma da shi gida, a ranar Hanne mai kula da su a gidan ta kwana tana ta kula da shi, sam ba su yi bacci ba, ita ce ta fi kowa sanin yadda ake yi wa yaran a gidan, har mamaki take yi wannan wace uwa ce ta tafi ta bar yaranta cikin wannan halin ko waiwaye ba ta yi? Ita zargi ma take yi sane aka ƙona shi, don haka wannan karon ta saka a ranta sai ta nemo uwar yaran nan ta karanta mata halin da suke ciki, ta dai san sunanta Maryam, a irin zagin da Sauda take yiwa yaran tana yawan cewa "Sai dai ku yiwa uwarku Maryam ba ni ba".
Da Alhaji ya dawo ya ga ƙunar sosai ya shiga damuwa, ya ce sai an kai shi a sibiti, suka je aka rubuta masa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 21