sai ka sake ni, ke Fatima wallahi ba za ki koma ba, dole sai ya sake ki, ai miji goma ba uba goma ba ne".
Uwani ta ce"To sai kuma Allah Ya sa ba ke ba ce! Ina ruwanki a maganar nan ma? Idan ke Allah Ya ba ki farinjinin zuwan masu auren ita fa? So kike ta kashe auren ta zo ta zaune mini a gida? Ko kuwa so kike ta dinga yawon aure-aure kamar yadda kike yi ita ma a saka ta a lissafi?"
Duk da kallon uwa Maryam take yiwa Uwani amma sai ta ji kamar idan ita ce ta haife ta ba za ta faɗa mata haka ba, ta yi ɗan murmushi ta ce"Ni ma ƙaddara ce, da kuma sharrin magauta masu fuska biyu, amma in sha Allah zaman gidana ya kusa ƙarewa, kuma zan yi auren da zan zauna, har masu lissafin su manta da ni".
Daga haka ta fice daga ɗakin, jikin Uwani ya yi sanyi ta shiga auna maganganunta, maganar Fatima ce ta katse mata tunanin inda take cewa"Wallahi babarmu ba zan koma ba har abada, ko bai sake ni ba ba zan koma ba".
Uwani ta ce"Abin da za ki duba..."
Ta katse ta da faɗin"Ni ba zan duba komai ba, ta bakin Maryam ne ai miji goma ba uba goma ba ne!".
Daga haka ta nemi waje ta kwanta. Tun daga nan sai aka shiga case ɗin Fatima, mijin yana ta zuwa biko ta kafe kan ba za ta koma ba, a gaban Uwani Maryam take ƙara zugata baƙinciki kamar ta rufe Fatiman da duka, ƙarshe dai sai da mijin ya gaji ya sake ta, ta shiga sawun zawarci.
Tun wannan furucin da Uwani ta yi na ana lissafin auren Maryam maganar ta tsaya mata a rai, don haka yanzu auren take buƙata cikin gaggauwa ko don ra bar mata gida, sai dai fa ba ta jin za ta sauka daga tsanin da ta hau na ƙin auren mai mata, don haka dole ta bazama ta nemi wanda ba shi da mata, haƙiƙa duk saurayin da ya yi gangancin zuwa wajenta to fa ya zo kenan zuwan sojan badaskare, don kuwa sai ta laƙe shi tsaf ta aure shi, auren saurayi ba abu ba ne mai sauƙi ga bazawara mai haihuwa huɗu irinta, dole sai ta fara ɗaukar wanka ta nuna cewar har yanzu da ƙwarinta, da sauran ƙuruciyarta, don haka ta koma bussines ɗinta don samun kuɗin shiga ta fara shiga tana fita, tana kwalliyar kece raini, maza suna ƙara tunkarota tana ƙara dakatar da su, a haka har burinta ya cika, wani saurayi mai shagon provition a nan ƙasan layinsu ya ƙyalla ido ya ce ya ganta, ya ce yana sonta.
Usman wanda aka fi kira da Usi, saurayi ne mai shekara talatin da biyu, irin samarin nan ne ƴan ƙarya masu ji da gayu, ga wani abu davya zame masa tamkar jarabta ko ma ace musiba wato son mata, da ya ga ƴar buduruwa mai ji da gayunta to kuwa ba ya ƙasa a gwiwa wajen zuwa ya ce yana sonta, ya gama ginin gidansa tass, amma sam babu shirin auren a lissafinfa, a cewarsa aure tsufar da shi zai yi, gara sai gama cin samartakarsa da tsinke tukunna, matan da suka mato akan Usi suna da yawa, haka matan da ya yaudara da waɗanda yake kan yaudara a yanzu ba za su lissafu ba, kai kace laƙanin farinjini yake amfani da shi da wuya ya je wajen mace ta ce a'a, ƴan mata dai kwando-kwando suna nan a wajensa wayarsa kuwa sai Allah kawai.
Sanda suka sasanta da Maryam ya fara zuwa zance, waɗanda suka san halinsa suka dinga zuwa suna bata shawarar ta daina ɓata lokacinta, amma ita ta ce ta ji ta gani, Baba ma yana kallonta ya zuba mata ido, saboda tun da ta nuna masa ƙiri-ƙiri ba za ta koma gidan Alhaji ba sai ya sallamawa maganar aurenta, don ya ga gudun ruwanta.
Cikin lokaci ƙanƙani Maryam ta yi zurfi a ƙaunar Usi, saboda salon soyayyarsa na da ban ne, jin ta take ma tamkar ba ta taɓa soyayya ba sai yanzu, don haka ta saka a ranta ita sai yanzu ma za ta yi aure, yanzu ta ga mijin aure, don gidansa ma da ya nuna mata a wayarsa har ta gama kasafta yadda za ta jera kayanta.
Ba ta tabbatar da maganar mutane ba sai da ta yi wa Usi zancen ya kamata ya turo a yi maganar aure, a nan ta ga ya fara kwana-kwana, duk inda ya yi sai ta taro shi, idan ya kawo hujja ta raunanata, ƙarshe dai da ta ga har ya fara rage kiranta yana son baya-baya da ita sai ta nemi mafita, ta daɗe da jin labarin wata mata shahararriyar mai magani mai suna Hajiya Meerah, wacce take da ingantattun magungunan mallaka kala daban-daban, ciki har da na kafar da saurayi mai tsalle-tsalle wanda magunguna ne kawai za ta ba ka ka yi amfani da shi, idan saurayi ya zo, ya zo kenan duk taurin kansa dolensa ya aureka, haka idan miji ne mai tsalle-tsallen neman mata ko kula ƴan mata shi ma ki ƙamar da shi a kanki, ya manta da kowa da sai ke,(Ga lambar Hajiya Meera idan da mai buƙata 08142800199).
Kamar wasa sai ga Usi ya nutsu ya hau kan layin Maryam, babu shiri ya turo iyayensa aka saka ranar aurensu wata uku, kowa yana ta mamakin a ce duk farinjininsa da ruwan idonsa ya ƙare akan bazawara wacce ta yi haihuwa huɗu, ita dai Maryam ta toshe kunnuwanta ta fara shirin amarcewa.
Sosai Uwani take baƙincikin auren da Maryam za ta yi, inda a ce babu Fatima a gabanta da sauƙi, to ita ga ta nan babu mashinshinin, da mutum ya fara zuwa sai ta ji shiru ya daina, da ta matsa mata da kurarsu da take yi sai ta ce mata duk fa ba auren ne yake kawo su ba, idan kuma so take ta biye musu ta lalace sai ta ci gaba da kula su, abun duniya ya ishi Uwani, a ganinta me yasa ita Maryam ba ta rasa na auren? Ga shi yanzu ma wai saurayi za ta aura, haka dai ta zubawa sarautar Allah ido.
Alhaji bai tashi sanin Maryam ta tsayar da wanda za ta aura ba, sai da auren ya rage sati huɗu, shi ma ya zo ganin yaransa ne da suka gaisa da Baba yake sanar masa, a ranar ya kwana cikin damuwa, ya kuma yarda Maryam dai da gaske take, don haka ya sallama, ya kuma ɗaura niyyar sai ma ya riga ta yin aure. Akwai wata mata abokiyar kasuwancinsa, mai kamun kai da kirki sosai, ta daɗe tana burge shi, yana yabawa da halinta ƙwarai, ya jima da sanin ba ta da aure, har ma yana mamakin abin da ya hana ta samun miji har lokacin, don haka ya tuntuɓe ta da zancen so, Halima ta sanar da shi ita bazawara ce, ta taɓa yin aure, mutuwa auren ya yi saboda bincike ya tabbatar da ba ta cikin mata masu haihuwa, wannan dalilin ne ya sa ta yankewa kanta hukuncin ba za ma ta yi auren ba gabaɗaya domin gujewa gori da ganin wukaƙanci, Alhaji ya ji tausayinta sosai, nan ya bata tabbacin indai tana son shi zai aure ta ya rayu da ita da matsalarta har abada ba tare da gajiyawa ba, sannan zai ware mata gidanta ita kaɗai domin gujewa gorin da take gudu, kuma sannan zai ba ta kyautar yara maza har biyu ta riƙe su har ƙarshen rayuwa.
Ina ruwa yake Halima ta zuba a ƙasa ta sha? Tun kafin ta yi aure ita mace ce mai masifar son yara, don haka da ta fahimci ba ta haihuwa ta shiga damuwa sosai, ta shiga ƙunci da farko, amma da ta mai da lamarinta ga Allah sai ya cire mata damuwar, kuma ya sassauta mata zuciyarta, wannan magana ta Alhaji dole ta karɓe ta hannu biyu-biyu, domin mai ƙaunarsa da sonka da arziƙi ne kaɗai zai yi maka wannan, don haka nan take ta amince za ta aure shi.
Farinciki a wajen iyayenta ba ya misaltuwa, Alhaji ya nemi a saka wata ɗaya, ya ce shi zai yi mata komai na buƙata, nan da nan ya fara shirin aure, har ya sanarwa Inna yadda ya tsara, cewar ita zai bawa ruƙon Hassan da Husaini kuma ta amince, Inna ta ce "Allah Ya sanya alkhairi" Saboda aurensa da Maryam da albarkarsa ya saka ta daina nuna ba ta son ƙarin auren shi, domin kar ta je rabo ya kashe ta.
Sanda Sauda ta ji maganar auren nan ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba, ta birkice ta fara yi masa hauka, shi kuwa ko bi ta kanta bai yi ba, ya ci gaba da hidamar aurensa, dama akwai gidan da ya gina da niyyar saka ƴan haya, kaɗan ya rage a gama aikin, a nan zai saka Halima.
Saura sati biyu auren ya je ya kai wa Maryam katin gayyata, ya kuma yi mata bayanin idan aka yi auren zai ɗauki Hassan da Husaini ya bawa amaryar za su koma ƙarƙashin kulawarta, duk da ita ce ta ƙi shi sai da jikinta ya yi sanyi, ta nuna ta yi farinciki da hakan, har ma ta karɓi lambar Halima ta ce za ta kira ta ta yi mata godiya kuma ta bata amana, tun daga wayar da suka yi da Halima ta gane za ta samu tarba mai kyau, don haka ta nemi kwatancen gidansu ta je har gida tare da yaran, ai kuwa sun samu tarba mai kyau, Halima farinciki take yi sosai na za a bata yara sun zama nata, ita ce uwarsu ita ce za ta yi musu tarbiyya, farinciki take sosai, ganin ashe tana da rabon a kira ta da sunan Umma ko Mama, (Lallai haihuwa rahama ce ƴan'uwa, kuma kyauta ce maɗaukakiya da Allah Yake bawa wanda ya so)
An ɗaura auren Alhaji ranar Asabar, na Maryam kuma ranar Lahadi, ranar Litinin Alhaji ya zo ya kwashi ƴaƴansa ya kaiwa amarya, da yaƙinin za ta kula da su da zuciya ɗaya.
Cikin satin auren Sauda ta kasa jurewa, ta shiga damuwa sosai, suka yi shawara ita da ƙawarta Lubabatu da take zugata akan zuwa wajen bokaye suka shirya za su je ta rakata don a san yadda za a yi a daƙile auren, gidan bikin ƙawarsu suka ce za su je, suka kama hanya suka tafi, a hanyar dawowarsu ne motarsu ta yi hatsari mummuna, Sauda da direba ne kawai suka yi rai, amma Lubabatu nan take rai ya yi halinsa, ta tafi ta bar duniyar, ta tafi inda babu dawowa ballantana ta hana Aliyyu zama da wata macen bayan ita.
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin haɗarin motar ya karaɗe gari, Allah ma Ya sa irin direbobin nan ne masu ɗaukat sunan mutum da lambar waya kafin ka shiga, don haka aka ɗauki lambar Alhaji Hamza aka kira shi aka sanar da ni haɗarin da ya ritsa da wata mai suna Sauda, da kuma asitibitin da take, ana buƙatarsa cikin gaggawa, hankali a tashe ya tafi asibitin, yana tafe yana mamakin abin da ya kai ta hanyar ƙauyen da aka ce abun ya faru?
08028966015
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
31
Sanda ya ƙarasa asibitin ya ga Sauda sai da tsoron Allah Ya ƙara shigarsa, ya barta a gida lafiya ƙalau yanzu ta zama kamar ba ita ba, fuska ta yi suntum ta daddauje da ƙyar ma ake gane ta, ta samu karaya biyu a ƙafa ɗaya, hannu ya karye, ga raunuka munana, an yi mata allurar bacci ma ta ƙi ɗaukarta sai sambatu take yi tana cewa"Ka yafe mini Alhaji, na tuba, wallahi na tuba tsautsayi da zugar ƙawaye ne ya kai ni bin shawarar zuwa gidan boka, ka cewa Maryam ta yafe mini, yanzu na yarda zan zauna da duk wacce ka aura da zuciya ɗaya".
Kasa jure sauraron maganganun ya yi, ya fice daga ɗakin, har hawaye ya yi na tausayin halin da take ciki, da kuma rayuwar shirka da ta saka kanta saboda duniyar nan da ba matabbata ba, idan don ta shi ne ya yafe mata ko don izina da ta gani, amma shin Allah zai yafe mata? Maryam za ta yafe mata?
Zuwa dare duk ƴan'uwa an zo asibitin, sai shi ne yake ta cewa wani magani ta je karɓowa a ƙauyen abun ya ritsa da ita, ƴaƴan gidan Halima ya kaisu suka kwana a can, washegari ya canza mata asibiti, aka mayar da ita na kusa da su ana bata kulawa sosai. Kullum sai Halima ta yi girki ta kai asibitin sosai take tausayawa Sauda har ma da yaran bakiɗaya, har ta samu lafiya aka sallameta, sai wata ƴar'uwarsu ce ta dawo gidan da zama tana ci gaba da kula da ita, kullum ne sai ta ci kuka, kuma sai ta yi nadamar biyewa sharrin zuciya, ga shi dai Alhaji yana zaune da matarsa lafiya ƙalau, kuma ba ta da yadda za ta yi ta hana su farinciki, ita kuma ta rasa lafiyarta da martabarta a idon mijinta, duk da ya ce mata ya yafe mata amma ta ƙi samun nutsuwa.
INA MARYAM AMARYA?
Sosai ta ɗaura ɗamarar zaman aure a wannan karon, ta ɗaura niyyar kyautatawa Usi da iyayensa ta yadda za ta mallake zuciyarsa daga sauran mata, satin farko na auren an yi shi lafiya ƙalau, cikin soyayya da begen juna, kafin Maryam ta fara binciken wayarsa nan ta tarar da saƙonnin mata iri daban-daban, kuma yana biye musu suna fira sosai, ga kira ma da ta duba suna yawan yin waya, cikin whatsApp ɗinsa kuwa ba a magana, don nan ne wahen baje kolin ƴan'matansa, ta dinga duba chart, har da wacce yake ta lallaɓawa yana faɗa mata shi fa wannan auren bai san ya aka yi ya yi shi ba, yana faɗa mata biyayya kawai ya yi, iyayensa ne suka yi masa auren dole, abun ya ɓata mata rai sosai, sauƙin abun ɗaya ma ba ya chart ɗin banza, hakan ya ba ta tabbacin masifar son matan ne kawai a jininsa, amma ba ya nemansu. Ba ta ajiye wayar ba sai da ta kwashe lambobi sun kai goma, a wayarta, tagging ɗinta na farko ita ce wannan yarinyar da yake faɗawa auren dole aka yi masa.
Duka ya saka wayar a caji ya tafi sallar asuba ne ta yi wannan binciken, ta ajiye wayar tsam kamar ba ta yi komai ba, ko da ya dawo ba ta canza masa fuska ba, ba ta nuna ba sa wata alama da za ta sa ya gane tana fushi da shi ba, da safe ƙarfe bakwai ya fita shago, dama daidai lokacin yake fita, sai ƙarfe tara ya dawo ya ci abinci, idan zai je kasuwa sai ya tafi, yana fita ta ɗauki wayarta ta fara da kiran ta farkon, suka gaisa ta ce"Salma ce?"
Ta ce"E ni ce".
Ta ce"Dama ni ƙanwar saurayinki Usman ce, Usi ina ta so na zo gidanku mu gaisa ya hana ni zuwa, shi ne yanzu na ɗauki lambarki bai sani sai ki kwatanta mini na zo".
Salma ta ɗan yi jim, kafin ta ce"Ai ni a yanzu ba ni da wata alaƙa da yayanki, tun da dai ya yi aurensa".
Maryam ta ce"Haba Anti Salma don Allah ki tausayawa Yaya Usi, wallahi ke yake so, wacce ya aura ɗin ba sonta yake ba, da ƙyar ma fa ya koma gidan, ranar da aka ɗaura auren ma a gidanmu ya kwana, kuma ni ina da hanyar da zan bi na raba su, shiyasa na ce zan zo mu tattauna, amma don Allah kar ki faɗa masa".
Salma ta ce"Ok, zan turo miki kwatancen yanzu".
Maryam ta ce"Na gode".
Kafin ta ajiye wayar har ta turo mata, ta tashi ta saka hijjabi ta ɗauki jaka ta fita ta kulle gidan ta kama hanya, har wani tafasa zuciyarsa take yi, saboda yadda take mutuwar son mijinta da kuma yadda ta tsani kalmar kishiya, tiryan-tiryan ta bi kwatancen ya kaita gidan Salma, ta shiga da sallama, ta tarar da wata buduruwa tana wanke-wanke a tsakar gida, ta amsa mata sallamar tana yi mata kallon rashin sani, don ko da ta turawa ƙanwar Usi kwatance ba ta yi zaton a yau za ta zo ba, Maryam ta ƙaraso inda take ta ce"Don Allah ke ce Salma?"
Ta ce"E ni ce".
Babu zato ta ga Maryam ta ɗaga hannu ta sharara mata mari, ta tsaya mamaki ta ƙara mata, buduruwar ta kawo hannu za ta rama Maryam ta cafe hannun ta ɓurɗe sannan ta cakumeta, ta watsata kan kayan wanke-wanke, suka fara casuwa, ƙarar kwanukan ne ya ankarar da kakar Salma gidan babu lafiya, ta fito da lalube kasancewarta makauniya tana cewa"Salamatu, lafiya? Me yake faruwa?"
Salma da take faɗan ceton kanta don har yanzu ba ta san dalilin damben ba, daidai sanda Maryam ta haɗa ta da bango ta shaƙe ta ce"Ni ma ban santa ba, wata ce ta shigo ta fara dukana".
Iya ta fara salati tana lalube tana cewa"Ta ina? Me kika yi mata?"
Maryam ta ce"Kaka gargaɗi na zo yiwa ƴarki, wallahi idan ba ta fita sabgar mijina ba gobe idan na zo ke zan daka, ita kuwa sai na yi mata lahanin da babu wanda zai yi sha'awar kallonta".
Tana hararar Salma kamar idanunta za su zobo ta ce"Ni matar Usi ce, kuma ƙarya yake yi miki da ya ce auren dole aka yi masa, ba fi ƙarfinsa ne dai kawai, kuma gidana ramin kyra ne, kar ma ki yi sha'awar shigowa don kuwa za ki zama ƙaramar bazawara".
Iya ta fara salati jikinta ya hau tsuma ta ce"Yarinya ki yi haƙuri don Allah, indai Salma ce babu ita babu mijinki".
Maryam ta ce"Kar ma ta fasa, wallahi idan na ƙara ganin sun yi waya ko ya zo ta fita, idan na zo ta kanki zan fara".
Salma da ta sha duka sosai duk da ita ma ta daki Maryam ɗin, da fasasshen bakinta ta ce"Idan Allah Ya yi Usman mijina ne ke ba ki isa ki hana komai ba".
Iya ta yi farat tana yi mata daƙuwa ta ce"Ungo nan!Na ce gidanku, babu ƙaddarar da za ta sa ki auri mijin mata irin wannan, babu mai nakasa mini ke a banza".
Salma ta ce"Ai wallahi Iya sai na aure shi, idan kin ga ban auri Usi ba to mutuwa na yi".
Tana rufe baki Maryam ta yi kukan kura ta yi kanta, saboda kalamanta jinsu ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, Salma da sai yanzu ta san dalilin faɗan ita ma ta zage suka ci gaba da bawa hammata iska, tun Iya tana yi musu magiya har ta fita da lalube ta fara kiran maƙota tana"Jama'a ku kawo mini ɗauki, ga shaiɗaniya ta zo mana har gida za ta kashe mini jika".
Maryam da ta ji haka sai ta haƙura ta fice daga gidan, tana adaidaita sahu tana ta huci, ta koma gida fuska duk a yaƙushe an kumbura mata baki, sai a lokacin ta duba wayarta ta ga miss call ɗin Usi, ta san ya zo gidan nan ne ya tarar ba ta nan, shi kuwa mamakin inda ta tafi ne ya hana shi zaman shagon, ya sake dawowa gidan, ya tarar da shi a buɗe, ya shigo da sallama, yana kallonta gabansa ya faɗi, don kallo ɗaya ya yi mata ya san ba lafiya ba, ya ce"Subhanallah! Maryam daga ina kike? Ina kika je ba tare da izinina ba?"
Ta yi masa wani kallo mai cike da jin haushi wanda kishin da yake cin zuciyarta ne ya haddasa shi, ta ce"Daga gidan su Salma nake, yarinyar da ka faɗawa auren biyayya ka yi da ni, yanzu dama abin da kake yi kenan, mata kake kulawa har kana faɗa musu ba sona kake ba?" Sai ta fashe da kuka, saboda bil haƙƙi take jin mugun kishin shi a zuciyarta.
Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kika je gidansu Maryam?"
A fusace ta ce"Na je ɗin, kuma ɗaya bayan ɗaya sai na bi duka shegun da kake kulawa, ina alƙawarin da ka yi mini na daga ni babu ƙari? To wallahi ba ka isa ka auro wata, babu wacce za ta zo ta raba ni da kai".
Ransa ya ɓaci ya ce"Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, idan kika sake yi mini irin haka sai kin sha mamaki!".
Ta ce"Ai kuwa indai ba ka fasa ba ni ma ba zan fasa ba, sai dai mu zuba ni da kai".
Ya zaro ido ya ce"Da wa za ki zuba? Ai kuwa sai dai ki zuba a gidanku wallahi".
Gabanta ya faɗi, ta yi shiru ba ta sake cewa komai, ya fice yana ta masifa.
Amma zuwa dare da ya dawo sai ta nuna masa komai ya wuce, ta tare shi da wani nau'in soyayyar, shi ma da yake yana sonta sai ya saki jiki ya manta da komai, suka shirya.
Haka ta dinga bin lambobin tan kira amma idan ta yi musu irin ƙaryar da ta yi wa Salma sai ta ga sun ƙi yarda, wasu ma sai dai su ƙare da zage-zage, saboda ya riga ya sanar da su akwai wata yarinya da ta ɗauki wayarsa ta ɗauki lambobi take yin hakan.
Bayan kwana biyu kamar komai ya wuce, watarana Usi ya tashi da zazzaɓin da har ya kwana uku bai fita ba, Maryam tana ta hidima da shi, da ƴan'uwansa masu zuwa dubiya, gabaɗaya ta siye su da kyautatawa musamman mahaifiyarsa da take son Maryam ɗin kamar ƴarta. Da yamma tana girkin dare tana tsakar gida tana daka, shi kuma yana cikin ɗaki sai ga sallama da shigowar wata matashiya, ta amsa tana zaton ko daga maƙota ne, sai dai fa fuskarta a haɗe take, saboda ba ta ƙaunar abin da zai sa ƴan mata su dinga shigo mata gida, tun da ta san halin mijinta ba ya gani ya ƙyale, shiyasa duk ƴan'matan da suka shigo ba ta ba su fuskar dawowa ba.
Ta ce"Lafiya? Daga ina?"
Buduruwar ta ce"Nan ne gidan Usi?" Usi da yake jiyo su daga ɗaki gabansa ya faɗi, don sarai ya gane muryar yarinyar.
Maryam ta saki dakan da take yi ta riƙe ƙugu ta ce"E nan ne, mene ne? Waye yake nemansa?"
Buduruwar ta ce"Wajen shi na zo".
Maryam ta jinjina ƙarfin hali irin na yarinyar nan, sai ta danne ta saki murmushi ta ce"Ok, bacci yake yi, shiga daga falo bari na kira shi".
Babu musu buduruwar ta shiga, Maryam ta ciji yatsa zuciyarta na azalzala, ta kalli gabas ta kalli yamma, kudu da arewa tana neman abun duka, ba ta da niyyar yin kisa shiyasa ba za ta ɗauki taɓarya ba, can dai Usi da ya ji shiru sai ta tashi ta leƙo tsakar gidan, daidai sanda Maryam ta shiga falon ta banko ƙofar, kai tsaye wayoyin jikin TV ta fuzgo, ta yo kanta ta fara zabga mata, ai kuwa ta miƙe ta fara ƙoƙarin ramawa, amma ina da ƙarfin zuciya Maryam take zane ta ta kasa kataɓus sai ihu take yi tana zaginta.
Usi ban da salati babu abin da yake yi, ya fara buga ƙofar da ƙarfi yana cewa"Ke Maryam ba ki da hankali? Ki buɗe"
Kamar kurma haka ta zama, duk bugun da yake yi ba ta buɗe ba, sai da ta yi mata lilis sannan ta buɗe ta hankaɗata waje, ko hakarta ba ta tsaya ɗauka ba ta fice, Maryam ta bi ta da ita ta jefa mata tana ƙara zaginta.
Tana dawowa Usi ya ce"To ai sai ki ni ta ke ma ki tafi gidanku, don wallahi ba zan iya ba, ba za ki tada mini hankali ba, akan ki aka fara kishi? Ko da na yi miki alƙawarin ba zan yi miki kishiya ba ai ban ce ba zan kula ƴan mata ba, kuma ma na faɗa miki duk tsofaffi ne".
Ta ce"Wannan kai ta shafa, wallahi duk shegiyar da na san kuna soyayya da ita sai na yi maganinta".
Ya ce"Ai ni za ki yi magani ba ita ba!".
Ta yi ƙwafa ta ci gaba da dakanta.
Ya ce"Na ce fa ki tafi gidanku!".
Ta ce"Babu inda zan je".
Ya ce"Wallahi sai kin tafi, don kina da buƙatar a ƙara sanar da ke waye namiji".
Ta ci gaba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 21