Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta duba akwai cefanen komai, ta shiga tunanin yadda za ta yi girkin, har ita da Sauda su tara kenan, ban da yara, ba ta san adadin yaran ba, amma ta san dai har yaran gidansu sun fi goma kenan, ta ce"Tabɗijan!" Tana mamakin yau ita ce za ta yi abincin wajen mutum ashirin, ko sati ba ta yi ba a gidan miji, ta yi huci mai zafi, ta shiga duba tukwanenta ta ga ai babu ma wacce za ta isa wannan girkin, amma ta ga Sauda tana da manyan tukwane, don haka kawai sai ta ɗauki babbar tukunya ta wanke ta fara hada-hadar gyara kayan miya. Tana cikin aikin Sauda ta shigo, ta kalli tukunyarta da ke gefe ta ce"Malama wannan tukunyar me za ki yi da ita kika ɗakko mini?" Maryam ba ta kalle ta ba ta ce"Ba ni da babbar tukunyar da zan yi girki mai yawa haka". Sauda ta ce"Ai kuwa sai dai ki bar girkin idan sun zo sai ki sanar da su iyayenki ba su siya miki tukunyar girkin baƙi ba". Ta ɗauki tukunyarta ta mayar inda take, tana cewa"Wallahi inda kin ɗora sai na zubar da ko me na tarar a ciki, babu wannan cin albarkacin a tsakaninmu kowa ya yi ta kansa!". Maryam ba ta kula ta ba, da ta yi tunanin ta raba girkin gida huɗu tun da gas ɗin mai huɗu ne, sai kuma ta ga wahalar da kanta za ta yi, don haka ta kira Uwani a waya, ta ɗaga suka gaisa ta faɗa mata komai, Uwani ta ce"To yanzu ya kike so a yi?" Maryam ta ce"Ki aiko a kawo mini babbar tukunya, idan an kwana biyu zan siya ni ma". Uwani ta ce"Kina nufin da gaske girkin za ki yi musu? Saboda an mayar da ke baiwa daga zuwanki gidan za ki fara girkin mutum ashirin?" Maryam ta ce"To ƴan'uwanshi ne fa, kin ga dama ba wai so na suke yi ba, yanzu ko yaya aka samu matsala sun samu abun faɗa". Uwani ta ce"To su faɗa mana! Ba sai ki ce ta ƙi ara miki tukunyar ba ne, yaushe kika fara tsoron miji ma ballantana danginsa?" Maryam ta ce"Ni dai babarmu ki taimaka ki aiko mini yanzu kawai don Allah". Ta ce"To ai shikenan, ashe kuwa yanzu za ki bushe ki zama ƙashi, tun da dai bauta kike yi a gidan auren". Maryam ta ce"Ina jira don Allah". Babu jimawa kuwa aka buga gidan, Maryam ta fita ta karɓo tukunya, ta ɗora girkinta. Ko da suka zo ta fito ta yi musu sannu da zuwa ta gaishe su, suna amsawa a daƙile, ta dinga zubo abinci sai da ta sallami kowa, cincin da dubulan ɗinta kuwa duka ta juye musu, sannan ta shige ɗaki don ta ga hankalinsu ba ya kanta, firarsu kawai suke yi da Sauda. Sai da za su tafi ta fito ta yi musu sallama. Sai bayan magriba ta dafa jollop ɗin taliya suka ci, Sauda tana ta mitar gishiri ya yi yawa, alhalin babu wanda ya ji hakan sai ita, Alhaji dai bai ce komai ba, dare ya yi ya kwana a ɗakin Maryam. Washegari yaran suna dawowa daga boko ta haɗa musu kaya a jaka ta tafi kai su gidan Inna, bayan sun gaisa Inna ta ce"Ya na ganku da jaka? Ba dai yarinya ƙarama ta gagare ki ba?" Sauda ta ce"A'a fa, wallahi yaran ne ake firgita su da daddare, tun ranar da na koma shikenan dare yana yi sai su ce aljanu suke gani, haka nake kwanan zaune ina yi musu addu'a, Inna kin ga idona duk sun faɗa saboda rashin bacci, shiyasa na ce yau su zo nan su kwana ko na samu na rage baccin". Inna ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wata sabuwar fitinar ce kuma ta ɓullo? To aljanu kamar yaya?" Sauda ta ce"Ga shi nan dai, ni sai nake ganin kamar ture aka yi musu". Inna ta ce"Tabbas kuwa, tun da tun farkon gidan nan ba a taɓa jin an ga wani abu ba, sai yanzu rana tsaka da baƙuwa ta zo? A lallai dole mu tashi tsaye, Hamza ya ɗakkowa kansa masifa". Ta ce"To bari su kwana a nan ba gani, indai ba su ga komai ba kin ga a gidan ta ƙulla tsiyar ba a jikinsu, oh! Idan mutum bai zauna da kishiya ba bai ga rayuwa ba, ki yi haƙuri kin ji Sauda, wataran sai labari". Sauda ta marairaice kamar abar tausayi, a nan ta wuni kuma ita ce da girki, Maryam ta yi girki iya cikinta ta ci da rana tana jira ta ga sanda za ta dawo gidan. Dab da magriba ta dawo ta shiga kitchen ta ɗora musu taliya, Maryam ta taho kitchen ɗin don ba ta yi zaton ma Sauda ta ɗora girki ba, tana jin babu daɗi Alhaji ya dawo ya tarar babu abinci, shi ne ta yanke za ta dafa masa, kwatsam ta ji Sauda tana waya, ita kam Allah Ya hore mata iya laɓe, don haka ta laɓe tana sauraronta, daidai sanda Sauda take cewa"Wallahi kuwa Aliya, ke ba ki ga abun ba ɗan ɗiss da shi fa, ɗugo ɗaya ne, wallahi ta tabbatar mini idan na yi amfani da shi har ya fi bi ta salam". Can ta kwashe da dariya ta ce"Ke dai bari, ai wallahi yau dole ma ya saurare ni, har zumuɗi nake yi daren ya yi, ƴar ƙaramar kwalba fa ake zuba shi dubu hamsin, ita ma sammata aka yi, shi ne ta sammin". Sai da ta gama wayar tsaf sannan Maryam ta koma ɗakinta, ta fasa shiga kitchen, tsaf ta fahimci inda wayar ta dosa, don haka ta saka a ranta dole ta yiwa tufkar hanci, yau ko da yaƙi sai ta hana Alhaji kwana a ɗakin Sauda. 08028966015 https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3 17 Yau Sauda tana gama girki ta fesa wanka, ta manta rabon da ta yi wankan dare wai kawai saboda ta yi wa miji kwalliya, ta saka kayan bacci ta fesa turare, sai murmushi take yi, tana nan-nan da shi, har abun ya ba shi mamaki, amma dai ya yi shiru tun da abun arziƙi ta yi, dama shi gyara yake nema a tsakaninta da shi, don haka sai ya saki jiki da ita suna ta fira, tun da Maryam ta fito falon ta yi masa sannu da zuwa ta koma ɗakinta, sai da za su ci abinci ya ɗaga waya ya kirata, ta fito tana taliya lamo-lamo, ga hijjabi har ƙasa a jikinta wanda bai saba ganin haka ba, ta zauna tana cewa"Sannunku". Alhaji ya ce"Maryam ƙalau kike kuwa? Na ganki a sanyaye". Ta ce"Ba ni da lafiya wuni na yi da ciwon ciki". Ya ce"Subhanallah! Kin sha magani?" Ta ce"A'a abinci ma na kasa ci, tun karin safe". Ta yi maganar kamar za ta fashe da kuka, ta kwanta yaraf a kujerar da take. Ya ce"A haba Maryam, to ai dole abun ba zai yi sauƙi ba, kin ga tashi ki ci abinci, bari na samo miki magani, ko mu je asibiti?" Ta ce"A'a, ai dama ina yin irin wanna ciwon cikin, kuma maganin hausa nake sha, idan na sha na bature ƙara tsanani yake yi". Ya ce"Ikon Allah! To wane irin magani ne? A ina ake siyowa?" Ta ce"Daga ƙauye wani ƙanin babata yake kawo mini, sai dai gobe na faɗa masa idan zai shigo garin ya kawo mini". Ya ce"Kayya! Amma kin san da haka ai da ba za ki bari maganin ya dinga yanke miki ba". Ta ce"Gani na yi na daɗe ban yi ba shiyasa". Ya ce"Sannu yanzu tashi ki daure ki ci abincin ko yaya ne, ko kuma dai Sauda haɗo mata shayi don cikin ya warware tukunna". Sauda takaici ya hana ta magana ganin yadda duk ya ruɗe saboda ita, amma yau ɗin ba ta son su samu matsala don haka ta je ta haɗo shayin ta kawo, ya ɗagota ta tashi zaune, ta sha rabin kofin ta koma ta kwanta, ya ce"A'a ki tashi ki ci abincin". Ta ce"Ba zan iya cin taliya ba". Ya ce"To me za ki ci?" A shagwaɓe ta ce"Ta soya mini ƙwai". Sauda ta ji kamar ta je ta shaƙe ta, ta kasa jurewa ta tashi za ta bar falon, shi kuma ya zaci soya ƙwan ta tafi, ya ce"Yawwa hanzarta Sauda ki soya guda uku". Ta ce"Wallahi babu wata ƙatuwa da zan dinga yiwa bauta, kai da ka ajiye ta sai ka je ka soya mata, ko ka siyo mata a teburin mai shayi". Ta bar falon. Ya tashi yana cewa"Allah Ya kyauta". Ya shiga kitchen ɗin ya soyo ƙwan duk rabi ma ya ƙone ya kawo mata, ta ci kaɗan ta koma ta langwaɓe, duk sai ta damu ya ce"To kuma yanzu babu wani magani da za a gwada? Dare ake tsoro". Kamar za ta yi kuka ta ce"Kuma wallahi ya fi tsanani cikin daren, amma dai zan daure". Ya ce"To, sannu". Suna nan a haka, har ƙarfe tara ta gota, lokaci-lokaci Maryam sai ta yi juyi tana riƙe ciki tana wash, shi kuwa duk sai ya ruɗe, yana yi mata sannu, Sauda ta fito ta same su a haka, ita ta yi zaton ma har ya shige ɗakinsa yana jiranta ashe yana nan yana naniƙarta, ta gama shirinta tsaf ta yi amfani da maganinta, sannan ta sha sauran har fiye da ƙa'ida, ta zo ta yi tsaye a kansu ta ce"Wai dama ba ka kwanta ba? To ka wuce mu tafi" Ya ce"To na tafi ina? Kina kallon halin da take ciki". Sauda ta ce"To me kake nufi? Kenan kwanan nawa zan bar mata tun da ba ta da lafiya". Ya ce"Kai Sauda! Ana zancen rashin lafiya meye kuma kwana? Larura ai ta sha gaban komai". Ta ce"To ta je ta kwanta dai, Allah Ya sawaƙe". Ya ce"Maryam tashi ki shiga ciki". Ta tashi zaune, sai ta koma luuu ta kwanta tana riƙe ciki, Alhaji ya ce"Subhanallah!" Ya tashi ya ɗaga ta, amma ta lanƙwashe ƙafafunta kamar musaka, ya kasa tsaida ita, sai kawai ya ɗauke ta cak ya yi hanyar ɗakin, Sauda da take tsaye tana kallon ikon Allah ta bi bayansu cike da kishi tana cewa"Wai Alhaji me kake nufi ne? A ranar kwanana?" Ya yi tsaki, saboda takaici ya kasa cewa komai, shi a ganinsa mene ne don ya ɗauke ta saboda ta kasa tafiya? Ana ta rashin lafiya ita tana zancen kwana, ya sauke ta a kan gado, yana yi mata sannu, ya zauna a bakin gadon yana cewa"Yanzu kuma sai ki zauna da ciwo Maryam? Ba za a samo miki wani kalar maganin ba?" Ta ce"Na faɗa maka ƙaruwa yake yi idan na sha wani". Ya ce"Ai shikenan, sannu, Allah Ya yaye". Ya riƙe haɓa cike da damuwa yana kallonta, ita kuma Sauda tana tsaye a bakin ƙofa ya rasa me take jira. Suka yi kamar minti goma sha biyar a haka, Maryam ta bar mutsu-mutsun ta lumshe ido, Sauda kamar tana jira ta ce"Tun da ta yi bacci ai sai ka wuce mu je mu kwanta ko?" Yana tashi Maryam ta yi wata zabura tana riƙe cike da salati, sai kuwa ya dawo da sauri yana riƙe ta yana "Subhanallah! Sannu Maryam". Takaici ya sa Sauda barin ɗakin, ta je ta shiga ɗakin nasa ta kwanta tana jin tsanar Maryam tana hauhawa a zuciyarta, gefe guda kuma tana ayyana irin gashin da za ta yi mata kafin ta kore ta daga gidan, duk iskancin nata na yau ne kawai, wuyarta su keɓe da Alhaji, ta san magana ta ƙare, don ta yarda da maganin nan, tana ra saƙa da warwara ba ta san tsayin lokacin da Alhaji ya ɗauka a wajen Maryam ba sai da ta tashi ta duba wayarta ta ga sha ɗaya da rabi. Ga wani fitsari da take ji, ita kuwa ta yi rantsuwar ba za ta wanke maganin nan ba, ranta a ɓace ta fito ta nufi ɗakin Maryam ɗin, shi Alhaji ya fara jin bacci ma, amma ya kasa tafiya ya barta a halin rashin lafiya, ita kuwa Maryam idonta a soye yake don kuwa ba ta ga ta bacci ba, tun da ta san baccin nan daidai yake da samun lasisin shigarta zawarci. Sauda ta shigo tana cewa"Alhaji amma dai ka san ba ka yi mini adalci ba ko?" Ya ce"Da aka yi me?" Ta ce"Ka san ranar kwana ne ai, amma ka zo ka tare a wajenta, ka kalli agogo kuwa?" Ya ce"Haba Sauda, ko ke ce ba ki da lafiya ai haka zan yi miki, kuma na san Maryam ba za ta yi ƙorafi ba". Cikin muryar marasa lafiya Maryam ta ce"Alhaji ka je, babu komai, ko kuma ta haƙura gobe sai na ba ta kwanana". A fusace Sauda ta ce"Ba na so! Ku haɗa ku cinye!". Ta juya ta fita Maryam ta ce"Ka tafi kawai, ba na son ku samu matsala ta sanadina". Ya ce"To Allah Ya sawaƙe". Ya fita yana waiwayenta Ya samu Sauda a ɗakinsa, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, ya zo ya kwanta ya juya mata baya, ranta ya ƙara ɓaci, ta ce"Lallai Alhaji ka ba ni mamaki, ai ni wallahi na san ba za ka taɓa yin adalci ba, shiyasa tun farko na ƙi ka ƙara aure". Ya ce"Yanzu me nake yi miki na rashin adalci? Ke ce dai kika kasa tsayawa ki nutsu ki fahimci rayuwa". Ta ce"Tun kafin aurenka ma sati nawa ba mu haɗa shimfiɗa ba? Amma a ce yau ga ni ga ka ka juya mini baya?" Ya ce"To wannan kuma ai ke kika zaɓi haka, yau kuma ba na cikin wannan yanayin, ki yi haƙuri don Allah". Ta ce"To ni ina cikin yanayin, idan kuma za ka tauye mini haƙƙi ne sai ka yi bayani". Zai yi magana, suka jiyo Maryam ta ƙwalla ƙara, don sai da ta fito babban falo ma ta yi ƙarar don su fi ji, sannan ta koma ɗakinta a guje ta kwanta a ƙasa. Ai kuwa Alhaji a guje ya taho yana salati, duk ya ruɗe musamman da ya ganta a ƙasa tana juyi, ya ce"Maryam lafiya? Cikin ne?" Ta ce"Wayyo Alhaji, mutuwa zan yi". Ya zauna yana yi mata sannu, ya yi ta fama su je asibiti amma ta ƙi, suna zaune a haka har ƙarfe biyu. Lokacin Sauda ta ci kuka iya yinta, ganin dai da gaske ta yi asarar wannan maganin, a tsakar daren ta kira ƙawarta a waya, tana kuka ta faɗa mata, ta kuwa tabbatar mata shikenan ta rasa damarta, can dai wajen ƙarfe uku ta kasa haƙura, don haka ta shiga ɗakinta tana neman rigar bacci wacce za ta ɗauki hankali, sai dai duk babu, sai ta saka siket underwear, ta ja shi sama zuwa ƙirjinta, ya zamana ko rabin cinyarta bai zo ba, ta fito ta shiga ɗakin Maryam ɗin a haka, Sauda tana da ƙiba da tsayi, don haka sai ta fito kamar wata goɗiya. Babu zato Alhaji ya ga shigowarta, ya miƙe da sauri yana cewa"Subhanallah! Sauda mene ne haka? Ƙalau kike kuwa". Maryam ta ƙyallo ido ta kalle ta, dariya ta zo mata ganin Alhajin duk ya ruɗe, ransa ya ɓaci, sai ta yi juyi ta basu baya tana dariya ƙasa-ƙasa. Sauda ta ɓata rai ta ce"Me kake nufi?" Ya ce"Ta ya za ki fito a haka? Ni dai na san ko sanda kike amarya da ƙuruciya ba ki yi wannan abun ba, ballantana yanzu, kuma ma ba a ɗakina ki zo har wani ɗakin?" Ta ce"Amma dai ai ko me na yi ba haram ba ne, tun da a ranar kwanana ne, kuma ni na gaji da wannan makircin da kake yi wai kai mai jinya, ka wuce mu tafi mu kwanta, ni ma idan ba ni da lafiya a rabar kwananta ban ce ka ƙi bata haƙƙinta ba, na yafe kulawar taka!". Daidai nan Maryam ta ƙara ƙwalla ƙara, Alhaji kuwa ya yo kanta, ta kama hannun shi gam ta riƙe, ta ce"Kai ni banɗaki, zan yi fitsari". Ya ɗagata ta kasa tashi, ya ɗauke ta cak, sun zo shiga banɗakin ta faki idonsa ta yiwa Sauda gwalo tana murmushi. Gaban Sauda ya faɗi, har zuciyarta ta yi zaton ciwon cikin gaske ne, amma wanna abin da Maryam ɗin ta yi mata ya tabbatar mata na ƙarya ne, ta yi haka ne kawai saboda ta cuce ta, kuma ta san ko me za ta faɗa masa ba zai yarda ba, don haka kawai ta juya ta koma ɗakin nashi ta kwanta wani sabon kukan yana zuwar mata. Sai da aka kira sallar asuba sannan Maryam ta ce ya lafa mata, har ta tashi a gabansa ta shiga banɗaki don yin alwala, yana ta ma sha Allah! Ya tafi ɗakinsa don yin alwala ya tafi masallaci, yana shiga ya ga Sauda a zaune, ta taso tana riƙe shi, abun har ya ba shi mamaki, saboda tun da suke da ita ba ta taɓa neman shi ba, sai yau yake ganin sabon salo, ya ce"Sauda wai ƙalau kuwa? Kina ta ba ni mamaki". Ta ce"Kawai ka ba ni haƙƙina". Ya ce"Kai! Abu dai sai kace cin rabo? Ni masallaci zan tafi kin ga gar an shiga". Ya kauce ta ya shiga banɗaki, sai ta yi ɗakinta da gudu, ta kwanta tana fashewa da kuka, ta haƙura da wannan daren don ta kai ajin ƙarshe wajen jure wulaƙancinsa, amma ta saka a ranta sai ta rama, sai ta hana Maryam kwanciyar hankali, haka tana ji tana gani ta wanke maganin nan ta yi alwala ta yi sallah. Kuma da safe ya ce ta yi girki tun da Maryam ba ta da lafiya, a nan ne ta yi tsalle ta dire ta ce wallahi ba za ta yi ba, sai dai a zauna a haka, ƙarshe shi ya shiga kitchen ɗin ya dafa shayi suka sha da biredi. Wajen sha ɗaya na rana Maryam ta kira shi a waya ta faɗa masa an kawo mata maganin, har ta sha cikinta ya warware, don haka ta shiga kitchen ta yi girkin rana, tana ta harkokinta cikin sa jin daɗin ta tsallake wannan tarkon, da ta ga Sauda ta shiga ɗakinta ta ji ta shiru sai ta je ta yi mata laɓe ko za ta ji wani abun, amma yau ba ta ji komai ba. Da daddare ya kwana a ɗakin Maryam hankali kwance. Washegari da girkin Sauda ya zagayo ya yi niyyar ba ta haƙƙinta, amma fir ta ce ba ta so ya je ya kaiwa Maryam ita ce mai buƙatarsa, har abun ta ba shi mamaki duba da ganin yadda rannan duk ta addabi kanta a kan haƙƙinta, to shi ma dama ba matsuwa ya yi ba, kawai don ta sauƙe nauyinta dake kansa ne don haka ya juya ya yi baccinsa. 08028966015 https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3 18 Washegari da girkin Maryam ya zo sai Sauda ta ce ita ma ba ta da lafiya, ta dinga juyi tana wash, ta ce zazzaɓi ne take yi na cikin ƙashi, haka Alhaji ya ba ta magani, ta yi kamar ta sha, ta ƙi bacci tana ta wash, ita ma sai da ya kwana a ɗakinta, washegari kwananta ita ma Maryam ta ce ciwon cikinta ya motsa, ya kwana yana jinyarta. Daga nan fa Alhaji ya kasa gane kan matan nasa, duk wacce ba ita ce da girki ba to ya ma riga ya sani a ranar ba ta da lafiya, kuma ciwon ba ya tashi sai da daddare, da dai ya gane so suke kawai su yi ta wasa da hankalinsa su mayar da shi sususu sai ya zaunar da su ya ce"Sauda da Maryam, a gaskiya ba zan ɓoye muku ba na gaji da wannan rashin lafiyar taku wacce ba ta tashi sai da daddare, kusan sati biyu kenan fa ina fama da kewa ina kame-kame kamar gauro, ga rashin samun isasshen bacci, idan kun gaji da ni ne sai ku faɗa mini na samo ta uku na aura, gaskiya abun ya ishe ni, daga yanzu duk wacce ba ta da lafiya to wallahi ɗayan biyu ko dai ta yi jinyar kanta ko kuma da safe na zo na tarar da gawarta, babu wacce zan ƙara kwana a ɗakinta ina jinya, wannan shi ne". Bai ma ba su damar magana ba ya tashi ya fice daga gidan. To tun daga nan suka daina wannan, yaran sun dawo gidan, yanzu tsoron ya bar ransu, sai kuma Sauda ta shiga ƙuntatawa Maryam ta fannin abinci, sai ta yi abinci kai da kai, ta barwa Maryam ɗan mitsitsi kamar wata ƴar goye, sannan duk ranar girkinta sai Sauda ta zaɓi girki mai wahala ta ce Alhaji ya ce a dafa, kuma idan ta kira shi sai ta ji shi ɗin ne ya ce a yi, tun tana yin shiru har ta gaji. Watarana suna zaune da shi take cewa"Wai ni Alhaji me yasa idan za ka zaɓi girki ba ka faɗa mini baki da baki sai dai ka faɗawa maman Momy ta zo ta faɗa mini? Gaskiya ba na jin daɗin hakan". Ya ce"Ba haka ba ne, ita ce take kirana ta ce mini yaran nan abu kaza suke son ci kuma ba ita ce da girki ba, ni kuma sai na ce mata to ta faɗa miki mana". Maryam ta ce"Au to shikenan". A ranta ta fara tunanin lallai Sauda ta raina mata hankali, kenan dai zaɓar abin da za ta dafa take yi ta zo ta ba ta umarni ta dafa, ta ayyana daga yau an gama wallahi, don ita ba baiwarta ba ce. A ranar da safe Sauda ce ta tashe ta daga bacci, ta ce"Maryam ki fito kar yara su makara, ya ce yau alala da kunu za a yi". Maryam ta ce"Ai jiya an rage tuwo, shi za a ɗuma a dafa shayi, wanda ba zai ci tuwo ba akwai biredi". Sauda ta ce"Inyee! Wato riƙar taki har ta kai haka? Umarnin nashi ma a banza kika ɗauke shi?" Ta ce"Ai riƙata ta wuce inda kike zato, kuma na san ba umarninsa ba ne, ke ko na shi ne muddin ba zai zo ya faɗa mini baki da baki ba to wallahi babu wata ƴar aiken da ta isa ta ƙara saka ni na dafa abin da ban yi niyya ba". Ta wuce kitchen ɗin ta bar Sauda da sakakken baki, yadda ta ce ɗin kuwa haka ta yi, sai Sauda ta zuga yaranta ta ce su ce ba za su tuwo ba, biredin ma haka, Maryam ta kawo tuwo ta koma ta ɗakko shayi yaran duka suka ce ba za su ci ba sai alala, da ta dawo Alhaji ya ce"Maryam me yasa ba ki dafa musu wani abun ba? Kin ga wai ba sa son cin tuwon". Ta ce"To ai gani na yi tun da ga tuwon idan aka yi wani girkin kamar an yi almubazzaranci ne, tun da ka ga ba a zubar ba, sannan almajiran ne ba sosai suke zuwa ba, kuma ma ga biredi idan ba za su tuwo ba". Ya ce"E gaskiya haka ne, ku yi haƙuri ku ci, gobe sai ku ci alalan ko?" Nan kuwa suka ci tuwon, dama suna so kawai dai don uwarsu ta hana su ci ne. Da rana Sauda ta ce mata"To ai sai ki yi alalan ko?" Maryam ta ce"Idan na yi ra'ayi ba". Ai kuwa ta yi jollop ɗin taliya, gabaɗaya suka ƙi ci ita da yaran, suka barta a kula, dab da magirba Maryam ta shiga kitchen ta tarar da taliya shaƙe a kula kamar yadda ta barta, ta jinjina kai, ta juyeta a tukunya ta yayyafa ruwa ta ɗumama ta, ta sake zubawa a kular, har Alhaji da ya dawo ita ta ba shi, ita kuwa Sauda da ta ga taliyar ranta ya ɓaci ta ce"Wai ke yari yar nan me kike nufi ne?" Alhaji ya ce"Kamar ya? Me ta yi". Ta ce"Wannan taliyar fa tun ta rana ce ta ɗumamata, yanzu ni da yaran ba son taliya muke ba, ta dafa da rana haka muka wuni da yunwa,kuma yanzu abar ta sandare a kula sannan ta kwaso ta ce ita za mu ci? Ba mu ci da mutuncinta ba sai yanzu?" Alhaji ya ce"To ni dai ita na ci, kuma wallahi ban ji wani aibu a tarw da ita ba, lafiya lau na ci ni ban san ma ta rana ba ce". Ta ce"Dama ina za ka sani, tun da girkin amarya ne, ai ko me ta kwaɓa kai dama daɗi zai yi maka, amarya mai miya da daɗi, mai maganar sukari". Maryam ta ce"Alhaji ni fa ba na son hayaniya da abin da za a zo

Chapter 11 of 21