ce".
Sauda ta buɗe suka yi ido huɗu da Maryam, suka fara kallon-kallo, ganin ta tare ƙofa ba ta da niyyar ba ta waje ta shiga sai ta zo za ta raɓe ta ta shige, Sauda ta ce"Ke dakata mana, ina za ki shiga? Bashi kike bi na ko tara? Tukunna ma uban me ya kawo ki?"
Maryam ta ce"Bari na fara amsa miki daga tambayar ƙarshe, ubanki ne ya kawo ni, Sauda ba rigima ce ta kawo ni ba, ki sani ina da damar shiga gidan nan, saboda yarana da suke ciki, gara ma tun wuri ki mata mini na shiga kar ki tarawa kanki jama'a".
Sauda ta ce"Ai wallahi ba za ki shiga gidan nan ba! Kin damu da yaran kika ƙi nema musu mafita? Ai na faɗa miki gidana nawa ne ni kaɗai, amma saboda taurin kai kika baje kika haihu, yara sun zama nawa, a yanzu ba ki da iko da su! Don haka ki fice mini daga gida kafin na yi miki mugun duka".
Maryam ta banko da iya ƙarfinta ta shigo cikin gidan, ta ce"Ai wallahi ƙarya ne, ba a canzawa tuwo suna, ni ce uwarsu har abada, kuma ko ubansu bai isa ya hana ni iko da su ba, ballantana ke karan kaɗa miya!".
Ta yi wajen da yaran suke a tsaye sun dakata da wasan suna kallonta, ta haɗa su ta rungume, sai hawayen tausayinsu ya zubo mata, ita ma Sauda jikinta ya yi sanyi amma ba ta nuna ba, ta zo kanta ta ce"Wallahi Maryam idan kika tafi da yaran nan to kar ki sake ki dawo mini da su, sai dai ki riƙe su, su taso su ganki kina yawon zawarcin".
Maryam ba ta bi ta kanta ba, ta shiga duba kayan jikinsu wanda suka yi datti, tausayinsu ya ƙara kamata, sai a lokacin ta yi nadamar ƙin bin umarnin Alhaji har ya sake ta, ɗan hakin da ta raina ya tsole mata ido, da a ce ta yarda ta je ta jure duk wulaƙancin Sauda a lokacin da tuni komai ya wuce yanzu tana tare da yaranta, ta ja hannunsu ta yi cikin falon kamar yadda Sauda ma ta shige, ta hakimce a falo, kai tsaye ɗakinta ta dosa don ta yi amfani da banɗakin ta yi musu wanka, sai ta samu kayansu a ciki, ga shimfiɗa ba a naɗe ba da alama a nan suke kwana, ta tambaye su don tabbatarwa suka tabbatar mata, zuciyarta ta yi rauni sosai, har take jin a yanzu Sauda ko dambe ta zo su yi sai dai ta yi mata duka saboda jinta take yi kamar an zare mata laka.
Ta yi musu wanka fes, ta canza musu kaya, ta kwashe rabin kayansu ta fito da su, Sauda tana kallonta ba ta ce komai ba har ta fice, cikin ranta farinciki take yi sosai tana fatan sun tafi kenan, don kuwa dole ne Alhaji ya bi sharaɗinta na cewar idan suka tafi sun tafi kenan.
Maryam tana shiga gida da yaran Uwani ta ce"Sannu Maryam, har wata nawa za su yi da kika ɗakko su da jakar kaya? To ko dai shi Aliyyun ne ya ce ki tafi da su gidan naki?"
Maryam ba ta ce komai ba ta shige ɗaki, Uwani ta biyo ta, sai ta same ta tana kuka ta kwantar da yaran a cinyarta, jikinta ya yi sanyi ta ji tausayinta ya kamata, ta zauna ta tausasa murya ta ce"Tabbas akwai damuwa a rabuwar uwa da ƴaƴanta, amma ya za ki yi? Sai haƙuri, yanzu muna wani zamani wanda kowa nashi kawai ya sani, ba don haka ba da kin tafi da su gidan auren naki, to ƙila matsala ta biyo baya idan ma ya yarda ɗin kenan".
Maryam ta ce"Ni fa na fasa auren nan, na fasa, ba zan iya jure ganin ƴaƴana a wannan yanayin ba, gara na haƙura na zauna na yi nema na dinga samun abin da zan rufa musu asiri".
Uwani ta ce"Ba za a yi haka ba Maryam, ke fa kika ce kin ji kin gani, kuma dama shi yaro ai dole ya sha wahala, wuyar ba ta kisa, watarana sai labari".
Maryam ta ce"Amma ke ma a baya kin ce mini gara na haƙura da auren na zauna".
Ta ce"E an yi haka, amma lokacin ai ke kaɗai ce babu yara, Maryam ba zan taɓa goyon bayanki a kan karɓo yaran nan ba, da uba ake ado, ke mace ce, so kike su taso ana ce musu ƴaƴan mace, alhalin mahaifinsu yana raye? Ko kina ganin mahaifinki zai yarda ki ƙi yin aure saboda kula da yara? Ana yin haka, amma fa sai ta kama, ke kuwa ba ta kama ki ba wallahi, don haka idan yaran nan suka kwana biyu ko uku sawunki a likafa ki mayar da su gidan ubansu".
Maryam ta ce"Na ce fa na fasa auren".
Uwani ta ce"Ai sai ki yi". Ta fita ta bar mata ɗakin.
Da daddare da Baba ya dawo Uwani ta zauna ta karanta masa halin da ake ciki, Baba ya zaunar da Maryam ya nuna mata sam ba zai yiwu ba, ko ta fasa aure to fa tilas ta mayar da yara gidan ubansu, haka ta ci kuka ta yarda za ta mayar da su don dole.
Sauda har zumuɗi take Alhaji ya dawo, ya tarar da ita ta cika ta batse, sai da gabansa ya faɗi, ya ce"To yau kuma me yake faruwa, na ganki sam babu annuri".
Ta ce"Au wato tambayata ma kake yi ko? Ka san kana son Maryam me yasa ka sake ta wai?"
Ya ce"Ban gane ba, kamar ya ina sonta, me ya kawo maganar nan?"
Ta ce"Kar ka mayar da ni shashasha, ba ka turo ta har gida ta kwashe yaranta ba? Bayan ta gama yi mini zagin tsamar nama, har tana faɗa mini tana nan dawowa nan ba da jimawa ba, ashe banza ka mayar da ni, kana can kana zagaya kana zawarcinta ko? To dama na faɗa maka sharaɗina, yaran nan sun tafi kenan, kar a sake a dawo mini da su gidan nan, don ba zan riƙe ba".
Alhaji duk ya ruɗe, kuma ransa ya ɓaci ya ce"Wallahi ko me ta faɗa miki ƙarya ne, ban taɓa waya da ita ba sai jiya, kin gani, duba ki gani". Ya ciro wayarsa yana nuna mata.
Ta kau da kai gefe, a ƙasan ranta kuma tana jin sanyi, dama ta tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro, saboda ta fara tunanin kar dai yana zagayawa wajen Maryam ɗin.
Ya ce"Wallahi ban aiko ta ba, faɗa mata ma na yi ba zai yiwu a kai mata su ba, don raɗin kanta ta zo ta ɗauke su wallahi".
Ta ce"To ai sai ta je ta riƙe".
Ya ce"Ai shikenan, Allah Ya kyauta".
Daga haka zancen ya mutu.
Suna yin kwana uku Baba ya ce ta kira babansu ya ɗauke su, ta y ta kiran shi ba ya ɗagawa, ta faɗawa Baba, sai ya karɓi lambarsa ya kira shi, suka gaisa ya faɗa masa ya zo ya ɗauki yara, nan take Alhajin ya ce"Baba ai mun gama magana da ita, na faɗa mata idan ta ɗauke su sai dai ta riƙe su gabaɗaya". Bai jira cewarsa ba ya kashe wayar, ya dinga kira ya ƙi ɗagawa.
Washegari Baba ya tafi gidan mahaifansa, ya yi sallama da Inna ya karanta mata komai, sai ta ce ita wannan ba maganarta ba ce, haka ya dawo gwiwa a saluɓe, da ya faɗi yadda suka yi Maryam ta fara kuka ta ce"Baba yanzu da raina ake neman kau da ƴaƴana? Ni a ƙyale mini su, zan riƙe su".
Ya ce"Ba neman kai ba ne, neman maslaha ne Maryam, kin ga aure za ki yi, shi ma kuma ba lallai ya yarda ki je da yaran ba, kin ga su zauna a gidan ubansu shi ya fi".
Tun da ta ga ba zai fahimce ta ba sai ta ƙyale shi, ta fita a maganar, ƙarshe dai Baba Hizba ya je ya kai ƙara, sai a nan aka sasanta Alhaji ya karɓi yaran, ya je gida suka kwana suna gwabzawa da Sauda kafin ta haƙura ta yarda su zauna.
08028966015
https://chat.whatsapp.com/HgIpjvQkvUf7yzwrsNtfBs
27
Jiki a sanyaye Maryam ta yi wannan auren, sai dai cikin zuciyarta akwai jarumta, wacce ta saka a ranta ta jure zama da kowane irin miji ta aura, zama gida ɗaya da kishiya ba abu ba ne mai daɗi, saboda ta yi ta ga illarsa, ga shi za ta ƙara irin rayuwar a karo na biyu, kuma tare da wacce ba ta ji labarin wani halinta mai kyau ba, sai dai ta saka a ranta a wannan karon sai dai a yi kare jini, biri jini ita da kishiya. Ana gobe auren da aka je jere uwar gida ta hana a taɓa kitchen, ƴan jere suka kira Maryam suka faɗa mata, ta kira Aliyyu a waya sai ya ce ta yi haƙuri a ajiye kayan a ɗaki, idan ta tare sai a san yadda za a yi, tun daga nan jikinta ya ƙara yin sanyi. Haka dai aka ɗaura aure da magriba aka kai amarya, Baba bai gajiya da yi mata nasiha ba, kamar aurenta na farko, idan da hadda ta riga ta haddace ta, kuma da ya san yadda take son ta yi zaman auren da bai wahalar da bakinsa wajen maimaita mata kalmar haƙuri ba. A ɓangaren Uwani ba ta wahalar da kanta wajen yiwa Maryam nasihar da ta saba ba, saboda ta gane ba za ta saurare ta ba, tun da yanzu Maryam ɗin ta nuna mata ta zubar da karatunta ta shiga sabuwar makarantar zama da namiji, don haka fatan zaman lafiya kawai ta yi mata, a ranta kuma tana kyautata zaton yadda aka kwashi kayan nan haka za a dawo da su, itq da za ta ba ta shawara ta ji ma da ba ta yi kayan ɗakin ba, saboda asarar kuɗi ne kawai, dillalai kowa ya santa wajen siyar da kayan ɗaki.
A gidan suka tarar da wasu ƴan'uwan Aliyyu su biyu, suna jire gidan saboda Lubabatu ba ta nan, biki suke yi a danginta don haka ta shirya ta tafi, saboda ba ta ɗauki auren Aliyyu a bakin komai ba, ta san dai wannan amaryar tamkar break ta zo yi gidan ta gama ta koma gidansu, shiyasa duk yadda ƙawaye da ƴan'uwa suke cewa za a ce kishi ne ya sa ta ƙi zama a gidan ba ta bi ta kansu ba ta yi tafiyarta.
Bayan kowa ya watse ango ya shigo cike da farincikinsa, duk da ƙasan zuciyarsa akwai fargaba ta irin zaman da Maryam za su yi da uwar gidan nasa, tun asali shi mai ra'ayin mata biyu ne, fahimtar zafin kishi irin na Lubabatu ya sa ya haƙura, uwa-uba kuma son da yake yi mata, aurensu ko da ba na soyayya ba ne aure ne wanda za a iya ce masa mutu-ka-raba, domin auren zumunci ne, kuma kakansu wanda shi ne ya ƙirƙiri haɗa aure tsakanin zuri'arsu ya haramta saki, duk girman matsala kuwa, sai dai bai hana mutum ya ƙara aure ba, don haka da Lubabatu ta samu matsalar da aka cire mahaifarta da kansa ya yi masa umarnin ya ƙara aure, a auren da zai yi na farko dai babu kalar haukan kishin da ba ta yi ba, kafin ta samu mafitar fitar da amaryar tun auren bai je ko'ina ba, haka ya yi aure na biyu shi ma bai ci Talata ba, ballantana Laraba, duka su biyun babu wacce ta samu ciki ballantana a haihu, saboda zaman ma babu nutsuwar faruwar hakan.
Bayan ya gama nuna farincikinsa da zaƙin bakinsa a kan Maryam, ta ce"To yanzu ya zan yi da wannan kayan kitchen ɗin? Ka san dai ba za su zaunu a falo ba".
Ya yi jim, domin ba ƙaramin gargaɗi Lubabatu ta yi a kan kar a yadda a taɓa mata kitchen ba, kuma ya san zaman lafiyarsu shi da Maryam ɗin shi ne yin yadda ta ce, don haka ya ce"Amm...Maryam ni ina ganin ai ko a waje nan ƙofar ɗaki za ki iya yin girkinki, tun da gas ne ba hayaƙi ba, su kuma kayan ko a ƙarƙashin gado ki saka wasu, saboda dai a zauna lafiya".
Ta ce"Kamar ya? Kitchen ɗin ƙarami ne? Ba sai na raɓa nawa a gefe ba?"
Ya shafa kai ya ce"A gaskiya ba zan ɓoye miki ba, ita Lubabatu ce ta ce ba ta yarda da wannan tsarin ba, kin ga ita ce babba dole zan nemi amincewarta don tana da haƙƙi akan hakan, to shiyasa nake ganin a yi hakan kawai zai fi".
Maryam ta ce"Hmm! To su kuma sauran ɗakunan fa?"
Ya ce"E na yara ne su, ɗaya na yara maza, ɗaya na yara mata".
Ta ce"To ai na ji ka ce yaran naka duka maza ne, kenan zan iya ajiye kayana a na yara matan kafin a haife su ko?"
Ya ce"To sai dai hakan, duk da ban san ita a yadda za ta ɗauki abun ba".
Zuwa yanzu ranta ya fara ɓaci, na yadda yake nuna mata kamar ita ba matar gida ba ce ƴar karere ce, ta ce"Kamar ya yadda za ta ɗauki abun? Na ga ɗakin a rufe yake, kenan ni ba ni da iko da shi? Idan ni na fara haifar ƴaƴa matan fa? Ba zan iya ajiya a ɗakin yarana ba?"
Ya ce"A'a ba haka ba ne, na ga ita ma tana ajiya a ciki, amma ki ajiye ɗin, bari na taya ki".
Ya tashi ya fara ɗibar kayan, ita ma ta ajiye mayafinta suka zuba kayan kitchen a ɗakin tass, ta kullo ƙofar.
Washegari da ya kawo kayan abinci da cefane duka can ta kai, a ciki ta yi girki, a taƙaice dai ta samu kitchen, ta matsar da shirgin Lubabatu can gefe ita ta baje nata, da so ta yi ma ta mayar mata da su kitchen ɗinta Aliyyun ya ce ta ƙyale mata a nan.
Cikin kwana uku sun sha amarci, sosai suke rayuwar farinciki, duka da ba wani son shi Maryam take ji ba, amma tana ta ƙoƙarin nuna tana ƙaunarsa da jin daɗin zama da shi, don haka shi ransa fess, idan ya tuna matarsa za ta dawo ne kawai yake jin fargaba, shi da za ta shekara ma da zao fi son haka.
A ranar na huɗun Lubabatu ta dawo, dama a ƙa'ida a ranar girkin Maryam ya ƙare za a shiga nata, a rufe take barin gidan sai dai idan an buga ta buɗe, tayar da sallarta kenan ta fara jin bugun ƙofa na tashin hankali kamar za a cire ƙofar, daga ji za ka gane duwatsu aka saka ake bugawa, sai da gabanta ya faɗi don ta yi tunanin ba lafiya ba, ko wani saƙon tashin hankalin aka aiko a sanat ma tana shirin katsewa ta ji muryar mace wacce ko ba a faɗa ba ta san Lubabatu ce uwar gidanta, tana cewa"Wai kurame ne a gidan!? Uwan wa ya ce ana rufe mini ƙofar gida?"
Maryam sai ta fasa katsewa, ta ci gaba da sallarta, ita ma Lubabatu ta ci gaba da bugu kamar za ta tashi gidan, duk a tunaninta Aliyyun bai je aiki ba yana ciki maƙale da amarya shiyasa suka kulle ƙofa, da ta idar ma sai da ta yi addu'a ta shafa, ta cire hijjabin ta ajiye sannan ta je wajen wayarta da take ringin ta ga Aliyyu ne mai kiran, ta ɗauka da sallama, bai amsa ba ya ce"Maryam kina ina?"
Ta ce"Ina gida mana".
Ya ce"Kina ji ana buga ƙofa?"
Ta ce"Sallah nake yi, yanzu na idar".
Ya ce"To maza ki je ki buɗe, Lubabatu ce, don girman Allah kar ki kula ta, ko ta zo da wata fitinar ki yi haƙuri ki ƙyale ta, idan na zo sai ki sanar da ni, na yi wa tufkar ha ci".
"Ok" Kawai ta ce, ta ajiye wayar ta fita.
Tana buɗewa Lubabatu ta banko cikin gidan har tana bangaje ta ta ce"Gidan ubanki ne da za ki rufe ƙofa na yi ta bugawa ki ƙi buɗe mini?" Ta ƙarasa da haki kamar wacce ta ci gudu, gabaɗaya a zabure take kamar mai jiran a kaure da dambe.
Maryam ta ce"Ba gidan ubana ba ne, kamar yadda ke ma na san ba gidan naki uban ba ne, sallah nake yi, kuma ko mai gidan ne sai ya jira na idar zan buɗe".
Lubabatu ta riƙe ƙugu ta ce"Inyee! Lallai ƙedararriya Aliyyu ya ɗakko wannan karon, faɗi son ranki yarinya na ɗan lokaci ne".
Ta wuce cikin gidan tana jinjina kai ranta a ɓace, Maryam ta bi ta da kallo, sai tausayin Aliyyun ma ya kamata, ashe haka matar tashi take sam babu aji babu nutsuwa, kwata-kwata ba su dace ba ma, ta taɓe baki ta shige ɗakinta ta kwanta a kujera.
Babu jimawa ta ji ƙarar buɗe ɗakin da ta mayar da shi kitchen, can kuma ta ji an ƙunduma ashar, sannan aka fara watso kaya tsakar gida, ta fito da sauri ta ga Lubabatu ta ci ɗamara da ɗankwalinta tana watso mata kaya waje, "Ke mahaukaciya!" Maryam ta faɗa cikin daka mata tsawa daidai sanda ta jeho flas ɗin shayi ya fashe.
Lubabatu tana haki ta ce"Ke ce babbar mahaukaciya da har kike tunanin kin samu miji kin samu gidan zama, wato ke saboda shaharar taki ta fi ta sauran matan da yake aurowa har inda ya ba ki ma ya yi miki kaɗan sai da kika tsallako ɗakin ƴaƴana ko?"
Maryam ta ce"Matsayina da naki ɗaya ne a gidan nan, don haka ina da cikakken ƴancin baza kayana a inda na ga dama".
Ta ce"To ga shi na watso miki su waje, na nuna miki ba ki isa ba, sai me? Me za ki iya?"
Maryam ta yi murmushi ta ce"Wannan ba shi yake nuna ban isa ba, lokaci shi zai nuna hakan, watso kaya kuwa mijinki kika yi wa asara, domin wallahi daidai da cokali ɗaya ya samu matsala sai ya biya ni, kin ga ko yawan naman miya ya rage miki ke ma asara ta shafe ki".
Lubabatu ta yi shewa ta ce"Hehehe! To Allah Ya nuna mana lokacin, kin ga wannan gidan? Ramin kura ne, sai ƴaƴanta, wallahi yadda kika shigo salun-alun haka za ki fita, ai na ji labarinki yawo kike kina aure-aure, ga haihuwa kamar akuya, to a nan dai ko kaza ba za ki haifi ba, mijina nawa ne ni kaɗai don ni aka halicce shi, ni uwarsa Ladidi ta haifawa shi, don haka ƙaryar ƴan iskan titi irinku ku ce za ku shiga tsakaninmu!".
Daga haka ta fice daga gidan buguzun-buguzun kamar za ta dungura.
Maryam ta zauna a dokin ƙofa tana kallon kayanta da suke watse kamar a filin baje koli, ta ce"Wannan karon kuma da haka na fara? Ya Allah ka agaje ni, ka ba ni ikon jurewa".
Ta shiga ɗaki ta ɗauki waya ta kira Aliyyun ta zayyana masa komai, ya ruɗe yana faɗin"Ba ki kula ta ba ko? Ba ku yi faɗa ba? Ga ni nan zuwa".
Ta fito ta shiga ware waɗanda babu abin da ya same su, wanda suka fashe kuma tana ware su a gefe guda, ta gama ta zauna a tsakar gidan tana game a wayarta, duk da ba ta da cikakkiyar nutsuwa, a haka Lubabatu ta dawo tana ta zage-zage ta shige ɗaki da yaranta.
Babu jimawa Aliyyu ya shigo gidan da sallama, Maryam ta yi murmushin yaƙe ta ce"Sannu da zuwa".
Sai ya ji dama-dama a zuciyarsa don hakan ya nuna masa ba ta ɗauki abun da zafi ba, ya ƙarasa yana cewa"Yawwa Maryam, wai me yake faruwa?"
Ta ce"Ba fa wani abu ba ne, kawai tana dawowa ta shiga ta fara watso mini kaya waje, ai babu komai ya wuce".
Ya ce"Subhanallah! Don Allah ki yi haƙuri".
Ta yi murmushi ta ce"Ya wuce fa, kawai ga kayan nan ka nuna mini inda zan zuba su, don ba zan saka su a ɗaki ba, su kuma wanda suka fashe ka ga dole sai dai a biya ni, ko na lissafa maka ka biya ko kuma ita ta biya".
Ya ce"A'a zan biya ki, ki lissafa ɗin".
Ta ce"Ok, yanzu ina ne zai zama kitchen ɗin nawa?"
Ya yi jim kafin ya ce"Haƙuri fa za ki yi Maryam, saboda ba ni da inda zan ba ki wallahi, ki daure ki saka su a ɗakin kawai".
Ta yi shiru zuciyarta na ƙuna, amma da ta tuna shi yaƙi ɗan zambo ne sai ta ce"To shikenan, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Ya ce"Amin,Allah Ya shi miki albarka matata, na gode sosai".
Ya taya ta suka shiga da kayan ɗakin, wanda suka fashe kuma ta ce ya san yadda zai yi da su don ba ta son ganinsu, a dole ya fita da su daga gidan, ya dawo tarar da Lubabatu a tsakar gida tana hura hanci, ya ce"Ashe kin dawo".
Ta ce"Ga shi kuwa!".
Ya ce"Shi ne kuma kika dira da fitina, wai ke sai yaushe za ki girma?"
Ta ce"Sai ranar da ka gane na girma da yi mini kishiya".
Ya yi guntun murmushi ya ce"Yanzu me zan kawo? Me za ki dafa?"
Ta wani juya ido wanda Maryam da take leƙensu ta windo ta ga kamar da gayya ta yi hakan, ta ce"Kayan miya ne babu ai, sai ka haɗo da kaji biyu, idan da manyan mangwaro ma ka sako sai na yi mana lemo".
Ya ce"Babu matsala bari na je zan aiko".
Ta raka shi har zaure ta dawo ta shige ɗaki, Maryam ta zauna tana mamaki, kenan duk wannan ta'adin da ta yi ta yi a banza bai ma kai abin da ko faɗa za a yi mata ba? Kuma da alama yana sonta sosai, to idan haka ne me yasa dole sai ya ƙara auren? "Allah Ya ba ni ikon jurewa" Ta faɗa a fili tana jinjina kai, sannan ta lissafa asarar da aka yi mata ta tura masa kuɗin, ta ce kuma kayan zai siyo, aikuwa da daddare da su ya dawo yana ta ƙara ba ta haƙuri.
A ƙarƙashin gado ta zuba wasu kayan kitchen ɗin, na amfanin yau da gobe kuma ta zuba su a kwando ta ɗora a kan randarta dake cikin falon, akwai wata randar babba a waje, a nan ƙofar ƙofar ɗaki take yin girkinta, ta kwashe ta kai ɗaki, idan dare ya yi ta shiga da gas ɗin ɗaki, duk ranar da ba ita ce da girki ba to tsakaninta da Aliyyu sai dai idan sun haɗu a tsakar gida ta kalle shi ya kalle ta, wannan dokar Lubabatu ce, a ranar girkinta ko gaisuwa ba za ta shiga tsakaninsa da Maryam ba ballanata wata magana ko kuma ya leƙa ɗakinta, da farko abun kamar wasa Maryam ta ɗauke shi, sai da ta ga ko ta gaishe shi ɗin ba ya amsawa sannan ta shafawa kanta lafiya ta bi doka, amma abun mamaki ita idan ranar girkinta ne har ɗakin Lubabatun yana shiga ya zauna ya daɗe, amma dai haka ta yi shiru saboda a zauna lafiya.
Satin Maryam ɗaya a gidan ta yi wankin kayanta ta shanya a igiya, za ta bar wajen kenan Lubabatu ta fito cike da masifa ta ce"To sannu hamshaƙiya! Ita igiyar daga gidan tsoho kika zo da ita da za ki shanya ruɓaɓɓun tsummokaranki?"
Maryam ta ce"Ki iya bakinki dai, waje na gani shiyasa na yi shanyata, idan ma za ki hana ni ba ta wannan hanyar ya dace ki bi ba, idan kika ce na kwashe salun-alun zan iya kwashewa, mene ne igiya indai ba nuna tsiya ba?"
"Ai kin san ke ce kika fito daga gidan tsiya! Shiyasa ga tsiyar nan tana ta magana a jikinki" Lubabatu ta faɗa tana bin ta da harara.
Maryam ba ta kula ta ba, ta kwashe kayanta, ta mayar roba, ta shiga ɗaki ta kira Aliyyu ta ce ya aiko mata da igiya, babu jimawa kuwa ya aiko, ta shanya kayan ta shiga ɗaki ta kwanata Lubabatu ta fito da reza ta yanke igiyar, ji kake yifff! Kayan sun zubo ƙasa, ta yi wuf ta fice daga gidan, Maryan ta fito ta ƙara ɗaura igiya ta ɗauraye waɗanda suka ɓaci ta koma ɗaki, Lubabatu dake laɓe a ƙofar gida can ta leƙo ta ga ta ɗaura igiyar ta ƙara dawowa ta yanke ta, ta sake ficewa, sannan ta tafi inda za ta je, Maryam ta sakw ɗaurawa ta koma ɗaki.
Tun daga ranar indai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 21