Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
faru a gidan nan wanda ba zaka so faruwar shi ba," Tana kaiwa nan ta faɗa band'aki ta bar shi a wajen, shi kuwa Alhaji zama ya yi kawai yana nazarin maganganun ta yana so ya gano laifin shi, buɗe qofar uwar d'akin nasu akai babu sallama ba komai aka shiga, Alhaji na d'aga kai idanun su ya sarqe da na juna.......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH    💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 13: "Me ya shigo da kai har cikin bedroom ɗin  mu Sahabee?" " Ah Yayah dama kana nan, ai na yi ta sallama a can parlour na ji shiru kuma da fari na ji kamar hayaniya sanda na shigo ana daga muryoyi,to da nai ta sallama na ji shiru shi ne yasa na zaci ko wani abu ne ya faru kawai na shigo kai tsaye," wani irin kallon ka raina min hankali Alhaji ya yi masa sannan yace, "Babu komai to je ka kawai," Hajiya Babba ce ta fito daure da towel, tana ganin Sahabee ta daburce bakin ta ya hau rawa tana son tayi magana ta kasa, nan da nan Alhaji ya sak'awani zargi cikin zuciyar shi game da abinda ya faru,shin me ya sanya qanin nashi shigowa kai tsaye ba tare da neman izini ba? Me yasa Hajiya rikicewa daga ganin Sahabeen a d'akin tin kafin ta san dalilin zuwan shi?  Ɗauke kallon shi ya yi daga na ta, ya yada jikin shi kan gadon ya rufe idon shi yana tinani, a gaggauce ta saka riga ta fita waje, a farfajiyar gidan ta ga Sahabeen ya na ta Kai wa da komowa, cikin faɗa Hajiya tace masa, " kai wanne irin soko ne Sahabee, me ya kai ka zuwa yanzu?" "Ina zaune a d'aki ne kika fad'o min a rai sai na ji ina buqatar ki ko na minti gomane,to da yake d'azu na ga shigar shi wajen waccan yarinyar na san zai dad'e, Iya na can ta sani a gaba da zance bana ma gane ina ta dosa,to shine yanzu da ta shiga ciki ta kwanta dan ta huta kawai na yo nan, ban zaci ya dawo ba," Hararar shi ta yi,Sannan ta ce, " kai wane irin shiriritacce ne, amma dai kasan a qa'ida in yana nan baka zuwa ko so kake yi asirin mu ya tonu ne," Sosa qeyya ya yi ya sunkuyar da kai ,ita kuwa sai ta buga tsaki ta juya ta yi ciki, Alhaji duk yana kallon su ta window yana ayyana abubuwa da dama akan su, tana shiga sashen nata ya koma ya kwanta, duk da baya jin hirar su saboda tazarar dake tsakani,kallo ɗaya zaka yi musu ka gano akwai wani abu dake wakana a tsakanin su, Idon shi ya rufe kamar yanda ta bar shi, ta koma ta ɗauki mai ta fara shafawa a jikin ta da ya bushe. Hajiya Qarama ce kwance a gado tayi ruf da ciki tana waya cike da Jin dad'i kamar wata budurwar da ke  yin hira da saurayin ta. " Yanzu kana ganin za ka kai wani satin a gari ne?" " A'a gaskiya ina jin jibi ma zan koma, akwai matsala ne, ko kina son ganina ne?" " kwarai da gaske ina son ganin ka, dan akwai magana mai matuqar mahimmanci da za mu yi da kai," "To shikenan sai ki samu lokaci ki fito mu gana ko," Sai da suka  taba zantukan su na lalacewa kafin daga baya su yi sallama da juna, cike da fargabar me zai je ya zo ta yanke shawarar yanda za ta fita, ita zata karbi girki da dare dan haka ran ta kwal tana ta murna zata samu damar tambayar fita unguwa, Alhaji kuwa fatan shi bai wuce ace tayi wanka ta yi brush kafin dare, ga mace har mace amma ba gyara, dan gaskiya Hajiya Qarama bata da muni ga jikin ta mai kyau sai baqar qazanta da wari. A haka lokacin komawa sashen ta yayi sai ya tattara ya dawo bangaren ta, ba laifi tayi wanka tayi brush harda su sabon kitso,amma fa gaba ɗaya bata qamshi gata nan ne dai kawai a lallab'a auren zamani,a wannan karon Alhaji ya sha karairaya da gata dai-dai iyawar ta, har suka yi shirin kwaciya bacci,sai da komai ya gama kan kama ana soyayya warin hammatar ta duk ya cika masa ciki saboda sai ya zamana kamar tana aikin qarfi ne tana haɗa zufa warin na fitowa, cikin fada ya fara yi mata magana, "Wai ke sau nawa zan yi maki magana ne akan kina amfani da turaruka a jikin ki ne ? Ga su nan da yawa har ban san iya adadin su ba saboda naki ma na musamman nake siyo maki amma ke sam baki san meye amfani da tirare ba ko saka abun da zai ɗauke warin hammatar ki kamar Alimun ko lemon tsami, sai dai ki zauna kina wari malam meye hakan?" Tsaki ya yi ya zare jikin shi daga nata ya sauka daga gadon,da gudu ta bi shi zata maqale shi ya fizge ya bar inda take, kayan shi ya saka ya fice daga dakin,direct ban garen Eamaan ya je ya kwankwasa, Hafsat ce ta buɗe masa qofar idanun ta dauke da bacci, dik da haka sai da ta gane yana cikin damuwa, gefe ta koma ya shige ciki ko kula ta bai yi ba, direct d'akin Eamaan ya nufa,can ya hango ta tana zaune kan sallaya tana karanta qur'ani idanun ta ƙyamas bata jin bacci, agogo ya kalla yaga sha biyun dare ya ɗan gota, d'aga kai ta yi ta kalli cikin idanun shi,nan take yanayin fuskar shi da ya shigo da shi kamar mayaqi ta koma kamar ta qaramin yaron da kallon mahaifiyar shi ya saukar masa da natsuwa,kallon juna suka sake yi yaji farin ciki ya mamaye baqin cikin da ya zo da shi,cikin sanyin murya ya furta, " Tabbas Eamaan ke alkhairi ce a gare ni, ko raina ne ya ɓaci na gan ki hankali na sai ya kwanta,may i spend the night here with you please? Dan in baki barni ba yanda nake jina ɗin nan waje zan tafi," Ya qarasa Maganar cikin muryar tausayi, qur'anin ta ta rufe ta ajiye a gefe sannan ta yi masa nuni da hannu ya je gare ta,kamar qaramin yaro haka ya isa gare ta ya kwantar da kan shi a cinyar ta, ita kuwa nan take ta sanya lallausan hannun ta tana shafawa a hankali "Eamaan ina jin tsoro, ina matuqar jin tsoro, bana son abinda zuciya ta ke zargi game da matana ya zama gaskiya, in hakan ta kasance tabbas zuciya ta bugawa za ta yi na mutu, " Hawaye ne ke gangara daga idanun shi zuwa fuskar shi daga nan sai su yi masauki a cinyar ta,itan ma hawayen take share wa dan kar ya gani, amma inaa ya riga da ya gan su, " Eamaan kema kina zargin su akan cin amanar aure na ko? Please Eamaan tell me what you think maybe  going on in this house, coz i am going insane na rasa me yake faruwa na san cewa tabbas something is fishy in this house amma na kasa gano menene," Kama kan shi ta yi sosai ta manna da qirjin ta tana ci gaba da shafa bayan shi bata ce komai ba domin kuwa bata da abin fad'e ɗin,sai da ya yi kukan shi ya qoshi sannan ya gyara kwanciyar shi har a wannan lokacin bashi da walwala, babyn su ne yai first kick din shi aiko dukkan su suka zabura,cike da murna suke shafa cikin, "Alhamdu lilLAAH kaga baby tana baka hakuri ko, tace Daddy ya yi hakuri akan koma me ke faruwa dashi ya barwa Allah lamuran shi,abinda ake so kowanne bawan Allah yayi shine ya kiyaye dokokin Allah, to sai Allah ya kiyaye shi, sannan tace na sanar da kai ka zama mutum mai kare kanshi daga zina Allah zai kare masa iyalan shi da zuri'ar shi baki d'aya daga zinar, dan haka ina ganin saqon d'iyar ka ya isa ya sanya ka daidaita lamuran ka, ka rabu da zunubai ka yawaita istigifari, Allah mai yawan gafara ne ga bayin shi da suka nemi yafiyar shi, Allah Al-haleem ne, mai yawan kauda kai akan zunuban mu, bana son kana tada hankalin ka akan abunda bai zama gaskiya ba ka ji Babyna?" Maganganun ta sun samu kyakkyawan mazauni a ran shi, a cikin zuciyar shi ya qudirta yau kam ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ya daina neman mata har abada, kalmar ta ta qarshe ce ta sa shi murmusawa wai baby,rungume ta ya yi yana ta yi mata godiya, ita kuma ta ci gaba da shafa kan shi, a haka ya yi bacci yana jin kamar an dauke masa wani qaton dutse akan shi,miqa hannu ta yi ta dau qur'anin ta ta ci gaba da karantawa, shi kuma yana ta baccin shi k'wance da kan shi sannan cinyar ta,daga qarshe itama baccin ne ya dame ta ta miqa hannu ta d'akko masu pillo ta saka masu a wajen suka kwanta, bacci suka yi har asuba, sannan suka tashi suka yi brush su ka yi sallah, azkar ta yi ta taba karatu wanda shima ya qoqarta kwatantawa yin hakan, bayan sun gama ne ya miqe yayi mata sallama ya tafi, Hafsat ce ta shigo suka gaisa da qanwar ta ta tace, " Akwai wani abu da kike sha'awar ci ne yau?" " Eh dan Allah ki soyan chips ki baɗe shi da mai da yaji, amma kar ki soyan kwai bana son qarnin, kuma banda tea kawai zallan ruwan randar sanyinnan dana ce driver ya siyo jiya ya ishe ni, ina ce kin zuban ruwa a ciki," "Oh ni Hafsat wannan kwad'ayi na bani mamaki, eh na zuba maki ruwan maman biyu," Dariya suka yi sannan Hafsat ta qarasa shiga ta zauna a gaban Eamaan, " Eamaanii meke faruwa ne ke da Alhaji? Kar fa ki zama kina bashi had'in kai kuna shiga haqqin sauran matan shi dan na ga yana yawan zuwa nan ko ba lokacin girkin ki ba, kinsan shiga haqqin wani haramun ne ko?" Ta fuskanci inda yayar tata ta dosa,dan haka sau ta zauna ta sanar da ita dik abinda yake faruwa a gidan, Hafsat ta yi matuqar jinjinawa qanwar ta domin tayi qoqari ainun wajen cika dalilin da ya sa aka aura mata Alhajin, miqewa ta yi bayan ta yi addu'ar Allah ya kyauta, taje ta yi mata abinda take so taci ta kawo mata. Bayan komawar Alhaji sashen Hajiya Qarama wanka ya shiga ya sake yi sannan ya shirya cikin manyan kayan da suka fito da quruciyar da ta yi masa saura a tare da shi,yana tsaka da fesa turaruka Hajiya Qarama tace, " Alhaji ina son zuwa gidan mu na dad'e ban je ba Mama nata yin waya akan yaushe zan kai su Sabeerah, kaga week end ne zata ji daɗi idan na kai su yau, kai kan ka ka jima baka je gaida Mamana ba idan ka kai mu kuka gaisa sai ka tafi in yaso inna gama na kira driver ya dakko mu," "OK to ki shirya mu je na aje ku din," Cike da murnar samun nasara ta fara shiri ita da yaran, kwana biyu yaran na son zuwa gaida Aunty Eamaan amma an hana su sam,haka suka gama shirin su suka fita harabar gidan, Alhaji sai da ya sake leqa Eamaan suka gaisa again sannan ya fita,kan ya dawo Hajiya Qarama ta cika ta yi famm, a duniya ta tsani wannan mahimmancin da Alhaji ke baiwa Eamaan,kwafa ta yi tace muzuba mu gani idan tusa zata hura wuta kuma a juri zuwa rafi da tulu dan kuwa watarana zai tarwatse a qasa,shiga ya yi motar ya ja su sai gidan su hajiya qarama, maman ta ta ji dad'in ganin ta sosai,nan take sai Alhaji ya cire zargin komai da ke ran shi a ada game da yawan fitar ta, bayan sun gaisa ne kawai yayi masu sallama ya tafi,a can qasan layin su Hajiya Qaramar ne ya ga wani abokin shi nan ya tsayar fa mota a gefen titi suka tsaya gaisawa saboda an dad'e ba a haɗu ba. " Mama bari na je kasuwa na dawo, zan d'an sai wa abokiyar zamana wasu abubuwan da take kwad'ayi kin san me ciki," "  To shikenan Amma fa kar ki dad'e," Shine abinda maman ta ta ce ita kuma ta sa kai ta bar gidan,tana fita soron gidan su ta fesa turaruka masu daɗin qamshi sannan ta dauki sweet mai qamshi a jakarta ta saka a bakin ta( kun ji dai Hajiya Qaraman shagali abinda take yi ko? ta iya yi ma wani qato shiri mai kyau amma banda mijin ta) mai adaidaita sahu ta tare ta hau ta fad'a masa inda zai kai ta, babu b'ata lokaci ya yi hanyar gidan Alhaji Saminu na shaqatawa da ita, gilmawar ta Alhaji Abdullahi ya gani a cikin adaidaita sahu, cikin hanzari ya yi wa wannan abokin nashi sallama ya bi bayan su, daidai qofar gidan  ta tsaya ta sallami mutumin ta fad'a gate d'in da yake a bud'e ,dan ya san da zuwan ta yana ciki yana jiran ta, gidan ko mai gadi babu saboda baya son sa ido,tana shiga Alhaji ya qaraso da motar shi, ya shige ciki shima.......... *Chaiiiii shift let me faint i beg, dan na san Alhaji sai ya suma sau tara, na yi masa karar ɗaya ya cike goma*😱😱😭 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 14 : Tana shiga ta yi sallama Alhaji Saminu ya fito daga shi sai gajeren wando, yana ganin ta ya buɗe mata hannu alamar ta je gare shi, babu b'ata lokaci ta cire mayafi ta yar a qasa ta nufe shi da sassarfa zata rungume shi taji an daka mata wata gigitacciyar tsawa,Alhaji Abdullah ne yace, "Idan kika kuskura kika taɓa shi a gaban idona sai na kashe ku gaba ɗayan ku," Cike da fushi da d'acin rai yake yin maganar dake nuni akan zai iya aikata abinda ya furta akan nasu, kallon shi ta yi a kidime da tsantsar tashin hankali dan kuwa shine mutum na qarshe da take son gani a yanzu a kuma wannan halin da suke ciki,Alhaji  Saminu ne ya qarasa takowa gaban Hajiya Qarama ya sunkuyar da kan shi ya yi kissing ɗin lips d'in ta,ganin haka ne ya sanya Alhaji Abdullahi jingina da kujerar kusa da shi saboda ganin qarfin halin Alhaji Saminu, gaba ɗaya ji ya yi jiri na diban shi, Hajiya Qarama d'an baya ta ja daga jikin Alhaji Saminun idon ta sai zubda hawaye yake yi, haƙuri take son ta bud'e baki ta bashi amma inaa ta kasa, "Na san me ya kawo ki waje na Hajiya, kuma wannan ranar nake ta jira sai dai to my biggest suprise sai ga shi kin zo min da babban gift na zuwa da Alhaji" Ya juya ya kalli Alhaji Abdullahi da isa da ta qama sannan yace, "Ban fada maka ba?  I vow to destroy your life and family from the day you destroy mine, Alhamdu lilLAAH i have succeeded in destroying your family, yanzu sauran abunda ka mallaka ka jira ni ina nan tafe kan dukiyar ka,maza ka tarkata matar ka ku bar min gida kafin na sakar maku durwan kare na, yayi maku fata-fata," Komawa d'aki yayi ya dakko rigar shi ya saka,Hajiya Qarama ce tayi qarfin halin cewa, "Me ke faruwa ne a tsakanin ku mara daɗi har haka?me yayi maka kake fadan hakan?" Dariya Alhaji Saminu ya yi sosai sannan yace, "Lallai ne ashe fa ke baki san tarihi ba, to bari kiji me mijin ki yayi min har na fara neman ki dan baqanta ran shi, a shekaru masu yawa da suka wuce, lokacin mijin ki na tsakiyar akuyancin shi daga zuwa gidana mu ci abinci, ya qyalla ido akan qanwata kuma amana ta da iyayen mu suka rasu suka bar min, amma haka wannan d'an akuyan ya sata a gaba, sai da yayi mata ciki har sau uku yana kai ta ana zubarwa babu wanda ya sani, a na huɗun ne basu samu nasarar zubarwar ba, jini ya ɓalle mata sakamakon ji mata ciwo a mahaifa da aka yi, " Share hawaye suka yi kusan a tare shi da Alhaji Abdullahi wanda tin da Alhaji Saminu ya fara bada labarin ya hau tina yanda abubuwa suka kasance a tsakanin su a shekarun baya wanda har yanzu idan ya tuna kuka yake yi na tsantsan nadamar lalata kamilar yarinya da ya yi, Alhaji Saminu ne ya ci gaba da cewa, "Tin daga wannan aikin da aka yi mata ta dinga zubda jini kuma taqi fadawa kowa sai a ranar da zata koma ga Allah ne take neman gafarar mu ni da mata ta,a nan ne ta faɗa mana komai da ya faru tsakanin ta da kai, a dai-dai lokacin da qanwata ta mutu wannan bunsurun ya sake ɗaukan wata d'iyar abokin mu ya fita da ita qasar waje yana sheqe ayar shi da ita, duk sai da qanwata ta zo rasuwa ta faɗi abinda ke faruwa, domin kuwa qawar ta ce, a haka ta mutu bai zo ba daya dawo, sanda na je na same shi da zancen lokacin ya fini komai a rayuwa, kuɗi suna, mulki da iko sai yayi min korar kare, tin daga lokacin na quduri niyyar sanadin komai na farin cikin ka, ina fatan ɗaya tarkon dana d'ana a cikin gidan ka shima ya tashi bayan na dukiyar ka dana d'ana maka nan da wasu kwanaki ko watanni, Allah ne kawai masanin sanda zai tashi bummmm,se dai ka ga dukiyar ka ta zama tarihi" Maganganun shi sun yi matuqar tsorata Alhaji Abdullahi da Hajiya Qarama , Hajiya Qarama kuwa ji ta ke kamar ta kashe Kan ta ta huta dan takaici, Alhaji Saminu ne ya daka masu tsawa gaba ɗayan su yace su tashi su fitar masa a gida, " Ohhh na manta Hajiya ko zaki ɗan tsaya ne mu ɗan yi na yau kan ki tafi?" Sai ya isa wajen ta yana shafata cikin wani irin yanayi na duniyanci,janyewa take tana kuka sosai Alhaji ya rintse idon shi, ya miqe da kyar yana hada hanya ya fita daga gidan direct mota ya faɗa hankalin shi a tashe,da taimakon Allah ya isa gida, ita kuma gidan su ta koma ta d'ebi yaranta ta yi gidan Alhaji da su, kowa ya tambaye ta meya sa ta kuka taqi kulawa, ganin haka yasa suma yaran kawai suka fara kuka, a haka suka isa gida yara kuka Hajiya kuka, yana zaune cikin mota yana ta rusa kuka dan ya kasa fita balle ya shiga ciki be san wa zai tinkara da wannan musibar da ta same shi ba, a haka ta shiga gidan ita da yaran,d'aga rinannun idanun shi ya yi ya kalli hanyar da take son bi yace, "Ashe matar nan bata da kunya? Me kuma ya dawo da ita gidana bayan ta ji na san komai? Maybe ta na da death wish ne ya sa ta dawo," Cike da fishi ya ɓalle murfin motar ya nufe ta,wasu kyawawan maruka ya tintsira mata sai da ta kifa qasa, ya bita ya take mata qafa ihu ta zabga wanda ya sanya Sahabee da Hajiya Babba dake tsaka da holewar su suka miqe tsaye a firgice a gigice,nan take suka ɗauki kayan su suka mayar, Sahabee ne ya fara fitowa waje sannan Hajiya Babba, ball suka ga Alhaji na yi da Hajiya qarama yaran ta na ta ihu suna kiran Daddy kar ka kashe Mum din mu, ihun su ne ya fiddi Iya da Eamaan da Hafsat farfajiyar gidan suma, sai masu aikin gidan dake lab'e suna kallo ikon Allah Ita kuwa hakuri kawai take bashi amma yaqi ma yin magana, dan wani abu yake ji ya tokare masa maqoshin shi,Eamaan ce ta tako a hankali cikin ɗan cije lebe dan yanzu ciwon kai ke damun ta,yana ganin Eamaan ya nufe ta da sauri kamar qaramin yaro, ya fada jikin ta, saurin tsaida jikin ta ta yi saboda kar su faɗi,hannun ta dika biyun ta sanya ta zagaye jikin shi da su, kuka ya saki mai qarfi yana ta yi ba qaqqautawa, ita kuma bata hana shi ba sai buga bayan shi da take yi, Iya abun nan ya d'aure mata kai matuqa dan kuwa bata gane komai ba, cike da Umarni ta kira sunan shi, ya d'ago sai ajiyar zuciya yake yi ya kalle ta Iya tace, "Abdullahi sanar dani meke faruwa ne haka a gidan yau kuma?" Eamaan ce ta kama hannun shi ta ce ma Iya, "Iya mu shiga daga wajen ki ko kinga kowa na kallo har da masu aiki, ina ganin in ya zauna ma zuciyar shi zata fi sanyi ya ji dad'in sanar da ke komai," kallon Eamaan d'in Iya ta yi ta kad'a kai sannan ta yi gaba,dikkanin su d'iba suka yi zuwa part din Iya,kamar Sahabee ya gudu haka yake ji saboda kar asirin shi ya tonu, dan tabbas ya san asirin Hajiya Qarama ne ya tonu, suna isa kowa ya zauna Iya ta maimaita tambayar ta, Alhaji cikin kuka ya sanar da ita su Sabeerah ba yaran shi bane, ya qara da Sanar da ita wanene uban su, Salati Iya ta ɗauka,nan da nan ciwon ta ya tashi, da gudu suka nemo maganin ta suka hau dura mata, ana jera mata sannu, Eamaan ce tace a kaita daki ta kwanta ta huta in ta samu bacci tinda dana bacci ciki zata samu sauqi inshaa Allah, d'aki Sahabee ya kaita hankalin shi a matuqar tashe, qin komawa parloun ya yi ya zauna nan wajen Iya, Alhaji Abdullahi kuwa miqewa tsaye ya yi ya nunawa Hajiya Qarama hanya ya sanar da ita ya sake ta saki uku, kuma ko tsinke ba zata ɗauka a gidan ba tinda shi ya siyo mata dik abinda take taqama da shi dan haka ta fitar masa a gida yanda ta shigo, kuka take kamar ranta zai bar jikin ta amma ba wanda da ya tausaya mata,kowa ta kan shi yake yi a wajen, musamman Hajiya Babba da ta sa a ranta in dai aka kori Qarama zata tona masu asiri, nan ko bata san hankalin Hajiya qarama yayi tashin da ta manta da rayuwar su balle ta tona masu asiri, tankad'a ta Alhaji ya yi waje sannan ya yakice yaran dake ta kuka suna kiran Daddy kayi hakuri bazata sake ba, muma ba zamu sake ba, Eamaan ce ke kuka dan sabo da yaran da ta yi,yana ganin hawayen ta kuwa ya haukace da faɗin, "ku tafi nace shegu tsinannu kuna saka min mata kuka, tankad'a kan su ya yi, ya  kira masu aikin gidan maza tare da basu Umarnin a fitar Masa da su daga gidan,ya miqe ya nufi bangaren Eamaan,dan tinda ta ga ya haukace da korar yaran da mahaifiyar su ta bar wajen tsabar tausayi, tadda ita ya yi tana ta kuka bai hana ta ba,dan ya san ko giya ya sha ba zai dawo da Qarama ba ta tafi kenan, sai da ta yi mai isar ta sannan ta miqe ta yi toilet ta gyara fuskar ta ta fito, tana fitowa ta gan shi kwance sai hawaye ke tsiyaya daga idanun shi, "Dama abun da na aikata a baya na nan na bina ban sani ba? neman lokaci irin wannan yake ya d'aid'ai ta ni? to me ne ne Saminu yace sauran ɗaya bomb din? Me zai faru kuma bayan wannan cin amanar da Qarama tayi min?" "Ba abinda zai fatu sai alkairi, dan haka ka kwantar da hankalin ka ka ji," Da wannan ta ɗauke hankalin shi da salon ta da ya yi kewa. Ba dan k'warewar da Eamaan ta nuna masa ba da kuma son da yake yi mata baya jin akwai abunda zai ɗauke masa takaicin wannan ranar, ranar dai Hafsat barin bangaren su Eamaan tayi ta koma na Iya, dan gaba ɗaya Alhaji ya haukace a kan Eamaan, idan Alhaji yana gaban Eamaan jin shi yake yi kamar jaririn ta, zai iya yin komai gaban ta. A kwana a tashi cikin Eamaan ya kai wata bakwai kullum Alhaji cikin nasiha yake mata akan ta kula da abinda ke cikin ta,dan yasan ko bayan ba shi babu mai kula masa da abinda suka haifa a dangin shi,ba masu son shi domin Allah

Chapter 9 of 20