hayan da suka kama a cikin gari suka nufa dikkannin su babu mai cewa kowa komai a hanya,bayan tafiyar su kuwa Eamaan ta zauna dab'as a qasa tana ta kuka,cikin kuka ta ke faɗin,
"Na rantse ba wanda ya isa ya ɗauki Yarinyar nan a cikin azzaluman can, Ammaah dan Allah ku yi min alqawarin ko me zai faru ba zaku bada Fatee ga wad'ancan marasa Imanin ba, gwanda akai ta gidan marayu wasu su ɗauka su raine ta dana basu ita, Ammaah baku san halin mutanen nan bane,Sahabee shine ya yi sanadin da ciwon Alhaji ya tashi har ya kai shi ga mutuwa, a gaban Alhaji ya so keta min haddi Allah ya bani iko na yi masa duka da muciya,Sahabeen nan da kuke gani shine ke neman matar alhaji tin da ran shi, Iya ta sani amma bata d'auki mataki ba,Iya ta san Alhaji bashi da lafiya amma ko ta nuna damuwar ta akai, kaiiii wadannan ba mutane bane, they are monsters, they don't deserve to be called humans, ba su da humanity kwata-kwata a tare dasu Ammaaaaah,"
kuka take yi tin qarfin ta tana wata iriyar jijjiga,Ammaahn ta na gefe tana share hawayen ta itama,Mama ce ta zo ta rungume ta ta d'aga ta a wajen ta kaita d'aki ta kwantar da ita tana shafa kan ta a hankali da sigar lallashi,tana nan zaune da Eamaan har Eamaan tai bacci, Fatee ma dake kuka ma ta yi nata baccin Ammaah ta shiga ta kwantar da ita a gefen mahaifiyar ta da ke sauke ajiyar zuciya,ta ja masu qofar suka fita.
Parlour suka koma dukkan su suka zauna jigum-jigum suna jimanta abinda ya faru a zuciyoyin su, Daddy dake zaune bai ce qala ba tinda su Iya suka zo ya sake dafe kan shi dake sara masa ya fashe da wani matsanancin kuka,kukane na dana sani da nadamar sanya 'yar shi cikin damuwa da rud'anin rayuwa, ashe haka d'iyar shi ta qunshi baqin ciki kala-kala a gidan da yayi zaton tana zaune cikin farin ciki? Yayi zaton labarin kulawar da Alhaji ke baiwa Eamaan da yaji a wajen Hafsat shine asalin labarin rayuwar da 'yar shi ke fuskanta a gidan auren ta, ashe akwai wani qullalen qulli da take fuskanta wanda tsananin Biyayyar ta ya sanya bata taɓa kokawa ba, tabbas bai wa d'iyar shi adalcin haɗa ta aure da Alhaji ba,farin cikin shi ɗaya yanda abokin nashi ya daina neman mata kafin rasuwar shi, yasan inshaa Allah ya samu rahamar Allah, amma ta wani ɓangaren yayi sanadin samun tabo a zuciyar 'yar shi mai wuyar warkewa, dole ne ya bata hakuri ya nemi gafarar ta kada haqqin ta ya kama shi.
Ammaah da Mama ne suka zauna a kusa da shi suka dafa shi a hankali suke bashi baki dan ya kwantar da hankalin shi kar ciwon shi na hawan jini ya tashi,Ammaah ce tace,
"Ba ka da laifi akan dik abinda ya faru Alhaji,dan haka ka kwantar da hankalin ka kayi wa abokin ka addu'ar Allah ya jiqan shi, ka sanyawa 'yar ka da jikar ka albarka kayi musu fatan alkhairi a rayuwar su, Allah ya kyautata rayuwar su ya baiwa Eamaan ladan biyayyar da tayi mana,kar ka manta mahaifa suna da hakkin samarwa 'yar su budurwa miji dan haka babu laifin da ka aikata balle ka damu,"
Share hawayen shi ya yi ya murmusa yayi masu godiya ya shige d'aki ya rufe kan shi.
Bayan kwana biyu Sahabee ya haɗe kud'in da Eamaan ta basu da wanda ya sace na Hajiya Babba, wanda shi kaɗai yasan tana ajiya a kitchen cabinet ɗin ta,yayi mamaki shi kanshi da ya duba ya same su dan yayi zaton ta kwashe su da zata bar gidan,ana bashi albashi ya haɗe ya biya kudin gidan qasar da suke haya a ciki ya siye masu shi,abinda ya yi saura wanda bai wuce dubu saba'in ba kuma sai ya b'oye yana da wani quduri akan su wanda baya son sanar da Iya sai komai ya kankama.
Iya kuwa tinda ya haɗa ta da dubu talatin ta rufe bakin ta tayi shiru tana ganin ai ta samu kuɗi mai yawa duba da dama ba wani abune ya rage ba na Alhajin da suka gada da ya wuce wannan kuɗin da Emaan ta basu.
***************
Sauran kwana takwas Eamaan ta kammala takabar ta, wanda a cikin wannan kwanakin da tayi tana takaba ta fara maida jikin ta ta hakura ta dangana da rashin Alhaji ta barwa Allah komai,a yanzu tana zama a yi hira da ita sosai , a duk sanda ta tina da rashin Alhaji sai ta kaɗaici tai ta kuka, Fatee ta girma tana takawa ga wayo da take dashi bakin ta ya buɗe in tana magana sai kowa yayi mamaki saboda qarancin shekarun ta, kyawun yarinyar sai qara fitowa yake yi tare da kamannin da take yi da Alhaji.
Watarana Eamaan suna zaune ita da Yayar su da ta zo ganin gida ita da Hafsat,hira suke tayi har musu ya qarke tsakanin su kowa na cewa wajen shi Eamaan da Fatee zasu je dan su huta,Hafsa ce tace,
"Yayah ke fa kin ga baku rabuwa ke da ɗan tsohon mijin ki kullum kuna manne kamar chewing gum,sannan ba zama kuke ba a waje ɗaya, yau kuna wannan qasar gobe kuna waccan qasar ta ina zata ji daɗin zama da ku?dan Allah ki bar ta taje wajena idan yaso sanda kuka natsu waje ɗaya ta je maku, "
Hararar ta yayar sun ta yi tace,
" Lallai ma yarinyar nan baki da ta ido, to ni da ke ai anga mai mannewa miji, ke da har yanzu ba ku daina d'okin sabon aure ba yaushe zata je ta zauna da ku kuyi ta bata kunya? kinga in tana waje na ma zata fi sakewa in ba ma nan , she will have the house to her self sai abinda taga dama zata yi, pls just go with me dear ki rabu da Hafsy,"
Ta qarasa maganar ta cike da roqon Eamaan da idanun ta, dariya kawai Eamaan take yi musu tana kuma jin dad'in yanda yayun nata ke son ta, amma a can qasan ranta ta fi son taje wajen Hafsat,tinda sun fi shaquwa d'akin su d'aya sanda suna 'yammata, kusan komai a tare su keyi kamar wasu sa'annin juna, Hafsar ba ta da son girma, duk da ta baiwa Eamaan shekaru biyu da watanni amma kamar qawar ta ta dauke ta,shi yasa suka zauna lafiya tinda Eamaan ba ta da rashin kunya,a na haka Fatee ta zo sai Hafsat tace,
" Yauwa Yayah in kin yarda a baiwa Fatee zaɓin ina zasu je hutu,"
" Tab dan ku min wayo,na riga da na san ke za ta yi choosing in a minute or second ma, ban yarda ba gaskiya,"
"To Yayah ya kike so ayi kin san dai Eamaan ba zata zab'a inda zata je hutu a tsakanin mu ba ko,"
" Oh ok na yarda Fatee ta zab'a but no cheating,"
Dariya suka yi, sannan Yayah ta fara tambayar Fatee,
" My baby zaki je hutu wajena in dinga sai maki ice cream da sweets ko zaki wajen Aunt Hafsat ne?"
Kallon su ta yi Hafsat ta ɗauke kan ta tana kallon wani wajen tana dariya saboda in ba haka tayi ba Yaya zata ce tayi cheating, ita ko Yayah fuskar tausayi tasa ma yarinyar ta ci gaba da tambayar ta , gani tayi yarinya ta taka dugu-dugui ta yi wajen hafsat tana qoqarin hayewa cinyar ta cikin gwaranci tace,
"Mamaa" (haka take kiran Hafsat)
Nan da nan Yayah ta koma wajen zaman ta ta zauna ta dau lemon da take sha ta kurba ta ce,
" To kin yi nasara na amince su biki, next time sai su zo min hutu,"
Dariya suka hau yi suka ci gaba da hirar su, cikin dariya Eamaan ta kalle su cike da so tace,
" I love you guys ina alfahari da ku sosai,kuma Yayah kar ki damu dana gama hutawa gidan Hafsy zan zo wajen ki kema, sai na fi ma dad'ewa a wajen ki,"
Cikin tsamin baki Fatee tace,
"Ana sho Mamaa"
" To 'yannema mai kan buta naji kina son Mamaan na fasa baki sweet d'ina, dan kin ga ma Ina son ki shine kike min wulaqanci,nasan dan baki ganina ne sosai shi yasa da wacece wata Hafsat a kayan miya"
Dariya suka hau yi sosai, Hafsat kuwa sai ta qara rungume yarinyar a qirjin ta tana sumbatar ta,suna nan zaune suna hirar su suka ga ana buɗe gate wata had'ad'd'iyar mota mai kyau tana shigowa, kallon su suka mayar kan motar suna son suga wanene mamallakin ta,sai da yayi parking ya ɗan jima kafin ya fito cikin takun sa na isa da qasaita ya zo gaban su ya yi masu Sallama, Eamaan ba zata taba manta fuskar nan ba har bada, jikin ta nan da nan ya hau rawa ta miqe tsaye, idon ta cike da hawaye..........
*Many many many thanks to u BIYAYYAH FANS GROUP 1&2 tabbas masu son biyayyah daga gani ku masu biyayyah ne, ina jin dad'in yabawar ku a gare ni, musamman group din TAWHID IS THE KEY, a gaskiya sai godiya, sauran groups din na da yawa, ina godiya sosai, dan yabawar ku ke sa ko nai niyyar yin page d'aya na ji bari na qara maku, dan mai son abun ka sai ka taya shi so, na gode ba iyaka* *ME LOVE U ALL❤*
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 20:
Wani abu ne da ba zata Iya tantance mene ne ba ya ke taso mata a wuya, maqaqin da take ji baya yi mata dad'i, after all he put them through he have the nerve to show his stupid face a gidan su? lallai yau za a yi ta kenan dan kuwa sai ta nuna masa itama 'yar zamani ce.
Wata zuciyar ce ta taushe ta har taji a ranta tana son barin wajen tin kafin ta kasa riqe kanta, tashi tayi tsam daga sama kujerar robar da take kai zata shiga gida ɗauke da Fatee a hannun ta,tana zuwa gefen da yake zata zagaye shi ya sha gaban ta ya tsaida ita,wani kallo ta d'ago ta watsa masa da idanun ta da suka rine suka yi jawur kamar jan yadi,nan take jikin shi yayi sanyi izzar shi ta fara raguwa saboda kallon ya shige shi, sai dai taurin kai irin nashi ya hana shi ya kauce ya bata waje ta samu ta bar wajen,cikin muryar shi mai nuna isa da taqama yace,
" Hajiya Eamaan barka da war haka, ya qarin hakurin mu kuma?to Allah ya jiqan Alhaji yayi masa gafara,"
Haka ya gama gaishe-gaishen shi ba tare da ta ce masa kanzil ba, burin ta kawai ya matsa ya bata waje ta wuce, Hafsat na ganin yanayin da Eamaan ke ciki ta miqe ta isa gaban ta, hannun ta sai wata iriyar rawa yake yi,hannu ta sanya ta amshe Fatee daga wajen Eamaan ɗin ta tsaya a gefen qanwar tata.
" Uhum ina jin ka sai me ya kawo ka bayan fake concern din da ka gama nunawa yanzu? In ba ka da abin fad'a ka wuce ka tafi, kafin raina ya yi matuqar baci naka ran yafi nawa baci yanzun nan,"
" Eamaan na zo ne da magana mai mahimmanci, wanda ina ganin bai kamata muyi ta a tsaye ba,"
" Dakata min malam, kai har kana da magana mai amfani da zaka zauna ka yi min ne har na saurare ka? Waye kai? me kake taqama da shi da har zaka manta komai da ka aikata dan baka da kunya kazo min ta'aziyya? kayi kaɗan ka ce zaka yi amai ka lashe akaina, ka kama hanya tin bamu shiga wani hali na rashin mutunci da kai ba,"
" Ina son ki Eamaan kuma auren ki nake so nayi wannan shine muhimmin abinda ya kawo ni wajen ki, ina sane da kin gama......"
Wani shahararren mari ta ɗauke tsohon mutane da shi, ta qara yanka masa wani marin, haka ta dinga kifa masa mari tana kuka, Yayah ce ta iso gare ta da gudu ta riqe ta tace,
" Ke Eamaan baki da hankali ne kike marin babban mutum kamar wannan, me yake damun ki ne, kalmar so tana jawo qiyayya ne?"
Cikin qara da tsawa ta furta
" Eh Yayah ! kalmar so na jawo gaba ma ba qiyayya ba, Yayah wannan ne Alhaji Saminu, da ya shiga cikin taswirar rayuwar mu ya b'ata ta, ya nakasa min miji ta zahiri da bad'ini, sannan a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwar shi,waya baka damar zuwa min da shirmen kalmar so waje na? hhhhh idan ka amince zaka aure ni to zan aure ka, amma se dai in ni ce zan zama ajalin ka,shin ka yarda?"
Tinda mutanen gidan su suke da Eamaan ba su tab'a ganin ta yi faɗa da kowa ba balle har duka ya shiga tsakani irin haka sai yau, ko da ace bata tab'a son Alhaji Abdullah ba tabbas ya na da Wani babban matsayi a zuciyar ta Wanda ba zai gogu ba, Alhaji Mutum ne da ya so ta sama da yanda take ganin Anwar ma zai so ta, ya kula da ita sama da yanda ta ke tinanin Anwar zai kula da ita, Alhaji Mutum ne da baya son damuwar ta, ya tsare mata dikkan Wani haqqi na aure nata da ke Kan shi, ta ya ba zata ji mutuwar shi ba?shi ne fa uban 'yar ta tilo,
Cike da qunci da d'acin zuciya take bin shi da mugun kallo idanun ta na kwarar da hawayen baqin cikin da zuciyar ta ke ciki, 'yan uwan ta da masu aikin gidan har ma da iyayen ta da suka fito kowa sai mamakin yanayin da Eamaan mai sanyin hali da kunya tare da kawaici ta koma a cikin kankanin lokaci, yau har ta kai ga itace ke ikirarin kashe wani,cikin tsawa ta sake furta,
"Ka fita daga gidannan i don't want to see your face ever again, if you ever show your ugly face here i swear to God i will not hesitate to kill you"
Alhaji Saminu tin da ta fara kifa masa tafi ya qame qam a wajen cike da tsoron yarinyar, qasan ranshi kuwa wani ɓacin rai da qiyayyar ta ne ya mamaye zuciyar shi,ya kasa gaba ko baya ballantana yabi umarnin ta ya bar gidan,kallon idanun ta yayi yaga babu komai a cikin su face matsananciyar tsanar shi da qiyayyar shi,tabbas aka bar shi daga shi sai ita zata iya aikata abunda tace akan shi, bai ankara ba da tinanin shi ya hango glass cup na yowa ta wajen shi,alamar jefo masa akai, a qoqarin kauce masa ne ya daki kafadar shi, duk da babbar rigar dake jikin shi sai da ya ji wani zafin saukar shi a jikin shi, kafin yayun ta su kai hannu dan hana ta ta dakko wani zata kwad'a masa,yana ganin haka ya taka a sukwane ya isa gaban motar shi ya buɗe zai shige, Eamaan ta kwasa a guje ta bishi da wani cup ɗin a hannu ta saita shi ta wurga masa a kai, nan take cup ɗin ya fashe ya yanke shi a kan shi, ihu ya kurma yana fad'in,
"Ta hauka ku riqe ta kar ta kashe ni,"
A guje ya take motar shi yayi ribas ya bar gidan, banda zagin shi da tsine masa babu abinda Eamaan keyi, kuka ta durqushe a wajen tana yi mai ban tausayi, Mama ce ta iso wajen ta jata jikinta ta rungume ta tsam a qirjin ta, da fari sai tirjewa take yi tana fad'in a barta ta kashe shi tinda azzalumi ne, a hankali ta fara dawowa nutsuwar ta, sai kukan zuci da take yi hawaye na zuba mata a kuncin ta, cikin gida suka koma mama tayi mata masauki a dakin ta a gefen gadon tana shafa bayan ta a hankali,Eamaan kuwa sai ajiyar zuciya take, fuskar ta kuwa ta yi jawur kamar an kara a wuta,ruwa Ammaah ta kawo mata dan ta sha.
Ita kanta Ammaah idanun ta sun kad'a saboda ganin damuwar da Eamaan ke ciki,mamakin Alhaji Saminu kuwa ya kasa barin zuciyar ta, idan bata manta ba shine sanadin da Alhaji Abdullah ya kamu da ciwon shanyewar barin jiki, shine mutumin da ya nemi matar Alhaji Abdullah har suka haifi yara biyu,amma saboda rashin kunya ya lallabo zai ce yana son 'yar ta.
Ruwan ta kurb'a sau biyu ta ajiye saboda baya yi mata daɗi,ido ta lumshe kawai ta jingina da jikin gadon hawaye na zuba ta daga idon ta,lallai mutumin nan ya raina mata hankali, bayan duk abubuwan da yayi musu shine zai zo yace yana son ta da aure? Kwantawa ta yi ta dunqule a waje ɗaya sai sauke ajiyar zuciya take yi kamar yaron da ya yi rigima ya gaji ya yi shiru dan Kan shi,Mama da Ammaah na ganin ta kwanta sai suka bata waje suka koma parlour, cikin jimami Hafsat tace,
" Mama Ammaah ko zamu yi wa Daddy waya ne a sanar da shi abinda ya faru dan ina jin tsoron wannan mutumin, kuma ni a gani na da kawai mu tafi bauchi yau tinda bamu san me zai iya aikatawa ba, na tabbata a can ma Zata samu nutsuwa sosai,"
Mama ce tace,
" shawarar ki tayi Hafsat kuje ke da yayar ku ku fara parking kayan ku, bari na kira Daddyn ku na sanar dashi abinda yake faruwa,"
Direct daki ta wuce ta sami Eamaan kwance idanun ta kulle suna zubar da ruwan hawaye, tausayin ta ne ya kama ta, cikin sanyin murya tace mata,
" ki shirya mu tafi bauchi yanzu,na tabbata zaki fi jin daɗin zuciyar ki and ko babu komai zaki yi nesa da baqin cikin ki,"
Bude idonta ta yi da sauri ta bi Hafsat da kallon dan ta gasgata maganar ta,d'aga mata kai ta yi alamar da gaske take yi yanzu zasu tafi, cike da jin dad'i ta tashi zaune ta sauka daga gadon ta shige toilet ruwa ta watsa sannan ta shirya ta fito, Hafsat da Yaya na gama haɗa kayan su suka shirya Fatee, sun gama hada komai nasu kenan Daddyn su ya dawo.
Babh b'ata lokaci Mama ta sanar dashi dik abinda ya faru, cikin b'acin rai ya dinga masifa yana fad'in da sun sani tin zuwan shi suka sanar da shi ya dawo, hakuri suka.bashi, suka sanar da shi.plan din su, Shima ya yi.na'am da hakan, in dai Eamaan din na so, fitowa suka yi, yana ganin ta guiwar shi ta yi sanyi, yana dorawa kan shi laifin komawar ta haka,
" Eamaan ki yafe ni, i thought i did the right thing, ashe ba haka bane, dubi yanda kk koma, Eamaan ki kwantar da hankalin ki in kin je can kinji, ba zan qara saki ko wani ma yin abinda ba shi yake so ba,"
'Daga rinannun idanun ta ta yi da suka yi jawur ta kalle shi ta ce,
" Daddy ba laifin ka bane, haka Allah ya tsaran rayuwa ta,kowa da qaddarar shi, wanda ya yarda da Allah da ranar akhirah, dole ya yarda da qaddara mai kyau da mara kyau, kenan in dai ina son imanina ya cika sai na yarda hakan na cikin qaddara ta, d'ayan mu ba shi da ikon cutar da wanin shi face abinda Allah ya hukunta zai kasance, kai mahaifina ne in kana jin haka ni ba zan ji dad'i ba, kai min addu'ar samun sauqin abinda nake ji, ban tab'a dana sanin auren Alhaji ba, tinda shi d'in mutum ne da yasan haqqin zaman tare, kuma he gave me the most beautiful gift ever, gata nan Fateema, dan haka bana dana sani kuma har abada ba zan yi danasani ba thank u Daddy, for everything,"
Rungume ta ya yi sosai, hawayen shi na sauka akan ta, itama kukan take,haka duk wanda ke wajen banda Fatee dake ta wasan ta, a haka ya kai su waje, ya kira driver,
" Tinda tafiyar dare ne ka kai su washegari ka dawo a ta haya ka bar wa Eamaan motar ko zata buqace ta,"
"To ranka ya dade, Allah ya kai mu lfy,"
" Ameen"
kowa ya amsa , Daddy ya damqa wa driver kud'i shi da Hafsat da Eamaan d'in, ko da za su buqaci Wani abu, raka su suka yi har bakin mota, shigar da kayan su driver ya yi bayan motar,suka dau hanyar Bauchin Yakubu, ( yan bauchi kuna da babbar baquwa, a dafa mata shinkafa da wake😋🤣) sun dau hanya ba mai cewa komai, har suka yi nisa suka bar gari, Eamaan addu'a ta fara yi, domin ta san Allah na amsa addu'ar matafiyi, dan haka ta hau addu'a tana kokawa a wajen Allah da ya kawo mata komai da sauqi, Hafsat ce ta matsa kusa da ita ta kwantar da Kan Eamaan a jikin ta, Eamaan d'in kuwa ta kwanta ta yi shiru , Fatee ma bacci take.
Sun isa bauchi bayan isha'i, mijin Hafsat ne ya bud'e musu gate ya taya su d'ibar kayan su zuwa cikin parlour, bayan shi suka bi bayan Hafsat ta nuna wa driver d'akin da zai sauka, gidan ba Wani kantameme bane gida ne madaidaici me kyau, farfajiyar gidan bata wuce wajen aje motoci biyu ba,bayan ya ajiye kayan ne ya kama hannun matar shi ya na bin fuskar ta da kallo alamar ya yi kewar ta sosai, murmushi suka yi wa juna kafin ya saki hannayen ta ya dauki kayan su ya shigar musu d'aki, already sun yi waya da Hafsat ta Sanar da shi zuwan su tare da Eamaan d'in, d'akin ta bi bayan shi d'auke da Fatee a hannun ta ,ta masa godiya tare da qaramin murmushi, yana fita ta samu ta kwanta a gadon bayan ta kwantar da Fatee, kan ya fita sai da ya sanar da ita in ta gama.akwai abinci ta fito su ci, ta amsa masa da "To na gode"sannan ya fita, murnar dawowar Hafsat ce ta cika shi da zumud'in ganin ta kamar zai taka da gudu ya Isa gare ta yake ji, daki suka shige suka barni tsaye sororooo.
Eamaan wanka ta yi wa Fatee itama ta yi, tana ta ma ta dariya kuwa, da surutu kala kala, shiryawa ta qarasa yi itama ta fita parlour riqe da hannun Fatee,kamar yanda ya fad'a kuwa abinci ne me rai da lafiya kamar ba namiji bane ya dafa shi, zama ta yi a kujera ta kunna TV Dan ta Jira su.
Hafsat kuwa da mijin ta suna d'aki ana soye wa, an jima ba a gamu ba, Dan ma Hafsat na ta bashi hakuri ya Jira se an jima, kar Eamaan ta yi ta jiran su da kyar ya hakura ya taya ta wanka, ya bar ta ta qarasa, kafin ta fito ya dakko mata kayan da zata saka marasa nauyi, ya fesa musu turaruka, ya ajiye, ta na fita ya nufe ta ya na sake bin jikin ta da kallo, tare da fad'a mata yanda ya yi kewar ta, itan ma bayyana masa irin yanda ta yi kewar sa ta yi, sannan suka sake tambayar juna bayan rabuwa.
Ta na kammala shiri ya saqale hannun ta a nashi suka fita parlour, Eamaan na ganin su ta miqe ta sake gaishe shi, Yaya da ta kira shi da shi se ya bashi dariya, ya ce Dan Allah kar ta tsufar da shi, dariyar itama ta yi, ta ce dole ta kira shi da Yaya tinda mijin yayar ta ne shi, abinci suka ci har Fateema, suna gamawa ta miqe ta musu sai da safe, ko ba Dan komai ba ma ta gaji, sannan ta na kallon irin kallon zalamar da mijin Hafsat din ke bin Hafsat d'in da shi, be Kamata ta b'ata musu lokaci ba.
"Ba Zaki sha tea din naki ba na qa'ida Zaki kwanta Eamaan?"
"Na gaji mun had'u da safe"
Murmushi kawai Hafsat ta yi, ta kula Eamaan na Allah Allah ta Basu waje ne, Dan haka da Kan ta ta miqe ta kunna gas ta Dora ruwan tea, ya na gama dahuwa ta zuba a mug ta Dora a qaramin trey ta nufi d'akin Eamaan d'in, ta na shiga ta tarar har ta yi bacci, se surutai take a baccin nata,
" Alhaji ka dawo pls, ka zo wajen mu muna kewar ka,"
Tana ta surutai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 20