Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼 RUBUTAWA: HAERMERBRAERH MUTANEN KWARAI MASU ALBARKA GA EDITING DIN TSOFAFFIN NOVELS DINA NAN ZAN DINGA KAWO MAKU A HANKALI HAR NA KAMMALA, DAGA NAN SAI MU FAD'A SABO DA YARDAR ALLAH...A KARANTA DA HANKURI.....😆 Page 1: "Eamaan kin san ba wadda na ke so a fad'in duniyar nan da aure in ba ke ba, kema kuma na sani duk samarin da Allah ya azurta ki da su ba wanda kike so kike kulawa sai ni, to mai zai sa ki bari a raba mu?ki sani in bake ba zan iya rayuwa me dad'i ba, ba macen da zata zama madadin ki a waje na" Cike da qunar rai Anwar ke magana ya na kallon Eamaan da ke tsiyayar da hawaye saboda baqin cikin rabuwa da babban masoyin ta,a hankali cikin natsuwa ta bud'e baki ta ce , " Anwar kai ma ka san maganar iyaye tana sama da ta kowa ko? ba zai yu iyayena su ce ga abinda zan aikata ba ni kuma saboda son zuciya ta na qi aikata abinda suka umarce ni akai ba, kai ne kullum kake fada min yanda zan qara kyautata tsakanin mu'amalata dasu, me yasa yanzu kake son canjawa? ina kallon yanda kake yi ma iyayen ka biyayya,na tabbata da kai ne suka umarce ka da ka rabu da ni zakai hakan, me yasa ka me so ni na qi bin umarnin iyaye na? Ina zaton mun wuce wannan lokacin dani da kai, ka riga da ka sani kai nake so, duk duniya ma ta san hakan, kuma ba zan sake son kowa ba,na gama so a rayuwa ta, na gama mallaka maka soyayya ta, ba abinda yayi saura a rayuwa ta na soyayya da zan iya yi wa wani namijin, fatana kawai Allah yasa yanda nai karatun nan kar su tauye ni wajen yin aiki, domin yana ɗaya daga burina na rayuwa anan gaba," Eamaan ta qarasa zancenta tana share hawayen dake zuba mata masu zafi a fuskar ta, kallon ta Anwar yayi da girmama wa, sannan yayi mata fatan alkairi ya tafi, kuka suke sosai gaba ɗayan su, a haka ta shiga gidan ta faɗa gadon ta madaidaici da yake kusa da gadon yayar ta Hafsat, gaba ɗaya rayuwar gidan su take tinani, anya ba a qwarar su ita da mahaifiyar ta kuwa? sun taso suna masu son junan su tin yarinta ita da Anwar domin kuwa maqota ne su, iyayen su abokan juna ne, mahaifin Eamaan cikakken dan boko ne, mai ra'ayin kan shi, ba wanda ya isa ko da shawara a canja mai abinda yaso aikatawa, matan shi biyu,Kareema ita ce babba yaran ta biyu mata sun aurar da babbar mai suna Fa'iza,a nan cikin garin kano ga wani hamshaqin dan siyasa, sai ta biyun wato Hafsat ita kuma tana ci gaba da karatun ta a bangaren Law, Eaman d'iyar khadija ce,itace matar Alhaji Muhammad Kabeer ta biyu,mace ce mai biyayyar aure,halayyar su ta sha banban da uwar gidan ta dan kuwa ita Kareema bata yarda a na bata umarni ba sam, sai dai in ma za a bata umarnin to fa ya zama ba zai takura ta da yaran ta ba, saba'nin Khadeeja wadda ko me za a ce tayi indai bai zama haramun ba ko zai tauye haqqin ta da na d'iyar ta tilo to fa zata yarda. Hakane ke shirin faruwa yanzun ma a gidan na su Eamaan ,domin kuwa duk dad'ewar Anwar da Eamaan a soyayyan gashi Daddyn ta na neman raba su, sakamakon wani ra'ayin shi na son zuciya, domin kuwa wanda yake son bawa Eamaan sa'an shi ne mai shekaru kusan 55, a duniya, ita kuma ba zata wuce shekara 24 ba, a cikin wannan shekarar ta gama school of nursing ta fita a matsayin midwife, ba qaramin son aikin take yi ba, tayi wannan karatun ne dan taimakawa mata 'yan uwan ta, bata son taji labarin maza ko arna ke karb'ar haihuwa a asibiti,ranta na matuqar baci da hakan, tin a shekarar da zata gama secondary school suka yanke shawara ita da qawar ta A'ishaa zasu yi karatu a b'angaren ungozomanci, sai gashi Allah ya cika masu burin su, ita A'ishaa har ta fara aiki a wani asibiti mai zaman kan shi a unguwar da ta yi aure, kuma da taimakon mijin ta hakan ya samu, Eamaan ta taya ta murna sosai, itama taiwa kan ta fatan samun hakan, amma da dikkan alamu ba zai samu ba, na farko dai mijin da zata aura ba yaro bane, da gani zai yi ra'ayi irin na mahaifin ta, na biyu kuma dan siyasa ne shima, tasan kuwa da wahala ya barta zuwa aiki, ajiyar zuciya ta yi ta kalli sama " Allah gare ka nake neman zaɓin alkairi ba son zuciya ta ba, na sani duk abinda ka zab'a min dai-dai ne, aslamtu nafsi ilaika ya rahman," Hawaye ne masu zafi ke gangara ta gefen idon ta, shigowa aka yi dakin sai tai saurin goge su ta zauna, tare da sakin murmushin yaqe "Me kike yi anan tin ɗazu banga alamar kin je kin ci abinci ba yau? ɗazu naga kin je parlorn baqi Anwar ya zo ne?" Mahaifiyar ta da take kira da Ammaah ce ta ke mata wannan tambayar, " Eh Ammaah ya zo kuma har ya tafi, na yi mai bayanin komai akan auren da Daddy ke son yi min," Ta qarasa maganar ta cike da kyab'e baki irin na mai son yin kuka, hannu mahaifiyar ta ta sa ta jawo ta jikin ta sosai, ta kwantar da ita a qirjin ta,ta na shafa kanta zuwa fuskar ta, " Shiiiii my baby kar ki sa ka damuwa a zuciyar ki har ki zo kina samun ciwo kina qaramar ki, damuwa ba taki bace bayan kin san dama ba ke kika halicci kan ki ba ba kuma ke kika haifi kan ki ba,kina da iyaye kina da wanda zaki bautawa ya baki lada, dan haka in kika bi iyayen ki sai wanda zaki bautawa wato Allah ya baki lada mara yankewa, ko kina son saɓawa iyayen ki ki shiga fushin Allah?" Girgiza mata kai Eamaan ta yi alamar A'a, " Yauwa yarinyar kirki ki zama mai BIYAYYAH ga iyayen ki zaki zamo mai riba a rayuwar ki, beside Alhaji Abdullahi mai Nasara yana son ki, ba zai bar duk wani abu ya cutar da ke ba, matan shi ne kawai da mahaifiyar shi a gidan,suma kuma in kika zama good girl ba zasu zama matsala a gare ki ba kinji?" D'aga kai ta yi kawai,amma tasan Ammaahn ta na magana ne dan ta kwantar mata da hankali, sarai ta san gidan Alhaji Abdullahi, ba qaramin gidan da ake kwasar shokin tashin hankali bane, musamman da surukar su, ta tsufa tukuf amma sai rashin M, ga sa ido matan shi kuma kishin bala'i ne da su su biyu ne, Hajiya A'i itace babba ba ta da yara,saboda idan ta haihu komawa suke, sai Hajiya Rabi itace ta biyu, yaran ta qanana ne guda biyu dika mata, Ilham da Sabeerah, akan yaran nan sharrin ta ba qarami bane ga duk wanda ya masu kallon banza, amma in kaso su to fa zaku zauna lafiya da ita, wannan dalilin ne yasa ake dambace wa a gidan, dan kuwa Hajiya A'i bata son yaran nan sam, a cewar ta ma waya sani ko 'yan kwaroro ne, dan dai Hajiya Rabi akwai son zuwa unguwa, duk kullen Alhaji Abdullahi sai ta saci jiki ta fice, in tai sati bata fita ba to tabbas ya tsanan ta tsaro, in ko taje ta dawo sai Iya ta tona, daya gama fad'an da zai ya fita zata je ɓangaren Iya ta zazzage mata kwandon tijara. Miqewa Eamaan ta yi ta bi bayan Ammaahn ta domin cin abinci, a zaune ta tarar da Daddyn ta a parlour riqe da jarida ya na karantawa, ganin su ne ya Sanya shi cire gilashin idon shi ya nannade takardar ya ajiye gefe, cike da kulawa yake kallon su, nuni yayi mata da wajen zama a gefen shi, kafin ya yi magana ta bud'e baki ta ce, " Daddy na amince da zaɓin ka a gare ni, ina fatan ya zame mana alkairi gaba ɗayan mu," " Yauwa Mamana Allah ya albarkace ku ke da mahaifiyar ki, domin nasan akwai sa hannun ta a yardar ki,kinga wadancan 'yanneman masu kama da mutane dana roqi alfarmar ai qi suka yi, wai za a tauye mata karatun ta waye-waye, to taje ta auri biro ma qarewar karatu, nan da wata ɗaya za ai komai a gama, game da Anwar kuma kar ki damu, nama mahaifin shi bayani ya kuma gamsu, shima yaron mun yi magana dashi d'azu bayan kun gama, na kwantar masa da hankali ya kuma fahimce ni, duk da cewar yana cikin damuwa, Allah yayi muku albarka ya baku ladan BIYAYYAH," Murmushin yaqe ta yi masa tare da faɗin, "Ameen Daddyna," Miqewa ta yi ta shige d'akinta ta kwanta ta manta da Wani maganar cin abinci, haka hawaye suka dinga zuba daga idanun ta wani na korar wani a hankali take fitar da shassheqar kuka, kamar saukar aradu ta ji maganar 'yar uwar ta Hafsat a saman Kanta ta na fad'in, " ke kika sani wai ke me BIYAYYAH  zaki kai kan ki inda zaki wahala,na farko ma dai ba zaki more rayuwar aure ba, dan wannan tsohon bana jin zai ita tab'uka maki komai, na biyu kuma matan shi kaɗai jarabar su ta ishe ki, sannan ga mahaifiyar shi da qanin shi, dan ma dai qanin zuwa yake yi ya tafi, ke wahalar gidan bata qirguwa ko da girkin su aka bar ki kin wahala, ni ba zan taɓa yarda a min wannann aiki ba a tauye ni, kuma keda cika burin ki na aiki sai in wa'adin wannan tsohon ne ya cika kika gama takaba kin yi aikin inda rabon ki," Toshe kunnuwan ta Eamaan ta yi bayan Yayar ta ta ta gama zayyana mata abin da ta riga ta sani, kuka take yi sosai ga soyayyar Anwar da take jin kamar qara mata ita ake a zuciyar ta, ina zata sa kanta, " Ya Allah ka kawon komai da sauqi," " Ameen" shine abinda Hafsat ta faɗa cike da tausayin qanwar ta ta,da tana da iko da ta hana wannan auren, Yayar su ma auren ɗan siyasa ta yi, amma ita ta nace kuma shima abokin Abban su ne, fatan ta Allah karya qaddara mata irin wannan auren na 'yan siyasa, ita tafi son auren da zata sakata ta wala, ba wani surutai na masu mulki a cikin shi,juyawa tai ta kwanta tare da dora pillo a kanta, dan ba zata iya hana qanwar ta koka takaicin dake ran ta ba, Kuma ba za ta iya jure sauraron kukan nata ba. A cikin wannan satikan gaba ɗaya duk wanda ya san Eamaan sai ya tausaya mata domin kuwa tayi rama sosai,Eamaan yarinyace mai cikar halitta, ta na da cikar qirji da mazaunai fatar ta gogaggiya ce irin ta matan da ke kula da Kan su, Eamaan kuwa haka Allah ya yi mata tata fatar me sulbi da sheqi, ta na da duk Wani abu da za a gani a Kira ta da Mai kyau,Eamaan ta haɗu sosai, ga ilimi both western education and islamic education, dan saukar qur'anin da ta yi ma haddane, kusan dik littafin addinin da akai masu ta shanye shi akan ta, Alhaji Abdullahi yana son ta ne saboda kyawun ta, ba qaramin manemin matan tsiya bane, in ya shallake ya fita Abuja, sai sanda ya ga dama ya shigo gari, sarai Daddyn ta ya san hakan dan tin kafin zancen auren su shi ke ma Alhajin faɗa akan wannan mummunar dabi'a tashi, zancen auren su ya samo asali ne ta dalilin alqawari da Alhaji Abdullahi ya yi na in Daddyn Eamaan ya aura masa ita ko Hafsat ba zai sake neman matan banza ba, jin haka Daddyn ya ce zai aura mai Hafsat, amma ita da Maman ta suka qeqasa qasa suka ce sam ba da su ba gad'a a kushewa, kar Allah ya sa ya daina neman matan, hakura ya yi da maganar ta bangaren su, ya nemi alfarma wajen Ammaah, ita kuma ta tabbatar mai da ba komai, ai Eamaan mallakin shi ne, dan haka bazata taɓa hana shi iko da ita ba, wannan shine dalilin auren Eamaan da Alhaji Abdullahi........ *Wannan hadi anya zai haifar da d'a mai ido kuwa?* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼 WRITTEN BY: HAERMEEBRAERH page 2: Hidimar biki ta kankama ka'in da na'in,komai da ya Kamata a sai wa amarya Kuma a Yi wa amarya an Yi wa Eamaan, tasha gyara wajen Ammaan ta sosai, gyara kuma bana wasa ba, duk wanda ya kalle ta sai ya qara,Ammaa  ta yi iya yin ta dan ganin Eamaan ta dawo da jikin ta amma abun ya faskara, dik da kuwa sanya mata abincin da  take a gaba ta tsare ta sai ta cinye, amma hakan bai taimaka da komai ba Eamaan na nan a rame saboda damuwa,ita dai  ga ta nan ne dai kawai, 'yan uwa da abokan arziqi sun hallara domin gudanar da shagulgulan bikin da aka tanadar, wasu da suka san ta da Anwar sun yi matuqar tausaya mata, amma ba mai jajantawa saboda yanda kullum take cikin kuka ko a fuska da ka kalle ta zaka ganta kamar mai shirin fasa ihu, haka take a Koda yaushe  cikin quncin zuciya, Hafsat kullum sai ta taushi zuciyar ta amma bata samun wani sauqi, se dai ta na samu ta kwanta a jikin Hafsat d'in da Ammaanta ta Yi ta kuka a jikin su. Daga lefen da aka kawo kowa yasan gidan da za a kaita ba na wasa bane, wasu a unguwa ma cewa suke yi Daddy ya saida ita ne ga ɗan siyasar, wasu suce kwad'ayi ne irin na masu kuɗin yanzu suna da shi ammasai sun qara saboda babu wadatar zuci, masu fahimta ne suka san qaddara ce ta sauka akan ta, kuma sukai mata fatan wanyewa lfy,( ko ina ruwan masu cece kuce ɗin oho).  An daura auren Eamaan da Alhaji Abdullahi a ranar laraba tabawa ranar samu,taron daurin auren da ya qunshi manyan mutanen qasar mu ta Nigeria, motoci kuwa a layin su Eamaan har rasa wajen tsaiwa suka dinga yi, Daddy kam bakin shi yaqi rufuwa dan murna yake da aurar da d'iyar shi ma  ɗan siyasa a karo na biyu. Da dare bayan an kammala  dinner lafiya,an ci an sha an yi watsi da nera, sai aka koma gida aka hau shirin kai amarya d'akin ta,da misalin 9:30pm aka gama shirya amarya dan kai ta d'akin ta,Eamaan dama tunda aka fara maganar auren take kuka, dan haka a yau sai kukan nata ya tsananta,amma babu wanda ya bi ta kan kukan ta haka aka sanya ta a luntsumemiyar motar da ango ya aiko ɗaukan ta aka nufi gidan ta da ita,sauran motocin masu rakiya na take musu baya. ' Yan kai amarya na gano baki sake suna kallon gidan da aka kai Eamaan kowa sai san barka yake yi saboda ganin kyau da tsaruwar gidan, qawayen Hafsat ne ke mata tsiya da cewar, "Babe yanzu da kin yarda da tini muna zuwa ganin wannan makeken gidan, muci arziqi mu bar shi inda yake," "Hhmm baku da hankali, itama fatan Allah ya kub'utar da ita daga sharrin dake tattare da wannan gidan nake yi," A haka kowa ya dinga watsewa ana ma amarya fatan alkairi, bangaren ta ya rage ba kowa sai ita kadai, kafin su tafi saida suka qara gyare mata gidan tass ko ina sai daukan ido yake yi, komai na gidan pink ne da ratsin fari, gidan ya mata kyau sosai,rufe idon ta ta yi wasu hawaye suka zubo mata, wannan rana sun dad'e suna tsara ta ita da Anwar, gashi zata yi ta a wani gidan, gidan da bata tab'a mafarkin aure a cikin shi ba, " Ya Allah na roqe ka dan kyawawan sunayen ka tsarkaka,Allah ka ciren damuwar komai a raina, ka bani iko da juriyar yiwa mijina biyayya da mahaifiyar shi, Allah ka bamu zaman lafiya da abokan zamana, sharrin dake tattare da cikin gidan nan Allah ka kare ni da shi, ka haɗa ni da alkairin dake cikin gidannan ya raheem," Fashewa ta yi da kukan da ya taso mata na kadaici, ji take duk duniyar ita ɗaya ce bata da kowa,tinda ta rasa Anwar to fa ta rasa kowa nata, Anwar shine kowa nata, tabbas rabuwa da masoyi akwai ciwo akwai azaba, gashi tana d'and'anar hakan, gani tai har sha ɗaya angon nata bai shigo ba,sai ta miqe taje ta yi wanka tai brush ta gyare gashin ta, sannan ta fito, dan kuwa tana fashin sallah shi yasa ta yi alwala kawai ba tare da ta yi sallah ba, zuwa ta yi ta tofe qofar shigowar da addu'a ta dawo d'akin ta ta zauna a bakin gadon ta,se ta yi addu'ar bacci ta shafe jikin ta ta ja abun rufa har zuwa qirjinta ta kwanta, bata jima da kwanciya ba kuwa bacci ya ɗauke ta irin mai daɗin nan, bacci ne mai cike da mafarkai barkatai wanda ba zata iya tantance su ba, cikin baccin taji ana shafa ta, firgigit ta miqe tana tsilla idanu kamar mara gaskiya, Alhaji ta gani cikin qananan kaya ya fitso tsaf da shi kamar be kai shekarun da aka faɗa mata ba, dan kuwa tsufannan ya boye a qananan kayan da ya sanya,sai sheqin angonci yake yi abun shi, komawa ta yi ta ja abun rufan jikin ta sosai dan ganin sai kallon ta yake yana had'iye yawu, duqar da Kanta tayi ta gaida shi ya amsa, kanta na nan a qasa bata qara cewa komai ba tana jiran taji daga gare shi, ledar dake hannun shi ya miqa mata yace taci kan ta kwanta, dan ya ga alamar bacci take ji,ya hakura sai Wani lokacin kuma. Sanar da ita ya Yi cewar sun yi magana da sauran matan a babban parlorn gidan za a taru in safiya ta yi, parlourn ya na ta can bangaren mahaifiyar shi ne,dan haka itama ta shirya tare za su je in safiya ta yi, d'aga masa kai tayi sannan ta furta, " Allah ya kaimu safiyar...mu kwana lafiya sai da safe" Takalman qafar sa taga ya cire ya d'ale gadon ya janye abin rufar ajikin ta ya kwanta ya rufuda shi shi kaɗai ba tare da ya kula da abinda ya yi ba, a hankali shima yace mata " Sai da safe," Zare ido ta yi a hankali ta furta, "Anan zaka kwana Daddy?" 'Did she just call me Daddy? Oh my God noo,' Alhaji Abdullahi ya ayyana hakan a cikin zuciyar shi ya, tashi ya Yi ya juya ya d'an kalle ta sannan ya ce, "Me kika kira ni da shi?,"  A hankali ta furta, " Daddy," "No pls don't call me Daddy, i am ur husband not ur Daddy, call me with any sweet name.... like honey, sweetheart, baby and so on," Sake zare ido ta yi ta kame baki tana mamakin wannan tsoho mai budurwar zuciya, dan haka d'aga masa kai kawai ta yi, dan bata son komai ya yi nisa a tsakanin su, ledar dake hannun ta ya Karb'a ya jawo ta jikin shi ya zaunar zumbur ta yi ta miqe ya hannu ya sake maida ita jikin shi yace, " Ammaan ki da Daddyn ki basu ce maki banda yima miji musu ko gardama ba?" D'aga masa kai tayi, alamar sun fada mata banda yi wa miji gardama,sai Alhaji yace da Eamaan, "Oya zauna na baki abinci naji qarar da cikin ki ke yi irin na masu jin yunwa, ni gidana bana son ana zama da yunwa kin gane?," Sake  d'aga kai ta yi bakin ta na rawa jikin ta ma nayi, a baki ya dinga bata kazar tana ci da kyar a haka ya ciyar da ita ta qoshi ya bata fresh milk, sannan ta miqe taje ta yi brush ta dawo, shima hannun shi ya wanko ya koma gado ya kwanta, can qarshe taje ta takure saboda bata yi zaton zai kwana anan ba duba da cewa akwai wasu d'akunan a sashen nata, murmushi ya yi daya ga tayi haka, sai ya hau gadon ya jawo ta jikin shi yace, "Ba abinda zan yi miki bacci zamu yi,dan d'azu dana d'auke ki sai naji alamar baki sallah ko?" D'aga kai ta yi da sauri, dariya yayi mara sauti yace, " To yanzu yaushe zaki gama?"   Nuni ta mai da hannu alamar kwana biyar, " OK ba damuwa Allah ya kaimu, mu yi bacci kenan yanzu ba? naga kin gaji kema," Nan ma d'aga masa kai ta yi kawai, gani ta yi kawai ya rufe ido zai bacci ba addu'a ,se ta miqe ta fara addu'a a tafin hannun ta, tana gamawa ta fara shafawa, binta ya yi da kallon sha'awa dan gaba daya yanda take shafawar ya tafi da shi, ita kuma sam bada niyyar tada Masa sha'awa take yi ba, "Ni ma ko zaki min addu'ar ne," 'Daga masa kai ta Yi ta fara karantowa , tana gamawa ta hura masa iskar bakin ta, Cike da kasala ya ce " A'a ni kenan ba za a shafa min ba?" Kauda kai ta Yi cike da kunya ta koma makwancin da taiwa kan ta ta rufa, murmushi ya yi, ya matsa jikin ta ya ja ta na shi ya rungume ta yace, "Haka zamuna bacci bana son kina nisa dani kin ji ko?," D'aga kai ta yi cike da tsoro a ran ta sai wurga ido take yi kamar mara gaskiya, ga

Chapter 1 of 20