qoqarin mallake maku miji, na farko dai ma ku kunsan ni da Alhaji auren had'i ne ba wai son shi ne yasa nake duk abinda nake yi ba, ina yi ne dan taimakon ku da kare mutunci na,yau ace kamar ni Eamaan a ga mijina yana yawo yana raba jikin shi ma kowacce jaka da god'iya ni ina zaune a gida kamar hoto to na faɗi,dan haka dole na kare masa mutuncin shi wanda shine namu, ke hajiya qarama kina ɗaya daga mu'assasin yawon Alhaji, domin kuwa ko a yanzu kin isa misali,dan Allah dubi kayan jikin ki tinda ya tafi baki yi wanka ba da alama balle canja su,kuma a haka kike rayuwa koda yana nan, kin kasa gane cewar Alhaji mai tsafta ne, ta ya kike tsammanin ya kusance ki da datti haka? Ai dole tinda shi mai ra'ayin bin mata ne ya fita ko qarfe nawan dare ne akwai masu saidawa a waje yaje ya biya buqatar shi ya dawo.
Sannan da kike kirana karuwar gida Allah ya kiyaye kalmar karuwa ta rab'e ni, dan kuwa ni na fi qarfin karuwa, domin kuwa su zina suke yi ni kuwa jima'i nake yi da mijina halas d'ina babu tsoro sai nutsuwa,ba zunubi sai lada,dan haka kar ki sake kirana da karuwa tinda ni na fita gata da matsayi na fita sanin me mijina yake so menene idan na yi yake rikita shi, na fita bashi abinda ya dace,in kuma baki yarda ba zaki gani zai ci gaba da bin wasu qadangarun barikin ko zai daina? In kuka bani had'in kai sai mu haɗu mu riqe mijin mu mu zauna lafiya,in baku bani had'in kai ba na riqe shi ni kaɗai.
Sannan masu zuwa su yi ciki a waje su na qifad'in yaran su yaran cikin gida ne ina sane da su suma,su kuma masu zina a cikin gida su ci gaba kar su fasa"
Wata irin faduwar gaba ce ta kama Hajiya Qarama, bata san sanda ta zauna a bakin kujera ba saboda jiri da Wani duhu da ta fara gani,Eamaan kuwa ta kalle ta ta qura mata ido yanda take yiwa dik wani mara gaskiya, gaba ɗaya jikin Hajiya Qarama ya kama rawa,shin a ina yarinyar nan ta san sirrin ta? Yau ta shiga uku ta lalace sirrin boye ya fito fili,kullum suka yi faɗa da Hajiya Babba idan tana yi mata gorin haihuwa sai dai Hajiya Babbar ta zarge ta akan yaran ba yaran Alhaji bane amma ba dan ta san asalin gaskiya ba,murmushi mai sauti Eamaan ta yi ta kalle su dika tace,
" ku kiyayi Eamaan dikan ku,ni ina aiki da hankali da hangen nesa ne ba da wawanci ba, sanda Alhaji yasan abubuwan da kuke aikatawa tabbas bai isa ya ce komai ba dan shine sanadi,shi ya jawo kuka lalace a qarqashin ikon sa domin kuwa zina bashi ce,kunga kenan bashi ya biya da ku,indan Kun gama abinda ya kawo ku ku rufe min qofa saboda sauraye ni na yi ciki dan banda lokacin ku"
Eamaan sai ta yi shigewar ta uwar d'aka ta barsu zaune cike da tsoro da mamakin ta, da kyar suka ja tsumman rayuwar su suka bar wajen,Hajiya Babba ce tabi bayan Hajiya Qarama suka shiga bangaren ta,cikin jimanta abinda ya faru Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama,
"Me na faɗa maki game da yarinyar nan? Ai duk inda kike zaton ta ta wuce nan, yanzu sai ki bani labarin ya akai kika haifi yaran nan dan mu san mafita,saboda in bamu ɗauki mataki akan ta ba asirin mu zai tonu gaba ɗayan mu,"
kallon Hajiya Babba ta yi ɗauke da alamar tambaya, kenan itama nata asirin ya tonu Eamaan tasan sirrin ta,cikin sanyin murya Hajiya qarama tace,
" A gaskiyar magana Hajiya yaran nan bana Alhaji bane, Yaran abokin shi ne d'an majalisa dake a Abuja da zama, in ya shigo Kano sai ya min waya na je mu had'u,ni kuma sai na faɗa maku na tafi gidan mu,"
A razane hajiya Babba ta miqe tana bin ta da kallo, ita kuma sai kuka take yi, cikin kukan tace,
"Dan Allah ki rufa min asiri kar wani ya san maganar nan, ba wanda ya san zancen nan sai ku biyu,dan ko Alhaji Saminun ban sanar wa ba, in Alhaji yaji na shiga uku, na yi miki alqawarin zan riqe maku amanar ku ke da Sahabee,"
Hajiya Babba qara rikicewa ta yi da jin kalaman Hajiya qarama, kenan itama tana sane da neman juna da suke yi ita da Sahabee amma bata taɓa magana ba dan tasan itama tana fita nata yawon, dafe kan ta ta yi bata ce komai ba ta fice daga sashen Hajiya qarama, abun yayi mata yawa a zuciyar ta,shin meke faruwa ne a gidan nasu se kace ana annobar zina a gidan ? wanne irin shaid'anin ne ya shigo masu gida wai ace matan mutum ɗaya na yawon banza, suna mu'amalar aure ba da mijin su ba?
Hajiya Babba na cikin tinanin nan Sahabee ya same ta, ya na shigowa hannun shi ya sa a qirjin ta da ta daure cikin bra ya matsa ya kai bakin shi jiki kamar mijin ta na halal ya hau sha, a hankali ta saki ajiyar zuciya ta kalle shi, nan da nan kewar shi da ta yi na kwanaki ta taso mata har tayi sanadiyyar jan shi suka fara tattab'a junan su,tashi tayi ta nufi qofa ta rufe da key gudun afkuwar matsala sannan suka fara masha'ar tasu, ba kaɗan ba Sahabee ke yin dik abinda yaso da Hajiya Babba,nishin ta kawai ke tashi a d'akin hankalin ta kwance babu wata fargaba a tare da ita,da sauri Sahabee ya danne bakin ta da nashi, a haka yake yi mata rad'a kan ta yi ahankali kar ta jawo masu mutane, d'aga mai kai ta yi suka ci gaba da abinda suke yi, basu suka rabu da juna ba sai da aka yi isha'i sannan ya d'aga ta, duk ta yi laushi har ma ta fara bacci ya lallab'a ya sa kayan shi ya fice.
A ranshi yake ayyana,
'Ohh ka ji ikon Allah malam mace sai d'anneman muni amma gata nan zam zam da ita,'
Yana shiga ɓangaren su ya tadda Eamaan ta gama had'a wa Iya abinci ta d'aga kai ta kalle shi,nan take gaban shi ya yanke ya faɗi dan kuwa a zaton shi yau ma ta gan su,hankalin shi a tashe ya durqusa gaban ta zai fara magana ta bashi wani kallon kar ka kuskura, miqewa ya yi ya had'iye maganar shi sai kyarma yake yi,cikin dakewa Eamaan tace masa,
"Me ka yi min da zaka wani durqusa min haka salon Iya ta fito tace na yi maka wani abu? Kar ka kuskura ka sake yi min haka ni babu komai tsakanina da kai da ya wuce fatan shiriya, ba ni na halicce ka ba, dan me zaka ji tsoro na sama da wanda ya baka lafiyar da zaka bauta masa amma kake saɓa masa da lafiyar? Kar ka kuskura ka sake ganina ka nuna kana shakkata, domin ni din ban da wuta banda aljanna, ka qi bin dokar mai wuta da aljanna kaga sai ya saka ka a inda yaga dama,"
Rab'awa tai ta gefen shi ta shige ta je ta sanar da Iya ta gama haɗa abun kari sannann ta ja mata qofar ta tafi, ba laka a jikin shi ya wuce dakin shi ya rufe, Iya kuwa da ta fito sai da ta biya ta d'akin shi tai bugun duniya shiru yaqi bud'ewa,yana can kwance a gado maganganun Eamaan ke ratsa shi sosai,Iya ce ta harari qofar d'akin nashi tace,
" Jarababbe yau baqin halin naka ya motsa kenan, sai ka ci kan ka ai bari naje na kwashi girkina ni,naga yanzu kowa a gidan yayi sanyi, kowa ka taba kamar a firgice yake ku kuka sani 'yan wahala,"
Tinqis-tinqis ta wuce ta fara cin abincin ta hankali kwance Alhaji ya kira ta suka gaisa, ta sanar da shi yanzu Eamaan ma ta tafi ta gama yi mata abinci,wani dad'i ne ya kama shi,sai ya sanyawa Eamaan albarka,ya sanar da ita gobe zai dawo, sannan kuma yana son ta sa Sahabee ya kai Eamaan asibiti yanzu dan tana can yanzu ta kira shi cikin ta na ciwo sosai, amsawa ta yi sannan ta miqe ta je d'akin Sahabee ta hau bugawa amma duk bugu da kiran da take mai yaqi bud'ewa, waje tai ta kira driver dan ya je ya tada mota zai kai su asibiti da Eamaan, haka nan sai ta ji tana fatan Allah ya sa Ciki ne da Eamaan ɗin ,dan ko ita ta jima tana zargin su Sabeerah ba yaran ɗan ta bane duba da yawan yawon Hajiya Qarama da kuma rashin kama da yaran suke yi da Alhaji da ma zuri'ar su baki ɗaya, bata jin wani kusanci na musamman a tare da su iyaka dai ta na son su saboda yaran akwai shiga rai, tana qarasawa bangaren Eamaan ta tadda ta ta saka kaya da hijab, sai murqususu take yi sannu ta yi ta jera mata, sannan tace ta fita ta shiga mota bari ta koma ta d'akko mayafin ta,da kyar Eamaan ta iya qarasawa ta je wajen motar ta shiga, Iya kuwa ta dakko mayafi ta shiga mota driver ya tada suka bar gidan.
Asibiti suka je bayan bayanan da ta yi wa likitar se likita ta baiwa Eamaan gwajin jini,suka tafi lab aka ɗauki jinin ta aka gwada, bayan sakamako ya fito aka bata ta koma wajen likita, likita ta taya ta murnar samun qaruwa da tayi sannan daga baya ta yi wa Iya izinin shiga Office ɗin nata ta Sanar da Iya Eamaan na d'auke da cikin wata uku da sati biyu,sai dai kuma cikin ya na barazanar b'arewa saboda yawan ayyuka da take yi da damuwa, hankalin Iya a tashe ta dinga roqon su su taimaka mata kar ta rasa jikan nan nata tana son abunta, hakuri likitan ta bata ta sanar da ita za su yi iyakar qoqarin su dan suga sun kula da ita, tana buqatar hutu ne kawai.
washe gari da Alhaji ya iso kano ko gida bai bari an kai shi ba ya yi asibitin wajen ganin Eamaan,yana shiga d'akin da aka kwantar da ita yayi ido biyu da ita duk ta rame ta yi fari sosai, tabbas ga alama nan komai ya fito cikin wata uku ya kusa rifa na hudu ya d'ago kaɗan ana iya ganin alamun shi, kwallar dad'i da farin ciki ne ta ziraro wa Alhaji a fuska, Iya ta kalle shi itama da murmushi a fuskar ta tace,
"kai ma kaji dad'in ganin matar ka da ciki ko? ABDULLAHI ina son in mun koma gida ka tsannan ta bincike akan su Ilham,"
"Iya ban gane ba? Kamar ya na tsananta bincike akan yarana wani laifi suka yi?"
"Ina nufin ka nemo wane ne uban su, domin ni ka sani ba wai ina tsananin son yarinyar nan Eamaan bane,amma ina jin tana da cikin nan na ji wata qaunar ta ta kama ni, wanda duk son Hajiya Qarama danake ban taba jin haka ba in tana da ciki, hasali ma zargin ta nake yi da yawon banza ni, sannan ba wai dan wannan alaqar da bana ji game da ita idan tana da ciki ba nake zurfafa zargi na, ka San dai Qarama da shegen son yawo, yanda ka ke saka qafa ka fice ba da sanin mu ba itama haka take sa qafa ta fice, ta sha yin qaryar gidan su ta tafi ka Kira ace bata je ba ko ka manta? To Ina take zuwa? Ko da da farcen qafa ne yaran nan ba sa kama da Kai ko ni ko Wani naka, to dole ne ka tsananta bincike akan su"
wani irin duka qirjin Alhaji yake yi a dik fitar kalma ɗaya daga bakin Iya, nan take ya hadiyi wani yawun wahala,ya sassauta wa jikin shi ta hanyar cire babbar rigar shi ya riqe a hannu, tabbas maganar hajiya akwai qamshin gaskiya a cikin ta, amma in yaran nan ba nashi ba ne to na waye? Waye yake masa d'anyen aiki haka?............
*Hahaiiiii cassssss wanzami fa baya son jarfa*
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 12:
Gaba ɗaya hankalin Alhaji ya kasa kwanciya da matan nashi da ya kamata ace a wajen su ya sauka, dan haka a wajen Eamaan ya kwana ranar ,dik da cewa Iya tayi-tayi dashi ya tafi gida ya huta amma qi, baya son ya tafi ya bar ta a nan daga ita se Iya dan a ganin shi akwai abinda dole shi zai yi mata Iya baza ta iya ba.
Har suka yi kwana uku a asibitin babu wanda yazo duba Eamaan ding a cikin mutanen gidan Alhajin kama daga kan Hajiya Babba har zuwa Hajiya Qaramar balle kuma Sahabee dake a cikin damuwa, qarshe dai dole Alhaji ya yi waya gidan su Eamaan ya Sanar da su halin da Eamaan ke ciki, Hafsat aka umarta data zo ta zauna da ita har ta samu k'warin jikin ta tinda ita ta yi graduating yanzu haka tana aiki a camber din ta na kanta ne, sannan an kawo kuɗin auren ta har an saka ranar auren da wani abokin aikin ta mai suna Kamal, Iya da cewa ta yi a bar ta ba sai tazo ba tinda ga masu aikin gidan cikin su an samu mai zuwa ta zauna da ita, amma Eamaan ta ce a mata alfarmar barin yayar ta tazo wajen ta in zai samu, kan Iya tace komai Alhaji yace ba komai zai je da kan shi ya d'akko mata Hafsar,ita kanta Hafsar ta ji dad'in hakan dan tana son baiwa wa qanwar ta ta kulawa ta musamman.
Ammaah da Mama sun tausaya ma Eamaan dan sun tabbatar aiki take shaqa har hakan ta faru da ita, amma babu yanda za suyi da ya wuce suyi mata addu'ar samun sassauci,dama kowacce mace da qaddarar gidan auren ta,Daddy ma ranshi ya baci da jin cewa wai zata yi b'ari saboda yawan aiki da stress amma sai ya danne saboda baya son ya karya wa d'iyar shi mai BIYAYYAH qwarin guiwar ci gaba da yin BIYAYYAH a gidan mijin ta, sai kawai ya bi ta da addu'a da fatan alkhairi shima.
Wani irin haɗin kai ne yake wanzuwa a tsakanin matan na Alhaji da Sahabee wanda kai da ka gani kasan ba na Allah da Annabi bane akwai wata a qasa,dan kuwa kowa na nan na jin haushin 'yar uwar ta a qasan ran ta.
Tin bayan da aka kwantar da Eamaan sukan haɗu a sashen junan su suyi ta tattaunawa akan matsalar da suke ganin tana tunkaro su a gidan, dan haka yau ma zaune suke a sashen Hajiya Babba suna hira, cike da b'acin rai Hajiyan ta nisa tace,
" Hmmm wai baku san cewar an tabbatar da Eamaan na ɗauke da cikin watanni 3 zuwa 4 ba? Meye plan din mu akan hakan ne dan dai gaba d'ayan mu yanzu mu masu laifi ne a wajen Alhaji da ya san me muke aikatawa a bayan idanun shi kashin mu ya bushe, Qarama kin dai san baki da gadon yaran nan a gidannan dan ko in Alhaji ya fad'i ya mutu ni ko Sahabee ba bari zamu yi a raba da shegu ba tin da mun san komai,"
Wani mugun kallo Hajiya Qarama tai wa Hajiya Babba, sannan tace,
" Yo me zamu yi banda mu qoqarta zubda cikin tin kan yazo duniya? Ko dake na kula ku tsoron ta kuke ji har yanzu,"
Sahabee ne yayi mata kallon baki da hankali,
" ke kan ki tsoron ta kike yi balle mu,akan me ba zamu ji tsoron mace kamar Eamaan ba, macen da ta san me take yi, tasan ta kan tafi da abokin gaba ba tare da tada jijiyoyin wuya ba ko hargowa,tasan yanda zata saka duk wani wanda basa shiri da ita cikin fargaba da tashin hankali, dan haka ni ina ganin kar wadda ta yi yunqurin taba abinda ke cikin ta,koma dai menene Yayah dan uwana ne, dan haka zan so ace yau ko da d'a d'aya ne ya ga jinin shi shima a duniya ,dan haka ku kiyaye kar na ji labarin wani abu ya sami cikin nan,"
shiru suka yi, kowacce da abinda take saqawa,Hajiya Qarama ce ta buɗe baki tayi magana cikin fargaba da tsoro tace,
"Ni yanzu ku ban shawara dan Allah, ya zan yi na sanar da Alhaji Saminu ina ɗauke da yaran shi guda biyu ba tare da ya qi karb'ar su ba?"
" Kar kiji tsoron komai ki sanar da shi komai a wannan dawowar da zai yi in ya sani shikenan fargabar ki ta qare,idan yaso kina faɗa masa ki bashi sharuda biyu, na farko dai ko ya Karb'a cewa yara nashi ne ko ki masa barazanar tona maku asiri, ki nuna mai ke baki damu ba dan wani ya sani shi kike jiyewa,"
Gaba ɗayan su sunyi na'am da shawarar Sahabee, sannan suka shiga hirarrakin duniya daga qarshe suka tashi da fadan nasu na jaraba akan yara, Sabeerah ce ta shigo da gudu ta sanar da su dawowar su Eamaan da yayar ta,a sanadin gudun da tayi ne ta take Hajiya Babba a rashin sani,nan take tako ɗauke ta da mari, aiko nan fada ya rincab'e, Sahabee ya zame jikin shi ya fice,dan shi baya son wannan fadace2n nasu kamar kaji.
Gyara gidan Hafsat ta shiga yi dik da babu sani dattin a zo a ganj sai qura,Alhaji na shiga kuwa ya duba abubuwan da babu sai ya yi wa driver waya yace ya zo Eamaan ta zayyana masa abubuwan da take so, nan da nan aka bashi kuɗi ya tafi siyowa, Alhaji na manne da ita kamar za a kwace ta, sai faman sannu yake mata tare da shafa marar ta yana yin wani irin farin ciki na ratsa zuciyar shi.
Hafsat dake kallon yanda yake yi wa Eamaan dai ya sa take jin kunyar shi sosai, a ganin ta tsaf zai yi sa'an Daddyn su amma ya samu yarinya sai wani soyayya yake zubawa kamar saurayi,a haka ta kammala gyara wajen ta koma d'akin dakin da yake nan zata na zama, Alhaji ji yake kamar ya yi ta zama a wajen ta kar ya je wajen sauran matan, dan yaso matuqa da ya dawo ace girkin ta ne, kuma lafiyar ta qalaou yasan tabbas zata cika mai alqawurran da ta yi masa, amma ba yanda zai haka yayi mata kiss sannan ya ɗauki jakar shi ya yi ɓangaren hajiya Babba wadda ba jimawa su sahabee suka koma bangaren su suka barta ta hau 'yan gyare-gyaren da ya kamata mace tayi dan tarbon mijin da ya dawo daga tafiya,fuskar nan ta sha fenti kamar kullum sai tashin qamshi take yi,cikin ranshi yaji daɗin samun ta a haka, dan kuwa gwanda masa ita sau dubu akan Hajiya Qarama, abincin da masu aiki suka yi na gida ta yi masu izinin kawoma,a haka yaci saboda bashi da zaɓi,yana gamawa ya yi wanka ya kwanta nan take bacci mai daɗi ya ɗauke shi saboda tinda ya dawo daga asibiti yake kwana wajen Eamaan to baccin ba wani sosai yake.
yi ba.
Hajiya Babba na ganin haka ta kulu sosai,wato ya dawo ma bai zo gare su ba sai da matar so ta bashi izini shine ya wani baje yana kwasar munshari kamar shekararren jakin dawa,qwafa ta yi ta cire kayan ta ta kwanta gefen shi, ai kuwa Hajiya bata hakura ba sai da ta san yanda ta yi ta tada shi daga baccin nan mai daɗi da ya samu, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, nan take ya biye mata suka raya wannan daren, mamaki take yi na yanda Alhajin nasu sam baya tsufa,ko Sahabee da yake saurayi Alhaji ya fishi komai, amma dan jaraba da rud'in shaid'an bazata hakura a kan mijin ta ba sai ta qara da qanin shi.
Washe gari yana idar da sallar asuba ya ɗauki hanyar ɓangaren Eamaan dan yaga ya ta kwana da jikin nata,a parlour a kwance ya ganta a saman abun sallah ta yi lamo tana azkar,gaba daya jin jikin ta take yi babu k'wari shi yasa ta kwanta a wajen, zama ya yi a gefen ta ya janyo ta ya ɗora ta a cinyar shi yana shafa bayan ta,sake mannewa tayi a jikin shi kamar wata mage, a hankali ta buɗe idon ta ta kalle shi, tausayin ta ta gani kwance akan fuskar shi, murmushi tayi masa sannan ta gaida shi, bai amsa ba sai kawai ya haɗe bakin su waje ɗaya yana sumbatar ta a hankali, a hankali ya zame bakin nashi daga nata, sannan ya amsa da,
" Babeen Alhaji sannu kinji Allah ya baki lafiya, ya sa maki kaffara, Inshaa Allah zaki samu sauqi da wuri kin ji?"
D'aga masa kai ta yi idon ta fal hawaye dan kuwa tana jin jiki, Hafsat ce ta fito daga kitchen ɗauke da plate data dafa mata taliya irin jellop ɗin nan na manja da attaruhu sai naman qaramar dabba, dan sha'awar manjan take sosai shi yasa tace a yi mata me manja, tana shigowa taga Alhajin da Eamaan a rungume da juna sai ta rikice tace,
" I...I.... ammm sorry ban san ka shigo ba,"
" Barka da safiya Hafsat, ya aiki? sannun ki Allah ya baki lada ya sa ai bikin ki a sa'a,"
Ta ji dad'in addu'ar shi sosai amma fa yana matuqar bata kunya ita kam,a kunyace tace,
"Ameeen na gode,"
Murmushi Alhaji yayi yace mata,
" ki daina jin kunyata fa dan kuwa kin dinga ganin irin wannan abubuwan in dai kina gidannan,"
Dariya ta ɗan yi kaɗan sannan ta ajiye masu abincin zata koma ya ce ta hada mata tea, komawa ta yi ta had'o mata tea ta kawo mata,Alhaji ne ya Karb'a tare da yi wa Hafsat godiya ya fara bata a baki,Eamaan buɗe baki tayi ta dinga Karb'a har sai da ta ci abincin sosai tinda tana so dama,tea ɗin ne kawai bata sha sosai ba, wanka ya ɗauke ta yaje yayi mata, ya sa mata kaya marasa nauyi a jikin ta dan ta sha iska ya kamo hannun ta suka fito zuwa bedroom ɗin ta, taje mata kai ya yi ta d'aure da kanta,ya taimaka mata ta kwanta, yana shafa kan ta zuwa bayan ta a hankali nan take ta yi bacci, miqewa ya yi ya ja qofar a hankali ya fita, yace ma Hafsat kar ta tashe ta ta samu bacci idan ta tashi a bata maganin rana,sanan ya qara yi mata godiya sosai ,Hafsat ta ji dad'in ganin yanda yake kula da qanwar ta sosai,sai dai tana mamakin duk ba wanda yazo duba qanwar ta ta kaf gidan, daga Iya se Alhajin suke jinyar ta kamar mutan gidan basu san bata da lafiya ba, kyab'e bakin ta ta yi ta dan buɗe d'akin Eamaan ɗin a hankali ta leqa ta,sai tagan ta kwance ya tare ta da pillo kamar wata jaririya, sannan ga shi alamar yanda ya shafa mata gashi duk ya tarwatse, murmushi ta yi ta rife qofar ta koma d'akin ta suka hau waya da Kamal din ta suna ta shan soyayyar su.
Alhaji kuwa na komawa sashen Hajiya Babba ya tarar da ita a cikin dakin ta ta cika tayi famm kamar flour da aka sanya wa yisssss, cikin faɗa ta hau cewa,
"Dan me zaka dinga yi mana rashin adalci a gidannan ne eye? Akan me zaka tattare komai naka ka damqawa yarinya qarama baka da lokacin mu sai nata ,yanzu duba tin asuba sai qarfe 8 ka dawo sashe na akan me? Ko girkin tane? gaskiya ba zan dau wannan rashin adalcin ba daga gare ka akan 'yar cikin ka ka zauna kana rawar jiki,"
Cikin sanyin murya ya furta,
" Hajiya ki yi hakuri mana, kina ganin yarinya ce kuma ciki gare ta tana buqatar kulawa ta sosai a wannan gab'ar,"
"Yarinya? Yarinya fa kace, Eamaan ɗin ce yarinya? Yarinya ce tasan ya zata sami ciki da tsoho kamar ka? To bari kaji na faɗa maka Allah yasa a zanin goyo take bata fara haqora ba tsabar yarinta dole ka tsaida mana adalci,in ba haka ba gaskiya akwai abu mara dad'i da zai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 20