Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ba qarar shi ta kai ba baya son su sake had'uwa da Eamaan idanun ta na rikita shi kwarai da gaske. Eamaan na da wata baiwa da be tab'a had'uwa da mace kamar ta ba, kasa cewa komai ya yi da Alhaji ya nuna farin cikin ganin shi sai ya hau yashe haqora yana yaqe. "Yaushe ka dawo?" Qeya ya sosa kafin yace, "Jiya da daddare na dawo na isko kowa ya yi bacci, kawai sai ban tada kowa ba nima na kwanta, ina kwana Yaya?" Gaisawa suka yi sannan suka qarasa wajen Iya,tana ganin shi ta tashi tsaye tana washe baki murna a wajen ta kamar wanda ya b'ata aka  ganshi, sosai ta ji dad'in dawowar tashi, waya ta ɗauka tace bari na kira Eamaan ta zo ta haɗa maka abin karyawa, wata sufa ya yi ya damqe wayar yana in ina yace , " Baattaa kawaiii zan ci ko me aka dafa maki, ni daga yanzu ma ana haɗa mana abinci kawai ba sai an yi wa kowa nashi daban ba," Daga jin yanda yake maganar kasan akwai wata a qasa duk zufa ta tsattsafo a goshin shi kamar wanda ya yi gudu,mamaki ne fal a cikin ran su bama ya Alhaji wanda ya san halin Sahabee na son takurawa Eamaan ɗin ,nan take ya d'iga wa Sahabee alamar tambaya, tabbas akwai wani abu a qasa, yana ganin irin kallon da Alhaji ke bin shi da shi sai ya hau yaqe yana faɗin, "Ya naga duk kunyi shiru kuna kallo na? Na yi tunani ne saboda rashin lafiyar Iya na daina duk wani rashin da'a ko BIYAYYAH danake yi a baya,daga yanzu na dena qasqantar da na qasa dani," Murna ce ta cika zuciyar Iya a lokacin da ta ji kalaman autan nata, abinci Iya tai ta d'ura masa, shiko sai kwashewa yake yana ci dan kuwa ya yi kewar abincin Eamaan sosai. Eamaan na isa sashen ta ta rufe bangaren ta ta fara gyara gidan, ta goge shi tsaf, sannan ta haɗawa kanta oatmeal dan ta sha,zaune take saman dinning table ta na  wasa da spoon ɗin a cikin qaramin bowl ɗin da ta had'a oatmeal, wani tunani ya faɗo mata a rai, yau mijin ta ya je neman mata ya ci nasara a neman matan nashi,ita kuma qanin shi ya je neman ta Allah ya tsare ta wanda hakan baya rasa nasaba da kullum cikin sallolin ta na farillah da nafila tana neman tsarin Allah akan zina da dik abinda zai kusantar da ita wajen aikata zinar, musamman ma a wannan zamanin da zinar ta yi katutu a zuqatan mutane, ya zata yi a lokacin da jarabawa ta afka mata qanin shi ya ci nasara akan ta? kwallar ta ta share sannan ta kawar da wannan tunanin a ranta da addu'ar Allah ya ci gaba da bata kariya, sannan ta qarasa abincin ta ta wanke bowl din ta ajiye a inda ya dace ta fita daga kitchen ɗin, d'aki ta shiga ta fad'a bathroom ta yi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba balle wata kwalliya ta zira riga ta  kwanta baccin safe, nan take kuwa wani bacci mai dad'i ya ɗauke ta, Alhaji yazo ya yi ta bugun qofar ta  shiru ba ta bud'e ba, gashi ya San ba ta saba rufewa ba, kad'a kan shi yayi ya koma ɓangaren Hajiya qarama, wadda har a lokacin bata yi wanka ba, d'aki ya nufa shima ya rufe ya kwanta, wayar shi ya duba yaga missed calls din Eamaan a jiyan nan da nan yaji tashin hankali da damuwa sun mamaye shi, dan ya tabbata hakan ne ya sata fushi har ta qi buɗe masa qofa,ya qudurta kome zai faru zai shawo babyn shi tinda shi yayi mata laifi, kuma zai qoqarin daina bin mata kamar yanda take buri. Alhaji ya samu nasarar shawo Kan Eamaan ta hanyar yi mata alqawarin dena bin matan banza a waje, ita kuwa sai ta sanya shi ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ta nuna masa cewar Allah yake sab'awa ba ita ba,sannan ba Iya ba ba matan sa ba, Allah shi ke da wuta ya ke da aljannah, idan ya tuba ya dena cikin Rahamar Allah sai ya Sanya shi a aljannah, idan ya qi tuba ya ci gaba da aikata zina se ubangiji ya azabtar da shi da wutar shi, kar ya manta wutar duniya ma ba ya iyawa da ita balle ta lahira, da wannan nasihar Eamaan ta samu nasarar hana Alhaji Abdullahi yawon dare, ya kame kan shi ya ke qoqari wajen danne buqatar shi ta bin matan banza a duk sanda be samu yanda yake so ba a wajen sauran matan nashi,a haka yake hakuri ya Jira har ranar girkin Eamaan ɗin ya zagayo ko girkin Hajiya Babba, ita Kuma Eamaan sai take hakuri da danne duk Wani rashin so da qin kusantar ta da yake ta na nuna masa ta na so, Kuma ta na Jin dad'in kasancewar su tare a koda yaushe. A kwana a tashi Eamaan da Alhaji suna ta samun kusanci da junan sj da shaquwa,sai dai har yanzu babu wata soyayyar shi a ran ta sai girmamawa, komai nashi ta sani Kuma yana yin shawara da ita sosai. kwatsam watarana Alhaji Abdullah ya tashi da ciwon baya se yake sanar da ita, Eamaan tayi masa sannu sannan ta bashi maganin ciwon jiki ya sha, abu kamar wasa ciwo kullum na gaba har dai watarana suka shirya dan zuwa ganin likita game da ciwon bayan nashi fatan ta Allah ya sa ba wata mummunar cuta bace ta kama Alhajin nata......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 9:  Gaba ɗaya rayuwar Alhaji ta zama sai a hankali saboda yawan jin kasala a jikin shi da yake fama da ita,haka tafukan hannayen shi da qafafun shi suke kumbura,kai hatta da fuskar shi ma ta hau ta yi haske, uwa uba yawan jin qaiqayi da yake a jikin shi duk yafi damun shi saboda yawan susa da yake yi ba ya jin sauqin qaiqayin, sai dai ma da ya gama susar wasu quraje ne suke fito masa qanana a jikin shi,idan kuwa ya je yin fitsari to fa da kyar yake iya yi, rabon shi da Kashi kuwa ya kwana biyu, abubuwa dai sun taru sun yi mai yawa. Randa zasu je asibitin ya kama ranar girkin Hajiya Babba ne, ta sha kwalliyar ta kamar yanda ta saba suka shiga mota ita da Alhaji suka zauna a baya Sahabee da driver kuma na zaune a gaba, suna zuwa aka bashi gado, likita ya rubuta wa Alhajin gwaje-gwajen da ya Kamata a masa dan danin makamar ta inda za a yi masa magani, dik da cewa already akwai ciwon da yake zargi shi ke damun Alhajin duba da symptoms ɗin da suka bayyana a jikin shi. Ai kuwa gwajin  farko suka gano gaba ɗaya qodar shi sun samu matsala, d'aya ce kawai me ɗan sauqi-sauqi, akwai yiwuwar in ya sha magunguna aka wanke masa ita zai iya samun sauqi, hankalin Hajiya Babba da Sahabee ba qaramin tashi ya yi ba da jin wannan mummunan labarin,sanda suka yi waya suka sanar a gida kuwa kowa ya shiga  damuwa, a haka likitan ya bashi duk wata kulawa da ya Kamata a bawa mai irin ciwon. Iyalan Alhaji Abdullahi su na iya bakin qoqarin su dan bashi magani akan lokaci da bashi kulawar da likita ya umarta a bashi, duk da sun so matuqa a fita waje da shi amma likitan ya musu alqawarin za su bashi kulawa kamar ya na qasar waje,abokan shi na siyasa sun shiga damuwa Suma duba cewa kusan shi ne jigon jam'iyyar tasu, gashi mutane na son shi da girmama shi, addu'a suke tayi da fatan Allah ya tashi kafad'un shi. Matan Alhaji kuwa shifting ɗin zama a wajen shi suka fara yi kamar ma'aikatan gwamnati, in girkin wannan ya fita wannan ta zo, duk ranar da ta kasance ranar girkin Eamaan ne tofa ranar sahabee ba shi a zuwa asibiti, dan tinda abunnan ya faru yake toshe duk wata kafa da zata had'a su a waje guda. Wata rana Iya ta kira Eamaan sashen ta, duk da cewar washe gari ne zata karbi girki, kimtsawa ta yi ta saka hijab din ta ta fita zuwa wajen Iya, tana zuwa ta tadda ta da himilin rake a gaban ta,Eamaan zama ta yi ta tankwashe qafa a gaban Iya ta gaida Iyar,cikin tsuke fuska Iya tace wa Eamaan. " Ni ba gaishe-gaishe ne ya sa na kira ki nan wajen ba, ammmm kina jina ko wannan raken nake son ki samu ki markad'en shi ki tacen ruwan sa kamar yanda na ji ki a waya rannan kina gayawa wata,jarababbiya kamar ki wai har kin san hada maganin mata da rake, to ni na lafiya zaki haɗawa d'ana yanzu ba na kayan jarabar taki ba, dan haka ki kama ki markad'e shi kar ki sa masa wani kayan qamshi da madara, kawai zallan ruwan nake so a tace a saka a jug a kai masa ya shanye, dan naji ance ruwan raken yana wanke qoda," kanta a qasa cike da takaicin abubuwan da Iya ke yi mata ta ke ta gyad'a kai alamar amsawa,a zahiri dai gashi ita ake mora amma ita ce sharar gidan, fuskar ta cike da murmushi da annuri ta d'ago kanta ta kalli Iya tace, "To Iya yanda kika ce haka za a yi Allah ya bawa Alhaji lafiya," Cike da mamaki Iya take bin Eamaan da kallo, cikin taɓe baki da harara yace wa Eamaan ɗin, " Wai ke bakya fushi ne?" " Iya dawa zan yi fushin, da ke? Allah ya sawaqa na yi fushi dake,Allah kuma kar ya nuna min ranar da zan yi fushi da ke ,domin kuwa ke uwa ce a wajena d'an kirki kuwa baya fushi da iyayen sa sai ya zama marar rabo duniya da lahira, kuma ni na tabbata ba wai so na ne baki yi ba, wataqila wasu daga halaye na ne baki so, inshaa Allah kuma zan yi qoqarin gyarawa na zama d'iya ta gari me neman albarkar ki a koda yaushe, in kuma abubuwan da kike man dan kawai ki baqanta min ne kina son ganin fushina.... Hmmmmmm Iya kar Allah ya nuna maki fushina,"  Ta qarashe maganar ta cikin wani murmushin da ya sa Iya shan Jinin jikin ta,nan take ta ji yarinyar tayi mata kwarjini matuqa, a cikin kalamanta akwai hikima kuma a kwai tsantsar gaskiyar abinda ke ran ta, had'iye yawu Iya ta yi makwattt ta jingina da jikin kujera tabi bayan Eamaan da ke cike da mazaunai da kallo, nan take ta hau karantar wasu abubuwa daga halittar ta,kauda tinanin ta yi daga ranta ta miqe ta shige d'aki. Eamaan na gama had'a ruwan raken a jug ta yi sallama d'akin Iya ta  faɗa mata ta gama, Iya kuwa cewa ta yi ta bawa Sahabee ya kai asibitin sai ta amsa da "To" ta fita, har yanzu jikin Iya a sanyaye yake da kalaman da Eamaan tayi mata,dan haka shakkar yi mata rashin mutunci direct take yi kamar yanda ta saba yi a baya, dan kuwa  da dane sai ta yada mata da baqar magana kafin ta bata izinin tafiya. Eamaan kuwa fita ta yi farfajiyar gidan riqe da jug a hannu wanda ta saka cikin wata leda babba mai kauri,tafe take tana leqa wurare ta na neman Sahabee, tinda koda ta duba d'akin shi bata gan shi a can ba,hanyar backyard ta yi dan da damar lokuta yana zama wajen ya ɗan yi bushe-bushen kayan mayen shi ya sha iska, dai-dai zata gilma ta bangaren Hajiya Babba ta jiyo nishi irin na nishad'i ɗin nan,mamaki ne ya kama ta dan tasan dai Alhaji na asibiti bashi da lafiya,sai dai kuma kamar muryar shi take jiyowa, ɗaya muryar kuwa tabbas ta hajiya Babba ce shin meke faruwa ne a gidan? Qara matsawa ta yi sosai ta jikin window ta ji ana magana cike da nishad'i ana faɗin, "Wai yau Hajiyata me kika sha ne haka gaba ɗaya kin sa tin d'azu na kasa hakura dake? gaskiya Yayah yana morewa da yawa, amma tsabar rashin rabo yake tafiya yawon neman mata," Hajiya ma sambatu take yi tana faɗin, "Sahabeena bana so ka gaji kaga yau 'yar sa idon tamu tana asibiti da yara, waccan kuwa in ta kulle kan ta a d'aka ba fita take yi ba, balle kuma Iya da ta tsani zuwa sashe na, yau ai kaga sai mu kwana muna morar juna,mun dad'e bamu samu dama irin haka ba," Wata razana Eamaan ta yi ta ja da baya hannun ta sai rawa yake yi saboda tsoron da ya kamata, hankalin ta ba qaramin tashi ya yi ba,nan da nan idanu ta suka kawo ruwa suka fara zuba, bakin ta na rawa ta furta, " Sahabee da  Hajiya Babba?" A hankali ta fara takawa jiki babu k'wari ta lallab'a ta bar wajen, wajen mai gadi ta je ta damqa masa Jug ya kai asibitin, dan kuwa bata Jin zata iya komawa ta jira Sahabee ya gama tambad'ewar shi ta bashi saqon, a hankali ta ce ya bawa driver in ya dawo daga kai Hajiya Qarama asibiti ya koma ya kai asibitin ko kuma shi ya hau abun hawa ya kai, in kuma yana da no shi ya kira shi yanzunnan ya dawo ya Karb'a ya kai musu a bawa Alhaji, tana tafiya mai gadi ya tsaya yana kallon ta,sai yaga gaba ɗaya kamar hankalin ta a tashe yake, tausayin ta ne ya kama shi,dan yasan wataqila hajiya masifa ce ta sata a gaba, ko kuma Alhaji qarami(Sahabee) addu'a yayi mata a ran shi na samun sauqi akan komai dake faruwa a gidan, (wannan shine ya dace da kowanne musulmi, yi wa dan uwan ka addu'a a zuciyar ka a yayin da ka fuskanci yana cikin damuwa, in kana da hali ka taimaka masa ya fita a damuwar, in kuma babu,ka yi mai addu'a, ko ka hada dika biyun).   Direct ɓangaren Hajiya Babba ta nufa cikin ɓacin rai da qunar zuciya,cikin sa'a kuwa ta samu qofar farko ba a rufe take da key ba, murd'a wa ta yi a hankali ta shiga,nishin su kawai ke tashi a d'akin wanda hakan da Eamaan ke ji qara mata radadi a ranta yake. Hajiya babba ta girme wa Sahabee nesa ba kusa ba, amma ta bude masa jikin ta yake amfani da ita kamar matar shi,fuskar ta sharkaf da hawaye ta samu waje ta zauna ta ci kukan ta ta share hawayen ta tass, Eamaan ta koma kamar wata wadda bata taba sanin ya ake yin murmushi ko dariya, duk wanda ya kalli cikin idon ta mai baiwar tsorata duk wani mara gaskiya sai ya kusa sakin fitsari a jikin shi, tankad'a qofar tayi nan take suka zabura suka juyo cike da kid'ima da tashin hankali,kwance suke a rufe cikin bargo,hajiya babba ce a sama da wasu sakakkun qirjin ta da suka yamushe, in ba ma bariki ba dai da son aikata sab'on Allah yana saurayi me zai da mace kamar hajiya? Ido suka zaro cike da tsoro, wanda Sahabeee ya fi Hajiya shiga tashin hankali dan kuwa ya san wacece Eamaan a yanzu, rufe qofar ta yi ta koma ta zauna a kujera doguwa tana girgiza jikin ta tana jiran fitowar su, a sukwane Sahabee ya ture Hajiya daga saman shi ta kuwa faɗo qasa timm kamar buhun masara a saman hannun daman ta, wata iriyar qarar azaba ta saki ta fashe da kuka saboda azabar da ta ji ta ratsa ta, bata raba ɗayan biyu ko ta samu karaya ko kuma targad'e ,a haka ta miqe ta kama hannun ta tana nishin wahala dan kuwa da ke gaban ta yafi wannan tashin hankali, a haka ta zura kayan ta itama ta bi bayan Sahabee da ya yi waje daga shi sai gajeran wando, riga da dogon wando da hular shi a hannu ya riqo su ya fito kamar kwarto. A zaune suka tadda ita ta kura masu ido kawai tana kallon su ba tare da tace komai ba, shiru suka yi suma se zufa ke karyo musu,kowa kai duqe a qasa kamar suna gaban magabatan su, Hajiya Babba da Sahabee kuwa na jin yanda zuciyoyin su ke ta bugawa kamar ta bar qirjin su saboda damuwa, Sahabee ya fi Hajiya shiga tashin hankali idon shi ya kad'a ya yi jawur,Hajiya Babba kuwa jikin ta banda rawa ba abinda yake yi,ga azabar da hannun ta ke yi ta mata yana zogi da rad'ad'i,ta rasa ina zata saka kanta. A wajen su kuwa da wannan kallon da Eamaan ke bin su da shi gwanda ko duka ne ta rufe su da shi, sai da ta kai wajen minti goma tana kallon su sannan ta miqe kawai ta yi waje ba tare da ta ce musu ku ci kan ku ba, cike da d'imuwa suka kalli juna shin me hakan ke nufi? "Wani zata gaya wa Ko me?" Hajiya Babba da ta gigice ta kalli Sahabee ta yi masa wannan tambayar. Shima cikin damuwar ya amsa ta da cewar. "Indai Eamaan ce ba zata fad'awa kowa ba, sai dai zamu azabtu da ganin ta a cikin gidan nan Hajiya, duk sanda kika ganta ko kika ji muryar ta sai hankalin ki ya fi na yan gidan yari tashi," " Ya akai kasan ba zata faɗa wa kowa ba? Ta kama mu tirmi da tab'aryar kace bazata fad'awa kowa ba? Ka ko san me hakan ke nufi? Baka da hankali Sahabee, tabbas yarinyar nan ta zama masifa a cikin gidannan, ban taɓa ganin irin wannan kallon kashe wanda ake kallo ba sai a wajen ta, lallai gaskiyar bahaushe ne da yace Ido guba Kuma kallo zai iya kisa, yarinyar nan da ta zuba mana Ido ji na yi kamar zan had'iyi zuciya na mutu, rasa inda zan saka Kai na na yi" " Hmmm nina faɗa maki ba zata sanar da kowa ba, amma kam a wajen ta bamu isa koda gilmawa ba," Se a lokacin ya kula da hannun Hajiya Babba ya kumbura, cikin tsoron ganin yanda hannun ya haye yace, "Hajiya meye wannan naga hannun ki ya kumbura?"   Harara ta maka masa ta miqe daga duqen da Eamaan ta sa su yi na dole, ta fara takawa tana faɗin, " Ba kai ka wurga ni qasa ba na fada ta hannun," zuwa yayi ya kama ta suka zauna ya ja mata hannun dan kuwa baya jin zai iya binta ake wajen masu gyara, tana ihu tana komai ya gyara mata hannun ashe targad'e ne,kafin ya fita sai da suka jaddadawa kan su dole su hakura da juna na wani lokaci kafin su san abun yi. Eamaan kuwa da ta koma d'akin ta ba qaramin kuka ta sha ba, yanzu da Anwar ɗin ta ta aura duk ba zata ga waɗannan abubuwan ba tashin hankalin ba. " Allah kai ne masanin abinda ke b'oye da wanda ke fili Allah ka kawo min mafita, ka ban ikon cinye wannan jarabawar ,shi Kan shi ganin mutane na aikata zunubai irin wannan jarabawa ne,ya hayyu ya qayyum kar ka jarabce ni da aikata Zina da duk Wani abinda baka so" Hawayen ta ta goge ta kwanta tana ta tinani har bacci ya yi gaba da ita. ********************* Washe gari ta shirya zuwa asibiti bayan ta yi wa alhaji girki mai daɗin data saba,ta leqa wajen Iya ta gaishe ta sannan ta fita driver ya kaita, a ranar ne su Amman ta suka je duba Alhajin suma har da Hafsat da Mama aka je, tana ganin su ta fara murna fadawa ta yi jikin Ammahn ta, cike da shagwab'a take magana, " Ammah baku taɓa zuwa ganina ba sai ta dalilin rashin lafiyar Alhaji kuka zo asibiti,gobe fa za a sallame mu da bari ma kuka yi kuka je gidan kawai," Alhaji ne yace, "Gaskiya dai kam Hajiya ya akamata ku yi wa Eamaan zuwa na musamman, kullum sai ta yi maganar rashin zuwan ku gidan ta," " Inshaa Allahu Alhaji za mu zo gaba ɗayan mu har Daddyn su mu gaida Iya sai a gaggaisa baki ɗaya,dan dama muna da niyyar zuwa ɗin," " Allah ya sa to" In ji Eamaan dake murnar jin kalaman Mama. Gaishe gaishe aka shiga yi,tare da tambayar me jiki, anan zauna har a zahar kafin suka tafi,Eamaan ta ji dad'in ganin su sosai. Washegari aka sallame Alhaji ya koma gida,a bangaren Eamaan ya sauka ya ji sauqi sosai kamar be tab'a ciwon ba, tinda an cire masa qodar da ta lalace dika, d'ayar Kuma ta yi sauqi ,sannan likitoci sun dora shi akan abinci da abubuwan da ya kamata ya kiyaye, Iya se murnar samun sauqin shi ta ke yi, har lokacin nan Alhaji bai ga Sahabee da Hajiya babba sun je duba shi ba, ya yi tambaya amma ba wanda yasan dalilin rashin zuwan su, Alhaji bai bar bangaren Eamaan ba sai da yai kwana uku ya qara samu sauqi sosai,sannan ya koma bakin aikin shi. Bayan sati ɗaya yayi shirin komawa Abuja, taro ya kira a sashen Iya kowa ya taru amma banda Hajiya da Sahabee, Eamaan ce ta ce bari taje ta kira su, tashi ta yi taje d'akin Sahabee ta leqa ta ganshi sai safaa da marwa yake yi, a razane ya juyo yana kallon ta,cikin d'aure fuska Eamaan tace masa, "Na tabbata kai ba kurma ko bebe bane,kana jin neman ka da ake yi maka ko? ka na tinanin qin zuwan ka shi zai sa na fasa fad'in abinda na gani idan na yi niyya? To bari ka ji hakan da kake yi ne zai sa naji haushi na fad'awa kowa abinda ku ka yi," Daga nan ta ja dogon tsaki ta fice daga d'akin ,shi kuwa Sahabee ya hada gumi gaba ɗaya jikin shi har d'iga zufa take yi qasa daga hancin shi, ji yake yi anya ba zai fad'i meke faruwa ba da kan shi ya huta, gaba d'aya yarinyar nan na d'aga masa hankali in ya gan ta,ya tabbata da za a gwada jinin shi za a gano ya hau. A hankali ya sa hannu ya goge zufar da yake yi, bud'e qofar ya yi ya fita ya samu waje ya zauna a gefen Iya. Eamaan na shiga ɓangaren hajiya babba ta tarar da ita ta yi tagumi ga hannun ta ɗaya dake a kumbure ya ɗan fara sakewa idon ta ya yi jawur, dan tinda Sabeerahn Hajiya Qarama ta zo ta sanar da ita akwai taro a parlourn Iya hankalin ta ya tashi, ta rasa sukuni, tana ganin Eamaan kuwa sai ta miqe ta hau jan dankwali zata rife cinyayyen kanta da bata son d'aura masa d'ankwali, cikin yaqe tace, "Dama yanzu nake shirin fitowa na ji Alhaji na kira ko," Eamaan ce ta kalle ta ta kauda kai, dan jin tsanar matar take sosai da gaske a ranta " Hajiya wannan abubuwan da kuke yi ke da Sahabee su zasu sa kowa ya fahimci akwai wani abu, ni na wuce tsayawa ina faɗan abinda ku ka yi, tabbas kowanne ɗan Adam yana aikata zunubi, amma mafi alkairin bayin Allah shine wanda yake aikata sab'o kuma ya tuba, dan haka in kin tuba kin  huta, kin wa kan ki daidai,ki je Alhaji na jiran ku kar ya yi missing flight ɗin shi" Ta na gama fad'a mata haka ta sa kai ta fita, Hajiya kuwa ji ta yi kawai gwanda su faɗi me ya faru a tsakanin ta da Sahabeen su huta, musamman in aka tambaye ta game da hannun ta ba ta isa yin qarya a gaban Eamaan ba. Tana shiga sashen Iya................ *Eamaan tawa kin gagara.....tabbas gaskiya da ruqon amana tare da hakuri na saiwa mutum girma qima da kwarjini a idon kowa* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH   💅🏼    WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 10: Shigar Hajiya Babba ke da wuya ta samu waje ta zauna a gefen Hajiya Qarama da ta bi hannun ta da kallo,harara Iya ta banka mata saboda dad'ewar da tayi bata zo ba, daga baya kuma sai ta gyara zama ta fara da godewa Allah da ya bawa Alhaji Abdullahi lafiya ya kuma dawo mata da shi gida lafiya, daga nan ta hau qorafe-qorafen ta na babu gaira babu dalili kafin ta bawa Alhaji Abdullah damar ya yi magana shima. Shima ya fara ne da godewa Allah da ya

Chapter 6 of 20