bacci tana ji gashi kuma ta kasa yi, hawaye ne ke zuba mata daga idanun ta zuwa kuncin ta, yana jin haka ya sake ta ya juya baya dan ya kula ya takura ta da yawa, yana juyawa ta sa pillo tsakanin su ta koma can qarshen gadon ta takure kanta, da jin haka sai Alhaji ya yi murmushi, a haka suka kwanta har bacci ya ɗauke su.
Qarfe 3:30am nayi ta farka tai addu'ar tashi daga bacci, kallon shi ta yi ta ganshi shame-shame yana ta kwasar bacci,miqewa ta yi taje tai alwala ta fara karanta qur'ani da ka saboda mahaddaciya ce ita, daga qarshe ta kai kukan ta wajen Allah, lokacin sallar subh nayi ta kalle shi duk kiran sallar da ake a masallacin gidan bata ga ya motsa ba sam, sai da aka idar ne ma taga yai wani juyi tare da munshari ya qara jan bargo abun shi, tana so ta tada shi dan ya yi sallah amma tana tsoro, a haka tai shahada taje ta tada shi,ai kuwa haka ya juyo fuskar nan kamar jar wuta babu walwala a cikin ta,ita kuwa gata tsaye zulum a hijab, cikin wata iriyar murya yace mata,
" Ko dayake ke baquwa ce a gidannan baki san qa'idoji na da dokoki na ba,amma idan ina bacci ba a tada ni daga yau ki sani kuma ki kiyaye,"
Juyawa zai ya kwanta yaji tace masa,
" Wayyo ban sani ba ka yi hakuri inshaa Allahu zan kiyaye, wai dama na jiye maka tsoron fitar lokaci ne, tinda Allah yace azaba ta tabbata ga waɗanda basa sallah akan lokaci, naga in kai sallar zaka iya kwanciyar ka ka huta,amma tinda haka ne zan kiyaye daga yau,"
Duk bayanan da take yi masa sun dira a kunne da zuciyar shi, tsaki yaja ya miqe tsaye ya shige toilet,saida yai brush sannan ya yi alwala ya fito, Sallah ya tada ya burbura ta ya sallame ya haye gado ya koma baccin shi, mamaki ne fal cikin ta, dama haka masu kuɗi suke ko dai shi ke hakan?
Kafin ya tashi da safe ta yi wanka gudu-gudu sauri -sauri a ɗayan d'akin, dan bata son ya tadda ita tana wanka, tana gamawa sai ta sanya sabbin kayan da ta tafi da su d'akin, ta yi kwalliya sassauqa mai kyau, sannan ta koma d'akin nasu ,zaune ta tadda shi ya dafe kai yana murzawa a hankali,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa cikin ɗan sakin fuska, kallo ya bita da shi kamar zau had'iye ta, dan kuwa ba qaramin sha'awar yarinyar yake ba, dalilin da ya sa ya aure ta kenan, ba wai dan yana son ta ba, a hankali ya miqe ya shiga toilet yana saqa abubuwa da dama akan ta, wanka shima ya yi ya shirya sannan ya kama hannun ta suka fita dan zuwa sashen mahaifiyar shi, tana ganin sunyi hanyar waje tace,
"Bari na d'akko hijab,"
kallo ya bita da shi, sannan yace
"A cikin gidan ma sai kin saka hijab?"
"Dama naga kamar sai munbi ta wajen masu aiki ne, kar na haɗu da wani daga cikin masu aikin ba mayafi jikina kuma shi yasa,"
kad'a kai ya yi ya jingine yana jiran ta, koda ta dawo sai ya bita da kallo,dan kuwa da ta saka hijab din ma ba qaramin kyau yaga ta qara yiba a idon shi,
"Lallai Eamaan komai naki mai kyau ne,"
Murmushi ta yi tace Masa
" Na gode,"
Hajiya A'i dake tsaye jikin window ce ta hango su suna murmushi sai taji zuciyar ta kamar ta fito waje saboda kishi,
"Dubi dan Allah dan tsabar ya siya mana raini ya rasa wadda zai auro sai d'iyar cikin mu,hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, dan wannan irin su auren kuɗi ke kawo su, Allah ka azurtani da tsayyen d'an da nima za a dama da ni a cikin gidan nan,"
Sakin labulen ta yi taje d'aki ta saka d'ankwali, dan ita ba mace ce mai son d'aura d'ankwali ba a koda yaushe,tana gamawa sai ta fito tana takun qasaita, a babban parlour ta tadda Hajiya Rabi da yaran ta Sabeerah da Ilham suna ta shagwab'a a jikin Daddyn su, Eamaan ce ta shafa kan Ilham tace,
"Meye sunan ki?"
Tana mata murmushin dake nuna tsananin shiga ranta da yaran suka yi,Ilham tace,
" Suna na Ilham, amma Sabeerah na kirana da Elly, ni kuma ina kiran ta Saby,"
murmushi ta yi tace,
"Oh kenan wannan itace Sabeerah? Can i call u saby ?"
" Yeh u can, and let me tell you u a scret,"
Sai ta kai bakin ta dai-dai kunnen Eamaan tace mata,
" I like u, don't tell anyone,"
D'aga mata kai Eamaan ta yi cike da jin dariya,itama ta kai bakin ta kunnen Sabeeran tace mata,
"I like u too, u ar beautiful Maa shaa Allah,"
wani fari ta yi sosai tai tsallen murna, Daddyn su da Hajiya Rabi ba qaramin burge su Eamaan tai ba, Ilham ce ta b'ata rai,Eamaan na ganin haka sai ta kama hannun ta tace,
" Elly me ya faru,"
"Ba ku bane kuke gulmata,"
Daddyn ne ya fara dariya sannan Hajiya Rabi,
"Ba qulmar ki muka yi ba zo kiji wata magana kema,"
sanar da ita tai itama tana son ta, yaran sukai ta murna, suka rungume ta .
" Mtsssss aikin banza da asubar fari za a cika ma na kunnuwa, sai kace ku kad'ai ne yara a unguwar nan,"
"A'a fa Hajiya Babba, ba zai yu kawai ke baki so yarana ba Allah ya kawo mai son su kuma suma suna son ta ki zo ki kina qananan maganganun da kika saba, "
Habaaa ai akamar Jira Hajiya Babba take yi sai suka kacame da zage-zage sukai ta faɗa da junan su,nan da nan idon Eamaan ya kawo hawaye dan kuwa ita bata saba ganin wannan ba a gidan su, dik da cewa kuwa itama gidan su mata biyu ne.
"To kaji kun fara ko? kut kut kut kut, ga hatsi to kuzo ku tsattsaga, jarababbu, baku da aiki sai jaraba akan miji da 'ya'ya, ke wani ya hana ki yi cikin ki haifi naki? Ke kuma da kike jaraba akan yara naga dai yaran ba naki bane ke ɗaya, da anyi magana sai iko akan yara, wannan kuma yar afiruwar wace ce ita take zaune kuturinta dana Audu waje d'aya?"
Hajiya Iya kenan wato mahaifiyar Alhaji Abdullahi ke wannan maganganun tana kanne idanu tana nuni da yatsun ta da suka sha jan lalle irin na tsofaffi.......
*Iya jaraba kamar yanda Su Saby ke kiran ta ta fito fa*😱
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH
Page 3:
Cike da ladabi Eamaan ta zube a gaban Iya sannan ta ce,
" Barka da safiya Iya,"
Cikin isa da ɗauke kai ta amsa da,
" Lafiya ! baku ban amsa ta ba ai kan a kai ga gaishe-gaishen,"
Alhaji ne ya duqar da kai cike da biyayya yace,
" Iya amarya ta ce mai suna Eamaan, jiya ban shigo gida ba sai wajen 12am, shiyasa ban kawo maku ita ba ta gaishe ku,sannan nayi zaton ko dangin ta da suka kawo ta jiya sun kawo maki ita ta gaishe ki,"
" Eh sun kai ta, amma ai a qunshe ta ke waya gan ta? Miqe ka zauna abun ka,"
Miqewa yayi ya zauna kowa ya yi shiru,amma Hajiya A'i da Hajiya Rabi sai harare-hararen juna suke yi, Ilham ce ta gaida kakar tasu, cike da fara'a ta amsa mata, sannan Sabeerah ta gaida ta itama, amsawa tai sannan tace,
"Shin yau babu mai bamu abinci ne a gidan sai mun roqa?"
Kallon kallo suka fara yi a tsakanin su domin kowaccen su tana qyashin ace ita ce zatai directing masu aiki suyi girki bayan mijin na wajen amaryar shi, Hajiya Qarama ce wato Hajiya Rabi ta miqe ta fice hanyar da zata sada mutum da kitchen ɗin gidan,ma'aikata sun yi abinci kala-kala suna jira a kitchen ɗin suna zazzaune suna jiran me zai je ya zo tinda ba a basu umarnin kaiwa ba, tsoron masifar Iya kuma ya sa sun kasa yi wa kowa magana, a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru ta iske su, dan kusan suna jiyo tashin muryar ta koda basu fahimtar komai sin san masifar take saukewa, umarnin kawo abubuwan da suka dafa ta yi masu, suka ko biyo bayan ta da abincin kala-kala suka ajiye suka yi waje, a qaton carpet d'in da suke haɗuwa kowa yaci abincin suka baje, dan Iya bata son hawa dining table,dan haka dole kowa nan qaa zai zube in dai tare za a ci da ita, kowa na zaune yana kwasar girki banzda Eamaan, jita take yi duk a takure,saboda bata saba da su ba,Iyace ta kalle ta a yatsine cikin masifa tace,
" Malama idan za kici abinci ki kama ki ci,kina wani sunne kai kamar ta kwarai,"
Cike da jin tsoron Iya ta fara cin abincin, Alhaji kuma sai ya ji tausayin ta ya kama shi saboda ba haka ya san jikin ta ba duk ta rame, sai ya ji kamar ya bata a baki, gaba ɗaya ya kula a tsorace take da Iyan tashi, a haka aka ci aka gama, kowa ya tashi ya nufi sashen shi masu aiki suka ɗauke komai suka gyara wajen.
A hanyar su ta komawa sashen nata ne Alhaji ya kula da damuwar da ke tattare da Eamaan din, kafin ya gama nazarin ta ya ji ta na yi masa tambaya cike da damuwa.
" Alhaji kullum a babban parlor zamu dinga cin abinci?"
" A'a na yau ne kawai dama ina so ne na haɗa ki da sauran abokan zaman ki ku ga juna, to na zata Iya zata yi mana nasiha ne, amma na ga yau faɗan ta kamar yafi na kullum zan je na ji me ke damun ta yau ɗin, sannan kuma zamu haɗu a bangaren Hajiya Babba mu yi magana zuwa Wani lokacin,"
D'aga masa kai ta yi alamar gamsuwa da bayanan shi ,dan kuwa bata fatan sake zuwa wajen wannan tsohuwa mai faɗan tsiya.
Suna shiga d'aki ta cire hijabin ta ta ninke shi ta zauna waje d'aya a gefen gadon ta, kallo ya bita da shi yaga kamar har wannan lokacin a tsorace take, jan ta ya yi jikin shi ya fara lallashin ta,yanayin yanda yake yi mata ne ya sanya ta mamakin shi, da alama dai Alhaji baya tunawa da shekarun shi idan yana wasu abubuwan, luf ta yi a jikin shi tana zubar da hawaye a hankali dan bata son ya gane kuka take yi,sai kawai ta ja baya ta gyara kwanciyar ta kamar wadda ke yin bacci, murmushi ya yi dan a zaton shi wasannin da yayi mata ne suka sa mata kasala har ta yi bacci, miqewa ya yi yaje ya yi wanka ya fito tare da sanya kaya masu kyau, sannan ya dauki key na motar shi ya fice ya bar gidan dan zuwa wajen shaqatawar shi, wanda da fari ya zaci zai iya hakuri da ci gaba da neman matan banza, amma zuwan Eamaan da lamarin da ta zo da shi na baƙon wata na mata ba zai iya jurewa har ya jira ta gama ba,tana kallon shi ya gama duk abinda zai yi amma bata motsa ba, sai da ya fita ne taje ta rufe qofar ta jingina da murfin qofar ta hau kuka da qarfi, tabbas bata qaunar bawan Allah'n nan, gaba daya ba sa'an yin rayuwar auren ta bane, a ganin ta ko da cikin tsarki take yazo mata ai ganin shi zata yi kamar Daddyn ta, babban mutum haka ya dinga sauke buqatar shi akan ta da qananun shekarun ta? kaiii akwai takura sosai da jin nauyi gaskiya.
A haka tana kuka taje toilet dan ta gyara jikin ta, yatsina fuska ta yi ta cire rigar ta ta aje ta a cikin washing machine ta kunna ya shiga wankewa, saida ta gama wanka sannan ta fita ta shirya cikin shadda mai matuqar kyau kalar purple aikin jiki an yi shi da pink ɗin zare,ba qaramin kyau ta yi ba a cikin kayan,tirare gidan tai da tiraran wuta, sannann ta samu waje ta hau rera karatun qur'ani idanun ta lumshe, ta windown parlourn taji kamar ana motsi, aikuwa sai ta miqe a tsorace sannan bata daina karatun da take yi ba, tana leqawa bayan ta kai qarshen aya ta ce
"Waye a nan,"
Juyawa su ka yi za su gudu, a dai-dai lokacin Eamaan ta leqa taga ashe yaran ne, ajiyar zuciya ta sauke da qarfi sannan ta kira su ciki, a hankali suka je kamar masu jin tsoron ta, buɗe masu qoqafar ta yi suka shiga ciki suka tsaya suna jiran su ji ko zata yi musu faɗa.
Ba tare da sun san cewa Eamaan taji dad'in zuwan su ba suka hau bata hakuri,ita kuwa murmushi tayi dan dama a cikin kaɗaici take, nan da nan ta rungume su ta hau yi musu wasa har suka saki jikin su da ita.
Kafin minti goma sun sake da ita sosai sai wasa suke yi abun su, kan su ta kalla taga gaba ɗaya ya tsufa har tsagar ta haɗe waje ɗaya baka banbancewa tsakanin kitso da tsaga,ga gashi har gashi amma duk a cukurkude yake, kayan su ta cire masu ta wanke masu kan su tass, ta samu bands ɗin ta da take amfani da shi ta gyara masu kan bayan ta yi drying gashin ta yi oiling ɗin shi yana sheqi,kan su ya yi matuqar yin kyau sai sheqi yake yi, cike da murna suka kwasa suka yi wajen maman su dan su nuna mata,a lokacin kuwa Iya tana wajen tana zazzaga mata masifa akan ita zata kula da abinci har Alhaji ya gama angwanci ya raba masu kwana, ranta a haɗe sai qunquni take yi suka shiga,Iya ce tace,
"In kika zagen kin zagi ta gida 'yar nema kawai masu abun kunya, gaku nan rid'a-rid'an mata amma kuna zaune miji na neman matan banza a waje, ga shinan ai kun ja an kawo maku yar cikin ku se ku zauna ku yi ta goga kishin da ita,"
" A'a fa Iya kar ki ɗora mana laifin da ba namu ba ah toh,neman matan shi ba laifin mu bane tinda ba mu muka haife shi ba balle mu bashi tarbiyya,"
Ta fada tana murguda baki,
" Iyyee to me kike nufi tijararriya? Wato ni ce ban bashi tarbiyya ba ko? To a cikin tarbiyyar dana ba shi ne lokacin har ake cewa na yi mai auren wuri, ganin yana bin matan kar ya lalace da yawa ne ya sa na yi masa auren, amma aka kawo ku aka zuba gaku nan kun zama kamar hoto a gidan, shashashai kawai, ita waccan ta yi wani d'irim da ita da anyi magana ta ce ita tayi ta gaji ba zata kashe kan ta ba, amma ai bata gaji da tatse masa arziqi ba ko? Ke kuma da na ke gani a waye kike ashe kallon kitse nake wa ro,......" Yaran ne suka gaji da jin faɗan da ba gane inda aka dosa suke yi ba suka katse iya da faɗin,
"Mum kin ga kan mu,"
cike da murna suka haɗa baki suka fada,
" Wow kun yi kyau,waya kai ku saloon ba a faɗan ba na bada kud'in gyarn kai?"
"Mum ba saloon bane ba fa, Aunty Eamaan ce ta yi mana,"
Tin daga wannan lokacin Eamaan ta samu matsayi a zuciyar Hajiya Rabi, amma a wajen Iya kuwa cewa ta yi na neman gindin zama ne, sam ba a yi mata gwaninta ita, ko kwanta mata za ka yi tabi ta kai ta wuce sai ta kushe maka.
A haka Eamaan ta yi kwana shidda a gidan, a cikin waɗannan kwanaki Eamaan ta ga halayen mutanen gidan kala-kala, yau ne kwana na bakwai da kawo ta wanda daga shine Alhaji zai tattara ya tafi wajen Uwargida wato Hajiya Babbah.
Idar da sallahr ta kenan ta cire doguwar riga da hijab ɗin ta na sallah tana ninkewa sai ta mayar inda take ajiye su, ta dauki qur'anin ta da littafin addu'o'in ta tana dubawa,daga qarshe sai ta d'akko wayarta ta kunna data suka hau chatting da Aunty Fa'iza dake qasar waje, sunje shaqatawa ne da Alhajin ta,shawarwarin yanda zata zauna da mijin ta da surukar ta har da kishiyoyin ta lafiya take ta bata, hakan kuwa yasanya mata mutuwar jiki sosai ashe aiki ne babba a gaban ta bata sani ba wanda take ganin anya zata iya kuwa? In ko haka za ta yi ba qaramar wuya zata sha ba kenan a gidan?
Suna cikin hira taji shigowar shi gidan ,a ranta ta qudiri niyyar yin dukkan abubuwan da Auntyn ta ta faɗa mata dan samun zaman lafiyar zuciyar ta da gangar jikin ta ko da ran ta baya son Alhajin, wannan dalilin ne yasa ta miqe duk da dukan da zuciyar ta ke yi ta je gare shi dan tarbon shi, amsar kayan hannun shi ta yi,wanda ta kula kitchen ya Kamata ta yi da su dika,godiya ta yi masa tare da sannu da zuwa,shi kuwa cikin kashe murya kamar ba dattijo ba yace,
" Godiyar me kike yi min daga dawowa ta kuma? Ki jira mana anjima idan na yi maki babbar kyauta kin yi min godiyar ko?"
Murmushi ta yi kawai ta wuce dan ba ta gane abinda yake nufi ba, tana tafe take faɗin,
" Ai dole mace ta zama mai yiwa mijin ta godiya a kullum ko dan saka ta a cikin sutura da killace ta da yayi ya bata wajen kwana, balle kuma ya bata abinda zata ci ta sha ina ga ya gama mata komai,"
Murmusawa ya yi har saida haqoran shi suka bayyana, lallai yarinyar nan ta tarbiyyantu wajen iyayen ta,
" Ba komai Eamaan dolena ne biya maki dukkan buqatun ki, indai ina da hali da iko,"
Godiyar ta sake yi mai da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ta da matan shi, kitchen taje ta cire komai ta mai mahallin da ya dace sannan ta fito,zaune ta gan shi a saman kijera sai ta duqa ta cire masa takalmi da safa, Alhaji kuwa sai ya bi qirjin ta da kallo, wani yawu ya hadiya, hula da agogon shi ta cire ta yi d'aki ta ajiye ta dawo.
Kitchen taje ta d'ebo masa drinks data haɗa da kanta na pineapple da ginger da lemon, sai flavor da sugar data saka dan d'and'ano, yana sha ya lumshe idanun sa saboda yanda dad'in abun ke ratsa shi ,nan da nan kuwa ya shanye,ita kuwa sai ta qara masa wani, ya qara shanyewa, cikin dakewa da fad'uwar gaba ta fara qoqarin gwada abinda Auntyn ta ta koya mata,
" Sweet kar ka sha ka kasa cin komai,na yi girki me dad'i saboda kai gashi can ajiye a saman dining table kai kaɗai yake jira"
Sai da ya kusa k'warewa saboda yanda ya ji kalmar Sweet a bakin ta babu zato babu tsammani, tabbas a kunyace take itama amma tana son ta gwada abubuwan da aka koya mata,domin ba zata manta dalilin da ya sa aka aura mata shi ba dan haka zata yi iya bakin qoqarin ta dan ganin ta samu wannan ladan na tsamo shi daga halakar da ya jefa kan shi ciki ta neman matan banza, cike da jin daɗin maganar ta ya ajiye glass cup d'in ya fuskance ta yace,
" Eamaan me kika kirani da shi? Please kirani da sunan again,i want to hear it from your beautiful voice,"
Murmushi ta yi cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, hakan da ta yi sai ya qara jefa shi cikin qaunar ta,murmushin ta kaɗai ya tashi kanshi ya jefa shi a wani hali, cike da jin kunya ta sake maimaitawa tace,
" Cewa na yi Sweet kar ka sha ka cika cikin ka..."
Wata dariya Alhaji ya b'arke da ita ta Jin dad'i, a kunyace ta miqe tana tafiya ta daukar magana ta wuce dining table,tabbas ta san ta tarowa kan ta babban aiki ,amma ba damuwa indai kwalliya zata biya kud'in sabulu akan BIYAYYAHr iyaye ba abinda ba za tai ba se dai idan abun ya sab'awa Allah ne dole zata guje shi, abincin taje ta d'akko ta jere a gaban shi, sannan ta d'akko qaramin carpet ta shimfid'a,dan ta kula a gidan sun fi son cin abinci a qasa, tana bud'ewa Alhaji ya yi karo da alkubus ɗin flour da ta haɗa da alkama tayi masa miyar gyad'a wadda ta sha naman qaramar dabba, yaji kayan qamshi ba kadan ba sai tashin qamshi miyar take yi, gefe kuma ga kunun aya mai had'in dabino, kayan qamshi, da sugar sai zuma kaɗan da ta saka dan ya qara gard'i a baki da amfani a jiki, gefe kuma farfesun kan rago ne, daya umarci ayi mishi kan ya fita,baje ciki ya yi ya kwashi girkin nan da kyau,dan kuwa tin da ya fara ci ya kasa yin magana, tinani yake yi wannan girkin ko a hotels ɗin da ya sha zuwa Abuja da sauran wuraren 'yan gayu bai taɓa cin irin shi ba, wa yayi girkin nan ne? Daɗi da santi ya sanya ya kasa tambaya, zurawa kawai yake yi, ganin ya ci har ya wuce geji ne yasa ta saka hannu ta riqe hannun shi tace,
" Ka yi hakuri ka bar abincin nan haka,in ka ci da yawa ka qoshi bacci zai gagare ka mai dad'i yau ,ka San Annabi ya ce a raba ciki gida uku, Ɗaya na abincin, Ɗaya na ruwa, Ɗaya kuma na iska, da alama ka cika dika gurbin baka bar komai ba,"
Cike da jin daɗin kalaman ta masu yanga a ciki ya tashi tsaye bayan ya wanke hannu a robar data zubo ruwan wanke hannun,
"A gaskiya duk wadda tai girkin nan sai na bata kyauta mai tsoka,sai abinda ta zaba zan bata,"
Murmushi ta yi tace,
"Ni ce na dafa da kaina dan faranta maka,kuma albarkar ka kawai nake nema bana son komai bayan haka"
"In dai albarka ta ki ke nema kin samu, Allah ya albarkace ki, ya baki abinda kike so duniya da lahira,"
Jin hakan da ya fad'a sai da gaban ta ya faɗi dan kuwa Anwar ne zaɓin ran ta, shine abun son ta, yana yi mata wannan addu'ar shi ne ya gilma a idanun ta, dakewa ta yi ta miqe ta shige kitchen da kayyakin da ta kwashe bayan ya gama, zuciyar ta na saqa mata abubuwa da dama, tabbas bata jin son shi a ranta, a can cikin qasan ran ta a akwai Wanda take so, amma ba amfanin riqo da wannan soyayyar har ta b'ata rayuwar da Allah ne kad'ai ya San qarshen ta,dole ne ta yi hakuri, dole ne ta Yi BIYAYYAH, dole ne ta danne komai ta binne shi a qasan ran nata, dan ta samu farin ciki a gidan auren ta,takun da take yi ne dan zuwa d'aki ya sanya Alhaji Abdullah bin bayan ta ba tare da ya San ma ya na biye da itan ba........
Anya kuwa wannan BIYAYYAHr taki zata haifar maki da d'a mai ido kuwa Eamaan sai na ji ra'ayoyin ku makaranta?
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
RUBUTAWA :HAERMEEBRAERH
Page 4:
Suna shiga ciki Eamaan taji alamar yana biye da ita a baya, nan take zuciyarta kama rawa tana tsalle dan tsoro kamar zata fito waje,duk da cewa tasan yau ta ta qare, hawaye taji na son zubo mata amma ta yi saurin maida shi ciki, yaqe ta yi ta juyo shi kuma ya yi mata murmushi,juyawa ta yi da nufin shiga bathroom,hannun ta ya kama ya na bin ta da kallon tuhumar Ina zata je? Cikin yaqe dan kuwa murmushin be kai har zuci ba tace masa,
"Ruwa zan ɗan watsa, yanzun nan zan fito"
A qa'ida yanzu kam ai ba wani wanka da ze yi shi kam kawai baccin shi zai yi, amma da alama Shima yau ze gwada yin wankan daren, kafin ya gama tinanin da ya ke yi ya ji rufe qofar ta, fad'awa ta yi ciki da sauri ta rufe gam ta fara wanka, tana gamawa ta yi brush tai alwala, samun brush din shi ta yi ta saka masa toothpast a jiki ta ajiye sannan ta fito, ta yi masa nuni da toilet din tana murmushi mai cike da jin nauyin sa, shima cire kaya ya yi a gaban ta ko kunya baya ji, Eamaan kuwa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 20