takarda a aje an dora kwalbar Mai akai.
Buɗewa yayi ya ci karo da mummunan bayanin da ya sanya shi yin zaman ƴan bori a ƙasa,wasu zafafan hawaye ne suka fara tsartuw daga idanun shi,a guje ya fita zuwa d'akin Iya dan sanar da ita mummunan abinda ya same shi,yana zuwa sai ya ganta kwance yanda ya barta tin safe da zai fita aiki.
A hankali cikin rawar jiki ya qarasa shiga cikin d'akin ya sa hannu ya taɓa ta ya ji shiru bata motsa ba kuma bata ce komai ba,hannu biyu ya sa ya juyo da ita sai yaga bata motsi,da gudu ya fita tsakar gida ya samo ruwa ya hau yayyafa mata amma shiru Iya bata farka ba.
Ɗaukar ta yayi da kyar ya yi waje da ita ya ajiye ta a dakalin ƙofar gidan su ko riga babu a jikin shi, se da ya wahala kafin ya samu abun hawan da zai Kai su asibiti, dubu d'aya me adaidaita ya caje shi, ya ce su je ba komai ze biya, ko da suka Isa asibiti Sahabee kuka ya sa ya na neman a taimaka masa, ganin yanayin da yaje asibitin dashi ne daga shi sai gajeran wando ga Iya a kwance rai kwakwai mutu kwakwai ne yasa likita ya ce a shigar da ita ya duba ta sun kawo kuɗin daga baya.
Da kyar aka samu Iya ta farfad'o daga doguwar sumar da ta yi, takarda likita ya bashi me d'auke da magungunan da za a siya wa Iya, likita ya ce daga baya za a yi maganar bill na asibiti Kuma.
Likita ya shawarce shi akan ya samo mata abu me ruwa-ruwa da zata sha in ta farka saboda akwai yunwa a tattare da ita sosai, Sahabee tsugunnawa ya yi a wajen yayi tsuruu yana tunanin inda zai samo kud'ad'en da zai yi wannan hidimar da su.
Kamar wanda aka mintsina haka ya miƙe cikin hanzari ya nausa ya nufi ma'aikatar su,dan kuwa ya tabbata yanzu ba kowa dik an tafi gida, zai yi amfani da wannan damar dan ya samo wasu kud'ad'en a can,a guje yake tafiya yana haki duk inda ya wuce mutane sai sun bishi da kallo sai kace wani kwarto,a rayuwar shi kaf bai tab'a tinanin zai shiga damuwa irin haka ba,a yau ya gane ashe uwa uwace,dik duniya bayan Allah da manzon sa baka da kamar ta.
Kamar yanda ya zata kuwa ya na zuwa ya tarar da wajen a rufe ba kowa dik an tafi gida sai Mai gadi, zagayawa ya yi ya haura Katanga ya shige ya balle makullin cikin dabara da kwarewa irin ta tsoffin 'yan bariki, (Kun San Wanda ke bariki ba a raba shi da sata) dubu dari da hamsin ya qirga casss, ya zamana ya saci dubu dari uku da hamsin kenan, yana gamawa sai ya barbaza kayan wajen ya koma ya haura Katanga ya koma asibitin,yana zuwa ya biya komai da ya Kamata ya biya har ya samu na abinci da zasu ci, gida ya koma dan ya yi wanka ya d'an huta Kuma tinda Iya bacci take, ko da ya kammala duk abinda zai yi se ya kashingid'a da niyyar zuwa bayan isha'i se ya koma asibitin,bacci ne mai nauyi ya ɗauke shi ba shi ya farka ba se subahi tsabar gajiyar da ya kwasa.
Kwanan Iya biyar a asibiti jiki yayi sauƙi ta murmure, dan haka likita yace musu a yau zai sallame su, Iya na Jin maganar Sallama ta hau kuka ta na fad'in ita su bar ta a wajen su kawai kar a bari Sahabee ya Maida ta gida, kowa a wajen ya tausaya mata sosai dik da cewar basu san menene tsakanin su ba, ba yanda za su yi dole hakuri suka bata Sahabee yazo da yamma suka koma gida.
Tinda suka koma gida sai ya rage mugun hali ya ɗan fara kulawa da ita,dan kuwa watarana har yakan sai mata madara ta leda guda d'aya da bread yankan nera ɗari, sai ya dafa mata ruwan lipton ya sa mata sigan ashirin a ciki, shi kuwa kafin ya wuce aiki zai je wajen mai shayi ayi masa had'in kauri yaci ya sha ya ƙoshi.
A haka rayuwar Iya da Sahabee ta ci gaba har kud'in ya tasamma qarewa, a wajen aikin shi kuwa da fari sun zaci shiga aka yi akai sata, saboda samun wajen da suka yi a b'alle,sai da bincike yayi bincike suka gane cewar Sahabee ne ya yi satar.
Wata ranar talata suna zaune shi da Iya yana ta mata masifar ta yi fitsari a zaune, dan kawai bata jin dad'i ba zata qwarara jikin ta ba ta isa bayi sai ta saki fitsari a zaune? da anyi mata magana kuma tace qafa ke matsa mata,waye qafarshi bata ciwo amma haka yake tafiya bayi sai ita? Hawaye kawai take zubarwa tana jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu dan baƙin cikin sahabee ya ishe ta,yana nan yana sababi aka hau k'wank'wasa ƙofar gidan nasu, Sahabee ne ya miqe dan zuwa ya ga waye yake musu bugu kamar ya basu ajiya, dan shi ya riga ya cire ran waccan gantalalliyar zata dawo gare shi ma shi yasa ko neman ta baiyi ba, shi se yanzu ma yake danasanin auren ta da yayi dama haɗuwar bariki ta gaji haka,tafe yake ya na ci gaba da masifa har ya isa qofar gidan, a jingine da qofa yaga shugaban wajen aikin su da ƴan sanda biyu,wani tsallen bad'ake ya yi zai juya ciki a guje suka ko yi ram da shi, ihu yake yana fad'in,
"Ku yi min rai sharrin talauci ne ya sa na tab'a maku kuɗi amma zan biya ku ba sata nayi ba aro ne, kunga mahaifiyata ita ce ba lafiya na deb'o na ke mata magani dasu."
Ba wanda ya kula shi suka tasa ƙeyar shi gaba suka saka a mota, Iya na kuka shima yana yi, hakuri suka bata dan ba zasu iya yafe masa ba,bayan tafiyar su kuwa Iya ta sha kuka kamar babu gobe, ko ba komai mutum rahama ne, sannan hannun ka baya taɓa rub'ewa ka yanke ka yar in ji bahaushe. Kan dole ta hakura ta yi shiru, ga shi ita bata taɓa ma shiga maƙotan ta ba balle su san da zaman ta su taimaka mata, matar Sahabee duk ta gama sawa an tsani gidan nasu ba mai son su a unguwar kaff, haka Iya ta koma rayuwa ita d'aya da safe ta ja jiki ta yi bara a qofar gida har ta samu na siyan abinci, da yamma ma ta fita qofar gida ta zauna, in duhu ya fara ta ja jiki ta kulle gidan ta ci abinda ta samo ta yi sallah ta shige daki se Kuma wata safiyar.
***************************
Sauran kwana biyu a kai Amarya Eamaan d'akin ta, wasu daga cikin ƙawayen ta da suka yi makaranta a baya tare ne suka shirya dan zuwa bauchi, ciki har da babbar ƙawar ta Aisha,Yayah ma ta samu zuwa bauchi dan kuwa tace wannan karon ba zata yi missing bikin Eamaan ba.
Eamaan tayi wani irin kyau na musamman fatar ta har wani santsi da sheƙi take yi kamar wadda aka wanke da inji, ga wani irin mayen qamshi me kama jiki da take yi, gashin ta kuwa ya sake cika da tsaho kamar wanda ake bawa taki,Eamaan ta maida kayan fruits abincin ta,madarar shanu, zuma,da sauran kayayyaki masu gina jiki,in zata yi wanka sai an saka ruwan lalle a ruwan wankan nata da madarar turare.
Ranar kai amarya kuwa Hafsat Yayah da ƙawayen amarya sun shirya angwaye kawai suke jira dan su rankaya garin kano kai amarya ........
[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 27:
Yayun amarya da qawar ta Aysha sun gama shirin su tsaf dan dawowa da amarya garin kano ta dabo tumbin giwa,tafiyar awanni hud'u da minti arba'in ne ta iso da su har qofar gidan su Eamaan d'in, Wanda ta kula da shige da ficen mutane a gidan nasu,har hakan ya tuna mata da lokacin auren ta na fari, a wancan lokacin ma haka aka yi taron mutane sosai a gidan nasu, wannan karon bata zaci zata ga kowa ba duba da yanda auren nata ya zo da Kuma cewar ita fa yanzu bazawara ce ba budurwa ba, wanne taron mutane Kuma za a yi?
Anwar bai san da dawowar su ba, da ace ya sani to fa ba makawa sai ta ganshi a ƙofar gidan nasu,direct d'akin su suka nufa suka yada zango dan huce gajiyar da suka kwaso, sanin cewa amaren na tafe ne ya sa aka tanadar masu abinci da abin sha, Hafsat da ke Jin yunwa ce ta zuba masu ita da Fatee suka fara ci, a can tsakar gidan kuwa cike yake da 'yan biki mata, gaba d'ayan su mamakin taruwar mutane da yawa suka dinga yi, Yaya ce ta katse masu tinanin su ta hanyar cewa,
"Kun San yanzu fa aure ne za a yi na soyayya, aure ne za a yi Wanda tin fil azal dangi shi suka zaci zai faru, duba da cewar kowa ya San soyayyar dake tsakanin Eamaan da Anwar d'in to kuma qaddara ta riga fata, dole kuwa yanzu ku ga dangi ko ta Ina"
Su Kan su su Ammaah da Maman sun yi mamakin cikar dangin nasu, saboda ba su yi gayyata ba, sun dai Sanar da daurin auren Eamaan da Anwar d'in, saboda dangi su sani, se Kuma suka basu mamaki da zuwa, 'yan uwan Mama sun ce dole ne a yi yinin biki, ba ruwan su da Wani auren bazawara ne, mijin ta ai saurayi ne.
Shagalin biki kuwa ya kankama, Eamaan ta yi mamakin ganin uban lefen da aka kawo Daga gidan su Anwar, se Daga baya ta yi murmushi ta tabbata Anwar be tab'a cire ran zai aure ta ba, maqota da abokan arziqi an tsattsaya ganin lefen da ya ba wa kowa mamaki, akwati seti d'aya da rabi kowanne kalar shi daban, Goggon Anwar ce ke musu bayani, seti d'aya ango ne ya yi abun shi tin da jimawa ya aje, Rabin setin kuwa uwar ango ce ta yi shi, kowa ka kalla fuskar shi d'auke take da annashuwa da annuri.
Bayan su Eamaan sun huce gajiyar su ne su Kai shiri da yamma dan zuwa gidan Iya,Eamaan Hafsat Yayah da Fatee ne zaune a mota Yayah na tuqa su, sai da suka tsaya a Wani shago Eamaan ta yi musu tsaraba, duk Wani abu da Iya ke so se da ta siya mata dai-dai misali, sannan ta qara da d'an abubuwan ci da sha suka ci gaba da tafiya,da kwatance da tambaya aka kaisu har gidan Iya, tana kwance jikin nata ya motsa, maganin ta na hawan jini ya qare, ga ba kud'in siya ko da da kud'in ma wa zai siyo mata sahabee baya nan? Duk tayi kashi da fitsari a inda take kwancen a tsakar gidan, jikin ta ya yamushe ta rame kamar ba ita ba, cikin ta sai qara yake saboda yunwa Dake addabar ta,kwance kawai take bata san ina kan ta yake ba.
Ko da suka yi ta doka sallama suka ji shiru sun so su juya, a tinanin su ko wrong address ne aka basu,wata yarinya ce data nuna musu gidan ta basu tabbacin nan ne gidan, tsohuwar gidan na ciki yau kwata-kwata basu ga ta fito bara ba.
"Bara Kuma? Wanne irin bara, Iyan ce ke bara Kuma Ina Sahabeen?"
Inji Eamaan da kalmar barar ta gigita ta.
"Ai 'yan sanda sun kama shege, ya ishi kowa a unguwar nan da neman matan tsiya, matar shi kuwa bata da mutunci kwata-kwata bata raga wa kowa, to qarshe ma na ji ana cewa ta gudu ta bar shi, shi Kuma 'yan sanda sun tafi da shi shekaran jiya"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,"
Tini hawaye ya fara zarya da rige rige a kuncin Eamaan a hanzarce ta afka gidan, ganin Iya a yashe a qasa cikin Wani mawuyacin hali ne ya Sanya ta qarasawa a guje ta tallabi Kan Iyar ta Dora a cinyar ta ta na kuka ta na Kiran sunan ta, Iya da ke kwance magashiyan bata San wake Kan ta ba, sai qoqarin bude ido take amma ta kasa, haka dai Yayah da Eamaan suka d'agata daga qasan, Eamaan tana kuka sosai ta ke gyara mata jikin ta, jallabiyar ta data dora akan atampar ta ta cire ta nade Iya a ciki, ta ce ma Hafsar ta taimaka ta siyo mata pure water ,domin kuwa Eamaan ta kula farkon abinda ya Kamata su fara yi wa Iyar maganin shi a wannan lokacin shi ne yunwa, dan yanda cikin ta ke kukan yunwa abun ya ba su matuqar tausayi,yau ko me Sahabee ya yi a ganin Eamaan ya Kamata 'yan sandan da suka kama shi su tausaya musu, Hafsat na tsaye ta na jinjina irin tausayi na Eamaan.
Fita ta yi ta siyo ruwan roba ta kawo ma Eamaan d'in, shayi Eamaan ta had'a mata da ruwan pure watern da Kuma kayan tea din da ta yo mata tsarabar su, Eamaan ta hau d'ura wa Iyan a hankali, Wani ya shige Wani ya dawo, a haka ya qare,sun Kai kusan minti biyar zaune kafin Iya ta fara bude ido, tana juya shi a hankali, Eamaan na zaune a qasa Kan Iya na cinyar ta, cike da tausayawa take kallon Iyar se take ganin Bata kyauta wa Alhaji ba da ta bar mahaifiyar shi a wulaqance haka, to amma ba laifin ta bane, Bata San haka abun yake ba da ta taimaka musu.
Iya na fahimtar a saman cinyar wa take sai ta fashe da Wani irin kukan da ya sa Eamaan ma fashewa da kukan tausayin Iyan, ba komai ke sake Sanya ta kuka ba face ganin wai yau ace mahaifiyar Alhaji Abdullahi ce anan, kuma take a haka cikin mawuyacin halin jinya da talauci,yanda ya rayu ya na gatan ta mahaifiyar shi da kula da ita, gashi yanzu qanin shi da be San darajar ta ba Yana wulaqanta ta, Allah ya wa Alhaji rahama ko Dan yanda ya rayu ya na kula da mahaifiyar shi.
Tun Eamaan na yi wa Alhaji addu'a a zuci har ta fito Fili yayunta na amsawa da "Ameen" kafin Yayah ta dafa kafad'ar Eamaan d'in ta ce mata
"Kukan ya Isa haka dear ,ya kamata mu zo mu tafi dare nayi, mu miqata asibiti,dan wannan da gani ba yunwa bace kad'ai matsalar ta har da rashin lafiya,in yaso bayan an gama walima goben mun je asan ya za ai da ita,ni na maki alqawarin zan sauya mata gida zan aje mata wadda zata kula da ita,Ina ga ai hakan yayi ko?"
Gaba d'ayan su sunyi na'am da shawarar ta, nan suka dauke ta suka ja qyauren gidan, suka tafi da ita asibiti suka damqa a hannun kwararrun likitoci Dan mijin Yayah sanannen d'an siyasa ne da ake damawa da shi, transfer na kud'in da za a kula da Iya ta yi wa asibitin suka fara Shirin komawa gida, Eamaan kuwa zuciyar ta ta karaya ji take kamar kar ta tafi, zuwa ta yi wajen Dr. ta masa magana akan ya taimaka a ba wannan tsohuwar kulawa ta musamman, tabbaci ya bata akan kar su damu, za a kula da ita kamar yanda ya Kamata, a gaban ta ya kira wata nurse mai kamala ya damqa komai hannun ta sannan suka bar office din Dr. d'in, akan da safe zasu dawo.
Jaka Eamaan ta bude ta zaro kudi ta bawa Nurse d'in tace ta sai wa Iya kayan shayi, da Duk abinda zata buqata tana so a bata kulawa sosai, kar a barta da yunwa, ta dinga bata abinci ta ci ta qoshi, sauran canjin ta riqe, godiya ta mata sannan suka tafi, Yayah ce ta ke Jan motar ita ko Eamaan na gefe idon ta a rufe, tana ta tinani kala-kala ,a haka suka isa gida jikin ta ba kwari.
Washe gari da sassafe ta je kitchen da kan ta, ta haɗawa Iya kunun gyaɗar da ta saba haɗa mata a da, abokan wasan ta na ta mata tsiya, murmushi kawai take ba ta iya mayar musu,ta na gama kunun ta mata ferfesun kaza ya ji kayan qamshi ya nuna sosai ya yi luguf ,ta dora mata da bread mai laushi, ta saka a food flask, se da ta ga ta kammala komai sannan ta shiga wanka ta hau Shirin fita, ta gama shirin tafiya kenan Ammaah ta shigo,
"Ni kuwa Baki fad'an ya kuka samu su Iya ba jiya, Kun dawo Ina tare da mutane ban samu na tambaye ku ba"
Kwalla ce ta taru a idon Eamaan ta samu waje ta zauna a gefen gado, Ammaahn ma zama ta yi a gefen gadon tana bin Eamaan da kallon son Jin me ya faru a jiyan.
Cikin sharar kwalla ta fad'a mata abinda ya sami Iya, da inda suka kaita a jiyan, shine yanzu take son ta je ta gan ta, Ammaah ta jinjina wa d'iyarta ta da zuciyar tausayi,rungume ta kawai ta yi da fari bata San ma me zata ce ba kawai se ta hau shafa bayan ta, sun dan jima a haka kafin ta samu bakin magana,
" Allah yayi miki albarka Eamaan,ni dai a wannan lamarin zan iya qaryata bahaushe da ke cewa albasa batai halin ruwa ba, dan kuwa ni dai tawa albasar tayi halin ruwa a nan har ma ta fi yanda ake zaton ta,ana fad'in kyawawan halaye na Ina ganin anya haka nake? To Eamaan ke har kin fini kyawawan halaye ma, Allah ya qara maki imani, da tsoron shi, ina son ki Eamaan,Allah ya miki albarka da ke da zuri'ar ki da sauran yaran musulmi dika"
" Ameen Ammaahna nima ina son ki da yawa,"
Murmushi suka yi a tare sannan Ammaah ta share wa Eamaan hawayen ta,tare da miqa mata hijab din ta, Eamaan komawa kitchen ta yi ta dauki food flask da Kuma flask din ruwan zafi da ta zuba kunun ta zuba su a Wani basket na d'aukan abinci, sannan ta koma dakin su ta zauna tana jiran Hafsat ta dawo daga dakin Mama, dan da ta shiga nan toilet din nasu Dan wanka se ita da Fatee suka tafi na Mama,kafin su zo ta kira Anwar ta labarta masa komai, sannan ta bashi hakuri jiya ta fita ba da izinin shi ba, gashi yau ma suna Shirin komawa asibitin, nuna mata ya yi Babu komai, in da abinda take buqata ma ta Sanar da shi, in Kuma ya zo ya Kai su ne ma Duk se ya fito, da sauri ta dakatar da shi Dan Bata son abinda za a ga rashin kunyar ta Kuma, ta na zaune bayan ta gama wayar ne su Hafsat suka shiga suma sun kammala shirya wa se kawai suka fita mota suka wuce asibiti.
Suna isa suka tarar da Iya sai kuka take tana ba ma'aikaciyar da Eamaan ta sa ta kula da ita labarin Ƴan sanda sun tafi da Sahabee, jiya wasu suka je gidan ta suka mata wanka, bata san ko su waye ba, da sauri Eamaan taje ta kama hannun ta dika da take ta wurgawa a iska tana bayani,
" Iya nice Eamaan kin manta ne jiyan har ki ka kalle ni ki ke kuka, Iya ni ce Eamaaniin ki, ga Fateema ta zo ta gan ki Iya, jiya ita muka je kai miki amma se muka tarar da ke a cikin mawuyacin hali,se muka kawo ki nan,"
Qanqame hannun Eamaan Iya ta yi, ta fashe da kuka, ta kasa magana sai kuka,hakuri ta dinga bawa Eamaan, Eamaan ta nuna mata ba komai, komai ya wuce, labarin rayuwar da sukai da Sahabee da matar shi Iya ta ba wa Eamaan, da kuma yanda ta na zaune 'yan sanda su ka zo suka tafi da Sahabeen ta,ita kuma tana zuba mata abincin ta na sauraron ta tare da jimanta lamarin,sosai Eamaan ta tausaya wa Iya rayuwar da ta yi ,Sahabee kuwa can ta matse masa ai shi ya ja wa Kan shi rayuwar wahala to se ya ci wahalar shi shi kad'ai d'auke Iya za ta yi Daga wajen shi.
Ko sisin ta ba zata saka dan fidda shi ba, in ya dawo yana buqatar tsohuwar shi ga ta nan, amma ita da shi ko a hanya ba ragowa, shida ko mutuncin kanshi bai sani ba balle na wani? baiwa Iya kunu ta fara yi,Iya kuwa cikin sauri ta shanye cup ɗaya, tausayin ta ne ya qara kama Eamaan, Hafsat kuwa dariya ce ta kama ta ta kauda kai tare da shanye dariyar, naman Eamaan ta dakko ta yi ta zare mata qashi tana bata a Baki,sai da ta ga Iya ta qoshi ta Kai geji sannan ta kyale ta.
Iya da ta ji cikin ta ya d'auka ta kalli Hafsat da ke d'auke da Fatee ta ce,
" wannan itace jikallen tawa? Taho wajen kakar ki Fadhimatu kin ji"
Maqale kafad'a Fatee ta yi, Eamaan ta dauke ta zata miqa ma Iya ita ta tsanyara kuka tana kiran Daddyn ta,mamakin ta ne ya kama Eamaan da Hafsat wannan shi ake Kira da sabon salo, sarai sun gane wa take nufi (Anwar)
Iya ce ta share kwalla tace,
" ku kyale ta banga laifin ta ba, laifin mu ne da tun da bamu neme ta ba, dan yanzu ta qini ba laifi bane,"
Eamaan ce ta ji tausayin Iya ya ratsa ta,
" Iya dan Allah ki dena tuna baya komai ya wuce, sannan ina so in Sanar da ke yanzu in sun sallame ki zamu tafi dake gidan mu, na sake yin aure cikin satin nan, yau ne walima in Allah ya kaimu anjima da yamma da dare Kuma zan tare, in an kwan biyu kuma zamu koma bauchi da zama ni da mijina, ko da ace har aka sallame ki baki qara gani na ba,Iyayena da Yayah Babba zasu kula da ke, dan kuwa ko ba komai ni da Alhaji mun zama d'aya,Kuma mutuwa ce ta raba mu ba Wani tashin hankali ba, sannan kuma ke kakar Fatee ce dole mu girmama ki mu kula da ke"
Iya kam kunya ta gama baibaye ta, ta yi kukan har ta gaji, Hafsat ce ta fada ma Eamaan cikin harshen turanci akan taje ta ga likita ta ji ko za a iya Basu sallama a yau d'in se su tafi da ita kawai,haka akai kuwa, aka rubutawa Iya sallama da magunguna na hawan jinin ta suka tafi.
*****************************
Sahabee kuwa na can wajen 'yan sanda sun bar shi a cell ba a miƙa shi kotu ba ƴan duniya suna casa shi kamar masara a turmi,ihu kawai yake yana faɗin,
"Waaaayyoooo officer dan Allah ku ma wannan qaton magana ya daina kirbata kamar ya samu kub'ewa, wayyo Allah, na wayyoo Allah na,"
"Ba zaka rufe min baki ba,nace za kai shiru ko sai ka ci uwar ka, ai dama na gaya maka tin a alaba rago zamu had'e ne watarana, ga shi mun had'u, ka manta yanda kai kutun-kutun ka rabani da dadiro na sannan ka dawo ka aure min yarinyar da na yi niyyar aura, ka min asara Kai ma ai ga shi yanzu ta gudu ta barka kana cin kwakwa,"
Dariya suka d'auka gaba d'aya 'yan wajen, dan yanzu sun fahimci me yasa ogan nasu da suke Kira da Mugu ke ta jibgar shi tin da aka kawo shi dukan safe daban na dare daban, su kuwa ma'aikatan wajen dama suna tsoron mugu, dan costomer ne an Saba kawo shi, duk jikin Sahabee ba inda baya ciwo ya yi tsami sosai, ga targad'e da ya samu a hannu, ya daku iya dakuwa,Duk ya Wani bushe ya qara qobarewa, in an kawo wa mutanen wajen abinci cinyewa suke ba me sammasa,da fari har ya amsa laifin shi da bakin shi, da Jin an ce ya biya kud'in ya dawo ya ce ba shi bane, an kad'a an raya ya ce ba shi bane, a tunanin shi in yace bashi bane za su hakura su kyale shi, in kuwa suka ce ya biya da shekarun shi ze biya? Me ya ajiye ? Wannan ne dalilin da ya sa suka ki miqa shi kotu suka aje shi anan, in ya wahala ze amsa laifin shi,ma'aikatan wajen ba Wani abincin kirki suke bashi ba, in ma an bashi ya na fara ci Oga Mugu da yaran shi ke amshewa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 20